Showing 15001 words to 18000 words out of 83141 words
Chapter 6 - Daren Aurena Part 1 Complete Hausa Novel By Nana M Sha'aban .txt
yadda Malam Shu'aibu yake nuna damuwarsa a kan 'yar tasa kuma kullum cikin yi mata siyayyar tsire yake mata, shiyasa kullum ita ma take k'ara jin tsanar Amatullahi da kuma bakin cikin rashin samun cikin da bata yi ba.
*Wannan shine takaitatcen tarihin Amatullahi, yanzu zan dora labarinmu*
Yau ya kama su Amatullahi zasu fara zuwa makaranta, Amatullahi ta tattaro kayan da zata saka tazo gidan su Khadijatullahi domin ta shirya a gidan, kayan iri d'aya suka saka komai nasu iri d'aya sun yi kyau sosai, haka suka fita daga gidan zuciyoyinsu cike da farin ciki, Khadijatullahi ta tsinci kanta cikin wani irin farin ciki sosai mara misaltuwa, haka suka yiwa Aunty Murja sallama tayi musu addu'o'i ta samun nasara, suka kama hanyarsu ta zuwa poly, 'bangare d'aya suka cike gaba d'ayansu wato law, suna isa cikin makarantar suka tarar ana shirin shiga lecture bayan sun tambayi ina ne ajinsu aka nuna musu suka nufi ajin cikin farin ciki da annashuwa, suka shiga ajin bakinsu d'auke da sallama wasu daga cikin 'yan ajin suka amsa musu, suka nemi guri a gaba suka zauna suna yin hirarsu har Malami ya shigo kowa yayi shuru aka shiga lecture.
*'BANGAREN GIDANSU JABIR*
Jabir kuwa fitowa yayi daga d'akinsa a fusace ya nufi d'akin Aliyu ya shiga bugawa da k'arfinsa yana huci, Aliyu wanda yake kwance a kan d'aya daga cikin kujerun falon nasa yana ji yayi banza sai ma kunna t.v da yayi ya kai tashar Arewa 24 inda ya tarar suna film d'in *Rud'in zuciya* duk da kasancewar shi ba ma'abocin kallon indian film ba ne amman yau dan ya musgunawa Jabir ya k'unna, kiran layin Abba ya shiga yii ringing d'aya biyu Abba ya d'aga "Assalamu alaikum aminci Allah ya k'ara tabbata a gareka yarona" wani irin murmushi yayi wanda yake d'auke da tsantsar jin dadi "Wa'alakumussalam Abbana kai ma haka, ya dubai d'in Abba yaushe zaka dawo ina son yin magana da kai kuma gaskiya maganar ba zai yiyu muyi ta waya ba" ya k'arasa magana cikin wani irin yanayi na bakin ciki, Abba tunda ya ji Aliyu ya ce akwai maganar da zasu yi yasan maganar tana da matuk'ar muhimmanci dan haka bai yi niyyar dawowa kwanan nan ba amman ya cewa Aliyu "Insha Allahu zuwa jibi zan dawo, amman kowa lafiya dai ko" Aliyu ya kasa d'aurewa hawaye ne ya shiga zubo masa ya share da hannunsa cikin muryar kuka ya ce "Abba Jabir ne, Jabir yana zubar mana da mutunci Abba Jabir ya lalata rayuwar marainiyar Allah yarinyar da bata ji ba bata gani ba saboda son zuciyarsa shi da Mami, Abba labarin yana da tsayi Abba dan Allah ka dawo gobe gidan nan yana shirin tarwatsewa, Mami, Nihal da Jabir gaba d'aya sun had'u sun lalata rayuwar yarinya, Abba in takaice maka Nihal yanzu yau kwananta uku bata gidan nan wai saurayinta ne yazo ya d'auketa suka fita" ya k'arasa magana yana kuka mai tsima zuciyar mai sauraro, Abba kuwa sakin wayar yayi bayan ya gama jin duk bayanin Aliyu yanzu haka Asiya ta mayar masa da gida, ai kuwa babu shiri yasa aka yi masa visa zai biyo jirgin k'arfe biyar na yamma dan bazai ma bari ya kwana ba, Aliyu ya katse kiran sannan ya shiga kok'arin goge hawayensa.
