Showing 105001 words to 108000 words out of 109347 words

Chapter 36 - MEJO NAJEB Book 1 Complete Hausa Novels By Autar Alheri .txt

14 Jan 2025

14443

girma ne kose jikar Maryama ko jikinta sunzo duniya tukkunnah? Tafaɗa cikin sigar tsokana tana mannawa isseta kiss a goshi, kana ta ɗago tana karewa mutanen wurin kallo kafin tamayarda dubanta ga gimbiya mardeeya


"Miye hakan mardeeya zaki razanasune?? Cewar maaah...baki gimbiya mardeeya ta ɗan taɓe kana tace "ko ɗaya zasu gudune sanida ganinki batareda munyi abinda yakawomuba kuma idan razanarwane kece ai kika fara Kinwani zo kamar zaki tada gidan daruwa... murmushi kawai gimbiya laweesat tayi kana tace "assalamualaikum jama'a dan Allah kunutsu magana mukazo muyi daku ba'abinda zamuyi muku domin muma Musulmai ne bazamu iya cutarda kowaba se wanda yacuci kanshi, taƙarasa zancen da alamar roƙo. Cikin sauri isseta tace "Ammi maah ɗitace fa wadda tabaki magani mama bintu maah ce wadda nazauna wurinta alokacinda Abba ya koreni...se lokacin suka san saki jikinsu...cikin sakin fuska Ammi tace Masha Allah tabba Maryama da halima suna bani labarinki ashe Allah yayi zanganki baiwar Allah ngd sosai da ɗawainiyar ki akan ahalinmu Allah yabiyaki da aljana..Ameen ya Allah.


"Maah Kinga little mom kinshareniko? Cewar mejo idonshi na cika da ƙwallah... murmushi tayi kana tamiƙa Mishi hanninta alamar yazo...bamusu kuwa yasaka hannushi anata. "Najeebullah tafaɗi sunanshi tare da shafa kanshi. "Na'am maah. "Yayane yaron maah? Tatambaya domin tasan izuwa yanzu zuciyarshi atunkushe take da ƙunci amma idan yasamu yayi magana abin ze ɗan faɗa Mishi. "Maah naganota Maah duka zancenka gaskiya ne tabbas nagano wannan yarinyar kuma na tabbatar bazata taɓa barinaba kamar yadda kika faɗa kuma tadawomin da giɓin dana rasa arayuwata wato mahaifiya gashi kuma ta hanani ita duka kamar yadda kika faɗa itama taba duƙarta, Maah ashe dama little mom ce wannan yarinyar dake bani kariya a mafalki amma kikaƙi gayamin sedai kika bani ita? Ashe dama Hajiya umma itace keson ta hallakani itace cikin mace ta huɗu bayan yayun little mom? Maah wai Hajiya umma keson nayi lalata da ita? Wai itace ke leƙani abayi idan ina wanka wai itace keson nayi ma'amala da ita tamkar little mom Maah miyasa rayuwata tazo ahakan? Miyasa baki gayaminba tun farko na ƙauracewa wannan matar? Miyasa baki gayamin cewar ba ita bace mahaifiyata ba? Miyasa duk kika ɓoye mun wannan abun?? Yaƙarasa zancen yana sakin wani sabon kuka.


Kanshi gimbiya laweesat tashafa cikin rarrashi tace "ya isa najeebullah kayi haƙuri da yadda ƙaddara tazoma hakan Allah ya tsara ba abinda ze canjata, awancan gaya maka wacece jalima da aikinta ko abinda ke hannun Maryama duk bashida anfani sabida zaka kalli abinne a hagunce shiyasa nace ma kayi haƙuri komai Lokacine ze bayyana makashi zaka Ganshi da idonka kuma gaya kagani. Ɗan shiru tayi tana kallon mutanen wurin kana tacigabada da faɗar "yanzu ba kuka yadace kayiba godewa Allah ya dace kayi, mahaifiyarka ta bayyana agareka Hajiya jalima batasamu nasarar abinda takesoba akanka, yarinyar dakakeda burin mallaka tazama mallakika kaga kuwa ai addu'a yadace kayi da godiya ga Allah bawai kukaba...sekuma ta ɗago tana kallon mutanen dake wurin wanda suka maidasu kamar tv, murmushi tayi kana tace Bara dai nafara gabatar muku da kaina domin nasan shine abinda kukafi ƙaguwa kusani ayanzu.


