Showing 45001 words to 48000 words out of 83141 words

Chapter 16 - Daren Aurena Part 1 Complete Hausa Novel By Nana M Sha'aban .txt

10 Jan 2025

3081

ba","haba dai wannan kayan dad'in masu yawa ai sai kin taya ni ci ma dan yayi min yawa" Hannunta ya jawo ta zauna kusa dashi suka fara cin meatpie d'in hankalinsu a kwance sai da ta tabbatar ya koshi sannan ta kwashe plate d'in ta kai kitchen, haka suka jera a tare domin ta rakashi zuwa bakin mota ya tafi aiki, babu kowa a falon haka ta rakashi ya shiga mota har sai da ta ga ya fita daga gidan sannan ta koma ta shige d'akinta ta kulle da key.


*'BANGAREN SALIS😣*


Salis da taikamakon Allah likitoci suka samu suka yi nasara ya farfad'o amman duk da haka babu abin da yake iya cewa sai nishi da sauke ajiyar zuciya idan an ce masa ya jiki baya iya amsawa sai dai kawai ya gyad'a kai, bashi da wani tunani sai na babyn baby, kullum cikin addu'a yake Allah yasa tana cikin koshin lafiya, Allah ya bata kuwa juriyar rashin ganinsa da bata yi, yau kamar kullum yana kwance a kan gado Mama ta tafi gida domin dafa masa abinci babu kowa a d'akin.


Doctor Sadiya ce ta shigo d'akin domin duba yanayin jikinshi,bayan ta duba sa ta ga jikin nasa da sauk'i ta juya zata fita Salis cikin rawar murya yana maganar a harhard'e ya ce "doctor dan Allah taimakona nake so ki yi" Juyowa tayi tana murmushi jin yayi magana dan duk da ya farfad'o bai yi magana ba, sai dai kawai ya dinga bin mutane da ido "Wane irin taimako kenan?","wayarki na ke so ki ara min zan kira babyna" Babu musu ta mik'a masa wayar sannan ta fita daga d'akin, shi kuwa Salis ya saka number Nihal a wayar sannan ya kara wayar a kunnansa ring d'aya biyu ta d'auka tare da yin sallama "Assalamu alaikum","Babyna" Salis ya fad'a cikin yanayin farin ciki, Nihal wacce take cikin su Shahida duk ta rud'e hawaye suka fara zuba daga idonta "Babyn baby kai ne, ya jikin naka, ko har yanzu ba ka ji sauk'i ba na ji muryarka wani iri" Da kyar ya iya cewa "Babyna duk rashin ki kusa da ni ne ya saka ni, cikin wannan yanayin wallahi ina sonki sosai" Nihal ta k'ara k'ank'ame wayar dan ji take kamar idan bata rik'e wayar sosai da hakan zai nisantata daga mijin na ta, cikin shash-shekar kuka ta ce "Nima ina sonka sosai, kullum da tunaninka na ke kwana ba na iya bacci, yanzu shikenan saki na zaka yi, ba zamu k'ara zama a matsayin ma'aurata ba?","ba zan tab's iya sakinki ba Nihal domin kin ri ga kin zama wani b'angare na jikina, idan har nayi gangancin rabuwa da ke to tabbas kamar nayi gangancin rabuwa da rayuwata saboda ke ce rayuwata" Kuka ta saka sosai, Khadijatullahi ta rik'eta tana ba ta hak'uri shima Salis d'in kukan yake kuma bai kashe wayar ba, rarrashinta ya shiga yi da kalamai masu dad'i har ya samu tayi shuru, haka dai yayi ta yi mata kalaman soyayya ita ma tana mayar masa har sai da kud'in wayar ya k'are sannan Nihal ta ajiye wayar.


Shi kuma Salis a b'angarenshi ya samu sauk'in abin da yake ji a ranshi kuma ya samu nutsuwa doctor Sadiya ta shigo ya ba ta wayar tare da cewa "sai dai kuma mun k'arar miki da credit kuma gashi babu waya a hannuna da na saka miki","Laaa babu komai wallahi" Ta fad'a tare da fita waje, shi kuma ya kwanta wani irin bacci mai dad'i yayi awan gaba dashi.


