Showing 51001 words to 54000 words out of 109347 words
Chapter 18 - MEJO NAJEB Book 1 Complete Hausa Novels By Autar Alheri .txt
batason haya niya sedai duk wanda yatsokaneta seta rama gatada ƙarfin tsiya. sosai mama bintu taji daɗin yadda Isseta keramawa idan yara sa'anninta sukayimata wani abun domin bataso tayi magana ace tashiga faɗan yara kasan cewar gidan Yakoma gidan yawa yanzu tunda mamansu yah balah yaranta biyar. Yah balah shine babba agidan gaba ɗaya, se Hashimu, badauyi, hafizu sa'annan bilkisu...iyya hassi kuwa yaranta ukku hawwa'u zubaida sekuma juwaira..yayinda mama salmu keda ɗaya jidda....ita kuwa mama bintu Kabir ne kawai ɗanta sekuma Isseta ayanzu.
To ganin yadda Isseta ke dambe dayaransu kuma babu me iya doketa harmanyan rawar ƴan bori suke tsakaninsu da ita yasa iyayen fara tsanarta gaya kuma duk tafi yaran gidan kyau hakama abba yana nuna mata so dakulawa sosai kasan cewarta ƴar amana.
Bayan shekara ɗaya mama bintu tabuƙaci mayarda Isseta agun iyayenta sedai abin mamaki sam sunƙi amincewa dahakan Sema cewa sukayi taci gabada zama agunta domin tasan minene rayuwa kuma tayi karatun addini dana zamani anan bazasu karɓeta ba seta gama ƙaramar makaranta, Hakan yasa Alhaji Abdussalam aikowa da Abba maƙodan kuɗaɗe akan yasaka maryama makaranta dakuma bukatunta na yau da kullun...wannan abin baƙaramin mamaki yabawa su mama bintu ba amma Hakan suka danne inda Abba yasaka Isseta makarantar kuɗi dake cikin garin gwambe yayinda yaranshi keyin tacikin rugar tasu......Hakan kuwa yaɓullo da wani sabon tashin hankalin acikin gidanshi domin sosai su iyya hassi suka ɗauki abin da zafi inda suke faɗar yafifita Isseta akan sauran yaransu kamar itace ɗaya ƴarshi kokuwa ita ƴar gwalce. Da wannan ɓarakar takunno kai mama bintu taso sanardasu cewar Isseta baƴar mijinsu bace abbantane yabada kuɗin sakata makarantar ba mlm Musa ne yasakataba.....amma se mlm Musa yace tabarsu karta gaya musu domin ayanzuma dasuke kallon ƴarshi ce suna hantararta inaga sukasan baƴarshi bace....da mama bintu taji Hakan setace to lallai sedai yamaidasu makaranta ɗaya domin kawo zaman lafiya acikin gidanshi.
Haka kuwa akayi inda suma dukkansu yasakasu makarantar kuɗin tare da Isseta sukaci gabada karatu tare ananne Isseta tahaɗu da Halima har jininsu haɗu suka fara ƙawance sekuma yazama Halima ƴar umguwarsu ce basuda nisa tsakaninsu. Ahakan suke karatunsu hankali kwance suna ƙawancensu....bayan shekara ɗaya Isseta na class 2 amakaranta sunfito breakfast aka Nemi Isseta akarasa har akatashi daga makarantar babu Isseta babu dalilinta wannan abin yayi masifar ɗagawa malaman makarantar hankali sabida mlm Musa amanarta yadamƙa musu, Hakan yasa Basuyi ƙasa a guywaba suka kirashi sukasanar dashi abinda kefaruwa. Humm wannan lokacin kuwa mlm Musa yashiga tashin hankali marar misaltuwa inda yabazama neman Isseta lungu dasaƙo tare da kai repond awurin police ɗin garin....da labari yariski mama bintu kuwa ƴar ƙaramar hauka tayi akan wannan al'amarin domin kuwa har suma seda tayi inda daƙyar akasamu tafarfaɗo sedai fa firr anƙi samun kanta domin gabaki ɗaya ta birkice musu...abinda yaƙara ɗagawa waƴannan bayin Allah hankali shine har aka kwana biyu da wuni babu Isseta babu dalilinta kuma anyi neman duniya ba'agantaba...akwana na ukku ne bayan sallar magarib....!
