Showing 9001 words to 12000 words out of 83141 words

Chapter 4 - Daren Aurena Part 1 Complete Hausa Novel By Nana M Sha'aban .txt

10 Jan 2025

3075

Asiya da ta gaji daga baya komawa tayi d'akinta ta kulle da mukulli, haka suka cigaba da rainon cikin har ya kai lokacin haihuwa ranar wata alhamis ta haifi d'anta namiji tun a asibitin jama'a sukai ta zuwa barka har aka sallamesu suka dawo gida, mutane suka cika gidan ai kuwa Hajiya Asiya ta d'aure fuska saboda ita sam bata son wani talaka ya rab'eta amman kuma taga a cikin dangin mijin nata har da talakawa, haka dai babu yadda ta iya kullum cikin zuwa barka ake a gidan har ranar suna yaro ya ci suna Aliyu, anyi shagalin suna sosai anci ansha sai wajen magriba kowa ya watse aka bar Hajiya Asiya daga ita sai yaranta sai kuma mijinta, haka suka cigaba da nunawa junansu da yaransu kulawa da soyayya Aliyu yana da shekara hud'u ta sami wani cikin amman wannan yayi matuk'ar bata wahala sosai dan haka Aliyu da Jabir aka kai su gurin Kakarsu ta wajen uba, ta rik'esu har sai da Asiya ta haifi yaranta 'yan biyu duk mata aka sakawa d'aya sunan mahaifiyar Alhaji Mansur Nafisa d'aya kuma sunan mahaifiyarta Aisha, Nafisa suke ce mata Nihal, Aisha kuma Shahida ranar da Asiya tayi arba'in aka kai mata su Jabir saboda irin matsawar da tayi a dawo mata da yaranta, suka cigaba da rayuwa cikin farin ciki da kwanciyar hankali.


Wannan shine tarihin Jabir da Mahaifiyarsa.
Aliyu ne kwance a kan gadon d'akinsa wanda tunda Mami ta mareshi ya shiga ya rufe kansa bai k'ara fitowa ba gashi har safiya tayi kusan k'arfe 10am na safe ko abincin dare bai ciki ba sai ruwa da ya bud'e fridge ya sha kad'an, maganar da d'an uwansa ya fad'a masa ce da yake tambayarsa jiya da yarinyar tazo gidan ta shiga dawo masa "wata yarinya ce da muka yi Auren wucen gadi da ita" shi abin da bai gane ba shine me Jabir yake nufi da auren wucen gadi, shin yayi aure ne ba'a fad'a masa ba kuma da duk alamu indai yayi auren da gaske to Abbansu ma bai san yayi ba, dan inda ya sani zai fad'a masa, da ya ga zai tak'ura kansa da tambayoyin da bashi da amsa ya watsar dashi,sannan ya tashi ya shige toilet wanka yayi sannan ya fito ya shirya cikin wata had'addiyar shadda marun colour, kyau iya kyau ya riga da yayi ya fesa turare sannan ya fita ta kofar baya domin kuwa baya k'aunar ganin kowa daga cikin 'yan uwan nasa da mahaifiyarsa,motarsa ya shiga mai gadi ya bud'e masa gate d'in gidan ya ja motar ya nufi gidan Abokinsa Musbahu.


