Showing 81001 words to 83141 words out of 83141 words
Chapter 28 - Daren Aurena Part 1 Complete Hausa Novel By Nana M Sha'aban .txt
'yar asalin wani k'auye ne kantum sanadiyar gobarar da garin yayi ne yasa suka tattaro suka gudo a hanyarsu ta guduwa daga garin aka kashe mata iyayenta gaba d'ayansu" hawaye ne suka shiga zubowa Hajiya Asiya ta ce "To ina zan sami yaran na ta?","Murja da Khadijatullahi gaba d'aya sunyi aure, ita Murja ta auri Alhaji Mansur jikamshi ita kuma Khadijatullahi ta auri d'ansa" Da sauri Hajiya Asiya ta mik'e daga zaunan da take jikinta na rawa tare da sakin wayar dai-dai lokacin Inna ta k'ara dawowa d'akin "Lafiya Asiya","Inna ashe Murja da Khadijatullahi yaran Hajara ne" Nan ta kwashe duk abin da Labahani ya ce mata ta fad'a mata Inna ta ji matuk'ar dad'i, Hajiya Asiya ta d'auki mayafinta ta fita Inna ta bita da kallo, Hajiya Asiya tana fita ta tari mai adaidaita ta shiga tayi masa kwatancen gidan Alhaji Mansur, suna isa ta fito ta biyasa kud'insa tare da nufar kofar gidan tana bubbuga gate d'in mai gadi ya bud'e mata ta shiga kai tsaye falon ta nufa ta shiga bakinta d'auke da sallama Abba da Aunty Murja suna falon suna kallo, Alhaji Mansur ya kalleta cike da mamakin meya kawota gidan nan kuma "Ku yi hak'uri na shigo muku gida babu izini, Murja gurinki na zo ya ya sunan mamanki?" Aunty Murja ta mik'e tsaye tare da cewa "Mamana kuma sunanta Hajara" Hajiya Asiya ta ce "Kenan da gaske ke 'yar Hajara ce k'anwata" Zaro ido Aunty Murja tayi shima Alhaji Mansur ya mik'e tsaye yana mamakin wannan lamarin "Hajara kuma?" Ya tambayeta cike da tsananin mamaki "Eh Hajara k'anwata da aka nemeta aka rasa" Aunty Murja ta ce "Mami kenan ke Yayar Mamana ce, kune 'yan uwanmu" Hajiya Asiya ta fad'a mata komai game da Mamarta da har zuwa guduwar da Hajaran tayi aka nemeta aka rasa, Kuka Aunty Murja ta fara yi inda Mami ta juya ta fita daga falon, Alhaji Mansur ya biyo bayanta anan ya tarar har ta fita daga gidan, motarsa ya shiga ya ja mai gadi ya bud'e masa gate ya fita adaidaitar da ya ga Hajiya Asiya ta shiga ya bi bayanta a dai-dai kofar gidansu ta sauka ta biya mai adaidaitar kud'insa ya ja ya bar unguwar tana shirin shiga gidan ta ji muryar Alhaji Mansur yana kiranta "Hasiya" Juyawa tayi da sauri tana kallonsa k'arasowa ya yi gurin da take suka kallon juna "Ki shiga ki je ki yi sallama da Inna ki zo mu tafi gida" Alhaji Mansur ya yi maganar yana kallonta "A'a ka bari kawai","ban gane na bari ba" Yayi maganar cike da b'acin rai "Ka yi hak'uri ban yi hakan dan na b'ata maka rai ba" Alhaji Mansur ya ce "Ki shiga ki fito ina jiranki" Ta amsa masa da "To" Anan ta shiga take fad'awa Inna yadda su ka yi da Alhaji Mansur d'in Innar tayi mata nasiha sannan ta fito murfin motar ya bud'e mata ta shiga ya bud'e ya ja motar ya nufi gidansa yana jin wani irin farin ciki a cikin zuciyarsa.
