Showing 3001 words to 6000 words out of 54699 words
Chapter 2 - Mukaddari Ne Daga Allah Complete Hausa Novels By Suhaima Abubakar Shehu.txt
nan kayan na jikin sa an saka masa masu sauki nauyi yar yaloluwar riga ce ma sharara da Alili ke sawa idan yana son fita shan iska sai kuma wani son fita shan iska sai kuma wani karamin walki da suka d'ora masa a kugu,
Sosai kuwa ya fito sak kamar su kamar dama haifaffen garin ne sumar kansa kaka yasa Alili ya aske masa ita da askar da suke yiwa juna aski da ita
Sam idan ka kalli Khalil a yanzu ka had'a da hoton sa a kwana ki uku da suka wuce kafin karuwar wananan al'amari to tsaf zaka wuce ta gaban sa baka gano shine ba yanzu kam ba wannan Khalil din bane dan gayu mai ji da kansa dan kwali sa Khalil din dake gasawa mata aya hannu yanzu ya dawo Khalil dan daji
***
WAYE KHALIL
cikakken sunan sa Khalil Yahaya Chiroma inkiya KYC idan ka cire mahaifan sa kowa da KYC yake kiran sa shi ne babban dan agurin hajia Hafsatu Madaki wacce ake kira momy kuma d'anta guda d'aya tilo namiji tanada wasu yaran kannen Khalil din Khairat ita ke bi masa sai Khalisat Kulthum da Kausar wacce ta kasan ce autar su
Mahaifin sa Alh. Yahaya Ciroma yanada wasu yara da d'aya matar tasa Hajia Rahama Sunusi dake aka cewa umma kuma itace amaryar sa dan haka suka yaranta k'ananu ne sakamakon tsaikon haihuwa data samu dan da farko ma ganin sum shafe shekaru biyar da Alh. Yahaya bata haihu ba har an fara yada jita-jitar cewa juya Alhajin ya daukowa kansa amma da yake haihuwa ta Allah ce sai kuwa ga haihuwa ta rika zuwa mata a duk bayan shekaru biyu da Alhaji Yahaya uku mata sai biyu maza karima itace yarta ta farko wacce taci sunan mahaifiyar Alhaji mai suna Hauwa'u da suke kira Ammu sai Kasim Khalid da kuma Khariyyah sai autar su Khadija dukan su suna amsa KYC ne kamar yadda suka ji ana kiran yayan nasu wato Khalil shekarun Khalil a shirin da biyar zuwa da shida yana karatu a jami'ar bayaro dake kano duda ba itace farko jami'ar daya fara halarta ba zafin rai da zafin zuciya ne ke korar sa a duk inda aka kashi karatu
YALE UNIVERSITY dake kasar Amurka ce jami'a ta karshe ya je ko shekara bai rufe ba suka yi fada da wani dalibi yayi masa dukan tsiya
Bayan karbe lasisin karatun sa da makaranta tasa akayi sakamakon k'in bada hakuri abunda yayi har tsaresa akai wanda da Addu'o'i da matsalar suka bada belinsa daga nan ne kuma Abba yace gaskiya ya gaji
"in dai dai kudina yaro nan zai k'ara tafiya Turai karatu to wlh ya gama daga yau zai ari baki a sanda akayi nasarar sako Khalil din suka dawo Nigeria
Kowa ya taru a falo Abba inda ake jajantawa Khaliln din da mahaifan sa wannan abu daya faru
Momy dake zaune a matukar bacin ran irin halin Khalil na rashin hakuri cewa take "Khalil wlh naran tse da Allah ka kiyaye ni billahillazi zan iya sall....