"Sunana gimbiya laweesat taredani akwai ƙanwata gimbiya mardeeya gakuma ƙawata Umaima, Bara kuji yadda akayi nashigo rayuwar ahalinku...anan gimbiya laweesat tafara basu labarin tun farkon lokacinda mlm Mahaifin mama bintu yafara nemota akan aikin Hajiya Hannah hartayiwa Hajiya Hannah magani da yadda tarinƙa bibiyar rayuwar Hajiya Hannah har izuwa inda Takoma bibiyar isseta dakuma yadda akayi tasaka isseta nemawa Ammi magani harkawo lokacinda mlm Musa yakori isseta da lokacinda ta haɗa ta da nejo, har akazo inda gimbiya mardeeya tafara maidawa Hajiya jamila martanin abinda take yi dakuma lalata duk wani mugun aikinta tun lokacinda taraba mejo da ciwon data turo Mishi har inda ta kashe tsijuju harkawo yanzu da komai ya bayyana, seda takai ƙarshe kana tanisa tace kunji yadda akayi gimbiya laweesat da sister's ɗinta suka shigo rayuwar ahalinku.




Aitunda maaah tafara magana Ammi Hajiya Hannah Hajiya mama ke kuka wiwi hadda mama bintu,,,,su isseta da halima jidda Ummi kuwa duk ba'azancensu domin kuka sukeyi kamar wa'yanda ake zarewa rayuwa... Alhaji abdussalam da Alhaji Khamis ma kukan sukeyi hakama mejo da general Aliyu...gabaki ɗaya kowa kuka yake yi suna tunanin wannan ifta'in daketa faruwa acikin ahalinsu daga gefe ɗaya kuma suna godiya ga Allah daya turo wasu daga cikin bayinsa suke temakonsu akan abinda basu isa suma sandashi ba balle suyi ƙoƙarin yin maganinshi...sosai suka bawa gimbiya laweesat da Umaima tausayi dudda gimbiya mardeeya da bata cika damuwa da abubuwa ba awannan karon seda ta tausaya musu, daƙyar gimbiya laweesat ta rarrashesu cikin kalamanta masu sanyaya zuciya...bayan duk sun natsune tashiga yimusu nasiha meratsa zuciya akan rayuwa da abinda ke cikinta kana ta gaya musu bazasu bar rayuwarsu sunatare akoda yaushe domin sun rigada sunzama ƴan uwan juna....sosai su Abba suka shiga yimusu godiya dukkansu cikin soyayyar bayin Allah da Allah ya saka musu azuciarsu lokaci ɗaya....isseta kuwa cikin sanyi jiki tasaki Maah tare da nufar gimbiya mardeeya dake naɗe amacijiyarta..tana zuwa bata tsaya komaiba tafaɗa jikinta tare da rungumeta sosai tana sauke numfashi..se ayanzu gimbiya mardeeya tayi murmushi ganin isseta bataji tsorontaba se abin ya birgeta tashiga shafa bayanta, ahankali tace "i love You momma, tafaɗa tana ƙara ƙanƙame ta ajikinta... Murmushin gimbiya mardeeya yafaɗaɗa yau isseta takirata da uwa, cikin jin daɗi tace "i love You more ƴar lelen anty lawee, tafaɗa cikin barkwanci. "Nifa momma? Tatsinkayo Muryar mejo najeeb... murmushi taƙarayi kana tace "i love You yaron Maryama kuma mijin Maryama ɗan gaban goshin gimbiya laweesat shalelen Hajiya Hannah da abdussalam. Wani irin daɗi ne yarufe mejo wanda yakusan mantar dashi damuwarda yake ciki....duka mutanen wurin seda sukayi dariya, cikin nishaɗi Umaima tashafa kan Munir wanda kallo ɗaya zaka Mishi kasan cewar yana cikin kunci..aiko se yaji kamar ancire Mishi ƙaya azuciya, yasaki jikinshi aka cigaba da fira...sosai su gimbiya laweesat suka jima awurin suna tattaunawa akan rayuwa da abinda yashafeta kafin suyi musu sallama suka tafi cikeda kewar juna.


