Showing 78001 words to 81000 words out of 83141 words

Chapter 27 - Daren Aurena Part 1 Complete Hausa Novel By Nana M Sha'aban .txt

10 Jan 2025

3096

Khadijatullahi dan har an kusa saka ranar aurensu, tarin takaddu ne a gabansa wad'anda ake jira ya saka hannu, amman ya kasa duba koda guda d'aya baren tana ya saka hannun.


Mik'ewa ya yi da sauri ya d'auki wayarsa tare da mukullin motarsa, ya fita daga office d'in bayan ya kulleshi motarsa ya shiga yana tuk'i amman gaba d'aya hankalinsa baya kan titin ya lula tunanin Khadijatullahi da kuma yaronsa Affan, Jabir bai yi aune ba sai ji yayi ya daki wata k'atuwar mota, wanda haka ya yi sanadiyar motarsa ta fad'a cikin wani babban rami ta kama da wuta gaba d'aya motar ta cinye, Innalillahi wa inna'ilaihiraju'un mutanan gurin suke ta faman fad'a koda suka lek'a ramin basu ga alamar akwai mutum ba, dan kuwa komai a cikin motar ya k'one kurmus, da yake wasu a gurin sun san motar Jabir nan aka samu wanda yake da number wayar Alhaji Mansur nan suke fad'a masa Jabir ya yi hatsari kuma gaba d'aya motar ta k'one kuma yana cikin motar, Alhaji Mansur ana fad'a masa haka ya zube a k'asa tare da rushewa da kuka, Aunty Murja ta k'araso tana tambayarsa menene, ya kwashe duk abin aka fad'a masa ya fad'a mata yana kuka "Shikenan yanzu yarona ya mutu, ina tsananin son Jabir kamar raina amman yanzu ya mutu ya bar ni" Aunty Murja gaba d'aya hankalinta ya tashi, haka dai tai-ta rarrashin Alhaji Mansur har ya yi shuru, nan ya d'auki wayarsa ya kira Aliyu, Aliyu wanda yake zaune a falon Hajiya Mama suna hira ya ji wayarsa ta d'auki ruri ya yi tunanin Jabir ne, amman da ya kalli screen d'in wayar ya ga number Abba, ya d'aga jin muryar Abba a chan k'asa k'asa yasa Aliyu ya saka wayar a speaker don ya ji abin da Abban zai ce masa "Aliyu kazo yanzu, Allah ya yi wa d'an uwanka rasuwa a hanyarsa ta dawowa gida ya yi hatsari motar gaba d'aya ta k'one kuma yana cikin motar" Mik'ewa Aliyu ya yi jikinsa na rawa hawaye suka shiga zubo masa, nan da nan gumi ya dinga keto masa ya jik'ashi shark'af "A'a Abba d'an uwana bai mutu ba, yana raye ba zan yarda ba wallahi ba zan yarda ba" Aliyu ya yi maganar tare da yin jifa da wayar, Shahida kuwa hannu ta d'ora akai tare da kurma wani uban ihu "Mun shiga uku yayanmu ya mutu, innalillahi wa'inna ilaihi raju'un" Aliyu kuwa fita ya yi da sauri ya shiga motarsa ya nufi gurin da Jabir d'in ya yi hatsari.


