Showing 39001 words to 42000 words out of 168813 words
Chapter 14 - YARIMA SUHAIL COMPLETE BY SIS NERJA'ART .txt
saboda akwai theater d'in da zai yi ma wasu.
Sultana Sadiya cike da tashin hankali takoma 6angarensu a parlour tayada zango tare da korar duk ma'aikatan da suke ciki nan tafara saffa da marwa tana jiran Sultan Abbas da yatsaya suna magana da Daddyn yarima.
Bayan kamar minti biyar sai gashi ya shigo, da mamaki yatsaya yana kallonta yace lafiya Sadiya naganki haka?
Cike da 6acin rai tace haba Abban sumayya wannan wane irin cin mutuncine yaron nan yakeson yi mana, kaduba kaga duka yaushe akayi bikkinsu dukaba shekara d'aya da rabi kenan ammah wai aure zai k'ara.
Murmushi Sultan Abbas yayi yace toh menene dan zai k'ara aure?
Sultana Sadiya tace kai wai naga kamar baka damuba d'iyarka fa ce za'ayi ma kishiya saikace bakasan ciwontaba?
Murmushin takaici Sultan Abbas yayi yace sadiya nine bansan ciwon Sumayya ba? nine mahaifinta kuma ita da suhail basuda banbanci dukansu 'ya'yanane kuma bari kiji dakaina ma zan iya zuwa inneman masa aurenta dan haka idan zaki sa d'iyarki tanutsu tabi mijinta toh inkuma taje garin haukanta takashe aurenta toh baruwana dan haka shawara tarage taku, yana kaiwa nan yaficce yabarta nan tsaye.
da harara sultana sadiya tarakasa tace ai zamu gani, wayarta tad'auko takira sumayya.
Lokacin Sumayya tana kishingid'e tsakiyar kuyanginta nan aka mik'o mata wayar tayi picking tace ummah ya dai?
ummah cikin fad'a tace ke jakkar inace mijinki yana nan yana shirin k'ara aure.
'yar dariya sumayya tayi tare da mik'ewa tanufi bedroom d'inta tana cewa haba dai yariman nawa? taya zaiyi aure?
Sultana Sadiya ta k'ule sosai cikin tsawa tace ke wace irin bahuwace? ina fad'a miki ammah baki ma damuba.
Sumayya zama tayi saman bed d'inta tace ummah ai nad'auka tsokanata kike.
Sultana Sadiya tace wace irin tsokana yanzu muka zauna da iyayenku akayi maganar har da memartaba kece kawai baki saniba.
Sultana Sumayya a firgice tamik'e tsaye tace ummah yariman nawa zaiyi aure batare da na saniba?
Ummah tace k'warai kuwa sumayya abun bak'in cikinma har da mahaifinki cikin masu goya masa baya.
sumayya k'asa tazauna tare da fashewa da kuka tace ummah yanzu yarima ne zai yaudareni yak'ara aure?
ummah tace ai saisa naso kihaihu ammah kika k'i d'aukar shawarata daman abinda nake guje miki kenan domin nasan halin yaudarar maza saboda basuda tabbas.
Sumayya cikin kuka tace wlh bazan yaddaba babu macen da zata auri yarima duk ma wadda tayi gigin shigowa wlh sai na kasheta domin bazan zauna da kishiyaba.
ummah tace kisa kuma sumayya? kibari mubi komai a hankali nima kinsan ba zan ta6a amincewa ayi miki kishiyaba domin farin cikinki shine nawa.
Sumayya cikin kuka tace kuma dada tasan da maganar? Ummah tace babu fa Wanda bai saniba.
K'ara fashewa tayi da sabon kuka cikin d'aga murya tace wlh k'aryane babu macen da ta isa ta auri mijina wlh ko ma wacece sai na kasheta, tana fad'in haka tayi wurgi da wayarta tare da duk'ewa tana wani irin kuka me tsuma zuciyan mesaurare dasauri tatashi tafito tanufi 6angaren yarima ammah tana shiga taga baya nan.
dan haka tafito tadawo d'akinta tana wani sabon kukan nan tafara watsi da kayan d'akinta dan dressing mirror d'inta batabar komai ba duk ta watsesu k'asa masu fashewa sunayi masu zubewa sunayi sumbatu tafarayi wlh sai nakashe ko wacece ba zan ta6a yadda a auremin mijiba saman gado tafad'a tana me cigaba da risgar kuka,
ma'aikatanta tsaye sukayi daga wajen d'akin sukayi cirko-cirko suna jinta ammah ba mai iya shiga d'akin gudun kar suma 6acin ran yashefesu.....
