Showing 27001 words to 30000 words out of 109347 words

Chapter 10 - MEJO NAJEB Book 1 Complete Hausa Novels By Autar Alheri .txt

14 Jan 2025

14432

amma beko saurareshiba harseda suka kwashe komai sa'annan dakanshi yahaura danata, koda yashiga taduƙunƙune wuri ɗaya tanata sharar baccinta hankali kwance...betadataba illa loda mata kayan daya rinƙayi akan bed ɗin seda yakusan cikashi inda take kwance ne kawai beɗora kayanba seda yagama shigo mata da komai kana yaɗora abincin da suka shigo dashi a bedside table sa'annan yaficewar warshi nashi bedroom ɗin...wanka yaƙarayi kafin ya fito yashafa mayukan shi masu sanyin ƙamshi ɗaya siyo yanzu


wani mayen turare irin wanda yake anfani dashi agida yaɗauko yafeshe jikinshi dashi...yau ma shigar ƙananu kaya yayi inda yasaka wando dack blue riga kuma fara wadda taƙara fitoda asalin kyawunshi, agaskiya Mejo Najeeb yahaɗu Tako Ina..wayoyinshi yakwasa tare da laptop ɗinshi yafice inda ya samu captain Jameel aharabar gidan yana jiranshi, mota kawai yashiga captain Jameel yaja suka fice seda akazo buɗe get ne yatinada yanason kawo masu tsaro agidan dayaga captain Jameel yafita dakanshi yabuɗe get ɗin Hakan yasa yakira wani soja yace suzo gidan inda ya kwatanta musu inda yake da nomber gidan, kamin suka wuce airport kaitsaye acan suka samu general aliyu datashi zugar yaranshi bayan sungaisa suka Hau jirginsu izuwa birnin tarayya abuja...ana gida kuwa ɗagawarsu keda wuya Sega waƴannan sojojin kusan su huɗu suka dira agidan bayan sunyi ɗan zagayensu na tabbatar da tsaro agidanne kana suka dawo harabar gidan sukayi zamansu.


Isseta na farkawa Taga ƴanbanzan tulin kaya zagaye da ita atake tagano shine ya ajiyesu...shiko dama yayi hakanne danta gansu dawuri karyasaka a wardrobe tinda Batasan yakawoba taƙi dubawa..aiko hikimarshi tayi domin taji daɗin ganin kayan sosai Hakan yasa tamiƙe tashiga duba kayan wasu tayi dariya wasu tayi murna hardai tagama gani kana takwashe su tajera acikin wardrobe ɗin....!




















Autar alheri ✍️


🪽🪽🪽🪽🪽🪽🪽🪽🪽


MM _ NN


Book 2


Page 29 & 30


"Tana gama jerasu tashiga bathroom tayi wanka taƙara gasa jikinta bayan tafito tashafa mayukanda yasiya mata tayi simple makeup dama gata gwanar son kwalliya seta fito asalin maryamarta,,,kayan tabuɗe taɗauko wata doguwar riga milk color daratsin golden ajikinta sosai rigar tayimata ɗass kamar angwada a jikinta,, ribbon tasaka takama jular gashinta data sauko har gadon bayanta kana taɗaura mayafin abayar akanta.


Ahakan tafito perlorn ta tana ƙarewa tsarinshi kallo sosai yabirgeta Hakan yasa tashiga saukowa ƙasa cikin sanɗa gudun karta ganshi a general parlor harta sauko kobataga kowaba babuma alamun akwai mutun agidan,,nan tashiga zagayen perlor har kitchen da sauran bedrooms din ƙasa seda tashiga takashewa kanta ƙwarƙwatar ido🤩sosai tsarin gidan yabirgeta Masha allah tazaga ko ina seda tagama zagayen kana Takoma kitchen domin samawa kanta abunda zataci jin cikinta yafara Kiran chiroma 😅kayan abincinda ya'ajiye mata tashiga dubawa babu abinda babu aciki duk wani abinda zata buƙata na abinci da anfanin kitchen akwaishi aciki. Ajiyar zuciya tasauke bayan tagama duba kayan taɗauko indomie kawai taɗora tare da ruwan tea seda tagama girkin kana tagyara kitchen ɗin tsab kamar ba'ayi komai acikiba sa'annan taficewarta ɗakinta acewarta karyazo yasameta anan tinda dai tagama buƙatarta.