Ya na zuwa gurin nan ya nufi gurin rumin gadan-gadan, da yake akwai hanyar da ake bi a shiga cikin ramin Aliyu yana shiga ramin ya nufi gurin motar Jabir da ta k'one, yana kuka jikinsa ya yi sanyi domin ganin irin yadda motar ta k'one tabbas ya san ya rasa d'an uwansa dan gaba d'aya motar ta zama toka, nishin da ya ji a bayansa ne yasa ya juya da sauri, Aliyu ya mik'e ganin Jabir a kwance cikin jini rumgumeshi ya yi yana jin wani irin farin ciki yana shiga zuciyarsa, d'aukarsa ya yi cak suka fita daga cikin ramin a mota ya sakashi ya nufi asibitin Abbansu, suna isa asibitin Aliyu ya fito daga cikin motar, wasu nurses guda goma suka nufo shi suna tura gadon da ake d'aukar mara lafiya idan an kawoshi, Aliyu ya fito da Jabir ya d'ora shi a kan gadon, nurses d'in suka tura gadon Aliyu yana bin bayansu har aka shiga da Jabir emergency room, Sai a lokacin Aliyu ya dawo cikin hayyacinsa ya zaro 'yar k'aramar wayarsa ya kira Abba ya fad'a masa Jabir bai mutu ba yanzu ma suna asibiti dashi, sannan ya kira Shahida ita ma ya fad'a mata, ko minti goma ba'ayi ba sai ga su Hajiya Mama da Abba sun shigo cikin asibitin suka yo kan Aliyu suna tambayarsa "Ina Jabir d'in" Nan yake nuna musu d'akin da aka shiga da Jabir "Alhamdulillahi Allah mun gode maka, ya ubangiji ka tashi kafad'un wannan bawan na ka" Hajiya Mama ta yi maganar tana kuka, dukansu suka amsa da "Amin" Khadijatullahi ta ce "Yaya Aliyu ka tabbatar Jabir bai mutu ba" Ta yi maganar cikin yanayin damuwa "Eh Dija Mijinki bai mutu ba" Khadijatullahi ta kalli Aliyu cike da mamaki amman ba ta iya cewa komai ba, Teemarh ce ta rumgume Khadijatullahi tana kuka "Dan Allah Khadija ki taimakawa mijina ki yafe masa, ina da tabbacin sanadiyar tunaninki ne yasa ya yi hatsarin nan" Khadijatullahi gaba d'aya ta rud'e ta ma kasa magana, sai bin mutune da ta ke yi da ido, haka dai suka nemi guri kowa ya zauna, kowannansu ka kalli fuskarsa zaka ga tarin damuwa da tashin hankali mara misaltuwa.


*'BANGAREN LADO DA INNA LARAI💃🏽💞*


Durk'ushe yake a gaba mahaifiyar ta sa yana kuka yana neman gafararta "Dan Allah Innata ki yi hak'uri da duk abubuwan da nayi miki ki yafe min na san tabbas ban kyauta miki ba, na zalince ki ni ba d'a na gari ba ne" Inna Larai tayi murmushi ta ce "Bakomai Lado na yafe maka, abin da na shuka ne nake girbarsa" Lado ya ce "Nagode Innata Allah ya saka miki da alkhairi, ki tashi muje d'akina ni zan koma d'akinsu Lawal" Inna Larai ta mik'e Lado tana gaba Lado yana bin ta a baya, ta shiga d'akin Lado, kayansa ya shiga tattarawa yana kaiwa d'akinsu Lawal har ya gama ya zauna suka d'an yi hira da Innar ta sa, daga k'arshe ya yi mata sallama ya fita.


Yana fita su ka yi kicibus da Zaituna, kallonsa tayi cike da girmamawa tana sakar masa murmushi "Yaya dan Allah kayi hak'uri ka yafe min, ban yi maka rashin kunya dan"............. "Yi shuru Zaituna meyasa ki ke ba ni hak'uri, ai gaskiya kika fad'a min kuma nagode da kika dawo da ni hanya madaidaiciya, kuma insha Allahu zan gyara kuskuren da nayi a baya" Murmushi Zaituna tayi ta ce "Indai kayi hakan ni kuma na amince zan aureka, domin kuwa kasan Ina tsananin son Inna" Zaituna tayi maganar tana rufe fuskarta, Lado ya ji matuk'ar dad'in kalaman Zaituna wani farin ciki ya shiga tsarga masa, ita kuma Zaituna ganin kallon da Ladon ya ke yi mata yasa ta shige d'akin da Inna Larai take da gudu tana dariya, shima ya nufi d'akin su Lawal yana jin dad'i a cikin zuciyarsa.


*BAYAN KWANA BIYU✌🏽*


Aka saka ranar auren Zaituna da Lado wata d'aya farin ciki gurin wad'annan masoyan ba'a magana, nan suka shiga nunawa junansu wata iriyar sabuwar k'auna kamar su cinye junansu, kullum suna tare Lado yana zuba mara ruwan kalaman soyayya, ni kuwa er mutan zazzau nace Lado ya za ka yi mana haka Amatullahi fa😅Karka manta ita ce tsohuwar zuma🤣.


