Showing 57001 words to 60000 words out of 83141 words

Chapter 20 - Daren Aurena Part 1 Complete Hausa Novel By Nana M Sha'aban .txt

10 Jan 2025

3095

tabbatar nasa kin fahimci cewa ba duka maza ne suke da hali irin na Jabir ba ina sonki babyna".


Khadijatullahi ta sauko daga iriyar muguwar k'iyayyar da take yiwa Affan har tana jin son yaron a cikin zuciyarta, Amatullahi kullum Affan yana gurinta ba ta ba wa Khadijatullahi shi har sai idan yana kuka alamar yana jin yunwa tana gama shayar dashi za ta karb'eshi tayi ta lallab'a yaron kamar wani kwai, Affan yafi sabawa da Amatullahi a kan Khadijatullahi, Nihal da Shahida kuwa ba'a magana dan kuwa kullum tare suke kwana dashi suna jin d'uminsa, ko kuka suka ga yana yi hankalinsu ya tashi har sai sun ga ya daina.


Zaune suke a tsakar gida kamar yadda suka saba kullum da yamma zasu shimfid'a taburma su yi ta hirarsu ta duniya, Aliyu ne ya fito daga d'akinsa sanye yake cikin wani yadi tsadadde brown yayi kyau sosai tafiya yake a hankali kamar wani mai sand'a har ya k'araso inda suke ya tsugunna har k'asa yana gaisar da Hajiya Mama "Ina yini Hajiya","Lafiya alhamdulillahi" Hajiya Mama ta fad'a tana sakar masa murmushi, guri ya samu ya zauna yana satar kallon Khadijatullahi wacce tun zuwansa ta had'e fuska kamar wacce ba ta tab'a yin dariya ba, Nihal ta kalli Aliyu tana murmushi ta ce "Yaya Haidar wai kwana biyun nan na ga ka na d'aukar wanka da yamma, ko dai an samo mana Aunty ne" Harara ya wurga mata sannan cikin muryarsa mai jan hankali ya ce "To ke kuma uwar 'yan sa ido, meye ruwanki da ni ko kuma so kike ki ganni kace-kace kamar wata ke" Zaro ido Nihal tayi tare da dafe k'irji kamar wacce tai gano ta ce "na shiga uku Yaya Haidar ni ce 'yar sa ido, kuma k'azama" Tayi maganar cikin muryar shagwab'a.


Shahida ta ce "Ai Other half wallahi Yaya Aliyu Haidar ya fad'a mai zurfin baki ga kwana biyun nan ba sai ki ga yana ta wani smiling shi kad'ai" Dariya su ka yi gaba d'ayansu amman ban da Khadijatullahi wacce har lokacin fuskarta babu alamar murmushi "Awww har da ke ko darling sister"Aliyu yayi maganar tare da satar kallon Khadijatullahi "Eh mana Yaya Aliyu Haidar ai ina kula da kai sosai yanzu fad'a mana wannan wace mai sa'a ce tayi sa'a sace zuciyar Yayanmu, zuciyar da take da matuk'ar tsada 'yan mata da yawa suna son su ga cewa wannan kyakkyawar zuciyar ta so su","hmmm! Shahida kenan kawai ku ta ya ni da addu'a kun ji, dan ina tsananin buk'atar haka a halin da nake ciki yanzu" Nihal ta kalli Aliyu sosai, ta fuskanci yana cikin tsananin damuwa "To Yaya Allah Ubangiji ya fitar da kai" Nihal ta fad'a tana cigaba da kallon d'an uwan na ta, Shahida ta ce "Amin ya rabbi".


Amatullahi da ta fuskanci inda maganar Aliyu ta dosa dan ta fahimci cewa Aliyu yana tsananin son Khadijatullahi, saboda irin yadda yake nuna kulawarsa a kan ta, da kuma yadda yake sadaukar da abubuwa da yawa a kan ta, amman kuma tana tausaya masa saboda ta san cewa Khadijatullahi ba lallai ta yarda ta so shi ba, kuma ko da zata yarda gaskiya sai an kai ruwa rana "Yaya Aliyu Allah ya fitar da kai ya dora ka a kan wacce ka ke so, tayi maka son da ba ka tab'a tunani ba, ta so ka da dukkanin zuciyarta" Murmushin jin dad'in Addu'ar da Amatullahi tayi masa yayi sannan ya ce "Amin Allah ya sa sister nagode sosai","Amin" Suka amsa gaba d'ayansu.


