Showing 51001 words to 54000 words out of 83141 words

Chapter 18 - Daren Aurena Part 1 Complete Hausa Novel By Nana M Sha'aban .txt

10 Jan 2025

3093

Aunty Murja suka yi suna kwasar gaisuwa gurin Hajiya Mama, ta amsa musu cikin sakin fuska sannan suka nufi d'akin da Khadijatullah take duk inda suka huce sai ma'aikatan gurin da likitoci sun tsugunna suna ta kwasar gaisuwa suna shiga Amatullahi ta nufi gurin da Shahida da Nihal suke ta ce "kun kira besty kuwa?","A'a yanzu zan kirata" Shahida tayi maganar tare da d'auko wayarta Hafsa ta kira take fad'a mata Hafsa ta haihu,babu shiri ta fito ta Ado driver ya nufi da ita asibitin da yake asibitin ba wani boyayye ba ne, a cikin awa minti talatin asibitin ya cika damkam da jama'a Jabir,Teemarh da mahaifiyarsa Asiya kuwa ba su san abin da ke faruwa ba, kuma babu wanda yayi gangancin sanar dasu, domin a cewarsu ba yanzu ya kamata su san komai ba, akwai abin da Hajiya Mama da kuma Alhaji Mansur suke shiryawa wanda babu wanda suka sanar sun barshi a cikin zuciyarsu.


*'BANGAREN SAFWAN DA SAFNA*


Safna wata iriyar kulawa ta musamman take ba wa Safwan kullum tana manne dashi, ji take wannan karayar dama a k'afarta take ba a tasa ba, wani irin sonshi da k'aunarshi take ji suna k'ara ratsata domin kuwa Safwan kullum cikin kasheta yake da kalaman soyayya ita kuma sai k'ara narkuwa take a cikin kogin soyayyarta, yau ma kamar kullum tana zaune a kan kujera kusa dashi ta dora kanta a kan kafad'arsa idanuwanta a lumshe ta kama hannayensa duka biyun ta rike "Ruhina" Safwan ya kirata cikin wata iriyar murya mai rikita zuciya "Na'am Ruhina'' Safna ta amsa tana mai bud'e idanuwanta tare da d'ago kanta tana kallonsa ido cikin ido tana sakar masa wani irin murmushi.


"Ruhina ban san meyasa ba kullum nake k'ara jin sonki da k'aunarki a cikin zuciyata, ina sonki sosai Ruhina tabbas na k'ara yarda cewa Safna ke ce Ruhina", Safwan yayi maganar yana kallonta cikin wani irin yanayin soyayya, "Hafsa kuma zuciyarka kuma Rayuwarka ko?" Tayi maganar hawaye na zuba daga cikin idanuwanta domin kuwa duk sanda ta tuno cewar Safwan zai auri Hafsa kuma daga ranar da ya aureta shikenan ya zama ba na ta ita kad'ai ba, kuma ita ma Hafsan haka zai dinga yi mata kalamai kuma gashi ma a gabanta ya ce Hafaa zuciyarsa ce kuma Rayuwarsa ita kuma kawai Ruhinsa ce kuma tana tunanin kawai dai dan ya ga tana son shi sosai ne shiyasa yake biye mata kuma uwa uba saboda d'ansu Khalid.


Safwan cikin yanayin damuwa ya shiga share mata hawayenta yana cewa "Haba menene haka Safna matsayin da kike dashi daban haka ma, matsayin da Hafsa take dashi daban yake da naki, yanzu kenan ba ki yarda cewa ina tsananin sonki ba, haba Safna ka da kishi ya rufe miki ido mana, duk abubuwan da nake ce miki wallahi har cikin zuciyata nake fad'a".


