Showing 21001 words to 24000 words out of 83141 words

Chapter 8 - Daren Aurena Part 1 Complete Hausa Novel By Nana M Sha'aban .txt

10 Jan 2025

3075

rigar abaya plum colour ta yafa mayafin abayar rik'e da jakarta ta zuwa makaranta tayi kyau sosai sai kamshi take yi murmushi tayi ta tsugunna har k'asa ta gaisar da Abbanta, abin da ya bawa su Innah Larai mamaki sai suka ga Malam Shu'aibu yayi murmushi ya amsa gaisuwar da tayi yayi mata umarni da ta tashi tsaye ta mik'e, anan ya shiga tambayarta "Mamana meyasa idan kin je makaranta bakya dawowa da wuri sai goma na dare kuma ajiye ki ake yi a mota, kuma kika watsa Larai mai a fuska ita da Lado" cikin mamaki ta ce "Abbana ni kuma wallahi Abba kullum da wuri nake dawowa kuma ni da Khadijatullahi muke dawowa a adaidaita, kasan dai ba na kula kowane saurayi kai ma shaidata ne bare har in shiga motarsa wallahi zan iya dafa al'kur'ani ban tab'a shiga motar kowa ba kuma ban tab'a kai wa goma na dare a waje ba kuma Innah Larai da Lado sune suka ja duk abin da nayi musu anan ta fad'a masa duk abin da ya faru" ta k'arasa maganar tana kuka, anan Malam Shu'aibu ya shiga rarrashin 'yar tasa har tayi shuru ya kama hannunta suka yi hanyar waje, Amatullahi idanuwanta a kan su Inna Larai da fuskokinsu suka chanza saboda basu yi nasarar had'a uba da 'yar ba tasan tabbas sune suka had'a mata mak'ircin nan kuma wallahi ba za ta kyalesu ba sai ta rama (ni kuwa 'yar mutanan zazzau na ce su inna larai an taro match🤣) haka suka fita daga gidan mahaifinta na rik'e da hannunta a kofar gida suka tsaya mahaifina ta ya kalleta cike da so da k'auna "Mamana kiyi hak'uri nasan kina hak'uri zama dasu Larai daman nasan ni ba halinki ba ne, amman nasan yadda zan shawo kan abin" hannu ya zura a aljihu ta d'auko 2k (dubu biyu) ya mik'a mata sannan ya cigaba da magana "gashi nan kiyi amfani dashi dan ba lallai ki dawo ki same ni ba, zan koma chan companyn namu yanzu ma jirana ake yi" Amatullahi ta karb'a tare da yi masa godiya, ta nufi gidansu Khadijatullahi zuciyarta fal farin ciki domin kuwa taji dad'i da Abbana ta ya ce zai koma wannan zai bata damar had'a musu nata mak'irci amman kuma ita ba k'arya zata musu ba, a kan abin da suke aikatawa a gidan zata yi musu basu san dawa suke zancen ba ne, da wannan tunanin ta k'arasa gidansu Khadijatullahi ta tarar ita ma har ta gama shiryawa doguwar rigar abayar tasa komai iri d'aya haka suka yi wa Aunty Murja sallama suka nufi hanyar fita daga gidan.


Suna fitowa suka yi sa'a ga wani mai adaidaita zai fita daga layin suka tsayar dashi suka shiga Amatullahi ta ce "Baba poly zaka kai mu ta gadon k'aya" kasancewar mai adaidaitar tsoho ne, shiyasa ta ce masa Baba, ya amsa mata da "to" suna isa Khadijatullahi ta bud'e jakarta ta d'auko naira d'ari biyar wacce ita kenan da ita zata mik'awa mai adaidatan Amatullahi ta dakatar da ita da cewa "to Hajiyata ai sai ki bari in biya ko?" ta fad'a tana mik'awa mai adaidatan naira d'ari biyar tunda daman a haka ake kawo su makarantar, suka shiga makarantar suna zuwa suka tarar da Hafsa har tazo abin da ya basu mamaki shine abayar da Hafsa ta saka komai iri d'aya da tasu babu abin da ya bambanta k'arasawa gurinta suka yi Amatullahi ta ce "Besty Hafseyy yau fa kinsa mun shiga mamaki sosai" murmushi tayi ta ce "Saboda kayan da nasa irin naku ko?" Khadijatullahi ta ce "Wallahi kuwa komai irin d'aya" Hafsa ta ce "ba abin mamaki ba ne ai, saboda tun jiya da muka je gidanku na ga abayar Khadijatullahi a kan gado kawai naji jikina ya bani ita zaku saka yau sai na k'are mata kallo Allah yasa naga kwalliyar jikin abayar duk da cewa ba duk na gani ba, shine muna tafiya na tsaya na saya a wani super market, murmushi suka yi gaba d'ayansu sannan suka nufi hanyar ajinsu domin an kusan fara lecture, basu dad'e da shiga ba Malam ya shigo suka fara lectures.