*'BANGAREN KHADIJATULLAH*


Tun da ta tashi take kwarara amai daman gashi babu komai a cikin nata dan haka aman ma dakyar dake yinsa duk ta gama galabaita, Aunty Murja ce taje ta kirawo doctor Halima saboda ganin amai yak'i tsayawa, koda doctor Halima tazo ta ga yanayin da take, allura tayi mata wacce zata tsayar da aman ko minti 5 ba'ayi ba aman ya tsaya, kwantawa tayi tare da jero ajiyar zuciya, suna yi mata sannu tana amsa musu da kai doctor Halima ta ce "karku bata abinci yanzu ku bari sai wajen 12am sai a bata tea mai zafi tunda kun ga yanzu k'arfe 10:30am na safe" suka amsa da "to insha Allahu, zamu kiyaye" daga nan doctor Halima ta fita ta koma office d'inta, Amatullahi ta kalli Aunty Murja ta ce "Aunty Murja bari inje gida daga nan na taho mana da abincin da zamu ci" murmushi Aunty Murja tayi sannan ta ce "To Amatullahi" ta shi tayi sannan ta ce mata "Sai na dawo", "A dawo lafiya" Aunty Murja ta fad'a fuskarta d'auke da murmushi, fita Amatullahi tayi da saurinta tana fita daga asibitin ta dad'e a bakin titi duk mai adaidaitar da zata gani a cike yake da mutane, ta tafiya tayi domin ta ga idan ta tsaya ba zata samu masu adaidaita ba, Ai kuwa tayi sa'a ta hango wani mai adaidaita babu kowa a cikinsa da sauri ta tsayar dashi ta shiga tare da yi masa kwatancen gidansu, sai da mai adaidaitan ya kai ta har kofar gida sannan ta biyasa ta shiga gidan bakinta d'auke da sallama "Assalamu alaikum" Inna larai wacce take gaban murhu tana had'a wutar girki tayi mata wani irin kallon k'ask'anci ita ma Amatullahi ta mai dan mata da martanin kallon nata,ba tare da ta amsa sallamar ba ta ce "to 'yar gantali ina kika je kika kwana saboda tsabar rashin kamun kai irin naki da wannan shegiyar uwar taki bata koya miki tarbiyya ba har ki je ki kwana a wani wajen koda yake naji ance dangin nata gaba d'aya 'yan bariki ne anyi gadon tsiya" tayi maganar tana d'ora tukunyar ruwan kokon da zata yi, fusata iya fusata Amatullahi ta riga da tayi,tana raye a gabanta a zagi mahaifiyarta kuma har ace danginta 'yan bariki ne ace bata d'auki mataki ba "Lallai yau akwai bala'i" ta fad'a a cikin zuciyarta, wucewa d'akinta tayi wanka tayi ta chanza kayan jikinta sannan ta fito, lokacin har Inna larai ta gama dama kokon tana soya kosai, wani irin murmushin mugunta Amatullahi tayi sannan taje ta zauna a kan 'yar k'aramar kujerar k'arfe ta dora k'afa daya kan d'aya, cikin jin haushin Amatullahi Inna larai ta ce "Wai ke rashin tarbiyyar taki har ta kai ina aiki ba zaki zo ki k'arb'a ba, koda yake ba laifinki bane laifin wannan k'anjamamman uban naki ne, daga anyi magana sai ya ce ke marainiya ce to uban waye ba marayan ba" magana take cikin fushi, ita dai Amatullahi ba ce komai ba sai murmushi take domin kuwa yau zata koyawa Inna larai hankali "daga yau ba zaki sake bud'ar baki da niyyar zagin iyayena ba, sai nayi miki abin da zaki fi wata d'aya kina jinya baki warke ba" Amatullahi ta fad'a tana 'yar dariyar mugunta sai da ta gama soya kosan gaba d'aya Amatullahi ta tafi gadan-gadan ta hankad'a Inna larai ta fad'a kan wannan man da ta gama suyar kosai gaba d'aya man ya kelayo mata a fuskarta, Amatullahi ta d'auki wannan koko da kosan ta fita domin komawa asibitin tana fita ta bata samu mai adaidaita ba har sai da taje bakin titi ta shiga tace masa "Asibitin nasarawa zaka kai ni" mai adaidaitan ya amsa da "to hajiya" suna isa bakin asibitin nasarawa Amatullahi ta ga Aunty Murja ta fito daga cikin asibitin bayan ta sallami mai adaidaitan ta nufo gurin da Aunty Murjan take da sauri tana cewa "Aunty Murja ina zaki?" k'arb'ar bokitin kokon tayi tare da cewa "Liptom da sugar na fito na siya domin a had'awa Khadijatullahi ta sha, kamar yadda doctor tace naga sha biyun takusa, Amatullahi ta mik'awa Aunty Murja bokitin kosan sannan ta ce "Kawo naje na siyo, ki koma ciki Khadijatullahi tana buk'atar wani a kusa da ita bai kamata mu dinga tafiya muna barinta ita kad'ai ba, Aunty Murja ta k'arbi bokitin kosan sannan ta bata kud'in da fad'a mata abubuwan da suke buk'ata da zata siyo, Amatullahi ta nufi shagon da yake jikin asibitin domin siyo kayan da Aunty Murja ta fad'a mata, ita kuwa Aunty Murja ta koma cikin asibitin, Amatullahi tana gama siyayyar ta nufi cikin asibitin d'akin da aka kwantar da Khadijatullahi ta nufa ta shiga da sallama, suka amsa mata ta k'arasa ta bawa Aunty Murja siyayyar da tayi sannan ta koma gurin da Khadijatullahi take kwance ta d'agota ta taimaka mata ta zauna sannan ita ma ta zauna Aunty Murja ta had'a mata tea ta mik'owa Amatullahi ta ce "Gashi bata ta sha", k'arb'a Amatullahi tayi ta shiga bawa Khadijatullah tea d'in sai da ta koshi ta ture kofin daga bakinta Amatullahi ta ce "Kin koshi ne" kai ta gyad'a mata alamar "Eh" Amatullahi ta ajiye kofin a kan d'an k'aramin teburin da yake d'akin ta sauka k'asa domin ta zuba musu koko da kosan ita da Aunty Murja su ci, Aunty Murja sauka k'asan tayi ita ma tare da cewa "Kin ga tsaya muci a faranti d'aya ba sai kin raba ba" Amatullahi ta ce "to" suna ci suna hira har suka gama abin gwanin ban sha'awa.


