Showing 102001 words to 105000 words out of 109347 words

Chapter 35 - MEJO NAJEB Book 1 Complete Hausa Novels By Autar Alheri .txt

14 Jan 2025

14455

cikin mamaki yace "miyasa za'abi nann? "Sorry Sr Hajiya umma ce takirani yanzu tace idan mufito musameta anan tana neman ka.. rass gaban mejo yafaɗi amma yadake bece komaiba gudun kar Captain jameel yagane wani abun......danugun sauri tafito daga bedroom ɗinta kamar zata tashi sama hakan tafito tsakiyar gidan tanufi get...cikin sauri su Captain Umar dake gadin gida sukabiyota suna faɗar "lafiya dai Madam? Amma ina kafin suzo harta fice daga get ɗin, koda suka ƙaraso suka suka fito farfajiyar gidan taɓacewa ganinsu sam basuga ko me Kamada ita ba kamar wata aljana...arikice Captain Umar yaɗauki waya yana kiran mejo amma bugun duniya yaƙi ɗagawa hakan yasa yanayarda kiran gun general Aliyu, yana ɗagawa cikin tashin hankali Captain Umar kegaya Mishi abinda ke faruwa...arazane yamiƙe tsaye yana faɗar whatt?...!


























Autar alheri ✍️🪽🪽🪽🪽🪽🪽🪽🪽🪽🪽




MM _ NN


Book 6


Page 105 & 106




"What?? Tunyoshe tafita? Yatambaya cikin tashin hankali. "Yanzunnan sr kuma gashi munfito babu ita. Kukoma gidan kawai zanzo yafaɗa tare da yanke wayar.....mejo wani gidan gona suka nufa bayan Captain jameel yayi Perking shikaɗai yafito yace sujirashi yana zuwa kana yanufi cikin gidan danufin yiwa Hajiya umma gargaɗi taneda Mishi hakan bayaso,,,,sedai koda yashiga bakowa a Perlor hakan yasa yanufi cikin bedroom ɗin dake perlor, tura ƙofar yayi yashiga sedai Bega kowaba, ɗan tsaki yaja tare da juyawa zekoma kawai yaga anrufo ƙofar ɗakin, da mamaki yaɗago yana kallonta sedai cikin sauri ya kauda idonshi yana faɗar, innalillahi wa'innailaihi raji'un astagafurullah wa'stubu alaihi, saka makon mugun ganinda idonshi suka Mishi. Hajiya umma tsaye agabanshi tsirara tana kallonshi...ganin yadda yayi yasa tayi wani shi'umin murmushi kana tace "dana kadena wahalarda kanka my son domin kuwa yau dai seka lasawa mamanka jarumtarka tamori abinda ta rena, taƙarasa zancen tana tunkaroshi cikin sigar karuwanci domin taja hankalinshi gareta. Mejo kam tun lokacinda yayi ido huɗu da ita tunɓur haihuwar uwarta tanemi natsuwarshi yarasa wani irin abu yakeji nataso Mishi tun daga ƙasan zuciyarshi mekamada feeling ba feeling ba kunci ba kuncuba yama rasa awanne matsayi yarasa ɗora kanshi




