Showing 6001 words to 9000 words out of 83141 words

Chapter 3 - Daren Aurena Part 1 Complete Hausa Novel By Nana M Sha'aban .txt

10 Jan 2025

3076

ba" tayi maganar cikin ladabi. kama hannun Khadijatullahi wacce hawaye sai ambaliya suke a fuskarta, ta shiga goge mata cikin muryar rarrashi ta fara magana "ki yi hak'uri kinji besty, bai kamata ki damu kan ki a kan wannan cikin ba, tunda dai ta hanyar aure kika same shi, nasan dai dole ki ji zafi da bak'in cikin samin cikin saboda irin abin da a kai miki A daren Aurenki". Da kallo kawai Khadijatullahi ta bi ta ba tare da ta ce mata komai ba, zamewa tayi ta kwanta a kan gadon ta rufe idonta zuciyarta na cigaba da k'una, Amatullahi ta kafeta da ido cike da tausayawa, har hawaye na kok'arin zubo mata, amman tayi saurin share hawayen dan kar Aunty Murja ta gani, jin Muryar Aunty Murja tayi tana cewa "Amatullahi ya kamata ki tafi gida tunda kin ga dare yayi k'arfe 9pm yanzu, in yaso gobe sai ki dawo" girgiza kai Amatullahi tayi tana cewa "A'a sam Aunty Murja ba zan iya tafiya gida ba, anan zan kwana dan Allah karki ce in tafi ko na tafi ba zan tab'a samun kwanciyar hankali ba", dafata Aunty Murja tayi cikin so da k'aunar yarinyar ta ce "Haba Amatullahi kina gani fa mun taho dake asibiti ba tare da kin je kin sanar a gida ba, kin ga bai kamata a ce kin kwana ba, kar hankalin iyayenki ya tashi basu san inda kike ba", "girgiza kai tayi a karo na biyu ta ce "waye zan damu idan bai ganni ba, Abbana ne kawai kuma baya gari yayi tafi ba yanzu zai dawo ba, kin san dai irin zaman da nake da step mother tunda Mamana ta mutu, ni yanzu ban da kowa daga Abbana sai kuma ku da nake ganinku tamkar 'yan uwana" ta k'arasa maganar cikin muryar kuka.


Babu yadda Aunty Murja ta iya dole ta kyale Amatullahi domin ta kwana a gurinsu, Amatullahi ta zame ta kwanta, kanta na kusa da k'afafuwan Khadijatullahi ita kuma Aunty Murja daman tana zaune a kan kujerar roba dan haka ta k'ara gyara zamanta domin ta ji dad'in baccin, har sukai bacci idan Khadijatullahi biyu domin kuwa ita ba bacci take ba kawai rufe idonta tayi, tashi tayi zaune tare da d'aga hannayenta biyu sama hawaye na zuba daga idanuwanta ta fara jerowa Jabir mugayen Addu'o'i "ya Allah kaga abin da azzalumin bawanka yayi min, ya Allah na rok'eka kayi min muguwar sakayya, ya Allah kasa Jabir yayi mutuwar wulak'anci, ya Allah ka tarwatsa masa duk wani farin cikinsa ka maye gurin binsa da bakin ciki, bakin cikin da zai dauwama a cikinsa har izuwa ranar tashin alk'ima, ya Allah na rok'eka kafin Jabir ya mutu ka d'ora masa cutar da kowa zai dinga gurinsa ya zama abin k'yamata ga jama'a" sai kuma ta fashe da kuka mara sauti tare k'ank'ame jikinta guri d'aya, ta d'auki kusan mintina goma tana kuka bacci mai nauyi yayi awan gaba da ita.


*B'ANGAREN GIDANSU JABIR*


Kwance yayi a kan tafkeken gadonsa wanda mutane goma sha biyar ma zasu iya kwanciya ba tare da yayi musu kad'an ba, maganar da Amatullahi tayi masa ne ta tsaya masa take ta yawo a kunnansa "yarinyar da ka wulak'anka ka tozarta yanzu tana da ciki" bai san meyasa duk a maganganun da Amatullahi tayi masa ba wannan ta tsaye masa a rai, duk da cewa ba wai Khadijatullahi ce kawai ya tab'awa ciki ba, mata da yawa yayi musu ciki wad'anda ma bazai tab'a arga adadin su ba, amman wasu daga cikin matan su suke kawo kansu wasu kuma ta k'arfi yake yi musu, amman bai tab'a damuwa ba, amman gashi yau a kan cikin Khadijatullahi yayi matuk'ar damuwa har ya kasa yin bacci, wani dogon tsaki ya ja tare da cewa "koma dai menene bazan tab'a yarda cikina ne ba, domin ni bazan had'a zuri'a da 'yar gidan matsiyata ba" a haka dai ya rufe idanuwansa yana cigaba da saka abubuwa da yawa a ransa har bacci b'arawo yayi awan gaba dashi.


