Showing 27001 words to 30000 words out of 83141 words
Chapter 10 - Daren Aurena Part 1 Complete Hausa Novel By Nana M Sha'aban .txt
yanzu wasan ya fara tagumi yanzu ka fara yin shi, ai wallahi sai ka gane kurinka, banza kawai" Jabir yayi murmushi tare da cewa "Teemarh kenan nii Jabir d'an tuwa kika yi wa wannan abin ko? To wallahi zan nuna miki cewa nii babban d'an iska ne, karki ga wai ina tagumi kiyi tunanin wai tsoron ki nake ji, to wallahi ba'ayi macen da zan ji tsoronta ko kuma ta takura min ba, Teemarh ki rubuta ki ajiye Jabir yana nan sai ya rugu rayuwarki gaba d'aya" Teemarh ta zauna a kan kujera tana murmushi tare da cewa "Me kake cewa maimaita inyi hadda" tsaki ya ja ya fita daga d'akin kai tsaye gurin da aka tanada dan ajiye motoci ya nufa ya ja motar da gudu har yana kok'arin kwarfe mai gadin da motar Allah ya taimaka ya kauce masa (ni kuwa 'yar mutanan zazzau nace wai Jabir an had'u da k'arfen k'afa ko nace gaba da gabanta Aljani ya taka wuta😂).
~*BAYAN WATA DAYA*~
Cikin Khadijatullahi yana k'ara girma dan yanzu watansa hud'u, duk da cewa yanzu ta rage yawan damuwa sai dai idan abin da Jabir yayi mata ya fad'o mata ta shige b'and'aki tayi kukanta mai isarta ta wanke fuskarta ta fito, ga laulayi ya sakata a gaba duk abin da ta ci sai ya dawo shiyasa kwana biyu basa zuwa makaranta ita da Amatullahi saboda Amatullahi ba za ta tab'a iya zuwa makarantar ba tare da Khadijatullahi ba, Hafsa kuwa tayi matuk'ar damuwar rashin zuwa makarantar da basa yi, shiyasa ita ma ta daina zuwa ya zamana kullum ita da Khalid suna gidansu Khadijatullahi, Aunty Murja da ta ga abin nasu ba na k'are ba ne, ranar wata Asabar bayan sun zo suna ta hira ta zauna tare da fara yi musu fad'a "Gaskiya mun ba ni mamaki sosai, yanzu ace kun daina zuwa makaranta saboda Khadijatullahi bata da lafiya bata zuwa, to insha Allahu gobe kowannan ku ya shirya zaku koma makaranta dan na gaji da zaman da kuke kullum kuka kullum cikin damuwa kuke ba za ku iya d'aukar k'addara ba kenan" Amatullahi ta kalli Aunty Murja cikin yanayin damuwa ta ce "Aunty Murja ba zamu iya zuwa makaranta ba tare da Khadijatullahi ba" Hafsa ta ce "Wallahi Aunty Murja gaskiya Amatullahi ta fad'a ba zamu iya zuwa makaranta ba tare da besty ba" Aunty Murja ta ce "Ai shine nace ku shirya gobe har Khadijatullahi dukkanku makaranta zaku tafi" suka amsa da "to shikenan Aunty Murja".
Haka kuwa aka yi washe gari kowannen su ya shirya suka fito su uku, kayansu iri d'aya motar Hafsa suka shiga drivernta ya ja su suka nufi makarantar, a makarantar ma haka Khadijatullahi tai-tayin Amai dan da har zasu dawo gida Khadijatullahi ta ce ba za ta koma gida ba har sai an tashi haka suka kyaleta har sai da aka tashi drivern Hafsa ya zo ya kai su har kofar gidan sannan ya nufi gidansu Hafsa, Amatullahi ta kama Khadijatullahi dan wani irin jiri take ji yana neman fad'ar da ita, suka shiga gidan kai tsaye d'aki suka nufa suka tarar da Aunty Murja tana share d'akin Amatullahi ta taimakawa Khadijatullahi ta kwanta a kan gadon, Amatullahi tayi wa Aunty Murja sannu da gida Aunty Murja ta amsa da "yawwa" Amatullahi ta ce "Aunty Murja zan koma gida zuwa anjima zan dawo naga jikin bestyna" Aunty Murja ta ce "to shikenan k'anwata sai kin dawo d'in" Amatullahi ta amsa da "yawwa" sannan ta fita zuwa gida.
