Showing 42001 words to 45000 words out of 54699 words

Chapter 15 - Mukaddari Ne Daga Allah Complete Hausa Novels By Suhaima Abubakar Shehu.txt

da dama suna wannan kwanciya ta rub da ciki wanda mafi yawa suka mai dashi a matsayin kwanciyar da tafi musu dadi ba tare da sun san cewa kwanciyar ce wacce Allah baya so kuma Annabi (saw) yayi hani akan hakan ba wasu daga ciki kuma sun san cewa ba kyau, amma suna yin irin wannan kwanciyar ba tare da sun damu ba, "

Nufashawa Khalil yayi ya kara kwantar da kan Bintu a kirjin sa, kana yadaura dacewa, "haka nan akwai wadanda daga anyi magana akan wannan kwanciyar ta rub da ciki sai suce ai camfi ne (ma'ana maganganun mutane) ne kawai,

To a hakikannin gaskiya babu maganar chamfi an samo hadisi ingantacce daga hanin manzon Allah (swt) akan ita wannan kwanciya ta rub da ciki kamar haka


Idanuwar Bintu Khalil ya duba ko tana sauraran sa hada idanuwa sukayi tayi lamo a jikin sa Khalil yace "Mimi na kina jina kuwa? Bintu tace ina jinka miji nagari,

Khalil yace ai nazata kin koma bacci ne, numfasawa Bintu tayi tace ai kaima kasan bazan iya bacci ba yayin da mijina yana fada mun magana masu daraja wanda zasu amfani ni dan haka ina jinka miji nagari,

Numfashawa Khalil yayi kana ya daura dacewa, " Annabi (saw) yace ita dai kwanciyar (rub da ciki) kwanciya ce ta yan-wuta kuma kwanciya ce da Allah yake fushi da ita (Abu dawud ne ya ruwaito shi da isnadi ingantacce)

Haka nan hadisi ya inganta cikin sunani Abu Dawud ta Turmizhi daga ya'ish Bn duhful gifari (RA) daga baban sa cewa wata rana Annabi (saw) yazo wucewa ya same ni a masallaci ina kwance rub da ciki sai ya zungureni da kafar sa yace kadai na irin wannan kwanciyar saboda kwanciya ce da Allah yake fushi da ita,

Khalil yasake rumgumar Bintu yaci gaba da magana,

Haka nan masana bincike sun gano cewa rub da ciki wajen bacci yana da matukar illa ga kashin gadon baya,

Mimi na nasha ganin kina wannan baccin ina gyra ki amma kuma har yanzu kinayi shiyasa nace bari na fada miki babu kyau dan Allah kidai na nasan da wuya kadaina abun da kajima kanayi amma dan Allah kikokar ta kinji Mimi na


Numfasawa Bintu tayi tasake kwanciya a jikin sa hannu ta ta tusa a cikin kashin kirjin sa tace "insha Allahu zan gyra Allah nagode naka da kaban miji mai tattaku mai jan matar sa a jikin sa naji dadi kuma ina alfahari dakai masoyina,

Tace nagode nagode sosai ina son ka, Khalil ya kalle ta yace nice da godiya ai yanzu mutashi muyi sallah kafin asubahi tayi, kinsan yau zamu shiga kasuwa da Alili kuma yace mun inshirya da wuri, Bintu tace haka ne kam suka mike sukaje sukayi alola har da Khalil din

Da safiya Bintu tagama hada musu abun karyawa bayan sun yi wanka Khalil ya kira Bintu yace tazo suyi addu'ar safiya kamun su karya haka kuwa sukayi

Ayatu kursiyyu sukayi sau uku, sai sukayi Qul huwallahu Ahad shima sau uku, sai Qul a'udhu rabbil falaq sau uku sai Qul a'udhu bi rabbin naas sau uku

Addu'o'i Khalil ya yacigaba dayi Bintu tana cewa Amin Khalil yace Allah ya ubangiji mu mai rahma kashiga cikin lamuran mu kamana jagora akan duk abunda mukasa gaba na alkhairi ya ubangiji Allah karemu da kariyar ka kadaura mu akan makiyar ka, Bintu tana tacewa Amin

Bayan sun kammala addu'an suka karya suna gama karyawa Alili yazo, Khalil yayiwa Bintu sai mun dawo, dawo lapi Bintu ta musu baki dayan su suka tafi,



