Showing 39001 words to 42000 words out of 83141 words

Chapter 14 - Daren Aurena Part 1 Complete Hausa Novel By Nana M Sha'aban .txt

10 Jan 2025

3094

d'akinta domin shiryawa zuwa walimar bikin Abba.


Jabir ya ji haushin maganganun da Teemarh ta fad'awa Maminshi amman yanzu ba ta ita yake ba, domin kuwa suna cikin tashin hankali shi da mahaifiyarsa, haka dai suka zauna kowan ne daga cikinsu zuciyarsa kamar zata fashe saboda bak'in ciki musamman Hajiya Asiya.




(ni kuwa nace Alhaji Mansur ka yi min dai-dai😂😂Hajiya Asiya Allah ya k'ara😹💃🏽💃🏽yau akwai shagali a gidan Hajiya Mama💃🏽💃🏽ina kuke Ummu juwairiyya djamila da dai sauransu ana gayyatar ku fa💃🏽💃🏽)


*'BANGAREN LADO DA INNA LARAI😹*


Lado ya tadawa Inna Larai hankali a kan sai ta biya shi kud'insa gaba d'aya ya chanza mata, kullum cikin bala'i yake mata ita kuma Inna Larai ba ta san inda zata samu kud'i ta biya shi ba domin kuwa akalla kud'in zai kai naira dubu goma sha biyu, Lado kuwa ko bacci ba ya iyawa dan har zazzab'i yayi saboda kud'insa dakyar Inna Larai ta lallab'ashi a kan zata ce Malam Shu'aibu ya turo mata da kud'i idan ya turo mata sai ta biya shi, Lado bai yarda ba har sai da Inna Larai ta je wajen masu kira, ta basu number Malam Shu'aibu suka kira shi ta fad'a masa cewa tana buk'atar kud'i naira dubu sha biyar domin katangar d'akinta ta fad'i ta kira masu gyara sun gyara amman kuma ba ta da kud'in da za ta biya su, Malam Shu'aibu ya ce zai turo mata da kud'in a cikin satin nan sai ta biya masu gyaran, sannan Lado ya hak'ura zuwa lokacin da Malam Shu'aibu zai turo kud'in.


*'BANGAREN NIHAL🥳*


Tun da suka koma gidan Nihal ta shiga nunawa Mijinta Salis soyayya a waje d'aya suke samun matsala idan zai kwanta da ita dan kullum sai sun yi fad'a da ita duk da cewa Salis d'in shima yana kok'arin ganin ya nunawa Nihal d'in soyayya amman shi yana da k'arfin sha'awa ba zai iya jurewa ba, yau ma kamar kullum tana kwance a kan gado tana bacci sai jin mutum ta yi a jikinta yana ta tsotsarta kuka ta saka ta fara rok'onsa "Dan Allah Yaya Salis kabarni haka na d'azu ma bai warke ba, wallahi zan iya mutuwa" Yau kam Salis ya zo da mutunci rarrashinta ya shiga yii cikin wata iriyar murya mai narkar da zuciya "Haba babyna ki yi hak'uri kinji ba zan miki da zafi ba, zan miki a hankali ba za ki ji zafi ba, kin san dai ina sonki ba na son abin da zai dinga saka ki kuka kema kuma na san kina sona ba za ki so ace na shiga wahala ba, ki taimaka min kinji babyna" ya k'arasa maganar cikin muryar tausayi.




Nihal ta kalleshi sosai cikin sanyi murya ta ce "da gaske ba za ka min da zafi ba?" kai ya gyad'a mata alamar "eh" Nihal tayi murmushi sannan ta ce "Ok babyn baby go ahead" Murmushi yayi sosai tare da cewa "to babyn baby na gode da aka bani izini". Haka Salis yayi ta bin ta a hankali har sai da ya gama shan zumarta sannan ya sauka daga kanta tare suka yi wanka sun d'auki kusan awa guda suna wankan kamar ba zasu fito ba, bayan sun fito suka shirya cikin wasu riga da wando pink colour komai iri d'aya ne, sun yi kyau sosai zama suka yi a falo suna kallo, nan Salis yake shaida mata Abba yau ya k'ara aure abin ya girgizata sosai, amman kuma a wani b'angaren ta ta ya Abban farin ciki sabida ta san zaman hak'uri yake da ita.