Autar alheri ✍️
🪽🪽🪽🪽🪽🪽🪽🪽🪽
MM _ NN
Book 3
Page 53 & 54
"Wata mata takawowa mama bintu Isseta hargida inda tace tsintarta tayi tana kuka shine tamayarda ita gidan...faɗin farin cikinda mama bintu da mlm Musa suka shigama ɓata lokacine, sosai sukayi murna da bayyanar Isseta cikin farin ciki suke yiwa wannan matar godiya batareda suntsaya tunanin ina ta tsinci Isseta ba harta maidata gida sam idonsu yarufe da murnar dawowar ƴar amanar tasu..ahakan wannan matar tayimusu sallama tafi.
Tofa jama'a wannan matar bakowa bace face gimbiya mardiya domin itace takarɓi Isseta agun hatsabiban aljannu da suka saceta abisa umurnin Haniya tabawa...ito gimbiya mardiya tagane yarinyar ne sakamakon suntaɓa zuwa ganinta a Niger itada umaima alokacinda gimbiya laweesat taturasu amadadinta domin tunda Hannah tahaifi yarinyar Allah yasakawa gimbiya laweesat son yarinyar sedai ba yadda zatayi tunda ba jinsinsu ɗaya ba amma lokaci zuwa lokaci tana sakawa umaima taɗauko mata ita taganta batareda Hajiya Hannah tasaniba domin ita Hajiya Hannah sam batasan da gimbiya laweesat ba balle tasan tasaka ana bibiyarta domin bata tsaro. To kunji yadda gimbiya mardiya tasan Isseta Hakan yasa dataganta taganeta kuma da takaita gun gimbiya laweesat setake gayamata abinda kefaruwa wanda yasa Maryama tadawo ƙasar Nigeria dazama hannun mama bintu.
To daga wannan ranar kullun se gimbiya mardiya takawowa Isseta ziyara kuma tana ɗaukarta takaita gun gimbiya laweesat tajima acan inda gimbiya laweesat kezo mata afili taganta rabi mutun rabi kifi shiyasa sam Isseta bata tsoron Maah tun tana ƙaramarta domin sosai take wasa da jilar kifin maah idan tazo...sannu ahankali shaƙuwa meƙarfi tashiga tsakanin gimbiya laweesat da Maryama inda take kiranta da Maah tun tana ƙarama.....sannu ahankali tafiya tabi hanya har maryama tagirma tafara zama cikakkiyar budurwa kuma ahakan shaƙuwarsu da Maah naƙara ƙaruwa hartakai dakanta take zuwa domin taganta taɗauke ta uwa mahaifiya, Itama taɗauke ta amatsayin ƴa Hakan yasa duk wanda ketareda gimbiya laweesat yasanda zaman maryama kuma suke iyakacin bakin ƙoƙarin su wurin ganin sunbata kariya 💯 akan sharrin Hajiya tabawa.
Daga gefe ɗaya kuwa sewani abin ya ɓullah acikin gidansu Isseta
Wannan abin kuwa bakomai bane face yadda mama bintu Takoma yiwa Isseta halin ko inkula sam babu ruwanta da sha'anin yarinyar kuma komi za'amata batacewa komai inkuwa yankata akayi agabanta ku kallonsu bazatayiba sedai idan angama tashige ɗalinta tayita kuka tarasa yazatayi Allah yasani tanason saka yarinyar ajikinta tazame mata uwa tagari me share hawayen ƴaƴanta amma tarasa miyasa kotaso tayi Hakan takejin kamar asaka mata takunkumi abakinta....inda kuwa matan gidan suka samu wannan damar suna musguna wa Isseta suka maidata baiwa acikin ƴaƴan su, har aka kawo wannan lokacin dazamanta gidan yaƙare tahanyar korarda Abba yayi mata....duk tsawon wannan shekarun da Isseta tayi ahannun mama bintu Hajiya Hannah takasa zuwa Taga halinda yarta keciki kuma Haka Alhaji Abdussalam dukkansu sun wofantarda rayuwar yarinyar har inda Alhaji Abdussalam yafara mulkin ƙasar Niger Basuyi tunanin karɓar ƴarsu ba sedai suka aikawa mlm Musa maƙodan kuɗaɗe domin kulada ita...amma fa wani lokacin dukkansu suka shiga damuwa marar misaltuwa akan rashin yarinyar sedai kosunso sayi wani yunƙurin akanta bazasu iyaba....kuma duk wannan abin dake faruwa dasu har su mama bintu sharrin Hajiya tabawa ne domin tasamu damar ɗauke maryama Takoma hannunta sabida tasamu nasarar samun saka hannunta akan takardun kadararta da Alhaji madu ya mallaka mata, kuma gashi haryanzu batayi nasara ba.....koyanzu da mama bintu ta'iya buɗa baki tayiwa mlm Musa magana akan zancen Isseta da wannan zuwan da Hajiya Hannah tayi duk yasamu asaline akan lalata wasu tsafukan Hajiya tabawa da gimbiya mardiya tayi har suka samu damar waiwayar rayuwar yarsu.....wannan shine asalin labarin Isseta.