*'BANGAREN NIHAL💔😰*


Shuru tayi tana jin wani irin sabon son Salis d'in yana k'ara ratsata, Shahida ta ce "to romeo sai ki daina kukan haka ko?" Amatullahi ta ce "Ahhh kin ji mu da wannan tsohuwar ba dole tayi kuka ba ana shirin rabata da kunun zak'in zuciyarta" Khadijatullhi ta ce "Allah ya shiryeki besty wallahi ke ko, meye wani kunun zak'in zuciya da yake duk salon magana kin san shi" Dariya sosai suka dinga yi dan kuwa maganar Khadijatullahi ta basu dariya Hafsa ta ce "wai besty ya kuwa ginin na ki?","Wallahi Allah ya taimake ni, yana daf da rugujewa na isa na samu na k'ara had'eshi da juna","Allah ya shiryeki to" Khadijatullahi tayi magana tana dariya haka dai sukai ta hirarsu abin ban sha'awa wajen k'arfe hud'u Safwan ya zo d'aukan Hafsa har bakin motar suka raka ta, Khadijatullahi ta so ta nok'e tak'i zuwa Hafsa ta b'ata rai shiyasa a dole ta bi su, suka gaisa da Yaya Safwan d'in sannan suka koma gida.


Hajiya Mama wacce take zaune a kan kujera ita da Aliyi suna hira ta kallesu ganinsu reras ta ce "Ohhh ai kuwa idan na zo aurar da ku zan sha kud'i dan ma d'aya daga cikinku ita tana da aure" Tab'e baki Khadijatullahi tayi sannan ta shige d'aki dan ita ba ta son duk abin da ya danganci aure ko kuma namiji "to matar d'aki d'azu kin fito yanzu daga maganar aure shi ne zaki koma"Hajiya Mama ta fad'a tana bin bayan Khadijatullahi da kallo ma d'akin suka nufa Amatullahi ta ce Hajiya Mama "ai ke dai bari wallahi ni zan dinga tara miki kud'in ma, ki dinga shan farfesu" Ta yi maganar tare da shigewa d'akin.


Hirarsu suka shiga yi daga k'arshe Nihal ta ce "ya kamata mu je gurin Aunty Murja yau kwananta d'aya kar ta ga ba mu je ba","hakane kam" Amatullahi ta fad'a "ku bari sai gobe kun ga yanzu yamma tayi sosai" Khadijatullahi ta fad'a "Allah ya kai mu goben lafiya" Shahida tayi maganar tana murmushi "Amin ya rabbi" suka amsa gaba d'ayansu.


*'WASHE GARI💥🔱*


Hankalin Safna a tashe yake gaba d'aya ta kasa tsaye ta kasa zaune, saboda tun da jiya da ruhinta ya fita bai dawo ba, kuma da dare yayi ta ga bai dawo ba ta shirya ta tafi gidan su Hafsa ta ga ko yana chan tana zuwa ta shiga gidan da sallama duk a firgice take dukansu suna falo har da Abbansu Hafsa tana rumgume da Khalid tana yi masa wasa, kai tsaye gurin Hafsa ta nufi tana tambayarta "Hafsa ina ruhina","wanene kuma ruhinki" Hafsa ta tambayeta dan gaba d'aya ta yi tunanin Khalid ta zo d'auka "to ya zaki tambayeki ki fito min da mijina" Sai a sannan Hafsa abin da Safna take nufi ta ce "ni tun jiya da ya kawo ni gidan wajen k'arfe hud'u ya ce gida zai tafi ban sake ganinshi ba","ki ka ce tun jiya ba ki ganshi ba?" Safna ta fad'a hawaye na zuba daga idanta Khalid ya matso kusa da ita yana cewa "Mommy ina Abbana","Ban san inda yake ba, tun jiya da ya dawo d'aukar wata takarda ban sake ganinshi ba" Safna ta fad'a tare da zubewa tana kuka, Khalid ma jikinta ya fad'a yana kuka yana kiran "Wayyo Abbana" Hafsa tun da ta ji abin da Safna ta ce hankalinta ya tashi, mikewa tsaye tayi ta nufi d'akinta da gudu tana kuka, Mama da Abba ne suka lallab'a Safna ta tashi da kyar tare da zaunar da Khalid d'in ta fita daga gidan, haka ta koma gidan zuciyarta babu dad'i, ba ta iya yin bacci ba, har gari ya waye yadda ta ga rana haka ta ga dare.