Talatu kuwa tunda ta koma gidansu ita da yaronta take ta kulla makirci iri-iri tana zuwa tana kai wa mahaifiyar Salis d'in labarai a kan Nihal d'in karuwa ce saboda an rasa waye zai aureta shiyasa a ka mak'alawa Salis aurenta tun Mama bata yarda har ta saka akai mata binkice a kan Nihal d'in aka tabbatar mata da cewa Nihal ta tab'a karuwanci dan saboda haka ne ma a ka yi mata aure, ran Mama ya b'aci sosai nan ta shirya ta nufi gidan Salis tana zuwa gidan ta shiga falon babu ko sallama a zaune ta tarar dasu suna kallo tashi suka yi suna mata sannu da zuwa.


Wata uwar harara ta shiga hurgawa Nihal d'in cikin masifa ta shiga cewa "To munafuka tsohuwar kilaki asirinki ya tonu wato kin je kin gama yawon iskancinki shine zaki zo ki mak'alewa yarona to wallahi ba'a nan gidan ba dan yanzun nan ba sai anjima ba Salis zai sake ki ki je ki cigaba da yawon barikin na ki" tana gama fad'ar haka ta juyo kan Salis tana cewa "ka saketa ko kuma na tsine maka",Salis ya shiga tashin hankali ya shiga kok'arin rarrashin Mama amman sam ta tubure a kan ko ya saketa ko ta tsine masa.


Nihal tana kuka ta kalli Salis tana cewa "Yaya Salis ka bi umarnin da Mama ta ba ka, ba na so na zama silar rabuwarka da mahaifiyarka ka sake ni kawai na sani kana sona sosai nima ina sonka amman ya zama dole mu rabu da juna" Salis ya rintse ido zuciyarsa nayi masa zafi cikin rawar murya ya ce "Nihal ki je gida" Luuuuuu ya fad'i k'asa sumamme Nihal ta saka kuka ta nufeshi amman Mama ta daka mata tsawa tare da cewa "ki tafi gidan ubanki, ba ya buk'atarki" Haka Nihal ta shiga d'aki ta had'a kayanta a akwati ta fito tana jan akwatin gidan Hajiya Mama ta nufa tana kuka, a zaune ta tarar da ita tare da Abbansu da wasu 'yanmata guda biyu a jikin Hajiya Mamar ta fad'a tare da fashewa da kuka tana fad'in.
"Hajiya Mama na shiga uku dan Allah ki taimaka min" Tayi maganar tana k'ara sautin kukanta, Hajiya Mama ta ce "meya faru takwarata","Hajiya ta raba ni da Yaya Salis, Hajiya ta ce sai ya sake ni ba za ta yarda ya kuma zama da ni a matsayin matarsa ba" Kuka take yi sosai har sai da kan ta ya fara sara Mata, Hajiya Mama cike da tashin hankali ta ce "wacece wannan da d'anyen hukunci","Maminsa ce"Nihal ta bata amsa tana cigaba da kuka.


Shuru Hajiya Mama tayi "tabbas abin da ka yi sai anyi wa naka, Jabir ya wulak'anta marainiya gashi ita ma k'anwarsa anyi mata" Tayi maganar cikin zuciyarta, Shi ma Alhaji Mansur Abin da yake fad'a a tasa zuciyar kenan, Hajiya Mama ta d'ago ta dai-dai lokacin Amatullahi ta kai fuskarta kan Nihal d'in a firgice take nuna Nihal tana cewa "ke ce daman" Da sauri Nihal ta juya tana kallon Amatullahi tabbas duk da tana cikin matsanancin tashin hankali Amman ba za ta, tab'a mantawa da wannan fuskar ba ita ma cike da mamaki ta ce "ke ce anan?".


Sai kuma ta tashi ta nufi gurin da su Amatullah da Khadijatullah suke zaune ita ma ta zauna tana fuskantarsu hawaye na zuba daga cikin idanuwanta "ke ce Amaryar Abbanmu ko Kuma ke ce Khadijatullah" Khadijatullah ta kalli Nihal gabanta na fad'uwa "Wacece wannan? A Ina ta san sunana" Tambayar da take yi a zuciyarta kenan ba ta san ta fito fili ba, sai jin Nihal tai tana nuna ta tana cewa "ke ce Khadijatullah?"Kai ta gyad'a Mata alamar "Eh".


