Showing 33001 words to 36000 words out of 109347 words

Chapter 12 - MEJO NAJEB Book 1 Complete Hausa Novels By Autar Alheri .txt

14 Jan 2025

14435

general aliyu yasamu yazauna Yana kallon aminin nashi kafin yayi gyaran murya cikin kulawa yake faɗar " afternoon my man how your work?? Mejo Najeeb bece komaiba yamiƙawa general aliyu hannu kawai sukayi musabaha kana yashiga haɗa kayanshi domin lokacin tafiyarshi yayi kasan cewar bayajin daɗin jikinshi tun lokacinda ciwonshi yatashi...da kallo general aliyu yabishi harya gama haɗa kayan sa'annan ya kalleshi dakulawa yace "Se ina yanzu mejo? amma dai ba gida zakajeba gidanka zakaje gun sister ko? Yatambayeshi yana kafeshi da golden eyes ɗinshi......shikuwa Mejo Najeeb wani irin faɗuwa gabanshi yayi Allah yasani sam yamanta da wata yarinya daya ajiye agidanshi dudda cewar bata cikin lissafinshi amma koba komai ita ɗin amanar maahh ce bedace yawo fatarda itaba, blue eyes ɗinshi yawaro tunowada Ita kaɗai cefa agidan kaddai wani abun yasameta besaniba, inko Hakan tafaru meze gayawa maah "innalillahi wa'inna ilaihiraji'un yafaɗa daɗan ƙarfi kafin yayi waje asukwane batareda yabawa general aliyu amsar tambayar shi ba secewa dayayi "please bro follow me now.....ganin Hakan yasa general aliyu mara mishi baya kawai Shima batareda yaƙara cewa komaiba domin ya san koyayi maganar ba amsawa zeyiba...koda general aliyu yafito harabar wurin harya shiga mota captain Jameel yaja suna ɗauki hanya, Hakan yasa Shima yashiga tashi motar captain Ameer yaja sukabi bayanshi.




Isseta


Zaune take a general parlor gidan domin yanzu nanne wurin zamanta tinda tagano bakowa agidan, fruit salad ne agabanta tanasha gaya tayi wankan wasu mayun riga da wando wanda tagani acikin kayanda yasiya mata tinda dukkansu ƙananun kayane, wandon roba ne red color bakin guywarta yayi masifar ɗame mata ajiki inda dukkanin ilahirin halittar mazaunanta suka bayyana acikinshi kamar bata saka komaiba aciki,, sekuma rigar data kasance kamar bubu roba domin bata kamata ba hasalima setayi mata kamar ɗinkin unburela kuma batada dogon hannu iya kacinshi hannun bra, gabaki ɗaya ta bayyana asalin Nashanunta kuma tasauka ƙasa har mazaunanta sedai kuma kamar ƙara temaka musu tayi wurin bayyana.. sa'annan kuma ta gyara gidan ko ina yaɗauki ƙamshi sekace jihar barno😅...zaune take hankali kwance tana kallo a YouTube channel na s Zaria Hausa tv inda take kallon wani lbr mesuna SIRRI tana kallo tana saurara domin sosai lbr yaɗauki hankalinta dubada yadda ƴan ukkun cikin labarin ke masifar kama dajuna, Sam bataji tsayuwar motaba balle tasanda akwai wanda yashigo gidan...ahakan harya buɗe ƙofar perlor yashigo asukwane wanda rufe ƙofar dayayine yadawo da ita duniyar data tafi taɗago arazane tana kallon wanda yashigo mata bako sallama domin a iya tinaninta bakowa agidan bancin masu gadi sukuma iya kacinsu waje basu basu taɓa shigowa wurintaba...ido huɗu tayi dashi wanda harta fara manta kaman ninsa segaya yau yazo mata kamar daga sama aka jefoshi.




