Showing 36001 words to 39000 words out of 83141 words
Chapter 13 - Daren Aurena Part 1 Complete Hausa Novel By Nana M Sha'aban .txt
tare da cewa "Amman Yaya Safwan, nayi tunanin kafi kowa sani na, ka san ba zan iya yin irin wannan ba, ka ba ni mamaki ban yi tunanin haka daga gurinka ba", ta fad'a tana kuka Mai tsuma zuciya "na sani ban kyauta ba, ki yafe min insha Allahu hakan ba zai sake faruwa ba","Shikenan ya huce Yayana" wani irin farin ciki ne ya kama shi haka suka jera har wajen motarsa, sun dad'e suna hirarsu ta masoya daga k'arshe kuma suka yi sallama Hafsa ta koma gida zuciyarta cike da farin ciki, daman ta fito daga gidan ne saboda ba ta k'aunar su yi magana da Yaya Safwan d'in shine ya biyo ta, d'akinta ta shiga ta tarar Khalid ya kwanta Yana bacci fad'awa kan gadon tayi ta lula duniyar soyayya.
*WASHE GARI☄️*
Nihal ta farfad'o Shahida ta kira Hajiya Asiya ta fad'a mata babu shiri ta fito kamar wata korarriya tana zuwa Asibitin ta rumgume Nihal d'in tana kuka "yarinyata" Teemarh wacce take tsaye dan yanzu ta ji sauk'i tun da aka yi Mata allurai da k'arin ruwa ta Warware sosai, Baki ta tab'e Hajiya Asiya ta kudurce a zuciyarta Nihal ba za ta sake komawa gidan Salis ba sai ya saketa sai dai duk abin da zai faru ya faru.
Alhaji Mansur ne yake tafiya cikin motarsa a nutse yake tukin gidan Hajiya Mama ya nufa domin shi bai San ma abin da ya faru da Nihal d'in ba, Yana zuwa ya tarar da Aunty Murja tana wanke-wanke yayi sallama tare da ja ya tsaya Yana kallonta, tabbas nan da sati mai zuwa zai yi kok'arin ganin an d'aura aurensu domin ba zai iya hak'ura ace har sai sati uku ba, Aunty Murja ta d'ago suka had'a ido dashi murmushi ya sakar Mata tare da cewa.
"Amincin Allah ya k'ara tabbata a gareki ma'abociyar nutsuwa da hankali kyakkyawar Matata wacce nake saka ran a cikin wannan satin zan fara tunanin samun 'ya'yana daga gareki".
Murmushi kawai tayi tare da sunkuyar da Kai, Amman kalmar da ta tsaya mata ita ce da Alhaji Mansur d'in ya ce a cikin wannan satin zai fara saka ran samun 'ya'ya, to shine ta rasa gane meyake nufi.
'yar k'aramar kujerar k'arfe ya d'auko ya ajiye kusa da ita ya zauna, da sauri ta kallesa domin kuwa gurin da rana sosai "ka tashi daga nan akwai rana sosai, karka sami matsala","A'a na k'i" ya fad'a yana mak'e kafad'a kamar wani k'aramin yaro, abin ya ba wa Aunty Murja dariya sosai, tsayawa yayi Yana kallonta tare da cewa "Murjanatu dariyarki tana saka ni nishad'i fi ye da yadda bakya tunani".
Kallonsa ta yi sosai ta ce "Kai ne ai ka ke ba ni dariyar, nagode sosai Kuma......" Sai kuma tayi shuru tare da yin wasa da zoben hannunta, Alhaji Mansur ya k'ura Mata ido tare da cewa "Kuma me?","Bakomai"ta bashi amsa har lokacin tana wasa da zoben hannunta, "ba za ki fad'a min ba ko?", Kai ta girgiza Masa alamar "A'a".
Mik'ewa yayi fuskarsa ta chanza zuwa yanayin fushi ya nufi hanyar waje, da sauri Aunty Murja ta bi bayansa a gabansa ta tsaya tana cewa "Dan Allah ka yi hak'uri","to fad'a min kuma me?" Aunty Murja ta ce "Daman godiya kawai zan maka" ta fad'a dan ba za ta iya fad'a masa abin da ke ranta ba, tana jin tsananin kunyarsa.