*'BANGAREN SAFNA😟🥰*
Duk da irin tsananin bak'in ciki da zafin kishin da take ji a kan Hafsa amman tunda ta shigo ta ga irin yadda take kula da Khalid da kuma yadda take girmamata yasa ta zubar da makaman kishinta, ta rumgumi Hafsa a matsayin 'yar uwa, komai na su tare su ke yi sun had'a kansu sosai suna kula da mijinsu yadda ya kamata, Safwan shi kansa hankalinsa ya kwanta sosai har wata 'yar k'iba yayi.
Teemarh ce zaune a kan gadonta ta zabga tagumi Jabir ya shigo d'akin ya k'ura mata ido, ya zauna a bakin gadon tare da hurgo mata tambaya "Yaushe kika dawo? Meyasa baki dawo jiya ba?" Teemarh ta ce "Jiyan na dawo" Ta bashi amsa tana kallonsa "Meyake damunki? Bana son ki yi min k'arya" Teemarh idanuwanta suka ciko da kwalla "Bakomai darling" Jabir cikin fushi ya ce "Ba za ki fad'a min ba" Teemarh ta ce "Ni ba zan haihu ba kenan" Tayi maganar hawaye na zuba daga idanuwanta, shuru Jabir ya yi yana kallonta wato kenan Teemarh saboda ba ta haihu ta shiga damuwa "Waya ce miki ba za ki haihu ba, zaki haihu mana ai kin san komai lokaci ne kema lokacinki yana nan zuwa","to Allah yasa" Jabir ya yi murmushi yana cewa "Ko kefa darling" Anan suka shiga yin hirarsu ta masoya har sai da Jabir ya tabbatar Teemarh ta fita daga cikin damuwar da take ciki.
*'BAYAN WATA HUD'U🤙🏾*
Gaba d'aya amaren suna zaune cikin farin ciki da kwanciyar hankali, Aunty Murja ta haifi 'yarta mace inda aka sha suna kamar ba gobe, dare ya yi kowa ya koma gidansa, a cikin watan kuma Amatullahi da Khadijatullahi suka shiga yin laulayi koda aka tabbatar musu da cewa suna da ciki Jabir ya yi murna amman da ya tuna irin damuwar da Teemarh take ciki akan rashin haihuwar da ba tayi ba, duk ya ji jikinsa ya yi sanyi ya san idan Teemarh ta ji Khadijatullahi tana da ciki to zata shiga damuwa fiye da wacce ta shiga a baya, amman ya san koda bai fad'a mata ba dole ta sani "Ya rahim" Ya fad'a tare da dafe kansa, haka dai ya shiga gidan nan Khadijatullahi ta huce 'bangarenta shi kuma ya huce gurin Teemarh yana shiga nan ya tarar da ita tana bacci ya k'arasa kusa da ita tare da shafa kanta yana murmushi, daga k'arshe ya fita ya koma gurin Khadijatullahi.
Bayan wata biyu yau ya kama za'ayi bikin 'yar Kawu Bala haka kowannansu suka ta ho gidan Hajiya Mama,Nihal, Amatullahi, Shahida,Khadijatullahi da kuma Hafsa da yake ita ma ta zo gida shine ta biyo gidan Hajiya Mama da yake ta san su Amatullahi zasu zo gidan gaba d'ayansu suna da ciki har ya fito ma, Teemarh tana zaune wacce ita kad'ai ce ba ta da cikin hankalinta ya tashi ta ware kanta a gefe tana tunanin ita ma ya za'ayi ta samu cikin? Amman ta rasa mafita Jabir da Aliyu ne suka shigo Idanuwan Jabir ya sauka akan Teemarh wacce ta ware kanta "Zahra" Ya kira sunanta d'agowa tayi da sauri tana kallonsa bata iya amsawa ba saboda kukan da ya taho mata "Ki zo falon bak'i ina son ganinki" Yana gama fad'ar haka ya fita daga falon, Teemarh ta mik'e ta bi bayansa tana shiga falon bak'in ta zauna a kan kujera "Darling nayi mamaki sosai, wannan abin da ki ke yi fa kamar kina jaa da hukuncin ubangiji bai kamata kina damun kanki ba, haihuwa Allah ne mai badawa kuma ina da tabbacin kema zaki samu ciki ki daina damun kanki dan manzon Allah darling" Teemarh hawaye suka fara bin kuncinta "Shikenan badamuwa" Abin da ta ce kenan tana goge hawayen fuskarta haka dai yai-yi ta rarrashinta har tayi fara walwala daga nan suka fito tare dashi a gurin Hajiya Mama ta zauna a tsakar gida Jabir ya bita da kallo ya girgiza kai kawai ya shiga falon, haka aka yi bikin aka gama kowannansu ya koma gidansa.