Tana zuwa gidan ta tarar da Lado a tsakar gida yana zaman jiranta domin kuwa yanzu soyayyar bogin da suke yi tayi nisa sosai,yana ganinta ya washe baki kamar da gaske sannan ya tashi ya nufeta yana cewa "Sweety shine yau kika yi tafiyarki baki fad'a min ba" Amatullahi ta kalleshi sosai A zuciyarta ta ce "ji shashasha,mahaukaci wallahi ina nan ina had'a muku tarko kai da wannan shakatafin uwar ta ka, za ku san dawa kuke zancen, kayi tunanin zan fad'a tarkonka ne" amman a fili sai tayi wani irin kayatatcen murmushi tare da cewa "Sorry my love wallahi hankalina gaba d'aya baya jikina su besty suna jirana shiyasa" Lado ya ce "Allah sarki to shikenan ba komai kin san bakya laifi a gurina" haka suka jera a kan taburma suka yada zango suna ta hira kamar wasu masoyan gaske (kai Allah ya kyauta miki Amatullahi).
*'BANGAREN HAFSA*
Suna isa gidan ta fito daga mota Khalid ya nufota da gudu yana cewa "Mommy oyoyo" rumgumeshi tayi tare da sumbatarshi a goshinsa kamar ance ta d'ago sai ganin Yaya Safwan yayi a kusa dasu ya rumgume hannuwansa a k'irji yana kallonsu yana murmushi, mik'ewa tayi sannan ta kama hannu Khalid dan har yanzu haushin Yaya Safwan d'in take ji sosai kuma bata tunanin zata iya k'ara soyayya dashi har abada, har sun fara tafiya Khalid ya ce "Mommy kin ga Abbana fa tun d'azu ya zo yana jiranki" Kallon Khalid tayi sannan ta ce "zaka zo mu shiga gidan ne ko kuma suturu zaka yi min" Khalid ganin yadda Hafsa ta chanza masa fuska lokaci d'aya har hawaye yana kok'arin zubowa daga idonta ya ce "Mommy kiyi hak'uri bana son kiyi kuka saboda ni, ki yafe min" Hafsa tayi murmushi sannan ta ce "To mu shiga ciki ko yaron k'irki" Duk abin da suke fad'a Yaya Safwan yana jin su, da sauri ya tsaya a gaban Hafsa tare da saka guiwoyinsa a k'asa cikin muryar tausayi ya fara magana "Hafsa nasan nayi miki abubuwa da dama na wulak'anta soyayyarki na muzguna miki, Hafsa gani a gabanki kiyi min duk hukuncin da kike so zan karb'eshi hannu bibbiyu amman dan Allah ki karb'i soyayyata a karo na biyu wallahi ina tsananin sonki sosai ina k'aunarki Hafsa dan Allah ki tausaya min, karki yi watsi dani dan manzon Allah Hafsa" wani irin kuka Hafsa ta saka tare da jan Khalid suka shige cikin gidan, kai tsaye b'angarenta suka shiga ta fad'a kan gado tana cigaba da kuka, Khalid da ke tsaye a bakin gadon ya zuba mata ido yana kallonta shima yana kukan (Allah sarki soyayya), shi kuwa Yaya Safwan tashi yayi ya shiga cikin motarsa dan ya dad'e da zuwa gidan ya fito zai tafi shine ya ga dawowar Hafsa, Mai gadin ya bud'e masa gate ya fita daga gidan zuciyarsa nayi masa zafi.
*'BANGAREN GIDANSU JABIR*
Yau aka d'aura auren Nihal da wani yaron Alhaji Mansur mai suna Salis, matarsa d'aya da d'ansa namiji sunansa Khamis, iyayen Salis talakawa ne kuma shi kad'ai ne suka haifa da yake Baban Salis yana gadi a ma'aikatar Alhaji Mansur shine ya nemi Alfarma da ya kawo d'ansa domin ya samu aikin yi shima Alhaji Mansur bai k'i ba ya amince aka d'auke shi aiki wannan shine takaitatcen tahirin Salis.