_Comments_
*nd*
_Share_
_Sis Nerja'artโ๐ป_
๐๐๐
_*YARIMA SUHAIL*_
๐๐๐
_*Written By~Sis Nerja'art*_
_*DEDICATED TO MY DAUGHTER ZARAH*_
https://m.facebook.com/Intelligent-Writes-ASSO-294634797868361/
*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION ยฎ*
*[onward together]*
*{ we give the readers of ours the best out of the bests,,our inks are melodious and dropping a kinda lights to readers }*
THE PEN OF LOVE ๐ HEART TORCHING โค TEARS OF SORROWS ๐ญ CURDLES ๐ GIGGLES ๐ AND MARRIEGE THINK๐
*JUST GIVE US FOLLOW....*โ
_*Wannan page d'in na sadaukar da shi agareku Mamansadiq, Mummyn khadija nd Mrs Dawud ina alfahari da ku a kodayaushe, godia ta agareku bazata ta6a gushewaba wlh ko da page ko ba page nariga na ajeku waje guda acikin zuciyata๐*_
*PAGE* 1โฃ8โฃ
Jin abun gimbiya ya k'i k'arewa yasa haule tafita dagudu tanufi turakar yarima tana zuwa nan guards suke shaidamata baya nan, juyowar da tayi zata koma taji tsayuwar motar yarima dagudu tafita tanufi inda yake.
yarima yana fitowa daga mota daidai lokacin haule ta iso dasauri tazube gaban yarima yarima kallonta yake cike da mamaki, tace ranka yadad'e kagafarceni daman gimbiyace tana cikin d'aki.
yarima shuru yayi kamar ba zaiyi magana ba sai kuma chan yace me yasameta?
Haule duk'ar da kanta tak'ara yi tace ranka yadad'e gaskiya bamu saniba mun dai jiyota a d'aki kamar tana kuka.
yarima baice komai ba domin yagane dalilin da yasa sumayya yin hakan, wucewa yayi yabar wajen, da har zai shige part d'insa domin baiyi niyar zuwa wajentaba, chan kuma sai yafasa yanufi 6angarenta har a lokacin kuyanginta suna tsaye cirko-cirko anrasa mai iya ta6uka wani abu.
ganin yarima yasa suka zube suna k'wasar gaisuwa sannan suka tashi sumi-sumi suka fita sukabar d'akin.
ahankali yabud'e bedroom d'in yashiga mamakine yakamasa ganin yadda tawatse komai na d'akin, sannan yasafke kallonsa kan sumayya da take raku6e k'asa saikace wadda tayi rashin iyayenta tana ruzgar kuka, jin anshigo yasa tad'ago kai ganin yarima yasa tamik'e dasauri tanufi wajensa tare da rungumesa tana shashek'ar kuka tace yarima kafad'a min cewar abinda naji ana fad'a akanka k'aryane.
yarima da yake tsaye yace sumayya me kikaji akaina?
sumayya d'ago kai tayi takallesa tace aure wai zaka k'ara.
janye idonsa yayi daga kallonta yace hakane aure zanyi.
gimbiya turesa tayi a firgice tare da matsawa tace suhail aure? ni zakayi ma kishiya?
Yarima Suhail murmushin mugunta yayi yace tabbas aure zanyi sumayya domin ke tuni kikayi wasa da damarki.
cikin d'aga murya sumayya tace enough suhail! enough!!! nan tafashe da sabon kuka tace dan Allah kafasa auren nan wlh zan kula da kai.
ta6e baki yarima yayi yace kin rin rasa damarki dan haka k'ara kawai kiyi hak'uri koma wacece tashigo kikar6eta hannu biyu kuyi zaman lafiya.
sumayya cikin k'araji tace ank'i d'in, wlh babu wadda ta isa ta auremin miji domin gidan nan ba za'a ta6a samun zaman lafiya ba.
yarima suhail fuskarsa babu alamun wasa yace kidinga tace maganar da kike a gaban yarima suhail domin kinsan wanene ni bana son raini, sannan indai kinason zaman gidana dole kiso abinda nakeso kuma kuyi zaman lafiya.
gimbiya sumayya a fusace tace Idan ank'i fa?
murmushin mugunta yarima yayi yace igiyar aurenki zata fara rawa, yana kaiwa nan yajuya yaficce yabar sumayya tsaye sake da baki tana binsa da kallon mamaki, yana fita tasake rushewa da kuka tace nashiga ukku yanzu ni suhail zai yaudara?
kamata ace zaiyi ma kishiya har yana ik'irarin sakina.
saida taci kuka me isarta sannan tajawo wayarta da tawullar taga har screen d'in yatsage dan haka tad'auko d'ayar takira zinat har tatsinke ammah zinat bata d'agaba.