Khadijatullahi yau ne cikinta ya kai watan haihuwarta tun da safe Jabir ya kai ta Asibitin, inda anan suka tarar da Aliyu ya kawo Amatullahi har an shiga da ita labour room, ita ma Khadijatullahi ana shiga da Amatullahi ta fara labour nan ita ma aka an ta ya ta labour room, ni kam nace Amatullahi Allah ya sauke ku lafiya🥲.
Wajen awanni biyu Jabir da Aliyu suna jiran su ga nurse ta fita ta shaida musu matarsu ta haihu amman shuru, chan sai ga nurses guda biyu d'aya ta fito daga cikin d'akin da aka shiga da Amatullahi d'aya kuma daga cikin d'akin da aka shiga da Khadijatullahi kowannansu fuskarta d'auke da murmushi "Congrats matarka ta haihu ta samu d'a namiji" Nurse d'in farko take fad'awa Aliyu d'ayar kuma ta ce Khadijatullahi ta haifi 'ya mace haka suka shiga d'akin suna farin ciki aka sallamesu suka dawo gida, nan 'yan barka suka cika gidan har aka rasa in ma za'aje gidan Amatullahi ko Khadijatullahi, ranar suna kuwa gidan Hajiya Mama suka ta ho gaba d'ayansu aka yi sunan a chan yarinyar Khadijatullahi ta ci sunan Mami (Asiya) Inda suke ce mata Mummy, d'an Amatullahi kuwa aka saka masa sunan Alhaji Mansur suke ce masa Pappy, inda a ranar sunan da daddare Nihal da Shahida suka haihu farin ciki gurin ahalin nan ba'a magana ji suke kamar su zuba ruwa a k'asa su sha, haka su ma ranar suna aka sha suna a gidan Hajiya Mama, Teemarh tana kwance kusa da Hajiya Mama duk ta rasa meke yi mata dad'i yau ta tashi da tsanancin ciwon kai ga kuma amai da ta ke yi komai ta ci sai ta amayoshi, gaba d'aya ta fita a hayyacinta Hajiya Mama ta ce mata ta tashi su je asibiti ta ce A'a ba sai sun je ba ta ji sauk'i, haka ta barta babu yadda ta iya da ita, Jabir ne ya yi sallama ya shigo falon Aliyu yana biye dashi a baya "Yawwah d'an nan zo ga matarka nan sai fama take da amai da ciwon kai amman ta k'i yarda akai ta asibiti" Jabir ya k'arasa gurin da Teemarh ta e kwance ya ce "Zahra tashi muje asibiti kin ta b'a ganin mutun bashi da lafiya ya zauna a gida","Ni fa na warke fa, kan ya daina min ciwo" Aliyu cie da tsokana ya ce "A'a fa Aunty Fatima kodai d'a muka samu ne" Teemarh ta kalleshi kawai bata ce masa komai ba, dan kuwa ita ta ma fitar da rai da samun haihuwa "Kin ga ni ki tashi ko kin warke ko baki warke ba mu je asibiti, idan kuma kika dage a kan ba za ki je ba hmmm!" Ya yi maganar yana d'aure fuska, haka Teemarh ta mik'e dak'yar ta yafa mayafi ta fita daga falon kamar wacce aka bugawa iska😅.
