Showing 54001 words to 57000 words out of 83141 words
Chapter 19 - Daren Aurena Part 1 Complete Hausa Novel By Nana M Sha'aban .txt
ta koma ta zauna ta karbi yaron daga hannun Aliyu ta dora mata a cinyarta "ga shi nan idan kin ga dama karki shayar dashi, tunda ke kwata-kwara baki da hankali ki je ki yi duk abin da zaki yi dan kin ga an zauna ana lallab'aki to dan manzon Allah karki shayar dashi ki barshi ya mutu shashasha kawai mara tunani" Tana gama fad'ar haka ta fita ta zauna a kan taburma a tsakar gida wani irin haushin Khadijatullahi take ji, saboda irin maganganun da tayi a gaban 'yan uwan Jabir d'in.
Amatullahi ta kalleta tare da cewa "Ai kin huta tunda har kin sa Aunty Murja fushi saboda wannan bak'ar zuciyar ta ki ai sai ki yi ta yi, dan Annabi tsabar tsanar da kike yi wa Jabir ki kashe jaririn idan kin kashe shi, shi ba asararsa ba ce, tun da bai san ma kina yi ba kuma ko yau jariri ya mutu ko a jikinsa, amman ki yi abin da kika ga dama tun da haka kika zab'arwa kanki".
Ita ma Amatullahi fita tayi kusa da Aunty Murja ta zauna tana raya abubuwa da yawa a ranta, tana son d'aukarwa bestyn ta ta fansar abin da Jabir yayi mata dan yanzu ma shirin da take yi kenan, amman yau bestyn ta ta taba ta haushi sosai, saboda Amatullahi ranta yana matuk'ar son jaririn dan har suna ta bashi Affan dan da haka take kiranshi.
Khadijatullahi kuwa kukanta ya k'ara sauti tana kallon Aliyu shi ma d'in ita yake kallo, yana durkushe a gabanta, "ka ce musu zan shayar dasu su yi hak'uri ba zan k'ara ba","to idan kina son na fad'a musu to ki shayar dashi yanzun nan dan na fad'a musu, kuma na basu hak'uri, kin ga sai kuka yake yi" Aliyu ya fad'a idanuwansa na cikin na ta.
Kallon jaririn take yi wanda sai tsala kuka yake yi ta saka shi a cikin hijabinta sannan ta shiga shayar dashi, shuru Affan yayi yana tsotsar abincinsa, Hajiya Mama,Nihal,Shahida da Aliyu ajiyar zuciya suka sauke tare da godewa Allah da Khadijatullahi yau ta shayar da Affan.
Tashi Aliyu yayi gurinsu Aunty Murja yake basu hak'uri kuma ya fad'a musu Khadijatullahi yanzu haka tana shayar da Affan ne, sun ji dad'i sosai suka tashi suka shiga d'akin Khadijatullahi tana ganinsu ta saka kuka tana cewa "dan Allah ku yi hak'uri ku yafe min na dena" Zama Amatullahi tayi kusa da ita tare da rumgumeta ta ce "Ai yanzu komai ya huce indai zaki dinga kular mana da Affan d'inmu babu wanda zai dinga jin kanmu","Hakane kam indai kina so mu shirya to ki kula da Affan amman wallahi na k'ara jin kina tsangwamar yaron ko kina cewa bakya sonshi to wallahi idan na tafi ba za ki sake ganina ba" Aunty Murja ta fad'a fuskarta babu alamun wasa.
"ba zan sake ba"Khadijatullahi ta fad'a muryarta na rawa dan tasan Aunty Murja tunda ta fad'i haka to zata aikata kuma ita bata son ace yau Aunty Murja tayi fushi da ita dan ita kad'ai ta rage mata a duniya, zama suka yi suna yin hira sama sama Khadijatullahi ta fito da Affan daga cikin hijabi baccinshi yake yi hankalinsa kwance, Nihal ce ta karb'eshi ta goyashi.