*BAYAN AWANNI GOMA SHA BIYAR🤧*


Da taimakon Allah Likitoci su ka yi nasarar, ceto rayuwar Jabir bayan gwagwarmayar da suka sha, kafin su yi nasarar ceto rayuwarsa dan gaba d'aya likitocin jikinsu ya yi sanyi ganin irin yadda jini yake zuba kamar famfo daga jikin Jabir, dakyar suka samu suka yi masa aiki har jinin ya tsaya, Doctor Isham ne ya fito daga d'akin yana gyara rigar jikinsa da sauri Alhaji Mansur ya taresa yana tambayarsa "Ya jikin Jabir" Murmushi Doctor Isham yayi ya ce "Alhamdullahi da taimakon ubangiji mun yi nasarar ceto rayuwar Jabir, yanzu dai mun yi masa allurai nan da awa d'aya zai iya farfad'owa" Kowannansu ya shiga furta "Alhamdulillahi" Doctor Isham ya nufi office d'insa, Nihal ce ta shigo asibitin da gudu tana kuka dan Shahida ta kirata ta fad'a mata Jabir ya yi hatsari "Abbanmu ina Yaya Jabir d'in yake" Abba ya ce "Ki kwantar da hankalinki yana nan lafiya" Shiga d'akin su ka yi gaba d'ayansu, zama su ka yi a kan kujerun dake d'akin suna kallon yadda Jabir d'in ya ji raunika a jikinsa, masu kuka nayi masu tagumi da jimami nayi.


Bayan awa d'aya Jabir ya fara motsi da 'yan yatsun hannunsa tare da kiran sunan Khadijatullahi, ras gaban Khadijatullahi ya yi mummunan bugu, duk da irin yadda ta tsani Jabir yanzu kam wani irin tausayinsa take ji saboda ganin irin yadda gaba d'aya kamanninsa suka chanza "Na'am" Ta amsa tana zubar da wasu zafafan hawaye, hannun Teemarh ta kama suka k'arasa gurin gadon zama su ka yi a kan gadon, Jabir a hankali ya bud'e idanuwansa ya dorasu a kan Teemarh "Zahra" Ya kira sunanta a hankali, duk da irin yadda Teemarh take cikin tashin hankali sai da tayi mamakin a ina Jabir yasan sunan da danginta ne kawai suke fad'a mata "Na'am" Cikin wata iriyar wahalalliyar murya ya ce "Ina Khadijatullahi?" Khadijatullahi ta ce "Gani nan" Ya juya a hankali dan Khadijatullahi ta zauna ta wajen kansa ita kuma Teemarh ta wajen k'afafuwansa, hannuwanta ya kama yana kok'arin fashewa da kuka "Dan Allah ki yafe min, nasan ban kyauta miki ba kuma"......... "Na yafe maka tuntuni Allah ya yafe mana ga baki d'aya" Khadijatullahi ta k'atseshi daga k'arasa maganar da zai yi "Nagode sosai, ina yarona?" Khadijatullahi ta karb'i Affan daga hannun Amatullahi ta ajiyeshi kusa da Jabir tana cewa "Gashi nan" Hannun Affan ya rik'e yana murmushi, gaba d'aya su Abba sun ji matuk'ar dad'in yadda Khadijatullahi tayi wa Jabir kuma sun san nan da 'yan lokaci kad'an burinsu zai cika, wasu kawar da k'iyayyar da Khadijatullahi ta ke yi wa Jabir.




Bayan sati uku aka sallami Jabir suka daga gidan Hajiya Mama dan ya ji sauk'i sosai, yana iya tashi da kansa kuma raunikan da ya ji sun fara warkewa, kullum yana tare da Teemarh da Khadijatullahi a gefensa dan bai yarda d'aya daga cikinsu tayi nesa dashi ba, Affan kuwa kullum yana mak'ale dashi, a yau aka saka ranar auren Khadijatullahi da Jabir da kuma Amatullahi da Aliyu wanda babu wanda ya san da haka gaba d'ayansu, Shahida ce ta fad'o falon da gudu tana tsalle, kallonta su ka yi gaba d'ayansu Aliyu wanda yake zaune yana chatting da abokinsa ya ce "Lafiya kuwa kodai duk a cikin gwaurancin ne" Dariya Jabir ya yi ya ce "Wallahi kuwa bro wannan yarinyar ai sai ana yi mata uzuri" Amatullahi da Khadijatullahi suka fashe da dariya "Kaiii sister ce fa, ita ma ta kusan shiga daga ciki Ammar zai yi wuff da ita" Khadijatullahi tayi maganar tana kallon Shahida wacce ta had'e ranta jin ance Ammar "Allah Aunty kina yi min wulak'anci sosai ni fa ba na son wannan mutumin" Teemarh ta ce "Kin ga kyalesu me ki ka zo fad'a mana na san wannan bakin na ki akwai news da yawa" Shahida ta ce "Yawwah Aunty Fatima shiyasa nake sonki da yawa, A yau ne ranar laraba da misalin k'arfe hud'u da rabi na rana aka saka ranar auren Amatullahi da Yaya Aliyu sannan kuma aka saka ranar auren Khadijatullahi da Yaya Jabir inda za'ayi bikin nan da sati d'aya" Amatullahi a firgice ta ce "Ke! Sister dan Allah ba na son irin wannan wasa ki daina" Shahida ta bud'e baki zatai magana suka ji muryar Nihal tana cewa "Sannan kuma aka saka ranar Aisha Mansur jik'amshi wacce aka fi sani da Shahida da kuma angonta Ammar Muhammad wanda za'ayi bikin rana d'aya da su Yaya Aliyu" Duk da irin yadda Khadijatullahi da Amatullahi suka shiga cikin firgici amman da suka ji abin da Nihal ta ce suka fashe da dariya "Wayyo cicina" Khadijatullahi tayi maganar tana kallon Shahida wacce ta shiga zubar da hawaye, Teemarh ma dariyar ta ke yi "Kai wannan sanarwar tayi min dad'i sosai" Ta yi maganar tana kallon Shahida.


