Showing 1 words to 3000 words out of 109347 words
Chapter 1 - MEJO NAJEB Book 1 Complete Hausa Novels By Autar Alheri .txt
🪽🪽🪽🪽🪽🪽🪽🪽
🧜♀️🧜♀️🧜♀️🧜♀️🧜♀️🧜♀️
🪽🪽 *MEJO NAJEEB*🪽🪽
(Labari me sark'ak'iya, ban al'ajabi rikici zalunci soyayya cin Amana dakuma romantic 💗)
Daga alkalamin Autar alheri ✍️
MEJO NAJEEB PAID BOOK NE YANZU MUKE FREE BOOK 1 IDAN MUKA SHIGO BOOK 2 SHINE ZAKI BIYA KARKI KARANTAMUN ABUNA BATAREDA KINBIYANI HAKKINABA MUDDIN KIKA FITARMUN DA BOOK KO KIKAKARANTA BATAREDA KINBIYANIBA KEDA ALLAH.
Please idan bakida Aure ko kinkusa aureba karki karanta please ba iskanci bane aciki Amma akwai love sosai da rayuwar ma'aurata. Ina fatar za'akiyaye🙏
Wannan book yazone dawani sabon kabce me ban mamaki Amma fa sekagani zaka tabbatar sabida gani yakoriji.
Bismillahirahmanirahim
Book 1
Page 1 & 2
"Tafiya sukeyi cikin nutsuwa acikin wani Dan jeji daga dukkan alamu Rafi suka nufa konace gulbi inkagansu kamar wasu tagwaye Amma kallo Daya zakamusu kasan cewar batagwaye bane sedai k'awayene na Amana, Sund'anyi tafiya menisa kamun d'ayar tad'ago tana fad'ar Isseta Allah nagaji wai haryanzu bamukaiba Allah nafara gajiya nidai ko mukoma gida kawai na hak'ura da ganin maman taki.....ahankali wadda akakirada Isseta tad'ago da Dara daran idanuwanta tazubawa k'awar tata kana tabude Baki cikin wani Dan iskan sexy voice me masifar ratsa jiki tace "ayya yi hak'uri halima ai munkusa k'arasawa kecefa kikace nagaya mata zakizo kiganta yanzu idan bamuje tareba bazataji dad'iba. Takarasa zancen tana matse hannun halima sosai. Da kallo nabisu dukkansu Jin yadda Isseta ke maganar hausarta Bata bita da kyau sosai dajin yadda bakinta yake baseka tambayaba kasan bafulatanace ta'asali, shiyasa nake kallonsu. Ayadda idona sukayi tozalida Isseta seda nayi jinjinaga uban gijin talikai Daya halicci wannan kyakkyawar budurwar me cikar haiba da Kamala cikakkiyar mace Ako Ina son kowa kin wanda yarasa komai yaji ajikin Isseta abun ba'amagana babban abunda yafi birgeni atareda ita shine Dara daran idanuwanta dakuma sexy voice d'inda Allah yabata domin bawai namijiba macema idan taji voice d'inta se yabirgeta....tobawai Isseta ba halima ma ba'abaya takeba wurin kyau da d'aukar hankali abundai sewanda yagani mekaratu ka misilta kyawun way'annan y'anmatan dakanka musamman Isseta domin duk yadda zanmisilta bezama lallai kufahimtaba asalima semucinye page d'in bamu k'areba.......sunyi tafiya menisa kamun suzo bakin wani gab'ar ruwa masu yawan gaske daga dukkan alamu yankin wani tekune acikin rugar tasu idan anshigo wannan jejin.
Tsayawa sukayi awurin halima na karewa ruwan kallo cikin tsoron ganin yawansu yayinda Isseta keta famar doka murmushinda yak'ara fitoda asalin kyauta na fulanin asali.....tsayuwa Isseta tagyara kamun tabud'e Baki cikin sweet voice d'inta tace maaaahhhh. Tafad'a dakarfi yadda duk seda wurin ya amsa, atakeko ruwannan suka d'auki rugugi suna torok'o ijiyar ruwan nayi sama tana dawowa alamar wani abun nason bayyana acikinsu.....arazane halima tarik'e hannun k'awar tata tana fad'ar nashiga ukku Isseta minene kikayi Hakan ? Miyasa wannan ruwan keyin Hakan dubafa kigani tafad'a duk a tsorace...kamun Isseta tabud'e Baki Tayi maga sekawai gawani katon jelar kifi Irin shape dinnan me had'iye mutane Tayo Saman ruwan kamun suyi wani k'wak'k'waran motsi sekawai ga mamallakin jelar ta bayyana wato hajo ruwa Rabi mutin Rabi kifi(🧜♀️) wani Irin waro Ido halima Tayi tana Munata da yatsa tanaja dabaya Tama kasayin magana gabaki d'aya jikinta ko a'ina rawa yakeyi kamar mazari, cikin wani Irin tsoro da rud'ani take fad'ar innalillahi Isseta munshiga ukku haj...kafin tak'arasa Isseta Tayi saurin rufe mata Baki tana girgiza mata kanta cikin damuwar ganin k'awar tata atsorace tace "Dan Allah halima kinutsu wannan fa mamata ce bawai wadda kike tinaniba Kuma babu abunda zata mana hasalima idan Taga wanda zecutamana bazata bariba Dan Allah kinutsu.
