Showing 15001 words to 18000 words out of 168813 words
Chapter 6 - YARIMA SUHAIL COMPLETE BY SIS NERJA'ART .txt
ai nafad'a maka 'ya'ya mata dad'i garesu,
malam yace hakane sannan yakai dubansa ga zarah da take tsugunne tana ta wanke-wanke, yamutsa fuska yayi yace Asma'u wlh d'iyar chan duk cikin 'ya'yana ita kad'aice batada k'ashin arzik'i wani ma lokacin ji nake anya jininace?
ummah tayi karaf tace a'ah malam wannan cin mutuncin da me yayi kama idan ba d'iyarka bace toh wanene ubanta? ko akwai wani mijin da na aura bayanka? ko kuma kana nufin ina bin mazan banza.
malam yace a"a zainabu nidai ina nufin kwata-kwata bata d'auko halinaba, kiduba kiga ko farin jinin samarin nan ita batadashi,
ummah tace ah toh yanzu naji bayani, ai malam kakalli wannan munafukar kawai bak'in ciki kawai take yi mana dan kar muci moriyarta kasan yanzu sai kahaifi d'a baka haifi halinsaba, wlh akwai samarin wulak'antasu kawai take tana korarsu sai wannan matsiyacin malamin nata da ta lik'e mawa me na k'asa yaci bare yaba nasama.
malam yace oh ni wlh daman nayi zaton haka ni wlh wannan sakaryar d'iyar bansan yaushe zata waye kamar 'yan uwantaba, Allah dai yashiryata.
mama tace Ameen dai
malam yace yanzu dai dafa mana kazar a d'ansa kayan yaji nasan zatafi dad'i haka bari ind'an fita.
ummah tace toh malam adawo lafiya.
zarah dai zaune take tana wanke-wankenta duk firar da iyayenta sukeyi akan kunnenta hawayene yacika mata ido tana jin wani abu ya tokare mata mak'oshi saboda takaicin halin iyayenta, cikin ranta addu'a take Allah yashirya mata iyayenta da 'yan uwanta sugane gaskiya.
bayan ta gama alwallah tad'aura sannan tad'auki hijab d'inta tashige d'akinsu, lokacin yaya rauda tana shafa da alamu daga wanka tafito.
zarah shimfid'a darduma tayi tad'auko alk'ur'aninta tana karantawa har aka tada sallar magrib sannan tatashi tayi sallah
ido tazuba ma rauda tana kallon yadda take sallah cikin sauri babu alamun nutsuwa atare da sallartata
ko da rauda tagama sallar zarah kallonta tayi cike da nutsuwa tace yaya rauda ya kamata idan kina sallah kidinga nutsuwa domin duk abinda zakije nema yana a hannun wanda kike gabansa a yanzu.
harararta Rauda tayi tace toh malama yimin wa'azi tunda kinfini sani, kinsan Allah zarah idan baki fita daga hancinaba sai na 6a66allaki a cikin gidan nan
kuma da kike maganar sallah ai Allah da zuciyar mutum yake amfani, kuma idan ke kike raba ladar toh dan girman Allah kihanani 'yar bak'in ciki kawai.
tana gama fad'in haka tatashi fuuuu taficce tabar d'akin tana ta mita.......
_Comments_
*nd*
_Share_
_Sis Nerja'artโ๐ป_
๐๐๐
_*YARIMA SUHAIL*_
๐๐๐
_*Written By~Sis Nerja'art*_
_*DEDICATED TO MY DAUGHTER ZARAH*_
*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION ยฎ*
*[onward together]*
*{ we give the readers of ours the best out of the bests,,our inks are melodious and dropping a kinda lights to readers }*
THE PEN OF LOVE ๐ HEART TORCHING โค TEARS OF SORROWS ๐ญ CURDLES ๐ GIGGLES ๐ AND MARRIEGE THINK๐
*JUST GIVE US FOLLOW....*โ
page 8โฃ
tashi tayi fuuu tawuce tabar d'akin tana mita ita dai zarah bin rauda tayi da kallo cike da bak'in cikin halin 'yan gidansu a kullum addu'anta Allah yasa sugane gaskiya.
addu'a tayi sannan tatashi tacire hijab d'inta tafito takar6i kayan miyan da suke hannun mama tajajjaga mata sannan tatambayeta idan akwai abinda za'a, mama tace a'a,
sannan tawuce takoma d'aki koda tayi sallar isha'i zama tayi tana ta bitar karatunta sai wajen k'arfe takwas sannan k'anwarta Aysha tadawo gida hannunta d'auke da leda tun daga zaure tafara kwalah ma mama kira
mama da take tsugunne tana hura huta jikinta yana 6ari tamik'e tana washe baki tace a'ah autata har kin dawo.