Mukoma cikin labarinmu kaitsaye.
Tunda Hajiya Hannah tafita daga gidansu Isseta ranta ke masifar yimata ƙuna sosai take jawa Hajiya tabawa Allah ya'isa babu adadi domin kuwa duk itace musabbin wannan al'amarin, kuka takeyi sosai azuciyarta wanda babu hawaye tanajin tausayin tillon ƴar tata kotana ina ahalin yanzu? Ko awanne hali take? Allah kaɗai yasani har suka isa masaukinsu batadena wannan kukan zucinba....iyya hassi kuwa sojojinnan nafita da ita Basu zarce ko ina da itaba se hidikwatar sojojin Nigeria dake cikin garin gwambe inda suka Nemi alfarman su ajiye musu ita tare da horo me tsani harsu tashi komawa Nigar kuma umurnine daga matar shugaban kasar Niger ɗin...aiko sunajin Hakan suka karɓi iyya hassi tare da turata wani ɗakin suka garƙame.
Lagos
Seda suka gama duk abinda zasuyi agidansu general aliyu kana suka fito atare kamar yadda suka shiga, mufeedah naganin fitowarsu tataso cikin sauri domin ita tashirya dama fitowarsu take jira....bawanda yace da'ita komai harsukayiwa habbey sallama sukabar gidan...sunyi tafiya meɗan nisa inda suke cikin mota ɗaya su ukku mufeedah na agaba tare da diriver wato captain Ameer babban yaron general aliyu. Ɗagowa mejo yayi yabuɗe baki ahankali yacewa capital Ameen sunufi gidanshi dake cikin banana island ɗin... okay kawai captain Ameer yace inda general aliyu yabishi da kallon meɗaukeda tambaya tamizasuyi acan?? Basarwa yayi kamar beganshi ba har suka ƙarasa gidan...fitowa yayi yanufi cikin gidan kaitsaye bayan captain Ameer yayi Perking, da kallo suka bishi dukkansu amma ba wanda yace komai....ko minti 5 beyida shigaba segasu sunfito ajere kamar wasu taurari Isseta tayi shirinta cikin doguwar rigar less Marron color merashin baƙi kana taɗora baƙin mayafi akanta, haƙiƙa tayi kyau iya kyau duk sharrin mutum be Issa ya kusheba.
Tunda suka fito daga cikin gidan general faruk yace "wow Masha allah wacece wannan beautiful baby ɗin friend? Yatambayi general aliyu....Ɗan murmushi general aliyu yayi kamun yace "ato gadai tanan ƙanwarmu ce amma wlh karufawa kanka asiri dazancenta indai mejo nakusa nadai nagayama, yaƙarasa zancen cikin tsokana..."tofa iKon Allah aa to nadena bazan ƙaraba koya kikace ƙanwata? Yayi maganar yana tambayar mufeedah datayi mutuwar zaune wurin kallon Isseta domin baƙarya tatafi da imaninta...ajiyar zuciya tasauke tana murmushi tace "wlh kuwa yanana haka zancen yake.
Kafin waninsu yaƙara yin magana ne sukaga motar mejo ɗin yashigo gidan wadda captain Jameel keja,,ita yabuɗewa Isseta tashiga Shima yashiga kana suka Halba motocin akwalta...gabaki ɗaya general faruk da mufeedah suncika da mamakinshi amma general aliyu ko ajikinshi hasalima cewa yayi aiki yasameku indai mamakin najeeb zakuyi.....ahakan har sukazo wani mool, sukayi Perking motocinsu sukafito tare da nufar cikin wurin...babban wurine sosaina manyan mutane.