Se yanzu halima tadanji sanyi aranta Jin kalaman k'awar tata ahankali tad'an sassauta rik'on datayiwa Isseta d'in Amma Bata saketa dukaba.......itako wannan kifanyar kallonsu kawai takeyi fuskarta d'aukeda kyakkyawan murmushi gata kamanninta yafito Sak balarabiya.
Ahankali tabud'e Baki tace *MARYAMA* Baki bawa k'awarki labarin mamarki ba bil'adama bace ne? Aidakinga gaya mata bazata tsorataba....murmushi Isseta Tayi ahankali tace "bangaya mataba maahh nasha'afane wlh inata d'aukin zuwa ganinki yau kwana biyufa bangankiba. Tafad'a tana turo Dan k'aramun bakinta gaba.
"Ikon Allah kwana biyu shine abun rigimar maryama? "To ai yayi yawane maah... murmushi maah tak'arayi kana tace shikenan naji yanzu ya kuke keda aminiyarki yakuma gidan naku dasauk'iko? Ta tambayeta cikin kulawa kamar batasan abunda ke faruwaba....ajiyar zuciya Isseta tasauke kana tace "babu sauki maah komai nanan yadda yake Sema abunda yak'aru Allah nafara gajiya da wannan rayuwar maah...tak'arasa fad'a idonta na cikowa da k'wallah.
"Humm kiyi hakuri maryama komai nada lokacinshi Ina gaya Miki akwai ranar da za'ayi walk'iya agidanku ranarda kwaizefashe me masifar wari ranarda Zaki banbace tsakanin Dede da ba dedeba abunda zan gayamiki ayanzu shinedai wanda nasaba gaya Miki shine kiyi hakuri Kuma ban yadda kiyiwa kowa rashin kunyaba agidanku kinjiko Amma bance kibari atakakiba.
Nisawa Isseta Tayi kana tace to maah kid'auki mataki akansu mana...Humm maryama kenan zan d'auka Amma kamar yadda nake gaya Miki komai nada lokacinshi kijira lokaci Yana zuwa dazan dauki matakin kinji y'ar albarka.....to shikenan maah. Tafad'a tana murmushi...itama wannan kifanyar murmushi Tayi ganin Isseta tasaki ranta kana takarabo tamannawa Isseta kiss agoshi Kuma tayiwa halima datayi mutuwar tsaye ganin Rabi mutin Rabi kifi na magana agabanta. Amma wannan kiss da maah tayimata yadawo da ita duniyarmu...sedai ta makara domin lokacinda tadawo hayyacinta tuni maah ta nutsa cikin ruwa har sund'auki rugugi kamar yadda sukayi daga farko. Hakan yasa tak'ara k'ank'ame Isseta sosai domin ita kam haryanzu a tsorace take......wannan ruwan kuwa suna gama rugugi suka koma normal yadda suke kamar babu wani abunda yafaru yanzu acikinsu. Rik'on hannun halima Isseta Tayi sukanufi gun wani dutse inda suka samu kud'i masu yawa awurin duk'awa Isseta Tayi tad'auka domin tasan maahh d'inta ce ta ajiye mata kamar yadda tasaba....itako halima da kallo kawai takebin Isseta Amma takasa cemata komai ahakan suka dauko hanyar komawa gida.
