Showing 75001 words to 78000 words out of 83141 words
Chapter 26 - Daren Aurena Part 1 Complete Hausa Novel By Nana M Sha'aban .txt
shiga zubowa Amatullahi, ta mik'e tana goge hawayen na ta da gefen hijabinta "Ke Amatullahi dawo ki zauna" Aliyu ya yi maganar lokacin da Amatullahi take shirin fita daga falon, juyowa ta yi ta koma ta zauna dan ita sam ba ta ma kula da Aliyu yana falon ba, "Meya had'aku?" Ya yi maganar yana kallon Khadijatullahi wacce ita ma shi take kallo "Hmmm!" Abin da Khadijatullahi ta ce kenan "Yaya Aliyu ni ban tab'a yi mata k'arya ba, wallahi da gaske na ke yi maka" Amatullahi ta yi maganar tana kuka "Ai yau kuma kin yi min, kuma ni ba na mu'amala da mak'aryaci" Khadijatullhi ta yi maganar tana hararar Amatullahi, Aliyi ya ce "To ya isa haka, Amatullahi me ki ka yi mata?" Amatullahi ta ce "Ni Yaya Aliyu gurin Jabir na je" Wata iriyar zabura Khadijatullahi ta yi "Me ki ka je yi gurin wannan shegen d'an iskan" Nan Amatullahi ta bata labarin duk abin da take shirin yi wa Jabir d'in domin d'aukar mata fansa ta dora da cewa "Kuma duk zuwan da na ke yi sau d'aya na samu na fara isar masa da sakona, yau kuma da na je shine me shagon ya ke ce min ya daina zuwa club d'in saboda matarsa" Khadijatullahi ta matso kusa da Amatullahi ta rumgumeta tana kuka "Besty meyasa baki fad'a min ba, ki ka yi min shuru kin san wannan d'an iskan, kuma kin san halinsa, bai kamata kina saka kanki a tsari saboda ni ba, dan Allah ki daina saboda idan wani abu ya sameki ba zan tab'a iya yafewa kaina ba" Amatullahi ta d'agota tana goge mata hawayen fuskarta "Ki daina kuka ya isa haka, ka da kanki ya yi ciwo" Murmushi Khadijatullahi ta yi "To na dena dan Allah ki yi hak'uri da"..... Rufe mata baki Amatullahi ta yi "Dan Allah ki manta da komai ai ya wuce, bari na baku wajen ko kuna hirarku na katse ku, Yaya Aliyu a sha soyayya lafiya" Ta yi maganar tana dariya tare da fita daga falon.
_Masu son daren aurena daga farko zuwa inda aka tsaya ya yi min magana ta wannan number 08122188717_
"My Heartbeat wallahi kun burgeni sosai, tunda na ke ban tab'a ganin k'awaye irin ku ba, kuna son junanku kuna tsananin k'aunar junanku, Allah ubangiji ya bar ku tare" Aliyu ya yi maganar yana murmushi "Amin Yayana" Khadijatullahi ta yi maganar ita ma tana sakar masa murmushi, nan suka shiga yin hirarsu irin ta masoya sun kai kusan rabin awa suna hira daga nan su ka yi sallama, Aliyu ya tafi gidan abokinsa musaddik.
