Showing 48001 words to 51000 words out of 83141 words
Chapter 17 - Daren Aurena Part 1 Complete Hausa Novel By Nana M Sha'aban .txt
dalilin yasa suka d'aga zuwa gurin Aunty Murja domin ba za su iya tafiya ba, ba tare da Hafsa ba zama suka yi jugum-jugum suna ta ya 'yar uwar ta su bak'in cikin rashin masoyin nata, ba'a fi awa biyu ba sai ga Hafsa ta sake kiran Shahida tana fad'a musu Yaya Safwan d'in bai mutu ba yanzu haka ma suna asibiti amman da dukkan alamu ya samu mummunar rauni, sun ji dad'in da Safwan d'in bai mutu ba, haka suka barshi a zuwan idan Safwan d'in sun koma gida sai su je su dubashi.
Nihal kuwa kwana yau da kewar mijinta ta tashi, dan haka da ta ji cewa Safwan bai mutu ba, haka ta faki idonsu Shahida ta shige bedroom d'in Hajiya Mama, ta kira number da Salis d'in ya kirawota jiya da ita ringing d'aya biyu doctor Maryam ta d'aga wayar tare da yin sallama, daman Salis ya fad'a mata cewa aran wayar doctor Sadiya yayi dan haka Nihal ta amsa mata sallamar tare da cewa "Ina wuni doctor","lafiya alhamdullahi da wa nake magana?" Murmushi Nihal tayi sannan ta ce "Nihal ce matar Salis, wanda ya ari wayarki jiya","Ohhhh nagane ya kike" Nihal cike da kosawa ta ce "Lafiya alhamdulillahi, dan Allah zaki iya had'a ni da babyn baby".
Murmushi doctor Sadiya tayi tare da cewa "me zai hana babyn baby" Wani irin kayatatcen murmushi Nihal tayi tare da cewa "To nagode Amman idan Mama tana nan kawai ki san dabarar da zaki Dan Allah ko muryarsa ne, naji dan nasan ba za ta bari munyi waya ba" Tayi maganar Cikin muryar kuka hawaye na zubo Mata, nan doctor Sadiya ta san da akwai matsala tsakanin wad'annan ma'auratan duk da ta ga irin yadda kowannan su ya damu da d'an uwansa.
"Meyasa bakya son Mama ta san kuna waya da mijinki","Saboda ta tsaneni, tana kok'arin rabani da babyna, Kuma saboda hakane Yaya Salis yake cikin wannan halin da yake a yanzu" Nan ta kwashe duk yadda suka yi ta fad'awa doctor Sadiya tana kuka tana ba ta labarin.
Doctor Sadiya tayi matuk'ar tausaya musu dan haka ta d'auki Alk'awarin taimaka musu a zuciyarta, Amman a fili rarrashin Nihal tayi tare da cewa "ki yi hak'uri kinji insha Allahu komai zai yi dai-dai Kuma Mama da kanta zata zo gurinki rok'on ki koma gidan Salis Allah yasa mudace","Amin" Nihal ta fad'a "Yanzu gaskiya Mama tana nan, Amman kamar yadda kike so zan shiga d'akin a zuwan duba yanayin jikinsa na zo yi na d'anyi Masa tambayoyi idan yayi magana hakan zai saka ki farin ciki ko?","Eh doctor nagode nagode sosai" Doctor Sadiya ta ce "karki damu".
Sannan ta nufi d'akin da aka kwantar da Salis d'in Bata kashe kiran ba, Amman ta cireta daga kunnanta,bata k'ara cewa komai ba ita ma Nihal d'in bata ce komai ba kawai dai ta rik'e wayar sosai a kunnanta.
Da sallama doctor Sadiya ta shiga d'akin, Mama da Salis Wanda yake kwance a kan gado Yana hutawa gaba d'aya kewar Nihal ta hana shi sukuni, suka amsa Mata sallamar "Mama barka da hutawa","yawwa doctor" Doctor Sadiya ta nufi gurin Salis tare da cewa "Sannu Salis ya jikin","doctor jiki alhamdulillah" Karaf idanuwansa suka sauka a kan screen d'in wayar number babynsa ya gani wani irin farin ciki ya kama shi.
Ya kalli Mama tare da cewa "Mama Ina son cin tuwo miyar busasshiyar kubewa","Wayyo yanzu Kuma Nafisa ta tafi gida, Amman Bari na je da kai na nayi na kawo maka" Murmushi Salis yayi tare da cewa "to Mama nagode" Fita Mama tayi daga Asibitin ta hau adaidaita ya suka nufi gidanta.