Tunkaroshi tayi cikin kissa da karuwanci tana wani shi'umin murmushi ganin takonta t
Yakama kurciya a nata tunanin, hannunshi tariƙo tare da ɗorawa akan jagwal ɗin nonuwanta,,,, beƙarasa kaiwa ba tasaki wata irin raza nanniyar ƙara cikin azaba da ihu tana gan tsarewa, Sakamakon wata irin azaba dataji taratsa bayanta,,,,da sauri mejo dayayi mutuwar tsaye yajuya yana kallon minene abinda yasamu Hajiya ummar, itamadai juyawar tayi cikin tashin hankali tana kallon kominene hakan yadaketa me masifar zafi da azaba. Da jelar macijinta suka fara cin karo tana wani mirɗeta ta ɗaga ta sama tana shirin koma shauɗa mata ita akarona biyu...ido suka zaro atare suna kallon Isseta wanda azahiri dukkansu isseta suke gani amma a ba ɗini gimbiya mardeeya ce ajikinta. "Ido Hajiya umma tawaro tana kallon gimbiya mardeeya da fuskar isseta wadda ke watsa mata muguwar harara, cikin jin haushin ta tace"Jamila kinyi asara kin cuci kanki kin cuci rayuwarki kisani najeebullah yarigada yayi miki nisa tun lokacinda kika fidda maitarki akanshi kuma ina Miki albishir da cewar Maryama tana kan hanyar zuwa gidan mijinta sa'anan hukuma na nemanki akan miyagun aiyukanki, kinga ko a iya hakan aka tsaya Jamila munyi nasara akanki gimbiya laweesat da gimbiya mardeeya sunyi nasara akan mushirika kuma buɗararriyar bil adama, kisani natsaneki tun lokacin da nasan wacece ke banida burin daya wuce nakasheki kamar yadda nakashe abokin tsafin naki tsijuju domin narage ɓata iri acikin duniya amma bazan kashekiba ayanzu domin inason kigirbi abinda kika shuka dakanki duniya tagama yimiki Gwalo tukunnah kiga ƙarshenki ganin idonki....tunda gimbiya mardeeya tafara magana mejo yadawo hayyacinshi ananne yafahimci tabbas ba little mom ɗinshi bace maybe maah ce ko wadda general Aliyu kebashi labari..Itako Hajiya umma tunda taji kalaman gimbiya mardeeya tanemi natsuwarta tarasa babu abinda kemata yawo irin Maryama na hanyar zuwa gidan mijinta gimbiya laweesat tayi nasara akanta kuma gimbiya mardeeya takashe mata tsijuju hakanne yasa idan takirashi baya zuwa, kenan wata tunuwar asirintane yatsaya ina bazeyuba, tafaɗa abayyane tare da nufar hanyar barin bedroom ɗin agigice seda takai perlor tukkunnah tadawo neman suturar dazata saka domin sam tamanta da tsirara take, abaibaice tasaka kayan ko mayafi babu tafigi mota tafice daga gidan.


Se alokacin gimbiya mardeeya ta kalli mejo kana tace "mardeeya ce ƙanwar maah ɗinku kayi sauri kaɗauki matarka kuje gidan Alhaji Khamis domin can Jamila tanufa Maryama kuma na kan hanya ayau komi ze warware amma fa idan kabari Jamila tagudu to tabbas za'akoma kamar bayane, tana gama faɗar hakan tazamewarta daga jikin isseta anan tazube ajikin mejo,,,,cikin sauri yaɗauketa yanufi motarshi batareda ma yatsaya bitakan tafarkaba...yana fitowa Captain jameel yataso cikin mamakin ganinshi da ita tunda yasan batare sukazoba gaya kuma Hajiya umma tafoto itama agigice, buɗe mishi motar kawai yayi yasakata cikin bada umurni yace muje gidan Abba yanzu, aiko cikin sauri Captain jameel yafigi motar sauran security ɗinsu suka mara musu baya.


Suna isa gidan ko gama Perking Captain jameel beyiba mejo yaɗauko isseta suka fito tare da nufar cikin gidan, Hajiya mama ce da Munir zaune a perlor lokacinda Hajiya umma tashigo Karaye, hakan yasa duk suka bita da kallo basukai ga samun yin magana ba mejo yashigo ɗaukeda isseta. Cikin mamaki Hajiya mama ke kallon kamin su haɗa baki itada Munir wurin tambayar lafiya???




