Showing 63001 words to 66000 words out of 109347 words
Chapter 22 - MEJO NAJEB Book 1 Complete Hausa Novels By Autar Alheri .txt
mama tacewa Ummi takai anty hawwa part ɗinta tunda juwaira nacan sunzauna tare su ukku. 😱
Gombe
Abakin kogi
Isseta nahango rungume da maah ɗinta se shagwaɓa take zubawa yayinda Maah keta doka murmushi tana kaɗa jelar kifinta..
Cikin taushin murya tace "wai yoshene Maryama zata girmane? Tunda harna aurarda ita bata girmaba amma inaga laifin najeebullah ne nidakaina zan bashi shawarar yasakaki kigirma Hakan maybe kyadena taɓara, taƙarasa zancen tana shafa fuskar Isseta...baki tatura gaba kamar yadda tasaba tace"Allah ni maah nagirma bakigaba nazama ƙatuwa, tafaɗa tana ɗago hannun rigarta....kafin maah tayi magana umaima dake gefe tana kallon diramar uwa da ƴarta tace "iko se Allah maah kisako muna ƴar taki Hakan domin halima tuni takai asibiti tana jiran ƙawar tata.....murmushi maah tayi kana tace "shikenan umaima barana sallami maryama domin daga asibiti idan kungama abinda yadace karku dawonan kemaidata gidan mijinta. "To shikenan in sha Allah Hakan za'ayi. Cewar umaima.
Wani abun maah tamiƙawa Isseta ahannu kamar ƙololon daimon..seda Isseta takarɓa tariƙe shi sosai kana tace "maryama lokaci yayi da amminki zata samu lafiya biqudiratillah dama nasan haukarta bana asibiti bane amma alokacinda akakaita asibitin canne yafi dacewa da tazauna domin tasamu kyakkyawar kulawa shiyasa nabari kikakaita amma ayanzu inaso tadawo cikin hayya cinta kamar kowa sabida Hakan kijeda wannan idan kukaje asibitin kunemi asallameta daganan kukaita gun innar halima in sha Allah bazaku samu matsala da itaba...bayan kunkaita gidansu halima sekisamu zam zam kisaka wannan aciki idan yanarke ko bata tasha sauran kishafa mata akanta zuwa fuskarta in sha Allah itada hauka har ibada..wani irin waro ido Isseta tayi cikin mugun farin ciki tace "maah ammina zata warke? Dagaske zata dawo lafiya qalau kamar kowa?? Wayyoo Allahna maahhhh tafaɗa daƙarfi cikin ɗauki tarungume maahh ɗin tata.....Itama rungumetan tayi sosai kamin tacigaba faɗar sekuma abu na biyu maryama akwai wani labari daze riskeki acikin kwana kinan dan Allah duk lokacinda yasameki Karki ɗaga hankalinki kinji ƴata kisani duk abinda kijaji gaskiya ne Karkiyi kokwanto aciki....ahankali taɗago tana kallon maah ɗin tata kana tace "wanne irin labari ne wannan maah?? Tatambaya cikin mamaki...Zaki sani maryama duk ranarda kika haɗu da mamarki bintu yanzu dai kuyi sauri kuje kar halima tagaji dajiranku kinjiko...zatakomayin magana kawai Taganta bakin get ɗin shiga asibitin mahaukatan...ido tazaro atsorace tana waige waige idonta yasauka akan umaima dake tsaye tana murmushi..fuska takwaɓe kamar zata saki kuka domin tagano ɗauketa ne umaima tayi dankarta ƙara yiwa maah ɗinta wata tambayar...umaima kuwa bata batadamar yin maganaba tanuna mata halima dake can nesa dasu zaune tana bin mutanen dake wucewa wurin da kallo, ai aguje Isseta takwasa tana tunkarar halima cikin farin cikin ganinta