⏰5pm
K'arfe biyar na yamma dai-dai Teemarh ta isa gidan Hajiya Mama "Assalamu alaikum" Ta yi sallama tare da shiga cikin gidan, su ka yi ido biyu da Shahida "Laaa Aunty Fatima ke ce" Murmushi Teemarh ta yi tare da k'arasawa gurin da Hajiya Mama ta ke zaune ta tsugunna har k'asa tana gaisheta "Ina wuni Hajiya","Lafiya lau ina d'an duniyar mijin na ki?" Teemarh ta sunkuyar da kai tare da cewa " Yana gida" Tashi ta yi ta koma kusa da Shahida tana cewa "Hmm! Ai babu abin da za ki ce min" Dariya Shahida ta yi ta ce "Ki yi hak'uri Aunty Fatima akasi aka samu, kuma kin san gidan Hajiya Mama idan ka zo,to fa sai ka yi da gaske zaka iya fita" Teemarh ta ce "Gaskiya kam ga Aliyu ma ya k'i dawowa" Teemarh ta kalli su Khadijatullahi ta ce " Sannunku 'yan uwa ya ku ke" Murmushi su ka yi "Lafiya alhamdullahi" Suka amsa a tare "Wai Aunty Fati ina Yaya Jabir" Teemarh ta ce "Yana gida wallahi", "Wannan ita ce matar Jabir" Amatullahi ta yi tambayar tare da kafe Teemarh da ido, ita ma Teemarh jiyowa ta yi tana kallon Amatullahi tana murmushi, Shahida ta ce "Eh mana ita ce, sunanta Aunty Fatima" Amatullahi ta ce "Ohhh lallai kam, kin cika 'yar kasada" Ta yi maganar ciki-ciki, Teemarh ta ce "Sistoo magana ki ke yi ne?" Amatullahi ta yi murmushin yak'e tare da cewa "A'a fa, lazimi na ke yi" Khadijatullahi dariya ce ta kwace mata dan ta ji abin da Amatullahi ta ce, kuma ga maganar da ta fad'awa Teemarh "Tabbas Lazimi kike bestyna" Amatullahi ta kalleta tana murmushi "Bestyna abin k'aunata,me ya baki dariya kuma?" Khadijatullahi ta ce "No! Bakomai, kawai dai lazimin ki ne ya ba ni dariya, ya kamata ki nutsu sosai" Hararar wasa Amatullahi ta hurga mata, tare da d'auko wata hirar ta daban dan ta san indai ta biyewa Khadijatullahi to Teeamarh zata iya fahimtar inda zancensu ya nufa.
Har wajen k'arfe 10pm na dare Teemarh tana gidan Hajiya Mama, Hajiya Mama da ta ga ba ta da niyyar tafiya ta ce "Yau Fatima kwana za ki yi ne?" Teemarh wacce take kwance a kan doguwar kujera ta ce "A'a Hajiya yau zan tafi" Hajiya Mama ta ce "To ikon Allah yaushe za ki tafi kenan, kin san k'arfe nawa yanzu kuwa?" Dariya Teemarh ta yi ta ce "Hajiya Mama na sani mana k'arfe goma har da 'yan mintina, ai Yaya Jabir ne ya ce zai zo ya d'auke ni" Tana rufe bakinta sai ga Jabir ya yi sallama ya shigo falon "Assalamu alaikum" Karaf su ka yi ido biyu da Khadijatullahi, duk da irin yadda ta chanza masa, amman ba zan tab'a mantawa da wannan fuskar ba "Khadijatullahi" Ya kira sunanta a gigice gumi yana k'aryo masa, Yaron da ke kan cinyar Khadijatullahi ya k'urawa ido, shima Affan kallonsa yake yana dariyarsu irin ta yara, yana gwarancinsa don yanzu watan Affan biyar "Kenan wannan yaron nawa ne" Yayi maganar a zuciyarsa, Teemarh ta mik'e ta k'araso gurin da yake tsaya ta ce "Darling lafiya kuwa? Ka santa ne?" Bai kalli inda Teemarh take ba, dan har lokacin idanuwansa suna kan Khadijatullahi da Affan, Amatullahi ta ce "Fatima kina son jin irin rashin mutuncin da mijinki yayi wa 'yar uwata ne?" Da sauri Teemarh ta juya tana kallon Amatullahi ta ce "Meya faru ni na rasa gane kan wannan abin" Amatullahi tayi gajeren murmushi tare da cewa "To yanzu zan warware miki komai, wannan shaid'anin mijin na ki ya auri 'yar uwata, bayan ya gama biyan buk'atarsa da ita ya saketa a cikin daren nan, bai tausaya mata ba, kuma wannan yaron da yake kan cinyarta, d'an wannan shaid'anin mijin na ki ne" Teemarh ta zaro ido domin ta san Jabir ya tab'a yin aure, amman ba ta tab'a yin tunanin ta tambayesa ina matarsa ba, "kina nufin Dijah matar Jabir ce" Cikin muryar b'acin rai Khadijatullahi ta ce "Karki k'ara ce min matarsa domin ni, ba matarsa ba ce Allah ubangiji ya kiyayeni na auri wannan tak'adirin d'an iskan, wancan lokacin da na aureshi akan babu yadda na iya ne" Jabir dai bai iya yin koda motsi daga inda yake ba, barantana har ya iya magana, Hajiya Mama wacce take zaune ta zuba musu idanuwa tana kallonsu ta ce "Kai Jabir shigowa za ka yi ne, ko kuma tsayuwar za ka yi ta yi ne kamar wani gunki" Dakyar Jabir ya fara tafiya gaba d'aya jikinsa a sanyaye yake, Zama ya yi kan kujera nadamar abin da ya yi wa Khadijatullahi ta shiga zuciyarsa, wani irin zafi yake ji a cikin zuciyarsa wanda bai san dalilin jin sa ba, "Hajiya Mama Dan Allah"...... Hajiya Mama ta yi saurin dakatar dashi da cewa "Jabir yanzu dare ya yi ka d'auki matarka ku tafi gida, gobe idan Allah ya kaimu sai mu yi magana" Jabir bai musa mata ba ya amsa mata da "to" Sannan ya mik'e ya nufi hanyar fita daga d'akin, ya juyo ya kalli gurin da Khadijatullahi take, sannan ya fita daga falon, Teemarh ta d'auki Jakarta da mayafinta ta bi bayansa, ita ma jikinta a sanyaye ya ke.