BUSHAR

Bushar yaran sa gabaki dayan su sunkewaye sa, Bushar yace yau zamu kashe wannan mutumin da yarabani da Bintu na naji na labarin zasu tafi kasuwa shi da wannan yaron Alili to yau gabaki dayan su zamu gama dasu amma sai da yamma zamuje hanya mujirasu mugama dasu yaran Bushar sunyi na'am da batun sa kuma sun tsayar da cewa yau zasu kashe mutum nan da kuma Alili,


Khalil da Alili sunshiga kasuwa asa'a atake suka sara kayyan miya kuma suka siyar agun sai daf da bangari ba suka sake saran kayyan miyyan wanda Khalil zai siyar akofar gidan sa, khalil ya siyawa Bintu abubuwa da yawa natsaraba suka nufo gida,

Bushar da yaran sa kuma sunkewaye hanya dan yau basuga abunda zai hana su kashe Khalil,

Bintu tayi wanka ta tashirya tana jiran mijin ta dan gaskiya yau tayi kewar mijin ta tamasa abinci sa mai dadi wanda yafi so sosai Bintu tagama abunta dan tarban mijinta,


Bangaran Khalil ma yayi kewar matar sa sosai suna cikin koma kauyen guma motan amalalke ta samu matsala gabaki dayan su suka fito a cikin motar sai da sukayi kusan tara na dare akafu aka gyra suka dau hanya,

___Khalil tafiya suka cigaba dayi cikin moton amalanke, mutani da yawwa suka gani akwance a kasa duk jini yabata musu jikin su wasu kam ma babu rai a jikin su, tsoro da firgici duk yagama gauraye zuciyoyin su Khalil addu'a kawai suke fatan su Allah yakai su gida lapiya,

Bintu duk tashiga cikin rudani da damuwa narashin jin mijin ta, takasa zama kuma takasa tsaye duk a cikin damuwa take fatan ta Allah yasa gabaki dayan su suna lpa,

Har kusan goma na dare Khalil bai shigo gida ba anan ne Bintu tagama rudewa, hijabin ta tadauku zata tafi gidan Kaka taji ko lapiya, saka hijabin tayi ta nufi kofar gida dan zuwa gun Kaka, har tasaka kafar ta a kofar gidan taji karo da Khalil sai sauke numfashi yakeyi,

Kamashi Bintu tayi tana kuma tambayar sa lapiya mai yafaru dakai kake haki wani abu yafaru daku ne, ina yaa Alili fatan kuna lpa gabaki daya tajero masa tambayan lokaci guda kuma duka tambayan ta babu wanda tasamu sa'ar amsa mata dan Khalil sai sauke numfashi yake,

Kama shi tayi ta nufi d'aki dashi zaunar dashi tayi abakin gado tafita a d'akin ruwan zafi sosai ta hada masa takai masa bayan gida, komawa tayi d'akin tace na kai maka ruwan wanka idan kayi wanka jikin ka zai warar-ware, Khalil sam baya cikin haiyacin sa da alama dai yau ciwon sa ya motsa ne, ganin hakan ne yasaka Bintu nufar wajan sa takama shi suka nufi toilet kayan jikin sa tayi kokari taci rai masa tafara masa wankan da ruwan zafi sosai ta masa wankan kana takama shi suka koma d'aki tazau nar dashi abakin gadon mai, tasha famasa bayan tagama ne kuma tasaka masa kayya mai sauki

Ta hada masa koko mai zafi tabashi yasha bayan yasha ta kwantar dashi akan gadon ai kuwa bacci ne tayi awun gaba dashi, itama kwantar da kanta tayi a kirjin sa bacci ya dauke ta,

Da a suba Khalil yafara mutsu-mutsun dube idanuwan sa da suka masa jaa sosai firgicin yanzu babu sai dai kawai kasala abunda yafaru dasu ne yafara dawo kan sa,

Suna cikin tafiya sukaci karo da mutani a kwance a kasa gabaki daya jikin su duk jini yabata musu, kafin subar wajan sai sukaji muryan mutani suna fadin kuka masu gasu nan,