Acan tazauna seda tagama cin abuncinta taƙoshi kana tamiƙe tashiga gyaran ɗakin dudda bawata datti yayiba amma kasancewar anjima ba kowa agidan yasa yayi ƴar ƙura aiko sosai Isseta tazage tagyara ko ina agidan tindaga bedroom ɗinta har zuwa nashi bedroom ɗin wanda batamasan nashi bane seda tagama gyaran tazo wanke banɗaki ananne Taga boxes ɗinshi daya cire lokacinda yayi wanka, ɗauka tayi tawanke mishi komai batareda damuwaba tinda tasaba wankin nasu ya balah, seda tagama gyaran part ɗin nashi tasaka mishi tirare kana tarufe kamar yadda taganshi


tukunnah tasauko ƙasa seda tagyara ko ina agidan kana takoma bedroom ɗinta izuwa wannan lokacin anyi sallar azzahar banɗaki kawai tafaɗa tare da sakeyin wanka da alwala tafito tayi sallar azahar bayan ta idar tayi kwanciyarta se bacci..


Gombe


Tafiya takeyi cikin sauri ita kaɗai akan hanya batada burin daya wuce taganta agaban aminiyar tata abakin tekun ta tsaya tana waige waige ganin bakomai awurin kamar anyi shara gaya kuma bataga ko motsin aminiyar tataba yasata tabuɗe baki ahankali tace "maahh tafaɗa cikin fargaba domin yanzu taɗanji tsoro saɓanin ɗazu datake kan hanyar zuwa....tanatsaye awurin kuwa Sega jilar kifin maah tabayyana daganan Itama tafito gaba ɗaya, kallon halima tayi cikin murmushi domin dajin Kiran tagane itace..cikin sauri halima tagaidata.


"Murmushi maah taƙarayi bayan ta amsa mata tace "ƙawarki kikazo ganiko halima?? Tatambeta da kulawa. "Kanta a ƙasa tace "Eh maah nazo nagantane.


Jinjina kai maah tayi kamin tafito daga cikin ruwan takamo hannun halimar suka zauna bakin tekun tace "halima.."na,am ta'amsa gabanta na faɗuwa. Sarai maah taganota amma seta share taci gabada faɗar




"ina mematuƙar baki haƙuri akan hukuncin danayanke akan ƙawarki sedai inaso kisani bayin kaina bane ƙaddarartace tazo ahakan kuma In sha allah komai zezama labari. Nisawa tayi kamin tacigabada magana kamar Hakan "kisani maryama tana garin Lagos ayanzu....ido halima tazaro cikin kaɗuwa take duban maah idonta suncika tabb da ƙwallah...kai maah tajinjina mata alamar tabbatarwa kana tace "kiyi haƙuri halima zuwan maryama Lagos bayana nufin rabuwarku bane sedai yana nufin faruwar wani al'amari megirma abunda nakeso dake ayanzu shine kisaka aranki cewar kinatareda maryama aduk inda kike kuma maryama Matana taredake, sa'annan kizamewa maryama abokiyar gwagwar mayarayuwa akowanne hali kinjiko halima...kai Hakima yaɗaga tana me haɗiye kukanta...murmushi maah Tayi kana tace yawwa ƴar albarka kikwantarda hankalinki kuma aduk lokacinda kikesan wani temako daga gareni kizo kawai kinji ƴata in sha Allah nidakaina zansa akaiki gun maryama Kona kawo Miki ita idan baki ɗaga hankalinkiba...ajiyar zuciya halima tasauke kana tace "toh maah in sha Allah zanyi Hakan ngd sosai...yawwa ƴar albarka yanzu maza kije gida gasaƙo can kiɗauka, Tana gama faɗar Hakan Takoma cikin ruwa.... miƙewa halima tayi jikibaƙwari tanufi wurin dutsen nan da suke zuwa itada Isseta aiko tasamu maƙodan kuɗaɗe awurin kamar yadda suka saba gani inatada Isseta hawayen idonta tashare kana tasaka hannu taɗauka tabar wurin....tana shiga cikin gari takalli tulin kuɗin hannunta atake tatunada abinda Isseta keyi da kuɗin idan takarɓo aiko babu ɓata lokaci tanufi majalisar su yaya shamsu...yana ganinta tafe yataso cikin sakin fuska suka gaisa anan yayi mata jajen ɓatan Isseta kamar yadda aka yaɗa agari...murmushin da yafi kuka ciwo halima tayi kana tace mishi bakomai ai ƙaddara ce domin tayiwa maah alƙawarin bawanda zeji Isseta nanan lpy,,,daganan tace mishi zuwa tayi suje asibiti gun mamin Isseta...murmushin yaya shamsu yayi kana yace "to shikenan halima kicedai Zaki ƙarasa aikin ladanda aminiyarki taɗauko kenan? To ai Hakan akeso Allah yabamu iKon yin abinda yadace...Ameen y rabbi kawai halima tace daganan suka sami adedeta yaɗauke su zuwa asibitin