*Bayan Sati d'aya*
Inna Larai ce zaune ta zabga tagumi ta rasa abin da yake mata dad'i gashi ta je gurin Lantana mai adashi dan ta karb'i kud'in adashinta amman Lantana ta ce mata wai ta zo ta karb'a, ita maganar nan ta d'aure mata kai ta ya ya za'a ce ta karb'i kud'in adashinta bayan ita ta san bata karb'a ba, har police station sai da suka je a kan maganar amman Lantana ta kawo shaida har guda uku da ya suka tabbatarwa da 'yan sanda a gaban su Inna Larai ta shigo ta karb'i kud'in adashinta, wannan dalilin ne yasa 'yan sanda suka yiwa Inna Larai kaca-kaca, tare da yi mata jan kunne a kan idan ta k'ara kawo musu irin wannan maganar sai sun kamata tunda ita macuciya ce, Lado kuma gashi ya gama d'aga mata hankali dan kuwa har 'yan sanda ya kirawo mata bayan ta dawo daga police station ganin zasu tafi da ita ne, yasa ta ce musu su tsaya zata kira dillaliya ta zo ta siyi kayan d'akinta ta biya shi kud'insa.
Lado ne ya tafi ya kira dillaliya ta siyi kayan d'akin naira dubu goma sha biyar a gurin ta ba wa Lado kud'insa sannan ta ce masa ya tafi gidan ubansa ba ta buk'atarsa, Lado bai damu ba ya tattara kayansa ya koma gidan mahaifinsa duk da cewa ba ya jin dad'in zamansa a gurin mahaifin nasa saboda irin yadda Matar mahaifinsa take yi masa wulak'anci ga tsangwama.
Duk abin da yake faruwa tsakanin Lado da Inna Larai Amatullahi tana sani kuma kud'in adashin Inna Larai ranar da zata d'auki kud'in ita ce ta saka kayan Inna Larai ta je gidan Lantana mai adashi irin yadda tayi shigar kai zaka rantse Inna Larai ce, ta karb'i kud'in adashin, ta koma gidan Hajiya Mama.
*(wayyo ni Amatullahi fa kin iya tsula tsiya😂😂wato ki kayi shigar inna larai kaii Amatullahi duniya🚴🏽♀️🚴🏽♀️😂)*
*'BANGAREN TALATU😂*
Babu irin bokayen da 'yan tsibun da bata bi ba, a kan su taimaka mata takoma gidan Salis kuma su sakawa Salis tsanar Nihal ya ji ko me, irin sunanta ya ji an ambata ya ji ya tsaneta, amman sai dai suyi ta karb'e mata kud'i amman har yau shuru babu alamar burinta zai cika dan haka ta d'auki d'amarar kashe Nihal ko ta halin ya ya dan a cewarta idan ta kashe Nihal dole Salis ya dawo gareta, shiri sosai ta shiga yi na ganin bayan Nihal har gidan Hajiya Mama sai da ta saka aka binciko mata.
Ranta ya b'aci matuk'a da ta ji cewar Salis d'in jikinsa ya k'ara tsananta baya fad'ar sunan kowa sai na Nihal kuma labarin da ya k'ara girgizata shine da ta ji cewar Mama ta je bikon Nihal, a ranar sai da Talatu ta zama kamar mahaukaciya gaba d'aya ta gigita mutanan gidan sai kulleta aka yi a d'aki ta gama zage-zagenta da buge-buge dan Inna tayi tunanin ma haukacewa tayi dan har ta cewa 'yan uwan Talatun su kira motar asibiti dan su tafi da ita, Delu k'anwar Talatu ta ce mata "lafiyarta k'alau kawai zafin kishi ne Inna" Sai da tayi kusan kwana biyu a d'aki ba'a bud'eta ba, sai da Inna ta tabbatar da cewa Talatu ba ta haukace ba sannan ta yarda aka bud'eta.
*'BANGAREN HAJIYA ASIYA👹*
Hajiya Asiya ta zama cikakkiyar 'yar k'ungiyar Matsafa ko kad'an tsoron da take ji na shan jini da kuma yanka jarirai yanzu ya fita daga ranta ta zama cikakkiyar mara imani dan wataran ita take yanka musu jarirai su sha jininsu kud'i kam Hajiya Asiya yanzu ta samesu dan kullum cikin k'ara samun kud'ad'e take yi yau Hajiya Suhaima aka cewa ta kowa mahaifiyarta domin suna buk'atar su sha jininta babu musu Hajiya Suhaima ta amince a daren ranar ta kawo mahaifiyarta kuma ita da kanta ta yankata suka sha jininta, A ranar wannan saurayin da na lura cewa shine shugabansu ya nad'a Hajiya Suhaima a wakiliyarsa domin kuwa tayi abin da ya kamata a yaba mata, kwana sukai suna tsaface-tsafacensu sai da gari ya waye sannan kowa ya fito ya kama hanyar gidansa.
