Showing 51001 words to 54000 words out of 54699 words
Chapter 18 - Mukaddari Ne Daga Allah Complete Hausa Novels By Suhaima Abubakar Shehu.txt
motsi baiyi ba...........
___jijiga shi tafara yi tana masa magana akan yatashi amma kuma shuru babu alamun ma ya jita hankalin ta yatashi sosai tarasa yadda zatayi dan taga ya tashi amma kuma inaa shuru ne ai kuwa ta fashe da kuka mai cin rai da tashin hankali sai suru rai takeyi tana sumbatu tana fadin nashiga uku na ina zan saka kai na mai yake faruwa da miji na yanzu yana lapiya kalau amma kuma gashi nan babu alamun numfashi ajikin sa wayyo Allah na nabanu na lalace Allah kai ne gata na kashiga cikin lamarin wannan bawan naka kuka take sosai kamar babu gobe zama tayi a gurin bata ko iyace komai kukan ma yanzu ta dai na sai zuba masa idanuwan ta da tayi,
A haka suka wuni tana zaune agaban sa ta zuba masa idanuwan ta tana kallon sa babu ko kiftawa rayuwa kenan kana naka shi kuma Allah ya kama nashi ɗazo fa Khalil lapiyan shi kalau har yana fadawa Bintu sa kamamai masu dadi amma kuma yanzu gashi nan shi kamar gawa akwance babu ko motsi atattare dashi oh Allah
Alili tun ɗazo gaban sa sai faduwa yakeyi kamar dai wani mummunan abu yafara haka yake ji ajikin sa kuma gashi tare da Kaka lapiya kalau sai firan su sukeyi mikewa Alili yayi ya dubi Kaka yace "Kaka zan je na duba Khalil na jisa shuru kuma yace mun zai zo muje wani waje dan haka zan je na duba sa, da to kaka ya amsa masa shi kuma Alili yayi gidan khalil, sallahma ya ringayi acikin gidan amma kuma shuru babu wanda ya amsa masa dan haka ya kusa kan sa cikin gidan a tsakar gida ma yana ta sallama amma shuru tsoro ne yasake shiga cikin zuciyar sa kardai wani abu ya faru dasu dan haka ya yanke shawaran shiga cikin ɗakin ai kuwa yana shiga yagan su a kwance kamar babu rai ajikin su, gaban sa ne yayi mummuna faduwa yayin da yasake zuba musu idanuwan sa akan su dan ya kara tabbatarwa kan gadon drect ya nufa yafara duba Khalil idanuwan sa duk sun kafe yayin da kuma wani farin ruwa mai warin tsiya yana fitowa daga cikin bakin sa, araza ne Alili ya fara jijigashi amma kuma babu wani alamun motsi atattare dashi ari kice yayi kan Bintu dan ya dubata amma itama a sume yasa meta rasa yadda zaiyi yayai tashin hankali wanda ba asaka mata rana rayuwa kenan ai da gudu Alili ya fita agidan drect gida ya nufa dan yasanarwa Kakan sa cewa fah Garkuwan su da kuma Bintu baki dayan su sun mutu, a mungun firgece yashigo gidan sai sauke numfashi yakeyi yayin da kuma hawaye sai fita daga cikin idanuwan sa suke yi sai nuna hanya yakeyiwa Kaka yana sauke numfashi,
Kaka kama hannun sa yayi ya zaunar dashi ya dauko ruwa ya kafa masa abaki sai da yashanye tass kafin Kaka ya dube sa ya fara magana to yanzu nutsu kamun bayani yadda zan fahimce ka kafadamun mai yake faruwa har kunce yadda zakuje din kai da Garkuwa mai ya faru acan din kadawo kana haki haka, fashewa da kuka Alili yayi yana furta gabaki dayan su sun mutu basu motsi basu numfashi sun tafi sun bar mu, kaka yace nifa ban fahimce abunda kake cewa ba kayi muna magana ta fahim ta waye suka mutu waye suka tafi suka barmu Alili da hawaye ya gama cika masa idanuwan sa sai zubowa suke kan kumatun sa ya furta "Kaka Garkuwan mu da shi da Bintu dukan su , sun mutu babu wanda nasa mu acikin su suna numfashi,