Koda sukaje alhmdllh sunsamu mamin Isseta yadda sukesan ganinta domin atsabtace take sabida tanasamun kyakkyawar kulawa komai sedai suce Masha allah abu ɗaya ne ya gagara samuwa shine lafiya amma Itama dassanu zatashiga ciwone kesamuwa lokaci ɗaya....godiya Sosai sukayiwa ma'aikatan wurin suka ƙara biyan wasu kuɗaɗen koda za'abuƙaci wani abu tare da yiwa ma'aikatan alheri suka tafi suna masuyiwa mamin Isseta addu'ar samun lafiya..


*TALLAH*
*TALLAH*
*TALLAH*


*Mematuƙar mahimmanci kidaure kikaranta kobazata anfanekiba maybe zata anfani wani ko wata naki idan kikaji*


*Maza💃 maza💃 maza*💃


Duk wata matsala danamuji kefama da ita agidanshi wadda ta shafi auratayya munada maganinta in sha Allah wannan babin maza ne🤩


mata ganaku👇


Albishirinki uwar gida haddama amarya🧏‍♀️


1, munada garin sha'shatau birkita ƙwaƙƙwalwar megida🙅‍♀️shinko kintaɓa jin lbarinsa???


Inamatan dake famada bushewar gaba???
Munada maganin ni'ima agun mace zata riƙa kawowa tamkar tana fitsari ruwa kuwa ajikinta setagaji da canja pant🥳🥳




Munada maganin matsi zekamaki kabbb kamar anɗinkaki namuji nashiga kina riƙeshi ni'imarki nabashi damar fitowaya dangwalo daɗi 🤩🤩🫣🫣


Munada kuka dole ɗanɗano kamar an haɗa madara dazuma Hakan Zaki koma agunshi y'ammata💃💃💃


Munada maganin mugun namuji komi zamanshi taure doline yadawo hanya da izinin Allah 💃🥳


Ina matsalar infection wanda ya haddasa wa rayuwar aurenki matsala ?? Sanyi ko haifaffene zebar jikinki da izinin Allah 🧏‍♀️


Hajiya kigarzayo kinemi naki cikin sauƙi da rahusa gakuma biyan buƙata cikin ƙanƙanin lokaci cikin iyawar uban giji 💪💪 mata harmada mazan zama seda gyara.


Munada maganin ƙiba dakuma na rage ƙibar munada na gyaran nono dakuma na duwawu suzama ɗima ɗima Hajiyata🫣🫣🫣💃


Gaduk me bukar maganinmu ze iya tuntuɓar wannan nomber 👉07037092136 or 09112799371 🙏🙏




Abuja


Jirginsu nasauka kaitsaye suka wuce babbar hidikwatar sojoji dake garin Abuja inda suka samu duk wasu manyan jami'an soja da'akeji dasu a Nigeria suna wurin hadda general faruk sojan ƙasar Niger shima datawagarshi duk suna wurin zuwansu kawai ake jira ashiga meeting Shima sabida general faruk yace bazeyi maganar komaiba harse jami'an sojojin dasukayi nasarar kama ƴan ta'addan sunzone sabida sune sukasamu information akansu..tofa wannan dalilinne yahana ashiga meeting ɗin.