Hajiya Mama tana jefe tana jin su ita dai ba ta ce musu komai ba dan kuwa ita ma tuntuni ta fahimci cewar Aliyu yana son Khadijatullahi, ta ji dad'i sosai amman kuma ta wani b'angare na zuciyarta tana tausayawa Aliyun saboda Khadijatullahi ba lallai ta so shi ba, ta tsani maza bayan haka kuma ta tsani Jabir wanda hakan ya shafi Aliyu shi ma ta tsane shi, Aliyu ya tashi daman ya zo ne ya ga Khadijatullahi ya kalli Hajiya Mama tare da cewa "Hajiya zan je gidan Musaddik ba zan dad'e ba zan dawo","to A dawo lafiya" Aliyu ya ce "Allah yasa'' Sannan ya fita daga gidan motarsa ya shiga ya d'auki hanyarsa zuwa gidan Abokinsa Musaddik.


Hajiya Mama suka cigaba da yin hirarsu har sai da aka kira sallar magriba sannan suka tashi kowannansu ya doro alwala suka gabatar da sallar magriba, ko da suka gama suka yi addu'o'in da ake yi bayan anyi sallah sannan suka dora hirarsu daga inda suka tsaya.


*'BANGAREN TEEMARH DA JABIR💕🥀*


Sanye take da wata doguwar riga tana share d'akin rigar tayi matuk'ar kamata sosai, ji tayi an bud'e kofar d'akin da sauri ta d'ago kai suka had'a ido da Jabir wanda yake tsaye a bakin kofar ya hard'e hannuwansa a k'irjinsa yana kallonta yana murmushi, a hankali kuma ya tako zuwa inda take "Love d'inta sannunki da aiki" Kallonsa tayi kamar ba za ta yi magana ba sai kuma ta ce "yawwa sannunka" Sannan ta cigaba da yin sharar sai da ta gama share d'akin gaba d'aya sannan ta zauna a ksn kujera ta kunna t.v, tashar Arewa 24 ta kai ta tarar ana yin episode d'in *k'addarar rayuwa* wani irin murmushi tayi dan tana bala'in son film d'in, Jabir yana kallonta dan yana tsaye a gurin da ta huce ta barshi ya k'i motsawa.




Sai da aka gama episode d'in ta juya dan ta ga inda Jabir d'in yayi dan ta ga yau bai takura mata ba, dan tayi tunanin ma ko ya fita daga d'akin ne, mamaki ya kamata ganinshi a tsaye kamar wani soja a gurin da ta huce shi kuma idanuwansa yana kanta, abin har ya so ya ba ta dariya amman ta shanye tare da cewa "menene ka ke yi a tsaye ko dai soja ka dawo ne ban sani ba?" Zuwa yayi ya zauna kusa da ita "ba dole na zama sojan k'arfi da yaji ba Love d'ita tana fushi da ni, kuma na rasa yadda zan yi nasa ta fahimci cewa ina sonta, amman ita ta fifita kallon film fiye da mijinta" Murmushi tayi sannan ta ce "hmmm Jabir kenan yaudararka wacece ban sani ba kai kan ka kasani na sanka sosai fiye da yadda baka tunani, na san wannan nacin da kake min akwai buk'atar da kake so ka cimma a kai na, dan haka wallahi ni ba zan tab'a yarda da kai ba".


Wata iriyar muguwar ajiyar zuciya ya sauke tabbas shi kansa yasan Teemarh ta san halinsa sosai, kuma yasan dole sai ya samu wannan k'alubalan wajen shawo kanta amman kuma dole sai ya tabbatar ya sa ta yarda da cewa yana sonta dan ya samu buk'atarsa a gurin Teemarh "Teemarh, nasan cewa ba za ki tab'a yarda da ni ba saboda irin abubuwan da nayi miki amman dan Allah ina so ki ba ni dama dan na tabbatar miki da cewa ina sonki","ko kuma kana son jikina ko?" Teemarh ta fad'a tana kallonsa ido cikin ido, Jabir ya rasa me zai ce mata kawai sai ya tashi ya fita wai shi a dole ya nuna mata yayi fushi, ita kuma Teemarh tab'e baki tayi sannan ta kwanta a kan kujera tana chatting, a haka har bacci ya kwasheta.


