Showing 3001 words to 6000 words out of 168813 words

Chapter 2 - YARIMA SUHAIL COMPLETE BY SIS NERJA'ART .txt

08 Aug 2024

100509

toh itace takirasa shima daga gaisuwa yake kashe wayarsa.




Bayan wata biyu akasha bikkunsu anyi shagali sosai ak'allah saida akayi events kusan guda biyar ammah dakyar aka samu yarima suhail yaje d'aya daga ciki shima saida ummi tasa baki, ammah sauran duk k'in zuwa yayi k'arshe idan yaga za'a takurasa sai yakashe wayoyinsa yace kar abari kowa yashigo sashensa,




ranar asabar aka d'aura aure, auren da dubban mutane daga nahiya dadama suka hallara,


amarya ta sha kyau har ta gaji, inda amarya tatare a part d'in yarima da aka fitar da shi a cikin gidan sarauta, k'arshen gata an nuna mata babu abinda ba a zuba masu na amfani ba.




kowa yazo sai ya yaba tsarin gidan domin babu wanda zai ce acikin gidan sarautane saboda part d'in yarima antsarasa kamar a turai inda aka fidda ma sumayya 6angarenta sai na yarima sai wani part d'in da aka fara ginawa aka aje sai kuma part na ma'aikata da bayinsu maza da mata.








da daddare saida shahid yayi dagaske sannan yasamu yarima suhail yayi wanka yashirya suka fito suka rakasa gidansa.


suna ta tsokanarsa shidai yayi shuru yakyalesu saboda wani irin haushi da yakeji, hatta su kansu haushinsu yakeji tunda su suka matsa masa sai yaje.
saida suka rakasa har part d'in amaryarsa sannan sukayi masa sallama suka tafi.




yarima suhail 6angarensa yabud'e da mamakinsa yaga dogarawansa zaune a k'asa suna ganinsa suka zube suna kwasar gaisuwa, yarima suhail batare da ya amsaba yace kun iya tafiya ,


k'ara kwasar gaisuwa sukayi sukace toh ranka yadad'e sannan sukace atashi lafiya sai suka tashi suka fita




bedroom d'insa yashiga komai na ciki very need da mamaki yakalli yadda aka shimfid'a masa farin bedsheet mai kyau a saman gadonsa d'auke kansa yayi yawuce yashiga toilet yawatsa ruwa , bayan ya fito yayi shirin kwanciyarsa yahaye gadonsa.






A 6angaren gimbiya sumayya bayan ta gama shirinta su jakkadiya suka take mata baya zuwa turakar yarima, da sallamarsu suka shiga ganin baya parlour yasa suka kwank'wasa masa bedroom,


yarima da yake kwance yabada izinin ashigo, da mamaki yake kallonsu sumayya da suka shigo, nan su jakkadiya suka zube k'asa suna kwasan gaisuwa, ita dai sumayya zuba masa ido tayi tana kallonsa cike da son mijinta,




haydar bai damu da kallon da take masaba yace lafiya kukazo man d'aki?


jakadiya da take durk'ushe tace ranka yadad'e yarima mai jiran gado daman dada ce tace mukawo maka amarya,




yarima suhail shuru yayi baice komaina yamaida idonsa yalumshe.
ganin haka yasa su jakadiya sukace mun barku lafiya gimbiya da yarima Allah yaja da ranku atashi lfy.




Gimbiya sumayya tace idan kun fita sai kurufe mana k'ofan,


yarima suhail yana jinta mamakine yakamasa domin bai ta6a ganin amarya hakaba.






suna fita sumayya tatako ta iso bakin gadon tazauna gefen da yarima yake kwance, suhail batare da ya bud'e idonsaba yace kije kid'auro alwallah,


sumayya turo baki tayi sannan tatashi tashiga toilet d'insa tad'auro alwallah,




lokacin da tafito yarima yana shimfid'a darduma nan yajasu sallah raka'a biyu sukayi sannan yakama kanta yayi mata addu'a.




bayan ya gama yayi mata tambayoyi akan addininta baiyi mamaki ba da yaga bakomai take iya basa amsaba, wata amsarma ba daidai take basaba nan ya Ida tsurewa da lamarin sumayya ammah kuma sai yashare, mik'ewa yayi yanufi saman gadonsa yabarta nan saida yakwanta sannan yace ga nama nan idan zaki ci.


haushine yakama sumayya ganin yadda takejin labari wajen friends d'inta yadda mazajensu suka nuna musu tattalin so a daren aurensu ammah ita ba hakaba, cikin ranta tace lallai yarima halinsa sai shi.