"Shikenan nagode miki sosai, kuma nasan matsayina a gurinki tunda kin k'i fad'a min kin nuna min ban kai matsayin da zan san abin da ke ranki ba" Yana gama fad'ar haka ya huce ya fita motarsa ya shiga ya ja ya bar unguwar, Aunty Murja tsugunnawa tayi a k'asa tare da fashewa da kuka gaba d'aya haushin kanta take jii a kan meyasa ba ta fad'a masa ba, har ta bari yayi fushi da ita.
Hajiya Mama kuwa duk abin da suka yi tana jin su, domin kuwa tana cikin toilet ne ta shiga kama ruwa kuma tsakanin toilet d'in da inda suke babu nisa, murmushi tayi sannan ta koma d'aki ba tare da ta bari Aunty Murjan ta ganta ba, a zuciyarta tana cewa "sai yanzu Mansur zaka san zakai aure".
Ita kuwa Aunty Murja haka ta gama shan kukanta sannan ta tashi ta k'arasa wanke-wanken ta kifesu a kwanbo sannan ta shiga d'akin Hajiya Mama ta yi Mata sallama ta fito ta nufi gida zuciyarta a cunkushe.
*POLY🚴🏽♀️🏦*
Zaune suke su uku kamar kullum komai nasu iri d'aya abin gwanin ban sha'awa, Hafsa tana ba su labarin yadda suka yi da Yaya Safwan, Amatullahi tayi murmushi tare da cewa "Ahhh Lallai lovers ina ta ya ki murna k'awata, ki ce mun kusan shan biki" murmushi Hafsa tayi tare da cewa "insha Allahu" Khadijatullah ta ce "Nima ina ta ya ki murna k'awar arzik'i","Nagode muku sosai k'awayen arzik'i" Hafsa ta fad'a tana murmushin jin dad'i haka dai sukai ta hirarsu abin burgewa gaba d'aya makarantar suna burgesu dan wasu ma sunyi tunanin 'yan uku ne, babu wanda yayi tunanin ya iyayensu d'aya ba, sai da aka koma aji sannan suka tashi domin komawa ajinsu.
Wajen k'arfe 6:00pm dai-dai aka tashi suka fito Yaya Safwan Hafsa ta hango ta saki wani irin murmushi sannan ta ce "yau fa, Yayana ne ya zo d'aukarmu" Murmushi Amatullahi tayi ta ce "gaskiya Yaya Safwan yana ji da Amaryarsa sosai" dariya Hafsa tayi sosai tare da cewa "ai dole ya ji da Amrish d'insa, ku taho mu tafi" Khadijatullahi ta ce "A'a zamu hau adaidaita Aunty Murja ta aikemu" babu yadda Hafsa ba tayi ba a kan su taho in ya so sai su biya wajen da Aunty Murja ta aikensu daga nan su kai su gida, amman Khadijatullahi ta kafe a kan Aunty Murja ta aikesu kuma gurin da nisa, haka Hafsa ta hak'ura ta tafi zuciyarta babu dad'i.
Amatullahi kuwa mamaki ne ya isheta ita dai ta san babu inda Aunty Murja ta aikesu, amman kuma Khadijatullahi ta ce ta aikesu, haka dai suka fita suka nemi adaidaita suka shiga, Amatullahi ta kalli Khadijatullahi sosai sannan ta ce "ina Aunty Murja ta aikemu?" Khadijatullahi ta kalleta tare da cewa "ba ko ina" Amatullahi ta ce "to meyasa ki ka cewa Hafsa Aunty Murja ta aikemu","Saboda ba na son ko gaisuwa ta k'ara had'a ni da wani namijin, na tsani maza wallahi ji nake kamar na kashesu" shuru Amatullahi tayi daman ta san za'a rina, shi kuwa mai adaidaita tsoro ya kamashi "to anya wannan yarinyar lafiyarta k'alau kuwa" ya fad'a a zuciyarsa haka dai yayi ta mamaki har ya kai su kofar gida suka sauka Khadijatullahi tayi gaba Amatullahi ta tsaya domin biyansa kud'insa.
Haka ta bi bayan Khadijatullahi suka shiga gidan da sallama Aunty Murja suka tarar kallo d'aya zakai mata kasan tana cikin damuwa zama suka yi kusa da ita suna tambayarta "me yake damunta" ta ce "bakomai" wannan karan basu takura mata ba domin kuwa kowannan su zuciyarsa cike take da damuwa.