Kafin ta karasa zance ne Alh. Amadu Chiroma wanda k'ani ne ga Abban yayi saurin katseta da subhanallahi haba Hafsatu yi ashe idan rai ya b'aci hankali ma tafiya yake shima cikin b'acin rai yake mata fad'a abunda take kokarin yi da alama bai ji dadin furucin ta ba " yau Khalil koda bake kika haifesa zaki so wani yayi masa baki? idan lalacewar Khalil tafi haka ai kuwa ba iya kuka zai saka ku ba Allah ya tsare ya kara ko wannan halin ma fata muke Allah ya yaye masa bare kuma wani abu yakaru a kan wannan din Addu'ar nan dai da ake masa za'a cigaba shiriya a hannun Allah take kuma shi kadai za'a iya fadawa ya kawo mana dauki dan idan na ya lalacen dai dole a kirasa da suna zuri'ar Chiroma"
wayannan kalamai na Amadu ba kad'a suka tasirantu a zuciyar momy ba har Abba dake jin kamar ya sallamwa duniya Khalil din ji yayi k'anin sa yafi bukata samada adu'a da farko niyyar Abba shine har anan gida Nigeria bazai biyawa Khalil din ya cigaba da karatun sa ba amma zuwan maganar gurin yayan su gabiki daya yasa ya saussauta daga fushin sa
Yanzu nufin ka Khalil bazai cigaba da karatun sa ba ko anan ma? Baba Abdullahi Chiroma yayan Abba ya tambaya lokacin da yaji hukuncin da Abba ya dauka game da karatun Khalil din yakira shi gidan sa yake tambayar dalili
Shin idan akwai wani wanda yafi kowa sanin muhimmancin ilimi da tagomashin dake cikin sa yakai ka ne? Ina ce ilimi ne ya kawo ka wannan matsayin dakake da kamfani naka kanka shin yanzu idan babu wani babba mai ilimi daga ciki yaran ka da zai rika kula maka da dukiyar ka kana ganin ko da ranka ba za'a cuceka ba bare kuma ka mutu"
Nan ya shiga yi masa nasiha da nusantar dashi irin hadarin dake tattare da fushin mahaifa dake tattare da fushin mahaifa akan y'ay'an su
Sosai nasihar yayan nasa ta karya logon duk wani kudirin sa bai baro gidan sa ba har saida yayi masa alkawarin in sha Allahu zai nemawa Khalil din admisson a BUK
Haka kuwa akayi abokin sa yakira dake karantarwa a jami'ar ya fada masa taimakon dayake nema.
Haba Alhaji ai matsayin ka a gurina ya wuce ka kira ni kana cewa na taimaka maka wlh ko wani yayi karya da sunan ka to sunan ka to sai nayi masa abunda ya nema bare kuma kai kaga ma anyi sa'a ba'a riga an rufe bada gurbin karatu ba in sha Allah har gida zan zo na kawo maka admission farm sai acika.
Sosai Abba yaji dadin wannan karamci irin na Dr. Sani Gusau ba'a rufe wata d'aya ba akayi kome da kome aka kare sakamakon Dr. Sani daya tsaya kan lamarin.
Rananr litinin ta kama ranar da Khalil din zai fara shiga aji tun a ranar lahadi da daddare bayan dawowar Abba yasa akira masa shi dan har wannan lokacin bai gama saukowa daga fushin Khalil din ba wanda da dane dakuwa kansa Abban yafi son Khalil din da son yin hira dashi fiyeda sauran yayan sa ba'a jima ba kuwa Khalil din ya shigo jiki a sanyaye bawai dan yaji fadan da aketa masa bitansa ba tun faruwar wancan al'amarin saida dan tunanin yanzu shi taya zai iya fuskantar bakin da abokan sa musamman ma samir yayi masa
" Khalil ko yaje kasar waje karatu sai ya dawo"
Me yale university kace Billyboy ya fada yana tintsirewa da wata dariya irinta ayi dai mugani samir ko dake duba list din abinci da waitress ta kawo masa dan yi musu order abunda zasu ci cewa yayi dude yale university jami'ar ce mai kyau amma naso ka zabi stanford uni baba Stanford duniya ce yanzu haka na tura musu duk wasu credentials nawa admission kowane lokaci zai iya fita
Khalil da izuwa wannan lokacin ya fara hawa sama da dariyar da Billyboy yake masa girgiza kai yayi alamar No No No ina son yale university ya fad'a adame kafin cikin matukar fusata ya saka kafa ya daki kujerar da Billy saiji yayi yadaki sauran teburan da aka ajiyewa wasu abinci suna ci anan take daga abincin har teburin da kuma kujera ya Billy yake kai suka zube kasa
Ai kuwa hankalin kowa ya dawo. Kan Billy dake kwance a kasa samir kuma wani kallo yake aikawa Khalil din na wannan wane irin banzan wasa ne
Khalil kuwa da har jikin sa wani b'ari yake tsabar fuahi baima ko san kallon da samir din yake masa idon sa akan Billyboy yana jiran ya gani ko zai iya ramawa
Wanan tazarcin da Khalil yayiwa Billy yayi matukar hassala shi musamman ma daya ga yan matan dake me zai wasu ma har dariya suke jefo masa kasa-kasa wannan sosai yayi tasiri gurinnk'ara tunzura Billyboy cikin sauri ya tashi ya nufo Khalil yana cewa kai dan ubanla ni zakaiwa raahin mutumci duda kokarin da samir yayi dan ganin ya dakatar da Billyn amma ina.