Halima kuwa nacan zaune kamar ance taɗago kanta aiko tayi ido huɗu da Isseta wani irin waro ido tayi tare da daka tsallen Itama tanufo Isseta ɗin cikin matsanancin farin cikin ganinta, gudusukeyi amma ganisuke kamar basa kaiwaga juna sabida tazararda ke tsakaninsu....gabaki ɗaya ma'aikatan dake harabar asibitin baki suka saki da hanci suna kallonsu...wani irin rungume juna sukayi atare suna sauke ajiyar zuciya lokacinda suka haɗu wuri ɗaya shakka babu waƴannan aminan sunyi matukar kewar junansu bakaɗanba dubada yanayinsu ayanzu...sunjima maƙale dajuna seda umaima Taga abin nasu banaƙare bane tazo kusadasu cikin tsokana tace "to tip da taya kuyi haƙuri Hakan muyi abinda yakawomu kinsan dai maryama nayiwa mijinki alkawarin zanmaidaki dawuri..ido halima tazaro cikin mamaki "Isseta mijifa naji tace dama aure kikayi? Bayan wanda abbanku yayi Miki lokacinda bakyanan? Aure akan aure Isseta? Duk atare halima kejero mata wannan tambayoyin...ɗan murmushi Isseta tayi cikin sexy voice ɗinta tace "duk ba abinda kike tunani bane halima amma zanyi Miki bayanin komai idan mukaje gida yanzudai please Ina ammina? Inamatuƙar so naganta...halima Bata ƙara cewa Isseta komaiba taja hannunta zuwa inda amminta take......baiwar Allah tana zaune kamar yadda tasaba ita kaɗai tana kallon wuri ɗaya...dasauri Isseta taƙarasa gareta tare da rungumeta tace ammina nayi missing ɗinki ammina yajikinki wlh naji daɗin yadda naganki kincanja Ammi bawanda ze kalleki yace bakida hankali Ammi idan bayasaniba, tafaɗa kamar memagana da wadda ke fahimtar abinda take faɗa tana share ƙwallar idonta...itadai Ammin kallonta kawai takeyi tana doka murmushi daya kayara mata kyau dagani kasan cewar taji daɗin ganin Isseta Sedai babu bakin magana.
Ɗagowa Isseta tayi tana kallon halima da Itama Ita ɗin take kallo sekawai tarungumeta tare da fashewada kukan farin ciki tana faɗar "ngd ngd sosai aminayata Allah yasaka muki da gidan aljannah tabbas samun ƙawa irinki zeyi wahala aduniya halima kintayani aikin alkhairi danakeyi munyi tare kuma anzo daga baya bana'nan kuma kika ɗora daga inda natsaya yanzu kalli yadda Ammi Takoma Sam bawanda zece batada hankali Inba yasaniba niko ma zanyi Miki aduniya halima? Inba addu'a ba alhmdllh alhmdllh alhmdllh Ina godiya ga Allah ina gode miki Allah yabamu iKon riƙe amintakarmu har mutuwa...Ameen y hayyu y qayyum Isseta Dan Allah kedena wannan zantukan nima Ammi uwace agareni kamar yadda kika ɗauketa nima Hakan naɗauka dudda cewar bamusan ko wacece itaba amma Hakan baze canja mata suna na uwa agaremuba dan Allah kiyi shiru kawai da bakinki.
"Gaskiya kam yanzu kuje kusaka asallameta kuzo muje lokaci na tafiya, cewar umaima. "Sallama kuma ainaga haryanzu bawarkeba, halima tafaɗa cikin mamaki..."eh halima Maah ce tace ayi Hakan kuma idan ansallameta akaita gurin inna tazauna. "Inna agidanmu kenan? Halima taƙara tambaya.."eh a can, Isseta tabata amsa atakyaice. Baki halima tawashe cikin farin ciki tace to muje asallametan tafaɗa tanayi gaba domin baƙaramin daɗi tajiba da Isseta tace agidansu Ammi zata zauna....murmushi sukayi kamin sunufi gun amaikatan Ashe Ammi namaƙale da mayafin Isseta tariƙe shi tamau kamar wata me hankali dan karta tafi tabarta,,su Sam Basusan abinda kefaruwa ba seda wata ma'aikaciyar wurin tayi musu magana tukunnah...dasuka juya suka ganta murmushi kawai sukayi dukkansu Isseta tace "ayya ammina yi haƙuri yau ƙafana ƙafarki in sha Allah...daga Hakan suka gayawa ma'aikatan buƙatarsu,,cikin sauƙi kuwa suka amince tunda sunga babu wata matsala dama agun marar lafiyar tasu kawaide dan Batasan abinda takeyibane...ahakan dai suka yi duk wani abinda yadace suka sallami Ammi daga anan umaima taɗaukesu dukkansu bata ajiyesu Ako inaba se gidansu halima...!