A fusace gimbiya tamik'e tad'auko alk'yabbarta tasaka tafito nan duk kuyanginta suka take mata baya duk wanda zai ganta a lokacin yasan tana cikin 6acin rai, tana fitowa bata zarce ko'inaba sai sai turakar iyayenta, a parlour ana ta kwasar gaisuwa bata kalli kowaba ganin ummanta bata parlour yasa tashige bedroom.
lokacin sultana sadiya tana zaune saman bed d'inta tana waya, ganin yadda sumayya tashigo yasa arikice tamik'e tsaye tace sumayya lafiya?
dagudu sumayya tazo tafad'a jikinta tare da fashewa da sabon kuka tace ummah nashiga ukku yanzu ni suhail zaiyi ma kishiya.
Sultana Sadiya rarrashinta tashiga yi tace haba sumayya kiyi hak'uri man kinsan dai tunda memartaba ya amince toh babu wanda ya isa yace a'a dan haka kibarsa kawai yayi auren munga ta yadda amaryar zata zauna lafiya, sai tasan tashiga rayuwarki dakanta zata fita tabar miki gidan.
sumayya kallon sultana sadiya take cikin rashin gamsuwa, ta bud'e baki zatayi magana kenan nan wayarta tafara ringing ganin zinat ce yasa takalli sultana sadiya tace ummah ina zuwa.
mik'ewa tayi tafito tashiga d'ayan bedroom d'in sannan tayi picking d'in wayar ko sallama batayiba tafashe da kuka tace zinat nashiga ukku.
zinat a firgice tace sumayya me yake faruwane?
sumayya kasa magana tayi sai ma kuka da takeyi, zinat cewa take sumayya kiyi min magana mana please nima inbaso kike inyi kukanba.
sumayya tsagaitawa tayi daga kukan da take tace zinat yarimana kasheni yakeson yi wai aure zai k'ara.
'yar dariya zinat tayi tace yoh d'an wannan zaisa hankalinki yatashi?
sumayya daina kukan tayi tace zinat kin ko ji abinda nace?
zinat tace na ji man ba aureba? yaje yayi kema ai wani sauk'in ne zaki samu domin yanzu zaki samu right d'in zuwa inda kikeso kinga business d'inmu zaya ha66aka, koma wacece kibarta tashigo wlh dakanta zata bar miki gidan.
sumayya tace haba zinat kamar ya inbari yayi aure ya za'ayi kamata ace anmini kishiya
zinat tace haba sumayya matsalata da ke kiyita abu kamar baki wayeba, kinsan ni kaina ba zan amince ayi miki kishiyaba dakanmu zamu fitar da ita gidan.
Sumayya jinjina kai tayi tace yanzu nafahimceki baby, zinat tace yauwa dear ai nasan zaki fahimceni nan zinat taita k'unsa mata makirci saida taga sumayya tad'auka sannan sukayi sallama takashe wayarta.
sumayya dawowa tayi wajen sultana sadiya tace ummah shikenan nad'auki shawararki ammah wlh bazan ta6a bari amaryar tasamu zaman lafiya a gidanaba.
cike da jin dad'i sultana sadiya tace gaskiya naji dad'i da kika fahimceni ai inma kin bari tazauna lafiya toh baki haihuba kibarshi kawai daga shi har amaryar tasa sai sun san sun ta6o tsuliyar dodo.
dariyar jin dad'i sumayya tayi tace za'a fara babban wasa dominba mai ta6a gimbiya sumayya azauna lafiya, muje zuwa.
__________________
Zarah duk yadda taso tacire damuwa a ranta ammah ta kasa kawai dai tana 6oyewane dan kar iyayenta sukaranto halin da take ciki, ga malam bello da kusan kullum sai ya kirata ammah takasa fad'a masa matsalar da ake ciki.
shi kansa ya sha tambayarta abinda yake faruwa domin jin yadda duk tacanza masa saidai tace bakomai.