Har ya kai ga jikin Khalil din sun kacame da wani sabon fad'a da Khalil gangancin fad'a da khalil kwai yayi domin duda yafi Khalil din karfi amma yasan Khalil yafisa karfin zuciya hannuwa Billy ya murd'e dake kokarin riko wuyan sa yasaka d'aya kafar sa ya kwashe k'afafun Billy ai kuwa saiga Billy kasa tim kafin ma ya gama jin dumin kasa Khalil din ya d'agosa sama ya jefasa cikin wasu teburan cin abincim kamar wani kayan waki bai gama shanye wannan azabar yaji Khalil din sake damko sa ya k'arasa karya kafar teburan da suka kakkarye a guron da nufin banka masa a fuska.
Samir da wasu mutanen suka rirrikesa dak'yar suka iya suka k'waci Billyboy daga rikon da Khalil din yayi masa fuskan Billy kamar wanda yayi karo da bishiya tayi sumtul musamman gefen bakin sa
Wannan wane irin jahilci da dak'ik'anci ne Kyc? Samir ne yake zazzage masa tsantsar bacin ransa da takaicin da zuciyar sa keji game da abinda yayiwa abokin su wlh kyc da dai irin wannan bak'in halin naka bazaka tab'a abokai ba a rayuwar ka saidai ka kare a haka bara kaji kyc ko dabba ya fadi hakan ne yana nuna dan yatsan sa a fuskar Khalil din ko dabba bazata yi irin wannan dabbanci da kayi ba.
Jin wannan kalma ta dabban fa abokin sa ya kirasa dashi yasa cikin fushi ya kira sunan sa SAMIRRR cikin alamar ka kiyaye harshen ka.
Ko nima dukana zaka yi Khalil? cikin d'aga murya shima yake masa maganar fine ka dake ni Kyc wannan karon ya matso daf da Khalil Khalil din ko motsi baiyi ba yasa yayi taku. biyu bayan kafin yakai hannun sa gurin fuskar Khalil din yana k'yasta yatsun sa da cewa da irin wannan zafin zuciyar Khalil babu wata nasara da zaka iya cimmawa a rayuwa ka bi a hankali da zuciya domin kamar yadda ka rasa mu. ayau idon kawai zai kaika Amerika amma ba karatu saboda ba kada hakuri zama a aji yana gama fadar wannan ya juya a fusace yaji Billyboy suka fice daga restaurant din.
Khalil kuwa yafi rabin awa a tsaye a gurin yana maida ajiyar zuciya kafin ya zira hannun sa a aljihun sa ya cire wasu kudin da shi kansa bai san nawa bane yayiwa wata waitress da sukayi cirko-cirko a guri d'aya sauran ma'aikatan gurin suna Allah-Allah kada fushin zuciya ya dawo kansu
Da sauri waitress din daya kira ta k'araso jikinta na bari bai ce mata komai ba ya bata wayannan kudin......