"Ruhina ina ka tafi, kasan ba zan tab'a iya rayuwa ba tare da kai ba, idan har ban ganka ba rayuwata zata lalace, dan Allah ka dawo gareni" Haka tai tayin sambatu abin ban tausayi, t.v da ke manne a falon wacce tun jiya da yamma wajen k'arfe uku da Safna ta kunnata tana kallon bbc hausa ba ta kashe ta ba, ta ji abin da ya saka ta tashin hankali, sanarwa ta ji anyi a kan jiya da yamma anyi hatsari a wajen club road kuma ta san tanan Ruhinta yake bi kullum idan zai dawo gida.


Anan fa aka shiga nuna gawarwakin mutanan da suka mutu hango motar Safwan tayi a gefen titin duk ta farfashe wata iriyar gigitatciyar k'ara ta kwalla tare da zubewa a k'asa sumammiya...................!😉💕


Hafsa ce ta shigo gidan a firgice saboda ita ma ta ga hatsarin da aka nuna a bbc hausa k'afafuwanta babu takalmi ko mayafi ba ta tsaya d'auka ba wata huta ce a kan ta, haka ta fito daga gidannasu tana gudu kamar wata mahaukaciya har ta iso gidan Safwan d'in.


Kai tsaye falon ta nufa tana gudu, tana shiga ta ga Safna ta baje a k'asa, ta nufeta tana girgizata tana kiran sunanta Amman shuru, wata dabara ce ta fad'o mata da sauri ta nufi fridge ta d'auko ruwa Mai sanyi ta shek'awa Safna, ai kuwa sai gashi ko second d'aya Safna ba ta yi ba, ta farfad'o tare da rushewa da wani irin kuka, rumgumeta Hafsa tayi sukai ta rara kuka.


Mama,Abba da Khalid ne suka danno cikin gidan daman gate d'in gidan a wangale yake domin kuwa, saboda dokar da Safwan ya sakawa mai gadin cewar idan lokacin dawowarsa yayi to ya dinga bud'e gate d'in dan baya son ya dawo gidan yayi tayin hon,shi kan shi mai gadi a gigice yake, tun da ya ji labarin hatsarin, a parking space sukai parking, kowanne daga cikinsu hankalinsa a tashe yake, sun fito kenan sun nufi hanyar da zata sadasu da falon gidan sai jin tsayawar mota suka yi a bayansu, ba su iya juyawa ba,sai ma cigaba da tafiya da suka yi sai jin muryar Alhaji Yahaya mahaifin Safwan yana kiran sunansa, da sauri suka tsaya tare da juyawa.


K'arasowa suka yi gurin da suke, babu wanda ya cewa d'an uwansa komai suka rankaya suka shiga cikin gidan, ganin yanayin da suka sami su Hafsa yayi matuk'ar ta yar musu da hankali, zama suka yi gaba d'ayansu "ya kamata ku daina kukan nan domin kuwa, ina tunanin Safwan bai mutu ba, dan an duba min gawarwakin mutanan ba'a ga gawar Safwan ba, amman ance min an kai wad'ansu asibiti wad'anda ake tunanin basu kai ga mutuwa ba, na sa Hafiz ya je asibitin domin ya duba ko har da Safwan" A zabure suka tashi jin Abin da Alhaji Yahaya ya ce Safna ta tsugunna a gabansa tana kuka "Dan Allah Abbu ka min rai ka taimaka min ka fad'a min asibitin, na je na duba da kai na ka taimaka min dan manzon Allah" Ta k'arada maganar tana fashewa da kuka mai tsima zuciya.


"Safna ki kwantar da hankalinki zuwan da nayi yanzu na zo ne domin, na kai ki asibitin kuma...............","Dan Allah Abbu ka tashi mu tafi to dan Allah dan Allah" Safna ta katse Abbu da maganar da yake shirin fad'a, tare da had'e hannayenta waje guda tana kuka sosai.