••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••


*'BANGAREN GIDANSU JABIR*


Jabir ne tsaye a gaban madubi yana kallon kansa ya gama shirinsa tsaf cikin wasu kaya gajeren wando ne wanda ko guiwarsa bai kai ba sai wata farar riga wanda a bayanta an rubuta *JABIR D'AN TUWA* da manyan harafai gashin kansa ya kwanta luf sai shek'i yake yi, haka ya fito babban falo, babu kowa a falon dan haka ya nufi kofar fita daga falon, Jabir yana bud'e kofar falon Aliyu na fitowa daga d'akinsa kallo d'aya yayi masa ya d'auke kansa domin kuwa wani irin haushin Jabir d'in yake ji, shi kuwa Jabir bai ga Aliyu ba saboda ya riga ya fita daga falon, motarsa ya nufa ya shiga ya jaa ta da gudu mai gadi yayi saurin bud'e masa gate ya fita daga gidan wak'ar babban mawak'in yahudawa ya saka Ojoro wanda Omale yayi ya k'ure kid'an yana bin wak'ar a hankali, Club ya nufa yana isa farfagiyar club d'in ya tarar da wasu 'yammata su biyu a tsaye, fita yayi daga cikin motar ya nufi inda wad'annan 'yanmatan suke kai masha Allahu kyawawa ne ajin farko, sanye suke da wasu d'ammun riga da wando sun yafa wani d'an k'aramin mayafi, k'are musu kallo yayi bai tab'a ganinsu a club d'in ba "Yau akwai chilling kenan, wad'annan daga ganinsu sababbin hannu ne" ya fad'a a zuciyarsa a fili kuma ya ce "Hi bebs" cikin wata iriyar muryarsa ta shu'uman 'yan bariki, murmushi suka sannan suka ce Jabir d'an tuwa, bai yi mamakin jin sun fad'i sunansa ba domin kuwa Jabir yayi k'aurin suna gurin iskanci da shaye-shaye, murmushi yayi sannan ya ce "Sannunku bebs ya kamata ku fad'a min sunayenku domin nima nasani" d'aya daga ciki ta ce "sunana zulaihat amman zaka iya kirana da Zuly baby, sai ta nuna d'ayar ta ce wannan kuma sunanta Ummita" Jabir yayi kayatatcen murmushi sannan ya kama hannayensu yayi cikin hotel d'akinsa ya nufa ya bud'e sannan suka shiga gaba d'ayansu suka bage hajarsu a kan gado Jabir yana kwance a kan gadon su kuma sun kwanta a jikinsa suna shafa shi tare da kissing d'in jikinsa (tofa jama'a Jabir bai saduda ba, Allah dai ya kyauta) haka sukai ta aikata bad'ala har sai wajen k'arfen biyar da rabi sannan Jabir ya tashi daga kan su Zuly yayi wanka ya dawo ya fara kok'arin shiryawa Zuly da Ummita suka matso kusa dashi suka shiga shiryashi Jabir kuwa wani irin farin ciki ne ya kamashi tabbas wad'annan 'yammatan sun iya soyayya sai da suka gama tsaf sannan ya tashi ya bashi rabar 'yan dubu dubu ya fita daga d'akin Zuly da Ummita murna fal ciki dan tunda suke harkar bariki babu wanda ya tab'a basu dubu ashirin ma barantana har a basu rabar 'yan dubu dubu, shi kuwa Jabir ko cikin club d'in bai shiga ba ya shiga mota ya nufi layinsu Khadijatullahi.