Alhaji Mansur ya yaba da hankalin Salis shiyasa har ya bashi auren Nihal, lokacin da labari yazowa Nihal fad'uwa k'asa tayi sumammiya, Shahida ta d'auko ruwa mai sanyi ta watsa mata nan fa ta farfad'o ta rumgume Hajiya Asiya wacce take gefenta tana kuka, "Mami dan girman Allah ki cewa Abba zan dinga yi masa duk abin da yake so kuma ba zan sake fita daga gidan nan ba har sai idan shine ya bani umarni Amman dan Allah kice a fasa auren nan wallahi bana son shi" ta k'arasa maganar tana kuka kamar ranta zai fita, Teemarh take zaune tana kallonsu kawai ta ja tsaki ta kawar da kanta Abba ne yayi sallama ya shigo d'akin Aliyu da Ango Salis suna biye dashi a baya, Teemarh da Shahid suka amsa sallamar tare da yi musu sannu da zuwa zama suka yi suna amsa musu da "Yawwa" Salis kuwa tunda ya shigo yake kallon Nihal wacce take ta shan kuka zuciyarsa cike da farin ciki, Abba ya fara magana cike da farin ciki bayan yayi addu'o'i ya ce.
"Nihal kamar yadda nasa aka shaida muku an d'aura aurenki yanzun nan to haka yake shiyasa ma nazo tare da mijinki domin ku tafi tare dashi" Amman yayi maganar cikin sanyayaryiyar muryarsa.
Hajiya Asiya tana kuka ta ce "haba Abban Jabir a ina aka tab'a yin haka, ka aurar da yarinya ba tare da ka sanar da ita ba, kuma maimakon ka bari ta fito da zab'in ranta kawai sai ka aura mata wannan matsiyacin" Mami ta k'arasa maganar cike da bak'in cikin mijin nata.
Alhaji Mansur ya ji matuk'ar zafin yadda ta ci mutuncin Salis d'in abin yayi matuk'ar k'ona masa rai amman ya da ke tare da cewa "Ai da ba'a san asalin balbala ba da sai ta ce daga madina take" yayi maganar yana harararta, Salis ma ya ji matuk'ar bak'in cikin yadda Hajiya Asiyan ta ce masa matsiyaci, amman zai tabbatar mata da cewa shi d'in matsiyaci ne a kan 'yarta, sai kuma yayi wani murmushi da ban san ma'anarshi ba.
Hajiya Asiya kuwa mutuwar zaune tayi jin abin da mijin nata ya ce mata tun da take dashi bai tab'a yi mata gorin cewa ita 'yar talakawa ce ba sai yau, tsoronta d'aya kada yaranta su gane cewa ita 'yar talakawa ce dan kuwa idan suka gane ba za ta tab'a yafewa Alhaji Mansur ba, ganin babu wanda ya fahimci abin da Abba ya ke nufi yasa ta sauke ajiyar zuciya a b'oye, tare da godewa Allah.
Muryar Alhaji Mansur ce ta dawo da Nihal daga dogon tunanin da take yi fuskarta shab'e-shab'e da hawaye, "Ke Nihal tashi taje ki shirya ki zo ku tafi domin k'afarki k'afar mijinki" haka Nihal ta mik'e jira na kok'arin d'ibanta ta fara tafiya tana dafa bango, Salis ya bi ta da kallo yana ra ya abubuwa da yawa a zuciyarsa, fuskarsa kuma har yanzu kunshe take da wannan murmushin nashi.
Nihal tana shiga d'akinta tayi saurin shiryawa dan tasan halin Abbanta idan ta dad'e sai ya shigo har d'akin yayi mata dukan tsiya, cikin wata atamfa coffe brown ko mai bata shafa ba ta yafa mayafi ta fito, Salis ya mik'e suka yi sallama da Abba da Aliyu ya saka Nihal a gaba suka nufi gurin da yayi parking d'in motarsa, ya bud'e mata murfin motar ta shiga wajen mai zaman banza, sannan ya mayar ya rufe ya zagaya mazaunin driver sai da ya kalleta ya ga fuskar nan babu alamar murmushi ta had'e fuskar nan kamar bata tab'a murmushi a duniya ba.