Bayan tafiyarsu Abba yasaka General Aliyu ɗauke Hajiya umma akaita gidan ma haukata sedai suna buɗe ɗakin tabankesu tare da kwasar akuge tana ihu tana wlh seya cuta itabaza yardaba seya kwanta da ita tanayi tana tura hannunta gaba gareta,,,dagudun gaske suka dafa mata sedai kafin su risketa tuni ta ɓacewa ganinsu, hakan sukayi bulayin nemanta suka gaji doli suka dawo gida.


Bayan mako biyu... acikin wannan makon biyu sosai wannan ahalin sukayi jimamin abinda ya faru dasu daga ƙarshe kowa ya watsarda abin tunda Allah yakawo musu shauƙinshi, acikin wannan lokacin ne akayi neman auren general Aliyu da halima haka mutanen Niger sukazo nemawa general Faruk auren Ummi aka nemawa nazeer auren mufeedah hadda Alhaji abdussalam hakan yasa aka wuce Gombe aka nemawa Sapwan auren zubaida agidansu isseta, daganan aka tsayar da rana wata ukku masu zuwa...awannan lukacin gidansu isseta yakoma kamar inda ake zaman makoki domin kuwa kowa yayi karatun ta nutsu, tsaida wannan ranar ne yasa mlm Musa cewar su anty hawwa sufitarda miji domin aranarda za'ayi auren zubaida aranar suma ze ɗaura musu aure da koma waye....jidda koda tadawo gida taga gidan ya canja bawanda yayi yunƙurin gaya mata abinda ya faru dubada mahaifiyarta ce tayi wannan aika aikan.


A Lagos kuwa sosai ake zaune lafiya cikin farin ciki da ƙaunar juna tsakanin Ammi da mama,,,,hakama yaransu kamar ba wani abinda ya faru har auta siyana dabatasan abinda yafaruba kuma bata tambayi mahaifiyar tataba fidda cewar bata gantaba Allah yashafe mata abin aranta....Munir ne ma wani lokacin abin ke ɗan taɓashi domin yana masifar jin kunyar mejo najeeb da Ammi...fahimtar hakan yasa Ammi sakashi ajikinta tamkar itace ta haifeshi tana ƙoƙarin kwantar masa da hankali domin karya saka abin Aranshi....hakama mejo sosai ake sakashi ajikinshi fiyeda yadda yake yi ada.... Isseta kuwa kusan kullun tana gidan Abba se mejo yayi da dagake takebinshi gida ko in jarabar Tata tashi domin abin har mamaki yake bawa mejo...yau ma kamar kullun suna zaune a perlor gidan Abba dukkansu Itako tana kwance tayi matashin kai da cinyar Ammi, ta kalli Ummi tace "please Ummi wai akwai garin rogo gidannan? "Garin Togo kuma cewar Hajiya mama? "Eh mama wlh teba nake sha'awarci se muje muyi. Ikon Allah lallai kam babu garin rogo agidannan sedai anemo miki. "Hhhh barana siyo mata Ammi ai inaga cin garin rogon namune mune sila Munir yafaɗa cikin nishaɗi domin shi yajima yana yimata kallon me ciki, kuma dama ba kunyace dashiba, dariya mutanen perlor sukayi,,,,shiko Munir yamiƙe yafice.....ko minti 40 beyi da fitaba yadawo ɗaukeda manyan ledojo da kayan ƙwalam bayan garin rogon...aiko tashiga buɗewa agwaima ce da mango se samiyan birai se kayan chocolate masu shegen yawa acikin...cikin farin ciki yashuga wankin agwaima tanasha kamar wata zarriya...Itako Ummi taɗauki garin rogon tanufi kitchen domin tayi mata tebar...!






























Autar alheri ✍️🪽🪽🪽🪽🪽🪽🪽🪽🪽🪽


MM _ NN


Book 6


Page 109 & 110




"Ikon Allah 🤔 cewar Hajiya mama,,,,dariya sajad yayi kana yace anty nazo kisammin please.."ɗagowa tayi tana hararshi kana tace tab ɗijam baka siyominba kuma ka karɓe nawa, aikuwa bazan bakaba. Tofa anty abun hadda rowa? "Eh ɗin, kafin tarufe bakinta tafigi agwalimar dake gefenta, ihu tabuga tana faɗar Ammi kinganshi ko Allah seka bani abuna.