Hajiya Asiya tana shiga motarta ta js da gudu ta bar gurin abin Hajiya Suhaima tayi yayi matuk'ar bata mamaki dan kuwa ta san irin yadda Hajiya Suhaima da mahaifiyarta suke matuk'ar son junansu kuma mahaifiyarta tana yi mata duk abin da take so kwata-kwata bata son b'acin ranta, amman ace ta yankata da hannunta kuma ba tare da ta nuna damuwarta ba.
Da wannan tunanin ta k'arasa gida tana shiga ba ta tarar da kowa a falo ba dan haka ta huce d'akinta Alhaji Mansur ta gani zaune a bakin gadon d'akin ya k'urawa kofar shigowa ido, ko da suka had'a ido ta kawar da kanta gefe, Alhaji Mansur ya k'araso har inda take fuskarsa a murtuke kamar wanda bai tab'a yin murmushi ba "daga ina kike?" Kok'arin tureshi take ta huce amman ya rik'eta cikin tsawa yake cewa "ba tambayarki nake yi ba" Kuka ta fashe masa dashi tare da cewa "menene amfanin amsa maka tambayarka bayan baka damu da ni ba, kafi damuwa da wannan shegiyar matar ta ka, ka fifita ta fiye da ni, kullum kana ik'irarin kana sona to wannan shine soyayyar da ka ke yi min?","Asiya kome nake yi miki a yanzu ke kika jawowa kanki kin b'ata min tarbiyyar yara kin lalata musu rayuwarsu, kuma uwa uba baki d'auke ni a matsayin mijinki ba tunda har zaki iya saka k'afa ki fita har ki je wani gurin ki kwana baki fad'a min ba kai ni na fuskanci ma kwanannan bakya kwana a gida, ina kike zuwa?"
Kukanta ya tsananta domin kuwa tasan haka shi zai saka Alhaji Mansur ya rabu da ita da tambayoyin da yake mata da bata da amsar da zata bashi, dan tasan a duniya babu abin da ya tsana irin ya ga matarsa tana kuka, ganin irin kukan da take yi ne yasa Alhaji Mansur ya rabu da ita ya fita daga d'akin zuciyarsa cike da tambayoyi a kan Hajiya Asiya dan kuwa ya d'auki alk'awari sai ya binciko abin da Asiya take b'oyewa domin kuwa zuciyarsa ta fara zarginta.
*'BANGAREN SAFWAN,HAFSA DA SAFNA👨👩👦*
Zaune suke a farfagiyar gidan suna hirarsu ta masoya Hafsa ta kalli Safwan ta ce "Ruhina" Tayi maganar cike da tsokanarsa, zaro Ido yayi tare da cewa "Lallai na ga alamar so kike Ruhina ta Zane ki, kin satar Mata suna" Dariya tayi sosai sannan ta ce "A'a fa Allah ya huci zuciyar Ruhin Ruhi" Shima dariyar yayi sannan ya ce "Awww haka ne kam fad'i ki k'ara fad'a, ke Kuma zuciyata ba","A'a nima Ruhinka ce na barwa Aunty Safna nawa Nima nasan zata bar min na ta" Tayi maganar cike da Shagwab'a.
"Hakane kam" Safwan ya fad'a tare cigaba da kallonta, suka cigaba da yin hirarsu sai wajen k'arfe 4pm ya bar gidansu Hafsa ya nufi gidansa, da sallama ya shiga falon Amman abin da ya bashi mamaki bai ga Safna ba, domin ya Saba Yana shigowa da ita yake fara cin karo zata rumgumeshi tayi Masa sannu da zuwa.
D'akinta ya shiga ya tarar da ita ta kifa kanta a kan guiyoyinta sai shash-shekar kukanta ka ke ji yana tashi da sauri ya k'arasa kusa da ita Yana cewa "Subhanallahi Ruhina me ya faru Baki da lafiya ne?" Yayi maganar Yana d'ago Mata kanta kallonsa take shima ita yake kallo cikin muryar kuka ta ce "Lafiya k'alau nake","to meya sa ki kuka?","bakomai" Safna ta yi maganar tare da fashewa da sabon kuka.