Salis yayi wani gajeran murmushi sannan ya ja motar mai gadi ya bud'e gate d'in gidan suka fita ya nufi gidansa gudu yake sosai a kan titin har suka isa gidansa, masha Allah gaskiya gidan ya had'u domin kuwa an zubda naira sosai wajen gina gidan, Nihal dai kallon gate d'in gidan take yi har mai gadi ya bud'e gate d'in gidan sannan suka shiga, a parking space yayi parking sannan ya fito ya bud'e mata murfin motar ta fito, hannunta ya kama da sauri ta shiga kok'arin kwacewa amman inaaa ta kasa saboda ya rik'e hannun nata sosai ta yadda ba za ta iya kwacewa ba, babu yadda ta iya haka ta barshi suka jera a tare suka shiga cikin madaidaicin falon, wata shirgegiyar mata ta gani a falon ga wani yaro shima k'ato gaba d'ayansu daga matar har yaron sun ba wa Nihal tsoro jikinta ya fara rawa.
Talatu tana ganinsu ta mik'e dakyar fuskarta a murtuke ta fara magana cikin bala'i da masifa "to ma ci amana ka yaudareni wallahi Allah ya isa tsakanina da kai kuma wallahi sai na ga mai wannan shegiyar yarinyar ta fini dashi da har zaka aurota a matsayin matarka" nan ta nufo inda Nihal take gadan-gadan, Nihal kuwa ganin ta nufota ta k'ank'ame Salis tana cewa "Dan Allah kayi mata magana ni bana so" Salis ya rumgumeta sosai sannan ya kalli Talatu wacce ta kai hannunta zata jayo Nihal cikin tsawa ya ce "ke Talatu ki shiga hankalinki idan ba so kike yanzun nan nayi k'asa-k'asa da ke ba" yayi maganar yana nuna ta da yatsa.
Talatu kuwa harara ta wurga masa tana gigiza ta kama k'ugunta da hannunta biyu, Salis ya nufi d'akinsa da Nihal a jikinsa Talatu tayi saurin zuwa ta tare kofar d'akin tana cewa "me zaka shiga kayi a ciki, wallahi baka isa ka kwanta da wannan yarinyar ba, dan ni ba zan had'a miji da wata shashasha ba, ni kad'ai zan zauna a gidan mijina" Salis yayi murmushi tare da cewa "Ai kin makaro, zaki ba mu hanya mu huce ko kuwa?" Talatu ta ce "baka ji mai nace ba" wani irin kallo Salis yayi mata sannan ya ce "to sannu uwata" ya bangajeta suka shige d'akin ya kullo ya saka key.
Da sauri Nihal ta zame daga jikin Salis sannan ta zauna bakin gadon tare da dafe k'irji tana sauke ajiyar zuciya, Salis ya kalleta kamar zai yi dariya sai kuma ya had'iye tare da ce mata "menene? Kike faman sauke ajiyar zuciya sai ka ce wacce ta had'u da zaki", Nihal ta kalleshi ta ce "Wannan wacece Mamin ka ce?" ta tambayeshi tana kallonsa, bai yi niyyar yin dariya ba amman sai da maganarta ta bashi dariya zama yayi a kusa da ita yana cewa "Mamina kuma? Chabb wannan tayi miki kama da mahaifiyata, matata ce" zaro ido Nihal tayi tana kallonsa ido cikin ido, mamaki ya isheta "to shi wannan Salis d'in wane irin namiji ne da har zai auri wannan k'atuwar matar" ta fad'a a zuciyarta amman a fili ta tab'e baki tayi sannan ta ce "Amman lokacin da ka aureta tuwo ne ya mak'ale maka a ido ko?" harararta yayi sannan ya ce "A'a alkaki ne ya mak'ale min a ido ba tuwo ba" jawota yayi jikinsa tayi saurin zabura ta mik'e tsaye domin tayi wa kanta alk'awarin ba zata tab'a yarda Salis ya kusance ta ba saboda kwata-kwata baya cikin tsarin irin mijin da take so ta aura, dan Nihal halinta d'aya da Hajiya Asiya tana son ta auri mai kud'i kuma ta tsani talakawa.
