Showing 21001 words to 24000 words out of 54699 words

Chapter 8 - Mukaddari Ne Daga Allah Complete Hausa Novels By Suhaima Abubakar Shehu.txt

abu mai mahimmanci ne yataso mun dan haka ina fada miki ina fada miki ina fada miki Bintu wallahi karna dawo kauye nan nasamu wata labari dan kin san akan ki zan iya komai innace komai ina nufin komai dan haka kifita harkan kowa kuma nace karki raga wa Jummai wallahi tamiki kimata nafadami dai fatan kingane sannan kuma ina dawowa aure zamuyi babu wata bata lokaci sosai yake mata fada kamar wata yarsa ita kuma sai girgiza kai take amun tana fahimta, wannan tafiyar tayi matukar dadiwa Alili dan sun samu daman da Bintu zatabawa garkuwa lokacinta sosai,


Wata sanyanyiyan shakuwace tashiga tsakanin Khalil da Bintu shakuwa ce wace mutanin kauyen guma suke matukar mamakin ta shakuwace wanda akoda yaushe Khalil yana tare da Bintu ba iya Bintu ita daya ba kowa yana son mu'amala da Khalil domin Khalil yarasa tunanin sa na baya amma kuma gabaki daya abun da yashafi fannin adinin sa babu abunda ya manta, amma asanda yake da hankalin sa yasha babban da haka domin alokacin abaton Allah wahala take masa sosai amma yanzu wai Khalil ne ke yawan yi wa mutani garin nasiha insunyi abunda bai kamata ba Khalil tunanin sa nabaya kawai yamanta amma ta bangaran adini kam masha Allahu,

Yadauki Alili tamkar dan uwan sa wanda suka fito ciki daya dan shi azaton sa ma uwa daya uba daya suke kaka kuma kaka ne agun su, saidai wani abunda yake damun su da Khalil abu kalilan zai sakashi kuka bashida juriya ko kadan ne mutum ne mai saurin kuka da raunin zuciya,


Baffah zaune adakin sa Bintu agaban sa yayin da Khalil agefan sa, Baffah yadubi Bintu yace ina jin tsoron wani abu yasamu yaro nan Bintu yaro nan dake kawai yake sakewa har yayi wa mutani magana ina tsoron Bushar yadawo yasamu labari nan ya illata yaro nan wallahi tun farkon ganina da yaron nan naji hankalina ya kwanta akan sa gashi da adini Bintu dan Allah karki bari wani abu yasame sa, Bintu tace insha Allahu Baffah dama nikam bason Bushar nake ba kawai takuramun yake ni wallahi Alili nake so Baffah, Baffah yace tooo ae Alili akwai hankali insha Allahu zanyi abunda yakamata dan bazan bari amiki auran dole ba, sosai Bintu taji dadi, Baffah idanuwa yazubawa Khalil da yake ta sauke murmushi yana kara matsowa kusa da Bintu girgiza kai kawai Baffah yayi


Inna Jummai ne tashigo gidan babu koda sallama ne magana tafara ke yar tsutuwa fito nan karuwa mai bin maza duk namijin da tagani saita manne masa ae wlh sai kinwaso cikin shege magana take tana daukan muciya dakin Baffah ta nufa tana zuwa kan Bintu tayi tana dukanta da muciya sosai take dukan ta Allah sarki Baffah bai isa yayi magana ba tadawo kan sa,


Khalil kuka yake sosai yana cewa kibari kibar dukan ta kidaena, Inna Jummai ne tajuya tadawo kan sa kai karka sake mun magana dan wallahi yanzu zandawo kanka dan ba imani nake dashi ba, ae kuwa Khalil yafita adakin da gudu yanufi tsakar gida yana y'an dube dube adaidai lokacin da Alili yashiga cikin gidan ae kuwa Khalil bai ko lura da Alili ba yanufi ice dake ci da wuta kai tsaye ya koma dakin shigan shi keda wuya kuwa yazubawa Inna Jummai ice nan mai ci da wuta ae kuwa radadi da zafi lokaci guda yazuraci fuskan ta, bata sanda muciya nan yafadi ahanun taba, magana yafara mata cikin kakauran murya maicike da gargadi wallahi wallahi wallahi Allah dayane daga yau daga yau daga yau karki kara shiga tsafgar mimi dan zan iya komai akan ta dan haka nafadami tare da mikawa Bintu hannun sa akan tazo