Salis kuwa Mama tana fita yayi saurin k'arb'ar wayar yana cewa "Nagode sosai Doctor","bakomai babyn baby sai a Sha soyayya lafiya" Ta fad'a tana dariya sannan ta fita daga d'akin.
"Babyna Ashe dai zai ji muryarka yau" Murmushi Salis yayi ya ce "Eh mana babyn baby, Ina cikin tsananin kewarki sai Kuma gashi nan zan samu kewarta ki ta d'an ragu dan kuwa waya ba zai saka ni na daina kewarki ba, babyna I really miss you badly, yaushe zaki zo ki duba babynki yau satina d'aya a asibiti Amman ace babyna ba ta zo ba","Ka yi hak'uri Ina tsoron Mama ne shiyasa Amman Ina son na zo gurinka, Kuma Nima nayi kewarka sosai" Salis ya ce "Ohh saboda Mama ne shine ba zaki zo ki duba babynki ba, ai shikenan" Yayi maganar tare da kashe wayar.
Nihal ta kira wayar kusan sau goma Amman Salis bai d'aga ba, hankalinta yayi matuk'ar tashi ta rasa inda zata tsoma ranta, kuka ta zauna tai-tayi "haba babyn baby meyasa zaka min haka, kai ma kasan ina tsananin son na zo na ganka" Ji tayi an dafata da sauri ta juya tana kallon wacce ta dafata Khadijatullahi tana bin ta da kallon tausayi, zama tayi kusa da ita tare da cewa "Sister na san dole ki ji ranki babu dad'i, amman duk da nasan Mama ba ta son ki tare Salis, ya kamata ki je ki duba yadda jikinsa ya ke hakan zai saka shi cikin farin ciki","to ya ya zan duba shi Sister ko so kike na je ta wulak'antani" Murmushi Khadijatullahi tayi sannan ta ce "menene amfanin nik'af" Wani irin farin ciki ne ya kama Nihal ta ce "kai Sister na ji matuk'ar farin ciki da wannan shawarar","Amman ya kamata ki bari sai gobe, sai ki saka hijabi har k'asa ki saka nik'af babu mai gane ki","to shikenan Allah ya kaimu goben Auntyna" Dariya Khadijatullahi tayi sannan ta ce "Amin amman dai ki ce min Sister zan fi son haka","to shikenan Sister".
Haka dai suka tashi suka fito zuwa falo inda su Amatullahi da Shahida suke zama suka yi suka shiga yin hirarsu ta duniya.
*'BANGAREN INNA LARAI DA LADO😂*
Lado ya gama d'agawa Inna Larai hankali gashi ko da ta je domin ta kirawo Malam Shu'aibu ta ji ya bai turo kud'in ba har yanzu, amman kiran duniya tayi masa ya k'i d'agawa, 'yar yaloluwar katifar d'akinta ta kira wata dillaliya ta shiyeta a dubu biyar, haka dai ta samu ta lallab'a Ladon ta bashi naira dubu biyar d'in bayan sun yi yarjejeniya a kan cewa idan ta d'auki adashinta wani satin zata cika masa kud'insa, ta ce masa ta yarda sannan ya karb'a, amman duk da haka kullum sai yayi mata masifa, haka dai take toshe kunnuwanta.
Inna Larai ta cigaba da kok'arin kulluwa Amatullahi makirci saboda tana zargin cewa da hannunta wajen k'in turo da kud'in da Malam Shu'aibu yayi, saboda mai kiran wayar ya fad'a mata cewa Amatullahi ta zo gurinsa ta kira waya ammam bata yi magana a gabansa ba, sai da ta matsa nesa dashi, ai kuwa Inna Larai ta k'ara jin tsanar Amatullahi ta ji zata iya yin komai dan ta ga ta wulak'anta, gashi abin takaicin Lado yanzu baya sauraronta ya ce idan ta ga ya fara sauraronta to ta biya shi ragowar kud'insa, sannan sai su koma kamar da.