Hannunta ta kama sosai ta k'ara fashewa da kuka "Ki yi hak'uri duk da cewa ni ban da laifi, amman nasan alhakinki ne yake ta bibiyata, na san Yaya Jabir bai kyauta miki....................." A zaburai Khadijatullahi ta mik'e dai-dai lokacin Aunty Murja ta fito ta ji duk abin da Nihal ta ce wato hakan na nufin mahaifin Jabir shi ne mijinta, kanta ne yayi matuk'ar sarawa ta shiga maimaita innalillahi wa'inna ilaihi raju'un a fili.


Alhaji Mansur da Hajiya Maama sun yi matuk'ar jirjiga da jin wannan al'amarin "wato daman Khadija ita ce wacce wannan tsohon d'an iskan ya lalata rayuwarta" Hajiya Mama ta fad'a tana cigaba da jinjina lamarin, Khadijatullahi kuwa fita tayi da gudu Aunty Murja ta bi bayanta domin tsayar da ita, Nihal ma bin bayan su tayi ita kuma Amatullahi zama tayi tana cigaba da jin farin ciki domin kuma ta dad'e tana neman hanyar da zata addabawa Jabir sai gashi yau ta samu cikin sauk'i "ai kuwa sai na tabbatar na gasa maka aya a hannunka Jabir" Amatullahi ta fad'a a cikin zuciyarta.


A zaure Aunty Murja ta rik'e Khadijatullahi ta rungume nan suka shiga kuka, Nihal ma zuwa tayi ta rungume su tana ita ma kukan take tana jin sonsu yana ratsa dukkannin zuciyarta, Shahida da Yaya Aliyu ne suka shigo gidan suka tarar da su sun rungume juna suna kuka, da sauri Shahida ta k'arasa kusa da su tana tambayar "meya faru? Ko mutuwa aka yi?" Nihal ce ta fad'a musu duk abin da yake faruwa, nan fa ita ma Shahida ta fashe da kuka har da kururuwa ta rumgumesu suna kukan tare.


Aliyu ne ya shiga rarrashinsu da kalamai masu dad'i har ya samu kayi shuru haka suka koma cikin gidan Shahida da Nihal suna rik'e da hannun Khadijatullahi, zama suka yi jungum-jungum kamar gidan makoki, Amatullahi ce ta shiga jan su da hira domin kuwa ita kad'ai ta san abin da take shiryawa a kan Jabir domin kuwa sai ta tabbatar ta wulak'antasa sai ta saka shi a cikin bala'i da masifa sai ta hanashi kwanciyar hankali.


(ni kuwa na ce Jabir ka shiga uku gurin Amatullahi iyayen fitina, ba'a tab'a ma yi take barantana an tab'o bestynta😂😂🥳)


Haka kowa ya sake suka fara tab'a hira sama-sama, suka shiga gyara gidan da yin girke-girke duk da cewa Alhaji Mansur ya saka ayi musu order abincin bikin amman Hajiya Mama ta ce su ma ba za su zauna ba dole su k'ayin wasu abincin, shi kuwa Aliyu idanuwansa suna kan Khadijatullahi duk inda tayi sai ya bi ta da kallo tausayin yarinyar yake matuk'ar ji sosai sai kuma a yau ya k'ara tabbatarwa da cewa Jabir tabbas baya cikin jinsin mutane, sai dai aljanu domin kuwa ko wasu aljanun ma ba zasu iya aikata abin da yayi wa baiwar Allah salihar mace irin Khadijatullahi ba.


Daman duk abin da aka sakawa lokaci dole sai ya zo tun kafin k'arfe 2:00pm 'yan uwa da abokan nan arzik'i suka cika gidan damkam har wajen gidan Teemarh ma ta zo, walimar tayi matuk'ar k'awatarwa domin kaf mutanan da suka cika gidan har da wajen gidan sai da suka samu abin ci wadatatce, shi kuwa Alhaji Mansur gidan ya tafi domin shirya tarbar Amaryarsa bayan sun keb'e shi da mahaifinyarsa sun tattauna a kan yadda zasu shawo kan matsalar Khadijatullahi, haka aka shiga yin walima sai wajen k'arfe 7:00pm sannan kowa ya watse aka shiga kuma shirye-shiryen kai Amarya, Hajiya Mama ta ce ita da kan ta zata kai Aunty Murja gidanta bata buk'atar kowa.