Ita dai ba ta iya cewa komai ba, sai shash-shekar kuka da take yi rumgumeta Safwan yayi yana bubbuga mata bayanta yana cigaba da yi mata kalaman soyayya har ya samu tayi shiru "Safna d'in ruhina ce kuma sarauniyar zuciyata, wallahi da gaske nake babyna ki kalli cikin idona zaki tabbatar da abin da nake fad'a miki" Safna ta d'ago tana murmushi dan kuwa yanzu burinta ya cika ita ma dai sun zama dai-dai da Hafsa, "Da gaske ni ce sarauniyar zuciyarka kuma ruhinka", Kai ya d'aga mata alamar eh, dariya ta fara yi tare da rumgumeshi tana cewa "na ji dad'i sosai ruhina". Murmushi yayi kuma sai yanzu ya fahimci a kan abin da Safna yasa take kuka saboda ya ce Hafsa ita zuciyarsa ce kuma rayuwarsa ita kuma ya ce ruhinsa ce kad'ai amman yanzu da ya ce ita ce sarauniyar zuciyarsa har ta sake ta fara dariya "hmmm Safna kenan wato bakya k'aunar ace Hafsa ta fiki ko kad'an a gurina" Yayi maganara zuciyarsa haka dai yayi ta lallab'ata har tayi bacci a jikinsa ya gyara mata kwanciyarta sannan ya kunna t.v yana kallon labarai.


*'BANGAREN TEEMARH DA JABIR*


Teemarh kam tun da Jabir kwanta da ita bata sallah anan ta tabbatar shi d'in cikakken jahili ne ko ita da take ganin cewar bata da ilimin addini sosai amman tabbas ta san abubuwa sosai da ya danganci musulunci, kuma tana ji ana cewa babu kyau a kwanta da macen da take yin jinin haila, to kuma gashi shi ya aikata harumun, shi kuwa Jabir abin nasa sai gaba gaba yake yi sai ya shafe wata biyu baya gidan yana club yana shek'e ayarsa ita kuwa Teemarh ko a jikinta dan kuwa yanzu ta fara jin son Jabir yana fita daga cikin ranta.


Kwance take a kan kujera tana kallon episode d'in *Kwana casa'in a tashar arewa 24* gaba d'aya ta mai da hankalinta da tunaninta a kan t.v domin kuwa tana son Film d'in yana burgeta sosai, daga ita sai vest da wani dogon wando ya matseta sosai, tsaye yake ya k'ura mata ido rabonshi da ya ganta yau sati hud'u kenan, bai san meyasa ba yanzu wata iriyar Sha'awar Teemarh yake ji duk sanda ya dora idonsa a kan ta sai ya ji wata muguwar sha'awarta kamar zai mutu.


D'aukarta yayi cak kamar wata jaririya, a gigice Teemarh ta shiga dukanshi tana cewa "Sauke ni, ka sauke ni na ce", Sai da ya zauna sannan ya ajiyeta yana yi mata wani murmushi "ki kwantar da hankalinki, ba zan k'ara yi miki abin da bakya so ba kinji babyna" Wata iriyar muguwar harara ta yi masa domin kuwa ita bata ga dad'in bakin da Jabir zai yi mata ba da har zata fad'a tarkonshi domin kuwa ta san wannan abin da yake yi mata akwai wata a k'asa kallonta ta cigaba da yi ta ba wa banza ajiyarsa, shi kuwa Jabir bai damu ba domin kuwa yasan idan ya lallab'a Teemarh yasan dole zata fad'a tarkonshi sai ya dinga biyan buk'atarsa da ita hankalinsa kwance dole sai ya ribace ta ya nuna mata cewar yana sonta sosai amman a zuciyarsa sha'awarta kawai yake yi.


(to fa ko Teemarh zata amince ta fad'a tarkon nasa kuwa, ko kuma dai ba za ta amince ba, nima ban san amsar ba amman idan kun cigaba da biyoni zaku ji amsoshin tambayoyinku).