Ae kuwa Bintu zuba masa idanuwan ta tayi tana kallon sa yayi matukar burge ta duk da yana gargadin Inna Jummai akan tadaena dukan ta yana kuka yana magana abun yabata mamaki sosai

Khalil kallon Bintu yayi yace tashi mutafi shuru ta tsaya kallon sa shikuma Alili idanuwa yazuba musu yana son ganin yadda zata kare wannan draman,

Bintu kallon hannun Khalil tacigaba dayi bata mika hannun taba, wani uban tsawa yadaka mata saida ta girkiza nace to zuciya ta mutsa, wani uban burkice Bintu ta mike, yatsa khalil yanuna mata ya soma magana.........


Khalil magana yafara mata cikin tsawa da tsantsan bacin rai wanda duk iya tsawon rayuwar sa da Bintu bata taba ganin sa cikin wannan yanayin ba magana yake mata da babban murya MIMI kin san matsayin ki arai na kuwa? kinsan mai aeke nufi da so kuwa? yadan numfasa kana yadaura dace wa bakin sannan yadda nake jinki cikin wannan zuciya tan ba? ko ina miki son da nikaina banayiwa hakui dukan ki akeyi amma ajikina nake jin dukan Mimi yakuma daura da tsawa karshen magana nan sa! amma shine ina miki magana kizo mutafi kina kallo na! Yakarisa magana sa cikin tsawa,

maida duban sa yayi kan Inna Jummai yafaramata magana "wallahi wallahi wallahi Allah daya narantsemiki da Allah daga yau daga yau idanuwa na suka sake ganin kin dauki hannayen ki kin duki Mimi na wallah narantse dawanda raina ke wajan sa sai na yanke hannu idan kuma kina ganin hakan baizai faru ba kikara, "

Yakuma komawa bangaran Bintu yace ke kuma daga yau karna sake miki magana kishare kumakina jina kimun shuru ba amun haka dan haka karki kara wallahi hannun ta yafincika ya jata da karfin da Allah yabashi yafitar da ita acikin gidan, kai tsaye wajan kaka yayi da Bintu Alili bayan sa yabi, yayin da Baffah yayi shuru yafada duniyar tunin da sake-sake acikin zuciyar sa,


Kaka kaka kaka Khalih yake kwala masa kira kaka arude yafito daga cikin daki, arude yana duban Khalil da yake tasoke numfashi kamar wanda aka biyu sa da gudun mutuwa ga kuma Bintu rike da hannun sa , kaka binsu yayi da idanuwa da ko kiftawa bayayi, kariso wajan sa yayi Khalil magana yafarayiwa kaka "kaka ina son ka aura mun Mimi ina son ta bana son rasata kai daya zaka goyamun baya wajan ganin na aure ta babu bata lokaci, " Kaka kallon sa yakeyi cikin rashin fahimta, Khalil kuma ganin Kaka yazuba masa idanuwa yasa shi fashewa da kuka tare da riko hannun Kaka yana masa magiya, "

Kaka yace haba Khalil meye na kuka kuma bayan kasan Kakan ka zai goya maka baya akan dukan abunda kasa agaba ina dai Bintu kake son aura to ka kwantar da hankalin ka insha Allahu zan samu mahaifin ta da maganan kaji sosai Kaka ya kwantarwa Khalil hankali,

Khalil yajidadin maganan Kaka dan haka yace "nagode sosai Kakana Allah yasaka maka da alakhairi Allahu yashiga cikin lamarin ka kamar yadda kafaran tamun Allah ya faran tamaka kakana" sosai Khalil yayiwa Kaka addu'a,

Khalil yamai da idanuwan sa kan Bintu yace Mimina ina daf da samun ki arayuwata Mimi ina miki son dani kaina banayiwa kaina dan haka kije gida anjima zanzo fira dare, Bintu kawai girgiza kanta tayi gabaki daya hankalin ta atashe yake bawai dan Khalil bai mataba bakuma dan Khalil bashi da kowa ba a'a saidan Bushar tasan bazai bar Khalil yasame taba wata kila ma yakashe sa duk tashiga cikin rudani ahaka ta nufi gida,