Aysha tana yatsine fuska tace eh wlh ,
mama kar6ar ledar hannun Aysha tayi tace me kuma muka samu?
Aysha kar6e ledarta tayi tace kai mamanmu ba fa wani abu bane d'inkinane nabiya na amso,
fara'ar da take d'auke a fuskar mama ce taragu tace kina nufin babu abinda kika kawo mana? kiduba kiga 'yar uwarki kaza takawo mana gata chan saman wuta ina mana ferfesu,
Aysha tace oh mama kedai kullum burinki abaki kud'i, jakkarta tabud'e tad'auko 2k tace gashinan kid'auki d'aya kiba abbah d'aya.
mama kar6a tayi tana washe baki tace kai 'yar albarka gaskiya naji dad'i ammah ba zan ba mahaifinkuba dan shima d'azun ya samu kud'i kar ma kikuskura kifad'a masa kin bamu kud'i, Aysha wucewa tayi tanufi d'akinsu tana cewa nidai mamanmu wannan tsakaninku da abbane,
zarah tana zaune saman darduma tana sauraren dukkan abinda suke tattaunawa,
Aysha ce tashigo d'akin tana cewa wash wlh na gaji, jafe jakkarta tayi bisa katifa takalli zarah tace yaya zarah kina nan kina ta bitar karatun?
zarah batare da takalletaba tace Aysha daga ina kike? meyasa kikeso kiga kinyi dare a waje a matsayinki na mace?
Aysha turo baki tayi tace ammah ai mama tasan da tafiyata, zarah aje littafin da yake hannunta tayi tare da tattara dukkan hankalinta ga k'anwarta tace Aysha wannan rayuwar da kika d'aukar ma kanki ba mai 6ullewa bace k'ara tun wuri kigyara tun kan lokaci yak'uremiki gudun kar kiyi nadamar da batada amfani.
mama ce da tazo wucewa tajiyota tana magana lek'owatayi d'akin takalli zarah taharareta tace toh sarkin 6akin ciki mekike ce mata? badai hure mata kunne kikeyi ba dai ko?
zarah kallon mama tayi tace a'a mama kawai ina bata shawarace d's zata fisheta.
salati mama tahau yi tace nashiga ukku ni Zainabu yau Allah yabani d'iya mai bak'in ciki da ni, yanzu 'yan kud'in da take kawo mana ne kike ma bak'in ciki? toh idan suka zauna gidan ubanwa zai dinga ciyar da mu? kinsan dai mahaifinku bai bada abinda zamu ci muk'oshi .
zarah cikin lallashi tace mama kiyi hak'uri ni ba haka nake nufiba, idan na 6ata miki rai kiyi hak'uri.
mama tace daman ai haka zakice munafuka kawai wlh da ace ba ni nahaifekiba da na ce ke ba jinina bace.
zarah dai shuru tayi tana sauraren maganganun mama har mama tagama fad'anta tafita tabar d'akin.
karatunma zarah kasa cigaba tayi saboda haushi nan ta tattare littafan tamaida su ajakkarta, sannan tahaye saman katifarsu takwanta.
Aysha wanka tayo tashirya akan idon zarah wani yakirata a waya tafita tabar gidan, 'yar nokianta ce da taji tana ruri yasa takai idanunta a wajen ganin wanda yake kiranta saka tayi murmushi har dimples d'inta suka lotsa cike da farin ciki tayi picking domin tasan ko bakomai Malam Bello zai d'ebe mata kewa sallamata tayi masa, shima cike da farin ciki ya amsa mata, bayan sun gaisa malam Bello yace gimbiya zarah ya gida?
murmushi zarah tayi tace wai gimbiya dan Allah kama daina kar kaja akamani
dariya malam Bello yayi yace ai gimbiyarce.
zarah tace hmm dan Allah kadaina.
malam Bello yace toh malama zarah ta gida da mutanen gida?
zarah tace Lafiya lou Alhmdllh.
malam musa gyaran murya yayi yace zarah wlh ina sonki so nagaskiya dan Allah kitaimaka kirik'e min amanar kanki domin har ga Allah aurenki nake son yi, dama zaki bani dama da naturo an aje maganata inyaso daga baya idan nak'are karatuna sai muyi aure.
zarah murmushi tayi tace kar kadamu malam ba ma sai ka turoba insha Allahu banda miji sai kai domin ka cancanchi kakasance mijina inko kaga ban aurekaba toh wannan daga Allah ne,
malam Bello dogon numfashi yaja yace Allah yasa haka my zarah, wlh gani nake idan narasaki toh na rasa farin cikina domin kece kawai kika dace da rayuwata.
zarah cike da tausayinsa tace kar kadamu malam insha Allahu ma ba zaka ta6a rasaniba.