Shiko tinda idonshi yasauka akanta yakasa koda kiftasu sakamakon wani mugun kyau dayaga taƙara taƙara ƙiba da haske harwani sheƙi fatarta keyi a idonshi...itako ganin bece komaiba se kallon ƙurillar dayake binta dashi yasa tabi jikinta da kallo Taga miyake kallo aiko tawaro ido waje ganin kayanda ke jikinta domin Allah yasani sam batayi tunanin zezo gidanba Dama bazata sakasuba inkuwa taska to zata nemi hajab tasaka, ai a 360 tamiƙe dagudu tanufi Saman benen...Shima ɗin sake waro Blue eyes ɗinshi yayi cikin mugun mamakin ganin yadda kayan alatun jikinta ketafasa kamar ana dafa ruwan zafi, domin duk ilahirin halittar jikinta juyawa takeyi tana kaɗawa kamar zasubar jikinta sufaɗo....cikin giɗima yadafe setin mejo ɗinshi yana sauke numfashinda besan dalilin yinshiba acewarshi akuma Dede wannan lokacinne general aliyu yabuɗe ƙofar perlor yashigo...!


















Autar alheri✍️


🪽🪽🪽🪽🪽🪽🪽🪽🪽


MM _ NN


Book 2


Page 35 & 36


"Cikin mamaki yakebin aminin nashi da kallo ganin inda yaɗora hannunshi ga wurin yayi bala'in tasowa shikuwa se famar sauke numfarfashi yakeyi kamar wanda yayi gasar tsere, kallon inda yakafe da ido yayi kozega abinda yake kallo wanda yaɗaga mishi hankali Hakan amma wayam bakomai,, cikin mamakin da yakasa ɓoyuwa ataredashi yace "my man lafiya kuwa? Yatambaya yana kallonshi amma shiru babu amsa, seda Yafaɗa kusan sau huɗu tare da dukan shoulder ɗinshi, tukunna yazabura kamar wanda yaɗanji tsoro yana duban general aliyu.


'mejo miyafaru ne naganka abirkice Hakan kaga yadda kakoma lokaci ɗaya??🤔 general aliyu ya tambaye shi cikin mamaki.


Ɗan dafe kanshi yayi yanasauke tagwayen ajiyar zuciya kamin ya yamutsa kyakkyawar fuskarshi yana faɗar nothing tareda nufar cikin perlor..."ah,ah bawani nothing mejo kawai kagayamin ai hankali baze ɗauki wannan zancenba tukunnah ma ina Maryam ɗin takene?? Seda mejo yaji kalimar Maryam tukunnah yatinada sunanta aranshi yananata Maryam kafin kuma wani abin yafaɗo mishi arai cikin sauri yajuya yana kallo general aliyu kamin yace "tin yoshe kashigo perlor nan? Kaganta ne? Yatambaya fuskarshi ba walwala.. "no inna naganta zan tambayeka ne. Cewar general aliyu Yana ƙarasawa cikin perlor yazauna...Shikuwa jan ƙafafunshi yayi yahaura Saman batareda yasake cewa general aliyu komaiba....shimadai bebi takan shiba domin ya san halin kayanshi.


mejo kam part ɗinshi yanufa kaitsaye yana buɗe ƙofar perlor wani daddaɗan ƙamshi yaziyarci hancinshi wanda yasakashi lumshe blue eyes ɗinshi babu shiri yana shaƙar ƙamshin meratsa zuciya, da kallo yabi perlor inda yaga komai ƙal kamar yanzu aka buɗasu aleda, seda yagama ƙarewa perlor kallo tsab kana yanufi bathroom ɗinshi yana sauraren baƙon yanayinda jikinshi kekarɓa....a bedroom ɗinma yayi mamaki dudda cewar yasan bazama akayi acikiba amma yayi mamakin ganinshi ba yadda yabarshiba komai a gyare tsab kamar ba'ataɓa anfani dashi ba, wayoyinshi kawai ya'ajiye tare da cire kayan jikinshi yanufi bathroom, ruwa yasakarwa kanshi yana jin yadda ƙofofin gashin jikinshi ke ƙara buɗewa sakamakon wannan yanayin daya shiga ayanzu wanda yakasa tantance dalilin faruwar Hakan agareshi shida sam mata basa gabanshi ko kaɗan amma yanzu daga kallon wannan aljanar tasauya mishi yanayi. Ɗan tsaki yaja kana ya duƙa yana kallon mejo ɗinshi data cika tayi fam tana neman abuncinta sefamar harbin iska takeyi. "Ya salam Yafaɗa yaname dafeta dominfa sam taƙi ko rusunawa ganindai dagaske ba kwanciyar zatayiba yasa dole yayi wankan hakanan yafito daureda towel aƙugunshi, wurin mirror yanufa mayukanshi yaɗauka masu sanyin ƙamshi yashiga shafe jikinshi dashi kowanne part najikinshi da kalar man dayake anfani dashi na gashi daban na komai daban,, seda yagama shafe shafenshi kamar wata mace hankali kwance ba inda yanayi ana leƙenshi ba🤭kana yaɗauki kayanshi na shan iska yasaka wando 3kwata ash color da farar Riga me gajeren hannu, kana yafeshi jikinshi da sihirtaccen turarenshi daganan ya kwashi wayoyinshi yafito.