Kuyi haƙuri da wannan anjima zaku samu wani in sha Allah.
Kuma iname matukar baku haƙuri akan rashin update 2 days bawai da gangan nayi Hakanba kawai uzirine ya gitta I'm very very very sorry please I'm very sorry for that all. 🙏
Autar alheri ✍️
🪽🪽🪽🪽🪽🪽🪽🪽🪽
MM _ NN
Book 4
Page 67 & 68
"Acikin soron gidan kuma setayi zamanta anan halima da Isseta kuwa suka riƙa hannun Ammi suka nufi cikin gidan...abakin panpo sukasamu innar halima tana wankin kayan sakawa.
"Innarmu oyoyo innarmu cewar Isseta tana rungume innar halima datasaki baki kallonsu. "Maryama kece Hakan? Allahu Akbar maryama ina kikaje ne? Ina kikashiga aduniyarnan Maryama?
Ina kikadosa alokacinda kikabar gidan mahaifinki? Maryama miyasa kakayi Hakan kina ƴamace? Maryama miye anfanin zamanki tare da halima idan bazaki iya ɗaukana uwa agarekiba, tanacikin maganar kuka yaci ƙarfinta...cikin sauri Isseta taƙara rungumeta sosai ajikinta cikin kukan itama tace "please innarmu Dan Allah kiyi haƙuri nayi kuskure amma kiyafemun wlh duk abinda kike tunani bahaka bane amma zanyi Miki bayanin komai dan Allah kiyi shiru...."bakomai maryama babu komai tafaɗa tana share ƙwallar idonta...hannunta Isseta taja sukaje suka zauna akan shimfiɗar da Halima tayi tazaunarda Ammin Isseta....Seda suka zauna tukunna Isseta taƙara bawa innar halima haƙuri tukunnah tashiga bata labarin abinda yafaru tsakaninta da mutanen gidansu abbanta yakoreta dakumu inda taje har kawo yanzu datake gidansu mijinta....tunda Isseta tafara bawa innar halima labarinta take kuka cikin mugun tausayin yarinyar shakka babu Taga rayuwa dominma Allah yatemaketa da wannan baiwar Allah (maah kenan) tashiga lamarinta da ba'asan iya inda abin zekaiwaba Allah yaƙara tsare gaba..
Kallon Ammi tayi tace "wannan baiwar Allah fa daga ina kukazo da ita?? "Ammin Isseta ce inna itace wadda nake zuwa gunta asibitin mahaukata wadda kike bawa abinci idan zanje nakai mata.."ahh too Masha allah itace aibanganetaba halima tunda naji kince batada hankali amma kuma naga wannan kamar lafiyarta qalau.. "Hakane wlh inna bawanda zega Ammi yace batada lafiya kawaide dan bata maganane yanzuma Maah ce tace akawota wurinki Anan zata ɗan zauna kwana biyu muga yadda jikin nata yayi...Hakane kam to babu damuwa ai Allah dai yabata lafiya..Ameen y Allah suka amsa atare kana Isseta tace "inna akwai zam zam agidannan kuwa?? "Eh akwai barana ɗauko Miki tafaɗa tana Miƙewa domin taɗauko mata...Suna'nan zaune suna jiranta segata ko tadawo da gorar zam zam ahannunta tamiƙawa Isseta ɗin...bayan ta karɓa tayi kamar yadda maah Tagaya mata na saka wannan ƙololon acikinsu..
Acikin gari
Sosai brothers ɗin Isseta suka hargitsa garin gombe wurin neman ƙanwar tasu..domin kuwa nazeer yasanarda wani abokinshi yaron minister kuɗi dake garin Abuja wato fadeel sosai fadeel yashiga tashin hankali inda yabaza jami'an tsaro akan neman Isseta kab garin gombe dama wasu garuruwan dake cikin Nigeria....lokacinda su police ɗin suka Nemi picture ɗin yarinyar don anemota dakyar akasamu wani wanda suke tare itada zubaida da halima tun suna ƴan 10 year Kuma yanzu Isseta tazama cikakkiyar budurwa amma ba yadda za'ayi doline dashi za'ayi anfani wurin nemanta tunda babuwani, dashi suka shiga neman Isseta babuji babu gani..tofa Hakan yasa sosai police suka haddabi garin gombe babu shiga babu fita indai bayazama doliba kuma kowacce mota zata wuce se anbinciketa tukunnah zata samu damar wucewa ko governor jihar gombe dayaji labarin abinda police keyi a jihar yabincika se aka gaya mishi ƴar shugaban ƙasar Niger ce ta ɓata Alhaji Abdussalam idiris...aiyanajin Hakan yace aƙara lunka bincike da'akeyi duk inda wannan yarinyar tashiga abincikota yabada kwana ukku.😱 Tofa abu yabirkice agarin gombe abaki ɗaya duk wanda kecikin garin yasanda labarin ɓatan ƴar shugaban kasar Niger Hakan yasa abin ya fara yawo a social media.