"What happened my little mom? Waya taɓaki, cewar mejo da shigowarshi kenan yaji ihunta...dukkansu da kallo suka bishi, Itako cikin taɓara tamiƙe tare da nufar shi,,,cikin sauri yatarota tafaɗo jikinshi, "minene sweet life waya taɓa ki? Yatambaya aɗan rikice domin kuwa duk abinda zasuyi agaban kowa suke yin abinsu babu ko kunya...baki tatura gaba kana tanuna Mishi sajad dake zaune kamar yadda yara keyi...dakallo yabi sajad kafin yace mata minene? Ganin sajad ɗin na dariya gaya kuma duk su mama na wurin da babu abinda ze habashi ɗan lallasa sajad ɗin. "Bashi bane yakarɓe min agwalima da Munir yasiyomin yanzu.. "to akanme ze karɓe Miki? Kyaleshi muje gida nasiya Miki wani tunda yazama ƙaton banza me karɓe abin little mom, yafaɗa yana hara rar sajad. "Kai sajad Allah zan saɓa maka bata abunta kajiko aikoma minene babyn ku ne yasakata yinshi amma kazo kana sakata kuka, Hajiya mama tafaɗa tana dungurewa sajad kai...ido suka waro daga sajad ɗin har mejo da ita isseta, cikin mamaki mejo kebin isseta da kallo, shiko sajad cikin zumuɗi yace "kai haba mama juna biyu ne da anty? "Sosaima kuwa ko kuma tantama ne? Zeyi magana kenan sega ummi tafito riƙeda plate ɗin data zubo mata teba, ci kin sauri ta karɓa kamar mayya tazauna tare da zazzaga yaji tahauci babuji babu gani...dukkansu baki suka saki suna kallonta cikin mamaki musamman mejo,,,,Seyanzu wasu abubuwa datakeyi suka dawo Mishi akai, kamar irin yawan son sex kuma idan anyi tariƙa zazzaɓi yawan maƙale mishi, ci wancan tarkacen ci wannan duk tabi ta yamutsa kanta gakuma ƙiba datayi kamar zata fashe, ajiyar zuciya yasauke tare da sakin wani shi'umin murmushi farin ciki batareda yace Komaiba yazauna yana jiran tagama cin tebar sutafi....seda tagama ci tukunnah Ummi takoma saka mata wata a kula tukunnah suka tafi sajad da Munir se tsokanarta sukeyi, suna fita memakon yawuce da ita gida sekawai yawuce asibiti gun Dr ziyad, bayani yayi mishi na abinda yakeso cikinko ƙanƙanin lokaci akayi komai aka gama inda aka tabbatar mishi da tana ɗauke da ciki natsawon wata biyu da sati ɗaya...cikin farin ciki yashiga yiwa Dr ziyad godiya Aranshi yana tunanin kenan tun zuwan Farko ƙwallonshi yashige raga🤩 ahakan yaɗauke ta suka tafi gida...tundaga wannan lokacin yalunka kulawarda yake bawa isseta sex ko se idan tace tagaji kullun suna maƙale da juna kamar wani yace ze rabasu....hakama su Hajiya mama da Ummi tasu kulawar ta musamman ce da Alhaji Khamis, alokacinda labarin cikin isseta ya riski mutanen Niger Hajiya Hannah kamar tazuba ruwa aƙasa tasha dan murna, hakan rayuwa taji gabada tafiya acikin wannan ahalin cikin farin ciki da ƙaunar juna, kamar ba wani abun daya taɓa faruwa acikinsu.




Bayan wata ukku.