Tashin hankali wanda ba'a saka masa rana Kaka yace kamar ya sun mutu bayan yanzu suka bar nan Allah sarki Kaka tsabar ruɗani ya matan ikon Allah akan bawan sa, Alili yace wallahi Kaka basu numfashi, Kaka bai tsaya sauraran suba yabar gun kai tsaye ya nufi gidan su Khalil yana tafiya yana hada hanya babu wani nutsuwa a jikin sa duk wanda ya kalli Kaka sai yasan yana cikim tashin hankali sosai, Alili yabi bayan sa,
____________A firgi ce Kaka ya shiga cikin gidan ko sallama babu kai tsaye ɗakin yayi ganin su a kwance ne yasa shi da fa bango yana jin jiri-jiri yana ɗiban kan sa idanuwan sa kuma sunyi jaa lokaci gudu tsayawa yayi dafe da bango kusan mintuna kafin yayi kan Khalil da yake kwance kamar gawa jijigashi ya shikayi yana ambaton sunan sa amma kuma ina babu alamun zai farka Kaka komawa yayi kan Bintu itama yafara jijigata shuru itama zama yayi yayi shuru ya zuba musu idanuwan sa da gabaki dayan su, sunyi jaa sosai ko kiftawa bayayi, Alili ne yashigo ɗakin ganin kakan sa yayi zaman dirshin yasa shi wani irin razana sosai zuciyar za sai bugawa takeyi kardai mutuwa sukayi dagaske, ganin kakan sa babu wani abun kirki dazai iya ne tunda yana cikin rudani yasashi tunkaran wajan mai gari dan yasanar masa abunda yake faruwa ko Allah zaisa yataimaka masu,
Sauri-sauri har yana hadawa da gudun sa dan ya isa gurin mai gari shima kan sa Alilin karfin haline kawai amma zuciyar sa zafi take masa sosai, afigice ya isa gun mai gari sai sauk numfashi yakeyi na huci zama yayi ya fara zai yana masa duk abunda yake faruwa bayan mai gari ya gama saurara ne yasaka liman yayi masa jagora izuwa gidan Khalil din, liman da Alili suka dau hanya sai gidan Khalil yadda Alili ya tafi yabar Kaka haka sukazo suka samai sa a yadda yabar shi, liman ganin duk karfin zuciya irin na Kaka a irin wannan halin sai da jikin sa yayi sanyi mutum mai yarda da kaddara duk yadda tazo masa mutum min da yake fadawa mutum idan wani abu yasa mu bawa tofa tabbas wannan MUKADDARI NE GADA ALLAH amma yau shine a zaune haka, gyra zama liman yayi ya fara raira karatun alkur ani mai girma sosai yake karanta suratun bakara, a hankali-a hankali kuma kaka nutsuwa tafara shiga jikin sa ya fara sauke numfashi sai da nutsuwan sa ta dawo jikin sa kuma sai yafashe da kuka yana magana cikin kukan sa, "wannan yaron ya gara jarabawa a rayuwar sa shikam haka Allah ya kaddara masa naso wannan bawan Allah aje tunanin sa yadawo ya je wajan iyayan sa dan nasan suna matukar mukatar sa amma kuma haka Allah yatsara abun sa wannan yaron bazai koma cikin dangin saba, rayuwa kenan Allahu yajikan ka Allah yama rahama, liman ya amsa da amin yayi da Alili kum hawaye yagama wanke masa fuskan sa,
Mikewa liman yayi ya nufi gun da Khalil yake yafara kokarin fara masa addu'an mamaci kafin kuma asalla ce sa akai sa gidansa nagaskiya kawai idanuwan sa ya sauka akan yatsan Khalil ya yake ta motsi yana ai kuwa da sauri yake furta bai mutu ba yanan da ran shi ai daga Kaka har Alili awani figice suka mike suka nufi gun Khalil suka fara jijigashi suna magana suna murmushi tare da sauke ajiyar zuciya duk da halin da Khalil din yake amma sunji dadin ganin shi yana raye wannan yayi matukar faran ta musa, Alili ya dube Kaka yace Kaka yakamata mukai sa asibiti Kaka ya dube sa yace "kana ganin wannan jinyar ta asibiti ne aa wannan jinyar bata asibiti bane daukan sa zamuyi muje gida amafara masa jinya har Allah yasa yasamu lapiya,
