Showing 66001 words to 69000 words out of 83141 words
Chapter 23 - Daren Aurena Part 1 Complete Hausa Novel By Nana M Sha'aban .txt
yayi ya zura kansa yana kallonta ita kuma sai turo masa baki take idanuwanta sun cicciko da kwalla za ta yi kuka ta ce "Yau ma ba za ka je da ni ba ko?" Tayi maganar hawaye na gangarowa daga idanuwanta, hannunsa yasa yana goge mata hawayen fuskarsa ta chanza zuwa yanayin damuwa ya ce "Am sorry Babyna na saka ki kuka, kin san ina sonki da yawa ba na son kowane banza ya dinga kalle min fuskar kyakkyawar matata, ina matuk'ar kishinki sosai kin ga Ma'aikatarmu gaba d'ayanmu maza ne, babu mata wannan shine dalilin" Nihal ta ce "to na ji zan zauna a mota" Salis ya shiga motar dan kuwa yasan daman idan Nihal tayi irin wannan rigimar sai yayi da gaske yake shawo kanta "Ta ya ya zan bar gimbiyata a cikin mota ni kuma na tafi office kina tunanin zan iya barinki a cikin mota, to Wallahi Nafisa ba zan tab'a tafi na barki a cikin mota ko da kuma na minti d'aya ne barantana na awanni.
Murmushi Nihal tayi jin ya fad'i sunata na gaskiya dan ba ta tab'a jin ya fad'a ba sai yau, irin yadda ya fad'i sunan nata cikin wani irin salo yayi matuk'ar sakata nishad'i kuma ta ji tana matuk'ar k'aunar sunan na ta, "to amman ni ina jin tsoron in zauna ni kad'ai a gidan nan" Murmushi yayi ya ce "to sai na ka na kai ki gidan Mama idan na dawo sai na biya na d'auke ki","Yawwa to shikenan" Fita Salis yayi ya koma mazaunin driver ya ja motar ya nufi gidan mahaifiyarsa, suna isa suka fita a tare suka shiga gidan, Mama tayi matuk'ar yin farin cikin ganinsu tare nan suka gaisheta sannan Salis ya tashi ya fita dan yayi lating ya shiga motarsa ya ja ya nufi ma'aikatarsu.
*'BANGAREN HAJIYA ASIYA👹*
Kwance take a gadon asibiti Alhaji Mukhtar wanda suke tare dashi a k'ungiyar matsafa yana zaune a kan kujera ya zabga tagumi yana kallonta, Alhaji Mukhtar jiya ya makara bai je gidan da wuri ba har bayan da Abba da Aunty Murja suka tafi sannan ya iso gidan yana shiga ya tarar da Hajiya Asiya kwance male-male cikin jini, bai tsaya yin wani tunani ba shine ya d'auketa ya sakata a mota ya kawota asibiti, wani irin sonta ne yake ji yana ratsa masa cikin jini daman ya dad'e yana son ya nuna mata yana tsananin sonta amman ya rasa yadda zai yi ya sanar da ita, amman abin da ya shige masa duhu shine meyafaru da gidan matsafan nasu ko da wani ne yayi musu lek'en asiri yayi musu shunan 'yan sanda? Amman bashi da me basa amsa dan haka ya watsar da tambayoyi ya shiga yin tunani a kan soyayyar da za su yi da Hajiya Asiya da zarar ta amince masa, shi kuma a shirye yake da yayi komai saboda ita.
Haka dai har wajen k'arfe biyar babu alamar Hajiya Asiya zata farfad'o ko da yake daman likitan ya ce masa zata jima sosai kafin ta farfad'o dan kuma ba k'aramin duka a ka yi mata ba, dan da ba'a kawota asibitin da wuri ba da zata iya rasa ranta, Alhaji Mukhtar ya tashi ya fita domin ya samarwa kansa abin da zai saka a bakinsa wani babban shago ya shiga yayi musu siyayya kusan leda biyar manya-manyan ledoji ne kuma gaba d'aya kayan ciye-ciye ne, ya dawo d'akin da aka kwantar da Hajiya Asiya ya zauna yana jiran farfad'owarta.