Zaune suke adakin su dama dakin su daya ne Khalil da Alili, Alili yaduba Khalil yace masa ina son namaka wasu yan tambayoyi, Khalil cikin farin cikin da Kaka yasa shi yace nabaka dama kamun kowata tambaya nikuma insha Allahu zan baka amsa idan nasani,

Alili duban sayayi tare da soma magana ina son kafada mun sunan tauraro wanda kasani cikin rayuwar ka, dan jam kadan Khalil yayi kafun ya furta cewa Fatima zarah, abirkice Alili yadube sa yace wace Fatima zarah, Khalil yayi murmushi yace masa Mimi mana, Alili yace Mimi kuma bayan da sunan da kake kiran ta dashi kenan Mimi banta jin ka ambaci Bintu ba bayan kaf gari nan da Bintu ake ce mata,

Numfasawa Khalil yayi yace "ae sunan danaji nafada mata kenan Mimi amma nasan sunan ta kenan Fatima zarah, "

Sosai Alili yashiga cikin mamaki akan lamarin wannan bawan Allah anya ba lafiyan sa kalau ba yana abu cikin hankali da tunani, cikin sanyi jiki Alili yace gaskiya kana son ta, sosai Khalil yace, Alili yadaura dacewa sai tambaya nagaba, ina jin ka Khalil yace yana gyra zaman sa,

Alili yace fadamun sunan macen da kasani, Khalil yace "hallou dai Fatima zarah ce, cikin mamaki yace masa gaskiya kana ji da zarah, Khalil yace sosai ma kuwa, " Alili yace sai tambaya tagaba, Khalil yace ina jin ka

Alili yace fadamun abu daya dakake so a rayuwar ka,

Murmushi Khalil yayi yace "Fatima zarah itace kadai nake so arayuwa ta , "

Alili ya numfasa yadaura dacewa fadamun abu daya dakake tsoran rasawa arayuwar ka,

Khalil yanumfa sa yace "tsoro na daya ne shine narasa Fatima zarah, "

Alili yace fadamun bukata daya dakafi rokon Allah,

Kahili ya numfasa yace "shine Allah kabani Fatima zarah, "

Girgiza kai Alili yayi yace gaskia kana son Fatima zarah amma kuma banajin akwai alaman zaka aure ta, cikin firgici Khalil yamike yana fadin babu abunda zai hanani auran Mimi na babu shi, Alili kire hanun sa yayi yace zauna namaka wata bayani, zama Khalil yayi,

Duban sa Alili yayi yace kasan maiyasa namaka dukan wadanan tambaya, girgiza kai Khalil yayi yace a'a Alili yace saboda infada maka akwai kalubali daywa agaban ka idan harkana son kasamu Bintu too dole sai kadage saboda akwai wani mutum daya sunan sa Bushar yana masifan son Bintu arayuwar sa kuma babu wani matashi agari nan wanda yaisa yace yana son Bintu, yana da matukar hadari arayuwar sa, mutum ne mai amfani da tsafi ajikin sa, idan kana son Bintu dole sai kadage da addu'a duk dana san kanayi,

Sosai Khalil yashiga tashin hankali yana girgiza kai yana fadin indai yafi karfin mutani to ae baifi karfin Allah ba dan haka daga yau zan dage da addu'a ae Allah yafisa, sosai Khalil yayi wa Alili godya,

Tunda daga lokacin da Khalil da Alili sukayi wannan maganan Khalil yadage da addu'a Allah yabashi Mimin sa,

Soyayya shakuwa da fahimtar juna tazauna atsakanin Bintu da Khali wanda ayanzu kaf garin guma kowa yasan da wannan soyayya, idan kaga Bintu tofa tabbas zakaga Khalil suna rayuwa cikin farin ciki,