*'BANGAREN NIHAL😹🚴🏽♀️*
Hajiya Asiya haka ta tattara Nihal ta nufi gida da itaba tare da Salis ya sani ba, Nihal ba ta san k'udurin Mamin ba dan duk a tunaninta sun fad'awa Salis d'in zata yi jinya a gida ne idan ta warke sai ta koma, dan da Alhaji Mansur ya dawo ya ga Nihal d'in yake tambayar meya sameta, Hajiya Asiya ta bashi labarin k'arya da gaskiya ta fad'a masa, da ya tambaya an fad'awa Salis d'in za'a taho da ita gida, Mami ta ce Eh an fad'a masa, Alhaji Mansur bai zurfafa bincike ba, domin duk ya d'auka da sanin Salis d'in.
Kwanan Nihal biyar a gidansu sai ga Salis ya zo gidan domin jin shuru Nihal ba ta dawo ba, Nihal ta fito raka wasu k'awayenta ta hango Salis d'in da sauri ta k'arasa gurin da yake tana murmushi, shi kuma ya had'e fuska, Mamaki ta shiga yi "Yaya Salis me ya faru?" Harararta yayi sannan ya ce "ban sani ba, tunda ke kwata-kwata bakya tausayina","Ayya sorry Yayana, tuba nake ba zan sake ba" Salis ya ce "babu abin da zaki ce min tunda baki fad'a min zaki dawo gida ba, kuma gashi kwananki uku" ido Nihal ta zaro tare da cewa "wai daman Mami ba ta fad'a maka ba ta ce mana ta fad'a maka zan dawo gida har sai nayi wata d'aya zan koma" Mamaki ya kama Salis ya ce "ni d'in ne na fad'i haka, to wallahi Mami ba ta kirani ba" Shuru Nihal tayi na wani lokaci sannan ta ce "kayi hak'uri Yaya wallahi......" Dakatar da ita yayi yana murmishi "haba Sweetheart bakomai wallahi, yanzu ki je ki shirya ki zo mu tafi gida" ta ce "to shikenan" ta juya ta nufi gidan, d'akinta ta nufa ta hijabinta ta d'auka sannan ta fito kallonta suke cike da mamaki Shahida ta ce "Otherhalf ina zaki je?","Yaya Salis ne yake jirana zamu tafi" Mami ta mik'e cikin fushi tare da cewa "babu inda zaki je, kin dawo kenan" Abba ya kalleta cike da mamaki sannan ya ce "ba Salis d'in ya ce sai nan da wata d'aya ba fasawa yayi ne" Nihal ta ce "Abba Yaya Salis bashi da masaniya a kan wannan zance Mami ce ta fad'a yanzu yake fad'a min, wai na taho gida ba'a fad'a masa ba" Abba ya ce "daman baki fad'a masa ba Nihal" Nihal ta ce "Abba ba laifina ba ne Mami ce ta ce min ta fad'a masa kuma ta kwacen waya ni nayi tunanin d gaske take yi, ashe sharri tayi masa" Wani irin wawan mari Mami ta d'auke ta dashi tana cewa "Wani k'aton banza zaki fifita a kai na to wallahi ba zaki koma ba, shegiya wacce ba ta san ciwon kanta ba" Abba kuwa cikim fushi ya tashi ya nufi inda Mamin take ya zabga mata mari yana cewa "to sai mu gani, tunda ke baki da hankali, ke Nihal wuce ki bi mijinki ku tafi gida" Nihal ta ce "to Abba" ta fita da sauri tana kuka tana zuwa gurin Salis yake tambayarta "menene take kuka?" ta fad'a masa komai da komai nan ya shiga rarrashinta sannan ya bud'e mata mota ta shiga ya koma mazaunin driver ya ja mota suka bar gidan.
*BAYAN KWANA BIYU*
A yau ne aka d'aura auren Alhaji Mansur da Aunty Murja wanda aka biya sadaki naira dubu dari biyar kwata-kwata Aunty Murja ba ta da masaniya a kan auren ta zo gidan Hajiya Mama tana yi aiki ta gama wanke-wankr ta fara shara har ta kusan gama sharar sai ga Alhaji Mansur ya shigo gidan, da sauri Aunty Murja ta d'ago saboda jin kamshin turararsa wata iriyar nannanyan ajiuar zuciya ta sauke wani irin farin ciki ya ziyarci zuciyarta rabon da ta ganshi tayi kusan kwana biyar amman ji take kamar tayi shekara biyar ba ta ganshi ba a fili ta ce.