*'BANGAREN BAFFAN SALIS🚴🏽‍♀️💕*


Washe gari kamar yadda yayi wa Mama alk'awari da misalin k'arfe 2:00pm na yamma bayan yayi sallar azahar ya nufi gidan Alhaji Mansur, yana isa mai gadi yayi masa iso Alhaji Mansur ya cewa mai gadin ya kai shi falon bak'i gashi nan zuwa, haka ya fita ya shiga da Baffa falon bak'i, ba'a fi minti d'aya ba sai ga Alhaji Mansur ya shigo falon bakinsa d'auke da sallama "Assalamu alaikum" Da sauri Baffa ya tashi tsaye tare da amsa masa sallama "Wa'aikumussalam ranka ya dad'e" D'aure fuska Alhaji Mansur yayi tare da cewa "Amman ka ba ni mamaki sosai, ta ya za'ai ka na zaune ina shigowa ka tashi tsaye, raina yayi matuk'ar b'aci sosai" Baffa cikin girmamawa ya ce "Allah ya huci zuciyarka insha Allahu zan kiyaye gaba" Murmushi Alhaji Mansur yayi sannan ya ce "Allah ya sa, zaka iya zama" Ya fad'a yana nuna masa kujera".


Zama yayi sannan suka gaisa Baffa ya fara fad'a masa abin da ya kawo shi "da farko dai Alhaji ina mai ba ku hak'uri a kan irin abin da Mahaifiyar Salis tayi muku na sa ni bata kyauta ba kuma na ji matuk'ar kunyarka saboda na san anyi muku ba dai-dai ba, amman ina mai neman alfarmar da Nihal ta dawo d'akinta" Alhaji Mansur ya gyara zamansa sannan ya ce "Haba dan Allah sirikina saboda haka ne daman ka zo har nan, ai na ga Salis ba sakinta yayi ba dan haka insha Allahu gobe zan dawo da ita har asibitin kuma dan Allah kayi wa Salis d'in ya jiki kafin na zo" Baffa yayi wa Abba godiya sosai sannan ya tashi ya tafi shima Abba ya koma d'akin Hajiya Asiya dan yau anan yake.




*'BANGAREN ALIYU💃🏽💕*


Dawowarsa kenan daga gidan Musaddik sai ga Nihal da Shahida sun shigo d'akin sun zauna kusa dashi, kallonsu yayi tare da sakar musu murmushi ya ce " 'yan biyu meya faru?" Nihal ta ce "Yaya Haidar gurinka muka zo" Kallonsu yayi sannan ya ce "To gani nan 'yan k'annai na" Shahida ta ce "Yaya Aliyu Haidar wa ka ke so?" Kallonta yayi kamar ba zai yi magana ba sai kuma ya ce "Khadijatullahi" Waro ido Nihal tayi tare da fashewa da kukan tausayin d'an uwana ta tabbas daman ta so ta fahimci haka saboda irin yadda yake yi mata, amman ta ya ya Khadijatullahi zata karb'i soyayyarsa bayan ta tsani kowane namiji kuma tana ganin irin yadda Khadijatullahi take nuna tsantsar k'iyayyarta a kan Yayan na su.


"Haba darling sister idan kina kukan nan sai zuciyata ta k'arye ai" Aliyu yayi maganar zuciyarsa nayi masa zafi, Shahida ta ce "Yaya Aliyu Haidar ai dole tayi kuka, kai ma kasan dai Khadijatullahi irin yadda ta tsaneka sosai ta ya za'a ta so ka, Yaya Aliyu Haidar wallahi ni............" Sai kuma ita ma ta saka kuka, hankalinsa yayi matuk'ar tashi shima yasan ya d'aukowa kan sa babban aiki amman kuma ba laifinsa ba ne laifin zuciyarsa ne, rarrashinsu ya shiga yi sannan ya samu su ka yi shiru, nan da suka d'aukar masa alk'awarin zasu taimaka masa har sai Khadijatullahi ta so shi, suka shiga kwantar masa da hankali ganin irin yadda ya damu sosai, Aliyu cikin raunanniyar muryarsa ya ce "Nagode muku sosai darling sisters, na san kun damu da ni kuma na san na d'aukowa kai na babban aiki, shiyasa na ce muku ku ta ya ni da addu'a","Insha Allah zamu ta ya ka kuma zamu taimaka maka wajen ganin Khadijatullahi ta so ka" Nan dai suka yi masa alk'awari kala-kala a kan Khadijatullahi sai sun san yadda su ka yi ta so shi.