Mufeedah ce tazo wurinsu tana bawa Isseta hannu tace good evening antynmu....da mamaki Isseta da mejo ɗin duk ke kallonta kafin Isseta ta amsa mata tayi saurin cewa "Sunana mufeedah ni ƙanwar yah najeeb ce inasonki ƙawa antynmu kema zakiyi ƙawance Dani? Tatambaya tana riƙo hannun Isseta ɗin.... murmushi Isseta tayi wanda yaƙara bayyanarda asalin kyawunta kafin tabuɗe baki cikin sexy voice ɗinta tace "Masha allah mufeedah nikuwa sunana maryama ba anty ba kamar yadda kike faɗa, Itama tayi zancen tana riƙo hannun mufeedah ɗin....murmushi su general aliyu suka yi sunabinsu da kallon birgewa yayinda mejo kuwa yadasƙare yana kallon zallar kyawun Isseta yanajin yadda sexy voice ɗinta kehuda kowanne saƙo najikinshi yakafeta da blue eyes ɗinshi ko kiftawa babu, suko su general faruk se kallonshi sukeyi suna murmushi cikin mamakin yanayin da yashiga lokaci ɗaya....kamar daga sama suka tsinkayo muryar dady Alhaji Khamis kenan, yana faman dokawa mejo najeeb kira amma sam bejishiba harya ƙaraso inda suke tsaye......!
Autar alheri ✍️
🪽🪽🪽🪽🪽🪽🪽🪽🪽
MM _ NN
Book 3
Page 55 & 56
"Cikin mamaki yake kallon ɗan nashi dayakafe mace da ido ko kiftawa babu...suko su general aliyu gabaki ɗaya sun tsorata da ganin kallon da dady keyiwa majo ɗin...dasauri general aliyu yadoki shoulder ɗinshi tareda nuna mishi dady, wanda yakafeshi da ido Shima yana mishi kallon tuhuma.
Suko su general faruk gabaki ɗaya shunsha jinjin jikinsu musamman dasukaga ashe dady bashi kaɗai bane shida abokinshine Alhaji Abubakar mahaifin general aliyu...gaidasu suka shigayi cikin girmamawa, amma Alhaji Abubakar ne kawai ya'amasa shikam dady gaba ɗaya hankalinshi yatafi wurin mamakin ɗan nashi, juyawa yayi yakalli Isseta dakanta ke ƙasa kana yajiyo ga mejo din cikin kakkausar murya yace"wacece wannan yarinyar najeeb? Yatambaya idonshi akan najeeb ɗin cikin tuhuma...shiru yayi bece komaiba setaune lips ɗinshi naƙasa dayayi yana tsotsa..wannan abin kuwa yayi bala'in ƙularda Alhaji Khamis cikin fishi yakoma cewa "waiba dakai nake maganaba najeeb? Yar waye kaɗauko? Nace....cikin sauri general aliyu yace "please dady tsaya kaji wlh ba ɗaukota yayiba dama....ya'isa Aliyu bakai natambaya ba idanshi beda bakin Bani amsa yabari, zakacemun baɗaukota yayiba itace takawo kanta? Koni makahone? Tunshigo warkufa nake kiransa amma gabaki ɗaya idonshi da hankalinshi nakan yar mutane, "Magana zaka fara ɗauko minne najeeb? Dama abinda kakeyi kenan ɗaukar ƴaƴan mutane kana yawo dasu shiyasa kake hantarar ƙannen ka kana musu ƙazafi? Najeeb shine rayuwarda kaɗaukarwa kanka? Neman matan banza zakafar....tun dady beƙarasa faɗar abinda zefaɗa ba yayi saurin dakatardashi tahanyar faɗar "no dady please kadena wannan maganar wanne irin matatan banza kuma? Ita wannan fa dakake faɗa akanta dady nauyinace miysa kakemun irin wannan tunanin ne please? Yaƙarasa maganar cikin takaicin canjawar mahaifin nashi domin da abaya ne sam bazekawo irin wannan munanan kalaman agareshiba.......shikuwa dady cikin mugun mamaki yake kallon najeeb ɗin kafin yace"nauyinkafa kace? Ita wannan yarinyar?? Wacece ita dahar tazama nauyinka bansaniba?? Yayi maganar yana yiwa najeeb ɗin wani irin kallo nakama renamin hankali....shikuwa shiru yayi kamar beji abinda dadyn ketambayaba domin Allah yasani har kanshi yafara ciwo sabida bayasan yawan magana musamman cikin ɗaga murya kamar yadda dady kemishi ayanzu.. "badakai nake maganaba najeeb kayimun banza kosena saɓa maka yanzunnan bakin naka ze buɗe wacce ita nace? Yatsinkayo muryar dady yana magana cikin tsawa.