Lagos
Acikin katafariyar unguwarnan wato Banana island wani mahaukacin gidane me d'aukeda tangamemen gate wasu Dalla dallan motoci suka nufo cikin azababben gudu kamar zasu tashi sama suna zuwa kofar gate d'in ya wangale kanshi suka kutsa hancin motocin aciki....wuri suka samu a perking space d'in da'akaware domin ajiye motocin, seda suka gama dedeta tsayuwarsu kana sojojin dake ciki suka shiga dirowa ahanzarce suna nufar d'aya motar tareda kamewa wuri daya akusan motar alamar girmamawa ga wanda keciki. Wanda yayi nak'arsheda fitowone yazo cikin hanzari yabude bayan motar tareda sarama wanda keciki...Amma abun mamaki ko motsi wanda kecikin motar beyiba kamarma bakowa acikinta, kusan minti 20 suna ahakan sa'annan yazuro kafarshi fara sol med'aukeda Zara Zaran yatsu awaje Yana sanye da takalmi plate black color wanda sukayi mishi kyau sosai. Kusan minti 3 kamun yak'ara zuroda d'ayan sa'annan yafito gaba dayanshi. "Wow masha Allah 😱watafarakallah bi'ahasanilkhaliqeen, shine abunda yafito daga bakina domin wannan bawan Allah yacika kyakkyawan mutin duk inda kyakkyawa zeje to yazarta Hakan. Farineshi sol med'aukeda blue eyes manyan gaske masu matuk'ar kyau da d'aukar hankali, yanada hanci sosai masha Allah ga yada wani kaya taccen saje wanda yayiwa kyakkyawar fuskarshi k'anwanya yazo har zagayen Dan k'aramun bakinshi med'aukeda rite lips se makarkata sukeyi daga ganin yanayinshi base katambayaba kasan akwai abunda ke damunshi domin kallo d'aya zaka mishi kasan bashida lpy. Yana sanyi cikin kakinshi na sojoji wanda yayi masifar yimishi kyau kamar Dan fatarshi akayisu......cikin sassarfa yanufi cikin karafaren general parlor gidan batareda yabitakan yaranshiba daketa famar yimishi sannu.....captain Jameel ne kawai yabi bayanshi d'aukeda laptop dinshi da wayoyinshi.
Shiko Yana shiga perlor ya haura sama inda pert dinshi yake.....wasu manyan mata dake zaune a perlor wanda zasukai kimanin shekaru 45 suka bishida kallo cikin mamakin wannan shigowar tashi....kamun suyi wani yunkurinne captain Jameel yashigo Yana gaidasu cikin girmamawa....ba wadda ta amsa Sema d'ayar dake fad'ar "Jameel lpy kuwa naga son yashigo ahakan kodai bashida lpy ne? "Cikin nutsuwa captain Jameel yace "wlh bashida Hajiya umma inagama dakyar ba cinwonshine kesan tashiba Kuma ba yadda bamuso muwuce dashi hospital ba Amma yak'i. "Innalillahi wa'innailaihi raji'un tafad'a agigice tana mik'ewa tsaye tareda haurawa Saman benen....itako dakyar Baki kawai tatab'e kana tace Allah yabashi lpy. "Ameen mama cewar captain Jameel Shima Yanabin bayan Hajiya Umma....da kallo mama tabisu tana yamutsa fuska kafin tamik'e ahankali tanufi bedroom d'inta....!
Autar alheri ✍️
🪽🪽🪽🪽🪽🪽🪽🪽🪽
🧜♀️🧜♀️🧜♀️🧜♀️🧜♀️🧜♀️
🪽🪽 *MEJO NAJEEB*🪽🪽
(Lbari me sark'ak'iya ban al'ajabi rikici zalunci soyayya cin Amana dakuma romantic 💗)
Daga alkalamin Autar alheri ✍️
MEJO NAJEEB PAID BOOK NE YANZU MUKE FREE BOOK 1 IDAN MUKA SHIGO BOOK 2 SHINE ZAKI BIYA KARKI KARANTAMUN ABUNA BATAREDA KINBIYANI HAKKINABA MUDDIN KIKA FITARMUN DA BOOK KO KIKAKARANTA BATAREDA KINBIYANI HAKKINABA KEDA ALLAH.
Book 1
Page 3 & 4
"Captain Jameel kuwa abakin kobar bedroom d'in wannan matashin yasameta sefamar nocking takeyi Amma fir yak'i bud'ewa cikin alhini takalli captain Jameel idonta dahar suncikoda k'wallah tace "yak'i yabud'e Jameel bansan miyake damun *NAJEEB* ba sam bayasan zuwa asibiti aduba lafiyarshi Kuma yasan yadda ciwonnan yake masa narasa yazanyi dashi Jameel banasan wani abun yasamu yarona tak'arasa zancen tana sakin marayan kuka.....cikin damuwar da takasa boyuwa afuskar captain Jameel yace kiyi hakuri Hajiya Umma insha Allah y'allab'ai zesamu lpy addu'arki yake bukata ayanzu ba kukankiba..