Ku gyara b'arnar da akai muku fuuu ya wuce yabar waitress din nan rike da baki
Ashe yana da mutunci ta fada tana cigaba da kallon sa tafiyar sa har ya fice am burge ni ta k'ara fada wannan karon kam da karfi.
KO BAKAJI BANE maganar Abba ta dawo dashi daga duniyar data aura tunanin sa kamar wanda yayi mummu nan mafarki haka ya d'ago tareda samun kansa yana gyadawa Abba kai "ehh naji Abba in sha Allahu zanyi du abunda kace idan za'a dauki rayuwar sa ko ya fad'i kalma d'aya da Abba ya fada ba zai iya ba amma kuma harda wani bada amsar cewa ya fahimta da yake kuma anyi arashi shima Abban nasiha ce yayi masa akan yazamo mai hakuri da kuma kare martabar gidan su ko kadan bai fahimci cewa bada Khalil yayi magana ba hoton sa ne kawai nnan Abba ya sallamesa.
Nagode Abba saida safe ya fada yana tashi yafita
Abba kuwa binsa da kallo yayi cikin wani yanayin tausayi d'an nasa yana jin kaunar sa aran sa nan ya shige yi masa addu'o'i a bayyane
******
Washi gari ta kama monday kenan ya shirya cikin kananan kaya riga ce mai gajerun hannu launin ja mai d'abbara-d'abbaran bakin wanda jeans ne daya karawa shigar tasa armashi ya taje sumar nan tayi lif-lif kamar bak'in balarane agogon hannun sa ya saka sai takanlmi kirar gucci da ake yayi bayan ya gama feshe kansa da turarrika masu shegen kamshi designers farin glass dinsa kawai yamakala a idon sa jakar laptop dinsa ya rataya kafin ya dauko k'i sallar sa ya lafa aikuwa ya fito ma sha Allah
D'akin umma ya fara zuwa inda ya tadda su karima suna breakfast aikuwa da sauri daga Karima har Khalid Khariyya da Kasim suka shiga gaishe shi dan kada suyi wani laifi dan sosai suke tsoron sa ba dai Karima da ko zaka kwana kana rantse mata kan cewa Khalil baya shaye-shaye bata jin zata iya yarda
Mutumin da akullum neman haryar dazai ci zalin su yake indai yana gida ranar kamar anyi mutuwa kowa shan jinin jikin sa yake ba duka ba zagi amma sai mutum ya sha tsallen kwado kamar ba gobe k'arin abun mamakin ma wai harda su umma da momy kamar suma tsoron nasa suke ji babban abun haushi da takaicin ma irin yadda umma ke nuna tafi son sa fiyeda su.
Ya bude baki zai tambaye su ina umma sai jiyo muryar ta yayi daga bangaren kitchen ta fito rike da flask.
Sadauki haka take kiran sa ka fito kenan ehh umma ya fada fuskar sa ba yabo babu falla sa ya kara da cewa ina kwana umma lpfiya lau Ibrahim ta amsa cikin kulawa kafin ya d'ora da cewa Ibrahim ka zamo mai karbar abunda rayuwa tabaka koda kuwa ba shine zabin daka nema ba kayi hakuri kayiwa mahaifan ka biyayya kaji Ibrahim da wata kulawa ta musamman take masa nasiha kafin tace kayi sauri kaje kada ka makara
Nagode ua kawai ya fada ya nufi kofar fita aran sa yana jin dama ace umma ce ta haife sa dan tafi kowa tausayin da son sa
Ita ko umma da har lokacin take shimasa albarka har ya fice su Karima ta jiyo sun magana kasa-kasa amma da yale da turanci suke yi yasa ta daka musu harara kawai zaku yi sauri ku kammala cin abincin ku wuce makaranta ko sai kun gama gulmar da kuka saba
Gulmar umma kam sun saba dan duk sanda suka ga tana rawar kafa akan Khalil sai sun tattauna zafin da hakan yake musu da junan su amma cikin turanci dan sun san ummar bata ji ko yanzun ma Karima ce tacewa Kasim yanzu bara ka gani albarka zata saka masa aikuwa basu rufe baki ba kuwa umma ta fara zuba masa tuwan albarka yayin da zai fita Kasim ne ya dubi Karima wow kamar kin d'ora a bakin ta kuwa