Yau Zarah ita kad'aice gidan kasancewar mama taje asibiti raka yaya Rauda awo, Aysha kuma taje bikkin k'awarta da akeyi.
ji tayi bata iya barin malam bello batare da yasan halin da ake cikiba dan haka wayarta tad'auko tanaso takirasa ammah ta kasa sai juya wayar take a hannunta ta rasa yadda zatayi daga k'arshe dai tadaure takirasa.
malam bello baiyi picking ba har saida tatsinke tana shirin tak'ara kiransa sai gashi ya kira, zuba ma wayar ido tayi ta rasa yadda zatayi tad"auka domin batasan abinda zatace ba, saida taga takusan tsinkewa sannan tayi picking tare da yin sallama.
malam bello ya amsa mata nan suka gaisa sannan Zarah tace malam idan kana kusa dan Allah kazo akwai maganar da nakeso muyi.
Cike da jin dad'i malam bello yace ganinan ko zuwa kinsan dama nakwana biyu bansaki a idonaba fatana dai ba laifi nayiba.
Zarah duk yadda taso tamaida kukanta kasawa tayi muryarta tana rawa tace babu komai sai kazo, dasauri takashe wayar batare da taji abinda zai ceba takife kanta saman katifarsu tashiga rera kuka cike da tausayin malam bello da kanta domin batasan yadda shima zai fahimci maganarba
bayan kamar minti biyar wayarta tashiga ruri ganin malam bellone yasa dasauri tamik'e taje toilet tawanke fuskarta sannan tafito tasaka hijab d'inta tafita jikinta duk a sanyaye.
A k'ofar gidansu tasamesa tsaye yana jiranta kanta yana sadde k'asa gudun kar yagano yanayin da take nan tayi masa sallama
malam bello fuskarsa a sake ya amsa mata tare da tambayarta mutanen gida tace duk suna lafiya, daganan shuru yabiyo baya sai chan malam bello ya nisa yace Zarah Allah yasa ba laifi nayiba dan fitama zanyi nafasa nace bari infara amsa kiran gimbiyata sannan sai inwuce
Zarah runtse idonta tayi tana jin wani iri a ranta jin kanta yafara sarawa yasa tajingina da bango.
malam bello rikicewa yayi yace Zarah lafiya? meyake faruwane? wani abu yasamu su abbah? Please kifad'amin matsalarki.
Zarah batare da ta bud'e idontaba tashiga girgiza masa kai hawaye suna zuba cikin muryar kuka tace ko d'aya malam bello babu abinda yafaru, inaso ne kayafe min wlh ba a son raina hakan takasanceba saidai dan ba yarda zanyi kuma banaso ink'i bin umirnin iyayena kayi hak'uri da..... sai kuma tayi shuru tare da fashewa da kuka.
malam bello jikinsa ya yi sanyi sosai yace Zarah da me zan hak'ura? kiyi min bayani, su Abbah basu amince da ni inkasance surukinsuba ko?
Zarah dakyar tabud'e idanuwanta da suka kumbura saboda kuka tace su abbah sunyi min miji muhak'ura da juna haka Allah yak'addara kai ba mijina bane.
Malam bello murmushi yayi Wanda yafi kuka ciwo yana kallon Zarah da taketa kuka yace Zarah daman kan wannan 'yar maganar kike ta faman kuka?
Zarah tsagaitawa tayi da kukan da take tace bakaji abinda nace bane? miji fa akayi min?
Malam bello daurewa yayi cikin rashin damuwa yace najiki mana, toh menene Zarah? dole kiyi hak'uri kibi za6in iyayenki domin ba zan ta6a yadda inbaki shawara akan kibijire ma iyayenkiba, Allah daman ya k'addara ba matata bace ke, ita rayuwa duk yadda tazo maka kayi hak'uri kakar6eta domin shi aure nufine na ubangiji babu mai auren matar wani kar kimance mune muke haukanmu ammah Allah yariga da yatsara ma kowa yadda rayuwarsa zata kasance wlh nabaki goyon baya kiyi ma iyayenki biyayya insha Allahu zakici ribar biyayyar da zakiyi musu kema kuma Allah zai baki wad'anda zasuyi miki biyayya domin su iyaye sun wuce abin wasa yakamata muguji fushin iyaye, ni yanzu shawarar da zan baki itace kiyi ma iyayenki biyayya insha Allahu zakici moriyar hakan.
Zarah da tunda yafara maganar tazuba masa ido hawaye kawai suke zuba daga idonta dakyar tabud'e baki tace yanzu kana nufin ka rabu da ni?
malam bello murmushi yayi wanda iyakansa baki sannan yace tabbas Zarah narabu da ke domin ko nine bazan iya bujirema umirnin iyayenaba saidai inaso kisani sonkine da nake yajawo hakan kuma har abada bazan daina sonkiba saidai inyi addu'an Allah yarage min sonki a cikin zuciyana, fatana Allah yasa wanda zaki aura yasoki fiye da yadda nake sonki, kema inaso kiyi min alk'awali d'aya shine zai tabbatar min da kina sona.