Hankalin Safwan ya gama tashi ya jawo Safna gaba d'ayanta zuwa jikinsa Yana kissing d'inta har sai da ta yi shuru sannan ya cigaba da tambayarta "menene Ruhina?","bakomai Ruhina" Ta fad'a tana sauke ajiyar zuciya mai nauyi "ban kai matsayin da zan san damuwarki ba? Wato baki d'auke ni a matsayin Wanda zaki dinga fad'awa damuwarki ba ko?","A'a ba haka ba ne Ruhina kai d'in kana da matuk'ar muhimmanci a wajena"."To fad'a min me ya ke damunki?" D'agowa tayi tana kallonsa ta ce "Ruhina da gaske gobe za'a saka ranar aurenka?" Tayi maganar hawaye na kok'arin zubo Mata.
Shuru yayi Yana kallonta na tsawon mintina sannan ya ce "haka ne" Hawayen da suke kok'arin zubo tana mayar dasu suka samu damar silalowa zuwa kan kuncinta, hannunsa ya saka Yana goge Mata hawayen fuskarsa ta nuna tsantsar damuwa Amman haka ya shiga b'oye damuwarsa Yana murmushi ya ce "Ruhina saboda haka shine kike yi min asarar hawayenki, to ba na son na k'ara ganin wannan kyakkyawar fuskar tana kuka, saboda tana da matuk'ar tsada da muhimmanci gurina, kin san ko da na auri Hafsa ba zan tab'a wulak'anta ki ba, karki manta fa ke ce Ruhina" haka dai Safwan yayi ta tsara Mata kalamai har ya samu ta sauko ta dena kuka, hirar soyayya suka shiga yi da nunawa junansu irin yadda suka damu da juna.
*'BANGAREN TEEMARH DA JABIR😂*
"Darling! Darling!! Darling!!!" Jabir ya shigo d'akin yana zabgawa Teemarh Kira, Teemarh kuwa tana jinsa tayi banza dashi sai ma tsaki da ta ja ta koma kan gado tayi kamar wacce take yin bacci, Jabir kuwa ya ga sanda Teemarh ta kwanta dan haka ya nufi kan gadon gadan-gadan yana yin wani shu'umin murmushi.
Kwanta yayi kusa da ita tare da jan ta jikinsa da sauri ta tashi tana zabga Masa harara sauka tayi daga kan gado ta nufi kujerun d'akin ta zauna, biyota yayi ya zauna kusa da ita "darling wai me nayi miki ne, wallahi Ina sonki sosai sweetheart","to Jabir na ji Kuma nagode Amman Dan Allah ka kyaleni ba na sonka ni" duk da cewa ya ji haushin kalamanta, Amman Kuma ya zamar Masa dole ya kwantar da kansa ya samu abin da yake so gurin Teemarh.
"To na ji Darling bakya sona kuma na san duk abin da kika yi min zuciyata ce ta jawo min tunda ta kasa dai na sonki" Yana gama fad'ar haka ya tashi ya futa daga d'akin, Teemarh ta bi bayansa da kallo sai kuma ta ji ba ta ji dad'in abin da tayi masa ba, zuciyarta ta k'arye ji take kamar ta bi sa ta ce masa ta hak'ura kuma tana sonshi amman kuma ta san Jabir farin sa ni ta ya ya zata yarda cewa ba yaudararta zai yi ba, kuma da gaske yana sonta, dole sai ta tabbatar da cewa yana sonta ba yaudararta zai yi ba sannan zata yarda dashi.
Da wannan tunanin ta tattara ta koma kan gado ba'a fi minti d'aya da kwanciyarta ba wani irin bacci mai nauyi yayi awan gaba da ita.
*'BANGAREN ABBA DA AUNTY MURJA*
Tunda ya fito daga d'akin Hajiya Asiya ya shiga d'akin Aunty Murja kwance ya tarar da ita tana karatun littafi tana ganinsa ta ajiye littafin ta tashi ta zauna tana kallonsa fuskarsa ta nuna mata cewa yana cikin damuwa dan haka ita ma lokaci d'aya ta shiga tsananin damuwa, zama yayi kusa da ita tare da zabga tagumi, hannu ta saka ta cire masa tagumin tare da girgiza masa kai alamar "A'a" sannan ta ce "Yaya hankalina ya tashi zuciyata ta shiga tsananin damuwa saboda, sarkin da yake mulkarta yana cikin damuwa, shin ya zan yi da raina".