Masu karatu na san zaku so kuji shin a ina Aliyu yaji ta'asar da Jabir ya yi wa Khadijatullahi, ba'a gurin kowa ya ji ba Shahida ce ta fad'a masa komai, domin lokacin da ya shigo gidan ya tarar da ita tana kuka da sauri ya k'arasa kusa da ita yana tambayarta menene, anan take ta zai yana masa komai da komai ta dora da cewa "Yaya Aliyu ina tsoron abin da Yaya Jabir ya yi wa Khadijatullahi ya faru a kai na ko Nihal saboda kasan ance duk abin da ka yi wa d'an wani to kai ma sai an yi wa naka, Yaya Aliyu kuma abin takaicin Mami da sanin ta Yaya Jabir yake yin komai amman bata tab'a hanashi duk abin da yake yi ganin dai-dai take yi masa" kuka yake yi sosai amman haka ya dake ya shiga rarrashin k'anwar tasa da kalamai masu dad'i sannan ya nufi d'akin Jabir d'in.
Jabir kuwa da ya ga Aliyu bashi da niyyar bud'e kofar ya koma nashi d'akin, ya zauna wayarsa ya zaro a aljihu ya kira number Teemarh kamar jiransa take ya kirawo ko ringing wayar bata yi ba Teemarh ta d'aga tare da cewa "Hello baby" Jabir cikin yanayin damuwa ya ce "Ina son kizo gida yanzun nan" ya fad'a tare da kashe wayar, murmushi Teemarh tayi sannan ta shiga wanka ta fito d'aure da d'an k'aramin towel ta shirya cikin wata 'yar yaloluwar rigar bacci wacce iya karta rabin cinyarta gaba d'aya rabin k'irjinta duk a bud'e yake shara-shara ce wacce ana iya ganin bra da pant d'in da ta saka wannan riga dai zan iya cewa da ita gwara babu, ko d'an kwali bata saka, ta baza gashin dokin da ta saka a kanta ya sauka har gadon bayanta, ta d'auki wata 'yar k'aramar jaka.
Haka ta fito tana taku d'ay-d'ay ta nufi baki titi ta tari mai adaidaita tayi masa kwatancen gidansu Jabir suka d'auki hanya, suna isa ta sauka ta biya mai adaidaita kud'insa ta nufi gate d'in gidan ta shiga kwan'kwasawa mai gadi ya bud'e mata kofar 'yar k'aramar gate d'in dan daman Jabir ya sanar dashi zai yi bak'uwa, haka ta shiga gidan tana wani rangaji daman gidan ba yau ta saba zuwansa ba dan haka ta san ko ina a gidan, Babban falo ta shiga ta tarar babu kowa kai tsaye d'akin Jabir ta nufa tana tura kofar ta ga a bud'e take dan haka ta shiga tana girgiza ko ina na jikinta, a kan gado ta tarar dashi a kwance, ta nufi gadon tana zuwa ta hau kanshi tana sumbatarsa, duk da irin yadda yake cikin bak'in ciki sai da yaji zuciyarsa tayi wasai sabida yasan Teemarh zata bashi jin dadi, haka ya murgina Teemarh ta koma k'asa shi kuma ya hau kanta ya shiga kissing d'inta tare da zame rigar jikinta, ya shiga tsotsar ko ina na jikinta (ni kuma 'yar mutanan zazzau nace Allah ya kyauta Jabir anji kunya anyi asarar rayuwa) haka dai sukai ta shek'e ayar su.
