Showing 81001 words to 84000 words out of 109347 words

Chapter 28 - MEJO NAJEB Book 1 Complete Hausa Novels By Autar Alheri .txt

14 Jan 2025

14445

sakin kuka. "Innalillahi wa'innailaihi raji'un shine kawai abinda mejo kemai,maitawa aranshi yama kasa magana se ƙara rungume abban dayayi ajikinshi. Sunɗauki tsawon lokaci ahakan kafin Alhaji Khamis yafara magana cikin Muryar kuka yake faɗar "dan girman Allah kayafemun ɗana na ɗauki hakkinka dayawa nakasa sauke nauyin da Allah ya ɗoramin naka nawofantarda rayuwarka nayi fatalida duk wani abinda yashafeka dan Allah kayafemun, badan da Alhaji Abubakar ba mahaifin abokinka Aliyu da ilimi ma bazaka samuba najeebullah domin banida niyyar tsayama kayi karatun,, wlh bada niyya nayi hakanba Nima bansan miyasha kainaba harna aikatama hakan...ɗan shiru yayi yana sauke ajiyar zuciya kafin yaci gaba da faɗar alokacin kana ƙarami banida burin daya wuce na inganta rayuwarka naga ka kasance mutun mafi girma da daraja amma daga baya se abun yacanja wanda hakan yasa harnayima hukuncin ɗaura ma auren dole batareda kasaniba sabida tosashiyar ƙwaƙwalwata tana gayamin mace kakeso atareda kai shiyasa kake jifan Ummi da mansura da sharri harna fara tunanin karka fara nemansu hakan yasa nayanke wannan hukuncin wanda Alhaji Abubakar ne yajagoranci zuwa garinsu mahaifinshi yasamoma yarinyar kirki sabada ba yadda beyi daniba amma naƙi janye zancen auren hakan yasa aka aurama yara har biyu kuma ƴaƴan gida ɗaya,,,dudda wannan rashin adilcin danayima kuma kayi mini biyayya kakarɓi yarinyar hannu biyu, kamaidamin kunyata,,,sekuma yanzu gashi datemakon Allah dana Alhaji Abubakar kacikamin burina kazama babban mutun kuma shahararre wanda duniya ke alfahari dashi ko ina acikin ƙasarnan zancenku akeyi kaida ƴan uwanka kuma abokanan aikinka najeebullah ina alfahari dakai amatsayin ɗan cikina inasonka najeebullah Allah yayiwa rayuwarka data aurenka albarka in sha Allah gobe idan Allah yakaimu dasafe zamuje Gombe awarware auren ɗayar seka dawo da ɗayar kutare gidanku.


Tunda Abba yafara magana zuciyarshi ke dukan tara tara yanajin wani irin abu nashiga acikin ranshi mekamada sanyi ko nutsuwa,,,har yakai karshe bece komaiba yana saurarenshi seda yaji yadasa ayane "yacije lisp ɗinshi ahankali yace "Please kadena kuka Abba nibakamin komaiba hasalima gata kamun sewanda yakeda gata ne ake daurawa aure kawai abashi mata batareda ko sisinshiba musamman mace irin Maryam Abba ngd sosai da ka mallaka min mace data kasace abun alfari agareni amatsayin matar aurena, i love You more my lovely dad, yaƙarasa zancen yana mannawa Abba kiss a hannu tare da ƙanƙameshi ajikinshi....wani irin ajiyar zuciya Abba ke saukewa jiyakeyi kamar an sauke mai wani nauyi akanshi sedai kuma abinda ke buga Mishi zuciya bewuce sunan Maryam da mejo yafaɗa ba tunda yaji wannan kalmar akunnenshi zuciyarshi ke tsinkewa sedai yarasa miyakawo Mishi hakan.... ɗagowa yayi yana murmushi yace Allah yayi muku albarka kaida dukkanin ƴan uwanka, daga hakan Abba yajuya yafice...da kallon so yabi mahaifin nashi cikin mugun tausayinsa shidama betaɓa riƙa shi dakomaiba arayuwarshi, juyawa yayi yakoma bedroom ɗinshi.


Wani kayataccen murmushi gimbiya mardeeya dake zaune tana kallonsu tasaki kafin tace "dani kike zancen Jamila angama da wannan babin, Allah ya dawwa mardaku acikin farin cikin ahalin Hannah. Daga hakan taɓacewarta ɓatt kamar bata wanzu awurinba.