*POLY🏛️💕*
Tafiya suka suna hirarsu ta k'awaye suna dariya har suka iso gurin da suke zama, kowaccen su ta samu guri ta zauna Hafsa ta kalli Khadijatullahi ta ce "Amaryar Yaya Aliyu ina gaisuwa" Harararta Khadijatullahi tayi kawai ba tare da ta ce komai ba, sai jijjiga Affan ta ke yi Amatullahi ta ce "Lallai kuwa dai gwanda kema ki fad'a mata ta gyara halinta, dan kuwa duk wanda ya ce yana sonka ai ya gama yi maka komai","Wannan haka yake besty tabbas Yaya Aliyu yana matuk'ar son Khadijatullahi amman ita ta tsaya yi masa shakara (yanga)" Dariya Amatullahi tayi ta ce "Ai kuwa gwanda ta dai na dan kuma Aliyu d'aya ne tamkar da dubu, ba irinsa ake yi wa yanga ba","tabbas"Hafsa tayi maganar tana kallon Khadijatullahi.
Khadijatullahi ta ce " besty wai ba na ce miki shikenan ba"Tayi maganar cikin muryar kuka idanuwanta a kan Amatullahi, kallonta Amatullahi tayi ta ce "Ohh ni yau na ga abin da yafi k'arfina, ce miki nayi ki yi kuka" Khadijatullahi ta goge hawayen da suka zubo mata tare da sauke ajiyar zuciya, Hafsa ta dafata tana cewa "Besty wallahi Yaya Aliyu ba halinsu d'aya da wannan d'an iska kema iya zaman da ku ka yi dashi ya kamata ki fahimci hakan" Khadijatullahi ta kalli Hafsa ta ce "To shikenan Besty" Anan aka koma Aji suka tashi suka nufi ajin na su.
*'BANGAREN TALATU😂*
Lokacin da aka sanar da ita cewa Salis da Nihal sun koma gidansu kuma sun cigaba da yin rayuwarsu ta ma'aurata fad'uwa tayi ta suma har sai da aka kai ta asibiti haka tai-tayin zage-zage a asibitin nan da aka turasu asibitin mahaukata saboda irin yadda take dukan duk wanda ya matso kusa da ita, domin a cewarsu Talatun tana da matsala a kwakwalwarta.
*'BANGAREN ALIYU💔💍*
Da wuri ya dawo daga Office saboda ya d'auko su Khadijatullahi, ko gida bai je ba ya huce gurin da Shahida ta ke yin aiki ya kirata a waya ta ce masa yanzu zata fito ya jirata ta gama komai, ko minti d'aya ba'a yi ba sai ga Shahida ta fito gaban motar ta bud'e ta shiga, Aliyu ya ja motar ya huce makarantar su Khadijatullahi, ai kuwa yayi sa'a yana isa makarantar ana tashin su Khadijatullahi fitowa su ka yi daga motar suka jinjina a jikin motar, Khadijatullahi wacce tun fitowarta ta ga shigowar motar Aliyu gabanta yayi muguwae fad'uwa haka kawai ta ke jin wani irin abu a cikin zuciyarta, Amatullahi da Hafsa kuwa ba su gansu ba, sai da su ka zo daf dasu sannan Amatullahi ta gansu murmushi tayi tare da kallon Khadijatullahi "Besty ga mijinki ya zo d'aukarmu" Kallonta Khadijatullahi ta ce "Yaya Aliyu ai na ganshi tunda mu ka fito" Tayi maganar cikin wani irin yanayi dan ba ta son ran bestyn na ta ya b'aci.
K'arasawa gurin da suke tsaya su ka yi Hafsa ta rumgume Shahida tana cewa "Oyoyo sister ina Sister Nafisa" Shahida tayi murmushi ta ce "Nihal tana chan gidanta, ta koma yau satinta uku kenan da komawa" Hafsa ta ce "Allah sarki zan kirata kuwa" Sai kuma ta kalli Aliyu ta ce "Yaya Aliyu ina yini" Murmushi yayi sannan ya ce "Lafiya alhamdulillahi, ya karatu?",mun gode Allah" Hafsa ta fad'a tana kallon motar Yaya Safwan wacce ya kunno hancin motar cikin makarantar yayi parking sannan ya fito ya nufo gurin da su Hafsa suke dan ya gansu tun shigowarsa, hannu ya mik'awa Aliyu su ka yi musafaha Hafsa ta ce "Yaya Safwan wannan shine Yaya Aliyun da nake baka labarin cewar shi zai auri bestyna Khadijatullahi" Murmushi Safwan yayi ya ce "Ai na sanshi Aliyu Mansur Jikamshi"Aliyu ya ce "Wato Hafsyy har kin ba shi wannan labarin kenan" Yayi maganar cike da jin dad'in maganar Hafsa sannan ya dora da cewar "Ai mun san juna ni da Safwan sosai" Hafsa ta ce "Au to ai shikenan ma" Haka su ka yi d'an hira da bata huce minti biyu ba, Hafsa tayi musu sallama suka jera ita da Safwan suka shiga mota Hafsa tana d'agowa su Khadijatullahi hannu har suka fita daga makarantar.