"Nifa ba na son shi, wallahi ba zan au"........"Karki rantse Sister dukkanmu nan mun san bakya son shi, amman ya kamata ki yi hak'uri ki sani fa ai duk wanda yace yana sonka yafi wanda zai ce maka baya sonka Ammar yana sonki sosai to menene aibunsa da ke ba za ki so shi ba, me ya yi miki da kika d'auki tsanar duniya kika dora masa, ya kamata ki yi yak'i da shaid'anin da yake cikin zuciyarki yana kissa ki yi tsanar wanda bashi da wani aibu a rayuwarsa" Khadijatullahi tayi maganar tana kallon Shahida, Nihal ta ce "Dan Allah ki barta Aunty ai sai tai-tayi, tunda ita ma ta koyi wulak'anta mutane" Aliyi ya ce "Zo nan kinji k'anwata" Shahida ta k'arasa gurin da Aliyu yake ta zauna tana kuka "Yi shuru kin ji, karki yi kuka kan yi ya yi miki ciwo" Yayi maganar yana goge mata hawayen kan fuskarta "Yaya Aliyu ta ya zan iya zama dashi bayan ba na son shi" Aliyu ya ce "Shin Ammar akwai abin da ya tab'a yi miki ne? Ko kuma kun tab'a samum sab'ani dashi?" Ta girgiza kai alamar A'a "To meyasa bakya son shi" Shahida ta ce "Kawai Yaya Aliyu nima ban sani ba" Jabir ya ce "Kawai wulak'anci ne wallahi" Aliyu ya ce "Ina son ki yi min alk'awari guda d'aya" Shahida ta ce "Menene shi?","Ina son ki so Ammar kamar yadda yake sonki, idan kuma ki ka k'i to ba zan k'ara yi miki magana ba Yaya Jabir ma haka" Jabir ya ce "Ai ni tun yanzu babu ni babu ita, tunda wulak'anci take ji dashi" Shahida ta ce "Ku yi hak'uri zan aureshi" Aliyu ya ce "Yawwah ko ke fa" Daga nan suka d'an tab'a hirarsu abin sha'awa.


Shirye-shirye bikin ake yi dan sauran kwana d'aya a d'aura aure, bikin yazo dai-dai dana Hafsa dan haka aka ce za'a had'a party aka kama babban guri dan komai yazo musu da sauk'i, Teemarh ita ce uwar biki dan ita ce take shirya yadda take son bikin ya kasance dan har gurin da aka kama ita ta ce aje nan ayi partyn sai yafi, yau da misalin k'arfe hud'u za'ayi partyn Teemaeh ta shirya cikin wani material tayi kyau sosai yadda kasan ita ce amaryar, ta zauna a falon Hajiya Mama ta zabga tagumi komai take tunani oho, Jabir ne ya shigo falon ya tarar da ita zama ya yi kusa da ita yana kiran sunanta amman sam bata ma san yana yi ba, dan tayi nisa sosai wajen tunaninta, hannunta ya kama ya sauke mata tagumin da tayi da sauri ta kalleshi tana murmushi "Darling ashe kai ne, ka ba ni tsoro sosai" Jabir ya ce "Babyna na san dole zaki ji babu dad'i saboda zan yi aure, amman ki yi hak'uri kema ina sonki sosai wallahi" Teemarh tayi murmushi tare da cewa "Haka nace maka saboda za ka yi aure ne, na tsorata karka damu ka ji kawai ka cigaba da shirye-shiryen bikinka, Allah ya bamu zaman lafiya" Tayi maganar tare da mik'ewa ta fita daga falon, Jabir ya bita da kallon yana jin babu dad'i a zuciyarsa.