"Sannu da zuwa, dan Allah ka yi hak'uri" tayi maganar kamar za ta yi kuka, k'arasawa kusa da ita yayi yana murmushi jikinsa ya jawota ya rumgumeta, da sauri ta fizge jikinta daga cikin nasa bakinta na rawa ta ce "Hakan bai da ce ba, saboda ni ba muharramarka ba ce, ba za ka samu damar min irin haka ba har sai an d'aura mana aure" Murmushi ya kuma yi a karo na biyu sannan ya ce "Ai kin san ban tab'a yi miki irin haka ba, saboda nasan ke ba muharramata ba ce, amman yanzu ina da damar yin komai a kan ki, dan haka karki haka ni".
Shuru Aunty Murja tayi tana cewa "ban fahimci me kake nufi ba, dan Allah ka fahimtar da ni" jawota yayi jikinsa wannan karon bata yi yunk'urin hanashi ba,wayarsa ya d'auko ya kunna vedio da ya saka a ka yi a d'aurin aure ya ba ta a hannunta tana kalla, muryar liman ta ji yana cewa "An d'aura auren Alhaji Mansur jikamshi da Murjanatu Abbakar mai yak'i a kan sadaki naira dubu dari biyar" da sauri ta d'ago tana kallonsa tana cewa "wai da gaske ne, ba mafarki na ke ba an d'aura aurena da kai, idan har mafarki na ke yi zan so ace na dauwama cikin mafarkin nan ba tare da na farka ba" Sumbatarta yayi a goshi sannan ya ce "da gaske ne ba mafarki kike yi ba Amaryata, amman ni har yanzu ina fushi da ke sosai wallahi" idanuwanta suka ciko da kwalla ta ce "ka yi hak'uri","ni ba zan hak'ura ba, kawai ki fad'a min kuma me?" idanuwanta ta rufe a hankali ta ce "kuma ina sonka sosai" wani irin farin ciki ne ya kama shi ji yake kamar anyi masa albishir da gidan aljanna "nima ina sonki Murjanatu" ya fad'a cikin wani irin yanayin farin ciki.
Muryar Hajiya Mama suka ji tana kiranta da sauri ta bud'e ido tana kok'arin zame jikinta domin zuwa kiran Hajiya Mama, amman Alhaji Mansur ya k'i barinta ta je domin ya rumgumeta sosai a jikinsa "Dan Allah ka bar ni naje kiran da Hajiya take min","idan kina so na cika ki,ki je to ki fad'a min wani suna zaki dinga fad'a min, dan na fuskanci bakya son kirana da kowane irin suna" Aunty Murja ta yi shuru cike da jin kunya a zuciyarta tana cewa "lallai wannan mutumin na fuskanci d'an soyayya ne, ga rigima iri-iri a cikinsa" Amman a fili ba ta iya cewa komai ba, jin alamar Hajiya Mama tana kok'arin fitowa daga d'akin ta ce "Yaya zan dinga cewa maka" tayi maganar da sauri tana juya bayanta tana kallon falon dan ba ta son Hajiya Mama ta fito ta gansu a haka.
"To naji har a gaban kowa haka zaki dinga ce min?" Ta gyad'a kai alamar "eh" cika ta tayi dai-dai lokacin Hajiya Mama ta fito daga d'aki ganinsu a tsaye yasa tayi murmushi "Ashe Amaryar tana gurin Angonta shiyasa nayi ta kiranki na ji shuru" Aunty Murja kunya duk ta kama ta kamar ta nutse a k'asa, tsintsiyar ta tsugunna za ta d'auka domin ta cigaba da shara Hajiya Mama ta kira sunanta "Murjanatu ki bar sharar nan zan k'arasa ki zo ki shiga bayan gida ki yi wanka ki zo ki shirya anjima za'a yi walima","To" abin da Aunty Murja ta ce kenan sannan ta huce d'akin domin ta yi wanka kamar yadda Hajiya Mama ta ce mata.