Shigowarsuce tasa duk wanda ke wurin hankalinshi komawa kansu inda ƙananun jami'ai damanya keta ribibin sara musu sabida namijin ƙoƙarinda sukayi...cikin mamaki wasu daga cikin manyan jami'an Nigeria ke kallonsu domin Sam basuyi tinanin subane...wasu kuwa sunsan sune sabida sunansu da'akayi posting alhalin su basuma sanda abunba kawai Allah yayi ikonshi akan lamarin shiyasa har suka gani kuma suka yi aikin inda suka samu nasara cikin iyawar uban giji da buwayarsa.....general faruk ne yazo wurinsu kyakkyawan matashin sauri me farar zuciya. Hannu yabawa general aliyu suka yi musabaha tare da jinjinawa namijin ƙoƙarinsu akan wannan al'amarin kana yabawa mejo Najeeb daga baya sabida mutane da suka yaɓeshi suna girmama shi...Shima bayabo ba fallasa yabawa general faruk hannu suka gaisa cikin mutintawa daganan suka samu wuri suka zauna inda kowa yazauna mazaunin shi sedai abin mamaki general faruk yaƙi zama acikin tawagar shi yadawo kusada mejo Najeeb da general aliyu yazauna abin gwanin birgewa. Dudda manyan nasu sunkulada Hakan sedai bawanda yace komai domin sunsan waye mejo Najeeb bayabin ƙa'ida kuma baya sauren zancen magaba dashi balle sukawo mishi wargi ko renin hankalin manyan jami'ai Hakan yasa ko manyan shayinshi sukeji.


Sunjima suna tattaunawa akan wannan matsalolin inda general aliyu yace yanaso yasani waye yasaka sunansu amatsayin waƴanda zasuyi attack ɗin amma kuma ba'asanardasuba?shiru wurin yaɗauka kowa natinanin wannan al'amarin tayaya Hakan zatafaru...dagacan wani mejo tanimu yace "wannan wacce irin maganace general aliyu kakeyi Hakan tayaya zakuce ba'asanarda kuba kuma kukayi aikin kenan ku waliyaine dazakuyi abu bayan bakusanda shiba?? "Mikakesan cewa ne abb...beƙarasaba mejo Najeeb yadakatardashi tahanyar riƙo hannunshi yazaunar dashi..aiko yakoma yazauna batareda yaƙara cewa komaiba..duk abinda kefaruwa kowa dake wurin na kallo... miƙewa yayi tsaye cikin cool voice ɗinshi yafara magana kamar babu komai ataredashi amma anan dayake karkaso kaga zuciyarshi yadda take tafasa kamar anhasa mishi wuta. "The game is over but we I'll going to south Africa next month in sha Allah...yana gama faɗar Hakan yajuya zebar wurin...cikin daga murya wannan mejo tanimun yace "we not understand you najeeb sahabi mizakuyi a south Africa??? Ahasale yajiyo cikin daga murya yace "zamuje ƙarasa aikin da muka farane domin babu shugaban su anan kuma wlh semunje munkamoshi kuma nida brothers na kawai zamuje Bama buƙatar wata rundunar ko temakon wani se allah that's all.


Dukkansu sororo sukayi suna kallonshi...kamin wani dagacikinsu yace "bamugane kaida brothers ɗinka ba kana nufin bada jami'ai zakajeba mejo Najeeb tayaya Hakan zefaru?? Wani mugun kallo mejo yawatsawa mutumin kamun yace "yes of course nida brothers na zamuje kuma haziƙan jami'ai wanda sukasan aikinsu ba karnukan farautar ƴanta addaba masu ɓata mana ƙasa general aliyu Haidar & general Umar faruk Niger sune brothers na kuma sune zamuje dasu bakuma shawara nake nemaba kojiran umurni noo hukuncine narigada nayanke kuma na tabbatar Sena aikata biqudiratillah.




Yana gama faɗar Hakan yaficewarshi cikin takonshi na jaruman maza masuji da izza da dajarunta. miƙewa general aliyu yayi yabi bayanshi batareda yaƙara cewa komaiba hakama general faruk dayayi mutuwar zaune jin mejo Najeeb yakirashida brother ɗinshi tofa Shima ficewarsuce tadawo dashi hankalinshi Hakan yasa yamiƙe cikin sauri Shima yamara musu baya sukabar kowa dakewurin da baki asake..wani mugun ƙololo mejo tanimu ya haɗiye yanajin baƙi cikin yadda wannan yaron ketaka kowa ahukumar soja kuma bame tanka mishi gaskiya doline suyiwa tubkar hanci yaƙarasa zancen yaname barin hold ɗin Shima inda muƙarrabanshi suka takemai baya(hmm nikuwa nace aiki yasameka Alhaji tanimu🤩)