Kewaye su Khalil sukayi suka saka su a tsakiya Bushar yafito, akasa masa kujera yazauna ga bindigar sa agefen sa ya daura kafa daya kan daya ya dubi su Khalil ya soma magana "kai ne karaba ni da zabin rai na ka aure ta to yau zan rabaka da duniyar baki daya kuma na aura matar ka, kai kuma Alili dan gidan Kaka kai tun farko kafara kawo sa wannan kauyen to yau gaba ki dayan ku zan kashe ku,

Tsoro da firgici gabaki daya ya lulube su Khalil zufa sa tsa-tsafo musu yakeyi gabaki daya sun fita haiyacin su,

Mikewa Bushar yayi yana kewaye su yayin da bindigar tana kan kujeran, cigana da zagaye su Bushar yakeyi, Khalil idanuwan sane suka sauka akan bindigar nan da bara yakeyi yana zuwa gun bindigar a wayo dan yadauko ta, ai kuwa da taima kon Allah sai ga Khalil ya dauka wannan bindigar ya nuna Bushar dashi yana cewa "kabar mu mutafi idan ba haka ba sai na kashe ka "
haka kawai Khalil yake fada sai da ya harba bindigar kafin Bushar ya juya aguje kowa ya kama gaban sa shi kuma Khalil cigaba da harba bindigar yakeyi kamar babu gobe Alili da sauran mutanin duk sun gudu Khalil ne kawai yarage agun bai gudu ba,

yagama fita hai yacin sa yafara tafiya tai makon Allah ne kawai yakawo sa gida,

Bayan yagama tuno duk wata abunda ya faru dasu sai karan bindigan nan tadawo kan sa kamar yanzu ake harba ta rike kansa yayi sosai hawaye suna fita daga cikin idanuwan sa, da sauri Bintu datake gefan sa tamike tana mana magana "kana lpa kuwa? amma ina Khalil baisan tanayi ba, kuka yake sosai kamar karamin yaro kuma yarike kan sa kam............

Kuka yake kamar karamin yaro, Bintu kuma sai tambayan sa take amma kuma Khalil bai bama san Bintu tana tambayar saba gani Khalil yaciga da kukan ne yasa Bintu itama tacigaba da kukan, kuka suke sosai kamar babu gobe, sosai suke kuka Bintu ganin kuka bazai musu maganin komai ba yasa tamike ta dauka mayafin ta tasaka tafita a ɗakin taja,komar ɗakin gabaki daya gidan tabari, gidan Kaka tanufa dan sanar masa cewa fah tun jiya Khalil yake kuka,

sallama ta ringayi a kofar gidan amma kuma shuru babu amsa, dan haka takusa kanta cikin gidan amma kuma babu kowa a tsakar gidan ɗakunan gidan tafara dubawa amma kuma gabaki daya babu kowa a ciki ruɗani tafara shi amma kuma sai tace bari tazauna tajira zuwa anjima wata kila sun je daji dan nimowa mutani magani duk da akwai tunanin sahibin ta a ranta,


kusan la'asar amma kuma Kaka da Alili basu dawo gida ba dan haka tamike dan komawa gida dan tabar Khalil shikadai kuma bawani ishashen lapiya gare sa wani bangare kuma na zuciyar ta yana fada mata cewa su kaka anya suna lapiya,


Lokaci guda wani hadiri ne ya hadu gabaki daya garin yayi bakikirin sosai ko tafin hannun ka baka iya gani sosai garin yayi bakikirin haka Bintu tarin gabin bango dan komawa gida dan batasan awani hali Khalil yake ba taimakon Allah ne kawai yakawo Bintu gida tana shiga gida ɗaki tanufa dan ganin awani hali Khalil yake, amma kuma babu Khalil ko ina Bintu taduba amma babu Khalil hankalin ta yatashi sosai gabaki daya ta fita cikin haiyacin ta tazama kamar mahaukaciya duk yadda yakamata da duba taduba amma kuma babu shi ai kuka tafashe dashi mai cin rai koka take sosai tana fadin nashiga ukuna ina kake Sadauki ina katafi wayyo Allah bazan iya rayuwa babu kai ba kadawo gareni dan Allah kadawo idan wasa kake mun dan Allah kabari sai sumbatu take tana kuka ga kuma ruwan sama da yasako kamar da bakin kwarya,