tashi tayi itama taje saman gadon takwanta bayansa saida sukayi kusan minti goma ahaka ammah sumayya taga yarima bai da alaman nemanta dan haka tarungumesa ta baya,




yarima shareta yayi, ganin haka yasa sumayya tajuyosa tare da kwanciya saman jikinsa, yarima bud'e idanuwansa yayi da suke lumshe yawurga mata harara yace ke bakida kunya?


sumayya turo baki tayi tace yarima yau fa daren amarcinmune ammah shine kake shirin yin bacci kabarni hannu takai tana shafa jikinsa.




yarima da mamaki ya gama cikasa kasa komai yayi, jin hannunta yayi yana yawo cikin jikinsa, dasauri yarik'e hannun yace ke bakida kunya?




sumayya tace ammah ai naga ba abun kunya bane tunda munyi aure,
bakinta takai cikin nasa tana kissing d'insa cikin wani irin salo nan da nan yarima yafita hayyacinsa ya'aje sarautarsa gefe yabiye mata suka sha amarcinsu.




yayi mamaki sosai ganin yadda sumayya take zak'ewa babu alamun tsoro atare da ita,
a yadda yasameta bai kawo ma ransa komai ba gudun kar zargi yashiga tsakaninsu dan haka dayasamu nutsuwa janye jikinsa yayi yaje yayi wanka sannan yadawo yayaye bedsheet d'in yayi yakwanta tare da juya mata baya,


sumayya ma tashi tayi taje tayi wanka sannan tadawo bayansa yakwanta tare da rungumarsa ta baya,




da asuba yarima har yadawo masallaci ammah sumayya bata tashi tayi sallah ba, saida yayi dagaske sannan yasamu sumayya tatashi tayi sallah tana ta k'unk'uninta, komawa yayi yakwanta yana kallonta sallarma shaf-shaf tayita ko addu'a bata tsaya yiba tahaye gadon.






dasafe jakkadiya ce tatashesu nan tashigo takwashi gaisuwa sannan tad'auki bedsheet d'in tafita.




turakar dada taje, tun da dada tahangota take fara'a jakkadiya duk'ewa tayi takwashi gaisuwa sannan tace ranki yadad'e ga zanen gadon,


dada tace masha Allah bud'e mugani ko da jakkadiya tabud'e babu komai a jikinsa nan hankalin dada yatashi tace nashiga ukka ya akayi haka kar dai ace yarinyarnan ba budurwa bace.


jakkadiya duk'ar da kanta tayi tace ranki yadad'e ai ita mace budurwa ba dole sai anga jiniba ake gane budurwace wasu basu jinin budulci,




dogon numfashi dada taja tace hakane shikenan yanzu aje awankesa amaidasa ma'ajinsa ammah naso ace kowa ya shaida.








kowa na gidan kasa kunne yayi yaji ana gud'a ammah shuru kuma kowa tsoron tambaya yakeyi, kasancewar al'adarsuce duk amaryar da aka kowa idan budurwace da anga jinin ake ganewa nan za'a d'auki zanen gadon ayi ta yawo ana gwadawa daganan sarki zai bada shanuwa da rago ayanka ma amarya.






yarima suhail har yagama shirinsa ammah gimbiya sumayya tana kwance tana kwasar baccinta haushi ne yakamasa yaja tsaki yace mutum kamar kasa sai bacci, da mugunta yakai mata bugu, firgit tayi tafarka daga baccin




haushi ne yakamata ganin yarima tsaye, d'aure fuska tayi tace haba yarima ya za'ai katasheni bayan jiya kaine kahana ni bacci, gaskiya kadaina domin idan ina bacci ba'a tashina.
yarima da mamaki yake kallonta jin tace shi yahanata bacci bayan itace takawo kanta,






tashi tayi tad'auko alkyabbarta tasaka sannan taficce tabarmasa d'aki,
tsaki yarima yaja sannan yacigaba da abinda yake,


bayan ya gama yafito parlour yatarar da anshirya masa breakfast dogarawansa suna ganinsa suka zube suka kwashi gaisuwa sannan d'aya daga cikinsu yayi serving d'insa,


kad'an yaci sannan yatashi nan suka rufa masa baya sunacewa takawarka lafiya yarima.
tsayawa yayi batare da ya juyoba kamar ba zaiyi maganaba sai kuma yace kuje kawai zan nemeki,
su dukansa sukace angaisheka yarima umurninka muke cikawa Allah yatsare mana kai mun barka lafiya.