Suna fita mota kawai yashiga suma duk suka shiga hadda general faruk suka nufi gidan Mejo ɗin dake cikin garin abuja dukkansu wanka sukayi kana general aliyu yayi musu order abinci online kafin akawone suka shiga tsara yadda zasu ɓullowa lamarin kafin lokacinda mejo ɗin yaɗiba nazuwansu South Africa yayi sunjima a general parlor gidan kafin Mejo yamiƙe yashige warshi bedroom...da kallo general faruk yabishi harya ɓacewa ganinshi kana yasaki murmushi yana girgiza kanshi...taɓoshi general aliyu yayi Shima yana murmushi tare da ɗaga mishi gira ɗaya 🤨alamar yadai...murmushi Shima yaƙarayi yana shafa kwanta ciyar sumar kanshi ta buzayen asali yace "wlh kawai guy ɗin yana birgeni ne yadda yake komai ba tsoro balle fargaba gakuma miskilanci ko acikin maza seya bayyana gaskiya wannan kam mace zatasha fama ataredashi..dariya sosai zancen general faruk yabawa general aliyu Haidar seda yayi me isarshi kana yace "inafa kasani aibakaga komaiba indai najeeb ne iyaganin yau ne kake mamakinshi inaga dashi kake rayuwa? "Humm gaskiya kam abin dai Allah ya kyauta..to Ameen amma tabbas matarshi kam nada aiki zanso ganin yadda zeyi rayuwar auren shi cewar general aliyu..dariya general faruk yayi cikin mamaki yace badai bayada aureba?? "Aikuwadai kam bayadashi kamarni maybe Kaine kawai me mata acikinmu...wata dariyar yaƙarayi yana faɗar "tab dijam niɗin?? humm aiko duk mune sedai Allah yanuna mana munyi.. Ameen y rabbi cewar general aliyu Yana murmushi...abuncinda general aliyu yayi order ne aka kawo musu shine abinda yakatse musu fira, fita yayi yakarɓo abuncin kana yadawo perlor Anan sukaci abincinsu sukabarwa mejo nashi domin ga dukkan alamu bacci yakeyi,,seda suka ƙoshi kana kowannensu yanufi ɗaya bedroom ɗin suka kwanta se bacci..


Kwanansu mejo huɗu a Abuja kana kowannensu yanufi garinsu inda suka yi musayar nomber waya suda general faruk domin awannan ƴan kwanakin shaƙuwa me ƙarfice tashiga tsakaninsu Hakan yasa dasuka fito seda suka raka general faruk har airport inda tawagarshi take yashiga jirgin komawa ƙasar shi kana suma suka hau nasu jirgin zuwa Lagos suka rabu cikin kewar junansu kamar suwuce gari ɗaya amma ba damar yin hakan to sedai muce Allah ya saukeku lpy...!
















Autar alheri"🪽🪽🪽🪽🪽🪽🪽🪽🪽


MM _ NN


Book 2


Page 31 & 32


"Jirginsu nasauka suka samu dandazon yaransu suncika airport ɗin harda captain Jameel dakuma captain Ameer babban yaron general aliyu kenan suna jiransu....cikin takonsu na isa da taƙama suka sauko daga cikin jirgin cikin sauri captain Jameel yabuɗewa mejo Najeeb ƙofa inda captain Ameer yabuɗewa general aliyu Shima, aiko suna shiga suma sauran sojojin duk suka shiga Hakan yasa motocin tashi atare suna saka jiniya cikin gudu kamar zasu tsaga kwalta sukabar airport ɗin...Hakan yasa duk wanda ke airport ɗinnan hankalinshi yakoma kansu sedai tuni sunyi gaba abinsu....kowannensu gida yanufa suna shiga tangamemen get ɗin gidan yawan gale kanshi suka danna hancin motocinsu ciki tare da nufar Perking space....acikin gidan kuwa dukkan mutanen gidan na perlor ciki kuwa hadda sajad babban yaron mama wanda shikebin Munir acikin yaran gidan Shima jiyane yadawo daga wurin training.


Baki Hajiya Umma tawashe tana faɗar "lale marhabin da mazan fama andawo kenan...suma duka yaran gidan murna sukashigayi ciki kuwa hadda mansura domin Allah yagani tana kwaɗayin ganinshi tayi kewarshi sosai kamar zataci babu..agefen ummi kuwa fargaba ce fall ranta domin ɗazu sukayi wayada ƙawarta juwaira tace mata Tanakan hanya shiyasa sam bataso yah najeeb yadawo yanzuba taso ace har juwaira tagama zamanda zatayi takoma bataga yaya najeeb ba domin tasan tabbas inyasan manufar juwaira akanshi to ƙaryarta taƙare...tanacikin wannan tinanin ne tajiyo ihun Siyana tana faɗar "oyoyo yah najeeb na yadawo oyoyo yah najeeb..Hakan yasa tadawo cikin nutsuwarta izuwa wannan lokacin kuwa tuni mejo yaƙaraso cikin perlor ana gaisawa dashi.