Jabir yana zuwa wajen motar ya bud'e ya shiga, Teemarh ta shiga motar tare da kallonsa zuciyarta a cunkushe "Darling" Ta kira sunanshi muryarta a sanyaye, juyowa ya yi yana kallonta ba tare da ya ce komai ba, sai hawaye da yake zubowa daga cikin idanuwansa zuwa kan kuncinsa, hannunta ta saka tana goge masa hawayen tana yi masa murmushin yak'e "Ka daina kuka ka ji darling insha Allahu komai zai yi dai-dai" Jabir ya sauke ajiyar zuciya "Darling na san nayi wa Khadijatullahi abubuwan da basu dace ba, ban kyauta mata ba sam, idan har ba ta yake min ba tabbas ba zan tab'a yafewa kai na ba" Teemarh ta ce "Karka ce haka darling insha Allahu Dija zata yafe maka ka ji, yanzu tana cikin b'acin rai shiyasa,amman ka barta zuwa d'an wani lokaci kafin nan ta sauko" Murmushin jin dad'i ya yi tare da rumgume Teemarh "Nagode darling nagode sosai, da fatan zaki taimaka min wajen ganin Khadijatullahi ta yafe min","Insha Allahu" Teemarh tayi maganar tana murmushi, haka Jabir ya ja motar duk da cewar ba ya jin dad'in zuciyarsa, amman haka ya daure domin baya son ganin Teemarh cikin damuwa.
*'BANGAREN HAJIYA ASIYA*
Hajiya Asiya ta sha matuk'ar wahala a hannun Alhaji Mukhtar tun da ya samu abin da yake so daga gareta, ya ke nuna mata tsantsar tsana kullum cikin dukanta yake, gashi matarsa ma haka zatai mata rashin mutunci kuma ta sakata wankin kayanta dana yaranta, duk rashin mutuncin Hajiya Asiya sai da bakinta ya mutu, nadamar abin da tayi wa iyayenta da mijinta ta shiga zuciyarta, tunani ta shiga yi yadda zata samu ta rabu da auren Alhaji Mukhtar ta koma gurin mijinta ta nemi gafarsa kuma ta je gurin iyayenta duk da cewa ta san ba lallai su yafe mata ba, domin tayi masu rashin mutunci kala-kala, hawaye ne ya shiga zubo mata "Allah na tuba, Allah ya ubangiji ka yafe min kasa su Innata su yafe min, nasan na zalince su kuma abin da nayi musu ne yake bibiyata, tabbas hausawa sunyi gaskiya da suka ce abin da ka shuka shi zaka girba, yau gashi ina girban abin da na shuka" Ta k'arasa maganar tana kuka mai tab'a zuciya, ta d'auki kusan mintina talatin tana kukan nadamar abin da tayi daga k'arshe ta tashi ta shiga toilet, wanka tayi sannan ta dora alwala ta dawo falon ta shimfid'a dadduma tayi sallah raka'a biyu, ta dad'e tana rok'on Allah ya yafe mata, ta mik'e ta koma kan gado ta zabga tagumi.