A,inda yabar general aliyu anan yasameshi Zamanshi yana kallo kuma haryanzu Isseta bata fitoba...zama Shima yayi yana yamutsa fuskarshi sabida jin mararshi data fara mishi ciwo ahankali😱 "please kayi mana order coffee nakeson Sha, Yafaɗa kamar bashine yayi maganar ba...ɗagowa general aliyu yayi yana watsa mishi golden eyes ɗinshi kafin yace "kamarya nayi mana order sekace babu mace agidan? Barin Abinda yakeyi yayi Shima yaɗago yana watsa mishi nashi blue eyes ɗin kafin yace "am so what Dan akwai mace a gidan itace matar gidan balle kayi tunanin samun abinci awurinta? Ko angayama abinda tazoyi kenan agidan? Yafaɗa cikin hasala... 'tofa iKon Allah to kodai ba itace matar gidanba koma itace Allah ne kawai yasani domin kaima kanka bakasan wacece matar gidanba amma dai ayanzu itace mukagani aciki kuma ita zamu tambaya koma mimukeso, yanakaiwanan azancenshi bejira amsar mejo ba yadokawa Isseta kira tahanyar faɗar Maryam Yafaɗa cikin ɗan ɗaga murya yadda zata jishi.


Isseta kuwa tinda tagudu ɗakinta tarufe abakin gado tazauna tana sauke ajiyar zuciya aranta tana addu'ar Allah yasa kar yayi mata kallon ƴar iska ganinta da wannan kayan domin daganin kallonda yake mata akwai tuhuma acikinshi, tajima zaune tana wannan tinanin kamin tamiƙe dasauri tashiga cire kayan tanemi wata doguwar riga abaya tasaka me buɗewa sosai kana taɗora mayafin abayar akanta yasauko agabanta kamar mayafi. Humm abinda Isseta bata saniba wannan rigarma data saka da wancan kayan data cire duk ɗaya domin babu abinda taɓoye ajikinta komai najikinta juyawa yakeyi tunda abin badaga suturar data saka bane daga halittar jikinta ne Allah yayi mata wannan ni'imar..zama tayi abakin gadon tana tunanin koya fita koyana nan haryanzu?? Batasamu mebata wannan amsarba tajiyo kiranda general aliyu kemata, Ido tazaro domin tayi tunanin shine maybe tuhumarta zeyi atakeko tashiga salati idonta suka cikoda ƙwalla domin aduniya babu abinda ta tsana samada ayimata kallon ƴar iska marar tarbiya,,tana cikin wannan yanayinne Kiran general aliyu na biyu yasake dokan kunnenta Hakan yasa tamiƙe dasauri tafito perlor domin yazu taɗan so tagano ba muryarshi bace, saukowa tayi ƙasa ahankali tana tafiya jiki asanyaye hartazo tsakiyar perlor.


Baki tabuɗe ahankali cikin sexy voice ɗinta me ratsa zuciyar yan maza tace "inawuninku yah Haidar, domin taji sunanda mejo yakirashi dashi aranar dasukazo Hakan yasa tasan Sunanshi....murmushi yayi ahankali yace "lafiya qalau sis y baƙunta? "Alhmdllh tafaɗa atakyaice kana tace gani naji ankiranine. "Eh nine nakiraki please coffee mukeso da ɗan abinci wanda bayada nauyi please kozamu samu agidannan? "Eh bara nayi muku tafaɗa tana juyawa tanufi kitchen.....dasauri general aliyu yaɗauke kanshi daga kallonta yana istigifari aranshi yake faɗar "tab dijam gaskiya doline mejo yafita nutsuwarshi...shiko tinda tafara saukowa yakafeta da blue eyes ɗinshi ko kiftawa babu yana hamdala aranshi dayaga bakayan ɗazu ne ajikinta ba hartazo tsakiyar perlor seda yaji tana gaisarda general aliyu ne yalumshe kyawawan idanuwanshi yana sauraren sweet voice ɗinta mekashe zuciyar me sauraro,, Gabaki ɗaya jikinshi yakarɓi wannan muryar tata inbada tsima babu abinda yakeyi anan, seda yaji tajuya zuwa kitchen ne yaƙara buɗe dara daran idanuwanshi akanta, wani irin warosu yayi ganin yadda mazaunanta ke juyawa kamar zasu faɗo Sema yaga yanzu sunfi girma kuma sunfi ƙara fitowa,