A figice Baffah yashigo gidan yana ambaton sunan Bintu Bintu sai asanan Kaka ya tuno da Bintu datake kasa itama kamar wanda rai yayi halin sa, ai da sauri Kaka ya nufi gun da Bintu take ya dauko ruwa ya watsa mata a fuskan ta dagon ajiyar zuciya tasauke amma kuma idanuwan ta suna rufe bata bude ba ida dai fatan ta Allah yasa mafarki take, Baffah kanta yana nufa hawaye idanuwan sa yana jijigata akan ta tashi amma kuma Bintu idanuwan ta arufe suke gam, Kaka ne ya bada mumar ni akan su dauke su sukai sa gidan su haka kuma akayi gabaki dayan su suka dauki su sai gidan Kaka,
Bayan ankai su Khalil gidan Kaka agashiga masa magani sosai amma kuma babu wani cigaba Bintu na batsa dantse wajan kula da mijin ta Alili da Kaka su suke kai Khalil toilet Bintu kuma ta masa wanka kullum Bintu ita take mamatsa jikin mijnta tare da masa addu'oi yau kimani wata guda kenan amma har yanzu babu wani jigaba mutanin kauyen guma kuma ko albaracin bakinsa yake fada akan jinyar Khalil yayin da Bushar yake cikin farin ciki da labari yasame sa har yafara shirye shiryen raba Khalil da Bintu da kawai yaga ya aure ta,
Kaka yau da sassafe ya nufi daji dan nimo maganiwa Khalil duk maganin da yashafi na tsihiri sai ya nimo anyiwa Khalil amma kuma har yanzu abun daya ne shine babu wani cigaba a tafiya nimo magani,
Kwanaki na tafiya lokaci kuma yana shudewa yau takama Khalil yana da wata uku akwance yayin da cikin Bintu kuma wata hudu da kwana uku jikn Khalil sai gaba-gaba yakeyi babu wani sauki a tattare dashi dan haka Kaka yasake shiga cikin wata duniyar tunani ganin yamuwar lapiyar Khalil, amma har yanzu shuru, Kaka yasamu Baffah da magana akan Bintu akan ko zata dawo gida ne tunda ba ita daya bane yanzu kuma tana shan wahala sosai, Baffah yace to muji ta bakin ta, haka kuwa akayi suka saka Bintu agaba da magana nan akan ko zata koma gidane dan ta huta saboda cikin jikin ta, ai kuwa Bintu ta fashe musu da kuka mai cin rai tana cewa ita fa abarta tayi jinyar mijin ta babu wani abunda zai sa arabata da mijin ta jin hakan ne yasa Kaka da Baffah suka barta suka kuma saka mata albarka,
A hausa sukace dare ma hutun bawa amma kuma ban da kaka dan yanzu zaune yake yana tunanin maganin da baiyiwa Khalil ba tunini ya tsuguba ciki amma kuma har yanzu shuru babu wani abunda yasamu, tashi yayi yayi sallah bayan ya idar kuma ya fara zubo addu'a na samun lapiyawa wa Khalil yashafa ya kwanta,
Cikin barcin kaka yayi mafarkin khalil yasamu lapiya sanadiyar wani ganyen bishiya afirgice kaka ya tashi duk zufa ta wanke masa fuskan sa zama yayi yana tunan mafarkin sa tabbas yasan wannan bishiyar amma kuma zuwa gun ta akwai hatsari sosai dan haka washigari da sa ssafe ya kira Alili da kuma Bintu bayan gabaki dayan su sun zauna yafara zaiyana musu duk mafarki n da yayi jiya da dare shuru yayi bayan yagama fada musu, Alili yace Kaka muna jin ka kuma kayi shuru Kaka ya gyra zaman sa kana ya dan numfasa ya daura dacewa wannan bishiyar akwai hatsari zuwa gunta Alili yace wata irin matsa kuma Kaka, kaka ya numfasa kana ya daura idanuwan sa akan Alili yace idan bazaka manta ba lokacin da zaku dauko bulala na fada muku akwai hatsari sosai a cikin wannan dajin har nake fada muku hanya uku ne daya wannan hanyar zallan mayu ne masu cin naman mutani, dayan hanyan kuma sai mace ce kawai zata iya bi to wannan bishiyar a cikin wannan hanyar take kuma kaga babu wata mace da zata iya bi, Bintu datake hawayen farin ciki tace kaka ni fah mai yasa bazan jeba bayan kuma mijina ne bashi da lapiya, Kaka ya dube ta yace Bintu bazaki iyaba saboda cikin da yake jikin ki kuma wannan dajin idan anshiga babu wagen baya duk wanda yashiga wannan hanyar tofa tabbas bazai waga bayan saba sabda mutuwa akeyi duk wanda ya waiga bayan sa dan haka ke bazakije ba,