*Wanene Jabir?*


Jabir babban d'a ne ga Alhaji Mansur jikamshi wanda ya kasance shine minister mai fetur na k'asa nigeria, mahaifiyarsa hajiya Asiya 'yar wani malami ce wanda ya kasance yana koyar da almajirai karatu sun had'u ne ta sanadiyar mahaifinnata Malam kalla domin Alhaji Mansur idan ya samu lokaci yana shigowa unguwar tasu ya yiwa Malam kalla alheri da kuma almajiran da yake koyarwa, ranar nan yazo gurin Malam kalla sai ga Asiya ta fito daga cikin gidan sanye take da d'an k'aramin mayafi tsugunna har k'asa ta gaishesa cikin fara'a da sakin fuska ya amsa mata sannan ta fita zuwa aike da mahaifiyar ta tayi mata, haka ya tashi ya tafi gida tun daga ranar ya nemi nutsuwarsa ya rasa domin kuwa ya kamu da tsananin son Asiya da ya ga yana neman cutuwa dai haka ya shirya ya nufi unguwarsu Asiya domin ya sami babanta Malam kalla ya sheda masa abin da yake faruwa ya ji ko anyi mata miji.


Yana isa kofar gidan Malam Kalla ya fito daga cikin motar kamar yadda ya saba yaje har cikin rumfar da Malam Kalla yake koyar da Almajirai karatu ya zauna bayan sun gaisa ne.


Alhaji Mansur ya fara magana da cewa "daman Malam na ga 'yar wajen ka ce nace to bari in zo naji ko anyi mata miji ne, dan ni har ga Allah ina sonta da Aure ne a yanzu idan har ba'ayi mata miji ba ma zuwa nan da wata biyu ma nake son ayi biki" Alhaji Mansur yayi maganar cike da girmamawa, wani irin farin ciki ne ya kama Malam Kalla tabbas yayi matuk'ar farin cikin jin wannan furucin daga gurin Alhaji Mansur d'in domin kuwa Alhaji mansur mutum ne da kowane uba zai so ace 'yarsa ta aure sa" dan haka Malam Kalla ya fara magana cikin tsananin farin ciki "Alhamdulillahi Allah na gode maka a gaskiya Alhaji ba zan iya bayyana irin farin cikin da nake ciki ba domjn kuwa nasan kai d'in mutum ne na gari amman ban san wa ka gani ka ke so daga cikin yaran nawa ba?".
Cikin jin dad'in yabon da Malam Kalla yayi masa ya ce "Wacce ta fito ranar da muke zaune ta gaisar da ni ta fita da mayafi", "Ohhhh Asiya kenan" Malam Kalla ya fad'a domin kuwa yasan kaf cikin 'ya'yansa ita kad'ai ce take saka mayafi sauran duka hijabi suke sakawa.
"Eh ita nake nufi" Alhaji Mansur ya ce cikin Murmushin jin dad'i, Malam Kalla ya ce "A gaskiya Asiya ba'ayi mata miji ba, amman dai ban sani ba ko ita akwai wanda take so, ina son ka bani lokaci zuwa gobe domin in zauna da ita duk yadsa mukai da ita zaka ji insha Allahu". "To Malam insha Allahu goben zan dawo kamar dai-dai wannan lokacin", "To Allah ya kaimu" Malam Kalla ya fad'a da murmushi a kan fuskarsa, Alhaji Mansur bayan sun d'an yi hira sannan ya tashi ya ajiyewa Malam Kalla band'ir d'in kud'i ya rabawa almajirai kud'i sukai masa godiya ya tafi zuwa gidansa.
Malam Kalla tunda Alhaji ya tafi ya zauna yayi shuru tabbas yayi matuk'ar farin ciki da har Alhaji Mansur ya ga d'iyarsa ya nuna yana sonta, Amman yaso ace daga d'aya daga cikin 'yan uwan Asiya ya gani ya ce yana so ba Asiya ba, domin Asiya sam bata dace da Alhaji Mansur ba, Macece mai girman kai da nuna isa bata ganin kowa da mutunci hatta shi da yake mahaifinta bata ganinsa da mutunci gashi uwa uba bata da kamun kai kwata-kwata, amman bazai so ace shi da kanshi ya aibata 'yarsa ta cikinsa ba, shiyasa bai nunawa Alhaji Mansur komai ba, kila idan Allah yayi ta sanadiyar Auren da zata yi ta shiryu ta dena duk abin da take yii, a haka dai ya yi ta tunane-tunanansa har a kai sallar magriba ya tashi ya nufi masallaci, anan idarwa ya dawo gida kai tsaye d'akin mahaifiyar Asiya ya nufa, zaune ya tarar da Asiya a kan 'yar yaloluwar taburmar d'akin tana taunar cingum tana danna waya, sallama yayi ya shiga d'akin amman Asiya ko d'agowa ta k'allesa ba tayi ba, baran tana ta amsa sallamar, sai mahaifiyar Asiyar ce wacce take tankad'an garin masara ta amsa sallamar tare da yi masa sannu da zuwa, ya amsa da yawwa sannan ya samu guri ya zauna, ya fara koro bayani.