Bello cike da jin dad'i yace nagode sosai zarah, yanzu inzo mugaisa ko?
zarah kallon agogo tayi tace a'a malam yanzu dare yayi kadai bari sai gobe.
malam Bello yace toh malama zarah duk yadda kikeso ai haka za'ayi Allah yakaimu, murmushi zarah tayi tace toh malam ahuta lafiya sai Allah yakaimu.
malam bello yace au korata ma akeyi?
zarah tace wane ni inkoreka kawai dai zanyi bacci ne,
bello yace toh gimbiya atashi lafiya
zarah tace Allah yasa, nan sukayi sallama sannan suka kashe wayoyin.
zarah bin wayar tayi da kallo tana murmushi domin har cikin ranta tana jin malam bello ko da tasan mayuwacine iyayenta su amince da shi tunda baida kud'i ammah ta ci alwashin shikad'ai ne mutumin da zata iya aure saidai wani hukuncin daga ubangiji.....kiran da mama takeyi matane yakatseta daga tunanin da takeyi, dasauri tatashi tafita a tsakar gida tasamu mama da abba Zaune saman tabarma suna cin nama suna dangwala romon da bread,
kusa da mama tatsugunna tace mama gani, mama fuskarta a d'aure tace ga naki nan su kuma tunda su suka kawo saisa nafitar masu da nasu yafi yawa,
kar6a zarah tayi tace nagode sannan tatashi takoma d'akinta ,
abbah binta yayi da kallo cike da takaici yace ni inma rasa abinda yarinyarnan take k'unshewa a d'aki kullum tana d'aki ko fitowa batayi tasha iska.
ummah tana yagar nama tace ita dai tasani matsalarta.
zarah tana shiga d'akinsu zama tayi taci naman bayan ta gama tafiddo kwanon sannan tayi ma iyayen sallama takoma d'aki saida tayi wanka sannan takwanta.
duk yadda taso tayi bacci ammah takasa tunanin wulak'ancin da takesha wajen mutanene da halin iyayenta da gwagwarmayar da tasha ne yasa tafara hawaye kullum batada buri da yawuce taga iyayenta da 'yan uwanta sun canza hali musamman ma idan tatuna da lokacin da suna yara haka suka taso a sake iyayensu basa kwa6arsu
Malam musa da Zainab sune iyayensu su ukkune suka haifa, Rauda itace babba sai zarah da take bi mata sai 'yar autarsu Aysha ko da ba wani tserataiya bane irin sosai d'innan a tsakaninsu k'ara ma Rauda itace taba zarah shekara biyar, inda zarah kuma taba Aysha shekara biyu.
Suna da kyau sosai kasancewar iyayensu fulanine na usuli, saidai zarah itace zaka kallah kaga sak mama, inda su Rauda da Aysha suke kama da abbansu saisa zarah tayi musu fintinkau wajen kyau dan ma Suna halin rashi.
sunyi karatu bakin gwalgwado dan dukansu daga secondary school suka tsaya da karatunsu babu wacce tacigaba duk suna gida Zaune, zarah ma ce tashiga makarantar koyan sana'a tayi Catrine (6angaren girki) sannan itace mai zuwa islamiyya ammah su rauda babu wacce take da lokacin zuwa islamiyya sharholiyarsu kawai sukeyi.
abun mamakinma a gaban iyayen nasu ake zuwa ad'aukesu ammah iyayensu ko da sau d'aya basu ta6a nuna 6acin ransuba domin basuda burin da yawuce akawo musu kud'i,
hatta abincin da zasu ci wani lokacin rauda da Aysha ne suke ciyar da su kasancewar Abbah baida tak'amaiman aikinyi daman ginine da kanikanci shima sai idan ya samu yakeyi.
ahakanma iyayensu sun tsani suga talakawa suna ra6ar 'ya'yansu, su ma kansu su rauda basa son talakawa 'yan uwansu saisa duk samarinsu masu kud'ine.