*'BANGAREN GIDANSU JABIR*


Zaune suke a kan dinning table suna yin breakfast Mami ta kalli Jabir tare da cewa "Aliyu ya fito kuwa" tab'e baki Jabir yayi tare da cewa "tun jiya da ya shiga d'aki bai fito ba har yanzu" dafe k'irji Mami tayi tare da cewa "na shiga uku Aliyu na" da sauri ta nufi bangaren Aliyu har tana tuntub'e, rufa mata baya sukai gaba d'ayansu, Mami tana zuwa ta shiga bugun kofar tana kiran sunan Aliyu, "Aliyu! Aliyu!! Aliyu!!!" Amman shuru zub'ewa tayi a k'asa tare da fashewa da kuka "Wayyo Aliyu na ka bud'e kofar dan Allah kayi hak'uri" Shahida da Nihal suka zauna kusa da Mamin suna rarrashinta Jabir kuwa cikin zafin rai ya shiga buga kofar kamar zai k'arya "Aliyu ka bud'e kofar nan idan ka bari na k'arya kofar nan ba zaka ji da dad'i ba".
"Aliyu ka bud'e kofar nan nace maka"
Jabir ya d'auki kusan mintina 30 yana buga kofar tare da kiran sunan Aliyu amman shuru babu alamar za'a bud'e kofar kamar ance ya lek'a window sai ya ga kofar baya a bud'e take anan take ya ce "Mami kofar bayan d'akin Aliyu a bud'e take ko dai ya bar gidan nan ne" yayi maganar cike d tashin hankali, da sauri Mami ta mike ta zagaya suka bita a baya d'akin ta shiga ta shiga duba ko ina a d'akin amman babu Aliyu babu alamar sa, hakan yayi matuk'ar tayarwa da Hajiya Asiya hankali domin Aliyu bai tab'a fita ba tare da ya sanar da ita ba "to kodai Aliyu barin gidan yayi ya koma dubai" anan take ta zubai a kan gadon tare da dora hannu a kai, ta fashe da wani wahalallen kuka, Jabir kuwa wayarsa ya zaro a aljihu ya shiga kiran number Aliyu, amman a kashe, fita yayi da sauri bai zame ko ina ba sai wajen da aka tanada domin ajiye motoci, ya shiga d'aya daga cikin jerin motocin wacce ta kasance ta hajiya Asiya ce amman yaran nata suna d'aukar motar idan zasu fita, gidan kakarsu Hajiya Mama ya nufa domin duba Aliyun ko yana nan, yana zuwa ko sallama bai yi ba ya shiga kai tsaye, falon Hajiya Mama ya shiga ya tarar da ita tana kallo ta kishin gid'a a kan kujera, babu gaisuwa babu sallama Jabir ya ce "Hajiya Mama Aliyu yazo gidan nan kuwa" a zabure Hajiya Mama ta tashi har tana kok'arin fad'uwa, domin ko motsin shigowarsa bata ji ba, cike da bak'in cikin irin rashin tarbiyyar da Jabir bashi da ita ta rufe shi da fad'a "Kai wai meyasa baka da hankali ne kawai ka shigowa mutanan gidan zek'ek'e kamar wani bayahude, Aliyu da Shahida k'annanka ne amman sun fika hankali domin inda sune ba zasu tab'a shigowa ba tare da sunyi sallama ba, kuma suna shigowa kafin su fad'i abin da ya kawo su sai sun gaishe ni tukunna, daman wannan me kama da arnan bakin titin halinku d'aya" tana nufin Nihal domin haka take ce mata.