Fashewa da kuka Bintu tayi tana roko Kaka akan yabar ta taje dan babu wanda zai iya zuwa idan ba itaba dan haka dan Allah Kaka barni sosai Kaka yaji tausayin ta ya kuma numfasawa yace ni bazan ce komai ba sai naji tabakin mahaifin ki dan haka anjima zanje nasame sa dan gurin akwai hatsari sosai, da to Bintu ta amsa masa dan tasan Baffahn ta zai bar ta
Kaka yace yasamu da Baffah da magana nan bayan sun gama gaisawa sai yasanar masa abunda yakawo sa kuma ya fada masa duk yadda sukayi daBintu bayan Baffah yagama sauraran sa sai ya numfasa kana yace ai nikam babu wata damuwa Allah yasa tafiyar ta yazamu silar warakan sa, Amin kaka yace kuma yaji dadin abunda Kaka ya fada masa bayan sun gama tattaunawa kuma suka yi sallama kai tsaye gida ya nufa yasanarwa Bintu duk abunda suka tattauna dan haka Bintu ta haushirin tafiya dan nimawa sahibin ta lapya.........
Bintu tashirya tsaf dan zuwa wannan dajin dan nimowa mijin ta magani Kaka Alili sun mata fatan alkhairi da fatan nasara, Bintu nufar hanya tayi ita dayan ta ga ciki a jikin ta tana tafiya tana addu'a cikin zuciyar ta,
Har Allah ya iso da ita lapiya hanyar da Kaka ya fada mata shi tayi tafiya take babu waye-waye kuma dama kaka ya fada mata bishiyar ita daya ce atskar dajin gabaki daya Bintu a tsorace take duk addu'an da yazo bakin ta shi takeyi a gida ma su kaka da Baffah sai addu'a suke matana masha Allahu Bintu tayi nasarar samun ganyan bishiyar kuma ta ciro sa, ta nufo gida kuma tadawo gida lpya tana zuwa kaka ya daddaka maganin yasaka cikin tukunya ya daura akan wuta ya dahu sosai ya hada masa ruwan wanka akayi masa wanka kuma akabashi yasa suka gyra masa kwanciya suna jiran ko Allah zai sa adace,
Har kusan goma na dare Khalil bai farka ba haka Kaka da Alili sukayi sallamawa Bintu suka tafi ɗaki dan dare yayi sosai Bintu bar ci ne ya dauke ta kusan asuba Khalil ya fara bude idanuwan sa yana kara kallon cikin ɗakin Mimi yake furtawa a kasan makoshin sa kina ina kizo kimun magana ko zanji sanyi cikin zuciya ta, Mimi kinsan ina son ki ina son ki,kamar amafar ki Bintu taji muryan sahibin ta da saurin ta ta je gare sa tafara masa magana
"Sadauki katashi? Mimi kitai maka mun abunda Khalil kawai yake fada Bintu fita tayi a ɗakin ta nufi ɗakin da su kaka suke ta sanar musu cewa Khalil fa ya farka ai kuwa da saurin su suka nufi ɗakin samun sa sukayi a zaune ya mike kaffamun sa, yana ganin su Kaka ya mika hanun nuwan sa wakaka alaman yazau gare sa, dasauri Kaka yashe kare sa ya kwantar da kan Khalil a kirjin sa magana Kaka yafara masa"ya jikin ka Allah yabaka lapiya,
Khalil yadago fuskan sa daga kwancen da yake ya dauka akan Kaka yace "Kaka mai yasame ni" Kaka yace rashin lapiya kayi shine kajima akwance amma yanzu komai ya wuce tunda kasamu lapiya sosai Khalil yasake wantar da kansa akan Kaka yace Kaka ina Mimi,
Bintu da hawaye ya cika idanuwan ta tazo wajan sa tace gani gani Sadauki gabaki dayan su suka kwanta akafadar Kaka rayuwa ta musu dadi kuma sunkara jinjinawa Bintu.