Hafsa ma magiya ta shiga yi masa, haka Abbu ya tashi Mama da Abba su ma suka tashi, Hafsa ce ta kama hannun Khalid suka fita Hafsa,Safna da Khalid motar Abbu suka shiga, Mama da Abba kuma suka shiga motar da suka zo, Asibitin da aka ce ankai wad'anda sukai hatsarin suka nufi, suna zuwa kowanne daga cikinsu ya fito, gaskiya asibitin yayi matuk'ar had'uwa sosai tun daga farfagiyar asibitin zaka san tsadaddan asibiti ne a wani k'aton signboard an rubuta *JODA SPEACIAL HOSPITAL*


Haka suka shiga cikin asibitin wata nurse ce ta nuna musu b'angaren da aka kai wad'anda sukai hatsarin, sukai mata godiya sannan suka nufi b'angaren suna shiga sai ga Hafiz yana shirin fitowa, da sauri Safna ta takumeshi tana tambayarsa "Ina ruhina?","Aunty Safna Yaya Safwan bai mutu ba, yana cikin wanchan d'akin likitoci suna kok'arin ceto rayuwarsa" Yayi maganar yana nuna d'akin da Safwan d'akin yake.


Cika Hafiz tayi ta nufi d'akin da ya nuna mata da gudu tana shirin tura kofar wasu nurse suka yi saurin tare ta, cikin zafin nama ta shiga kok'arin ture nurses d'in Mama wad'annan nurses d'in ne suka rirrik'eta nan ta shiga kok'arin kwacewa tana kuka tana cewa "ku barni ina ganshi dan Allah wallahi sau d'aya zan ganshi, in fito ba zan zauna ba, na rokeku ku barni in ga ruhina" Gaba d'aya 'yan gurin ta basu tausayi, Hafsa kuwa gefe ta koma ta rumgume Khalid tana kuka tabbas a yau ta fahimci son da Safna take yiwa d'an uwan nata ba, na wasa ba ne, duk da cewa ita tana ganin ta fita sonshi.


Da kyar aka samu aka fitar da Safna daga gurin domin kuwa likitocin asibitin ba sa son hayaniya saboda marasa lafiyan da suke b'angaren masu hatsarin, wajen asibitin Mama ta fito da Safna suka zauna a wasu kujeru tana rarrashinta da kalamai masu dad'i har Safna tayi shiru, a cikin awa d'aya 'yan uwa da abokanan arzik'i suka cika asibitin, suna yi musu jajan abin da ya faru da Safwan d'in har wajen k'arfe biyu sannan kowa ya fara watsewa, Khalid ne shi fito daga cikin asibitin da gudu ya nufo gurin da su Safna suke yana cewa "Mommy ki zo ki gani Abbana ya tashi ya min magana ma" Ai Safna ba ta jira Khalid ya k'arasa fad'ar maganar ba, ta nufi cikin asibitin da gudu Mama da Khalid suna biye da ita.


D'akin da Safwan d'in yake ta nufa, ta tarar dashi yana zaune ya jingina da k'arfen jikin gadon idanuwansa suna kallon kofar shigowar an nannad'e masa goshinsa da bandage ga k'afafuwansa duka biyun nannad'e da alama karaya ya samu a duka k'afafuwan nasa, kuka ta fashe dashi lokacin da ta k'arasa kusa dashi.


Hannunsa ya saka yana goge mata hawayen fuskarta yana murmushi "meya faru ne ruhina, ya kamata ki daina kukan nan haka, kin gani lafiyata k'alau babu abin da ya sameni","A'a ba gaskiya ba ne, gashi nan goshinka da k'afafuwanka nan sun samu karaya, zaka ce min ka na lafiya, ba gaskiya ba ne na shiga uku" Ta fad'a tana cigaba da kuka.


"baki shiga uku ba Safna, saboda ruhinki yana lafiya zan iya yin tafiya sosai tun da kina kusa da ni,ke ce k'afafuwana na san ba za ki bari in ji cewa na samu karaya ba".


Hafsa jin irin yadda Safwan d'in yake yi wa Safna ya ma manta da akwai wata Hafsan a d'akin ta nufi hanyar fita daga d'akin har ta bud'e kofar ta ji muryar Safwan kamar daga sama yana cewa "Ina zaki je kuma zuciyata? Dawo nan ina buk'atarki kusa da ni" Hafsa dawowa tayi ta zauna bakin gadon, Abbu,Abba da kuma Mama fita suka yi daga d'akin ganin Safwan d'in ya farfad'o hira sukai tayi abin ban sha'awa domin kuwa Safwan haka yake buk'ata ya had'a kansu tun kafin a d'aura musu aure da Hafsa.