"Alhamdulillahi! Alhaji Mansur wanda yake zuwa gurina shine yau yazo min da maganar da ta sakani cikin farin ciki", cikin murna da farin ciki Inna ta ce "Wace magana ce wannan malam", "Wace yayi yana son Asiya zai aureta" ai kafin Malam Kalla ya k'arasa maganar Asiya ta mik'e tsaye cike da farin ciki, daman ta dad'e tana fatan Allah ubangiji ya mallaka mata Alhaji Mansur a matsayin mijinta domin kuwa tunda taga yana zuwa takanas yana yiwa mahaifinta alheri ta san ba k'aramin Attajiri bane shiyasa duk inda ta ganshi take tsugunawa har k'asa ta gaishe sa, gaba d'aya taji ta fara kyankyamin d'akin nasu ta fara magana cikin rashin girmamawa "Ai daman nasan zance yana sona domin na had'a dukkan abubuwan da ko shugaban k'asa ne ya ganni sai ya ce yana sona, daman na sha fad'a muku ni ba matar talakawa bace ai yanzu kun fara ganin gaskiyar al'amarin, kuma wannan gidan bai dace ace nii Asiya irin yadda nake da kyau ace ina zama a cikinsa ba, na de kusan na fita daga cikinsa na rabu da k'aya, ba zan sake gangancin k'ara shigowa ba". ta k'arasa maganar tare da fita daga gidan da sauri tana toshe hanci (ni kuwa 'yar mutanan zazzagawa nace daga baya kenan😂).


Wani irin kuka Inna ta fara yi tana cewa "na shiga uku ni Indo ya ubangiji meyasa ka jarabceni da yarinyar da bata ganin mutuncinmu ni da mahaifinta", cikin muryar rarrashi Malam ya shiga bata hak'uri, har ya samu tayi shuru, Malam Kalla da Indo aure gida aka yi musu kasancewar iyayensu sun yaya da k'anine, tun daga ranar da ya aureta yake nuna mata soyayya har kawo yau da suka haifi 'ya'ya hud'u dashi kuma duka mata Asiya ce babba sai mai bi mata Hauwa,Hafsa, Hajara sai kuma k'aramarsu Na'ima, sam Malam Kalla baya k'aunar ganin bacin ran matar tashi ko kuma ganinta cikin damuwa shiyasa sam yake jin zafin 'yar tasu Asiya saboda kusan kullum sai ta saka Indo hawaye.