Yana shiga ɗakin yaɗauko doguwar riga zesakawa Isseta, zuwa yayi wurin gadon yariƙo hannunta da nufin yatadata sedai yadda yaji jikinta da bala'in zafi kamar wuta yatada Mishi hankali, "innalillahi wa'innailaihi raji'un yafaɗa cikin tashin hankali kafin yace "zazzaɓi ne hakan Maryam? Ya Salam taso nasaka Miki riga Sena karɓo Miki magani, yafada, yana ƙoƙarin tadata zaune...ihu tasaki seyanzu tasamu zarafin yin kuka, cikin kukan take faɗar"washh Allahnaa yah najeeb bazan iya zamaba zafi nakeji sosai aƙasana...ido mejo najeeb yawaro cikin sabon tashin hankali yace "innalillahi kardai najiwa ƴar mutane rauni, baradai nasaka Miki rigar semuje hospital yafaɗa hankalinshi duk atashe yasaka mata rigar daganan kwance kana yasaka tashi yafito.




Abba nasauka perlor yagansu duka zaune...cikin kissa Hajiya umma tashiga yimishi sannu dazuwa kamin taɗora da faɗar "kazo ganin son ne? Hala kaga dawowarsu a TV? "Eh wlh jamila naga komai kuma naji daɗin hakan nama gaya Mishi yashirya gobe zamuje garinsu yarannan domin komai yazo ƙarshe. "Tunda yafara magana wani irin ƙunci da tuƙuƙi zuciyata keyi amma tadake tana sakin wani irin murmushi sabida zamanta makira tace "kai gaskiya naji daɗi sosai yau Alhaji dakanka kaje ganin my son ai wannan abun farin cikine....yabuɗe baki zeyi magana kenan Ummi tazo wurin tace "Abba wai anty hawwa tanaso taganka shine tace in gayama. Da mamaki Abba tace wacece anty hawwa kuma? "Au matar da ka aurawa my son mana ko kana nufin bakasan sunantaba? Hajiya umma takarɓe zancen. "Okay nagane jekice tazo to. "To Abba cewar ummi tana barin wurin...itadai Hajiya mama da kallo kawai take binsu tana jinjina girman makircin Hajiya umma dudda cewar tasaba dashi amma kullun tayishi mamaki take ƙara bata.


Ahankali anty hawwa tazauna ƙasa a perlor kusan Hajiya umma tana gaida Abba..ya amsa mata cikin sakin fuska kana yace "mike faruwa ne ƴata? Ina fatar babu matsala dai? "Kanta a ƙasa tace "bakomai Abba dama nace ina neman izinine nafara kulada girkin mijina da wasu abubuwan konima zan samu ladar hakan kamar yadda ƙanwata kesamu tunda naga yadawo gida yanzu, taƙarasa zancen kamar wata muna fuka... ɗan shiru Abba yayi yana jinjina girman rashin kunyar yarinyar...hajiya mama ma abinda take tunanin kenan domin yarinyar tayi tsaurin ido...nisawa Abba yayi kana yace "to shikenan ƴata karki damu in sha gobe duk komai zawuce. Itama ƙanwarki ba damar kula da lamarinshi aka bata tunda bazeyu yazauna daku ku biyu ba. "Amma Alhaji inaga itama waccen da mamarsu takai part ɗin son itama tadawo nan har idan yaɗauki wadda zezauna da ita inaga shine Adilci ko? "Au dama a pert ɗinshi take?? Cewar Abba..."eh acan take. "To shikenan Bara.. beƙarasa zancenshiba mejo yasauka daga part ɗinshi... dukkansu da kallo suka bishi kamar yadda shima ɗin kallonsu yakeyi...anty hawwa kuwa kamar tazo ta rungumeshi kozataji sanyi aranta.... ahankali yazauna yana gaisarda iyayen nashi tunda lokacinda yadawo isseta yahanashi ganin kowa se ita...cikin sakin fuska Hajiya mama ta amsa, Hajiya umma kuwa tashi tayi sada tazo inda yake zaune tazuuna kana tariƙo hannu tana faɗar "sannu my son ya gajiyar tafiya? Lpy qalau alhmdllh umma yafaɗa kanshi aƙasa domin bayaso tace zatayi kissing ɗinshi kamar yadda tasaba...hakance kuwa ta kasance domin ɗago kanshi tayi danufin yimai kiss ɗin setaji Hajiya mama na faɗar "nejeeb ina Maryam take ne? Naga bata fitoba kuma lokacin ɗora dinner yayi. Kafin takaiga yimai kiss ɗin yace "am dama dama batajin daɗi ne mama shine nace ko hospital zamujene? Yafaɗa ƙanshi aƙasa. "Innalillahi wa'innailaihi raji'un suka faɗa atare har Abba kafin Hajiya mama tace "miya sameta hakan?? Abba kuwa cewa yayi kakaita asibiti mana ana zaunawa daciwo agida.... Shidai kanshi na ƙasa yakasa cemusu komai seda yaji Hajiya mama na fadar "wai badakai nake
magana ba najeeb miyasamu ƴar mutane? Ahankali yamiƙe tsaye kana yaɗan sosa ƙeyarshi yace Nima bansaniba mama kawai zazzaɓi ne kuma bata iya tafiya kije kigani yana gama faɗar hakan yabar perlor, dukkansu baki suka saki suna kallonshi inda ƙirjin hajima Ummu ke dukan 100,100 Hajiya mama kuwa da hanzari tamiƙe zuwa pert ɗin nashi....!




