~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~

*Poly🔱🏨*


Wajen k'arfe shida dai-dai aka tashi daga makarantar, su Khadijatullahi suka fito daga aji Hafsa ta hango Yaya Safwan a jikin motarsa ya hard'e hannunsa a k'irjinsa yana ta baza idanuwana ya ga inda zai hango Hafsa gefensa wani kyakkyawan yaro ne wanda shekarunsa ba zai huce 6 ba,kamanninsa d'aya da yaron, Hafsa cike da mamaki had'i da bak'in ciki take nunawa su Amatullahi gurin da Yaya Safwan d'in yake ta ce "kun ga wanchan tsohon azzalumin yazo tare da d'ansa" Kallonsa suka yi sannan Amatullahi ta ce "gurinki ina ga ya zo" tsaki Hafsa ta ja sannan ta ce "wannan kuma shi ya sani" Yaya Safwan ya hango Hafsa tare da wasu yammata su biyu da sauri ya kamata hannun Khalid suka nufi gurin da suke, Hafsa ce a tsakiyarsu dan haka yana isa gurin yayi musu sallama "Assalamu alaikum" Khadijatullahi da Amatullahi ne suka amsa masa sallamar "Wa'alaikumussalam" suka yi gaba domin su basu damar yin magana, Hafsa ganin haka ita ma ta bi su da sauri Khalid ya kama hannun Hafsan yana cewa "Mommy ki tsaya Abbana zai yi magana dake dan Allah" kallon yaron tayi kamar ta ture yaron sai kuma ta tsaya Safwan ya k'araso inda suke ya dafa kan Khalid tare da cewa "Nagode yarona" Safwan ya bud'e baki zai yi mata magana ta dakatar dashi da cewa "yanzu ina tare da bestyna ka bari ka zo gida muyi magana" tayi maganar ba tare da ta kalleshi ba, tafiya ta fara yi Khalid yana biye da ita tsayawa tayi tana kallonsa ta bud'e baki zata yi masa magana Khalid ya rigata da cewa "Mommy zan biki dan Allah karki ce A'a" Hafsa ta ce "Ka tambayi Abbanka idan ya bar ka sai mu tafi" Safwan ya ce "Haba babyna ai kema Khalid kamar 'dan ki ne dan haka zaki iya tafiya dashi zan zo in d'aukeshi daga nan sai muyi maganar" kama hannu Khalid d'in tayi sannan ta nufi inda su Khadijatullahi suke d'an har sun fita daga cikin makarantar tana zuwa gurin da su Amatullahi suke ta watsa musu harara sannan ta ce "Shine zaku wani tafi ku bar ni" Murmushi Amatullahi tayi sannan ta ce "Ahh mun tsaya ai dole mu baku guri domin a ji dad'in bawa flower ruwa sosai".