Shahida ta ce "Wallahi daman Hajiya Mama ba na son komawa gidan nan, shiyasa na gudo nan, ba zan koma ba" Nihal ta ce "Hmm ai kuwa dai nima a nan zan zauna ba zan koma ba" Hajiya Mama ta ce "to su Khadija ma sai su zauna tare da ku nima ba zama zan yi ba ina kai ta zan dawo" suka amsa da "to a dawo lafiya" Haka suka fita daga gidan fuskar Aunty Murja a lillib'e take da mayafi, Aliyu yana biye da su domin shi ne zai kai su.


Bud'e musu murfin bayan motar yayi sannan suka shiga ya rufe ya shiga mazaunin driver ya ja motar sai gidansu yana zuwa mai gadi ya wangale masa tafkeken gate d'in gidan ya shiga yayi parking sannan ya fito ya bud'e musu motar suka fito, babban falon gidan suka nufa Teemarh wacce bata dad'e da dawowa daga walimar ba tana ganin shigowar Aunty Murja da Hajiya Mama ta fara yin gud'a wacce hakan ta jawo hankalin Hajiya Asiya da Jabir suka fito ganin Hajiya Mama da wata wacce suke da tabbacin ita ce Amaryar hankalinsu ya tashi zuciyarsu ta shiga harbawa da k'arfi ita kuwa Teemarh gud'ar ta cigaba da yi kamar zata fasa musu dodon kunne, a kan kujera Hajiya Mama ta zaunar da Aunty Murja sannan ita ma ta zauna Aliyu kuwa yana shigowa d'akinsa ya shige tun kafin su Jabir su fito.


Alhaji Mansur ne ya fito daga d'akinsa fuskarsa d'auke da murmushi yana yi musu sannu da zuwa, zama yayi Hajiya Asiya kuwa ta shiga zage-zage tana nuna Hajiya Mama da yatsa tana cewa "ke ce babbar munafukar da ki ka had'a auren nan ko to wallahi............" Ai bata k'arasa fad'ar abin da zata ce ba, sai jin saukar mari tayi a fuskarta Alhaji Mansur ne ya zabga mata mari yana cewa "tabbas yau kin k'ara nuna min cewa ke, babbar jahila ce, dak'ik'iya wacce kwata-kwata ba ta da tarbiyya dabba kawai" Jabir yayi matuk'ar fusata da jin abubuwan da mahaifinsu yayi wa Maminsa cikin hargagi ya fara cewa "Kai Abban nan wane irin mutum ne kwata-kwata zuciyarka kamar ta kare take ya kama......." Wani irin naushi Alhaji Mansur ya kai masa a biki domin cike yake da bakin cikinsa ai kuwa sai ga jini nan ya fara zuba kamar da bakin kwarya wani naushin ya k'ara kai masa a fuska, Hajiya Asiya ganin Alhaji Mansur yana ta yi musu rashin mutunci a gaban Amaryarsa da kuma sirikarta Teemarh Amman Hajiya Mama ba ta ce komai ba nan ta k'ara jin tsanar Hajiya Mama haka ta kama hannun Jabir suka shige d'akinta.


Teemarh kuwa ita ma d'akinta ta shiga tana jin dad'in hukuncin da Abba yayi wa mijinnata da uwarsa, Alhaji Mansur kuwa zama yayi a kan kujera yana huci haka Hajiya Mama tayi musu nasiha a kan zaman aure da kuma yin hak'uri da juna, ta tashi ta fita ado driver ya bud'e mata mota ya shiga mazaunin driver ya ja motar domin ya kai ta gida.


Aunty Murja ta tashi ta nufi gurin mijin nata ta zauna kusa dashi tare da cewa "Yaya ya kamata ka yi hak'uri ka tashi domin mu je mu kwanta nasan ka na jin bacci, b'acin rai bai chanchanta a wannan kyakkyawar fuskar ba" Duk da irin tsananin fushin da yake yi sai da yayi murmushi domin kuwa ko ba komai wannan daren bai kamata ace yana cikin bak'in ciki ba, ya kamata ace yana cikin farin ciki sosai, haka ya tashi suka shige cikin d'aki suka lula duniyar soyayya.