*'BANGAREN JABIR DA TEEMARH😂🚴🏽‍♀️*


Fitowarta daga wanka kenan d'aure take da towel a k'irjinta wanda ko cinyarta bai k'arasa ba, Jabir ya turo kofar d'akin ya shigo yana rera wak'ar gwarzon mawak'insa Omale tsayawa yayi cak ya k'urawa Teemarh ido yana kallonta daga farko har k'arshe gaba d'aya ya ji wata iriyar muguwar sha'awarta lokaci d'aya rabon da ya kwanta da Teemarh tun ranar da bata da lafiya ya samu yayi mata ta k'arfi bai k'ara kusantarta ba.


Teemarh kuwa bata ko kalli inda yake ba ta nufi drower tana tafiya jikinta yana rawa sai kayi tunanin tana sane take yin rawa da jikin nata amman ko d'aya ita bata ma san tana yi ba, wata doguwar riga ta d'auko blue colour.


Juyowar nan da zata yi sai tayi ido biyu da Jabir ya k'ura mata ido haushi da takaici suka kamata "to kai kuma menene ka ke kallona kamar wani maye?" Murmushin su irin na cikakkun 'yan bariki yayi mata sannan ya ce "ina kallon kayan dad'i ne" Wata uwar harara tayi masa sannan ta ce "To ta Allah ba ta ka ba kuma nan gani nan bari sai dai kallo da ido, kara ma na saka kayana domin maye irinka sai ka saka min ciwon jiki". Wata iriyar mahaukaciyar dariya ya bushe da ita yana cewa "haba yarinya wallahi ba ki isa ba, yadda ki ka ta yar min da sha'awa wallahi yau sai kin biya min buk'atata","to sai mu gani, idan zaka min dole kuma wallahi Jabir ka kiyaye ni, baka isa ka min komai ba wallahi kwalelen kare da hantar kura" Tayi magana tare da kok'arin saka rigar, bata an kara ba ta ji ya fuzge riga yayi wurgi da ita, ya jawota jikinshi yana kok'arin cire mata towel d'in nan fa suka shiga kokawa tana kai masa duka da kok'arin kai masa cizo a kafad'a ya kama bakinta ya saka 'yanyatsunsa guda biyu ya matse bakin da k'arfi har sai da ta fasa k'ara, Allah ya taimaketa ta daddage ta kai wa k'irjinsa wani irin hauri da gwiwar hannunta yayi saurin cikata tare da dafe k'irjin, ta d'auki hijabin sallanta tana kok'arin sakawa ya fincike towel d'in tare da fizge hijabin yayi wurgi dashi ya rage babu komai a jikinta.


Jawota yayi cikin zafin nama ya kwatar da ita a kan gadon ya kama lips d'inta yana tsotsa hawaye ne suka shiga zuba daga cikin idonta, da kyar ta samu ya saki bakinta yana kok'arin saka bakinta a k'irjinta ta shiga bashi hak'uri "dan Allah Jabir ka yi hak'uri ka kyale ba na sallah fa","Ai ko zakka ne bakya yi yau sai kin san wa kika tab'a","dan Allah wallahi na yi maka alk'awarin komai ka ke so zan yi maka dan Allah ka bar ni" Tsaki ya ja tare da cewa sai "kuma ki yi" Haka ya shiga tsotsarta ta ko ina har sai da biya buk'atarsa duk da cewa Teemarh ba ta sallah.


(Chabb d'ijam amman Jabir ka cika dabba, ba ta sallan ma ba ka kyaleta ba😂🚴🏽‍♀️❤️)


Haka ya shiga wanka ya fito ya shirya cikin wasu shegun riga da wando wad'anda da su gwara babu, ya fita zuwa club domin jiya yayi sababbin kamu, ita kuwa Teemarh haka ta tashi ta shiga wanka ta dago ta d'auki doguwar rigar ta saka, ta koma kan gadon ta kwanta tana k'ara jin haushin Jabir d'in tare da tsine masa har bacci ya d'auketa.


*'BANGAREN GIDAN HAJIYA MAMA🔱🌸*


Kamar yadda su Khadijatullahi suka ce zasu je gurin Aunty Murja sun gama shiryawa sai Hafsa ta kirawo Shahida tana fad'a musu cewa Yaya Safwan yayi hatsari kuma tana tunanin mutuwa yayi, wannan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login