Khadijatullahi tayi dariya ganin irin yadda Hafsan take hararar Amatullahi fuskarta a murtuke, drivern Hafsa ne ya zo suka nufi motar gaba d'aya, haka suka nufi layin gidansu Khadijatullahi suna isa, tun kafin su fito daga motar Khadijatullahi take bin wata mota mai numfashi da ta gani a kofar gidansu mamaki ya cika zuciyarta, haka suka fito daga motar bayan sunyi sallama da Hafsa, Amatullahi ta kalli Khadijatullahi ta ce "besty yau bazan shiga gida ba ki cewa Aunty Murja zuwa anjima zan dawo akwai abu mai muhimmancin da zan yi ne" Khadijatullahi ta ce "to shikenan besty" Amatullahi ta nufi hanyar gidansu domin kuwa yau su Inna Larai sai ta tabbatar ta koya musu hankali, Khadijatullahi haka ta nufi kofar gidansu zuciyarta na buguwa, Jabir kuwa yana ganin Khadijatullahi ya bud'e motar ya fito idanuwansu suka had'u Jabir yana mata wannan Shu'umin murmushin nasa, Khadijatullahi tayi baya zuciyarta na bugawa idanuwanta suka firfito jikinta ya maka rawa tana nuna sa da yatsa tana kok'arin kiran sunan "jaa.....ja....jabir".
Jabir ya nufi inda Khadijatullah take tsaye idanuwansa a kan cikinta "naji ance wai kina da ciki" sai Kuma yayi wani irin murmushin mugunta tare da ya mutse fuska sannan ya ce "Wayyo ni Jabir ina da k'arfin jini ace daga kwanci da mace sau d'aya har ta harbu ciki ya bayyana" cikin dakewa Khadijatullah ta fara magana "kaii tsinanne kayi gaggawar barin kofar gidan kafin na saka an jagaliya suyi min yaga-yaga da naman jikinka, shege d'an gidan shegiya" tayi maganar cikin zafin nama domin kuwa yau zata koyawa Jabir hankali zai san ita ma bawai k'anwar lasa ba ce Jabir ya kalleta sosai ya ga irin hucin da take kamar tsohuwar zakanya ya shek'e da wata iriyar dariya sannan ya ce "duk ki gama zagina karki ga nazo nan kofar wannan matsayacin gidan naku ki ce zaki yi min rashin mutunci ai kin san waye Jabir kuma kin san ba k'aramin aikina ba me wallahi yanzu a gaban kucakan 'yan layin naku nayi miki abin da ya faru ranar Asabar 26 ga wata march k'arfe 1 zuwa 2 na dare" wani irin a zababben mari ta wanke shi dashi hagu da dama sai da ta jera Masa sau biyar sannan fara magana "Eh tabbas nasan waye kai, Kai d'in ba kowa ba me in Banda dabba, Kuma ka sani idan a wanchan ranar kayi min ba yadda zan yi to yanzu baka Isa ba Jabir nima d'in nan da ka ke ganina ba k'aramar tantiriyar mara mutunci ba ce, wallahi Jabir na tsane ka na tsani duk wani Abu da ya dangance ka, Jabir idan baka bar nan kofar gidan ba zan iya kashe ka" magana take cikin wani irin yanayin bak'in ciki muryarta duk a shshshak'e, Jabir yaji matuk'ar jin zafin Marin da Khadijatullah tayi Masa domin kuwa tunda yake babu Wanda ya tab'a Marin shi, cikin zafin nama yake nuna Khadijatullah da yatsa Yana cewa "ba ni kika mara ba, wallahi ki jira zaki ga abin da zai biyo baya Kuma ki rubuta ki ajiye ni Jabir zan k'ara aurenki a Karo na biyu Kuma sai nayi miki abin da yafi Wanda nayi miki a baya" Yana fad'ar haka ya nufi motarsa ya bud'e zai shiga ya ji maganar Khadijatullah "Lallai Jabir sai yau na tabbatar Kai ka fi dabba ma, wa zaka aura?to Ina Mai tabbatar maka ni Khadijatullah na fi k'arfin ka, sai dai ka auri wannan shashashar uwar ta ka domin ita ce dai-dai kai, banza a jawo dak'ik'i Kuma insha Allahu sai kayi mutuwar da sai ana tattaro naman jikinka sai kayi mutuwar da ba za'a iya gane gawarka ba, na tsane ka na tsane shege Mai hali timakai" tana gama fad'ar haka ta shiga gida da gudu tana kuka, Jabir kuwa murmushi yayi domin kuwa yasan Yana zuwa gurin wad'annan kawun nata ya basu kud'i dole ko tana so ko Bata so a d'aura auren (ni kuwa 'yar mutanan zazzau nace Jabir ka makaro😂)


Ya shiga motarsa ya ja ya nufi gidansu kawun Khadijatullah, ko da ya je ya ga gidannasu gaba d'aya an ruguje shi, Nan ya tambayi wani saurayi a kan meya faru aka ruguje gidan Kuma Ina mutanan gidan, nan saurayin ya fad'a Masa duk abin da ya faru sannan ya d'ora da cewa "yaran gidan Kuma tun ranar da aka kawo gawarsu Kawu Sani suka tattara suka bar garin babu Wanda yasan inda suka je" Yana gama sanar dashi ya juya yayi gaba Jabir ya daki motarsa yanzu shikenan sai ya auri Teemarh damar abin da yaso shine ya samu a mayar da aurensa da Khadijatullah hakan ne zai saka ba zai auri Teemarh ba, gashi duk Shirin da yayi Yana nema ya ruguje, haka ya shiga motarsa ya nufi gida zuciyarsa cike da tashin hankali, Yana zuwa gidan ya tarar gaba d'ayansu suna falo Abba sai zagaye yake a falon kallo d'aya zaka yi masa ka tabbatar Yana cikin fushi ga Hajiya Asiya a gefe sai kuka take yi ita da Nihal saboda yau Alhaji Mansur tunda ya tashi ya tambaya Ina Jabir? Aliyu yace ya ganshi ya fita nan ya saka Hajiya Asiya a gaba yana Mata bala'i a kan ita ta saka shi a kan wannan tarbiyyar, Kuma yake shaida musu cewa Aure zai k'ara domin ya samarwa 'ya'yansa uwa ta gari shine fa suke ta kuka ita da Nihal, (ni kuwa nace wallahi Alhaji Mansur ka min dai-dai👏😂) Shahida da Aliyu basu ji haushi ko bakin ciki ba domin kuwa sun San tabbas Abbansu Yana buk'atar macen da zata kula dashi saboda Mami Sam Bata damu da ta kula dashi ba ita dai kawai tana zaune dashi ne saboda Yana da kud'i.


