Showing 30001 words to 33000 words out of 83141 words
Chapter 11 - Daren Aurena Part 1 Complete Hausa Novel By Nana M Sha'aban .txt
JABIR DA AMARYARSA*
Teemarh ce zaune a kan kujera tana kallon wani film d'in hausa episode mai suna *So k'addarar zuciya* Jabir ne ya shigo d'akin har ya nufi hanyar shiga toilet sai ya dawo ya d'auki remote d'in t.v ya chanza tasha ya kai wata tashar wacce kawai sex ake yi da sauri Teemarh ta rintse ido tare da yin saurin juyowa tana kallon Jabir cike da takaici tana cewa "Wai kai wane irin mahaukaci ne" Kallonta yayi yana wani lumshe ido yana murmushi "menai miki kuma?", "ban sani ba" ta bashi amsa jikinta sai rawa yake yi saboda ganin abin da ake yi a tashar yayi matuk'ar motsa mata da sha'awarta.
Jabir ya fara kok'arin jawo Teemarh jikinsa, ta tureshi da k'arfi Jabir nasan kayi haka ne domin ka tada min da sha'awa kuma wallahi ko zan mutu ba zan tab'a yarda na kwanta da kai ba har abada tayi maganar idanuwanta sun kad'a sun yi jajawur, Jabir wata iriyar mahaukaciyar dariya yayi sannan ya ce.
"My Teemarh kawai ki bada kai bari ya hau, kar ki tsaya yanga nasan kin fi ni buk'atar hakan". Yayi maganar yana kashe mata ido d'aya, Teemarh kuwa harara ta watsa masa da idanuwanta da suka kad'a suka yi jajir "Allah kiyaye wallahi sai dai in mutu, amman ba zan tab'a yarda na kwanta da kai ba, da na kwanta da kai kwanta na kwanta da kare domin kuwa shi kare yasan abin da yake yi kai kuwa ba, abin da ka sani sai dabbanci". tayi maganar cikin wata iriyar murya mai rauni, Jabir kuwa ya gama fusata wato har Teemarh ta isa ta ce masa wai gwanda ta kwanta da kare da ta kwanta dashi, ai kuwa yanzun nan zai koya mata hankali yadda gobe ba za ta sake fad'ar wata mummunar kalma a kan shi ba, hannunta ya kama da niyyar ya ja a amman Teemarh ta kama hannun ta gantsara masa cizo ya saki hannun yana yar far da hannun, ta fita daga d'akin da sauri har tana tuntub'e.
D'akin Shahida ta shiga jikinta sai rawa yake yi, Shahida tana kwance a kan gadonta wani irin mugun bacci ne yake kok'arin kwasheta, ta ji shigowar Teemarh da sauri ta tashi tana cewa "Aunty Fatima meyafaru? Ba ki da lafiya ne?" tayi maganar cike da tsantsar damuwa ganin yadda jikin Teemarh sai rawa yake "Shahida lafiyata 'kalau, ina son na shiga toilet d'inki" da sauri Shahida ta sauko daga kan gadon ta bud'e mata toilet d'in, Teemarh ta shiga sai da ta rage kayan jikinta sannan ta sakarwa kanta ruwan sanyi, a hankali ta fara samun nutsuwa, ta d'auki kusan rabin awa a cikin toilet d'in sannan ta mayar da kayan jikinta ta fito, in da ta sami Shahida a tsaye ta zabga tagumi, Teemarh tayi murmushi tare da dafata tana cewa "K'anwata lafiya kike kuwa?" Shahida ta ce "Aunty Fatima na ga kin shigo ne kamar ba'a cikin hayyacinki kike ba" Wani irin k'ayatatcen murmushi tayi tare da cewa "Haba kawai dai na d'an shiga cikin damuwana amman yanzu k'alau nake","To alhamdulillahi"Shahida ta fad'a tana murmushi, daga nan suka koma a kan kujera Teemarh ta cewa Shahida ta kunna mata tashar da ake So k'addarar zuciya domin ta cigaba da kallo, Shahida ta ce mata "to" sannan ta kai mata tashar ai kuwa tayi sa'a ba'a gama episode d'in ba dan haka suka zauna suna kallo.