"lafiya mama ina Hajiya umma yatambaya yana kwantarda isseta akan doguwar kujera kusan Hajiya mama. Kafin tabashi amsa Sega Hajiya umma tafito wuri janjan kamar an Korita tanufi haryar barin perlor "inzaki kuma umma? Cewar mejo yana nufota...ka kalloshi batayiba tabuɗe ƙofar perlor domin abinda ke gabanta yanzu yafi gaban na mejo,,,tana buɗe ƙofar ana turota daga waje, cak tatsaya kafin tazaro idonta cikin mugun tashin hankali tace "Maryama seda kuwa kika dawo?? Tafaɗa arazane...Abba dake gaba kafin Ammi dasu jidda dukkansu da kallo sukabita cikin mamaki Abba yace "miye hakan Jamila? Lafiya kuwa? Kafin tabashi amsa suka shigo perlor har Ammi...cikin wani irin farin cikin dake fita tundaga zuciya Hajiya mama tace "anty Maryama kece? Alhaji dagaske dai anty Ce tadawo? Ashe dagaske Ummi keyi alhmdlmulillah Allah mun godema daka muna mana wannan ranar anty Maryama, se kawai tarungumi Ammi tana sakin kuka....cikin ƙarfin hali da soyayyar ƙanwar Tata Ammi tarugumeta back tana shafa bayanta ahanki tace "Safiyya kuka ya isa hakan kika kuka agaban ƴaƴanki uhnm bagani agabankiba haba ƴar ƙanwata....murmushi me haɗe da kuka Hajiya mama tayi tana goge hawayenta. Ammi tabuɗe baki zatayi magana kenan sukaji Muryar Hajiya umma cikin amo marar daɗin sauraro tana faɗar ""inaa wlh sam bazeyuba ƙarya kikeyi wlh keba Maryama bace ƙarya ne wlh Maryama bazata taɓa dawowaba har abada domin tsijuju bazemun ƙarya ba.....ɗib kowa yayi awurin cikin mugun mamaki suna kallonta kafin Abba yace "mikike nufi Jamila bangane ba Maryama bace bazata taɓa dawowaba? Kinsan wani abunne akan ɓatan Maryama dakike wannan magar?? Yatambeta cikin tuhuma. Aiko kamar wata zarriya tashiga faɗar "eh mana wlh ba Maryama bace wannan yaudarar ka ce zatayi Alhaji domin kuwa bakina dana tsijuju yagayamin cewar Maryama tatafi kenan bazata taɓa dawowaba sabida tsafin damukayi mata baze taɓa barin jikintaba cikin sauƙi tayaya za'ace tadawo nayarda? Taƙarasa zancen tana wani zazzare ido kamar zata dakesu...ahasale mejo yazaburo zeyi kanta sedai kafin yakai Munir yarigashi yariƙo hannunta cikin mugun baƙin cikin furucinta yace "umma mikike faɗa hakan wacece Maryama? Kedawaye kuka mata tsafi? Kuma mitayi muku? "Wata irin dariya tasaki kafin ta haɗe rai tamau tace "wai wannan itace Maryama kuma karyane ba itace bace domin Maryama dakaina nasaka mata layarda ta haukatarda ita, Bara kaji abinda tayimun.


"Nida Maryama munraso tamkar tagwaye kuma Aminan juna munyi karatu tare munyi rayuwar budurcinmu tare dudda kasan cewar mahaifinta yafi nawa kuɗi amma hakan muke abotarmu,,,,kuma ina zuwa gidansu tana zuwa namu, tun lokacinda nagirma na mallaki hankalin kaina nakeson Khamis wato abbanku kuma Maryama da hakan domin kullun ina gaya mata irin son dana keyiwa Khamis kamar zan mutu. Wai kwatsam se Maryama tazo tana gayamin za'a ɗaura aurenta da Khamis inji abbanta kuma ita bazata iya bijirewa umurninshiba shiyasa take gayamin dan Allah nayi haƙuri idan inason yayanta abdussalam zatayi Mishi magana ya aureni bayan kuma tasan cewar abdussalam akwai wadda yakeso wato Hannah,, dudda naji baƙin jiƙin cikin wannan zancen nata amma Sena nuna mata ba komai kuma nayi mata fatan alkhairi sabida tama renamin hankali zuwamin da wannan zancen idan kuwa hakane babu amfanin nuna mata wata damuwar tunda wadda nake gaya mata tun abaya batayi anfaniba.


Hakan nashige gaba akayi komai ba hidimar bikin Maryama dani daga gefe ɗaya kuma ina neman hanyar dazan ɗauki fansar abinda tayimun domin bazan taɓa barinta taci bulus ba wannan alkawarina ne...bayan auren Maryama da mako ukku Mahaɗu dawani boka tsijuju shine yayimun maganin Maryama, alokacinda tahaifi najeeb bada jimawaba yabani laya dana saka mata aƙasan gadonta kuma nazuba mata magani acikin abinsha...hakan yasa cikin dare tsijuju yasamu damar ƙarasa aikinshi ta hanyar kiran maryama wanda yasakata tashi tafita daga gidan babu shiri kuma bada sanin kowaba tabi duniya kuma yayi mun alkawarin bazata taɓa dawowaba muddin nabi sharuɗanshi.