Aliyu ya bud'ewa Khadijatullahi gaban motar ta shiga dan su Shahida tunda motar su Hafsa ta fita daga makarantar suka bud'e bayan motar suka shiga, suka bar Khadijatullahi a tsaye ita da Aliyu, shima zagayawa yayi ya zauna mazaunin driver ya ja motar suka nufi gida, Aliyu yana tuki yana satar kallon Khadijatullahi ita kuwa tana lura dashi dan tana kallonsa ta jefen idonta amman ta nuna kamar ba ta san abin da ya ke yi ba.
Suna isa gidan Aliyu yayi parking sannan ya fito daga cikin motar cikin takunsa na isa da tak'ama ya zagayo ya bud'ewa Khadijatullahi motar ta fito su Shahida ma suka fito suka shige cikin gidan, Aliyu ya kalli Khadijatullahi ya ce "My heartbeat idan kin shiga gida kin huta ki zo falon bak'i ina son ganinki keda yarona","To Yaya Aliyu" Tayi maganar a sanyaye tare da nufar hanyar shiga gidan, shima ya bi bayanta zuciyarsa cike da farin ciki, ta huce zuwa falo, shi kuma Aliyu ya shige d'akinsa.
Wajen k'arfe 8:00pm na dare sai ga Khadijatullah ta nufi falon bak'i tana rumgume da Affan a k'irjinta, ta shiga falon bakinta d'auke da sallama "Assalamu alaikum" Ido biyu ta yi da Aliyu yana zaune yana kallon bbc hausa "Wa'alaikissalam Matata" Ya amsa mata sallamar ciki muryarsa me jan hankalin mutane da kuma rud'a 'yammata.
Khadijatullah ta shiga ta zauna a kan kujera tare da kwantar da Affan Wanda yake shan baccinsa hankalinsa kwance, Aliyu ya tashi daga gurin da yake ya koma kujerar da Khadijatullah take zaune, ya zauna da yake kujerar ta zaman mutum uku ce, Affan ya d'auka tare da sumbatarsa a kuncinsa, kallon Khadijatullah yayi ya ce "My wife to be, ya gajiya","ba gajiya" Ta ce a takaice.
"Khadijatullah wallahi ina sonki sosai, Dan Allah ki karb'i soyayyata, nayi miki Alk'awarin ba zan tab'a bari ki tozarta ba, Kuma ba zan yi miki irin abin da Yaya Jabir yayi miki ba, saboda ni da shi ba halinmu d'aya dashi ba, zaki iya gwada ni ta kowacce hanya domin ki tabbatar da abin da nake fad'a miki".
"Yaya Aliyu Ina tsoro kada.............." Sai ta fashe da kuka mai cin rai,hankalin Aliyu ya tashi "Final choice meyafaru?Dan Allah ki daina kukan nan haka" Shuru tayi tana sauke ajiyar zuciya ta ce "Yaya Aliyu kayi min Alk'awarin ba za ka tab'a cutar da ni ba, kuma idan munyi aure za ka rik'eni da amana" Murmushi yayi ya ce "Indai wannan ne matsalarki Matata kada ki damu, Kuma nayi miki Alk'awarin ba zan tab'a cutar da ke ba","To na amince da soyayyarka Yaya Aliyu".
"Da gaske babyna" Khadijatullah ta gyad'a masa kai alamar eh, anan fa Aliyu ya shiga zuba mata kalaman soyayya, sai wajen k'arfe 8:45pm sannan Aliyu ya rakata har bakin kofar falo ya mik'a mata Affan sannan su ka yi sallama ya koma d'akinsa ita kuma ta shige falon, kai tsaye bedroom ta nufa ta kwanta, bacci Mai nauyi yayi awon gaba da ita.
*'BANGAREN TEEMARH DA JABIR😂*
Zaune suke a kan kujera suna kallon *so k'addarar zuciya* Arewa 24 Jabir ya janyo Teemarh jikinsa tana shafata, Yana sumbatar kuncinta kallonsa Teemarh tayi tare da cewa "Dan Allah darling ka bari mu gama yin kallon nan, sai mu yi abin da ya dace","A'a darling yanzu nake so please ki tafi mu kwanta".