(Lado uban son kud'i wayyo cikina🤣hawan ruwan Inna Larai zai tashi😂🚴🏽♀️)
*'BANGAREN GIDANSU JABIR🤏🏾😎*
Zaune take a cikin d'akinta wata doguwar riga ce a jikinta pink mai ratsin blue a jiki ta d'aura mayafin rigar a kanta hannunta rik'e da littafin hausa tana karantawa hankalinta kwance, fizge littafin da aka yi ne yasa ta juya bayanta da sauri Alhaji Mansur ne fuskarsa d'auke da murmushi "Wato mijinki ma ya dawo ba ki sani ba kina karatu ko?" Sunkuyar da kanta tayi tana wasa da 'yanyatsun hannunta tana cewa "ka yi hak'uri wallahi ban san ka shigo ba, kuma ban fara karatun ba har sai da na ga lokacin dawowarka yayi ba ka dawo ba".
Mik'a mata littafin yayi yana cewa "to na hak'ura, kuma yau aikine yayi min yawa shiyasa ban dawo da wuri ba, na gaji sosai", Sannu ta shiga jera masa, zama yayi a kujerar da ta tashi sannan ya kamo hannunta ya jawota jikinsa yana wasa da ita cikin wani irin salo.
Bugun kofar da ake yi ne kamar za'a k'aryata, yasa su dawowa daga duniyar soyayyar da suka lula, Aunty Murja ce ta tashi ta nufi kofar sannan ta bud'e Hajiya Asiya ce, tana ganin an bud'e kofar ta bangaje Aunty Murja sannan ta nufi gurin Alhaji Mansur gadan-gadan "Mansur" Ta kirawo sunansa da k'arfi kai ka ce uwarsa ce ita, wani irin mugun kallo ya watsa mata bai ce mata komai ba ya kawar da kansa gefe "ina fad'a maka da k'akkausar murya ka saki wannan karuwar yarinyar tun kafin nayi maka rashin mutuncin da ba za ka iya dashi ba","to sannu uwata Asiya ban tab'a tunanin ke dabba ba ce sai yau na k'ara tabbatarwa, ko ba rashin mutunci ba bismillah karki fasa yi min, kuma ina sake fad's miki idan kika sake ki a fusata ni to zaki koma inda kika fito shashasha mai shashashar zuciya jahilar banza jahilar wofi" Wasu irin hawaye ne suka zubo mata, lallai ma wato har Mansur ya isa ya gaya mata haka, ai kuwa sai ta tabbatar ya biya abin da yayi mata haka ta fita daga d'akin fuuuuuuuu kamar wata kububuwa, tashi yayi ya nufi kofar ya saka mata mukulli sannan ya kalli Aunty Murja wacce take tsaye kamar an dasata ta kasa ko da motsawa, hannunta ya kama suka nufi kan gadon domin kuwa yana buk'atar ya jita a jikinshi a halin yanzu.
Aunty Murja ta bashi had'in kai domin kuwa ba ta da wani buri irin ta ga ta faranta ran mijinta, haka suka tsunduma duniyar soyayya.
Hajiya Asiya kuwa tun da ta fita ta shiga d'akinta ta kasa tsaye ta kasa zaune, hankalinta duk a tashe gashi har 'yar wata rama tayi saboda halin da take ciki "ya zama dole na nemi mafita dan kuwa wannan gidan da kuma duk kadarorin Alhaji Mansur nawa ne ni da yarana" Wayarta ta d'auka ta shiga kiran number k'awarta Hajiya Suhaima amman a kashe take wani irin mugun tsaki ta ja sannan ta zauna ta tura mata text kamar haka _Shegiya sai ayi ta kiranki wayarki a kashe to idan kin kunna wayarki, ina son yin magana da ke domin akwai matsala, kuma wannan tsohon najadun ba zai bari in fito yanzu ba_ tana gama rubuta sakon ta tura mata tare da kishin gid'a zuciyarta nayi mata zafi, bacci b'arawo ne yayi awan gaba da ita.
*'BANGAREN TALATU😂*
Tun ranar da Talatu ta ji cewar Salis yana asibiti hankalinta a tashe yake amman tun da ta ji cewar wai saboda Mama ta je gidansu a kan ya saki Nihal shi ne ya fad'i aka kai shi asibiti ta ji wani irin kishi tare da jin haushin Salis d'in gaba d'aya tashin hankalin da take ciki gamai da rashin lafiyarsa ta nemeshi ta rasa, kuma ta shiga kulla sabon makirci domin kuwa ta rantse ba za ta barsu su k'ara kasancewa a matsayin ma'aurata ba kuma sai ta sakawa Salis d'in tsanar Nihal a cikin zuciyarsa, haka dai kullum cikin sak'a makirci take yi domin kuwa idanuwanta duk sun rufe hatta Salis ji take kamar ta kashe shi kowa ma ya huta.