"Buɗe blue eyes ɗinshi yayi a kan dady dahar sunfara canza kala sabida ɓacin rai kamin yanisa yabuɗe baki cikin dakiya yace "SHE'S MY WIFE dady she's my marriage wife,(Ita ɗin matatace dady ita ɗin matar aurenace) 😳😱🙆♀️ yafaɗa cikin gaskiya da gaskiya babu fargaba balle danasani aranshi.
Wani irin waro ido daga dady har Alhaji Abubakar suka yi baki asake suna kallonshi..hakama general faruk da mufeedah dukkansu baki buɗe suke kallonshi cikin mugun mamakin furucinshi...shiko general aliyu wani irin ƙayataccen murmushi yayi yana duƙarda kanshi ƙasa...
Amarya anty hawwa
Dayamma liss sukashigo garin Lagos inda suka ɗauki hanyar gidan mijinta kaitsaye sedai da mugun mamaki nakebin motocin da kallo ganin sun nufi banana island, mamaki begama kasheniba seda suka nufi gert ɗin gidan Alhaji Khamis sahabi, inda suna zuwa Gert ɗin yawangale kanshi suka kutsakai ciki....bayan motocinsu sungama Perking ne suka shiga fitowa suna ƙarewa gidan kallo ganin girma da tsarinshi.. mamansu yah balah kuwa baki harkune itada wasu dangin iyya hassi dasukazo kawo amaryar, anty bilki ma sesantin gidan takeyi aranta tanajin dama itace Allah yakawo wannan danƙareren gidan cikin wannan daular....to aɓangaren anty hawwa amarya ma haka abin yake domin duk baƙin cikin datakeji na wannan Auren ayanzu seta nemeshi tarasa wani irin daɗi takeji tana godewa abbanta daya bada aurenta awannan gidan domin itakam Taga wurin zama...su zubaida da jidda kuwa beyedasu kawai suke suna debewa idonsu ƙwarƙwata...ahakan wasu sojoji cikin waƴannan dady yasa suka daukosu suka wuce gaba ƴan kawo amaryar natake musu baya har jikin perlor gidan.
Hajiya Umma nazaune itada Hajiya mama dasu ummi hadda juwaira waƴannan baƙin sukashigo perlor dasallamarsu.....cikin sakin fuska kuwa su Hajiya Umma sukatashi suna tarbarsu tare da yimusu yahanya...suma suka amsa musu baki awashe, bayan sunbasu wuri sunzauna ne akashiga gaishe gaishe....sosai su Hajiya mama suka tarbi waƴannan baƙin na dady kamar yadda Yagaya musu suna tafe...ƴammatan ne suka shiga gaida baƙin ananne idon juwaira yasauka akan ahalin nata ido tazaro cikin mugun mamaki tace"laaa anty bilki kune atafe dama??? Wannan tambayar datayi itace tasaka hankalin sauran mutanen kaiwa gareta.
"Laaa zuwaira dama kina'nan kinrigamu zuwa kenan? Waya gayamiki nan za'akawo amaryar Halan?? Cewar anty bilki Itama cikin mamakin ganin ƙanwar tasu anan.
Da mamaki zuwaira tace "amarya kuma wacce amarya? Kamarya wacce amarya ? Bakisaniba kika rigamu zuwa, cewar zubaida...kamin zuwaira tasake magana mamansu yah balah takatsesu tahanyar faɗar"iKon Allah dan Allah kuyiwa mutane shiru duk kuncikamu dasurutunku..aiko suka yi tsit...itako tayi hakanne sabida ganin kallonda Hajiya mama kemusu..haka dai kowa yabar zancen inda Hajiya Umma ta kalli ummi dake zaune tace "ummi maza jeki kuɗaukowa iyayen ƙawarki abin taɓa baki ashe dama iyayen ƙawarki ne zasuzo shine baki sanar munaba....tayi maganar tana murmushi..itadai ummi batace komaiba domin kanta ya kulle kuma dama ita ba ma'abuciya surutu bace....riƙo hannun juwaira kawai tayi suka nufi kitchen ɗin inda auta Siyana ma tabi bayansu suka shiga ɗaukowa baƙi abincinda aka shirya musu...sosai suka cika musu gabansu dakayan ciye ciye kala kala...Hakan ƴan kawo amaryarda babu biki suka zage suna bawa cikinsu hakkinshi🤩 anga jar Miya da kaji na bidiri aciki sekwasar gara akeyi. (Allah sarki ummu shuraim se raba ido takeyi tana haɗiyar yawu amma sunƙi tsammata☹️ daga ƙarshe dai seda ƴar mana ta rarrasheta tukunnah ta haƙura bayan maman Yasmeen dasauran team ɗin TEEMAH P R V sukayi alƙawarin Siya mata🥳🤣)
Seda suka gamacin abincinne tukunnah aka kaisu masaukinsu inda sukabar su Hajiya mama datarin tambayoyi akansu sabida Kalaman su anty bilki sunsakasu cikin zargin wani abun.