"Ke Asiya! Asiya dan ubanki kina ina ne?" A firgice Hajiya Asiya ta mik'e jikinta na rawa ta nufi kofar zata bud'e kamar ance ta lek'a ta window anan ta ga Alhaji Mukhtar ta wata sandar shan jini, gabanta ne ya fad'i, ta ja da baya, idanuwanta ne suka sauka akan wata 'yar k'aramar kofa da zata iya sadata da gate d'in da zata fita daga gidan, da sauri ta nufi wata drower ta d'auko key d'in kofar ta k'arasa gurin kofar ta bud'e ta fara gudu, Allah ya taimaketa gate d'in gidan a bud'e yake, tana fita ta ga wani mai adaidaita zai huce, ta tsayar dashi ta shiga tare da cewa masa "Ka yi sauri ka bar nan dan Allah zai kasheni" Mai adaidaitan ya ja da gudu sunyi nisa sosai, ya juyo yake tambayarta "Hajiya ina muka nufa?" Anan tayi masa kwatancen inda zai kai ta, suna k'arasowa, ta fita tare da ce masa "Ina zuwa yanzu zan shiga gidan, mai gadi zai kawo maka kud'inka" Mai adaidaitan ya ce "To shikenan babu damuwa" Juyawar da za ta yi suka had'a ido da Alhaji Mansur yana tsaye a bakin motarsa, da sauri ta k'arasa gurinshi tana kuka "Dan Allah Abban Jabir"........ "Ya isa Asiya ki yi min shuru, ba na buk'atar sake ganinki a rayuwata, tunda ke butulu ce baki san darajar d'an adam ba" Durk'ushewa tayi akan guiyoyinta tana kuka "Duk abin da ka fad'a min na san na chanchanci fiye da haka ma, zaka iya kirana da abin da ya fi butulu ma, Amman dan girman Allah Abban Jabir koda ace zaka yanke alak'ar da take tsakaninmu, ina rok'onka ka yafe min, na san nayi maka butulci ban kyauta maka ba, ka yafe min dan Manzon Allah" Alhaji Mansur jikinsa ne ya yi sanyi sosai, dan shi a rayuwarsa baya so ya ga matarsa tana kuk saboda shi "To na ji, ta shi tsaye" Mik'ewa tayi tana jin jiriri yana kok'arin kayar da ita, muryar Alhaji Mansur ta ji yana tambayarta "Wanchan fa, meya tsaya yi" Ya yi maganar yana nuna man adaidaita "Shi ya kawoni, kud'insa zan biya sa" Ta basa amsa kanta a sunkuye.
Zuwa ya yi gurin da mai adaidaitan yake tsaye ya d'auko naira dubu biyar ya mik'a masa, nan fa ya shiga godiya ya ja adaidaitarsa ya yi gaba, shi kuma Alhaji Mansur ya dawo gurin da Hajiya Asiya take tsaya ya ce "Yanzu ai kin ga abin da son zuciyarki ya janyo miki, ni dai yanzu na yafe miki Allah ubangiji ya yafe mana gaba d'ayanmu" Godiya Hajiya Asiya ta shiga yi masa tana kuka, ya dakatar da ita da cewa "Ya isa haka, ni yanzu ina da gurin zuwa zaki iya yin tafiyarki" Hajiya Asiya ta ce "To zan tafi amman dan Allah ina neman wata alfarma a gurinka, ina so ka zo muje tare na nemi yafiyar su Innata dan na san indai na je ni kad'ai ba za su saurareni ba" Alhaji Mansur bai mu sa mata ba ya ce ta shiga mota su je, ta shiga gurin mai zaman banza ta rufe, shi kuma Alhaji Mansur ya ja motar ya nufi gidan su Asiya.
To fa k'ak'ak'ara k'ak'a shin iyayen Hajiya Asiya zasu ya fe mata kuwa, ku biyoni dan jin yadda labarin zai kasance💃🏽.