'bangaren Asiya kuwa tana fita kai tsaye bakin titi ta nufa ta tari mai adaidaita tayi masa kwatancen inda zai kai ta, a wani k'aton super market ya sauketa daman ta akwai ragowar kud'in da ta d'auka a jakar Inna naira 200 ta bashi ta nufi super market d'in, tana zuwa bakin kofar shiga super market d'in masu gadi suka hanata shiga, anan take ta k'ara jin haushin Mahaifiyarta da bata tsaya ta auri mai kud'i ba ta auri wannan matsiyacin Malamin, ta san yanzu da sun ganta da kaya mai tsada basu isa sun hanata shiga ba,amman kuma da ta tuna gurin wanda tazo kuma zata aura anan ba da dad'ewa ba, sai ta ji wani farin ciki ya lullub'eta, "Hmm da kun san wanda zan aura ba zaku tsayar dani,ku hanani shiga ba", d'aya daga cikin masu gadin ya ce "to mu ina ruwanmu da wanda zaki aura" Asiya ta bud'e baki zata yi magana kenan ta hango Alhaji Mansur ya nufo kofar fita daga super market d'in, cikin farin ciki da jin dad'in ganinshi ta shiga gyara mayafin dake jikinta, Alhaji Mansur yana fitowa idanuwansa suka sauka a kan masoyiyar tasa a nan take wani farin ciki ya lullub'esa "Asiya!" ya kirawo sunanta cikin wata iriyar murya,wacce take d'auke da wani irin salo, "Na'am Alhaji" tayi maganar cikin yauk'i da yanga, "Me kika zo yi anan" murmushi tayi tare da cewa "Bakomai" tayi maganar a takaice, "To shikenan muje in kai ki gida ko?" yayi maganar tare da yin gaba, ta bisa a baya kamar wata gela (ni kuwa 'yar mutanan zazzau naje Asiya ko kunya baki ji ba🤔).


Bud'e mata gurin mai zaman banza yayi ta shiga da sauri sanyi A.C ya daki fuskarta ta lumshe ido, "Arzik'i dutse takashi ake ni dai kam na taka nawa" tayi maganar a cikin zuciyarta, Alhaji Mansur ya zagaya ya bud'e wajen driver ya shiga ya ja motar ya nufi gidansu Asiyan, sun d'an yi nisa sosai babu wanda ya kuma yin magana daga cikinsu, har sun kusan isa gidan Alhaji Mansur ya ce "Sarauniyar mata da fatan kin ji sakona gurin Malam" ta ce "Eh Alhaji na ji" tayi maganar tare da sunkuyar da kanta "to kin amince" wani kayatatcen murmushi tayi a zuciyarta ta ce "Anzo gurin, banda abin ka Alhaji wacce macen ce mai kud'i irin ka zai ce yana sonta ta k'i amincewa" a fili kuma ta gyad'a kai alamar "Eh". Alhaji Mansur ya ji dad'in amsar da ta bashi, suna isa gidan sun d'an dad'e suna hira sannan sukai sallama ta fito ta shige gidan cike da farin ciki fal zuciyarta.


Tun daga ranar soyayya mai k'arfi ta shiga tsakanin Alhaji Mansur da Asiya, ko sati uku basu yi da fara soyayya ba ya turo iyayensa aka saka ranar aurensu, wulak'anci da rashin mutunci Asiya ta shiga yiwa 'yan uwanta da iyayenta, domin kuwa har cewa take idan ta auri Alhaji Mansur suka sake, sukace zasu zo gurinta wallahi sai ta saka anyi musu korar k'are, shiyasa sam basa shshshige mata suka barta take hada-hadar bikinta ita kad'ai kuma kowaccensu tayi alk'awarin ko talauci zai kashesu ba zasu je gurinta da niyyar taimako ba ko ziyara.