"Ya salam darling Dan Allah........." Toshe bakinta yayi sannan ya d'auketa cak ya kai ta kan gado, kayan jikinta ya shiga kok'arin cire Mata, Teemarh ta saka kuka tana cewa "Darling Wai meyasa ba ka son, farin cikina kawai Kai burinka ka samu abin da daga gareni" Jabir Wanda yake kok'arin zame Mata riga jin abin da Teemarh take fad'a yasa ya tashi daga kanta, kayansa ya mayar jikinsa ya fita daga d'akin a fusace, Teemarh ta saka kuka, ita ma ta mayar da kayanta ta bi bayansa da sauri, Amman Bata ga koda k'eyar Jabir ba, barantana shi, durk'ushewa tayi a k'asa tana kuka, ji tayi an d'agota da sauri ta juya tare da tashi tsaye tana ci gaba da yin kukan, Aunty Murja ta kalleta sosai sannan ta ce "Fatima meyafaru ki ke kuka?","Bakomai Mummy" Teemarh tayi maganar cikin shash-shekar kuka, "ba za ki iya fad'a min damuwarki ba Fatima" Kukan Teemarh ya tsananta ta ce "Darling ne" Tayi maganar tana goge hawayen fuskarta.
Aunty Murja ta ce "koma Mai yayi miki bai kamata ace kin zo kina yin kuka ba, ya kamata ki zauna ki nutsu ki kirasa, sai ku tattauna a kan matsalarku, ta haka ne za ku fuskanci juna" Teemarh tayi murmushi ta ce "Nagode Mummy zan yi amfani da shawararki insha Allahu" Daga nan kowannan su ya koma d'akinsa, Teemarh ta d'auki wayarta ta shiga kiran layin Jabir Amman a kashe wayar take Dan haka ta zauna ta cigaba da yin kallonta Amman zuciyarta tana gurin Jabir.
*'BANGAREN SAFNA😔👏🏽*
Safna ta fito da gudu daga d'akinta tana murmushi suka had'a ido da Safwan ta matso kusa dashi zata rumgumeshi, yayi saurin tureta yana cewa "karki matso kusa da ni" Yayi maganar fuskarsa a d'aure, Safna ta ce "Ruhina ka yi hak'uri na tuba ba zan k'ara ba, Amman Dan Allah karka hukunta ta wannan hanyar ka yi min duk abin da ya dace da ni ka ji Ruhina" Kallonta yayi kamar ba zai yi magana ba sai Kuma ya ce "Akwai sharad'ai guda uku da zan fad'a miki, idan har ki ka amince dasu to shikenan komai zai huce" Safna ta ce "wad'anne sharad'ai ne?" Zama Safwan yayi ita kuma ta tsaya tana son jin wane sharad'i ne wannan "sharad'i na farko shine karki sa ke yin kishi a kan Hafsa ina son ki d'auketa tamkar Zahra k'anwarki wacce ku ka fito ciki d'aya, Sharad'i na biyu kuma karki sa ke yi min zancen yaushe Khalid zai dawo saboda ni nasan gurin da na kai shi babu abin da za'ayi masa na kuntatawa Sharad'i na uku kuma karki sa ke yi min maganar Hafsa idan muna tare da ke, idan kin yarda da su za ki iya zuwa" Safwan yayi maganar tare da bud'e hannayensa alamar Safnan ta zo jikinsa.
Hawaye ne suka shiga gangaro mata a hankali ta fara tafiya kamar mai sand'a, ta fad'a jikinsa tare da rushewa da wani irin kuka, tana tsananin jin kewar yaronta amman kuma anyi mata katangar k'arfe dashi, tana ji tana gani ba ta da damar da za ta tambayi yaronta, sai ya zama laifi, "na amince da sharad'anka ruhina amman dan Allah ka kawo min yarona koda sau d'aya ne na ganshi, idan na ganshi ba zan sake cewa a kawo min shi ba nayi maka alk'awari" Tausayinta ya kamashi amman ya zama dole yayi haka, domin ya k'ara saka son Hafsa a cikin zuciyar Safna "to shikenan zan kawo miki shi gobe insha Allahu","to nagode" Safna ta fad'a cikin rawar murya, daga nan suka dora soyayyarsu daga inda suka tsaya.