aganinshima kenan ɗazu matsesu ne tayi kodai cikone irin wanda mata keyi ayanzu? yayiwa kanshi wannan tambayar daba me bashi amsarta, tonowa yayi da bashi kaɗai bane a perlor Hakan yasa yayi saurin juyawa yana kallon general aliyu ganin ba ita yake kallah bane yasakashi sauke ajiyar zuciya domin general aliyu yawarshima yake danawa.


Mayarda idonshi yayi kanta amma yaga harta ɓacewa ganinshi. Komawa yayi yajingina dajikin kujerar yana sauke numfashi dasauri''dasauri gashi mejonshi sewani cika takeyi tana batsewa kamar zata fasa wandonshi tafito tsabar fitina....lumshe blue eyes ɗinshi kawai yayi yana sauraren wannan baƙon yanayin domin dai shi kanshi besan yanada sha'awa kamar hakanba kuma wai agun wannan aljanar kodai dan tana rabi mutun ne rabi aljan yasa takeyin galaba akanshine? Wata zuciyar tace mishi Humm najeeb wannan fa cikone tayi ba jikinta bane duka..ajiyar zuciya yaƙara saukewa jin abinda zuciyarshi taraya mishi Afili yace "komadai minene that's beautiful dress, tareda Kai hannu yadafe hajiyar da keneman ɓallowa tayo waje....cikin mamaki general aliyu ke kallonshi bayan yagamajin abinda Yafaɗa, hannunshi yabida kallo inda yaga abinda ya firgitashi wato yadda wandon mejo ɗin yaciko kamar anɗora mishi wani abun gaya se sauke numfashi yakeyi sama'sama. Atakyaice dai mejo yashiga wani yanayin kenan😍


Murmushi general aliyu yayi me sauti cikin tsokana yace "please mejo kadedeta nutsuwarka karka kunyatamu gaban ƴar ƙanwarmu please..Jin abinda Aliyu yace ne yasa yabuɗe blue eyes ɗinshi dasuka koma red lokaci ɗaya yana hara rar general aliyu.


"Bawani hararana dazakayi malam ai gaskiya ne jifa yadda kakoma kamar wani doki konace anɗora maka rodi wannan fitinar har ina..Yafaɗa Shima yana hara rarshi....dasauri mejo najeeb ya kalli ƙasanshi ido yazaro Shima ganin yadda yakoma atake wata irin kunyar aminin nashi tarufeshi, amma seya basar kawai yasake zabga mishi hararar tare da Miƙewa yanufi part ɗinshi yana faɗar "ɗan sa ido kawai, daga Hakan yayi hayewarshi sama.....dariya sosai general aliyu keyi seda yayi me isarshi kana yatsa gaita yana faɗar "hum najeeb sarkin kunya gakuma fitina zanga yadda zaku ƙare agidannan..yana cikin wannan tinanin Isseta tadawo perlor ɗaukeda madedecin tire ahannunta wanda taɗora coffee ɗin Akai cup 2 dakuma plate tazubo musu chips me haɗin salad tasaka wani palate ɗin tarufe.




Ajiyewa tayi a table ɗin tsakiyar perlor kana tajashi gaban general aliyu tace "gashi nan yah Haidar...murmushi general aliyu yayi Shima batareda ya kalletaba yace "thank you so much my little sis...itakam komai bata ƙara cewa ba tajuya abinta..Aliyu kuwa ɗagowa yayi danufin gani kotabar wurin ai dasauri yamaida kanshi ƙasa yana faɗar "tab dijam a gaskiya mejo ma yayi ƙarfin hali dabe sumaba domin wlh dashine yakafeta da ido yanamata kallon ƙurillar da mejo yayi mata Allah ya gama gigicewa a wurinnan yafaɗa a zuciyar shi, ahakan yake zancen zuci yana istigifari aranshi yake faɗar Allah kayafemin domin bada niyya na kalletaba....koda yasake ɗagowa domin yaci abunshi tuni taɓacewa ganinshi sabida ta haye warta sama, abincinshi yaci sosai Seda yaƙoshi shikam yaɗora ruwa akai kana yakwashi tarkacen wayoyinshi da laptop ɗinshi yafice daga cikin gidan yana me jinjinawa Isseta ta hanyar iya girki domin ya san cewa tabbas ba ƙarya ta iya girki ba kaɗan ba.