Hajiya Asiya kuwa tana zaune jigum sai ga k'awarta Hajiya Suhaima ta shigo gidan kyakkyawa ce ajin farko kallon d'aya zakai mata kasan kud'in sun zauna sark'arta abin hannunta duka na gwal ne zama tayi kusa da Hajiya Asiya sannan ta dafata tare da cewa "K'awata meyasa ne ki haka ne" Ajiyar zuciya tayi sannan ta ce "Abin duniya sun taru sun min yawa k'awata" Nan ta kwashe duk abin da ke faruwa ta fad'a mata, Hajiya Suhaima ta shek'e da wata iriyar mahaukaciyar dariya tare da cewa.
Hajiya Suhaima ta kalli Hajiya Asiya ta ce "Lallai k'awata kin yi babban sake da har ki ka bari aka auro miki wata a matsayin abokiyar zama,amman bakomai har yanzu lokaci bai k'ure mana ba, ki tashi ki je ki shirya zan kai ki wani guri in da za'a gama mana da ita ta bar duniyar ma baki d'aya kowa ma ya huta" Wani irin mugun Murmushi Hajiya Asiya tayi sannan ta ce "daman na san ke ce zaki fitar da ni daga cikin damuwar nan da nake cikinta a yanzu, dan haka na shirya yin komai dan na ga an kawar da wannan shegiyar 'yar matsiyata, kuma zance na je na shirya ai bai ta so ba,ni a shiryena na ke kawai tashi mu tafi" Wani mayafi ta d'auka ta yab'a a jikinta sannan suka fito zuwa farfagiyar gidan motar Hajiya Suhaima suka shiga tsadaddiyar mota ce mai numfashin gaske drivernta ya ja Hajiya Suhaima ta fad'a masa inda zai kai su daman ya san gurin dan kullum sai ya kai Hajiya Suhaima anan take kwana sai da safe yake zuwa ya d'auketa, sun yi tafiya mai nisa sannan suka isa wani babban daji ba gida gaba ba gida baya kofar wani gida suka tsaya sannan driver yayi parking d'in motar Hajiya Suhaima ta ce masa ya fita zasu yi magana,kafin ta rufe bakinta idris driver ya fita daga cikin motar ya tsaya nesa da motar.


Hajiya Suhaima ta kalli Hajiya Asiya ta ce "K'awata ina son ki yi mini alk'awarin ba za ki ba ni kunya ba idan mun shiga gidan nan, domin kuwa a gidan nan bayan kin cika burinki na gamawa da kishiyarki, to zaki samu dukiya mai tarin yawa, ni kai na ta dalilin gidan nan na samu kud'in da nake dashi a yanzu kuma ba na tunanin akwai ranar da zasu k'are, na sanki sosai k'awata kina da matuk'ar son ace gashi yau ke ma kina da tarin dukiya" Murmushi Hajiya Asiya tayi ba tare da tayi tunanin komai ba, domin kuwa tana tsananin son kud'i wannan dalilin ne ma yasa take son yaranta su auri masu kud'i kuma wannan dalilin ne yasa ta auri Alhaji Mansur.


''Ni wallahi kin ba ni mamaki, ke kan ki kin sani a kan kud'i zan iya yin komai kuma zan iya hallaka kowa, in dai burika na zasu cika na samun kud'i da kuma gamawa da waccen munafikar 'yar matsiyatan" Hajiya Suhaima ta ce "to shikenan na ji dad'i" Haka suka fita daga cikin motar suka nufi cikin gidan, daman Hajiya Suhaima ta fad'awa Hajiya Asiya cewar ba'a sallama a gidan daman ita ma ba yin sallamar take ba, dan kuwa rabon da tayi sallama har ta manta, Wani dogon bene suka hau wanda matattakalarsa zasu iya kai wa d'ari, Hajiya Asiya har ta fara gajiya da hawa benen amman haka ta d'aure har suka gama hawa benen, wani babbar kofa ta ga Hajiya Suhaima ta nufa ita ma ta bi ta a baya, suna shiga d'akin Hajiya Asiya ta ci karo da abin da ya gigizata ta kurma wata iriyar k'ara tare da rintse ido tana ja da baya wasu mutane ta gani sanye suke da jajayen kaya suna zazzaune hannayensu rik'e da k'atuwar k'warya ga wani jan abu a ciki da alama jini ne, ga wata jaririya nan an yanka mata wuya da alama dai ita suka yanka kuma suke shan jininta, ta juya domin ta fita daga d'akin amman ta nemi kofar da suka shigo ta rasa.


Gabanta ya shiga fad'uwa abin da take jin shi a radio yau ga shi ta ganshi da idanuwanta, kenan nan gidan 'yan mafiya ne masu shan jinin mutane, wannan yana nuna cewar Hajiya Suhaima ita ma tana cikin su kenan, ji tayi an dafata domin kuwa ta kasa juyowa ta kuma kallonsu, juyowa tayi da niyyar taa fusace domin a tunaninta Hajiya Suhaima ce amman sai ta ga akasin haka, wani kyakkyawan saurayi ne, son kowa k'in wanda ya rasa, kallonsa take cike da jin haushi shi kuma kallonta yake yana murmushi "Haba gimbiyar mata menene abin firgita anan dukanmu fa mutane ne, ko kin ga abin tsoro a jikinmu ne" Hajiya Asiya ta ce "Ku dawo da kofa ni zan fita domin kuwa duk rashin imani na ba zan iya abin da kuke aikatawa ba" Tayi maganar cikin wata iryar muryar tashin hankali.