duk wanda zai nuna yana son zarah toh wulak'ancine sai yasha wajenta,
mama tun tana fad'a har tagaji takyaleta,
hantarace da wulak'anci babu wanda bata sha wajensu, ko kud'in wata na islamiyya sai tayi dagaske take samu wajen iyayenta inma basu bataba toh wajen k'anwarta ko yaya rauda take samu su ma sai tasha wulak'anci da gori suke bata.
kayan shafa ma sai sunga dama idan zasu siyo nasu suke had'awa da ita suna d'an siyo mata mai da powder da turare shima a wulak'ance ake bata.
duk aikin gida ita aka sakarmawa inba ka saniba ba zaka ta6a cewa zarah d'iyar gidan bace sai kad'auka *'YAR RIK'O* ce,
wa'azi nasiha babu wanda batayi ma 'yan gidan nasuba ammah sunbi son zuciyansu da na iyayensu.
zarah tun abin yana damunta ammah yanzu ya rage damunta
Malam bello malamin islamiyyarsu zarah ne yana da kirki sosai jininsu ya had'u da zarah saisa suke mutunci, daga baya yanuna yana sonta dakyar yasamu zarah ta amince masa suna soyayya, duk wasu littafan karatun zarah shi yake siya mata.
zarah tun tana nuna bata so ammah daga baya tahak'ura tana kar6a dan tasan iyayenta ba zasu ta6a siya mataba kuma babu inda zata samu kud'i tasiya, shima dan taga yana da hankali da nutsuwa kuma a yadda yake nunawa shi dan Allah yakeyi mata kuma yana so yasamu lada idan ta karanta.
Malam Bello karatu yake a university sannan yana tsare ma wani mutum shago da kud'in islamiyya da ake biyansa a nan yake samun d'an abinda zai rik'e kasancewar iyayensa suma ba masu hali bane sosai.
mama lokacin da tagano zarah tana soyayya da shi har kusan dukanta tayi tace me zatayi da wannan talakkan me nak'asa yaci bare yaba nasama ita dai zarah shuru tayi domin tasan abinda mama take nufi, ammah a ranta itadai bata da burin auren kowa sai malam bello dan shine kad'ai yake taimakonta.
bud'a k'ofar da akayine yadawo da ita daga kogon tunanin da ta lula, Aysha ce tashigo da leda a hannunta tana waya, zarah duba agogo tayi taga kusan k'arfe goma da rabi dan haka tajuya domin tayi bacci cike da takaicin maganganun da Aysha takeyi a waya batare a taji kunya ko nauyin Zarah ba.
ahaka Aysha tagama wayan itama takwanta har sukayi bacci yaya Rauda bata dawoba.
da asuba zarah har tayi sallah ammah Aysha bata tatashi ko da zarah tak'ara tadata cewa tayi dan Allah kikyaleni idan natashi zanyi nace miki.
zarah tace haba Aysha yanzu har sai gari yayi haske sannan zaki tashi kiyi sallah?
Aysha tace ko ma dai yaushe nayi babu ruwanki malama dan haka kikyaleni.
zarah tsaki taja tace Allah yakyauta sannan tacigaba da laziminta har gari yafara haske sannan tamik'e taje tayi wanke-wanke tagyara gida bayan tagama tadawo tayi kwanciyarta sai alokacin Aysha tatashi tayi sallah.
wajen k'arfe goma zarah tafarka lokacin babu kowa d'akin batayi mamakin hakanba domin tasan Aysha ta tafi gantalinta daman ita yaya Raiuda ba gidan takwana ba.
zarah gyara d'akin tafara yi sannan tafito tayi brush tawuce d'akin mama lokacin Abbah yana shirin fita nan taduk'a bakin k'ofa tace Abbah ina kwananku.
Abbah ciki-ciki ya amsa mata, mama kau daman harararta tayi tace yanzu saboda Allah zarah sai yanzu kika tashi baccin?
zarah tace mama ai saida nagama komai sannan nakwanta,
mama cikin fad'a tace haka dai zaki k'are daga bacci sai zaman gida ko 'yan kud'in kashewar baki yarda kifita kisamo saboda bak'in cikin kar muma muci daga wajenki.
zarah shuru tayi mama tace toh yau dai ba ayi karin kumalloba muma nan ruwan Lipton da sauran biredin jiyane muka ci,
Kinga da ace kina da kud'inki ai da kin d'an siyo ko indomie ce kinci irin yadda 'yan uwanki sukeyi, yanzu dai bari inbaki kije kiyo mani cefane
zarah tace toh mama
mama kallon abbah tayi tace malam kabada kud'in cefanen.