*'BANGAREN NIHAL🥰*
Kamar yadda suka tsara ita da Khadijatullahi haka kuwa aka yi washe gari wajen k'arfe 4:00pm na yamma Nihal ta shirya cikin wata farar a atamfa da pupple sai shek'i take ta saka hijabinta har k'asa ta d'aura nik'af ta feshe jikinta da turarirrika kala kala masu kamshi sannan ta fito ta ce Hajiya Mama gida Mami zata je tunda ta dawo gida ba ta je ta ga Mamin ta ta ba, Hajiya Mama ta ce mata to sai ta dawo, saboda tasan idan ta fad'a mata gaskiyar in da zata je zata hanata zuwa, shiyasa ta ce mata hakan, ta fita kai tsaye asibitin da aka kwantar.
Doctor Sadiya ta kirawo a waya ta zo ta nuna mata d'akin da Salis d'in yake tayi mata godiya sannan ta shiga cikin d'akin da sallama a bakinta, da sauri Salis ya mik'e jin muryar babynsa domin kuwa ko da ace daga bacci ya tashi zai iya gane muryar Nihal, zama yayi yana sakin murmushi, tsugunwa tayi ta gaishe da Mama har k'asa, Mama ta amsa tana murmushi sannan Nihal ta ke tambayarta ya jikin Mama ta ce da sauk'i, "Allah ya k'ara sauk'i" Nihal ta fad'a tare da zama kusa da Mama wacce take zaune a kan k'atuwar taburma "Amin" Maganar Mama ta dawo da Nihal daga kallon Salis d'in da ta shagala tana yi.
Babu damar ta matsa kusa dashi, amman haka ma ta ji matuk'ar dad'i da ya kasance gata nan tana kallon babynta, mintuna ashirin Nihal tayi sannan ta tashi ta yi wa Mama sallama ta nufi gurin doctor Sadiya, Nihal tana fita Mama ta kalli Salis tana cewa "wannan yarinyar tana da hankali gashi ban san wacece ba","nima kam ban san ta ba Mama" Salis ya fad'a tare da komawa ya kwanta yana jin babu dad'i a zuciyarsa, saboda bai samu ya keb'e da babynsa ba.
Nihal kuwa tana zuwa gurin doctor Sadiya ta ba ta wata takarda ta ce ta ba wa Salis d'in sannan ta yi mata godiya ta nufi gida zuciyarta fal da farin ciki.
*Bayan wata d'aya*
Cikin Khadijatullahi ya kai lokacin haihuwa ko yau ko gobe Hajiya Mama ta dena barinta ta fita ko ina Allah ya taimaka lokacin an bada hutun makaranta na first semister wato hutun farkon zango, kullum tana jikin Hajiya Mama, Aliyu kuwa a b'angarensa kullum sai ya zo gidan Hajiya Mama yanzu kuwa da ya ga cikin Khadijatullahi ya kai lokacin haihuwarsa ya tattaro kayansa ya dawo gidan Hajiya Mama domin kuwa a cewarsa Khadijatullahi tana buk'atar kulawarsa shima ba iya kulawar da su Hajiya Mama suke ba ta ba, wani irin tausayinta yake ji kuma bai san meyasa ba duk sanda ya kalli Khadijatullahi sai ya ji wani abu a cikin zuciyarsa.
*BANGAREN GIDAN HAJIYA MAMA🌸*
A yau ranar talata tun da asuba Khadijatullah ta fara jin wani irin sauyi a tare da ita, Amman ta daure ba tare da ta fad'awa kowa ba, gashi Hajiya Mama ta su Nihal sun fita gidan Kawu Bala matarsa ta haihu kuma baya garin, gidan ya rage daga ita sai Amatullahi sai Kuma Aliyu dan shi kam k'in bin su yayi domin kuwa yana tsoron ya fita kuma Khadijatullah ta tashi nak'uda baya kusa da ita.