Mejo Najeeb kuwa yanacan bedroom ɗinshi kwance yana murƙususu yaji tashin motar General aliyu ƙara gyara kwanciyarshi kawai yayi yanajin yadda ciwon marar ke ƙara ta azzara,, kusan minti 45 yayi ahakan amma kuma memakon yaragu Sema ƙaruwa yayi miƙewa tsaye yayi daƙyar ganin ciwon mara naneman hallakashi yasa dole yafice daga bedroom ɗin. Harabar gidan yafito inda yanufi Perking space kaitsaye.....captain Jameel ne yataso yana faɗar "subahanallah miyafaru Sr? Yatambaya yana buɗe mishi ƙofar motar yashiga Shima yashiga tare da tada motar suka bar gidan batareda mejo yace mishi komaiba....da kallo su captain Umar suka bisu sunayiwa ogan nasu fatan samun lafiya dudda cewar sunso sugaidashi sabida ɗazu daya shigo kota kansu bebiba yanzu kuma gaya yafito babu lafiya to Allah ya kyauta daga Hakan suka koma bakin aikinsu....... Isseta kuwa tana zaune a bedroom ɗinta taji fitar motar General aliyu daga baya kuma tasakejin fitar motar shi se alokacin tasauke ajiyar zuciya domin taƙagu basubar gidan ba kamar akanta suke zaune😏




Suna hawa titi captain Jameel yasake cewa "Sr Ina muka nufa? Yatambaya cikin fargaba sedai kuma ga mamakinshi seyaji yace "hospital ɗin ziyad, yafaɗa cikin da sashiyar muryarshi data gama maƙilewa...okay kawai captain Jameel yace kana yajuya akalar motar izuwa asibitin basu wani ɓata lokaci ba suka isa Perking kawai yagamayi mejo yaɓalle marfin motar yafito kaitsaye yanufi office ɗin Doctor ziyad ɗin captain Jameel daya gama kashe motar ya mara mishi baya....!




















Autar alheri ✍️


🪽🪽🪽🪽🪽🪽🪽🪽🪽


MM _ NN


Book 2


Page 37 & 38


"Doctor ziyad yana zaune a office ɗinshi yaga anbanko ƙofar anshigo,,dasauri yaɗago kanshi domin ganin kowaye yayi masa wannan kutsen sedai ganin wanda yashigo ne dakuma yanayin daya shigo dashi yasakashi miƙewa dasauri yana faɗar "subahanallah mejo lafiya kuwa? Tare da riƙo hannunshi dayayi zafi kamar tuwa yana ƙoƙarin zaunardashi, captain Jameel ma yashigo, kallon captain Jameel doctor ziyad yayi tunda najeeb ɗin bayi magana ba yace "captain miyake damun najeeb ne miyafaru? Tatambaya cikin damuwa...."nima wlh bansaniba doctor kawai yafito ne daga gida naganshi ahakan shine yace nakawoshi gunka. Yaƙarasa zancen cikin tausayin megidan nashi....ido doctor ziyad yazaro yace "dakanshi yace kazo dashi wurina hospital??? Yatambayi capital Jameel cikin mugun mamaki domin idan akwai abinda mejo najeeb yatsana aduniya bewuce asibiti ba....kai captain Jameel yajinjina mishi alamar tabbatarwa.