Babu bata lokaci Kaka yasamu Baffa Bintu da magana nan, bayan Kaka sun zauna da Baffah Bintu Kaka yafara magana dama akan wannan mutumin da Alili yatsuto sa ne adaji kuma harmuka yi jinyan sa cikin iko na ubangiji Allah yasamu lapiya harya kai yamanta koman nakan sa baya iya tuno kamai nasa kuma mun kai sa asibiti likita yatabbatar mana zai iya samun lapiya idan ana tuno masa da rayuwar sa nabaya amma kuma bamu san waye shiba, amma nayarda da hankalin sa idan zaka iyabashi auran diyar ka dan Allah kashi yana son ta mutum ne mai addini nasan tabbas zai irike diyar ka cikin mutunci da mutumtawa koda kuwa ya dawo cikin haiyacin sane dan haka dan Allah idan zaka iya, sosai Baffah ya girgiza kai yace mai zai hana idan harya na son ta kuma kunyi na'am da hankalin sa dan haka nabashi ina fatan yazamo sanadiyar samun iyayan ta da kowa nata dan haka na amince nabashi Allah yasa alkhairi ciki, sosai Kaka kaji dadi kuma yamasa godiya

Har yamike zai tafi Baffa yatare sa da wata magana amma nasan kasani kowa yasan Bushar nason Bintu dan haka ina son kafun Bushar yadawo daga tafiyan da yayi amusu aure idan babu damuwa, sosai Kaka yaji dadin hakan, Kaka yace wannan hakane kaga kuwa idan yadawo yatarar da Bintu tayi aure dole ya hakura ne dahaka suka tsayar da rana sati uku,


Kaka yasamu Khalil da Alili ya sanar musu dukan magan-ganun da sukayi da Baffahn Bintu suji dadi sosai da sukaji ansanya ran auran Bintu da Garkuwa duk saboda Bushar, kaka yace to yanzu sai kufara ginin wanancen filin saboda kar lokaci yagure mana, haka kuwa akayi suka shiga gini sosai,

Gini yayini sa yayin da sauran kwana auran Bintu da garkuwa saura sati daya kowa yasan da zance auran agarin domin kuwa har gulma aekyi duk saboda Bushar ae baya nan ne hakan tafaru wasu sunyi murna haka yayin da wasu suke cewa ae dama Bintu yar tsutuwa ce dan haka babu laifi dan dan tsutuwa ya aure yar tsuwa,


Yau garin antashi ne da wata iska mai dadin shaka gamida sanyi sosai yayin dawani hazo-hazo yayiwa garin rumfa sosai, Bintu ne da Garkuwa awani bakin rafi iska sai kadasu yakeyi gawasu furanni yakewaye su kananu da manya kasama yayi jaa alamun dai ruwa yana daf da saukowa, garkuwa ya dubi Bintu yasoma magana cikin zakin muryan sa maidadin sauraro yace Mimina yau saura kwana uku rak kizamo malakina uwar y'ay'a na, muna aure zakidaena komai nine zanyi komai abinci ibo ruwa komai fah, murmushi Bintu tayi tace bazantaba barin mijina ya wahalaba dan haka babu abunda zakayi mun idan kuma kace dole sai kamun toofa tabbas saidai muyi tare, sosai Garkuwa wato Khalil yayi murmushi yace gaskiya banzan bari iyiba Allah, Bintu tace Allah zakabari muyi tare tafada cikin shagwaba ae tuni takashewa Garkuwa jiki to naji zamuyi tare amma kuma daka sanda kika samu ciki nine zanyi komai, cewar Khalil ae Bintu idanuwan ta ta rufe sosai suke hirar su gwanin ban sha'awa da nishadi


Adai-dai wannan lokacin kuma wani ganka ake dokawa acikin gari anawa ka ga ga Bushar yadawo ga Bushar yadawo ahaka har akawuce gidan Kaka da wakar, alokacin Alili suna fantin dakin amarya, yaji sunan da aka ambata kamar diran mikiya.........


Ganga ake dokawa ana waka ana cewa ga Bushr ga Bushr, Alili da suke ta panti dakin amarya yaji saukan sunan kamar diran mikiya sosai ya shiga cikin razana da furgici kai tsaye cikin gari yayi domin niman Khalil gabaki daya baya cikin haiyacin sa,


Khalil da Bintu da suke zaune abakin rafi da basusan abunda yake faruwa ba acikin gari sosai suke shan soyayyar su cikin farin ciki da fahimtar junan su
Bintu tace kasan me Khalil yace sai kin fada ae zan sani, sauke numfashi Bintu tayi ta soma magana cikin muryan ta maidadin sauraro tace atareyata dakai Saudauki na na ilimantu da wasu abubuwa masu yawa hakan ne yasa nakejin babu wani tamkar ka ina maka son da nidaina ban san adadin hakan ba zuciya ta babu wani tamkar ka zanciga ba da hidimtawa soyayyar ka har ranan da Allah zaisa kazamo mijina ina maturkar kaunar ka annurin raina ina son ka sosai Khalil yaji dadin maganta kuma yake jinkan sa babu wanda yakai sa sa'a awannan duniyan