Bayan ɓatan Maryama nasaka tsijuju yayimun aikin akan khamis ya aureni domin naga abdussalam nason ya aura Mishi ƙanwar Maryama Safiyya...hakan akayi aurena dana Safiyya babu shiri. Muna zaune anan tsijuju yace Sena karɓi renon yaron Maryama wato najeeb tukkunna aikinmu zetafi yadda mukeso...amma nazo abdussalam yahana abanishi ahakan yasa mukayiwa Khamis aiki babu shiri yatattaramu mukabar Niger muka koma Nigeria daga nan nasaka Khamis yakarɓi najeeb yabani...sedai yadda yake nunawa yaron soyayya baze bari muyi komi yadda mukesoba, hakan yasa tsijuju yafitarwada Alhaji khamis najeeb arai sam yatsaneshi kuma muka hanashi zuwa Niger domin abdussalam zekawo muna cikas a aikinmu....bayan najeeb yacika shekaru 16 duniya tsijuju tabani wani abun danake Mishi anfani dashi wanda kesaka wannan masifaffen ciwon dayakeyi domin wannan ciwon nashi yana ƙara nisantashine daga Alhaji Khamis kuma yana nisanta Maryama daga garesu domin har izuwa wannan lokacin tsijuju yagayamin tana raye....sedai dudda kasan cewar nice silar cinwonda najeeb keyi amma inajin tausayinshi sosai domin tun yana Yaro ƙarami aka jarabeni da sha'awarshi muguwar sha'awa wadda tasa bana iya control kaina akanshi....dana gayawa tsijuju shine yabani maganin danake anfani dashi acikin duka kayan abincin gidannan domin ɗauke hankalin mutanen gidan daga kan abinda zefaru tsakanina da najeeb domin kuwa yace haɗuwata da najeeb ashimfiɗa ɗaya shine ze tabba tarda cikar burina, hakan yasa duk abinda zan yi Mishi bawanda zece komai...hakan yasa nake bibiyarshi har banɗaki batareda yasaniba kuma hakan yasa natsani ƴata mansura domin naga itama shitake hari, duk wannan abun bawanda yasani ko yakula se shigowar wannan tsinanniyar yarinyar cikin gidannan tashiga ruguzamin komai daga tsakanina da ɗana har da mutanen gidan nan tahanyar kwashe duka kayan abincin gidannan da magungunan danake anfani dasu takuma shiga tsakanina da najeeb datemakon wannan muna fukar gimbiya mardeeya, bayan takashemun tsijuju yanzu kuma duk wannan be isheta se a wani ce Maryama tadawo bayan tsijuju yace karba yadda tashigo gidannan wlh sam bazeyuba ƙaryane ƙaryanee wahallahi, tafaɗa cikin ƙara ji ɗaga murya wadda kenuni dacewar tarigada ta haukace....!




