*'BANGAREN ASIYA👹*


Yau ya kasance za'a fad'i wanda zai kawo musu wanda za'a sha jininshi bayan sun gama tsaface-tsafacensu Wannan saurayin da har yau ban san sunansa ba ya mik'e ya gama zagaye su sannan ya zo gaban Hajiya Asiya ya tsaya tare da mik'a mata wata laya ta karb'a sannan ya ce "me za ki kawo mana kishiyarki da kuma mijinki dan muna buk'atar shan jininsu" Hajiya Asiya tayi tare da cewa.
"Alhaji kuma? Gaskiya ba zan iya ba da mijina ba" Ta yi maganar tana kallonshi ido cikin ido, ransa yayi matuk'ar b'aci cikin muryar da ta ke bayyanar da tsantsar b'acin rai ta ce "To idan kuwa ba za ki kawo shi mu sha jininsa ba to ki tabbatar da cewa lokacin mutuwarki yayiii dan kuwa za mu sha jininki, gobe da daddare mu ke buk'atar ki kawo su idan kuwa ba ki kawo su gaba d'aya ba to tabbas zan kasheki ne" Ya k'arasa maganar yana dora mata wata iriyar zagegiyar wuk'a a wuyanta, gabanta ne ya shiga fad'uwa, haka dai suka gama kowa ya fito dan tafiya gidansa, Hajiya Suhaima ce ta biyo bayan Hajiya Asiya wacce har ta bud'e motarta zata shiga kiran sunanta tayi da k'arfi "Asiya" Juyawa Hajiya Asiya tayi ranta a b'ace a halin yanzu wata iryar muguwar tsanar Hajiya Suhaima ta ke ji, domin kuwa ita ta ja mata ta kawota nan gidan, ita tayi tunanin ai gurin wani boka za su je ya gama musu da Aunty Murja.


"Menene?" Ta yi maganar tana wurga mata wani irin kallo, wata iriyar dariya Hajiya Suhaima ta fashe da ita tana cewa "Ke daman kina tunanin cewa zaki sha jinin iyayen wasu, mazajen wasu, da kuma 'yaya da k'annan wasu ki ce wai ke ba za'a sha na mijinki ba, to wallahi ba ki isa ba, dole sai mun sha jinin mijinki, kuma ni ba haka na so ba, na so ace jinin wannan tambad'adden d'an naki a ka ce, amman mu je zuwa na san wata rana dole sai mun sha jinin d'an tsinanniya" Wani irin mahaukacin mari Hajiya Asiya ta zabgawa Suhaima hagu da dama sai da ta jera mata kusan sau biyar, sannan ta ce "To wawiya dabba ki sa ni burinki ba zai tab'a cika ba, dan kuwa ko Abban Jabir ba za ku sha jininsa ba ballantana yarona Jabir, ke ce tsohuwar mahaukaciya da har zaki iya ba da mahaifiyarki tabbas asara da tab'ewa su tabbata a gareki shashasha jaka mara tunani" Tana gama fad'ar haka ta shige motarta ta ja da k'arfi ta nufi gidanta.


Wannan saurayin ya saki murmushi ya ce "Asiya kenan kina wasa da Jafar uban matsafa amman Allah ya kaimu gobe za ki ga aiki da cikawa, kar Allah ya sa ki kawo su ki ga abin da zai faru da ke" Yana gama fad'ar haka shi ma ya tafi gidansa, Hajiya Suhaima kuwa nan ta kuduri niyyar sai ta lalata Ahalin Asiya gaba d'aya, ta jima tana sake-sake sannan ta nufi motarta ta ja ta bar gurin, zuciyarta fal bak'in ciki.