*****************************************************
*'BANGARENSU AMATULLAHI DA KHADIJATULLAHI*
Kasancewar yau suka fara lecture basu wani dad'e a makarantar ba aka tashi wajen k'arfe 11:00am Amatullahi da Khadijatullahi suka fito daga ajin suna tafiya, Hafsa ce 'yar ajinsu ta nufosu da gudu tana cewa "Sisters! Sisters!! Sisters!!!" kasancewar bata san sunansu ba shiyasa ta kirasu da haka, gaba d'ayansu suka juya tare da tsayawa Hafsa ta k'araso tana murmushi ta mik'awa Amatullahi glass d'inta tare da cewa "kin yi mantuwa" murmushi Amatullahj tayi tare da cewa "nagode sosai" Hafsa ta ce "bakomai wallahi, amman meye sunan 'yan uwan nawa" Amatullahi ta ce "Ni dai sunana Amatullahi Shu'aibu mudassir" ta nuna Khadijatullahi ta ce "wannan kuma sunanta Khadijatullahi Abbakar mai yak'i" Murmushi Hafsa tayi tare da cewa "Am glad to meet you sisters (nayi farin cikin had'uwata da ku 'yan uwana)" Khadijatullahi wacce tun da suka fara magana ba ta ce komai ba sai yanzu saboda ta fuskanci Hafsa babu ruwanta tana da faran-faran "Mu ma munyi farin cikin had'uwa da ke, amman ke baki fad'a mana sunanki ba" Hafsa ta ce "Sunana Hafsa Alk'asim mai fata, amman idan babu damuwa zan iya zama k'awarku wallahi kawai ina ganinku naga kun shiga raina sosai", "ba damuwa" Amatullahi ta fad'a a takaice, haka suka nufi bakin gate d'in su uku Hafsa suna fita sai ga drivernta yazo d'aukanta, kallonsu tayi tare da cewa "Sisters kuzo mu rage mu rage muku hanya" babu musu suka nufi motar tare,domin kuwa sun san ko sun k'i yadda suka ga babu masu adaidaita a ta wajen dole sai anyi tafiya sosai kuma ga Khadijatullahi ba wata isasshiyar lafiya ce da ita ba, ba za ta iya tafiyar ba, Amatullahi ta ce tayi musu kwatancen unguwarta su har kofar gida, aka kai su suka sauka tare da yiwa Hafsa godiya Hafsa ta ce "Haba sisters menene na godiya ai mun zama d'aya" Amatullahi ta ce "Haka ne kam, sai mun had'u gobe" Hafsa ta ce "to shikenan" daga nan driver yayi wa motar key suka nufi gida, Amatullahi ta k'arb'i jakar Khadijatullahi suka nufi cikin gida, kai tsaye d'aki suka shiga bakinsu d'auke da sallama, Aunty Murja wacce take kan gado a kwance tana karanta wani littafi na *Na Hafsa Zubairu Sambo* me suna *Ikhlas* tashi tayi tana yi mush sannu da zuwa "Barkanku da dawowa 'yan k'annena" murmushi suka yi gaba d'aya Amatullahi ta zauna tana bawa Aunty Murja labarin Hafsa da kuma irin k'irkinta Aunty Murja ta ce "Ahhh gaskiya tana da kirki sosai Allah ya saka mata da mafificin alkhairi" suka amsa da "Amin" Khadijatullahi ta samu guri ta zauna a kan yaloluwar taburmar da take bage a d'akin wacce duk ta gama jin jiki ta yayyage, Aunty Murja ta shiga basu labarin littafin da take karantawa irin yadda Hilal yake wulak'anta Ikhlas wacce ta kasance tana mutuwar son shi kamar ranta, Amatullahi cike da jin haushi ta ce "Ai ni wallahi Aunty Murja babu ni babu maza shiyasa ni babu ruwana da saurayi namiji hmmm namiji kenan" Amatullahi ta k'arasa maganar cikin wani irin yanayi
Khadijatullahi dai sun sosa mata inda yake mata ciwo hawaye suka shiga zubo mata shar-shar da sauri Amatullahi ta zo tana goge mata tana bata hak'uri "ki yi hak'uri besty kin ji komai zai wuce kuma insha Allahu Jabir sai yayi mummunar k'arshe" Khadijatullahi ta ce "Allah ya yarda ya ubangiji ka saka min" tayi maganar tare da k'ank'ame Amatullahi tana kuka ita ma Amatullahi kukan ta fashe dashi, Aunty Murja ce ta sauko daga kan gado tana rarrashinsu, har suka yi shuru abinci ta zubo musu suka d'an tab'ashi kad'an suka tureshi, rufe musu abincin tayi "gashi nan idan kun gama k'uncin tunda ku baku san k'addara ba sai ku ci" ta fad'a tare da juyawa ta koma kan gadon zuciyarta cike da tausayin k'anwar ta ta.
~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~
*'BANGAREN GIDANSU JABIR*
Karfe biyar dai-dai goma dai-dai na dare girjin su Abba ya sauka a kano, Aliyu ya kira ya sheda masa ya sauka yana Airport haka Aliyu ya d'auki mukullin motarsa ya nufi Airport d'in ya d'auko Abba, a motar Aliyu ya shiga bawa Abba labarin duk abin da Jabir da mahaifiyarsu tare da Nihal suke aikatawa, kuma ya kwashe duk abin da Shahida ta fad'a masa a kan irin yadda Jabir d'in ya lalata rayuwar Khadijatullahi ya sana'ar dashi babu abin da ya boye masa, hankalin Abba ya tashi ransa kuma ya b'aci wato a gidansa za'a dinga yin irin wannan lalatar lallai zai d'auki mummunar mataki a kan Jabir, Nihal da mahaifiyarta su.