Autar alheri ✍️
Autar alheri ✍️🪽🪽🪽🪽🪽🪽🪽🪽🪽🪽


MM _ NN


Book 6


Page 107 & 108




"Gabaki ɗaya mutuwar tsaye mejo da Munir sukayi harmada sajad, Abba kam ba'amagana,,,yayinda Ammi da Hajiya mama keta rusar kukan takaicin zamada maƙiyinka batareda kasaniba. "Yanzu Jamila dama kece sanadin haukana? Dama kece sanadin danabar gida nabar yarona jinjiri? Nabar mijina dangina dakomai nawa? Mina aikata agareki hakan Jamila tun zamanada dake? Alokacinda ake zancen aurena da abban jazlan dakin gayamin har izuwa wannan lokacin kinason Jamila mize hana ya auremu dukanmu? Amma sekika nuna bakomai sabida mugun nufi, yanzu jalima har kika reni ɗana dawata mummunar manufa? Jalima kike sha'awar ɗan cikina wanda koba kece kika renishiba bazanyi tunanin hakan agarekiba, kilalatamin rayuwar yaro why jalima why please?? Ammi taƙarasa zancen tana koma sakin sabon kuka....Abba kam dajikinshi yarigada yayi sanyi cikin ƙarfin hali yazo gabanta kamar ze shiga jikinta yace "jalima, shiru bata amsa Mishi ba, ƙara kiranta yayi akaro na ukku kana tace"jalima kika sakawa yarona ciwon wanda ke gabda kaishi lahira kuma kina hanani tausaya masa kana kuma kinuna cewar kinfi kowa jin tausayinsa bayan kece silar komai, duk ina soyayyar dakikeyiwa najeeb Jamila? Da har zakiyi ƙoƙarin cutar dashi jalima miyasa hakan mimuka Miki dazafi hakan? Yatambaya idonshi na cika da ƙwallah....cikin takaici Hajiya umma tace bantaɓa son najeeb ba dededa ƙwayar azzara acikin raina sedai sha'awa, bantaɓa yimishi kallo ɗa ba sedai farka shiyasa bantaɓa yimishi addu'a ba balle fatan nasara, akulle idan yacemun tafita kozeyi tafiya iya kacina dashi sekadawo yaron umma,,,amma ita wannan munafukar hadda wani kinibibin yimasa addu'a bayan kuma addu'ar ki bazata ƙareshi dakomai domin bazata hanashi shiga farko naba, seka bani jarumtarka najeeb najika acikina shine cikar burina shine mafalkina zoka lasamun zumarka najeeb zokabani zo kacin...dasauri Munir yatoshe mata baki ciki kukan me nunida tsantsar bakin cikin dayake ciki nasamun mujirimar uwa irin Hajiya umma yace "sedai bakin cikin rashin samun yah najeeb amatsayin namiji agareki yakasheki umma yah najeeb baze taɓa aikata fasiƙanciba ko a gun wata daban balle ke dayake yiwa kallon uwa mahaifiya idan dai har wannan shine zezamo ajalinki to muna jira kiƙarasa cikawa semuje musadaki da mahaliccinku keda wa'yanda kika zalunta shine yasan abinda ya dace dake, kincucemu umma kin tozaltardamu kin wulakanta muna rayuwa umma najima ina zargin wani abu akanki tun lokacinda kike yawan yiwa yah najeeb wasu abubuwan dakuma yadda kika nuna kishinki ƙarara akan anty Maryam wannan yasa naƙara zarginki segaya kuma hasashena yazama gaskiya kinbar mana tabo umma kinbar mana Miki da dafi azuciya wanda zayataɓa goguwaba kincucemu umma kin cucirayurm...cikin sauri mejo yajanyo jikinshi tare da rungumeshi suna sakin kuka atare memugun tada hankali, dasauri sajad yazo yarungumesu duka shima yana sakin nashi kukan....kowa yayi tsitt awurin se sautin kukansu kawai ketashi.




Dasauri general Aliyu dayashigo gidan tun ɗazu yana kallon wannan badaƙalar yariƙe Hajiya umma yana faɗar "subhanallah please umma kitsaya Dan Allah, domin iya kacin gaskiyar ta nema takeyi ta yaga kayan jikinta....dukkansu juyowa sukayi suna kallon yadda yake kokawa da ita amma ba wanda yayi yunƙurin tayashi. Cikin marairaice fuska yace "please mejo kutayi mutafi da ita domin nemanta ma akeyi a office nazo zan kiraka bagayama cewar mejo tanimu yayi bayanin wacece Hajiya jamila domin bakowa bace face Hajiya umma ina tunanin yadda zan tareka da wannan zancen ne Captain Umar yakirani yana gayamin little mom tafita yanzu yaduba begantaba,,,shine fa naje gidan bansameta ba nazo nan koda nan tayo segaya kuma nasameku anan duka gakuma wannan rikitaccen al'amarin dan Allah kutayani muje da ita kartayi tsirara anan, yaƙarasa zancen cikin takaici shima.....ƙwallah Abba yashare a idonshi kana yace "wato wancin tsafi dabin bokaye har ta addanci kikeyi Jamila ? Innalillahi wa'innailaihi raji'un Allahumma ajirni fi musibatih wa'ahaliqni Khairan minhaa. Kinrigada kingama yimana tabo Jamila sedai kije zakiga abinki, sajad kuje da ita, cewar Abba.