Juwaira kuwa yadda tasamu suka ɗaga tacimmusu inda aka saukesu takira jidda tajata tafice da'ita can wurin lambun gidan..cikin sirri tace "jidda wai wacece amaryar dakuke maga akai wlh bansan komaiba? Kallonta jidda tayi cikin yarinta tace "anty hawwa mana itace amarya nanne gidanta. Ido juwaira tazaro tana faɗar"anty hawwa dai Tayaya Hakan tafaru kuma wanene mijin nata? Tatambaya cikin giɗimarda lokaci ɗaya tasameta, domin dai da anty hawwa da juwaira uwarsu ɗaya ubansu ɗaya dukkansu ƴaƴan iyya hassi ne... "Nima bansan waye mijinta ba amma dai Abba ne yace akawota, anan jidda tabawa juwaira labarin duk yadda akayi auren anty hawwa lokacinda batanan. Tashin hankali kenan, ai juwaira batasan lokacinda tafara sambatuba tana faɗar"nashiga ukku ni juwaira Allah yasa dai bashi bane Allah yasa bashi bane kai Bama shibane wlh sam bazeyuba. "Bashi bane waye anty juwaira? Muryar jidda tadawo da ita cikin hayya cinta....dasauri tace "bakomai jidda muje namaidaki daga Hakan tariƙo hannun jidda suka koma cikin gidan.
"Masu karatu idan baku mantaba koda akayi Auren anty hawwa zuwaira bata gidan iyya hassi tace taje gun danginta ne a Kano shiyasa batasan komai akan wannan Auren na yayarta ba... atakyaice dai zuwairar gombe tagidansu Isseta itace juwaira kawar ummi ƙanwar mejo najeeb a Lagos, a gombe ana kiranta zuwaira a Lagos kuma juwaira.
🧏♀️💃 *INA KUKE BIG LADY'S KIKARANTA KOBAZE ANFANEKIBA ZE AMFANI WANI NAKI* 🧏♀️💃
🤩MAGANA A KEYI TA GLOIN SKIN🤩
(GYARAN JIKI SHINE MECE) DUK MACEN DABATA GYARA TO MUNA MATACE BAKAI AKIRATA MACEBA🤷♀️
HADDA MAZANMA🤨
💫 Hajiya shin kina buƙatar jikinki yayi kyau fatarki Takoma ɗanya shakaf tamkar ta jarirai ??? Kikoma tamkar zarah acikin taurari acikin mata yan uwanki✨✨✨✨✨domin fa hasken zarah dabanne💃
💫shin kina buƙatar fatarki Takoma tamkar ta jaruman Kaneewood kona novel?? Humm kinsan cewar dafata ne matan waje kekarɓe mana mazaje??🙄🙄🙄 To idan baku saniba ayau kusani, ƙyalli fata shine keruɗar mazajenmu dakuma samari kai harmada ƴammata🤷♀️
💫💫idan kinshirya gyara jikinki Hajiya kigarzayo domin samun ingatattun haɗin daze wanke Miki fatarki tass kikoma tamkar bala rabiya✨sabida ƙyalli da kyau babu kwailin balle abata miki fata, se haɗin zallar gargajiya na ƴaƴan itatuwa masu inganta lafiyar fatarki, *SABULUN WANKA, MAN SHAFAWA GA ƘAMSHI GA DAƊi, SEKUMA DILKAH WADDA ZAKIYIWA KANKI A CIKIN MINCI* dukkansu afarashi ɗaya za'a haɗa Miki duka ukkun wlh wlh wlh summa tallahi acikin mako ɗaya (one week) Zaki banbata fatarki data sauran mutane domin ingatattun kayane kuma