haka ruwan nan yacigaba da dukan ta agun tana zaune a tsakar gida ruwa yana dukan ta tana kuka har ruwa ya dauke tana tsakar gida ganin ruwar ya dauke ne yasa tasa fita agidan baki daya da kuma jikan kayyan ajikin ta,

gidan Kaka tasake komawa amma kuma har yanzu babu su a cikin gidan, sake shiga cikin wata rudani tayi da kuma tsoro yasake shigan jikin ta rasa yadda zata nufa taji sanyi aran ta tayi ko ina zafi wannan shi ake kira da rana zafi inwa kuna,

saike komawa gida tayi tazauna a tsakar gida ta fashe da kuka mai karya zuciya tana kuka tana sumbatu,



SAUDI
_________________________________________

Har yanzu jikin momy kara gaba yakeyi babu wani sauki atattare da ita momy yanzu bata gane kowa batasanin waye akan ta

Haka Abba ya dauke ta yadawo da ita gida Negeria su Khairat ne masu kula da momyn su domin yanzu aiki ,yayiwa Abba,tabbas idan kasauke idanuwan ka akan momy sai ka tausaya mata tuni Mahaifinta mai martaba sarkin Bauchi yasaka adauko masa ƴar sa amma kuma Abba ya nuna ƙin amincewar sa akan hakan,


umma ce akan komai ita take kullawa da ita gabi daya gidan ya koma babu wata farin ciki haka suke rayuwa adaddafe,


AMERACA🇬🇧

💝💝💝💝💝💝💝💝💝💝💝💝💝💝💝


Sana da mom sundawo zaman gidan yana musu wahala kullum sai Abbi yazo ya zzzagamu su fada yana tambayar su ina Suha amma kuma magana daya Mom take fada masa nima bansan yadda take ba,


haka kullum rayuwar su take Sana ce tashiya cikin doguwar riga after the rest tayi kyau sosai samun mom tayi akasa tazo ta rumgume ta ta sumbace ta akumatu tace to nikam mom natafi school, mom tace adawo lapiya kuma ki kulla sosai Allau yakai ki lapiya sannan kuma yadawo dake lapiya, Amin Amin mom dina sai na dawo,


motan ta tashiga aka bude mata get tafita a gidan tana cikin tafi tana sauraran waka mai dadi tana tunanin kalbin ta kwai moton ta tafara jakin da alama dai wani abu acikin motar yasamu matsala,

parking tayi agefen hanya ta sauka a moton gashi ita ba gyran moto tayi ba tsyawa tayi cak tana tunanin abunyi wayar ta tafara ringing tana dubawa kuma Suha tagani ai da sauri ta dauka wayar takara a kunnan ta suka fara magana,

Suha tace ai daman kince bazaki kewata ba kuma ashe da gaske kike nikuma nayi kewar ki shiyasa nace bari nakira wanda batayi kewata muyi fadan da muka saba dan ajima bamuyi ba tun kafin natafi,

murmushi Sana tayi tace "Suha rigirma fatan kina lapiya bata jira amsata ba ta daura dacewa ai dana zata bazanyi kewar kiba ashe ba haka abun yake ba kewarki yagama shiga cikin jinin jikina kullum sai nayi kukar rashin ki akusa dani,

murmurshi Suha tayi Allah sarki rabin jiki fatan yanzu kin daina tunanin wannan mutumin ko?

murmursshi Sana tayi tace ai tunanin sa sai kara shiga cikin rai na yake kullum sai nayi kuma ince Allah sarki ƴar uwata da yanzu tana nan da itace zata rarrashe ni gabaki dayan suka fashe da dariya,

Suha tace sai yanzu nagano dalilin yin kewata ashe saboda haka ne ,

Murmanshi Sana tayi tace Suha sarkin rigima,

waya suke cikin nishadi har Sana ta hau kan titi batare da tasani ba,


Siddarth cikin jamfa da hula yayi matukar kyau sosai yana tafiya cikin moton sa, idanuwan ya sauke akan Sana da take waya akan titi dafa kan sa yayi yana girgiza kan sa yana furta "mai yasa yarinyar nan take son sa rayuwar ta cikin hadari,


wata babban moto ne tayi kan Sana bata rai da ta ankara ba Siddarth ganin hakan yasaka ya fito a moton sa yana furta keee keee, juyowa Sana tayi ta kafesa da idanuwar ta tana kallon sa,

shi kuma Siddarth alamu yake mata da hannun sa akan ta bar gun amma ina Sana bata fahimta ba kallon sa kawai takeyi


bangaran Suha kuma sai HELLO take tacewa,

a aguje Siddarth yatun karo Sana yana haki yana daf da ita moto nan yana karisowa gunta ai daguun sa ya zo gare ta ajefata agefan sa tayi gefen titin shima yayi gefen titin,.................