Gidansu Isseta
Yan kai amarya sun dawo lafiya Sedai sunzo suntararda baƙon al'amarin agarinsu dama gidansu baki ɗaya domin suna sauka kozama basuyiba samarin gidan suka Basu labarin abinda yafaru tundaga farkon zuwansu Hajiya Hannah harkawo yanzu...tunda mamansu yah balah taji wannan zancen hankalinta yayi mummunan tashi tanemi nutsarwa tarasa domin kuwa Taga zahiri tunda bataga iyya hassi ba agidan gaya kuma anbirkita garinsu sabida nemanta, "innalillahi wa'inna ilaihiraji'un to wai duk ya'akayi Hakan tafaru ya'akayi duk zamanda sukayida wannan yarinyar basusan cewar ba ƴar gidan bace seyanzu da rana taɓace? Wama zaatayiwa wannan tambayar acikin mutanen gidan? Mama bintu ko mlm Musa shida batama ganiba? Tab dijam lallai sun ɗaukowa kanshi jidalin dayafi karfinsu,,,tanacikin wannan zancen zucinne cikinta yamirda tasuri buta takewaya....afannin yaran gidan kuwa sosai zubaida da jidda suka yi farin cikin jin labarin Isseta ƴar wani babba ce ba ƴar gidan ba fatansu kawai ayanzu Allah ya bayyanata..anty bilki kuwa batayi farin ciki ba kuma batayi baƙin cikiba domin ita damuwarta ɗaya ce ƙwallafa ran datayi akan Isseta tasan ba samunta zatayiba domin kam koda anganta ayanzu tayi matanisa....haka dai gidan yazauna wasu na farin ciki wasuko na cikin magun tashin hankali yayinda yawon shiga ban ɗaki yaɗaurawa Mamansu yah balah aure.
South Africa
Jirginsu mejo Najeeb nasauka sekuwa ga motar hotel ɗin dasukayi bukking tazo ɗaukarsu dama su biyar sukaje captain Jameel, captain Ameer, sekuma su jagororin tafiyar...bayan sunje hotel ɗin kowannensu yaɗauki ɗaki ɗaya amma general parlor ɗaya ne bayan sunyi wanka sun huta duk suka bayyana a perlor suna fira inda kowannensu yabuɗe wayarshi tare da seta wayar da network ɗin ƙasar yadda Zasu iya magana a akowacce ƙasa batareda sunsaka layin ƙasar ba....aiko suna buɗewa Kiran Alhaji Abdussalam idiris nashigo wayar general faruk...cikin girmamawa yaɗaga yana gaida shugaban ƙasar nasu...Seda suka gama gaisawa kana Alhaji Abdussalam yashiga gaya mishi abinda kefaruwa dashi na ɓatan ƴarshi...cikin mugun mamaki general faruk yace "ranka yadaɗe dama Kanada ƴa mace bayan su sapwan?? "Eh faruk itace ƙanwarsu dan Allah idan kundawo daga tafiyar dakukayi kanemi temakon sojojin Nigeria wurin nemanta please, yafaɗa araunace cikin neman alfarma kamarba shugaba ba....ajiyar zuciya general faruk yasauke kana yace "shikenan ranka yadaɗe in sha Allah zamuyi iya baƙin ƙokarin mu Nida ƴan uwana zan sanar musu sutayani nemanta amma aturo muna picture ɗinta.. "toh shikenan za'aturo in sha Allah ngd sosai faruk.. "bakomai ranka yadaɗe Allah dai ya bayyana mana ita...ameen y Allah...daga Hakan sukayi sallama.