Ajiyar zuciyar yasauke batareda yaƙara cewa komaiba yariƙo hannun najeeb ɗin suka nufi wani bedroom dake cikin office ɗin nashi, akan bed yaɗora shi kana yaduƙa Dede kunnenshi yace "Mike damunka ne my friend? Miyasa Meka Hakan? "Seyanzu mejo yabuɗe rinannun idanuwanshi ya kalli doctor ziyad wanda seda gabanshi yafaɗi ganin yadda idanun abokin nashi suka koma kamar wuta..taune lips ɗinshi yayi kamin yaɗago hannunshi dake karkarwa yariƙo na doctor ziyad kana yaɗora akan mararshi dayakejin kamar zata ɓalle sabida azaba....ido doctor ziyad yaƙara warowa cikin mugun mamaki da tashin hankalin jin yadda mararshi tayi kamar an hasa mishi wuta ga alƙalaminshi tsaye ƙiƙam kamar rodi, ai cikin gaggawa shiga bashi temakon daya dace dashi domin tuni yagano inda matsalar tadosa,,sedai yasha mamaki wanda baze misaltuba ganin mejo najeeb acikin irin wannan yanayin domin ze iya cewa tunda suka taso ko zancen mace betaɓa ji agun mejo ba balle wata banzar magana ko mu'amilar mata yanzuto ya'akayi harya shiga wannan Condions ɗin?? Yana aiki yanayiwa kanshi tambayoyi da bashida amsar su harya gama yayi mishi allurar bacci kana yapice yabarshi zuciyarshi cike falda tambayoyi.


Abban Isseta


Sunje gidan mahaifin mijin su anty hawwa sunga gida Masha allah abin se wanda yagani gida danƙarere nagani na faɗa domin ko unguwar da gidan yake cikinta abin kalloce balle gidan kanshi,,, alhmdllh sunsamu tarba ta musamman daga mutanen gidan domin ba laifi akwai karamci agaresu....kwanansu ɗaya agarin sukace bazasu zaunaba komawa zasuyi dama sabida suga inda za'akawotane sukazo...Alhaji Abubakar daya yagoranci tafiyar beyimusu jayayyaba sedai yayi musu goma sha biyu ta arziki kana yasaka akamaidasu har gida garin gwambe.


Halima


Tinsafe yau halima tashirya zuwa asibiti gun ammin Isseta sedata tafito zata tafine mahaifiyata wato inna tabata dambun naman rago datayiwa baiwar Allar tinjiya da halima Tagayamata zataje ta ajiye domin ita tashi tafiya tabata...aiko halima taji daɗi sosai takarɓa tare da yiwa mahaifiyar tata sallama tatafi sabida yau ita kaɗai zataje batareda yaya shamsu ba....tana isa asibitin tun aharabar asibitin tahangota zaune gefe ita kaɗai sauran ma haukatan kuwa suna gefe kowa na sha'anin haukarshi domin yau ranarda ake fidda masu yar damane wanda Basu duka dan suɗan wala...dasauri halima taƙarasa inda take tazauna tana riƙo hannunta cikin farin cikin ganinta tace "ammin Isseta, tafaɗa tana murmushi...abin mamaki se kuwa tamaida mata martanin murmushin amma idonta tab da ƙwallah tana waiwayen bayan halima ga dukkan alamu Isseta take nema...Allah sarki halima Itama itake idonta suka cikoda ƙwalla cikin sauri tashare tana ƙaƙalo wani murmushin domin Allah yasani Itama tayi kewar aminiyar tata. Rungume ammin Isseta tayi tana shafa bayanta kamin taɗauko danbun nan tashiga bata tanaci ahankali harta ƙoshi tabata ruwa tasha...Suna'nan zaune wata ma aikaciyar asibitin tazo tafiya da ammin Isseta domin lokacin komawarsu yayi, Hakan yasa halima biyar su har ɗakin nata inda wannan ma aikaciyar tabata magani tasha kana ta kwanta aiko babu wani ɓata lokaci bacci yayi awun gaba da ita....ajiyar zuciya halima tasauke kana tamiƙe taje wurin ma'aikatan asibitin taji koda akwai abinda ake buƙata...bakomai suka cemata Hakan yasa tayi musu alkhairi tayi tafiyarta.....tana isa cikin gari kaitsaye bakin rafi tanufa inda tana zuwa tasamu umaima tsaye awurin ita kaɗai (amma a idon ita halima sabida ba ita kaɗai bace itada wasu ƴan uwantane sedai ita Halima bata ganinsu) tsaye tayi tana kallonta kafin tace "maahh domin ita Halima Batasan ummaima ba Hakan yasa bagabe ba maaah bace umaimar ce kawai tasanda halimar....jiyowa tayi tana murmushi tace "Halima kece atafe??

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login