A haka suka isa gidan kowan nan su zuciyarsa a jagule, Aliyu yayi parking a gurin da aka tanada dan ajiye motoci, Abbah ya fita daga motar ya nufi kofar da zata sadashi da babban falon gidan Aliyu na biye dashi, Abba yana tura kansa cikin falon ya hango wata yarinya daga ita sai wata arniyar riga wacce da ita da babu duk d'aya Jabir yana rumgume da ita yana shafa ko ina na jikinta ga Hajiya Asiya a zaune a falon tana kallonsu tana murmushi, gabansa yayi wani irin fad'uwa zuciyarsa ta fara kaiwa da komowa, cikin kakkausar murya Abba ya kira sunan Hajiya Asiya da k'arfi.
"Asiya"
Hajiya Asiya ta mik'e tsaye jikinta har rawa yake "shikenan yau ta faru ta k'are kashinta ya bushe" ta fad'a a zuciyarta Jabir kuwa da sauri ya ture Teemarh daga jikinshi jikinsa na b'ari, ita kuwa Teemarh ko a jikinta sai ma gyara jikinta da take yi, Abba kuwa yana zuwa ya d'auke Hajiya Asiya da wani wawan mari hagu da dama ji kake tas! tas!! tas!!! Sai da ya yi mata mari yafi goma sannan ya kama wuyanta ya shak'e shi sosai dan har ta fara kok'arin shid'ewa, Alhaji Mansur bashi da saurin fushi amman idan har ka sake yayi fushi to ka shiga uku domin bai iya fushi ba, Jabir cikin rawar murya ya ce "Abba karka kasheta Mami ce fa" ai bai san sanda yayi wurgi da Hajiya Asiya ba taje ta bugu da hannun kujera ta fad'i kasa sumammiya, Alhaji Mansur ya koma kan Jabir ya shiga dukanshi ta ko ina komai ya d'auka maka masa yake, Shahida ce ta fito daga d'akinta da gudu dan jin hayaniya a falon ganin Mami a k'asa Abba kuma yana d'aukar komai yazo masa a hannu yana makawa Jabir yasa ta kwalla wani irin ihu dai-dai lokacin Nihal ta shigo gidan cikin shigarta wacce sai ka rantse ba musulma ba ce, ai kuwa Aliyu yayi kanta da duka tana ihu ya gwara kanta a jikin bangon d'akin ta fad'i kasa kanta yana fitar da jini amman Aliyu bai kyaleta ba haka yayi ta dukanta kamar Allah ya aikoshi, Shahida ta rasa ya ya zata yi da ranta duk ta bi ta rud'e ruwa ta d'auko a fridge mai sanyi ta shek'awa Mami, ta farka a jijice tana kuka, Shahida ta koma gurin Abba tana rokonshi da ya dena dukan Jabir domin kuwa duk ya farfasa masa jiki ko ina na jikinsa jini yake fitarwa, da kyar ta samu Abba ya bar Jabir ta rik'eshi tana bashi hak'uri, Teemarh da taga gidan ya hargitse ta nufi hanyar fita da sauri domin kuwa tana tsoron kar kuma su juyo kanta, Abba cikin kakkausar murya ya tsayar da ita "Ke tsaya anan" tsayawa Teemarh tayi jikinta na rawa domin kuwa ta ji tsoron irin dukan da ya yiwa Jabir d'in, Shahida kuwa gurin Aliyu ta nufa "Yaya Aliyu dan Allah kayi hak'uri ka kyaleta please darling brother" tayi maganar cikin kuka, Aliyu ya je ya nufi kan kujera ya zauna zuciyarsa cike da bak'in ciki, da kyar Shahida ta iya d'aga Nihal dan kuwa Nihal ta gama galabaita bata iya tsotsi da jikinta numfashin ma dakyar take iya fitarwa, kusa da Mami ta zaunar da ita, ita ma ta zauna Abba kuwa yana tsaye cikin muryar da take nunawa yana tsantsar bakin cikin ya fara magana "nagode da irin yadda kuka mayar min da gida, gidan karuwai, amman ku sani daga yau ba zaku sake yin gangancin mayar min da gida na karuwai ba, ya nuna Jabir da yatsa sannan ya ce "nayi nadamar haihuwarka kuma nasan duk irin tarbiyyar da kake kai a yanzu uwarka ce ta dora ka a kai, dan haka nan da wata d'aya za'a d'aura aurenka da wannan yarinyar" ya nuna Teemarh da yatsa, wani irin farin ciki ne ya lillib'e Teemarh Jabir d'inta zai zama mallakinta, Jabir kuwa gabansa ne yayi mugun fad'uwar cikin muryar tashin hankali ya ce "Abbah dan Allah dan manzon Allah kayi hak'uri Teemarh ce fa, wallahi ba zan iya aurenta ba karuwa ce ta gama zubar da mutuncinta, duk wani d'an iska na garin nan babu wanda bai santa a mace ba, ni na yarda ka aura min duk wadda kaga dama amman dan Allah ban da Teemarh".