Suna cikin wannan tsayuwar ne baba inno tashigo parlor nashi wato me aikin Hajiya Umma. Gaidasu Tayi cikin girmamawa kana tace Hajiya kizo inji alhaji Yana part dinshi yadawo....to ganin tafad'a tareda kallon captain Jameel tace "please Jameel D'an Allah kak'ok'arta koza'asamu yabud'e bedroom d'innan. "To Hajiya Umma insha Allah....juyawa Tayi tanufi part d'in alhaji yayinda captain Jameel ya ajiye kayan ogan nashi akan dining table kana yad'auko wayarshi yashiga Kiran doctor ziyad abokin NAJEEB d'in.
Acan cikin bedroom d'in kuwa Yana shiga ya core kayan jikinshi yafad'a bathroom domin jiyakeyi kamar ana yankan Naman jikinshi ana zuba mishi wuta Sam yakasa samun nutsuwa se gumi ke tsafo mishi tako'ina ajikinshi...wanka yayi cikin azabar dayakeji wadda shikadai yasan halinda yake cikin kamun yafito daureda towel a k'ugunshi yazube akan bed d'in Yana mayarda numfashi gabaki d'aya jiyakeyi kamar ranshi zefita cikin mayuwacin hali yake juyi akan makeken gadon nashi Sam yarasa mike mishi Dad'i gabaki d'aya duniyar tajuya mishi baya idan wannan ciwon nashi yatashi jiyakeyi kamarma ba'ahaifeshi awannan duniyar ba domin komai da kowa b'ace mishi yakeyi baya Gane kanshima balle wani abun, addu'a ma baya iyayi domin besan ta'ina ze faraba....shiyasa be bud'ewa Hajiya Umma dakinba dudda Yana jinta Amma Sam baze iya tashiba.
Acan part d'in alhaji kuwa wanda yaranshi ke kirada Abba Hajiya Umma ce zaune agefenshi tana yanka mishi kayan fruit d'inda tad'auko mishi seda tagama yankawa tsab kana ta'ajiye mishi agabanshi. Murmushi yayi kamun yad'auka kana yace ngd sosai y'ar albarka. Itama murmushin tamaida mishi kamun tabud'e Baki cikin damuwa tace "alhaji son nefa yadawo gida ba lpy Kuma ga dukkan alamu cinwonshine yatashi Amma yarufe kanshi a d'aki Kuma nayi nayi yak'i yabud'e please kayi wani abun akai.....tinda Hajiya Umma tafara magana idon alhaji sahabi nakanta hartakai karshe...apple yasaka abakinshi kana yace "Allah yabashi lpy, yafad'a cikin ko in kula...marairaice fuska Hajiya Umma Tayi tace Ameen alhaji Amma please kayi wani abun karfa Azo wani abun Kuma yasameshi bazeyu mubarshi ahakanba, Dan Allah....katseta alhaji sahabi yayi batareda yabari ta k'arasa fad'ar abunda takesan fad'a ba cikin had'e fuska yace "Kinga Jamila banasan damuwafa idan damuna kikazoyi to kikoma bedroom d'in nashi can ku k'arata haba kinzo kinwani dameni shidin yarone k'arami dabaze iya nemawa kanshi maganiba se anwani kama lallab'ashi? Banasan shirme wlh aikin banza Kawai.
Shiru Hajiya Umma Tayi kamun tashare k'wallar idonta tana fad'ar Allah yahuci zuciyarka tak'arasa zancen tana me zuba mishi furardata dauko a glass cup.