Jabir ya bi bayanta suka shiga mota suna zuwa asibitin gwajin farko aka tabbatar musi da cewa Teemarh ciki gareta murna gurin Teemarh ba'a magana, ita ma ta samu ciki shikenan ita ma tana zata samu baby kamar dai su Shahida, haka suka dawo gida Khadijatullahi take tambayar Jabir meke damun Teemarh anan yake fad'a mata ciki ne da ita shine yake wujijjigata.
*BAYAN WATA BIYAR😤*
Cikin Teemarh ya girma sosai haihuwa ko yau ko gobe haka dai kullum tana jikin Jabir ta narke tana ta zuba masa shagwab'a iri-iri shi kuma yana biye mata anan yake tuna mata yadda ta shiga damuwa kafin ta samu ciki ta dinga yin dariya ta ce "Wallahi darling ba ka san yadda nake son na ga nima ina da baby ba ne shiyasa ka ke tsokanata" Jabir ya ce "Na sani mana tunda kin ta yar min da hankali lokacin, dan da ana siyan haihuwa da zan je na siyo miki ita na kawo miki dan hankalinki ya kwanta","Allah sarki darling ai yanzu komai ya huce" Cikinta ta ji yana murd'a mata mararta kuma ta d'aure da sauri ta rik'e Jabir tana cewa "Darling cikina" Da sauri ya mik'e ya samu ya taimaka mata suka shiga fita daga d'akin a mota ya sakata ya ja suka nufi asibiti, suna zuwa aka shiga da Teemarh labour room inda ko mintina hamsin ba ta yi ba ta haihu 'Yarta mace haka aka sallamesu suka dawo gida zuciyoyinsu cike da farin ciki, ranar suna anan gidan akayi suna anyi bidiri babu laifi an ci an sha, aka sakawa yarinya sunan Halima.
Lado da Zaituna su ma sunyi aure inda yanzu suna da d'a mai suna Ahmad, Hafsa ma ta haihu ita ma d'a namiji sunansa Sabir, inda Inna Larai ta auri wani mai wanki da guga a layinsu, Malam Shu'aibu ma ya yi aure a chan gurin aikin na su ya had'u da wata mai kawo musu abinci inda ya yaba da hankalinta yasa ya aureta, Haka rayuwar bayin Allah suka cigaba da gudana cikin farin ciki da kwanciyar hankali, kowannan burinsa ya ga ya kyautatawa d'an uwansa, Inda 'yan uwan Mahaifinsu Khadijatullahi wad'anda suka gudu suka dawo garesu tare da neman yafiyarsu, suka koma gidan su Khadijatullahi da suka tashi daman babu abin da gidan ya yi.
Zaune suke a falo suna hira Jabir ya kalli matan na sa da yaransa ya ce "A duk lokacin da na kalleku ina jin wani farin ciki a cikin zuciyata kuma ina godewa Allah, Alhamdulillahi ala kulli halin" Teemarh ta ce "Gaskiya kam darling dole ka godewa Allah" Khadijatullahi ta ce "Allah mun gode maka Alhamdulillahi😌"
Nima anan zance Alhamdullahi rabbil'alamin, anan na kawo k'arshen wannan littafin mai suna daren aurena Allah ubangiji ya sa mu amfana da abin da na fad'akar, kuskuren da nayi Allah ubangiji ya yafe min🥲😣👏🏽
Nasan a cikin ku zaku ce, to ya akayi Jabir ya auri Khadijatullah bayan saki uku yayi Mata? Amman karku manta fa a addinance idan mutum ya saki matarsa saki uku a lokaci d'aya to wannan sakin guda d'aya ne.
*'Yar mutan zazzau ce💃🏽💃🏽*