Autar alheri ✍️🪽🪽🪽🪽🪽🪽🪽🪽🪽🪽


MM _ NN




Page 85 & 86


"Akan gadon tahango isseta kwance tana rawar ɗari cikin sauri ta ƙarasa gareta tareda yaye blanket ɗin... subhanallah shine abinda ya fito daga bakin Hajiya mama ganin yadda isseta ke karkarwa jikinta na fitarda wani irin hucin zafi kamar wuta. Ahankali ta ɗagota domin ta tadata zaune, wani irin ihu tasaki tana ƙanƙame hannun Hajiya mama domin ta ɗauka mejo ne cikin Muryar shagwaɓa da kuka tace '"nashiga ukku wayyoo Allah yah najeeb please kabarni wlh bazan iya tashi ba nagayama, taƙasara zancen tare da komawa takwata tana karkarwa. Atake Hajiya mama tafahimci inda abun yadosa cikin ranta tace "ikon Allah wato najeeb muyarenawa hankali betaɓa kusantar yayinyar nan ba seyanzu amma yace yayi, Humm ai shikenan tunda ita kazaɓa nikaina nafi son yazauna da wannan ɗin domin hankalina yafi kwanciya da ita, da wannan tunanin hartazo general perlor ɗin, suna nan zaune inda ta barsu anty hawwa ce kawai batanan. Wayarta ta ɗauka tashiga kiranshi bugu ɗaya ya daga, batajira mizeceba tace "kana ina najeeb? Banji miyace mataba tace okay kazo yanzu, daga hakan tayanke wayar tare da komawa pert ɗin nashi....koda yashigo a perlor yasameta zaune cikin haɗe huska tace "seka ɗauketa kakaimin ita bathroom domin bazan iya daukar taba...bece komaiba yawuce tare da ɗaukar ta yakaita bathroom ɗin yadawo bedroom yazauna...itako Hajiya mama kayan gyaran data ɗauko ɗakinta tasaka a bath ɗin bayan ta tara ruwa masu ɗimi aciki kana tazuba kayan maganin tatemakawa isseta tashiga, sosai Hajiya mama tagasa isseta tare da temakon waƴannan magun gunnan...hakan yasa dasuka gama tafito da ƙafarta dudda cewar bata takawa dede amma taji daɗin jikinta sosai...da kallo yabisu seda Hajiya mama ta watsamai harara kana yamiƙe yana murmushi yafice daga bedroom ɗin....dakanta ta temaka mata tashirya kana tariƙo hannunta suka fito domin suje hospital sedai fa dasukazo matattakalar dazata sadasu da general perlor takasa takawa, seda Hajiya mama tace yazo yaɗauketa yasakata a mota tunda shine sanadin komai


Cakin sauri yazo ya ɗauketa kamar baby yanufi waje da ita. Abba yace "subhanallah abin haryakai hakan? To Allah yabata lpy konazo mutafi?? "Ah'ah base kazoba Alhaji aima yanzu zamu dawo in sha Allah...to shikenan Allah yabata lpy yawwa munir kuje kakaisu hospital matar najeeb ce balafiya, yafaɗa yana kallon munir ɗin da shigowarshi kenan..to Abba cewar Munir yanabin bayan su.