Teemarh ta kalli Jabir tana cike da mamakin kalamansa yau Jabir ne yake kiranta karuwa kuma yake cewa ba zai aureta ba, bayan shine mutum na farko da ya fara saninta a 'ya mace cikin muryar kuka ta fara magana "Lallai Jabir tabbas na yarda da cewa kai d'in macuci ne mayaudari ne kai har kana da bakin da zaka kirani da karuwa bayan kai ne ka fara lalata min rayuwa Jabir wallahi kai ba mutum bane kai shad'an ne, ko shad'an ba zai tab'a aika irin wannan abin ba" cikin tsawa Abba ya dakatar da ita "Ke ya isa haka, kai kuma d'an uwarka aure kamar anyi an gama". Fita Teemarh tayi daga gidan tana kuka mai ban tausayi, Jabir ya nufi d'akinsa zuciyarsa cike da tashin hankali tabbas zai bi ko wacce iriyar hanya domin ya ga bai auri Teemarh ba, Abba ya juyo kan Nihal yana nunata da yatsa "kema d'an uwarki ki shirya aure zan miki domin ba zaki jawo min magana ba shegiya 'yar gidan gantalalliya" yana gama fad'ar haka ya juya ya nufi d'akinsa Aliyu da Shahida ma kowannan su ya koma d'akinsa aka bar Mami da Nihal, Nihal ta rumgume Mami tana kuka tana son tayi magana amman ta kasa, haka dai suka zauna su kad'ai a falon kowannan su cike yake da tsantsar damuwa da tashin hankali a cikin zuciyar.
~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~
*'BANGAREN KHADIJATULLAHI DA AMATULLAHI*
Hankalin Khadijatullahi ya fara kwanciya kuma ta fara rage damuwa da tunanin da take yi, kullum a makaranta zaka gansu su uku ko a aji ma su uku suke zama a banci Hafsa tana matuk'ar jii dasu Khadijatullahi yau ma kamar kullum suna zaune a kujerun roba farfagiyar makarantar a k'asan wata bushiya, Hafsa ta kalli kayan jikinsu Khadijatullahi wanda ya kasance iri d'aya ta ce "Gaskiya fa bana jin dad'in abin da kuke min kuna ware ni a cikin ku" Amatullahi ta kalleta fuskarta d'auke da mamakin abin da Hafsa ta fad'a ta ce "Haba hafsiyy ya za'a yi mu ware ki a cikinmu bayan komai tare kuke yi da ke", Khadijatullahi ta ce "wai ma tsaya me muka yi miki da kika fad'i haka" Hafsa ta ce "gashi nan kuwa komai na ku tare kuke yi kama daga kaya, mayafi, hijabi, d'inki , takalmi, amman ni sai dai ku barni ni kad'ai kayana daban" murmushi suka yi gaba d'aya, Amatullahi ta bud'e baki zata yi magana wayar Hafsa ta hau ruri, Hafsa ta duba screen d'in wayar lokaci d'aya yanayin ta ya sauya hawaye suka fara ambaliya a fuskarta,l m hankalinsu Khadijatullahi yayi matuk'ar tashi cikin rawar murya Khadijatullahi ta ce "Hafsa me yafaru?" kallonsu tayi cikin tashin hankali ta fara magana "ina cikin tashin hankali sisters sabida irin muguwar yaudarar da namiji yayi min" Khadijatullahi da Amatullahi suka had'a ido gabansu yana fad'uwa, Amatullahi ta ce "Hafsa kenan kema kina nufin kin had'u da bakin cikin d'a namiji", Hafsa ta yi murmushi mai ciwo tare da cewa "Amatullahi kedai bari kawai", Khadijatullahi cikin sanyi murya