Gombe
Tin ahanya suka rabu itada k'awarta halima domin bayadda batayida halima ba akan takarbi kudin da mamanta ta ajiye musu Amma halima taki acewarta tafita bukatarsu sabida Hakan bazata karb'aba, wannan dalilinne yasaka Isseta yin fishi tatafi abunta...tin abakin kofar shiga soron gidan take jiyo hayaniyar mutanen gidan nasu kamar zasuci kasuwa, cikin d'ar,d'ar tanufi cikin gidan gabanta na fad'uwa....gabaki d'aya a tsakar gidan tasamesu tsai'tsaye kowana fad'ar albarkacin bakinshi yayinda mamansu Yah balah se masifa takeyi tana mita kamar zataci babu, tana hango shigowata agidan Tayo kaina tana "yawwa tsohuwar Muna fuka gatanan tadawo daga gidan uban waye kike? Wato shine kika d'aukemun kud'i kika shiga yawon banzarki ko? To wlh Baki Isa yau senaga wanda yatsaya Miki agidannan banza barauniya. Tafad'a tana janyoni kamar tajanyo kayan wani tashiga jibgata tako'ina tana fad'ar wlh senayi maganinki agidannan maryama tinda ke bakida Imani yoshe za'akawomun adashen mutane wai kizo ki kwashe sabida maita da bakin hali irinnaki. Ihu nakeyi Ina Neman d'auki amma babu wanda yakulani....Sema cewada iyya hassi Tayi daki y'ar banza wata kila ta fiddo Miki abunki shegiya mekamada aljana. Hawwa ce Tayi tsaki tana shifewa dakinsu domin duk itace babbar yayarmu agidan Kuna y'ar iyya hassi ce.
Cikin takaici mama salmu tace wai minene hakan Yaya ? Kinsamu yarinya kina duka Hakan sekace baiwa tukunna ma wayaga lokacinda tad'auki kudinki? Haba arikayin Abu babu adilci aciki. Tafad'a tana fincikeni daga jikin mamansu Yah balah da se haki takeyi kamar Tayi dambe da sa'arta.
K'wafa mamansu Yah balah tayi tana shigewa dakinta batareda Takoma cewa komaiba domin tana Dan shakkun mama salmu sabida batada mutinci kowa Bata dagawa kafa agidan.....itako mama salmu ajiyeni kawai Tayi acikin barandar narakub'e agefen dakinmu kamar wata marainiya wadda batada kowa aduniya Ina famar kukana domin wlh jinakeyi kamar da rodi aka dakeni.....mama bintu ce tafito daga kicin dinmu hannunta d'aukeda kwanon abunci ta'ajiyemun batareda tace komaiba domin ita kuwa idan za'atada gidanmu da yakin duniya bazatayi maganaba hasalima yi zatayi kamar babu acikin gidan wannan shine halayyarta.
Dagowa nayi Ina kallon bayanta domin tuni Tayi tafiyarta tana ajiyemun abuncin ko waigoni batayiba.... k'wallar idona nashafe kana namik'e ahankali nad'auki abuncin nawa nafice daga gidan dudda cewar jikina Namin mugun ciwo sabida dukan danaci agun mamansu Yah balah Amma ahakan nabar gidan...tafiya nakeyi kaina akasa Ina tinanin rayuwata jefi jefi nakan share k'wallar idona ahakan harna baro unguwarmu Nazo wani kangon gida nashiga.....azaune nasameta ko yau kamar yadda nasaba ganinta tasaka y'ar tsana agaba tana kallo. Zama nayi akusanta tareda dafata cikin tsoro domin haryanzu nakasa sabawada ita duk tsawon lokacinda nadauka atareda ita...dagowa Tayi tana duban maryama d'in kyakkyawar mata kamar bala rabiya Amma kallo d'aya zaka Mata kagane cewar mahaukaciya ce...da kallo tabi maryama ganin yadda fuskarta Tayi jajir dudda batada hankali Amma tafahimci yauma fatar maryama ta canja kamar yadda take ganin sauyin atareda ita lokuta da Dama, bace komaiba domin Bata magana sedai idonta suncika tab da k'wallah. Ganin Hakan yasa maryama k'ak'alo murmushin dole tana Dora mata abuncinda takawo mata akan cinyarta.....Aiko ba musu tadau zataci cikin sauri maryama tarik'e nata hannu kamun yad'auko ledar ruwa d'aya dake gefenta wanda taka ajiyewa matar tad'auka tawanke mata hannunta sa'annan tasaketa...Aiko cikin sauri tahaucin abuncin hannu baka hannu kwarya. Itadai maryama tana kallonta seda tacinye tass kana tad'ago tana kallon maryama d'in...itako wasu wuran tad'auka tabata Tasha tak'ara wanke mata hannunta. Bayan tagama ta mik'e tashiga gyara mata wurinda take zaune domin kullun tazo seta gyara mata wuri dudda cewar ba b'atawa takeyiba domin kullun tana zaune ne wuri d'aya maryama ce kawai ketadata idan ta fahimci tana tareda wata bukatar tashiga ban d'aki seta kaita can wani jeji idan tagama bukatar ta seta gyara mata jikinta tamaidata...wannan shine rayuwar maryama da wannan mahaukaciyar.