*'BANGAREN AMATULLAHI*
Lado ne da Amatullahi zaune a kan taburma suna hirar su ta masoya, Amatullahi ta kalli Lado sannan ta ce "Baby wai kwana biyu na ga Innah tana d'aukar kajinka tana siyarwa,lafiya kuwa?" hankalin Lado yayi matuk'ar tashi domin kuwa haka Innah ta ce masa mutuwa kajin suke yi amman kuma yanzu Amatullahi ta ce siyarwa take yi, Amatullahi kuwa tana sa ne ta fad'a masa domin kuwa ta ji lokacin da Innar take ce masa kajin mutuwa suke yi, ita kuma ta k'uduri niyyar sai ta fad'a masa gaskiya domin ya san wacece uwarsa.
Lado ya kalli Amatullahi ita ma shi take kallo ya ce "wai da gaske kike sweety Inna siyar min da kaji take yi?" Amatullahi ta ce "wallahi baby da gaske nake siyar da kajin take yi, amman ai nayi tunanin da sanin ka take siyarwa" hawaye ne ya fara zuba daga cikin idonsa yana fad'ar "Yanzu duk irin yadda nake yi wa Inna biyayya kuma nake nuna mata tsantsar soyayya, ina mata duk abin da take so dan ta ji dad'i amman tayi min haka ta yaudare ni" Amatullahi ta kawar da kan ta gefe tare da tab'e baki, zuciyarta fal farin ciki "wannan so min tab'i ne ma, yanzu aka fara wasan" ta fad'a a zuciyarta.
Lado ya mik'e yayi waje zuciyarsa na k'una kamar garwashin wuta, ji yake kamar ya bi Inna gidan baffa Usmanu domin yau a chan ta wuni, "amman bakomai ai zata dawo ta same sa, dan kuwa ba zai yarda ba da wannan ha'incin ba" yayi maganar a zuciyarsa.
Amatullahi kuwa Lado yana fita ta bi bayanshi da kallo tare da tintsirewa da wata iriyar mahaukaciyar dariya, "Kad'an ma ku ka fara gani wallahi, sai kun biya abin da ku kai min" ta fad'a a fili daga nan ta tashi tayi d'akinta ta kwanta tana rera wak'a zuciyarta fal da murna.
*BAYAN SATI BIYU💥*
Sauri sauri gudu gudu take ta isa gidan Hajiya Mama saboda yau ba ta samu ta fito da wuri ba, saboda jikin Khadijatullahi da yayi tsanani, tana isa gidan ta shiga da sallama d'auke a bakinta "Assalamu alaikum" Hajiya Mama da Alhaji Mansur suna zaune a tsakar gidan a kan taburma suna hirar su ta uwa da 'ya abin gwanin ban sha'awa suka amsa mata sallamar gaba d'ayansu "Wa'alaikumussalam" Aunty Murja ta k'arasa ta gaisar da su "Ina kwana Hajiya" Hajiya Mama ta amsa da "Lafiya k'alau Murjanatu yau kin dad'e nayi tunanin ba za ki zo ba ma" Aunty Murja ta ce "Wallahi Hajiya yau Khadijatullahi ce jikin nata yayi tsanani sosai shiyasa amman yanzu ta ji sauk'i", "Allah sarki, Allah ya bata lafiya" Hajiya Mama ta fad'a "Amin" Aunty Murja ta ce sannan ta kalli gurin da Alhaji Mansur ya ke zaune suka had'a ido shima gaisar da shi tayi sannan ta tashi ta shiga share gidan gaba d'aya sannan ta koma kitchen ta d'ebo kwanukan wanke-wanke sai da ta wanke su gaba d'aya suka fita tas, ta kife su gaba daya sannan ta dawo ta d'ora girki, wani littafi ta gani a kan window ta d'auke shi *Hajna* ta ga an rubutu da babba baki.
Duba sunan marubuciyar tayi sai ta ga *Queen Nasmarh* wani irin farin ciki ne ya kamata domin kuwa tana neman littafin sosai, Hajiya Mama ta kalleta tana cewa "to sarkin karance-karance za'a fara kenan" sunkuyar da kanta Aunty Murja tayi sannan ta ajiye littafin ta shige d'akin Hajiya Mama, Alhaji Mansur ya bi ta da kallo yana sak'a abubuwa da yawa a cikin ransa.