Murmushi yayi sannan ya ce "to matata ki kwantar da hankalinki ina cikin koshin lafiya kawai dai lamarin Asiya ne yake ba ni tsoro kullum abin ta cigaba yake yi, kwata-kwata bata ba ni matsayina na mijinta" Ajiyar zuciya Aunty Murja tayi sannan ta ce "Addu'a ya kamata mu dinga yi mata, insha Allahu wata rana zata fahimci cewa kuskure take aikatawa kuma ina mai tabbatar maka da cewa zata gyara duk kuskurenta ka ji dan Allah karka saka wannan a ranka".
Wani irin farin ciki ne ya kamasa tabbas yana matuk'ar alfahari da Murjanatu domin kuwa duk sanda ta ganshi cikin damuwa hankalinta ba ya kwanciya har sai ta ganshi yana cikin farin ciki, "Allah yayi miki albarka matata","Amin mijina" Ta fad'a tare da sakar mata murmushi, daga nan suka koma kan gado suka fad'a duniyar soyayya.
*'BANGAREN SALIS*
Mama hankalinta ya tashi matuk'ar tashi tun ranar da ta je gidan Hajiya Mama take ta faman jiran ganin Nihal amman gashi yau sati biyu babu Nihal babu alamarta, Salis kuwa jikin na shi kullum k'ara tsananta yake yayi bak'i ya rame sosai, Baffa mahaifin Salis ne ya shigo d'akin bakinsa d'auke da sallama da sauri Mama ta k'arasa gurinshi tare da fashewa da kuka tana cewa "Malam ka taimaka min ka je ka dawo masa da matarsa kar ya mutu dan Allah ba ni da wani d'a shi kad'ai ne gareni ina matuk'ar sonshi sosai dan Allah ka taimaka min Malam" Mama ta k'arasa maganar tare da had'e hannuwanta guri d'aya alamun rok'o.
Murmushi Baffa yayi sannan ya ce "Sai yanzu kenan kika sauko kin ga yaronki yana kok'arin mutuwa ko? To ba da ni ba wannan abin kunyar gwanda............'' ,"Dan Allah Malam karka min haka ka taimaka min wallahi sharrin shaid'an ne da kuma matarsa Talatu da tazo ta fad'a min k'arya da gaskiya a kan Nihal ni kuma na zauna a kai, amman yanzu na gane gaskiya wallahi ba zan sake ba" Mama ta k'atse Baffa da maganar da yake son yi, Baffa ya ji tausayinta matuk'a dan haka ya kalleta sosai sannan ya ce "Zan je na bada hak'uri kuma zan yi kok'ari na ga na dawo da Nihal k'afata k'afarta amman sai kin yi min alk'awarin duk wanda ya sake kawo miki wata magana a kan Nihal k'arki ji ta, kuma ki yi masa kaca-kaca","Wallahi nayi maka alk'awarin zan doshe kunnuwana daga jin maganganun Talatu a kan Nihal".
Jinjina kai yayi sannan ya ce "to shikenan zan je na dawo da ita zuwa gobe","Allah ya kaimu" Mama ta fad'a cike da farin ciki "Amin ya rabbil'almin"Baffa ya fad'a sannan ya mik'e saboda jin kiran sallar da yayi ya ce "bari na je nayi sallah","to a dawo Lafiya" Mama ta fad'a Baffa ya fita da sauri ya nufi masallaci.
*'BANGAREN ALIYU❤️*
Kwance yake a kan tafkeken gadon da ke d'akin nasa idanuwansa suna kallon saman d'akin gaba d'aya hankalinsa da tunaninsa suna kan Khadijatullahi wani irin abu yake ji duk sanda ya dora idanuwansa a kanta, ko da ace yana cikin bak'in ciki ne idan ya dora idonsa a kanta sai ya ji wani irin farin ciki yana ratsa zuciyarsa, idan kuwa ya wuni bai ganta ba baya tab'a samun nutsuwa har sai ya dawo yayi arba da kyakkyawar fuskarta, a hankali ya furta "Dija ta" tare da sakin wani irin murmushi wanda yake nuna tsantsar farin cikin da yake ciki "wai daman ashe haka so yake? ban tab'a tunanin haka so yake da dad'i ba sai da na fad'a sonki wanda ni kai na ban san lokacin da na fad'a cikin kogin soyayyarki ba sai ganina na yi a cikinsa Dija ta" Yayi maganar a fili tare da juyawa jikinsa "Dija ta na san cewa kin tsani maza sosai, amman insha Allahu ni zan cire miki wannan tsanar da ki kai wa maza, zan