*'BANGAREN HAFSA💓*


Hafsa da Safwan kuwa wata iriyar tsatatatciyar soyayya suke yi wa junansu ji suke kamar zasu cinye junansu kullum a rana sai sunyi waya ta kai sau ashirin kuma kullum a gidan yake breakfast idan ya dawo daga office ma sai ya biyo Hafsa ta cika masa ciki da dad'ad'an abincinta sannan yake hucewa gida, Khalid kuwa yanzu sam har baya so ayi masa maganar komawa gurin Mommynsa saboda irin yadda Hafsa take kula dashi kullum suna manne da juna kamar cingum zaune take a kan kujerar d'akinta zuciyarta babu dad'i ganin hoton katin d'aurin auren Aunty Murja da tayi a t.v gashi har gidan su Khadijatullahi ta je amman a rufe yake "yanzu duk yadda muke dasu Khadijatullahi zasu iya ware ni, har ayi bikin Aunty Murja ba su fad'a min ba" Wani irin kuka ne ya zo mata, a haka Safwan ya shigo d'akin nata ya tarar da ita tana kuka da sauri ya zauna kusa da ita yana tambayarta "Amrish me ya faru?","Su Khadijatullahi ne" ta fad'a cikin kuka, a rud'e ya ce "meya samesu?","bakomai Yayana su Khadijatullahi ba su kyauta min ba, har ayi bikin Aunty Murja ba su fad'a min ba, me na yi musu ai ko menayi musu bai kamata ace sunyi min haka ba". Shuru Safwan yayi yana jin wani irin zafi ganin hawaye yana zuba daga fuskar Amrish d'insa nan ya shiga rarrashinta anan ne take fad'a masa sunan mijin Aunty Murjan da taje an fad'a a t.v "Laaa ai nasan gidan Hajiyarsa har gidansa ma na sani, saboda a ma'aikatarsa nake aiki".


"Haba Yayana da gaske ka ke" Ta fad'a tana share hawayen fuskarta, "wallahi da gaske ki bari gobe zan zo da sassafe na kai ki gidan Hajiyarsa ina tunanin suna chan yanzu kin ga dare yayi k'arfe goma na dare babu damar fita" Ba'a san ranta ta yarda ba haka suka yi sallama ya tashi ya fita domin tafiya gida, ita ma Hafsan ta koma kan gadon domin tayi bacci zuciyarta a cunkushe.


*'BANGAREN SALIS😣*


Kwanan Salis uku a asibiti bai san wanda yake kansa ba hankalin Mama yayi matuk'ar tashi, ganin tilon d'an nata cikin yanayin rayuwa ko mutuwa, kuka take yi sosai kamar ranta zai fita ta kama hannun Salis d'in tana cewa "dan Allah tashi duk abin da kake so zan yi maka, kasan kai ne kad'ai yarona kai nake kallo na ji dad'i "Ai baki fara kuka ba, domin kuwa duk halin da Salis yake ciki ke kika jawo masa, ki ka je kika rabasa da matarsa ai gashi nan yanzu sai ki dafasa ki cinyesa" Mahaifin Salis ya fad'a cikin fushi, Mama bata iya tankawa ba, sai kuka shi kuwa takaici ma ya hanasa zama ya fita daga d'akin zuciyarsa cike da bak'in ciki.


*'BANGAREN AMINAN JUNA AMKHAHAF😂💓*


Kamar yadda Safwan ya ce mata zai zo da sassafe ya kai ta gidan Hajiya Mama haka kuwa aka yi yana zuwa ko yarda ya shiga gidan ba ta yi ba, ta taresa a farfagiyar gidan bai musa mata ba ya juya ya nufi motarsa ya bud'e mata gurin mai zaman banza ta shiga ya rufe ya zagaya gurin driver ya shiga ya ja motar ya nufi gidan Hajiya Mama yana zuwa ya nunawa Hafsan gidan ta fita suka yi sallama ya nufi ma'aikatarsu kasancewar su Hafsa yau lahadi babu makaranta.


Ta shiga gidan da sallama a bakinta suna zazzaune a tsakar gida Amatullahi da Khadijatullahi suna ganinta suka tashi da sauri suka nufi gurinta suna murmushi rungumeta zasu yi tayi saurin dakatar da su cikin muryar fushi da cewa.


"Ba na buk'atar jin komai daga bakinku nagode sosai, kun ji nasan irin zaman da zan yi da ku" Tana gama fad'ar haka ta juya zata fita Amatullahi ta rik'eta sosai tana cewa "Wallahi ba inda zaki je, nasan a kan bikin Aunty Murja da ba'a fad'a miki ba shiyasa kike fushi, to ki tsaya ki saurareni dan Allah

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login