daganan yawuce yacigaba da tafiyarsa shi kad'ai duk inda yagifta kwasar gaisuwa ake ahaka har yazo 6angaren gimbiya ko da yashigo parlour saida ma'aikatanta sukayita kwasar gaisuwa ko inda suke bai kallaba yawuce direct bedroom d'inta,


lokacin gimbiya sumayya tana zaune bayinta suna shiryata, bud'e k'ofar da akayine yasa duk suka maida hankalinsu domin suga mai shigowa ganin yarimane yasa suka zube gaba d'ayansu suka kwashi gaisuwa sannan suka mik'e zasu fita


gimbiya sumayya ce tace ina zakuje batare da kun gama shiryaniba,
yarima kallonta yake cike da mamaki sannan yanuna musu k'ofa dasauri dukansu suka fita har suna tuntu6e.




takowa yayi cikin takunsa na k'asaita ya iso bakin gadon, gimbiya sumayya tace haba yarima ya zaka korar minsu alhali basu gama shiryaniba,


zama yarima yayi kusa da ita batare da ya kalletaba yace ke ba zaki iya shiryawaba har sai sun shiryaki?
sumayya ta6e baki tayi tace ammah ai tun ina gaban iyayena su suke min kwalliya, banza yarima yayi yakyaleta dan haka taci gaba da shirinta.
banza yarima yayi yakyaleta.




bayan ta gama kiran jakkadiya tayi tace akawo mata breakfast d'inta a nan, cikin minti biyar ancika mata gabanta da abinci da kayan marmari iri-iri


nan tazauna zata ci kallon yarima tayi tace kaifa ba zakaciba,


yarima batare da ya kalletaba yace no kici kiyi sauri kigama muje mugaishe da su maimartaba,


gimbiya sumayya tace tun yanzu?
yarima bai tanka mataba,
ganin haka yasa tacigaba da breakfast d'inta domin tasan halin mutumin nata magana tsada take masa......










_Comments_
*nd*
_Share_














_Sis Nerja'artโœ๐Ÿป_
?๐Ÿ‘‘๐Ÿ‘‘


_*YARIMA SUHAIL*_

๐Ÿ‘‘๐Ÿ‘‘๐Ÿ‘‘






_*Written By~Sis Nerja'art*_






_*DEDICATED TO MY DAUGHTER ZARAH*_








*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION ยฎ*
*[onward together]*
*{ we give the readers of ours the best out of the bests,,our inks are melodious and dropping a kinda lights to readers }*
THE PEN OF LOVE ๐Ÿ˜˜ HEART TORCHING โค TEARS OF SORROWS ๐Ÿ˜ญ CURDLES ๐Ÿ™‚ GIGGLES ๐Ÿ˜ AND MARRIEGE THINK๐Ÿ’‘
*JUST GIVE US FOLLOW....*โœ”






_*Sak'on gaisuwata agareku My Haleema H.A.S nd mummy Zill๐Ÿ˜๐Ÿ‘Œ*_






_Wannan page d'in nakune nabaku shi a kyauta my fan's๐Ÿ˜˜_






page 3โƒฃ






bayan ta gama d'auko alkyabbarta tayi tasaka sannan suka jera ita da yarima suka fito, a k'asa suke tafiya a jere, kuyangin gimbiya suka take musu baya ahaka har suka isa fada nan mutane suka dinga kwasar gaisuwa, d'aga musu hannu kawai yarima yakeyi har suka isa gaban maimartaba dasauri dogarawa sukazo suka kare su yarima daga ganin mutane suna cewa Allah yataimaki yarima da gimbiya azauna lafiya, har saida suka tabbatar da yarima da gimbiya sun zauna sannan suka matsa nan su yarima suka kwashi gaisuwa wajen sarki nan fadawa suka d'auka, sarki ya amsa muku yarima da gimbiya, sarki yana godia yarima mai jiran gado ku ma angaisheku.








sannan yarima yatashi yaje kujerar da take kusa da sarki yazauna, ita dai gimbiya tana tsugunne a k'asa sai yatsina take tana kallon mutane a wulak'ance.




maimartaba ne yad'auko wata alkyabba maikyau da tsada yamik'a ma gimbiya sumayya hannu biyu gimbiya tasa takar6a tare da yin godia sannan tamik'a ma jakkadiya, jakkadiya tazube gaban sarki tace ranka yadad'e gimbiya tana k'ara godia Allah yaja da ran sarki mai adalci sarkin sarakai,


gyad'a kai sarki yayi nan fadawa gaba d'ayansu suka d'auka angaisheki gimbiya sarki ya ji godiar ki.