abbah laluba aljihun rigarsa yayi yad'auko d'ari biyu yamik'a mata, mama tsayawa tayi tana kallonsa
yace ki amsa mana,
mama tace haba malam me d'ari biyu zatayi mana bamu da fa abinda zamu dafa muci,
abbah yace toh nidai su gareni koma minene kujalabta kuyi abincin.
mama tace gaskiya wannan babu abinda zatayi mana.
abbah yace kihad'a da canjin jiya ai nasan dai anrage wani abu cikin d'ari biyar d'in.
mama tace naira sittin fa ce.
yace toh inbakuso sai inmaida abuna aljihu.
Jin haka yasa mama takar6i kud'in domin tasan zai iya.
bayan ya fita mama kallon zarah tayi tace ni tashi kimik'o min jakkata ko d'ari biyu ce ink'ara dan ma Allah yaso akwai kud'in da Aysha tabani jiya da ban san yau ya zamuyi ba.
zarah tashi tayi taje tad'auko ma mama jakkar tamik'a mata.
mama d'ari biyar tabata tace kisiyo garin d'an wake rabi sai mai rabin gwangwani da tashi da Maggi ko shine musamu abinda zamu saka ma bakunanmu kafin yarana sudawo
kar6a zarah tayi tace toh mama.
zarah tashi tayi taje tasako hijab d'inta sannan tafita taje tayo siyayyar, bayan ta dawo tad'aura girkin.
tana cikin yi mama tafito ta shirya sanye da gyale tace toh idan kin gama kijuye a cikin plastic d'innan zan je gidan mariya barka kuma kar kisaki kici kibari sai nadawo nad'ibar miki.
zarah cike da ladabi tace toh mama Allah yakiyaye hanya.
zarah bayan ta gama gyara gidan tak'ara yi sannan taje tayi wanka tashirya tayi sallah.
bayan ta gama saman katifarsu takwanta tana jiran mama tadawo saboda wata irin yunwa da takeji.
mama sai wajen k'arfe ukku tadawo lokacin bacci har ya d'auke zarah.
maganar mama ce tajiyo sama-sama dan haka firgit tayi tafarka.
mama tsaye take bakin k'ofa tace yanzu dan gidanku zarah bacci kikeyi kinbar mana gida bud'e?
Zarah mik'ewa tayi tace wlh mama ban san lokacin da bacci yad'aukeniba kiyi hak'uri.
tsaki mama tayi tace kullum bakida aiki saidai ayi hak'uri ke da ace bamu hak'uri da ke ai da tuni na 6allaki, ni kizo kikwaso mun kwanika inraba abincin.
zarah tace to mama sannan tabi bayan mama takwaso kwanuka.
Zarah bayan ta gama cin abincinta alk'ur'ani tad'auko tana bitar hardar da zata bada islamiyya har aka kira sallah la'asar tayi sannan tashirya taje d'akin mama tace mama zan tafi islamiyya.
mama harararta tayi tace ke ni banma yarda dakeba anya ma islamiyya kike zuwa? ko dai wajen wannan malamin naku kike zuwa.
zarah raurau tayi da ido tace wlh mama babu inda nake zuwa sai islamiyya.
mama tace eh ai dan kihad'u da shi islamiyyar saisa kike zuwa,
zarah tace a'a wlh mama.
mama tace munafuka kawai kedai kika sani ahaka dai zaki k'arata ni tashi kiban waje.
zarah tashi tayi tafita.
ko da taje islamiyya lokacin ajinsu har anfara taruwa kowa zaune yake yana bitar hardarsa kafin malam yashigo.
sit d'in gaba tazauna kusa da k'awarta khairy kasancewar nan ne wajen zamansu tare da mik'a ma khairy hannu suka gaisa.
khairy kallon zarah tayi tana murmushi tace yau dai na rigaki Zuwa.
itama zarah murmushi tayi tace nima dai nayi mamakin ganinki dawuri
khairy tace ai infad'amiki tun d'azun ina nan ina koyon harda kafin malam bello yashigo kedai nasan kinsha taki hardar.
murmushi zarah tayi tace kedai kicigaba da haddarki.
suna cikin bita malam bello yashigo idanuwansa akan zarah,
suna had'a ido dasauri zarah
08, February 2025
Shuraihu Usman
jjjjj