Cikin girmamawa ƙannen nashi kegaidashi inda Munir da sajad suka bashi hannu sunayin musabaha daganan kowannensu yarun gumeshi suna murnar ganin yayan nasu.. sajad ne yabuɗe baki ahankali yace 'yah najeeb I miss you so very much wlh yafaɗa yana share ƙwallar idonshi...bakinshi yaɗan ciza ahankali yanajin son yaron harcikin ranshi Yajima kamin sajad yaji saukar cool voice ɗinshi cikin dodon kunnen shi yana faɗar "miss you too my little bro ya school ɗin??? Tatambaya kamar bashine yayi maganar ba...ajiyar zuciya sajad yasauke kamun yaƙara ƙanƙame najeeb ɗin yace "alhmdllh yah najeeb amma ba daɗi wlh...se awannan karon najeeb yayi guntun murmushi kafin yace "to dama wayacema akwai daɗi...kafin sajad yayi wata maganar sukaji ihun Siyana tana faɗar "wayyo ita Allah yah najeeb yashareta yah sajad kawai yakeso...aiko duk wanda ke perlor seda yayi dariyarta...shiko dafe kanshi kawai yayi tare da duƙawa yaɗauketa bayan yacire sajad daga jikinshi kanshi yadafe kaɗan domin duk yagaji jima yakeyi duk sun haddasa mishi ciwon kai


seda yaɗan yamutsa kyakkyawar fuskarshi kana yace "sorry angel daga Hakan yashiga gaida iyayen nashi.


Cikin sakin fuska mama ta amsa mishi tana mishi barka da zuwa yayinda Hajiya Umma tamiƙe tsaye cikin murmushi tariƙo hannunshi suka haura pert ɗinshi da tuni Ummi tabuɗewa captain Jameel harya kaimishi laptop ɗinshi da wayoyinshi yaficewarshi...da kallo ƙurillah mansura tabishi harseda yaɓacewa ganinta kana tasauke ajiyar zuciya tana matse ƙwallar idonta tanason gaidashi amma tana shakku Hakan yasa batace mishi komaiba har suka ɓacewa ganinta...har cikin bedroom ɗinshi takaishi ta zaunar dashi abakin bed kana tashiga bathroom tahaɗa mishi ruwan wanka masu ɗimi tafito domin tasan tabbas yanzu wankan yafi buƙata, tana fitowa tace "my son jekayi wanka kahuta sekazo Kaci abinci kajiko? Kai kawai yaɗaga mata yana murmushi...itako hannun Siyana tariƙo tana faɗar"auta bari yayanki yayi wanka seki dawo kinji takarasa zancen tana saukowa da ita ƙasa.....shiko Mejo kayan jikinshi yarage tukunnah yamiƙe yasakawa ƙofarshi key kana yashiga bathroom ɗin nanma seda yasakawa ƙofar bathroom ɗin key sabida tsaro kana yacire boxes ɗinshi yafara wanka...sedai wani abin mamaki ko wankan begamaba yaji kamar sautin magana ƙasa ƙasa, shiru yayi yadakatarda wankan dayakeyi anan yaji ana faɗar "washh Allahnaa wayyoo sweet najeeb zanso ganin ranarda zanji jarumtarka ajikina wayyoo aranar Sena Suma uhmm ahhhh.. kowacece tafaɗa cikin shauƙi gadukkan alamu tafara lulawa duniyar begen najeeb ɗin...wani irin waro ido mejo Nejeeb yayi cikin mamaki da tsintsar kaɗuwa yajanyo towel yaɗaura tareda nufo ƙofar sedai yana ɗora hannu yabuɗe yaji ƙofar abuɗe domin yacire key Hakan nanufin wani key akasaka daga waje aka buɗe ɗakin har akashigo aka buɗe mishi bathroom ko yaya??


Yatambayi kanshi? Kuma bashida amsar tambayar..cikin hanzari yafito perlor amma bakowa, dafe kanshi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login