Shi kuwa Alhaji Mansur a tsakar gidan ya shimfid'a taburma suka zauna da Hajiya Mama suna hirarsu ta d'a da uwa, su Amatullahi da Khadijatullahi ne suka yi sallama domin yau sun ji Aunty Murjan ta dad'e sosai ba ta dawo ba shiyasa suka biyo bayanta "Lale da zuwa 'yan tagwaye wato yau kun ji auntyn ta ku shuru ba ta dawo ba ko?" Hajiya Mama tayi tunanin Amatullahi da Khadijatullahi 'yan biyu ne shiyasa take ce musu tagwaye"Eh Hajiya mun ga har yanzu k'arfe sha biyu na rana kuma idan ta koma tana dawowa k'arfe biyu shiyasa muka zo mu taimaka mata da aikin" Amatullahi ta fad'a sannan suka tsugunna suka gaishe da Hajiya Mama da Alhaji Mansur.
Suka amsa fuskarsu cike da fara'a Hajiya Mama ta dora da cewa "Ai kuwa daga yau tare da ku zamu dinga zama domin kuwa Auntynku yau an d'aura mata aure anjima kad'an za'ayi walima tana d'aki wanka take yi" Khadijatullahi ta d'ago da sauri tana mamaki "An d'aura mata aure kuma?","Eh Khadija" Hajiya Mama ta bata amsa a takaice, Amatullahi kuwa murna ce ta isheta "Kai Hajiya Mama amman na ji dad'i ya kamata na yi miki kyautar goro" Amatullahi ta fad'a tana murmushi, duk da yanayin da Khadijatullahi take ciki domin tsoro take kar ayi wa Aunty Murjan abin da Jabir yayi mata a daren aurensu sai da maganar Amatullahi ta bata da dariya ta ce "Hajiya karki yarda so take ta mayar da ke tsohuwa kuma fa tasan kin fi ta jii da kuruciya" Alhaji Mansur dariya yayi sosai sannan ya ce "Lallai 'yan k'annan nan na wa sai na zane ku Hajiyan ku ke yi wa tsiya haka" Hajiya Mama ta ce "Kyalesu ai Allah ya kawo mu, zasu fara yi min tsiya" Gaba d'ayansu dariya suka yi sosai.
Nan Hajiya Mama take fad'a musu cewa Alhaji Mansur shi ne ya auri Aunty Murja, sai a lokacin hankalin Khadijatullahi ya d'an kwanta domin ta fahimci Alhaji Mansur d'in ba zai tab'a iya aika irin abin da Jabir yayi mata ba, haka dai sukai ta wasa da dariya abin gwanin ban sha'awa.
*'BANGAREN GIDANSU JABIR😂*
Zaune suke a falo gaba d'ayansu suna kallon film d'in Tarkon k'auna a tasha arewa 24 Shahida da ke zaune a kan kujera one sitter ta d'auki remote ta chanza tasha zuwa Tauraruwa tv,Hajiya Asiya ta bud'e baki cike da masifa zata fara zazzagawa Shahida masifa sai ji tayi ana sanar da d'aurin auren Alhaji Mansur da Aunty Murja tare da katin Walimar da za'ayi a gidan Hajiya Mama da misalin k'arfe 2:00pm na rana.
A zabure Hajiya Asiya da Jabir suka tashi bakin Hajiya Asiya na rawa ta fara cewa "me nake ji a cikin t.v Abban Jabir yayi aure" Fad'uwa tayi k'asa sumammiya, Jabir kuwa zage-zage ya shiga yii, Aliyu ne ya d'auko ruwan sanyi ya watsawa Hajiya Asiya a fuska nan ta farfad'o wani irin kuka ta fashe dashi "na shiga uku innalillahi wa inna'ilaihi raju'un Alhaji ya kashe min rayuwa ya lalata min duk wani burina wallahi duk wacce tayi gangancin zuwa gidan nan da sunan kishiyata sai na kasheta wallahi sai na illatata sai dai a fita da gawarta wannan gidan da kuma Abban Jabir nawa ne ni kad'ai babu wata shegiyar da ta isa na had'a miji da ita, kuma wannan munafikar uwarta sa wallahi sai na yi mata abin da ba za ta tab'a mantawa da ni ba" Tana kuka take maganar.
Aliyu da Shahida kuwa tashi suka yi kowannan su ya nufi d'akinshi, Teemarh kuwa tashi tayi tare da fashewa da wata iriyar mahaukaciyar dariya "kai ya ubangiji yau ban san wane irin farin ciki na ke ciki ba, gaskiya zan je walima na ta ya Abba farin ciki, gwanda da yayi auren wannan shine abin da ya dace da jakar uwa irin ki" Tana gama fad'ar haka ta wuce