Jabir ya ji haushin maganganun Hajiya Mama dan sunyi matuk'ar kona masa rai, koda ya ga alamar Aliyu baya gidan ya ja tsaki sannan ya fita daga gidan a fusace yana jin Hajiya Mama tana cewa "uwarka ka yiwa tsaki mara tarbiyya kawai". Haka ya shiga motarsa ya ja ta sa k'arfi sai huci yake kamar wanda yaje dambe, kai tsaye club ya nufa, yana zuwa bai shiga cikin club d'in ba ya huce hostel d'in d'akinsa ya huce ya bud'e ya shiga, fridge ya nufa ya bud'e ya d'auko giya ya balle murfinta cikin zafin nama ya shiga kwank'wad'arta har sai da ya shanye gaba d'aya, haka ya k'arasa kan gadon yana tangad'in ya fad'a gadon, yana kwanciya wani amai ya taho masa ya mik'e dakyar da niyyar ya shiga toilet ya zube a kan carpet ya shiga kwara wani irin bak'in amai, sai da ya gama sannan ya mik'e ya koma kan gadon bacci mai nauyi yayi awan gaba dashi.


*'BANGAREN KHADIJATULLAHI*


Alhamdulillahi jikinta yayi sauk'i dan har tana yin hira sama-sama dasu Aunty Murja, ganin yadda jikin nata yayi sauk'i ne doctor Halima ta rubuta musu takardar sallama, suka koma gida suka cigaba da lura da Khadijatullahi, b'angaren Inna larai kuwa tunda Amatullahi tayi mata wannan aika-aikar ta fita ta shiga kurma ihu da neman taimako tayi sa'a kuwa d'anta lado ya shigo gidan yaga yanayin da take ciki dan har fuskarta ta fara sabulewa, a gigice ya k'arasa gurin da take a bage yana tambayarta "Inna meyafara wa yayi miki wannan aika-aikan" cikin rawar muryar ta bud'e bakj dakyar ta ce "Ama....Amatullahi ce lado ka taimkeni ka kaini asibiti" lado kuwa ransa ya b'aci matuk'a "wato rashin mutunci Amatullahi har ya kai ga ta illatawa mahaifiyarsa fuska" ya fad'a a zuciyarsa a fili kuwa ya ce "Wallahi wallahi na rantse miki da girman Allah Inna kamar yadda Amatullahi ta kona miki fuska wallahi nima sai na kona mata", (Ni kuwa 'yar mutanan zazzau nace lado kayi sauri ka kai mahaifiyarka asibiti kar fuskar ta rub'e domin kuwa Amatullahi ba kanwar lasa bace dai-dai take da kai😂🤸🏽‍♀️).


Haka Lado ya d'auki mahaifiyarsa a hannunsa ya nufi waje yayi sa'a yana fita ya tarar da abokinsa Tanimu a cikin motarsa da alama fita zai yi, Lado ya tsayar dashi da sauri, Tanimu ya tsaya Lado ya saka mahaifiyarsa sannan shima ya shiga, yana cewa "Tanimu dan Allah kaimu asibiti mafi kusa damu wallahi wannan shegiyar yarinyar ce ta hankad'a Inna cikin mai", cikin nuna damuwarsa Tanimu ya ce "Subhanallahi gari yaya haka ta faru" tsaki Lado ya ja cike da takaici ya ce "to wannan hatsabibiyar yarinyar ma har a tambaya garin yaya hakan ta faru, wallahi wannan yarinyar idan bata yi wasa ba siyar da ita zan yi kowa ya huta", dariya ce taso ta kwacewa Tanimu amman ya had'iye a zuciyarsa yana cewa "Kai banda abin ka Lado ai wannan yarinyar wallahi bata siyu ba dan duk wanda ya siyeta ya siyi jafa'i dan da kansa zai dawo da ita ya ce ya fasa". Abin da yasa Tanimu ya ce haka akwai wata rana da kanwarsa taje ta tsokani Amatullahi har gida Amatullahi taje ta zagesu gaba d'aya tare da cewa Innarsu "bata iya bada tarbiyya ba", Wani asibiti mai suna *BUBA SPEACIAL HOSPITAL* suka tsaya Lado ya fita da Innarsa ya shiga asibitin yana kiran "nurse! nurse!! nurse!!" Nurses kusan biyar ne suka fito suna tura gadon da ake dora marasa lafiya, Lado ya dora Innarsa ya taimakawa nurses d'in wajen tura innar sukai d'akin tiyata da ita (Allah sarki Inna larai anji bala😂😆). Haka su Tanimu suka zauna har tsawon awa d'aya babu wanda ya fito domin sanar dasu halin da Inna Laran take ciki, Tanimu ya kalli abokin nasa ya ce "Abokina zanje gurin Mama saboda zan kai ta unguwa kuma na barta tana ta jirana" Lado ya sauke ajiyar zuciya ya ce "to Abokina babu komai dan Allah ka mik'a min gaisuwata gurin Mama", "Insha Allahu" Tanimu ya fad'a tare da nufar kofar fita daga asibitin, Lado ya zabga tagumi zuciyarsa cike da tsanar Amatullahi, da kuma d'aukar fansar abin da tayi wa Innarsa.