Wani murmushin ya k'ara sakar mata sannan ya ce "me muka yi na rashin imani, dan mun nemi duniyarmu shine zai zama rashin imani, kuma zancen ki fita ai bai ta so ba, domin duk wanda ya shigo nan d'akin to sai na tabbatar ya zama d'aya daga cikin 'yan k'ungiyarmu sannan zan bar sa ya fita","to ni ba na buk'ata ana dole ne?" Tayi maganar cikin bala'i da masifa, murmushi yayi sannan ya ce "ba'a dole amman kuma zaki yi danasani mara adadi, domin kuwa zamu kashe 'ya'yanki ga baki d'ayansu, Jabir, Aliyu, Shahida da kuma 'yar autarsu wacce kika fi so Nihal, idan kina son ki tsetar da yaranki to idan kuma bakya buk'ata to ga hanya zaki iya tafiya"Ya k'arasa maganar tare da nuna mata kofar fita daga d'akin hankalin Hajiya Asiya ya tashi tabbas ba ta son wani abu ya faru da yaranta kuma tunda wad'annan mutane suka iya shafe kofar ta b'ace babu abin da ba zasu iya yi ba kallon saurayin tayi sannan ta ce "na yarda zanyi abin da kuke so, karku tab'a min yarana" Murmushi yayi sannan ya ce "shikenan ai kin tseratar da yaranki, tunda kin yarda" Anan dai wannan saurayin ya ba wa Hajiya Asiya wasu abubuwan na asiri wanda zasu kek'ashe mata zuciya ta ji ba ta tsoron duk abin da zata yi ko suka sakata tayi.


(tofa jama'a Hajiya Asiya ta shiga k'ungiyar masu asiri ya zata kaya kenan😎😳)


*'BANGAREN SALIS*


Jikin Salis ya dad'a rikicewa wanda a yanzu baya iya gane wanda ke kansa, babu abin da yake iya yi sai sunan Nihal da yake fad'a hankalin Mama yayi matuk'ar tashi ta rasa inda zata tsoma ranta, gashi doctor ya ce mata idan har ba'a ba sa abin da yake so ba to haka jikin nasa zai ta yi, ita kuma ta san Nihal yake son a dawo da masa da ita, dan haka babu shiri ta nufi gidan Hajiya Mama domin ta yi bikon Nihal.


Tana shiga gidan ta tarar da Hajiya Mama a tsakar gida tana shan iska su Nihal kuwa suna gidan Kawu Bala babu kowa a gidan ita kad'ai ce, Mama ta tsugunna har k'asa ta gaisar da Hajiya Mama bayan ta yi sallama ta k'araso gurin da Hajiya Mama take zaune,Hajiya Mama ta amsa mata cikin sakin fuska tare da yi mata izinin da ta zauna, ta zauna sannan suka d'an tab'a hirarsu ta duniya sannan Mama ta fara fad'ar abin da ya kawota "Hajiya Mama daman nazo ne a kan ina so Nihal ta koma d'akinta, saboda zamanta haka ba son shi muke ba gaba d'ayanmu" Murmushi Hajiya Mama tayi sannan ta ce "Ai wannan tsakaninku ne uwa da y'arta, yanzu dai suna gidan Kawunsu amman zuwa anjima zasu dawo zan turo miki ita" Mama tayi murmushi sannan ta ce ''to shikenan Hajiya Mama nagode sosai" Daga nan suka cigaba da yin hirarsu sannan Mama tayi wa Hajiya Mama sallama ta tafi, Mama tana fita Hajiya Mama ta ce "Ohh ni yau na ji ikon Allah, wato d'anki yana kok'arin mutuwa shine zaki rarrafo wani biko, to ko zata koma ma ba yanzu ba, sai nan da sati uku" Anan Hajiya Mama tai-tayin fad'a ta inda ta shiga ba tanan take shiga ba.