"A'a kudakata karku fita da ita agidan domin zatayi muku tonon sililine kawai kurufeta awani ɗakin tukkunnah har zuwa wani lokacin....dukkanku juyawa sukayi suna kallon me magana, Umaima ce tsaye abakin ƙofar shigowa ɗakin, kafin wani yayi magana halima tace "Umaima tafaɗa cikin zumuɗin ganinta, hakan yasa isseta data farka tunɗazu takaicin Hajiya umma yahanata tashi yasata miƙewa yanzu itama tana kallon Umaima da halima tanufa. "Wacece wannan? cewar Abba. "Umaima ce ƙawar maah ɗin su Maryama Ammi tafaɗa tunda ita tasan Umaima tun a Gombe gidansu halima. "Da mamaki yace wacce maah kuma wacece ? Kuma miyasa ita wannan ɗin shigowa cikin zancenmu kaitsaye dami tazo?? Isseta tabuɗe baki zatayi magana kenan Umaima tarigata ta hanyar faɗar"yishiru Maryama ƴar Maryama shalelen gimbiya laweesat wannan bayanin nikaina banawa bane barasu daga bakin jiga jigan abin tafaɗa tana nuna bakin ƙofar inda gimbiya mardeeya tashigo cikin shigar bil adama ashe kamarta ɗaya sak da gimbiya laweesat dan bata yawan bayyana ne a shigarta yasa ba'sfahim hakan. Fuskarnan Tata aɗan kame babu yabo babu fallasa, murmushi Umaima tayi aranta tace mehali baya fasawa gimbiya mardeeya. "Maaah halima tafaɗa cikin zumuɗi, aɗan kaikace ta kalli halima sedai batace komaiba. Itakam isseta batayi maganaba domin tagano ba maah ɗinta bace sedai Batasan ko wacece ba amma dudda hakan bataji tsorontaba...sukuwa duka mutanen dake perlor kallonta kawai sukeyi anrasa wanda zeji magana, ahankali tabuɗe baki cikin muryarta me furgita ƴan maza tace "ba maah ɗinku bace gimbiya mardeeya ce kanwarta. Tunkafin tarufe baki general Aliyu yawani zaro ido tareda dafekai besan lokacinda yace "maciya ba domin bemanta haɗuwarsu agidan mejo ba.... dukkansu kallonshi sukayi har ita amma batace Mishi Komaiba. Magana taci gaba dayi "nibazance Komaiba domin magana abakin me ita tafi daɗi kufito bakin swimming pool ɗinku gimbiya laweesat najiranku, tana gama faɗar hakan takama hanyar fita, cikin sauri isseta tabi bayanta hakama mejo da halima...Ammi kuwa kallon general Aliyu tayi kafin tayi magana Abba yace Aliyu kurufeta a ɗaki kaida sajad kusamemu a swimming ɗin...to Abba yafaɗa kana suka nufi bedroom ɗin dazasu rufe Hajiya umma aciki tanata ihun se mejo yazo yakwanta da ita, Abin takaici.


Abakin swimming pool ɗin suka samu Hajiya Hannah da Alhaji abdussalam mama bintu...cikin mamaki Alhaji abdussalam yace "au Alhaji khamis dama baku tafiba?? Shima Abba da mamaki yace"kamarya bamu tafiba bayan gamu a Nigeria kainedai zan tambaya dama tare mukazo? Kafin wani yaƙara yin magana gimbiya mardeeya tace nice nan nakawosu, sabida hakan kunutsu. Tsit kowa yayi awurin amma banda isseta da gabaki ɗaya hankalinta na kan inda Ataga maah ɗinta.


Wani irin rugugi swimming ɗin suka farayi dama wurin babba be kamar wani Teku hakan aka yi shi... dukkanku kallon ruwan sukeyi cikin tsoro da mamaki yayinda isseta da halima suka washe baki domin sunsan alamar bayyanar maah ɗinsu ce....aiko basu gama tinaniba jelar kefinta ta bayyana shirgegen kifi asaman duk seda yakusa cinye rabin su, kafin tabayyana gabaki ɗayanta fuskartata ɗaukeda lallausan murmushi kamar yadda tasaba...amugun razane wasu daga cikinsu sukaja baya zasu arce sedai tozali dasukayi da gimbiya mardeeya tazama wata irin ƙatuwar macijiya amma daga samanta tana anan a yadda take yasakasu haɗiye wasu miyagun yawu cikin mugun tashin hankali da tsoro.. isseta kuwa tuni takai inda maah take har acikin. Ruwan tarungumeta ciki matsanancin farin cikin ganinta..shafa kanta tayi kana tace "wai yoshe Maryama ƴar Maryama zata

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login