Wanda yayi dede da cikar wata shida ga cikin isseta kuma dede da lokacin aurensu general Aliyu da general Faruk...shirye shiryen biki akeyi akowane fanni daga Niger har Nigeria da Gombe. Gibdusu isseta kuwa tuni anty bilki tasamu wani saurayi agarin yazo yana sonta yanzu dashine za'adaura aurenta..Anty hawwa kuwa bata samuba kullun cikin fargaba take akan hukuncin da abbansu ze ɗauka akanta gaya saura kwana biyu duka ɗaurin auren, duk tazama wata iri kuma iya gwargwado sun nutsu dukkansu yaran gidan hakama mama salmu kullum cikin istigifari take da neman yafiyar uban giji dakuma mlm Musa tayi nadamar abinda ta aikata babu adadi.


Afannin angaye kuwa kullun suna busy har general Faruk yatare Nigeria hakama su nazeer da Safwan duk suna gidan Abban mejo gun Ammi wato gwaggonsu..su mejo anzama busy koganinshi wahala yakewa isseta,,,gaya itama ba abayaba domin kuwa itace agun halima itace Ummi itace mufeedah kullun tana hanyar zuwa Gombe da gidansu General Aliyu, daga ƙarshe dai Ammi tasaka aka ɗauko duka Ameenen suka tare gidan isseta acan aka kai musu megyaran jiki ciki da waje, hakan yayiwa isseta sauƙin yawo kodan tsohon cikinta.


Tofa rana bata ƙarya akace sedai uwar ɗiya taji kunya ayau assabar ne dubbannin mutane suka sheda ɗaurin auren general Aliyu Abubakar Gombe da halima mukhtar Gombe, general Faruk Yusuf maraɗi da Maryama Khamis sahabi(Ummi) se nazeer abdussalam Idris maraɗi da mufeedah Abubakar Gombe, dukkansu a babban masallacin juma'a dake cikin unguwar banana island acikin garin Lagos, semuce Allah yabada zama lafiya...daganan suka wuce Gombe inda aka ɗaura auren zubaida Musa Gombe da Sapwan abdussalam Idris maraɗi....bayan angama wannan gagarumin ɗaurin aurenne kana aka daura na anty bilki da saurayinta haka aka daurawa su yah balah da hafizu suma da wasu cousin sisters ɗinsu daga ƙarshe aka ɗaura na anty hawwa da megari, abinda yabawa kowa mamaki kenan domin megari yakusan haihuwar mlm Musa ma...daganan taro yawatse inda suka ɗauki zubaida zuwa Lagos domin daga can zasu wuce Niger ɗin.




Acan gidan Abba kuwa sosai jama'a suka cika babu Masoka tsinke se hidima akeyi babu kama hannun yaro su isseta ƙirjin biki se shige da fice akeyi, ana dawowa daga ɗaurin auren aka shirya Ummi da mufeedah dakuma zubaida zuwa kaisu gidan mazajensu dake Niger,,,sunsha kuka harsun gaji da haka aka tattara su zuwa Niger tare da rakkiyar su isseta da mejo, Itako halima aka kaita gidanta dake kusan na isseta acikin banana island... ƴan kai Amare kwanansu ɗaya a Niger suka dawo Alhaji abdussalam yayi farin ciki sosai daganin tilon ƴar tashi da tsohon cikinta abin gwanin sha'awa...suna dawowa suka wuce gidansu.


Jama'a fa yau general Aliyu ya angwance yaji abinda mejo keji yana ihu yau kam shima gaya yanayi babu ƙaƙƙautawa hardasu kuka da sambatu, halima tasha yabo da sanya albarka sedai kuma tasha uƙubarta agun jarimin mijin nata, sedai muce Allah ya bada zama lafiya amarya da ango.