Hajiya umma kuwa cikin mugun tashin hankali da firgici wanda makircinta yakasa ɓoyeshi tamiƙe tanufi bedroom ɗinta kamar zata tashi sama aranta kuwa se fatar takeyi Allah yasa ba kusantar isseta najeeb yayiba yau dakuwa ƙaryarta taƙare inkuwa hakane to setayi ajalinsu sedai dukkansu surasa, ahakan tafaɗa ɗakinta na sirri ido rufe sedai kiran duniya tayiwa tsijuju amma yaƙi zuwa hakan yasa doli ta haƙura har zuwa anjima ta ƙara kiranshi.


Suna zuwa asibitin aka karɓeta amma juyin duniya mejo yaƙi bari namiji yadubata kala Hajiya mama na faɗa harta dawo lallaɓashi amma firr yaƙi yadda ahaka doctor Ziyad yazo wurinshi amma yahaɗe fuska damma karyaga damarshi...murmushi doctor Ziyad yayi afili yace "saranka inuwa ƴallaɓai mejo nibazance namiji yaduba maka mataba wata doctor ce nakira dudda bata hospital ɗin amma tana zuwa yanzu, yaƙarasa zancen yana murmushi. Se alokacin yaɗan saki ranshi Munir kuwa se dariya yake musu aɓoye....lokacin da doctor deejah tazo tayi mugun mamakin ganin raunin dake jikin isseta cikin tashin hankali tace "innalillahi wa'innailaihi raji'un har mutun nawa sukayi Mata fyaɗe hakan Hajiya? Tatambayi Hajiya mama bayan ta fito...cikinjin kunya Hajiya mama tace "wlh ba fyaɗe aka mataba mijintane yayi mata hakan..ido doctor deejah tawaro tace "miji dai?? "Wlh kuwa kinsan halin yaran yanzu abunka kuma ga soja sedai Allah ya kyauta ina fatar dai be illatataba? "Humm lallai ma dan yana soja se'akace Mishi fagen yaƙi ne? Ina yake mijin nata? "Yana waje cewar Hajiya mama cikin rauni... tashi doctor deejah tayi tafito wajen tasamu Munir zaune yana danna wayarshi shiko gogan yana ɗan nesa dasu kaɗan shida doctor Ziyad. "Haba ɗana wannan wacce irin aika aika ce hakan? Kasamu ƴar mutane sekaje afagen yaƙi kake? Waya gayama anayiwa mace hakan? Abu kamar namuji goma sukayi anfani da ita wlh baka kyauta ba kuma kasani kaida ita sebayan wata biyu yanzu ma ɗinki zamu mata maza karɓi kakawo mana wannan kayan domin wlh se an mata dinki har huɗu wannan wanne irin rashin imanine da tausayi. "Sororo Munir yayi yama kasa karɓar takardar yana sauraren yadda doctor deejah ke surhuta Mishi masifa kamar shine mijin nata...sukuwa dagacan da suke tsaye doctor Ziyad yahangi doctor deejah kamar ranta a ɓace yake hakan yasa sukazo wurin..suna ƙarasowa Munir nakarɓar ta kaddar zebar wurin. "Miyafaru ne doctor? Cewar doctor Ziyad.. "aikomima yafaru Ziyad wannan marar imaninne nakeyiwa faɗa mana yasamu yarinya ƙarama sekace wanda akace filin yaƙine aka bashi inda ta nakasa aikanka kayiwa..tunkamin takai ƙarshe yadokawa Munir wata muguwar harara hakan yasa yabi bayansu yawuce yana dariya, faɗar yakeyi toni miye nawa aciki big bro kaine kayi ɓarna kasha daɗinka kuma anzo ana tuhumata kaikuwa kanamin wannan harar taka me tada hankali.