nan sarki yayi musu nasiha tare da yi musu addu'an zaman lafiya, sannan suka k'ara kwasar gaisuwa suka tashi suka fito, cikin gida suka shiga turakar dada,




nan suka gaisheta itama tayi ma gimbiya kyauta sannan suka wuce 6angaren ummi suka gaisheta itama kyauta tayi ma gimbiya sannan daganan sukaje 6angaren umman sumayya suka gaisa daga nan suka koma 6angarensu




suna shiga yarima yanufi hanyar zuwa 6angarensa ganin gimbiya tana niyar binsa yasa yadakata da tafiyar batare da ya kalletaba yace zaki iya tafiya 6angarenki domin yanzu inason inhuta bai jira jin abinda zata ce ba yawuce part d'insa.




Gimbiya sumayya tsaye tayi takaici duk ya cikata ganin yadda yarima yadizgata gaban bayinta, tsawa tadaka musu tace suwuce subata waje dasauri duk suka bar wajen,


nan gimbiya tanufi part d'inta cike da jin haushi.









haka sukayi sati d'aya suna shan amarcinsu tun yarima bai kulata daga baya sumayya saida tasan yadda tayi yarima suhail yad'an sake mata, ammah idan yana jin 'yan miskilancin ko sarautar takad'a masa toh ko kallon inda take bata yi.














bayan sati guda gimbiya sumayya ce kishingid'e a parlourn ta inda bayinta suke zagaye da ita wasu suna mata tausa wasu fifita, d'aya tana karanta mata labari, wayartace tashiga ruri baiwar da take rik'e da wayoyintane tamik'a mata, cike da Jin dad'i sumayya tayi picking d'in wayar ko sallama batayiba tace haba zinat ai ni fushi nake da ke wai har ayi aurene bakya garin,


daga chan 6angaren Zinat tace toh sarkin k'orafi yanzu dai gani a k'ofar gidanki dogarawa sun hanani shiga kituro a shigo da ni,


cike da jin dad'i sumayya tace yanzu ko zan aiko, kallon d'aya daga cikin bayinta tayi ta yamitse fuska tace ke jeki waje kishigo min da bak'uwata,


dasauri tamik'e tace angama ranki yadad'e


batafi minti biyar da fitaba sai gasu sun shigo da zinat, sumayya tashi tayi daga kishingid'en da take tace oyoyoo k'awata takaina, nan bayi suka zube suka kwashi gaisuwa wajen wadda aka kira da zinat sai yamutsa fuska take tana taunar chewing gum tazauna saman kujera, nan gimbiya sumayya takori duka bayin daga d'akin,




gimbiya sumayya kusa da ita takoma tazauna kafin kace mi ancika gaban zinat da kayan ciye-ciye da na shaye-shaye, sumayya cike da farin ciki tace k'awata kenan ai ban d'auka zan ganki a yanzu ba,


zinat kur6an ruwan inibi tayi sannan ta aje cup d'in tace wlh jiya nadawo garin shine nace ba zan fad'a mikiba surprise kawai zan baki yau.
.
murmushi Sumayya tayi tace kin ko kyauta wlh, na ma d'auka sai kin gama hutawa zaki dawo domin na sanki da son tafiya kihuta, zinat tace ai saboda ke nadawo amarya kinsha k'amshi kinga ko yadda kika koma?


murmushin jin dad'i gimbiya sumayya tayi tace ya nakoma dear?




zinat tace ai kin fito a gimbiyarki ta ainahi ke ni bani insha kifad'a min yadda kuke zaune da wannan miskilin mijin naki.


sumayya gyara zamanta tayi tace ai lafiya lou miskilanci kau saidai abinda yayi gaba, zinat tace ke ya batun first night d'inku,


dariya gimbiya sumayya tayi tace ai babu abinda yagane game da hakan kinsan nayi amfani da magungunan da kikasa aka had'a min wlh har tausayi yabani ganin bai gane komai ba.




ta6e baki zinat tayi tace ke inbanda abinki wa yace miki ana tausayin maza indai kina lalla6a miji ai sai yarainaki, shawarace zan baki daga inda miji yafara d'aga miki murya ke kinuna masa kinfi sa hauka,




sannan ba kowane lokaci zaki dinga ba mijinki kankiba saboda idan kika saba masa da haka toh sai kin gunduresa yaji ya gaji da ke daga k'arshema sai kiga kishiya




zaro ido sumayya tayi tace kishiya kuma? zinat gyad'a kai tayi tace eh man ai wlh namiji ba a basa amana ke nifa saboda tsoron halin maza yasa nakasa aure nake cin karena babu babbaka dukiya ce natara bakin gwargwado a lokacin da kuma naji ina buk'atar namiji ga mazanan birjit sai na za6a, inma macen nake buk'ata kema kin sanni.