*'BANGAREN SAFWAN*
Gaba d'aya Safna ta chanzawa Safwan ba ta yi masa girki ta daina kula dashi ta daina gyara gidan haka zata bar gidan kaca-kaca kamar babu mutane a cikinsa duk tana yin haka ne dan Safwan ya hak'ura da k'ara auran saboda ta san duk abubuwan da ta daina yi Safwan yana son su sosai musamman kulawa da tsafta domin Safwan mutum ne mai son kulawa kuma baya son k'azanta.
Shi kuwa Safwan ya nuna mata kamar bai san abin da take yi ba duk da kuwa abubuwan da take yi suna matuk'ar k'ona masa rai, amman ya k'uduri niyyar sai ya koya mata hankali kuma aure ne zai k'ara shi babu fashi da zarar ya shawo kan Hafsa ta sauko, tunda daman Safna ce silar rabuwarsa da Hafsan, domin ta samu ta auri Safwan shine ta had'a baki da wani domin su b'ata Hafsan a gurin Safwan, daga k'arshe kuma Safwan ya gano gaskiyar.
Zaune yake a d'akinsa yana kallon wani new a tashar *BBC Hausa* Safna ta banko kofar ta shigo tana huci kamar wata tsohuwar zakanya, Kallo d'aya Safwan yayi mata ya d'auke kansa ya cigaba da kallonsa, a kansa ta tsaya tana kiran sunansa "Safwan!Safwan!!Safwan da kai na ke magana fa" wani irin kallo yayi mata jin irin yadda take kiransa cike da gadara ji yake kamar ya tsinka mata mari amman kuma hakan ba halinsa ba ne dukan mace, "Safna ina matuk'ar hak'urin zama da ke, amman ina baki shawarar karki bari ki kai ni k'arshe domin kuwa komai zai iya faruwa", "Safwan ai baka nemi zaman lafiya ba tunda har ka na shirin auro wata shashasha, mai halin dabbobi, kuma..............." ai bata k'arasa ba sai ji tayi Safwan ya da ka mata wata iriyar tsawa wacce sai da ta jijita ta tayi baya da sauri jikinta har tsima yake yi.
"Safna ki tausasa harshen ki, ka da ki sake ki zagi Hafsa domin kuwa yanzu nan zan yi miki abin da baki yi tunani ba, domin Hafsa rayuwata ce kuma zuciyata". Safna ta fita daga d'akin da gudu tana kuka, kai tsaye d'akinta ta huce ta fad'a a kan gado, maganar Safwan tana k'ara dawo mata a zuciya *Domin Hafsa rayuwata ce kuma zuciyata* tana kuka take cewa "wallahi Safwan ba ka isa ba ko ka k'i ko ka so da ni kad'ai zaka rayu". A haka dai bacci b'arawo ya sace ta.
*'BANGAREN AMARYA NIHAL😂*
Kwance take a kan gadonta hawaye yana zuba daga cikin idanuwanta ita dai lamarin Salis yana bata tsoro kullum idan ya kusanceta kafin ya gama sai ta suma kusan uku ko biyu, kuma gashi baya kusantarta sau d'aya sai dai sau uku safe, rana da kuma dare ko da kuwa ace yana d'akin uwar gidansa sai ya zo gurinta.
Sallamar da aka yi ne ya dawo da ita daga dogon tunanin da ta shiga, a zabure ta mik'e jikinta ya fara rawa hawaye suka fara zuba daga idanuwanta "Dan Allah Yaya Salis yayi hak'uri wallahi ba na jin dad'i yau" murmushi yayi sannan ya ce "Menene na kuka babyna haba dan Allah ki daina kin ji" ba ta ce mata komai ba sai kukan da take yi, hawa kan gadon yayi sannan ta kai hannunsa wuyanta yana cewa "Me ke damunki zazzab'i ko kuma me?" Cikin rawam murya ta ce "Zazzab'i", "Wayyo Allah babyna sorry bari in d'auko miki magani ki sha, ko kuma tashi mu tafi asibiti" mik'ewa tayi da sauri ta d'auki mayafinta ta yafa, Salis ya tashi kenan sai suka ji a turo kofar da sauri Talatu ce tare da yaronta, fuskarta d'auke da fushi.