Wajen k'arfe 8:00am na safe Khadijatullah ta fito daga d'akin ta d'auki buta dan tana son ta kama ruwa, toilet ta nufa tana tafiya a hankali tana yi tana cije Baki a dai-dai kofar shiga toilet d'in ta saki buta tare da kwalla k'ara, a firgice Aliyu ya fito daga d'akinsa ya k'arasa kusa da ita tare da tambayarta "menene?","cikina ka taimaka min" Amatullahi ce ta fito daga d'aki da gudu har tana zabga tuntub'e kama Khadijatullah tayi tana cewa "besty haihuwar ce?" Aliyu ya ce "Amatullahi d'auko Mata hijabi ko mayafi mu tafi asibiti" Yana gama fad'ar haka ya shige d'akinsa ya d'auko mukullin mota Daman sanye yake da jallabiya fara ce sol kallo d'aya zakai mata kasan tsadaddiya ce sosai Yana fitowa ya tarar da Amatullahi har ta d'auko Mata mayafin, Amatullahi ba za ta iya kamata ba, dan haka Aliyu ya rumgumota suka fita har wajen da motarsa take, a bayan mota ya sakata sannan ya shiga mazaunin driver Amatullahi ta shiga bayan sannan ta rufe kofar motar Aliyu ya ja motar da k'arfi sai Asibitin Abbansu *MANSUR SPECIAL HOSPITAL*.
Amatullah ta dinga raya abubuwa da yawa a ranta tana ji dama ace Aliyu shine mijin bestynta domin kuwa ta Yaba da hankalinsa shi Sam bashi da hali irin na wannan shashashan d'an uwana sa Wanda bai San ciwon kansa ba.
Suna isa Asibitin sai ga wasu nurses da gadon d'aukar mara sa lafiya dan tun a hanya Aliyu ya kira waya a kan suna nan zuwa Asibitin, tare da nurses d'in aka fito da Khadijatullah wacce duk ta gama fita daga hayyacinta, haka aka dorata a kan gadon suka nufi Labour room da Khadijatullah, Aliyu ya so ya shiga Amman babu dama saboda shi ba likita ba ne, shi soja ne Jabir kuma engineer.
Haka sukai ta yawo a filin gurin Amatullahi kuka take tana fad'in "Dan Allah besty karki mutu Ina sonki sosai" Zama tayi a kan wata kujera tana cigaba da kukanta, Aliyu ma ji yake kamar yayi kukan Amman wannan lokacin ba lokacin kuka ba ne, dan haka ya shiga yi mata addu'ar Allah ya sauketa lafiya.
Sun d'auki kusan awa d'aya a haka Babu wani likita da ya fito, hankalinsu ya tashi, ji sukai tana kok'arin bud'e kofar labour room d'in da sauri suka nufi gurin kofar wata nurse ce ta fito rik'e da jariri a hannunta fuskarta d'auke da murmushi, "nurse ya jikin dija"Aliyu ya tambayeta a gaggauce "ta haihu lafiya an samu d'a namiji ga yaron ma" Ta yi maganar tare da mik'a Masa yaron k'arb'ar yaron yayi tare da k'ura Masa ido kamarsu d'aya sak da Jabir kamar an tsaga kara.
Amatullahi kuwa cikin farin ciki mara iyaka ta ce "Alhamdulillah, nurse yanzu zamu iya ganinta?","Eh zaku iya" Nurse d'in tayi maganar tana kok'arin barin gurin Aliyu ya kirata ta dawo aljihunsa ya saka hannu ya d'auko kud'i naira dubu hamsin ya Bata, tayi Masa godiya sannan ta koma gurin aikinta.
Shiga d'akin suka yi Khadijatullah suka tarar ita kad'ai tana kwance a kan gadon d'akin tana hawaye kwata-kwata bata k'aunar yaron, tun da ta samu ta haifeshi ta ji zuciyarta tayi mata haske domin kuwa ta rabu da k'aya.
Zama suka yi a kan kujerun dake d'akin na roba sai a lokacin Aliyu ya tuna su Hajiya Mama ba su san Khadijatullah ta haihu ba, wayarsa ya d'auko a aljihunsa sannan ya shiga kiran layin Nihal tana d'agawa yake fad'a mata Khadijatullah ta haihu, ihun murna tare da godewa Allah ta shiga yi sannan ta kashe wayar ta fad'awa su Hajiya Mama ai kuwa babu shiri suka fito daga gidan Kawu Bala suka nufi Asibitin a hanya Shahida ta kirawo Aunty Murja take fad'a Mata da yake Abba yana gida dan haka suka shirya suka nufi asibitin, a harabar Asibitin suka tarar da adaidatan da ya d'auko su Hajiya Mama suka k'arasa gurin da suke bayan sunyi parking d'in motarta su suka tsugunnawa har k'asa Abba da