Seda tagama gyara mata komai tsab kana tad'auki kwanon data kawo mata abunci Tayi tafiyarta ganin Tayi bacci....Koda Takoma gida kowa na dakinshi Hakan yasa tanufi nasu d'akin itada y'anmatan gidan Koda tashiga anty hawwa na kwance itada anty bilki da mejidda se zuwaira dake homework yayinda zubaida keta famar Danna wayarta....sallama kawai nayi tareda nufar y'ar tabarmata dake bayan gabun d'akin. bawanda ko yad'ago ya kalleni acikinsu balle nasaran zasu ansamun. Bandamuba domin idan da sabo nasaba da wannan halin nasu Dan dukkansu basuda kirki garama zubaida wani lokacin Muna Dan mutinci da ita itama ba koyosheba...jakar kayana najanyo nashiga fidda zanen da zan Daura domin wanka nakesanyi, seda na fidda zanen kana nashiga cire kayan jikina nadaura zanen. Hijab nad'auka kafin nasaka naji Anja wani Dan iskan tsaki...bance komaiba Kuma banjiyoba domin nasan kowacece tayishi Kuma bawai sabon Abu bane agun anty hawwa muddin zan cire kaya agabanta setayimun tsaki...nidai banbi takantaba nad'auki abunda zan buk'ata nabar d'akin.
"Shigiyar yarinya ni wlh haushi take bani yarinya kamar aljana ga kyau gayanda Maza keso komai ta had'a gawani Dan iskan sexy voice kamar da gayya takeyinshi. Anty hawwa tafad'a cikin Jin haushin maryama d'in....dariya anty bilki Tayi tana fad'ar nikuwa Kinga birgeni takeyi wlh domin za'ahuta ajikinta wannan kayan alatun nata ai ba'abarinsu Hakan ni wlh a duk lokacinda naganta jinake kamar na turmusheta way'annan nonuwan nata bala'in birgeni sukeyi wayyo kayan Dad'i tafad'a cikin shauk'i....tsaki anty hawwa tak'ara yi kamun tace aike aikinki kenan kwadayin mata kedai Allah ya shiryeki wlh bilki...dariya sosai anty bilki Tayi kana tace amin shirin jigida wanda baya katsewa, tana gama fad'ar Hakan tamik'e tareda kashe fitilar d'akin...cikin sauri mejidda tace "wayyo anty bilki homework fa nakeyi....eh nagani ki ajiye hadda safe domin bacci zamuyi inkuwa bazaki ajiyeba kikoma d'akin mama bintu kiyi...shiru jidda Tayi Bata Kara cewa komaiba domin tasan datayi magana zataci najaki agun antys d'in nata Hakan yasa Doli ta haura kan tata katifar ta kwanta....ita kuwa anty bilki tana haurawa kan katifarsu ta fad'awa anty hawwa tareda kama duka breast d'inta tarik'e tana sauke numfashi atakeko anty hawwa ma tararumi bakin anty bilki daganan suka shiga shek'e ayarsu suna gurnani kamar wasu mayu, ahakan maryama tashigo tasamesu.....!
Hummm wannan wanne Irin ahaline?🤔 To baradai muje zuwa maybe agaba zamu fahimta☺️
Autar alheri ✍️
🪽🪽🪽🪽🪽🪽🪽🪽🪽
🧜♀️🧜♀️🧜♀️🧜♀️🧜♀️🧜♀️
🪽🪽 *MEJO NAJEEB*🪽🪽
(Labari me sark'ak'iya ban al'ajabi rikici zalunci soyayya cin Amana dakuma romantic 💗)
Daga alkalamin Autar alheri ✍️
MEJO NAJEEB PAID BOOK NE YANZU MUKE FREE BOOK 1 IDAN MUKA SHIGO BOOK 2 SHINE ZAKI BIYA KARKI KARANTAMUN ABUNA BATAREDA KINBIYANI HAKKINABA MUDDIN KIKA FITARMUN DA BOOK KO KIKAKARANTA BATAREDA KINBIYANI HAKKINABA KEDA ALLAH.
Book 1
Page 5 & 6
"Wurin kayanta tanufa da lalabe domin sunyiwa d'akin d'ib bakaganin ko tafin hannunka, sewani D'an iskan Nishi sukiyi suna sambatu Irinna iskanci domin sunyi Nisa acikin duniyar abunda sukeyi duk sun haukata juna..... k'wallar data zubowa Isseta tashare