Wajen k'arfe hud'u aka kawo motoci sama da guda hamsin aka tafi gurin party, amaren gaba d'aya kowannansu kalar kayansa d'aya da angonta, sun yi kyau sosai Safna ita ma tazo bikin duk da cewa ba'a son ranta ta zo ba, Haka aka tashi daga party bayan anci an sha, suka koma gida kowannansu ya tafi d'akinsa dan ya yi bacci, Teemarh kuwa tun da ta shiga d'akin da aka bata take kuka wanda ni kai na ban san na menene ba, haka ta sha kukanta ta shiga toilet tayi alwala tayi sallah sannan ta koma kan gadonta ta kwanta a hankali bacci mai nauyi yayi awan gaba da ita.


Washe gari da misalin k'arfe sha d'aya na safe aka d'aura auren Khadijatullahi da Jabir, Amatullahi da Aliyu da Hafsa da Safwan da kuma Shahida da Ammar, Baban Amatullahi ya samu halattar d'aurin auren 'yar ta sa, inda bayan sun dawo daga gurin d'aurin auren ya saka aka kirata yayi mata nasiha mai ratsa zuciya, daga nan yayi sallama da ita ta koma cikin gidan, shagalin bikin ake yi ba ji ba gani har lokacin kai amarya yayi Jabir ya shigo gidan inda yayi ido biyu da Maminsa duk da cewar yana tsananin fushi da ita sai da ya sakin mata murmushi, ya k'arasa gurin da take ya gaisheta, ta amsa masa tana mai maidar masa da martanin murmushin na sa "Ina Teemarh tun jiya ban ganta ba?" Jabir ya yi maganar yana waige-waige ko zai ga giftawa Teemarh "Yanzu nan ta shiga d'aki za ta yi wanka" Hajiya Mama ta bashi amsarsa, Jabir dai bai ce komai ba dan ya fahimci Teemarh tana cikin damuwa kuma ta k'i bari su had'u tun jiya yake son suyi magana da ita fita Jabir ya yi jikinsa a sanyaye.


*7pm*


Motocin kai amarya suka cika layin, haka aka cika motocin gaba d'aya aka nufi gidan amaren, gidan Khadijatullahi suka fara zuwa inda Jabir yayi katafaren gini aka kai ta har cikin bedroom d'inta suka zaunar da ita a kan gado tare da yi mata nasiha, sannan aka fito aka nufi gidan Amatullahi komai iri d'aya ne da na gidan Khadijatullahi, ita ma sukayi mata nasiha sannan suka huce gidan Shahida shima babban gida ne sosai nasihar ita ma sukayi mata sannan suka koma gida, Jabir yana shiga gidansa yayi sallama kai tsaye 'bangaren Teemarh ya shiga amman abin mamakin a kulle ya tarar dashi, "To ina Teemarh ta ke? Kodai tana gidan Hajiya Mama?" Duk tambayoyin nan a fili yake yin sa, haka ya nufi 'bangaren Khadijatullahi jikinsa a sanyaye k'arasawa kan gadon da take ya yi inda ya yaye mayafin da ta lillib'e fuskarta dashi "Sweetheart" Ya kira sunanta yana murmushi, Khadijatullahi bata iya amsawa ba dan wata iriyar kunyarsa take ji haka dai suka raya wannan daren wajen nunawa junansu soyayya.


Hajiya Asiya ce zaune a d'akinta tana tunanin mijinta Innarta ce ta shigo bakinta d'auke da sallama "Assalamu alaikum" Hajiya Asiya ta amsa mata "Wa'alaikumussalam Inna barkanki da zuwa" Inna ta ce "Yawwah nagode sosai" Hira suka d'anyi sannan Inna ta fita ta koma d'akinta, Hajiya Asiya ta d'auki wayarta ta shiga kiran layin Labahani ringing d'aya biyu ya d'auka "Assalamu alaikum" Daga chan 'bangaren aka fad'a "Wa'alaikumussalam Labahani ya dai ka gano inda 'yar uwata take?" Labahani ya ce "Eh hajiya na dai gano inda yaranta suke amman ita ta dad'e da mutuwa, kuma na gano cewar 'yar uwarki

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login