Anan kuwa murmushi doctor Ziyad yayi kana yace "wanda kikeyiwa faɗa bafa shine mijintaba doctor Kinga mugun nan yafaɗa yana nuna mejo dayawani haɗe rai kamar besan minene dariyaba...juyawa doctor deejah tayi ta kalleshi sekuma yayi mata kwarjini amma dukka hakan seda ta balbaleshi da faɗa inda tace kuma seta gayawa iyayenshi kar abashi ita setayi wata biyu tawarke tukunnah....shidai bece komaiba illa ƙasa dayayi da kanshi yanajin tausayin Maryam ɗinshi...ba'ajimaba Munir yakawo kayan aikin,,,hakan akayiwa isseta ɗinki har huɗu abun tausayi,,, gaskiya mejo bekimantaba awannan gaɓar😢 bayan angama komai suka nufi gida...tun a harabar gidan sajad kemata sannu domin koyanzu ɗaukota mejo yayi. Shikuwa yana shirin biyar su hospital ɗinne segasu sundawo.


"Kai najeeb pert ɗina zaka Kaita cewar Hajiya mama lokacinda yanufi pert ɗinshi da ita...jiyowa yayi tare da narke fuska kamar zeyi kuka yabuɗe baki zeyi magana kenan ta ɗaga Mishi hannu...hakan yawuce da ita pert ɗin Hajiya mama dukkansu suna zaune a perlor su ukku, da kallo suka bishi cikin mamaki...shiko ko takansu bebiba yawuce da ita har bedroom ɗin Hajiya mama ya kwantar da ita kana ya manna mata kiss a lips ɗinta yafito, hakan yawucesu cikin tafiyarshi me jan hankalin ƴammata, seda yariƙa Handel ɗin ƙofar zebuɗe yafice cikin sauri anty hawwa tace "yaya najeeb kamar yadda taji ummi nakiranshi. Cak ya tsaya badan komaiba sedan yanason sanin wacece wannan memishi katsalan ɗan acikin al'amarinshi....itako wani mugun daɗi taji ganin yatsaya dudda bejuyoba...ahankali tatako hartazo inda yake cikin kissa tace "please yaya najeeb inaso zanyi magana dakaine idan badamuwa. Bece mata komai ba amma yajiyo yana fuskantarta...wani irin kwarjininshi anty hawwa tagani hakan yasa tashiga kame kame kafin tasamu zarafin cewa "dama nace inaso naɗan rinƙa yima wasu hidimarne kozan samu lada amatsayina na matarka, taƙarasa zancen kanta aƙasa....shiko gogan wani ɗan iskan kallo yake Binta dashi aranshi yake maimaita kallimar mata, kafin bayanan su Abba sudawo mai nacewa aida yarinya biyu aka ɗaura mai aure. Sajen fuskarshi yashafa yana sakin wani ɗan iskan murmushi kafin ta ɗage gira ɗaya cikin wani ɗan iskan sexy voice yace "au really? Aiban sankibane amma zaki iya zuwa pert na ummi kikaita daga hakan yajuya yabar perlor...wani irin ihu anty hawwa rasaki tare da juyi tana rawa tace "wlh seni hawwa'u nasan ba namijin daze ɗauke kanshi daga gareni sedai marar lafiya, tafaɗa cikin isa da nuna cewar ita ɗin wata ce...itadai Ummi tuni tabar wurin tanufi bedroom ɗin mama gun Isseta...juwaira kuwa wani uban tsaki taja tana barin perlor..




Gombe state


Yau garin Gombe sun tashi da baƙon al'amari domin ta ko ina shirin tarbar baƙon dazasuyi sukeyi wannan kuma umurnin megirma gwamna ne...damisalin karfe ɗaya narana jirgin dake ɗauke da baƙon yasauka, sedai dagani kowaye wannan babban mutun ne duba da yadda jami'an tsaro suka cika airport ɗin tako ina...nashi security ne suka fara saukowa manyan sojojin ƙasar Niger kowanne ɗauke da bindigarshi kana shi uban tafiyar yasauko,,, kyakkyawan dattijo buzun asali mecikar haiba da kamala gakuma kwarjini wannan baƙon bakowa bane face Alhaji abdussalam idis shugaban kasar Niger shine yadira Nigeria dakanshi neman ƴarshi a garin Gombe.....megirma gwamna dakanshi yazo tarbarshi cikin farin ciki da girmamawa...hakan yasa doli yashiga motocin da gwamna yazo dasu beshiga tasu sapwan ba...cikin girmamawa suma wasu security suka buɗe musu wata dalleliyar mota suka shiga sapwan da nazeer....cikin wadda Alhaji abdussalam yashiga kuwa ita hajiya Hannah tashiga. Yanzu kam babu zancen sauka hotel gidan gwamna kawai suka nufa..