Hmmm ai dama nasani mune fa kadai bata tokawa albarka ubangiji amma shi da yake dan gwal ne gashi bai nema ba ma ya samu
Jinjina kai kawai Kasim din yayi alamun lallai akwai gyara cikin ramarin umma kafin yayi ajiyar numfashi yace Allah ya kyauta dai-dai sanda umman ta jiyo su
Zaune yake akan kujera mai zaman mutum daya kan sa a kasa yayin da momy keyi masa nasihar sanin ciwon kai sosai ta masa jan kunne akan bin dokokin makaranta da kiyaye fushin zuciya da rike addu'a a duk sanda yaji bacin ran ya taso masa
Ka rika cewa A'uzubillahi mishshaidanirrajim wannan ingantacce maganin sukar fushi ne daga Annabi (saw)
Kwarai ko ya sani amma shi yana rasa abunda yake danne harshen sa daga ambaton Allah a zuciyar sa yana jin rashin kyautawar abubuwan dayake aikatawa amma ya rasa dalilin wanan zafin zuciya irin nasa da kuma k'ank'atar abun zai iya b'ata masa rai
Ganin lokacin yaja momy ta takaita zancen ta da Allah ya kareka daga shrrin mutum da aljanu kaje ka kada ka makara kaji to momy kawai ya fada cikin ladabi kafin ya fice izuwa harabar gidan motar sa kirar GLK da Abba yayi masa kyautar a shagalin bikin zagayowar haifuwar sa da yayi kafin zuwan sa Amerika ita yanufa dan yasa laminu mai kula da fulawoyin gidan ya wanke masa ita tas tun jiya
Key yayi mata ya danyi worming dinta kafin yayi horn mai gadi ya walle masa gate ya fice
" Karar fashewa yaji kuma da alama motor sa ce aka daka sakamakon girgizar daya ji tayi, d'okawar tayi dai-dai da lokacin daya kai hannun sa dan kashe sautin kid'a wacce tayi sanadin zamewar hannun nasa daga madannin daya kama ya danna wohoho kar ku so kuga yanda zuciyar sa tayi baki wani dokawar bacin rai take yi kamar wanda ake doka tanbarin yakin duniya ake doka tambarin yakin duniya na uku cikin ta nan take i danuwan sa suka kada sukayi jajir
Second d'aya bai kara shafewa a cikin motar ba ya fito fuuuu,
Dalibai masu wucewa kuwa tsaitsayawa suka yi suna labartawa wayanda basu ga faruwar abun ba kan kace kwabo an zagaye gurin anata maganganu kowa da abunda yake fadawa abokin sa nan dai aka shiga maida zance,
Shi ko Khalil ganin bumpar motar sa a kasa ga kuma singnals dinsa duk sun tarwatse ne yasa ya manta gurin da yake domin a zuciyar sa kawai hango kansa yake cikin wani masifaffen sansanin yak'i
Cikin daga murya ya dubi daliban da suka taru a gurin ! ππ½πΌπ ππΌππ ππΌ πΏπΌππΌπ πππ ππππΌ? yanda ya fada cikin masifa kai kace da wasu yara yan primary yake magana ba yan jami'a ba.
Babu wanda ya tanka masa saima darewa da akayi a gefe da gefe dan bashi damar ganin motar da tayi masa hakan
ai kuwa kamar an kara ninka bacin ransa ganin wanda yayi bar nar har wannan lokacin bai fito dan ganin abunda ya aikata ba wane shafaffe daman ne haka da zai nuna masa iko a garin kano,
"Ina karya ne wallahi babu wanda ya isa"
Da wanan shawarar da zuciyar sa ta d'ora sa a kaine ya karasa jikin motor inda baka iya ganin komai sakamakon tinted glass da aka zagaye ko ina dashi,
Fuskar nan kamar zata tarwatse irin yanda ya daureta yana mai dukan glass din motar da