_____bangaje ta Siddarth yayi tayi gefe shima yayi gefen titin..

Suha datake dacewa Hello Hello daga karshe kuma sai taji wayar taka tse.

Siddarth da gudun sa yakari so gun Sana yafara mata magana cikin fada "fadamu mai yake damunki yasa kike kai kan ki cikin halaka.


Shuru Sana tayi ta zuba masa idanuwan ta tana kallon sa, hannu ta Siddarth yakama yazo,daf daita yana mata magana yana zare mata idanuwan sa kifadamun nace ko mai yake damun rayuwar ki amma kuma kin mun shuru bazaki bani amsa ba.

okay bazaki mun magana ba shikenan tsaketa Siddarth yayi yabar gun yana mai ji ran sa sai yanimo abunda yake damun wannan yarinyar.


Sana ganin mutum da take mutuwar kauna awannan karon zai sake kufce mata yasa ta tashi tabisa da gudun ta, yana daf dashi ga moto Sanna ta rumgume sa tabaya ta fashe masa da kuka mai jin rai,

tsayawa Siddarth yayi cak shi bai yi kokarin hana taba kuma baice mata komai ba kawai tsayawa yayi yana sauraran kukan ta,


kuka sosai Sana take tana kara tusa kan ta a tsakiyar bayan sa,

sai da yaji alamun tadan sauko da kukan tan yasa ya juyo da ita suka fuskan ta junan su, zuba idanuwa sukayiwa junan su suna kallon juna su sun shafi lokaci mai dan tsawo kafin Siddarth ya katse kallon yaja hannun Sana yasaka cikin moton sa shima yashiga yazauna, shi bai ja moton ba ya tsaya agun,


sai sukayi kusan minti na 30 kafi Siddarth ya lumshe idanuwan sa kana ya dubi Sana yace kin shirya fadamun abunda yake damun ki kenan?


Girgiza kai Sana tayi alamun ehh,

Ina jin ki cewar Siddarth ya mai da idanuwar sa akan ta kana kuma ya lumshe idanuwan sa alamun dai ina jinki,

Sana rasa yadda zata masa magana tayi gabaki daya idanuwan sa da yazuba mata yagama burki tata duk sai yama kwarjini,

Shuru tayi da zuba masa idanuwan ta tana kallon sa tana ji aran ta ina ace sutabbata ahaka,

kin zuba mun idanuwa kina kallo na kuma kinsan ke kadai nake sauraru Sana ta tsinka ya muryan sa kamar bashi yayi magana nan ba domin idanuwar sa arufe suke

Sana ta gyra zama tafara fai yace masa abunda take ji aran ta kuma akan sa,

sai da tagama magana tukuna Siddarth yafurta tun yaushe kika fara jin kina sona,

tun lokacin da kataima keni daga saman bene, cewar Sana

saboda haka kikaji kin fara sona? girgiza kai tayi alamun ehhh


Bude idanuwar sa Siddarth yayi yace "tabbas kina so nane saboda na tai makeyi kuma saboda kyawun da Allah yabani ko kuma saboda kudina ko?

girgiza kai Sana tayi tace a'a ba saboda haka bane,

Siddarth yace to saboda me kike sona yan numfasa kana ya daura dacewa idan ma saboda kyawu na kike sona tabbas kinyi gangganci arayuwar ki dan ni ban son mace wanda zata soni saboda kyawuna idan kuma saboda kudi ne ni bani da komai a cikin rayuwa ta dan kar kiga wannan moton kizata nawa ne na mai gida na nee ya kuma numfasawa kana ya daura dace idan duk saboda haka ne bana bukatar ki kifita mun amoto kuma na tsana macce da zatace tana son namiji na tsana irin wannan matan..



___Tsawa Siddarth ya doka wa Sana yana kuma maimai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login