Lagos


Wanka yayi yafito perlor bayan ya gama shirinshi yazauna yana wayada general Faruk.. sallama sukayi itada ummi suka sahigo, cikin sauri Ummi tace "ina wuni yah najeeb wai anty hawwa tace kace nakawota pert ɗinka,,, tafaɗa cikin fargaba kar anty hawwa taja mata duka idan bashine yaceba...kai kawai ya ɗaga mata tare da nuna mata hanyar barin pert ɗin.....!




















Autar alheri ✍️🪽🪽🪽🪽🪽🪽🪽🪽🪽🪽


MM _ NN


Book 5


Page 87 & 88


"Cikin sauri ummi tafice daga pert ɗin..shiko yaci gaba da wayarshi dayakeyi cikin nutsuwa yana lunshe kyawawan blue eyes ɗinshi...sosai anty hawwa tashagala da kallonshi yadda ɗan ƙaramin bakinshi kejuwa yana magana cikin aji kamar ba namujiba, ita kanta datake macen seda tarena kanta agabanshi, jitakeyi kamar taje yarungumeshi kozataji sanyi aranta,,,harya gama wayar yaɗago yana ƙare mata kallo batasan yagamaba tanacan talula duniyar shauƙinshi gaya atufe bashida riga sedai dogon wando kawai faffaɗan girjishi awaje sumar dake kwance akai se sheƙi takeyi gwanin sha'awa...ganin gaba ɗaya tamutu da kalloshi yasa yaɗan taɓe bakinshi yana ɗauke kanshi daga gareta. Kusan minti 10 suna ahakan kafin yamiƙe zuwa bedroom ɗinshi yabartanan a tsaye....bata Ankara daya tashiba seda taji ƙarar rufe Ƙofa dayayi...wuri tasamu tazauna tana sauke numfashi se matsar ƙafa takeyi dan masifa😹daganin ɗan kyakkyawan sauri seki ɗarsawa kanki lalura haba anty babba🤩 najeeb kam bayan yashiga bedroom ɗin seda yaɓata kusan awa ɗaya befitoba yanacan kwancinshi suna tattaunawa akan wannan shugaban ƴan ta'addan domin kuwa mejo tanimu yaje binciken inda suka kaishi amma an hanashi shiga a dokar wurin duk wanda ya ajiye mailaifi shine kawai keda damar shiga, wannan abun kuwa yaƙonaran Alhaji tanimu shiyasa General Aliyu yace dasun dawo daga Gombe zasu fiddashi sumakashi koto kar wani abun yabiyo baya, seda suka gama zancensu tukkunna yamiƙe yaƙara yin wanka yafita...anan yasameta inda yabarta ko kallon inda take beyiba yafice warshi...itako
Jakar ko ajikinta tunanin matakeyi maybe yana saurine shiyasa bemata magana, hakan yasa tagyara kawai tayi kwanciyar ta akan kujera( nikuwa nace kina ruwa anty hawwa)




Mejo nafita Captain jameel yataso yabuɗe Mishi mota suka fice segidansu general Aliyu...koda yashigo gidan bakowa a perlor se TV kawai dake kunne. Jin motsi a kitchen yasa yaƙarasa can aiko habbey naciki tana aikinta kamar yadda yayi tunani,,gaidata yayi cikin girmama, takuwa amsa Mishi cikin sakin fuska tare da yimusu murnar samun nasara a aikinsu. Dazefita ne yaɗauki plate yazubo farfesun naman rago da babbey tasauke daga wuta kana yaɗauki donut ɗaya yafito. "Yeee yah najeeb oyoyo mufeedah tafaɗa cikin farin cikin ganinshi tanayowa kanshi...murmushi yasakar mata batareda yace komaiba. "Yah najeeb kundawo lpy? "Lpy qalau rigimammiyar habbey y kk y school? "Ɗan turo bakinta tayi cikin shagwaɓar dasuka saba mata da ita tace "nidai Allah ba rigimammiya bace, yawwa garama da kadawo yau bazaka fitaba seka kaini gun anty Maryam.. tafaɗa dede lokacinda suka shigo

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login