*'BANGAREN AMATULLAHI👰🏼‍♀*


Tafiya ta ke yi cikin nutsuwa da kuma aji, a haka har ta isa club d'in da Jabir ya ke zuwa, nesa da club d'in ta tsaya,daga gurin da take ana iya hango cikin club d'in ta jima tana raba ido ta ga ta ina zata hango Jabir amman babu alamar Jabir a gurin ta shafe kusan awa d'aya tana tsaye sai chan ta hango Jabir ya fito daga hotel yana rumgume da wata budurwa da alama ta sha ta bugu sosai "Shege d'an gidan mahaukaciya, wallahi na juyo gareka sai ka gommace kid'a da karatu" Wani yaro ne ya zo hucewa ta yi saurin kiransa "kai yaro dan Allah zo" Zuwa yaron yayi tare da cewa "ga ni" Wata takadda ta ba shi, sannan ta nuna masa Jabir tare da cewa "Wanchan za ka kaiwa wannan takaddar dan Allah" karb'a yayi tare da cewa "to zan ba shi" Yaron ya nufi gurin da Jabir yake sai da Amatullahi ta tabbatar yaron ya ba wa Jabir wannan takaddar sannan ta juya ta nufi gidansu dan ta ga halin da 'yan gidan su ke.


Amatullahi irin yadda take bibiyar Jabir ko mahaifiyarsa Hajiya Asiya ba ta yi masa, dan kuwa duk guraren da ya ke zuwa sai da ta bincikosu kuma duk motsin da yake yi tana sane dashi dan kuwa ya d'auki aniyyar d'aukarwa Khadijatullahi fansar abin da yayi mata sai ta tabbatar da wulak'antasa ta hana shi sukuni, tana shiga gidan ta tarar da abin da ya bata tsoro Inna Larai ta gani tare da Malam d'an ladi mai guga sun fito daga d'akin Inna Larai wani irin ihu ta fasa tare da fita waje ta tsaya dai-dai kofar gidan tana cigaba da kurma ihu, ai kuwa mutane su ka yi kanta suna tambayarta meya faru? "Inna Larai da Malam d'an Ladi mai guga na gani sun fito daga d'aki" Ta yi maganar tana kuka, ai kuwa nan jama'a su ka shiga gidan suka tarar da su Inna Larai da Malam d'an Ladi a tsaye duk sun rud'e dan sun san yau asirinsu ya gama tonuwa, dukan Malam d'an Ladi suka shiga yi ba ji ba gani, Inna Larai ta shige d'aki tare da kulle kofar tana kuka.


Amatullahi kuwa wayar wani Adamu ta ara ta kira Mahaifinta ba fad'a masa komai ba bu abin da ta b'oye masa, hankalinsa ya tashi anan take ya ce ta ba wa Inna Larai ta ce ai ta shiga d'aki ta kulle ya ce to ki ce mata ta gaggauta fitar min daga gida na saketa saki uku, ba na buk'atar sa ke ganinta, a rayuwata yana gama fad'ar haka ya kashe wayar zuciyarsa na yi masa zafi, Adamu ta ba wa wayarsa tare da shiga gidan dan kuwa ba za ta bar Inna Larai ta k'ara ko da minti biyar ba a gidan, d'akinta ta nufa ta d'auko wani k'arfe mai tsini sannan ta nufi d'akin Inna Larai tana buga kofar d'akin da k'arfi tare da cewa "to tsinanniya tsohuwar 'yar bariki ki bud'e kofar nan ki bar mana gida dan Babana ya sake ki saki uku, sai ki je ki cigaba da yin karuwancin na ki a chan wani gurin amman ba'a gidan nan ba" Tana magana tana buga kofar kuma irin bugun da ta ke yi wa kofar ba na wasa ba ne, Inna Larai jin abin da Amatullahi ta ce ta fashe da kuka tare da saka kayanta a buhu ta bud'e kofar dan ta san halin Amatullahi ba ta k'i ta k'arya kofar ba kuma ta yi mata rashin mutunci.


Hanyar fita daga gidan Inna Larai ta nufa tana jin kunyar kanta saboda irin mugayen maganganun da 'yan unguwar ta su suke fad'a mata Amatullahi ta bi ta a baya tana zungurarta da k'arfen tana cewa "Allah ya ra ka taki gona, sai a bi wani sarkin ba dai Yarima ba" Jama'a Unguwar kuwa bayan sun gama yi wa Malam d'an Ladi duka suka cukumeshi sau police station, Amatullahi ta ja kofar gidan ta mukulle da mukulli sannan ta nufi gidan Hajiya Mama ranta fas, dan kuma a rana d'aya ta jefi tsuntsu biyu da dutse d'aya.


*'BANGAREN HAFSA, SAFWAN DA SAFNA😉*


A yau aka saka ranar Safwan da Hafsa wata hud'u aka saka, ta kira Shahida ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login