"Munafikin Allah ta'ala shi ne kace min kana zuwa yanzu zaka dawo ashe gurin wannan shafaffiyar ka zo, bayan kuma kasan yau ba'a d'akinta ka ke ba", murmushi yayi sannan ya ce "Talatu kenan, to ai gurin matata na zo dan haka ba wani abu mugun abu na aikata ba", harara Talatu ta shiga wurga musu ji take kamar ta shak'e Nihal domin wani irin haushinta take ji, domin tun da ya aureta Salis ya rage yin sex da ita, wani lokacin ma ba'a son ransa yake kusantarta ba wanda a da ba haka yake mata ba, amman ta san maganinta zasu had'u da ita tana nan tana tara ta, Salis ta kalla sannan ta ce masa "Ka zo mu tafi to" Nihal ta kallesa sannan ta ce "Yaya Salis ka je kawai na ji sauk'i zan sha magani" ta fad'a sannan ta koma ta zauna a kan gadon, Salis ya fita daga d'akin tare da Talatu, Nihal tayi saurin zuwa ta kulle kofar ta saka key ta sauke ajiyar zuciya, tare da godewa Allah.
Haka ta koma kan gadon farin ciki fal zuciyarta ji take kamar ta zuba ruwa a k'asa ta sha, yau dai ta huta da wannan jarababben namijin (ni kuwa nace nihal daga baya kenan wai anyi sadaka da karuwa🤣😂).
*'BANGAREN ABBA*
Tunda ya d'ora idanuwanshi a kan Aunty Murja ya ji gaba d'aya hankalinsa ya kwanta da yarinyar domin kuwa tana da saurin shiga ran mutane, yau kwana uku kenan amman kullum da tunaninta yake wuni a zuciyarsa, shiryawa yayi kyaf domin kuwa yau zai je ya fad'awa Hajiya Mama abin da ke cikin zuciyarsa ga me da Aunty Murja, motarsa ya shiga mai gadi ya bud'e masa gate d'in gidan ya fita daga gidan ya nufi gidan Hajiya Mama.
Alhaji Mansur yana isa gidan Hajiya Mama yayi parking d'in motarsa ya shiga gidan bakinsa d'auke da sallama "Assalamu alaikum" babu kowa a tsakar gidan dan haka ya nufi d'akin Hajiya Mama ya shiga d'akin da sallama Aunty Murja ya gani zaune tana karatun wani littafi mai suna *Magajin masarauta* wanda *Murjanatu bintu Al'amin ce ta rubutashi* da sauri ta d'ago kanta suka had'a ido da ita zuciyar Alhaji Mansur ta shiga bugawa da k'arfi gaba d'aya ya shagala da kallo Aunty Murja ita kuma ganin irin kallon da yake mata duk gaba d'aya ta rikice ta kasa amsa sallamar da yayi sunkuyar da kanta k'asa tayi tana wasa da littafin da yake hannunta, Hajiya Mama ce ta fito daga bedroom d'inta ta tsaya tana kallon irin yadda d'an nata yake kallon Aunty Murja yana murmushi ko kifta idanuwansa ba ya yi, wani irin murmushin su na manya tayi tare da godewa Allah daman tana son ace d'an nata ya ga Aunty Murja ya ce yana sonta, kuma daman tana son ta yi masa magana a kan ya aureta, domin kuwa ta san zai more da mata kuma 'ya'yansa zasu taso cikin tarbiyya.
Gyaran murya tayi Alhaji Mansur ya d'ago yana sosa kai tare da cewa "Hajiya ashe daman kina nan nayi tunanin ai bakya nan" harara ta watsa masa tare da cewa "To yau kuma da sabon salon da ka zo kenan, ka tab'a ganin ka zo gidan nan ba ka same ni ba" murmushi yayi tare da neman guri ya zauna yana cewa "A'a Hajiya ai nayi tunanin ko suna ki ka je", "A'a dambe na je ba suna ba" wannan maganar da Hajiya Mama ta yi ba k'aramar ba wa Aunty Murja dariya ta yi ba har ta kasa b'oye dariyar sai da ta yi ta a fili, Alhaji Mansur ya kalli yadda Aunty Murjan take dariya, ya k'ara jin ta shiga ransa domin ita kanta dariyar ta ta abin tsayawa a kalla ce "Murjanatu kema maganar Hajiya ta baki dariya kenan" ya fad'a yana kallonta, Aunty Murja ta yi mamaki domin jin Alhaji Mansur ya fad'i sunanta "to a ina yasan sunana?" ta fad'a a zuciyarta.