"Miyake faruwane General?? Cewar general aliyu. "Wlh yarinyar shugaban kasarmu ne ta ɓata a Nigeria nan yabasu labarin abinda kefaruwa kamar yadda Shima alhaji Abdussalam ɗin yafaɗa mishi yanzu.. tunda yafara maganar gaban mejo Najeeb kefaɗuwa besan daliliba amma zancen yadakeshi sosai domin jiyayi kamar maryam ɗinshi ce taɓata🤩(alsarki mejo rashin sani tafi dare duhu) general aliyu kuwa sosai yajajanta abin shida su captain Jameel daganan suka shiga tsara yadda Zasu fuskanci abinda yakawosu..
Gombe
Gidansu Halima
Wannan ƙololon na narkewa Isseta taɗauki ruwan taɗorawa amminta abaki tare da temakon halima suka samu tashinye kana suka shafe mata sauran akanta zuwa fuska kamar yadda Maah ta umurceta, bayan sungama suka zuba mata ido kawai suna kallonta kusan minti 10 basuga sauyi atareda itaba har aka yi minti 40 har sun fidda rai suna tunanin maybe bayanzu abin zeyi aiki ajikintaba kawai sukaga tafara hamma tana miƙa kamar wadda ake miƙewa duka kasusuwan jikinta namiƙewa arazane duk suka yi kanta suna neman riƙota kawai se sukaga tayi baya tafaɗi kwance se bacci.....dukkansu da ido kawai suka bita cikin tsoro da fargaba innar halima kuwa se addu'a take tofa mata domin dukkansu sun tsorata, kusan minti 30 tana akwance kamar matacciya sekawai sukaga tabuɗe idonta tare da yunƙurin mikewa zaune tana salati da bakinta take faɗar hasbinallah wani'imalwakin wani imalmaula wani imalnaseer...ido suka zaro atare suna ƙokarin temaka mata tamiƙe zaunen cikin mugun mamaki da tsantsar farin cikin ganin yau ɗaya sunga maganarta ara yuwarsu...seda tazauna Dede tukunnah tashiga binsu da kallo kamar yadda suma suke kallonta kafin tabuɗe bakinta dayayi mata nauyi dakyar tace hubbey...!
Autar alheri ✍️
🪽🪽🪽🪽🪽🪽🪽🪽🪽
MM _ NN
Book 4
Page 69 & 70
"Kallon juna akayi tsakanin Isseta da halima kamin Isseta tayiwa wannan baiwar Allah kyakkyawar runguma tana fashewa kuka cikin kukan take faɗar"Alhmdllh Allah alhmdllh ammina wayyo daɗi halima ammina tasamu lafiya Allah nagodema Ammi tadawo hayyacinta alhmdllh sekuma tasake sake saka kuka cikin mugun farin cikin datakeji aranta...ahankali Ammi taɗago hannunta Itama tana ɗan buga bayan Isseta alamar rarrashi Itama idonta tab da ƙwallah sedai kuma murmushi takeyi, sunjima ahakan kamin Isseta taɗago daga jikinta tana kallonta tana sakin dariyar farin ciki....halima ma ahankali tarungume ta tareda faɗar "tabbas kuwa Isseta Ammi tasamu lafiya doline kiyi kuka amma na farin ciki Allah mungode ma dakabawa wannan baiwa taka lafiya, Taƙarasa zancen tana ɗagowa daga jikinta Itama tana murmushi.
Itadai Ammi da ido kawai takebinsu tana murmushin yaƙe amma takasa cewa komai, ganin Hakan yasa innar halima cewa "sannu baiwar Allah. "Ido tazubawa innar halima ɗin kafin tabuɗe bakinta dake mata mugun nauyi tace yawwa sannu,,,tana cewa Hakan sekuma tabi gidan da kallo tare da maida idonta akan innar halima tace "baiwar Allah dan Allah nan inane? A,ina nake? Ina hubbey? Ina jazlan? Ina yayana? Ina matarshi ? Mikuma nakeyi anan ɗin? Kuɗin suwaye? Duk atare tarinƙa jerowa innar halima tambaya babu ko pustop 🤩
"Nisawa innar halima tayi kana tace "nan garin gombe ne baiwai Allah kuma duk waƴannda dakike tambaya mu bamusan kowa ba daga cikinsu kekawai muka sani...idon Ammi ne suka ƙara cikowada ƙwallah tace "gombe inane kuma gombe? Tatambaya ga dukkan alamu tunkamin wannan matsalar tasameta batasan inane gombe ba. "Garine baiwar Allah acikin ƙasar Nigeria yake keba ƴar Nigeria bace halan? Ƙwallar data cika idontace tazubo mata kamin tace niba ƴar Nigeria bace minene zekawoni Nigeria kuma? Innalillahi wa'inna ilaihiraji'un dan Allah kukaigi gun ahalina Ina matuƙar kewarsu, Taƙarasa zancen cikin kuka.