.......Sosai kwanaki suke shudewa yayin da wata shakuwa tasake shiga tsakin ma aura ta biyu Khalil da Bintu yayin da cikin Bintu yanzu yana da wata shida aduniya, sosai Khalil yake kula da Bintun sa komai tare sukeyi
Bushar sosai yashiga tashin hankali da yasamu labarin Khalil yasamu lapiya ransa sosai yaɓaci dan haka yasake sabon shiri akan Khalil
Yau garin da zafi aka tashi Khalil ya dubi Bintu ya fara mata magana cikin sanyin jiki dan yau haka kawai yake jin sa wani iri kallon ta yayi yace zan fita Mimi amma zan dawo da wuri kuma ki kulamun da kanki gabaki daya yau jikina wani iri yake mun bana jin dadin jikina dan Alili ya matsamun dole na fito ne da bazan fito ba amma ina zuwa ina gama abunda zanyi zan dawo, Bintu ta ce babu komai Allah ya tsare mun kai ina son ka mijina sosai tamasa addu'a shikuma ya fita,
Khalil yana cikin tafiya yaji ansha gaban sa tsayawa yayi yana kallon wanda suka shagaban sa har Khalil ya bude baki zaiyi magana kawai yaga Bushar a gaban sa, Bushar ya kalle sa ya sake kallon sa bai ce masa komai ba kuma bai furta komai ba kawai suka hau dukan sa da kota ina dukan sa suke babu gaggautawa wani katoton ice Busher ya dauka ya kwadawa Khalil a tsakiyar kansa,
Wari razanana ihuu! Khalil yayi tare da nadi agun sumama me ganin baya motsi ne yasa gabaki dayan su sukabar gun
Bintu tagama koman ta girkin ta tana jiran mijin ta amma kuma shuru babu shi babu alaman shi hakan ne yasa tafara tsoro sosai,
Alili ya jira zuwan Khalil amma ganin baizoba sai ya hada komai nashi ya nufi gida yana cikin tafiya yaga muta ne da yawa sunkewaye wani waje haka yake tazuwa har ya isa gun ya fara tura mutani har yasamu ya kutsa kansa cikin gun idanuwan sa da gangan jikin sa ne sukashiga cikin rudani gani abunda suke gani kamar Garkuwa zuciyar sa bata gama yanke hukunci ba kawai ya tsinka muryan wani daga cikin mutanin yana cewa yauwa ga Alili nan Alili zubawa Khalil idanuwa yayi kamar babu gobe tabbas shine amma kuma waye ya masa duka har haka? kafadun sa wani aciki yataba yace yakamata mukai sa wajan Kakan ka dan zai iya rasa rayuwan sa,
A zahirin gaskiya Alili suke gani amma kuma gangan jikin sa ne kawai a gun zuciyar sa ta jima da daina aiki, ganin Alili yatsaya ne yasa suka dauki Khalil suka nufi gun Kaka dashi wani bawan Allah ne a ciki ya kama hanun Alili suka bi bayan mutani da suka dauki Khalil din
Kaka yana zaune a kofar gida sai yaka mutani sunyi kan sa a tunanin Kaka wani bashi da lapiya aka kawo masa shi dan haka ya meke ya shiga cikin gida ya bude ɗakin dake maganiwa mutani aka shigar dashi bayan sun kwantar da Khalil ne Kaka ya fara ko karin masa magani kawai idanuwan sa ya sauka akan Khalil tsayawa yayi cak yafara tunani amma kuma sai yaga tunani babu wani abunda zai masa kawai sai yafara addu'a yana kuma masa abunda