Bayan wata ukku


Awannan lukacin cikin isseta yashigo watan haihuwa yayi girma sosai yanzu ko kusanta bataso mejo yazo...yau Laraba misalin ƙarfe 11 nadare, kwance take akan ƙirjinshi amma se murƙususu takeyi sabida azaba gabaki ɗaya tajiƙe sharkaf da gumi amma takasa gayawa mejo sabida bataso ta tadashi daga bacci, seda gumin datakeyi yatadashi, arazane yamiƙe ganin duk sunjiƙe sharkaf dagashi har ita, cikin tashin hankali ya kunna fitilar ɗakin yana faɗar "lafiya kuwa sweet life mine...beƙarasa ba sabida ganin isseta na nishi da ƙarfin Allah kamar zata fitoda hanjinta, ido yawaro kafin yamiƙe agigice yasun gumeta yafito daga bedroom ɗin seda yazo perlor yaga babu kayan kirki ajikinsu dukkansu hakan yasa ya ajiyeta tukkunna yajuya yaɗauko mata hijab sedai koda yadawo aikin gama yagama domin kuwa har kan yaro yadanno...cikin mugun giɗima tashin hankali ruɗu da duk suka rufeshi saka makon betaɓa ganin haihuwaba se yau, baki narawa yake maimaita sunan Allah yana neman ɗauki daga gareshi, itama hakan, cikin iyawar Allah da buwayarsa Sega yaro santa lele ya faɗo yana tsadara ihu gwanin sha'awa. Hakan yasa mejo ƙara waro blue eyes ɗinshi yana kallon kyakkyawan yaron dake kwance acikin ƙazantar haihuwa yana tsandara ihu, jikinshi har rawa yakeyi yana furta "alhmdlmulillah alhmdlmulillah alhmdlmulillah kafin yace little mom yazanyi dashi?? "Agalabaice isseta tace "nima bansaniba yayana...ya salam barana kura Dr ziyad hakan yazaro waya yakirashi aiko ko minti 10 ba'ayiba Sega wata malamar asibiti tazo gidan abisa umurnin Dr ziyad,,,tana zuwa dole mejo yabata wuri tashiga gyara jijirin da mamanshi....shiko yafito asukwane yanufi gidan General Aliyu, cikin mamaki general yafiro ganin mejo acikin dare,,,aitunda yaji abinda ke faruwa ya shiga murna dayiwa Allah godiya sunzama iyaye suma, haka halima tafito cikin farin ciki tanufi gidan isseta,,,suka haɗu itada wannan matar suka gyara isseta da babynta abin gwanin sha'awa


Seda suka gama gyara komai Kana suka kirasu mejo,,,cikin zumuɗi sukashigo perlor angyarashi tsab kamar ba'a haihu ananba, halima ce taɗauko yaron tabawa mejo,,,cikin tsananin farin cikin yake kallon ɗan nashi me tsananin kama dashi kamar antsaga kara, addu'a yayiwa yaron sosai kana yamiƙawa general Aliyu yaron shiko yanufi little mom ɗinshi dake zaune gefe tana kallonsu....yana zuwa betsaya kamaiba yarun gumeta tsam ajikinshi yana sauke ajiyar zuciya "alhmdlmulillah thank you so very much my sweet life my everything haƙiƙa ke alkhairice agareni Maryam kinbani farin cikin dabazan iya bawa kainaba kin haskaka mini rayuwata kin tsamoni daga hallaka kuma kinmayemun gurbinta da sawabar rayuwa, inasonki matata kuma abin alfaharina inamiki sonda bantaɓa yiwa Komaiba aduniya daga Allah da Manzonsa se iyayena sukemu Maryamata i love You more sweet sis sweet life sweet 🤭sekuma yarufe baki yana dariya...itama rungumeshi tayi sosai ajikinta tana faɗar "baki baze iya furta kalmar sanda nakemaba yah najeeb ido bazasu iya nunawaba jikina baze iya misiltawaba domin kuwa komi zanyima kona faɗa baze iya fallasa asalin abinda ke zuciyata da rayuwataba sedai nasan cewa soyayyarka araina dashene na uban giji wanda bawa baze iya ganin farkonshi ba balle ƙarshe ina matuƙar ƙaunarka yayana mijina abokin rayuwata kuma uban ƴaƴan...cikin wani irin mugun farin ciki mejo yaƙara janyota jikinshi idonshi ba zubda hawaye yace "soyayyarmu kaika ginata Allah kaine sanin dalili dakuma mafarin hakan rabbi kabarni da Abar ƙauna ta 😥...wani irin murmushi general Aliyu dake kallonsu keyi halima kuwa da wannan malamar asibitin hadda ƙwallarsu suna murmushi tabbas wannan soyayyar dashen Allah ne... general Aliyu ne dakanshi ya sallami wannan matar datarin alkairai kana yashiga kiran Hajiya mama da habbey Yagaya musu haihuwar isseta daganan yakira nazeer da general Faruk

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login