Isseta da halima ma kukan sukeyi suna kallonta...yayinda innar halima ke share ƙwalla afakaice kar yaran nata suga rauninta tace "wlh baiwar Allah bamusan komaiba gamedake domin wannan yarinyar dakike gani itace sanadiyar haɗuwarmu dake kamar yadda suka bani labari tace wata rana tafito zataje isilamiyya ne taganki kwance bakida lafiya agefen wani shago babu kowa awurin, tayi ƙokarin temakawa takaiki gidanki domin atunaninta ke ƴar uguwarce sekuma Taga batasankiba data tambeki ananne tagano akwai alamun hauka ataredake dubada kalar shigar jikinki dakuma yanayinki to daganan setakaiki wani kangon gidan biredi ta'ajiye ki taje tasiyo ruwa tawanke Miki baki tukunnah tabaki maganin ciwon ciki sekikaƙi sha abin yabata mamaki sosai sedai ganin yadda kiketa dafe cikine yasa tayi tunanin ko yunwace kikeji Hakan yasa tanufi gidansu taɗauko Miki abinci abinmamaki kuwa sekika karɓe abuncin dasauri kika hauci wannan abin yatsawa wannan yarinyar arai sosai daga wannan lokaci tafara dawainiyar kulawa dake tamkar mahaifiyata tamaida Miki gidan biredi tamkar gidanki kullun tana kan hanyar gyaranki keda muhallin datayi Miki kayan abinci kayan anfani omo sabulu komai ajiye Miki takeyi kamar yadda ake ajiyewa kowacce mace dudda cewar bakyayin anfani dakomai Sedai idan itace tazo tayi Miki kuma tundaga lokacin kike zaune agidan biredin Bakije ko inaba kina zaune aƙarƙashin kulawar ta har inda akazo lokacinda tamaidaki asibitin mahaukata dake garinnan domin sama Miki lafiya abisa temakon wata baiwar Allah wadda Bama jinsinmu ɗaya da itaba, bayan Maryama tayi aurene ƴar uwarta taci gabada kula dake acan asibin har izuwa yau da ita wannan baiwar Allah tace suɗaukoki sukawoki wurina kuma tabasu maganin dasukayi Miki anfani dashi cikin iyawar Allah da buwayarsa gashi kinsamu lafiya.....tunda innar halima tafara magana Ammi takafeta da ido ko kiftawa batayi babu abinda kemata yawo akai se kallimar hauka, tambayar datake yiwa kanta ɗaya ce wai itace mahaukaciya? Itace tayi hauka? To garin yaya? Ina ahalinta suke? Miyakawota Nigeria? Gabaki ɗaya ƙwaƙwalwarta tatoshe..wani irin kukane yazo mata me cinrai sosai takeyinshi tana girmama ubangijinta dayayi mata wannan jarabawar domin haqiqa shine kawai ze iya jarabtar bayinsa aduk ta hanyarda yaso babu mahani.....Isseta ma kukan takeyi hakama halima...sosai Ammi tayi kuka tajima tanayi kamin tatsagaita tashiga rarrashin su Isseta Hakan tasakasu ajikinta tana shafa bayansu, cikin muryar kuka tace "ngd ngd sosai yarnan sekuma kuka yaƙara cin ƙarfinta...cikin sauri Isseta tarufe mata baki tare da faɗar"dan Allah kiyi shiru Ammi dan Allah karkice komai ni wlh duk abinda nayi Miki nayine sabida Allah kuma wlh tamkar mahaifiyata Hakan nakejinki araina bantaɓa yimiki wani kallo wanda bana uwa ba dan Allah idan har kin ɗauke ni ƴarki karki ƙara yimana dogiya albarkarki kawai muke buƙata Ammi...ɗan murmushi Ammi tayi kana tace "Allah yayi muku albarka Allah yabiyaku da gidan aljannah