dariya sumayya tayi tace hakane k'awata wlh kin kawo shawara mai kyau, ke nima fa sonake inga natara dukiya dan ban had'a kud'i da komai ba tunda ga mulki ga miji kinga dukiya yarage dan haka business zan fara. saidai anya zamu kwashe lafiya da yarima?






harararta zinat tayi tace kefa matsalata da ke wani lokacin baki da ganewa ammah asannu zan ganar da ke yadda zaki fahimta, ammah nagargad'eki da lallashin miji bare ma wannan mijin naki idan yashareki kema kifita harkarsa ke da nice da nasan yadda zan juyasa yakoma a tafin hannuna,




gimbiya sumayya tace hmm ba dai yarima ba anya akwai macen da zata iya juyasa?
zinat tace kefa matsalata da ke kenan bakida ganewa, kedai kigwada kigani dakanki zaki bani labari, yanzu dai taso mushiga daga ciki.




mik'ewa sumayya tayi tana dariya zinat tana binta a baya suka shige bedroom,
a ranar haka zinat tawuni gidan gimbiya sumayya tana k'imsa mata makirci iri-iri har saida taga gimbiya sumayya ta hau ta zauna sannan tabarta.










Tun daga ranar gimbiya sumayya tadaina shiga sabgar yarima shima shareta yayi yacigaba da hidimar gabansa,




yarima tun bai damuwa har abun yazo yafara damunsa yanzu tsawon wata d'aya da aurensu tun satin farko rabonsa da gimbiya domin ko d'akinsa bata zuwa.








yau da dare kasa daurewa yayi dan haka yatashi yasaka alkyabbarsa yafito yanufi 6angaren gimbiya sumayya, da key d'insa yabud'e direct bedroom d'inta yashiga chan tsakiyar gado yahangota ta baje sai baccinta take ahankali yataka yaje yahau saman gadon.






gimbiya sumayya da take bacci jin ana shafata yasa tafarka, da mamaki take kallon yarima, chan kuma sai tad'aure fuska tace lafiya?


yarima cigaba yayi da abinda yake kamar ba zaiyi magana ba sai kuma chan yace sumayya yanzu saboda Allah hakan da kike min kina ganin kin kyauta? hak'k'ina nazo kar6a,




gimbiya sumayya janye idonta tayi daga kallonsa cikin ranta tana jin dad'in shawarar da k'awarta tabata ganin yau dakansa ya aje girman kan yazo d'akinta,


ganin yarima suhail yana shirin rikitata yasa tajanye jikinta gefe tace haba dan Allah yarima wai menene haka nifa a gajiye nake.




da mamaki yarima yake kallonta yace haba sumayya saikace wadda tayi wani aiki nidai yanzu kibari inyi inyaso daga baya sai kiyita baccinki.




gimbiya sumayya komawa tayi takwanta tare da juya masa baya tace ni ba zan iyaba gaskiya, yarima binta yayi yana lallashi dakyar ta amince masa shima saida taita masa k'orafin ta gaji kan dole a k'arshe yahak'ura yabarta batare da ya ida samun nutsuwaba,




toilet d'inta yashiga yayi wanka sannan yadawo yakwanta tare da juya mata baya cike da mamakin yadda sumayya tasauya hali .






gimbiya sumayya ko murna takeyi ganin ta d'an ci nasara har Yarima suhail ya zo d'akinta yau, kuma ya aje girman kai da sarautar ya lallasheta.












Tun daga lokacin yarima shi yake biyota d'akinta ko da ace ya yi mata wulak'anci a wani wajen ita kuma sai ya nemeta take ramawa sai ya-yi dagaske yake samun hak'insa a wajenta ahaka suka haura wata shidda ammah ko 6atan wata bata ta6a yi ba,




dada ta fi kowa damuwa domin tisata gaba take a d'aki tana tambayarta ko akwai abinda take sha ita dai gimbiya a'a take cewa, dada tace a'a gimbiya indai akwai abinda kikeyi, gimbiya saidai tayi dariya tace dada inda ina yin wani abu ai da kun gane, dada saidai tace toh Allah yakawo.






ko da yarima yazo yagaishe da dada bayan sun gaisa dada tace yarima wai

08, February 2025
Shuraihu Usman

jjjjj

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login