Alhaji Mansur ranar da ya fara ganin Aunty Murja, ya ji Hajiya Mama ta kira ta da Murjanatu shikenan shima ya rik'e sunan, Kallonsa Aunty Murja ta yi sannan ta ce "Eh".
Hajiya Mama ta samu guri ta zauna tana cewa "to ai sai kuyi ta dariyar, idan kun zare na kai ku dawanau" dariya Alhaji Mansur ya yi sannan ya ce "To mun dena Hajiya. yau fa zuwan nawa na musamman ne, na zo neman wani abu mai muhimmanci ne ban sani ba ko zan dace na same shi ya zama mallakina".
Hajiya Mama duk da cewa ta san inda zancen sa ya dosa, amman sai ta nuna masa ba ta gane ma yake nufi ba ta ce "Wane irin abu ne wannan mai muhimmanci?"
Ajiyar zuciya ya sauke sannan ya kalli gurin da Aunty Murja take zaune suka had'a ido a karo na biyu, gabanta ne ta ji ya fad'i gaba d'aya ta ji zuciyarta tana bugawa da sauri, tashi ta yi sannan ta ce "Hajiya bari inje tsakar gida na k'arasa tankad'en na san yanzu ruwan ya tafasa" Hajiya ta ce "to shikenan" fita tayi da sauri ta zauna a tsakar gidan tana tankad'en, Alhaji Mansur kuwa Aunty Murja tana fita ya juyo yana kallon Hajiya Mama yana cewa "Hajiya Mama kin san dai irin zaman da nake da Asiya, gaba d'aya ta lalata min tarbiyyar yara Shahida da Aliyu ne kad'ai suka fita zakka, kuma uwa uba Asiya sam bata k'aunar 'yan uwana,Hajiya Mama ina buk'atar na k'ara aure tunda dai ina da halin da zan iya rik'e mace sama da d'aya, kuma ina son na auri Murjanatu idan ba'ayi mata miji ba domin na yaba da halayenta"
Murmushi Hajiya Mama ta yi sannan ta ce "Alhamdulillahi daman ina da burin na ga ance yau kai ne zaka auri Murjanatu domin yarinyar tana da hankali sosai, kuma gaskiya ba na tunanin anyi mata miji saboda a yadda ta ba ni labari iyayensu sun mutu kuma ita kad'ai ce take kula da 'yan uwanta ita suke kallo a matsayin uwa kuma yayarsu" Alhaji Mansur ya ji matuk'ar dad'i ya ce "to yanzu Hajiya ya ya za'ai ina son nan da sati uku masu zuwa a d'aura auren saboda ba na son a ja wani dogon lokaci" Hajiya Mama ta ce "to ai sai ka bari muji ta bakinta ko?" Alhaji Mansur ya ce "Hakane kam Hajiya Mama" Hajiya Mama ta kira sunan Aunty Murja, ta amsa tare da ajiye tankad'en ta shigo d'akin har lokacin zuciyarta bata dena bugawa ba, zama ta yi a kujerar da ta tashi tare da sunkuyar da kanta tana cewa "Gani Hajiya" Hajiya Mama ta ce "Mansur ne ya zo min da wata magana wacce ta saka ni cikin tsananin farin ciki, da ina da dama da tun kafin ya rufe bakinsa zan basa abin da ya ke buk'ata amman ban da wannan damar shiyasa na ce bari in kirawo ki domin muji ta bakinki, Mansur yana so ya aureki kuma baya so a ja lokaci mai tsayi" Aunty Murja ta d'ago da sauri suka had'a ido da Alhaji Mansur wata iriyar kunya duk ta lillib'eta ta saka kanta a kan cinyarta tare da jan hijabinta ya rufe mata fuska, Hajiya da Alhaji Mansur murmushi kawai suka yi, Hajiya ta mik'e ta shiga bedroom domin ta basu guri su yi magana.
Alhaji Mansur ya ce "Murjanatu ki d'ago domin ki ba ni amsa, kina sona? kuma zaki aure ni?" bata d'ago ba domin gaba d'aya ji ta yi kamar ta nitse a gurin saboda kunya "Dan Allah ki d'ago ki ba ni amsa kinji ki cire kunya domin in san in da na dosa" d'agowa ta yi kanta