Zarah cikin kuka tace wane irin alk'awali kakeso inyi maka wlh indai shi zaisa kagane ina sonka toh na amince koma minene kafad'a.
malam bello d'an guntun murmushi yayi sannan yace inaso kiso mijinki fiye da yadda kike sona sannan kinuna masa kulawa kar kisa6a masa kiyi masa biyayya indai ba hanyar Allah yanemi yakauceba.
Zarah girgiza kai tashiga yi tace bana tunanin zan iya son wani fiye da yadda nake sonka bazan iya d'aukar alk'awalin da nasan bazan iya cikawaba.
malam bello juyawa yayi cikin dabara yagoge hawayen da suke shirin zubo masa sannan yace wannan zai shaida min da cewar bakya sona.
Zarah girgiza kai tashiga yi tace malam kar kace haka wlh ina sonka shikenan na amince zanyi duk abinda kace.
malam bello juyowa yayi yace dagaske kin d'aukar min alk'awali?
gyad'a masa kai tayi tace eh saidai kayi hak'uri ba zan iya tursasa zuciyana taso wani fiye da yadda take sonkaba.
murmushi malam bello yayi yace natabbata zaki ma soshi indai ya amsa sunansa namiji wanda yadace mace taso, dan haka ina miki fatan alkhairi zarah idan nasa6a miki kiyafemin domin inaso wannan takasance had'uwarmu tak'arshe.
zarah fashewa tayi da wani sabon kukan tare da durk'ushewa k'asa cikin kuka tace nagode sosai malam bello hak'ik'a kai masoyinane nagaskiya tabbas duk macen da ta aureka tayi dacen miji fatana Allah yabaka wadda zata soka fiye da ni, bazan ta6a daina yi maka addu'a ba domin kabani gudunmawa sosai a rayuwana wlh *K'ADDARA CE* kawai tarabani da kai ammah ka cancanci kasancewarka mijina.
malam bello murmushi yayi yace kar kidamu zarah daman kyaun kowane musulmi ya yarda da k'addara me kyau da marar kyau, ina miki fatan alkhairi nabarki lafiya .
juyawa malam bello yayi yatafi yana jin wani k'unci acikin ransa ji yake inama yayi kuka ko yasamu sauk'in abinda yake ji, yana jin kukan zarah tana ta kiransa ammah yak'i juyowa gudun kar shima yaga yanayin da take yayi kuka.
zarah da take tsugunne tana kuka tare da k'walah masa kira saida taga yayi mata nisa sannan tatashi takoma gida tafad'a saman katifarsu tacigaba da kukanta.
Tun daga ranar zarah da malam bello suka daina waya saidai text shima na gaisuwane kawai sukeyi, daurewa kawai take tacigaba da addu'a akan Allah yaza6a mata wanda zaifi zama alkhairi, su yaya Rauda su suke k'ara kwantar mata da hankali da tayi hak'uri tacigaba da addu'a.
**** ***** ***** ****
memartaba kamar yadda yafad'a hakan kuwa akayi domin kiran yarima suhail yayi yace yafad'a ma iyayen yarinyar zuwa gobe zasu aiko da komai na neman aure domin basuson aja lokaci dayawa.
yarima suhail a firgice yad'ago yakalli memartaba yace ranka yadad'e duk dawuri za'ayi haka? nad'auka za a bi Komai ahankali.
murmushi memartaba yayi yace suhail kenan toh me zamu jira? k'ara dai muyi komai dawuri domin banaso ana d'aukar lokaci dayawa ammah indai iyayen yarinyar suka nemi aja lokaci toh lafiya lau saidai bazanso hakaba
yarima yace toh ranka yadad'e.
memartaba yace koma mi kenan kaje kuyi magana da waziri domin shine zaije yanemo maka auren sai ku yanke shawarar yadda zaku tafiyar da komai.
duk'awa suhail yayi yakwashi gaisuwa sannan yayi ma memartaba sallama yatashi yafita yanufi 6angaren iyayensa.
yana shiga daidai lokacin daddynsa yana shirin fita ummi tana bayansa cike da girmamawa yagaishesu sannan suka koma suka zauna, nan yake fad'a musu yadda sukayi da memartaba gabad'ayansu sun nuna farin cikinsu.
ummi tace toh zan kira iyayen yarinyar infad'a musu halin da ake ciki, sannan driver d'in da yakaini shine
08, February 2025
Shuraihu Usman
jjjjj