Suna isa gidan Hajiya Asiya ta ga gaba d'aya ya chanza mata ya koma irin na manyan masu kud'i ta san ko ba'a fad'a ba, Alhaji Mansur ne ya gyara gidan ya zama abin ban sha'awa, ta bud'e murfin motar ta fita amman me sai ta kasa motsawa daga gurin da take, wasu zafafan hawaye suna zubowa daga cikin idanuwanta yanzu da wane idon zata kalli iyayenata wanda rabon da ta saka su a idonta tun ranar aurenta da ta fita ta koma gidan k'awarta Aisha, Alhaji Mansur wanda har ya yi nisa ya juyo yana kallon Asiya, tabbas yasan tafi nadama amman ya kamata ya koya mata hankali sosai "Me ki ka tsaya yi anan? Kin kawo ni ne dan ki tsaya kina kuka" Tafiya ta fara yi inda Alhaji Mansur yayi gaba tana bin sa a baya, wani babban falo suka shiga inda nan take tayi ido biyu da iyayen nata, kuka ta saka tare da k'arasawa gabansu ta zube, magana take son yi amman ta kasa saboda irin kukan da ya ci k'arfinta, su kuwa Malam Kalla ido kawai suka zuba mata, "Dan Allah Inna da baffa ku yafe min abin da nayi muku, na san ban kyauta muku ba idan har baku yafe min ba, to tabbas haka rayuwata zata cigaba da tafiya cikin bak'in ciki da k'unci, ba zan tab'a ganin dai-dai ba, dan Allah ku yafe min na tuba" Alhaji Mansur ya ce "Baffa ku yi hak'uri ku yafewa Asiya tabbas tayi nadamar abin da tayi a baya, dan Allah ku yafe mata" Inna ta sauke ajiyar zuciya tare da cewa "Bakomai Mansur na yafe mata" Malam Kalla ya ce "Tabbas Asiya kin ci darajar Mansur yau da ke kad'ai ki ka zo gidan nan sai na b'alb'allaki, amman bakomai na yafe miki Allah ubangiji ya shiryeki" Nan Alhaji Mansur yayi musu godiya sannan ya mik'e tare da yi musu sallama, ya fita daga falon.
Inna ta cewa Hajiya Asiya "Tashi na nuna miki d'akinki","To" Tayi maganar tare da mik'ewa ta bi bayan Innar, suna shiga d'akin Hajiya Asiya ta ce "Innata ina 'yan uwana","Gaba d'ayansu sun yi aure, amman Hajara tun tafiyarki da 'yan kwanaki aka nemeta aka rasa har yau ba'a ganta ba" Zaro ido Hajiya Asiya tayi ta ce "Inna na shiga uku ina Hajara ta je?" Inna ta ce "Wallahi bamu sani ba, ni na rasa ma ya zan yi"Ta k'arasa maganar tare da fashewa da kuka "Kiyi hak'uri Innata ai na dawo zan je zan nemo duk inda 'yar uwata ta je, zan dawo da ita gida" Hajiya Asiya tayi maganar tare da rumgume Innar tana rarrashinta, har tayi shuru haka dai Innar tayi ta ba wa Asiya labarin irin neman da su ka yi wajen neman Hajara amman ba su sameta ba, kuma basu ji labarin komai a kanta ba "Ina tunanin wani ne ya bata labarinta, shiyasa ta gudu" Hajiya Asiya ta juyo cike da rashin fahimtar inda maganar Innar ta nufa "Inna ban gane ba, labarinta kuma, wane irin labari ne?" Inna ta gyara zama tare da cewa "Hajara ba 'yarmu ba ce tsintota Baffanku ya yi, mun b'oye muku ne saboda ba ma son ku nuna mata wani abu da zai sa ta fahimci ba iyayenku d'aya ba, musamman ke dan nasan indai kika san hakan za ki yi mata gori ne" Hawaye ne ya shiga zubowa Asiya "Innata insha Allah zan nemota, duk inda taje ai bai kamata tayi mana haka ba, ko da ace wani ne ya fad'a mata asalinta ya kamata,ta fad'a muku domin mu ta ya ta nemo iyayenta, bai kamata ta gudu ba" Haka dai Hajiya Asiya tayi ta kwantarwa da mahaifiyar hankali abin gwanin ban sha'awa, ni kam 'yar mutan zazzau nace Hajiya Asiya ko ke fa🤣.
*BAYAN WATA 'DAYA DA SATI BIYU🌼*
Jabir hankalinsa ya gama tashi ko bacci ba ya iya yi saboda tunanin Khadijatullahi, zuwansa gidan Hajiya Mama yafi sau ashirin dan ya samu ya ga Khadijatullahi ya nemi yafiyarta amman kullum yaje baya samun damar ganinta, zaune yake a cikin office d'insa kasancewa Abba ya bashi jagorancin ma'aikatarsa wacce ake yin shainkafa, ya zabga tagumi wayarsa ce ta shiga ruri ya kalli wayar wacce take ajiye a kan taburin office d'in *Bro Aliyu* shine ya bayyana a kan screen d'in wayar, Jabir cike da jin haushin Aliyu gami da wani a zababban kishi da ya taso masa, ya katse kiran Aliyun tare da sakashi a blacklist dan Shahida ta bashi labarin Aliyu ne yake son