Jabir tunda yayi musu kallo d'aya ya watsar haka ya nufi d'akinsa yana cika yana batsewa kamar zai fashe, Abba ya k'are masa kallo daga sama har k'asa wai ace wannan d'ansa ne yake irin wannan shigar ya fita waje sai kace tsohon shaid'ani (ni kuwa nace Abba ai Jabir wallahi yafi shaid'an🤣) cikin zafin nama ya nufeshi gadan gadan ya jawoshi ya kifa masa mari wanda har sai da ya rasa ganinsa na tsawon dak'ik'a guda ya fad'a kan kujerar da take kusa da kujerar da Aliyu yake zaune, Abba ya ce "dan ubanka ina ka je tun safe sai yanzu ka dawo" Jabir ya d'ago ya kalli mahaifinnasa da rinannun idanuwansa ya ce "Club naje kuma......" Ai jin wani sabon marin da ya ji a fuskarsa yasa yayi shuru da maganar da zai k'arasa, haka Alhaji Mansur ya rufeshi, Aliyu ya tashi ya rik'e Abban yana bashi hak'uri shi kuwa Jabir tashi yayi sai da ya kusan shiga d'akinsa ya juyo ya kalli mahaifinnasa ya ja tsaki tare da tofar da yahu, nan fa Alhaji Mansur ya fusata yana kok'arin fusge rikon da Aliyu yayi masa, amman Aliyu ya riga ya rik'eshi sosai Jabir ya shiga d'akinsa ya saka mukulli, Abbah ya ce "to wallahi ka shirya goben nan za'a d'aura maka aure da wannan k'aruwar yarinyar shege gantalallan banza d'an iska mara kunya mara tarbiyya" Jabir duk yaji abin da mahaifinnasa ya ce dan da k'arfi yake magana, kwanciya yayi a kan gado yana tuna maganganun da Khadijatullahi ta fad'a masa "na tsaneka insha Allah sai kayi mutuwar sai ana tattaro naman jikinka sai kayi mutuwar da ba za'a iya gane gawarka ba" bai san meyasa ba wannan maganar ta tsaye masa a rai kuma ya ji son cikin da Khadijatullahi take dashi a zuciyarsa, tsaki ya ja tare da cewa "aikin banza" haka ya cigaba da sake-sake a cikin zuciyarsa.


Abbah kuwa dakyar Aliyu da Shahida suka lallab'ashi ya shiga d'akinsa su ma suka shiga nasu d'akin, Mami da Nihal kuma abin duniya duk ya ishe su, haka dai suma suka nufi nash d'akin kowannan su zuciyarsa cike da bakin ciki da tashin hankali.




••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••


*'BANGAREN KHADIJATULLAHI*


Tana shiga gidan da gudu tayi gurin da Aunty Murja take zaune tana tankad'an garin tuwo ta fad'a jikinta tana kuka cikin jijicewa Aunty Murja ta ce "Khadijatullahi meyafaru? Wani abun aka yi miki?" cikin kuka mai tsima zuciyar me sauraro ta fara magana "Aunty Jabir Jabir ne" zaro ido Aunty Murja tayi tare da cewa "A'uzubillahi minashshed'anir rajim Allah kayi mana tsari dashi, a ina kika ganshi" anan ta kwashe labarin duk yadda suka yi dashi ta fad'a mata, Aunty Murja ta ce "to aniyyarsa ta bi sa wallahi mun fi k'arfinsa, ki daina damuwa kin ji k'anwata

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login