Ana saura kwana uku d'aurin aure Asiya ta tattara kayanta wad'anda Alhaji Mansur ya bata kud'ad'e ta siyo su ta saka su a d'an k'aramin akwati ta fito kallonsu take yi d'add'e a wulak'ance tare da cewa "to sai anjimanku sai mun had'u a darussalam" ta fad'a tare da fita daga gidan Hajara cike da mamaki da tashin hankali ta ce "Innarmu wai Aunty Asiya yau ne bikin nata" cike da bak'in ciki Inna ta ce "Oho ita ta sani ai duniya ce ta isa kowa riga da wando wanda bai zo bama jiransa take" ina tak'arasa maganar tare da fashewa da kuka gaba d'ayansu sukai kanta suna rarrashinta da kalamai masu dad'i tabbas ta ji dad'i da ya kasance tana da wasu yaran dan da Asiya ce kad'ai 'yarta da bak'in ciki ya kasheta,Asiya kuwa tana fita gidan k'awarta Azima ta nufa daman har an ware mata d'akinta da zata zauna a ciki, Azima k'awar Asiya ce, ta gudo daga garinsu saboda auren dolen da iyayenta zasu yi mata tazo ta kama gida anan garin kano take zaune Alhazawa suna zuwa su d'auketa a tafi hutun yawon shak'atawada ita, wannan shine takaitatcen tarihin Azima k'awar Asiya, Anan gidan Asiya ta zauna har ranar d'aurin aure Azima ta gayyato k'awayenta 'yan bariki sukai ta shek'e ayarsu, har lokacin kai Amarya ya yi Alhaji Mansur ya turo motoci gidansu Asiya amman aka ce musu ba anan take ba, a kasa rakasu har gidan A ka fito da Amarya aka nufi makeken gidanta, suna zuwa suka kai ta har kan gadonta, sukai mata sallama domin suna da fita club yau akwai casun da za'ayi, suka tafi, Asiya ta yaye mayafin da aka lillib'eta ta shiga zata gidan lungu da sako tana dad'a godewa Allah, da ya mallaka mata Alhaji Mansur a matsayin mijinta, A babban falo ta ci karo da Alhaji Mansur murmushi suka sakarwa juna sannan Asiya ta koma d'akin da sauri shima ya rufa mata baya, daga nan suka shiga cin amarcin su har na tsawon kwana bakwai Alhaji Mansur yayi musu visa zuwa dubai, murna a gurin Asiya ba'a magana ta rasa inda zata tsoma ranta dan dad'i wai yau ita ake cewa zata je dubai,muryar Alhaji Mansur taji yana cewa "To gobe sai mu je ki yiwa su Malam da Mamata sallama tunda jibi zamu tafi" anan take Asiya ta b'ata rai ba tare da ta ce komai ba, domin kuwa tunda ta samu ta rabu da wad'annan iyayennata bata k'aunar sake ganinsu har abada, kuma uwar mijin nata ma bakyata tayi ba, domin akwai ranar da ta kira a waya ta ce ta bata su gaisa ta ce kunnanta ne yake ciwo ba zata iya amsa kira ba.


Washe gari kuwa da duku-duku ta fara k'irk'irar rashin lafiyar k'arya domin karta je gurin iyayenta da kuma iyayen mijin nata,Alhaji Mansur hankalinsa yayi matuk'ar tashi jin matar tasa bata da lafiya, bayan ya bata abincin ya bata magani yaje shi kad'ai yayi musu sallama tare da basu uzurin Asiyan bata da lafiya ne shiyasa bata zo ba, shi dai Malam Kalla yana fad'a masa yasan k'arya take kawai bata son zuwa ne, washe gari da sassafe jirginsu ya d'aga zuwa dubai, watan su d'aya a dubai Asiya ta samu ciki zo kaga murna gurin masoyan biyu tamkar zasu had'iye junansu, haka sukai ta rainon cikin har ya kai watansa na haihuwa, a ranar wata labara ta haifi kyakkyawan d'anta mai kama da mahaifinsa, ranar suna a kasa saka masa suna Jabir a ranar da akai sunan da daddare Mahaifiyar Alhaji mansur ta kira a waya tayi ta masa fad'a a kan cewa yaje chan wata k'asa har matarsa ta haihu amman ba zan dawo a yi sunan a kano ba, hak'uri yayi ta bata ita kuwa Asiya tab'e baki tayi tare da jan ga gejeren tsaki, da yake suna da d'an tazara tsakaninsu Alhaji Mansur bai ji tsakin ba, haka ya katse wayar rayuwarsu ta cigaba da tafiya cikin farin ciki da walwala, Jabir ya taso cikin sangarci da gata daman ta yaya za'ai mara tarbiyya ace zata bawa wani tarbiyya dan haka Jabir ya debo gaba d'aya halayyar mahaifiyarsa a lokacin da Jabir yake shekara bakwai Asiya ta kuma samun ciki, suka dawo kano domin kuwa wannan cikin cewa Alhaji Mansur yayi a garin kano zata haifeshi kuma Jabir ya je ya ga kakanninsa domin ya sansu haka dai suka tahi ba dan ran Hajiya Asiya yaso ba, suna isa suka tarar har an gyara gidan haka aka zo ana tayi musu sannu da zuwa amman

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login