Salis ya gama fusata ganin irin yadda Nihal d'in ta zabura daman yana bin ta a hankali ne saboda mahaifinta amman ya ga ita so take ya bi ta ta kofar matsiyata, wata iriyar sha'awarta ce ta ta so masa ya fisgota da k'arfi ya kwantar da ita a kan gadon nan ta shiga dukanshi ya had'a hannayenta duka biyun ya rik'e ya sakar mata nauyinsa gaba d'aya, dakyar take iya numfashi saboda ya danneta sosai bata ma iya motsi, "daman ina so na nunawa mahaifiyarki ni cikakken matsiyaci ne" nan ya shiga cire mata kayan jikinta yana wurgi dasu, duk tsoro ya cika Nihal saboda abin da Salis ya ce "to me yake nufin zai yi mata?" tayi tambayar a zuciyarta, "Dan Allah yaya Salis kayi hak'uri ai ba ni bace nace maka matsiyacin ba, kuma da Mami ta ce ban......" bata iya k'arasawa ba ta kwalla ihu sabon wata iriyar azaba da tayi duk da cewa ita tana yawa maza da yawa sunyi sex da ita bata tab'a jin azaba irin ta hau ba, gaba d'aya jikinta ya shiga rad'ad'i, shi kuwa Salis ko a jikinsa bai san ma tana yi ba, ya cigaba da gana mata azaba iri-iri sai da yayi dan kansa ya gaji sannan ya tashi daga kanta a lokacin Nihal har ta kuma suma domin sumanta uku idan ta suma ya yayyafa mata ruwa.
Wanka ya shiga ko da ya fito ya ganta kwance ya matsa kusa da ita ya tabbatar ta kuma suma yayi murmushi "kin farfad'o dan kanki ma, indai suma ne yanzu kika fara sumar ma" sannan ya shirya cikin k'ananun kaya, ya kunna t.v yana kallon sa hankalinsa kwance.
*'BANGAREN YAYA SAFWAN*
Yana isa gida matarsa ta taresa a bakin kofar shiga falon fuskarta cike da masifa take cewa "ina d'ana?" wani iri kallo yayi mata ji yake kamar ya zazzabga mata mari "bani guri in huce" yayi maganar fuskarsa babu alamar wasa, ganin haka yasa Safna matsawa ya huce har ya kusan shiga d'akinsa ya ji muryarta tana cewa "wallahi a yau d'in nan ba sai gobe ba zan je na d'auko yarona, dan ba zan bari wata shashasha wacce bata san ciwon haihuwa ba ta rik'e min yarona" Yaya Safwan cikin zafin nama yayo kanta, Safna ganin ya nufota gadan-gadan yasa ta fad'a d'akinta ta kulle, kofar d'akin ya nufa yana bubbugawa da k'arfi yana cewa "idan kika sake ki ka taka k'afarki ki ka fita daga gidan nan ta a bakin aurenki, idan kin d'auko yaron naki ki huce gidan ubanki dashi" yana gama fad'ar haka ya nufi d'akinsa ya shige, a kan gado ya kwanta zuciyarsa na cigaba da yi masa zafi.
Safna kuwa kuka ta fashe dashi jin abin da mijin nata yake tana tsananin son Yaya Safwan tana kishinsa sosai, shiyasa ta ji duk duniyar nan babu wacce ta tsana irin Hafsa saboda ita ce take kok'arin rabata da farin cikinta, ta zabga tagumi tana cigaba da kuka mai tsima zuciya jinjina tayi da gadon tana saka-saka abubuwan da yawa a ranta har bacci ya d'ebeta.
*'BANGAREN KHADIJATULLAHI DA AMATULLAHI*
Kasancewar yau basu da lectures da yawa guda biyu ce dan haka suka dawo gida da wuri suna shiga gida suka tarar da Aunty Murja ta shirya zata je gidan da take yin aiki, Amatullahi ta ce "Aunty Murja zaki fita gidan Hajiya Mama ne?" Aunty Murja ta ce "Eh wallahi yau kun dawo da wuri lafiya dai ko?" Khadijatullahi ta kalli 'yar uwar ta ta cike da tausayawa sannan ta ce "Eh lafiya alhamdulillahi, yau bamu da lecture da yawa ne shiyasa" Aunty Murja ta ce "Allah sarki bari in je na dawo kar nayi ranar aiki" suka had'a baki wajen cewa "to sai kin dawo" fita tayi da sauri wasu hawaye ne suka gangarowa Khadijatullahi, Amatullahi tayi saurin dafata tana tambayarta "me yafaru" Khadijatullahi ta ce "besty ina tausayawa Aunty Murja sosai duk a kaina take ta wannan fad'i tashin duk ta hana kanta hutawa duk saboda ni ta k'arasa maganar tana kuka, Amatullahi ta rumgumeta tana bubbuga bayanta d'akin suka shiga a kan taburma suka zauna Amatullahi tana jan Khadijatullahi da hira har ta saki fuskarta.
*'BANGAREN ANGO