*'BANGAREN TEEMARH DA JABIR🤣*


Jabir babu yadda bai yi ba a kan ya shawo kan Teemarh ta fad'a tarkonsa amman Teemarh ta gama sanin wanene Jabir da kuma shaid'ancinsa, ya dena fita ko ina kullum yana gida dan ya samu ya yaudari Teemarh tayi tunanin kamar ya dena abin da yake yi, amman a banza domin kuwa Teemarh sam magana ma bata barin ya shiga tsakaninsu, fitowarsa kenan daga toilet yana d'aure da towel ya kalli Teemarh da take zaune a kan kujera tana kallon wani series a Arewa 24 na indian *'kaddarar rayuwa* "darling ki zo ki taimaka min in shirya kinji" Yayi maganar yana marairaice murya, Teemarh tayi kamar ba ta ji mai yace ba, dan ko kallo bai isheta ba, har sai da ya k'ara maimaita maganar da yayi sau biyu sannan ta ce "indai ni zan taimaka maka ka shirya ai kuwa zaka dad'e baka saka kaya ba" Tayi maganar ba tare da ta kallesa ba.


K'arasowa yayi har inda take sannan ya zauna kusa da ita suna fuskantar juna "darling" Ya fad'a tare da mayar da fuskarsa ta tausayi "menene?,wai Jabir me na tsare maka a duniya ka dameni?","babu komai kawai ina so na nuna miki irin yadda na ke sonki ne","hmmmm" Abin da Teemarh ta ce kenan, haka dai Jabir ya k'ara ci suturansa ya tashi ta je drower wasu kayan ball ya d'auko green colour a bayan rigar an rubuta Jabir d'in Teemarh, zama yayi kusa da ita suna yin kallon tare Teemarh dai kam ba ta da lokacin biye masa shiyasa tayi shuru ba ta ce masa komai ba.


*'BANGAREN KHADIJATULLAHI*


Zaune suke a falon Hajiya Mama dukansu sun sakata a gaba yau kwana uku kenan da Khadijatullahi ta haihu amman bata tab'a shayar da jaririn ba, da an zaunar mata da yaron ance ta shayar dashi sai ta saka kuka ta ce ita ba ta so, haka zasu yi su gama har su hak'ura Hajiya Mama ta kalli Khadijatullahi wacce sai kuka take yi sosai tare da cewa "Khadijatu yanzu haka ake rayuwa ace ba za ki shayar sa yaro ba, so kika ya mutu ne?" Ba ta ce komai ba sai ma k'ara sautin kukanta da tayi Aliyu wanda ya zuba mata ido yana kallonta ya ce.
"Dija me jaririn nan yayi miki, dan manzon Allah karki hukuntashi a kan laifin da ba na saba, ki sani fa shi yaro ne k'arami bai san meyafaru a tsakaninki da Yaya Jabir ba, ida da ace yaron nan zai girma a bashi labarin irin abin da Yayana yayi miki to wallahi sai ya fi ki shiga damuwa, tunda an wulak'anta masa mahaifiyarsa, dan Allah Dija ki karb'eshi ki shayar dashi kar ya mutu". Ya k'arasa maganar cikin yanayin tashin hankali zuciyarsa cike da bak'in cikin Halin da Khadijatullahi take cikin yanzu musamman da ya ga hawaye na zubowa daga idonta duk sai ya ji ya tsani duniyar da abin da ke cikinta, domin kuwa ya tsani ya ga tana kuka.


Karb'ar yaron yayi daga hannun Hajiya Mama ya mik'a mata, tare da cewa "Dan Allah ki tausaya masa ki bashi abinci kar ya mutu","ba na son shi" Amin da ace kenan tana kuka, "to na ji bakya sonshi, ina son ki shayar da yaron nan na wata bakwai ni kuma nayi miki alk'awarin ki fad'a min komai kike so zan yi miki shi" Kallonsa tayi tare da d'an tsagaitawa da kukan na ta "da gaske", kai ya gyad'a mata alamar "eh".


"Ina son Jabir ya wulak'anta, ina son yayi mutuwar da ko gawarsa ba za'a iya ganewa ba, sai ana tattaro naman jikinsa saboda irin yadda ya ragargaje kuma..............." Saukar marin da Aunty Murja tayi mata ne, yasa ta rik'e gurin kuma ta kasa k'arasa abin da take son ta fad'a kuka ta saka tare da yunk'urin tashi Aunty Murja ta hankad'ata

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login