*Team Khadijatullahi where you😂😂yau fa ta gwangwaje ku da kalamai masu dad'i*
*'BANGAREN HAJIYA ASIYA DA ALHAJI MUKHTAR🤔*
Sai da Hajiya Asiya ta kwana biyu sannan ta farfad'o wajen k'arfe 8:00am na safe Alhaji Mukhtar yana zaune kusa da ita ya zuba mata ido yana kallonta cike da so da k'aunarta, a hankali ta fara bud'e idanuwanta ta zuba su a saman d'akin abubuwan da suka faru suka shiga fad'o mata hawaye na zuba daga idanuwanta, yanzu shikenan ta san gurin wad'annan wahalallun iyayen nata zata koma ta ci gaba da shan wahala, Alhaji Mukhtar ya saki murmushi tare da kiran sunanta "Asiya" A hankali ta juya ta kalli mai kiran na ta ganin Alhaji Mukhtar yayi matuk'ar ba ta mamaki tare da jefo masa tambayoyi "Ina ne nan? Me na zo yi nan? Waya kawo ni? Ina yarana? Ina Abban Jabir" Murmushi yayi mai cin rai jin ta ambaci sunan mijinta amman ya danne ya fara ba ta amsoshinta "kina asibiti ne, na je gidan tsafi ne na tarar da ke kwance cikin jini shine ya d'aukoki na kawoki, kuma tun da na kawoki babu wanda ya zo gurinki amman gaskiya nayi mamaki sosai yaranki ko mijinki babu wanda ya nemeki kenan hakan na nufin basa buk'atarki a rayuwarsu, ko kuma basu damu da ke ba?".
Hawaye Hajiya Asiya tashi zubarwa tana cewa "A'a yarana suna sona sosai ba za su iya juya min baya ba kuma"............"To gashi sun juya miki kuwa tunda yau kusan kwananki goma babu wanda ya zo asibitin nan kuma har gidan na je amman su ka yi min rashin mutunci suka ce basa sonki a rayuwarsu" Alhaji Muhktar ya fad'a cikin yanayin damuwa dan kuwa ya fad'i haka ne kawai dan Hajiya Asiya ta ji haushi kar ta ce zata koma gidan mijin na ta, dan kuwa shi bai ma san ina ne gidan Hajiya Asiyan ba, kuma bai san waye mijin na ta ba.
"Yanzu haka su Jabir za su yi min ban yi tunanin haka daga garesu ba kuma nima insha Allahu zan fita a rayuwarsu kamar yadda nima suka fita a rayuwata" Hajiya Asiya tayi magana tare da goge hawayen fuskarta, Alhaji Mukhtar kuwa murmushi yayi ganin cikin k'ank'anin lokaci yayi nasarar raba tsakanin Hajiya Asiya da mijinta da kuma yaranta yanzu shikenan dole yasan shi za ta bi ya kai ta gidansa ya samu ya biya buk'atarsa da ita dan a iya zaman da su ka yi da ita ya fuskanci cewar Hajiya Asiya macece mai shegen son kud'in tsiya, dan haka ya san da zarar yana sakar mata kud'i to bashi da wata damuwa,haka dai yayi ta rarrashinta tare da cusa mata tsanar yaranta da kuma mijinta.
*'BANGAREN INNA LARAI DA LADO😂😣*
Tun ranar da Inna Larai ta dawo gida, yaronta da iyayenta suka d'auki karan tsana suka dora mata domin sun ji labarin irin abin da ta aikata domin a cewarsu kaf danginsu babu mazinaci, dan haka suka cireta daga cikinsu wani d'an k'aramin d'aki suka ba ta wanda ake kiwon kaji a cikinsa, kaji ne gaba d'aya a cikin d'akin dan su kansu kajin ma d'akin yayi musu kad'an, a haka amman Inna Larai take rab'awa take zama duk a takure, ga shi sunyi mata gargad'in kar su sake su ga k'afarta a waje idan har ba su suka bata izinin ta fito ba, ba'a ba ta aminci sai kowa ya ci ragowar da aka rage shi za'a gefa mata a jikinta ya zube kajin su yo kanta su yi ta caccakarta sun cin abincin, wata ran kuwa ba za su bata ba haka zata wuni da kwana ba ta ci abinci ba.
Lado kuwa duk irin abin da ake yi wa mahaifiyarsa ko a jikinsa dan wani abun ma shi yake tsara yadda za'ayi mata