*'BANGAREN JABIR*


Jabir bai tashi daga baccin ba sai wajen k'arfe uku, ya bud'e idanuwansa ya dorasu a kan wasu kyawawan yammata guda uku kowaccensu sanye take cikin kananun kaya riga da wando, wani kayatatcen murmushi yayi tare da kirawo sunansu "Leemsha, summy,Ammi" kowaccen su ta amsa da "Na'am sweety". Jawo su yayi jikinsa yana shafasu suma suna mai dar masa martani (Ni kuwa 'yar mutanan zazzau nace na shiga uku Jabir sai kace bursuru🙆🏼‍♀️),"Leemsha wacce ta kwanta a kan k'irjinsa tana tana kissing d'in lips d'insa ta ce "Sweetheart meyafaru da kai ne, dan naga kabar kofa a bud'e kuma nasan indai kazo kabar kofa a bud'e kana cikin damuwa ne"


Cikin wata iriyar murya mai wani irin salo mai d'aukar hankali ya ce "Wallahi wata tsohuwar banza ce ta b'ata min rai", Leemsha kuwa bata k'ara cewa komai ba, suka shiga yin bad'alarsu.


*'BANGAREN KHADIJATULLAHI*


Yanzu Khadijatullahi ta fara sakin jikinta kuma ta rage yin koke-kokenta Amman kuma kullum ne babu ranar banza sai tayi wa Jabir mugayen addu'o'i tare da tsine masa, Amatullahi kuwa tunda ta koma gida taga babu kowa tayi wata shegiyar dariya tare da cewa "Yau asibiti yayi d'iba kenan, ai Inna Larai kad'an kika gani indai zaki dinga zagin iyayena zan cigaba da baki wahala wallahi".


Yau kamar kullum suna zaune Amatullahi ta ce"Aunty Murja ya kamata mu fara shirye-shiryen makaranta domin nan da Sati d'aya insha Allahu zamu fara lecture" Khadijatullahi ta kalli Amatullahi domin kuwa ita har ta manta da sun sami admision ta ce "Amatullahi ni na hak'ura da zuwa makarantar kawai ke ki tafi" nan da nan hawaye ya fara zuba daga idon Amatullahi cikin muryar kuka ta fara magana da cewa "kina tunanin zan iya zuwa makaranta ba tare da ke ba, tun muna yara muke tare komai namu tare muke yinsa tun daga primary har zuwa yau babu abin da nake iyawa ba tare da ke ba yanzu kuma ina murna zamu fara zuwa makaranta zamu cigaba da kasancewa tare shine rana tsaka zaki ce min ba zaki je ba ai shikenan nagode sosai" tana gama fad'ar haka ta tashj ta fita daga gidan da saurinta tana kuka, hankalin Khadijatullahi ya tashi mik'ewa tayi ta d'auki hijabi ta saka duk sa cewa bata jin dad'in jikinnata haka ta bi Amatullahi domin ta bata hak'uri, Aunty Murja ta bisu da kallo tabbas k'awancen nasu yana matuk'ar burgeta "Allah ubangiji ya barku tare har abada". Ta fad'a a fili tana murmushi.
Haka Khadijatullah ta bi bayan Amatullah tana kiran sunanta Amman Amatullah ta k'i tsayawa har sai da suka kusan isa gidansu Amatullah, Khadijatullah ta tsaya tana sauke numfashi domin cikin nata Yana tsananin bata wahala, wannan tafiyar ma da tayi ji take tamkar k'afafuwanta zasu fita daga jikinta, ganin Amatullahi tana kok'arin shigewa gidan yasa Khadijatullah ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login