Bintu tace inama muna aure dani dakai mubar wannan garin mai cike da masifa agaremu,

Khalil adan razane yace masifa kuma Mimi,

Bintu tace ehh masifar Bushar koda yadawo munyi aure bazai barmu muzauna lapiya dakai ba ina jin tsoran ya cutar mun dakai, Khalil yace karki damu ae Allah yafisa, sosai suke cikin nishadin su,


Alili ko ina yaduba bai ga Khalil ba dan haka yayi tunanin yana can gunda suka saba zama dashi da Bintun sa dan haka kai tsaye rafi yanufa cikin tashin hankali,

Numfashi yake ta saukewa yana kara saukewa Khalil yafara ganin sa cikin wannan yanayin yazo gare shi yafara masa magana Alili meyafaru kake ta sauke numfashi haka fadamana Alili yadubi Khalil yace ka gudu ka gudu zai kashe ka yadawo yadawo yadawa abunda Alili yake fada kenan kawai



Khalil yace kanutsu kafadamun maiyakw faruwa, Alili yace Bushar yadawo, daga Khalil har Bintu tsaya sukayi cak zuciyar su tana bugawa ,

Bintu tace shikenan nashiga uku na kashe mun kai zaiyi yanzu yazanyi kuka take sosai kamar wanda aka mata mutuwa yo ae mutuwar ce ae Bushri babban mungu ne kuma matsafi ne

Tashin hankali wanda ba asama rana kenan Alili yace mufi daya ce shine Khalil ya bar gari nan, shine kawai zamu kare sa daga azabar Bushar, Khalil da tun farkon da Alili yafada musu cewa Bushar yadawo bai sake magana sai yanzu dayaji abunda Alili yafada masa cewa ae ya gudu,

Girgiza kai yakeyi yana fadin a'a babu inda zan tafi na bar Mimisaidai mutafi tare da ita cikin kuka yake fadin haka babu inda zan tafi nikam ae Mimi ce rayuwa ta idan har bada Mimi zan bar garin mahaifa na ba too wallahi zan tsaya ne duk abunda Bushar ya mun zan jure, sosai Khalil yake sun batu cikin fitar haiyacin sa,


Alili yace garkuwa dole ka gudu guduwa yazama dole, maida kallon sa yayi kan Bintu ya fara magana cikin sanyi murya mai cike da tsoro yace Bintu kibi sa wata kila Allah yahada ki da iyayan ki nikuma zanyi wa Baffan ki bayani yadda zai fahimta, kinji,

Cikin kuka Bintu tace too dan Allah ka kulamun da Baffah na sosai Alili yana kuka yana cewa insha Allahu zanyi hakan nidae fatana watara na kudawo gida,

Khalil yace bazan taba manta gida ba dan haka dole nadawo gida sosai suke kuka abun yataba zuciya ta, Khalil Bintu Alili dukan su kuka suke kamar wanda ace idan suka tafi bazasu kara ganin junan suba.


Dukan tattaunawan dasu Khalil sukayi duka akunnan iro aboki ga Bushar kai tsaye yayi cikin gari domin sanarwa abokin sa.


Sosai iro yake sauri dan zuwa sanarwa Bushar cewa fa Bintu zata gudu da wani mutum suje can suyi rayuwar su,


Bushar zaune akan kujeran sa da akoda yaushe yake zama ga mukarrabon sa sun kewaye shi cikin tsoron son fada masa fa Bintun sa yau saura kwana uku kacal auran ta, iro da gudu yazo yasame sa yana haki yana fadin oga Bushar wanda babu kaman sa akaf kauyan guma nakawo maka babban labari, Bushar kada kai yakeyi yana fadin ina jinka fadamun, iro yace Bintun ka matar ka tana shirin gudu da wani acan bakin rafi, mikewa yayi da sauri yana haki yana yacewa a'a karya kake babu wanda ya isa yashiga gona ta, Iro yace wallahi Allah dagaske ne Bintu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login