Showing 72001 words to 75000 words out of 109347 words
Chapter 25 - MEJO NAJEB Book 1 Complete Hausa Novels By Autar Alheri .txt
arai inaso naganshi please.. "hummm kawai Ummu tace tareda janyo wayarya tabuɗe wata folder meɗaukeda picture ɗin mejo najeeb sunfi 50 tamiƙa mata, kawai batareda tace mata komaiba.
Karɓa tayi tana kallon picture ɗin, ido tazaro cikin mugun ruɗani murya na rawa take nuna picture ɗin inda yake sanye da kayan sojoji yana zaune akan mota waya maƙale akunnenshi tace "wan..wan..wannnan shine mijin nawa wannan ɗin?? Wayyoo Allah Abba ka kyauta mun daka aurar dani ga wannan haɗɗen guy ɗin wow he's very handsome wlh. Tafaɗa cikin nuna zalamarta akanshi afili, tana kallon sauran picture ɗin...wani mugun tsaki juwaira taja kamin tace "iska nawahalarda me kayan kara anty hawwa domin wannan guy ɗin yamiki nisa kima Sena murnar mijinkine domin wlh baze zauna dakeba.
Ɗan shiru anty hawwa tayi tana kallon ƙanwar Tata kamin tace "mikike nufi juwaira muguwar fata zakimun baƙin ciki kikemun kome? Wannan wacce irin banzar maganace hakan? To tunda baze zauna daniba aike sekije ya zauna dake wai ko sonshi kikeyine bansaniba?? "Au seyanzu kikasani? Cewar juwaira kafin tayi guntun murmushi taci gaba da faɗar"idan nasoshi laifine? Tunkafin kisanshi nasanshi kuma nake dakon soyayyar shi, shiyasa nace baze zauna dakeba domin kuwa bazan bari kurasamin farin cikinaba sabida babu yadda za'ayi yazauna damu duka ukku ita isseta ubanmu ɗaya kekuwa uwarmu ɗaya ubanmu ɗaya sabida hakan doline ɗaya ce zayi nasara kuma wlh komizefaru sedai yafaru amma srkunbarmin mijina domin yah najeeb nawane dan ki kaɗai akayi shi kuma zan nuna muku nawane ɗin da gaske.. "tasss kikaji anty hawwa taɗauke ta da kyakkyawan mari tana watsa mata mugun kallo cikin takaici take faɗar"yoshe kikazama marar hankali juwaira?? Mijin nawa? Kuma agabana? Yoshe reni yashiga tsakanina dake hakan?? "Tun ranar da kika kulla alaqa da muradin raina tun lokacin reni yashiga tsakaninmu bakuma mari ba kokasheni zakiyi wlh sedai kikasheni amma bazan barmiki yah najeeb ba, cewar juwaira cikin tafasar zuciya da baƙin kishinda kecinta.
"Tofa 🤔yau inaganin ikon Allah wai miye hakan kukeyine? Duk akan namuji ɗaya wanda bemasanda ku ba a duniya kuke wannan tashin hankali? Ummi tafaɗa cikin mamakin wannan lamarin nasu....wani mugun kallo anty hawwa tawatsawa Ummu kana tace "besanda niba amma yasanda aurena akanshi kuma yasan inada hakki akanshi sabida doline zesan dani wlh daya dawo gidannan zakuga asalin wacece hawwa.....wani mugun kallo juwaira tawatsa mata zatayi magana kenan isseta tashigo perlor dauke da sallama abakinta.
Dukkansu da kallo suka bita...itama kallonsu tayi sheƙeƙe kafin tayi magana ummi tace "anty Maryam harkin fito?? "Eh nafito Ummi ina mama? Tana ɗaki inaga sallah takeyi..."okay dama zan tambetane miza'agirka agidan yau?? Idan tafito kitambeta seki sameni a perlor.. "okay to amma ai yau Hajiya umma ce dagirki domin yau girkin mama yafita baranazo na tambeta. "No yizamanki barana tambeta dakaina cewar isseta tana barin perlor.....wani mugun tsaki anty hawwa taja afili tace "wai neman gidin zama aiko duk wannan bata fiddake wlh isseta dama bansan wannan ne mijinba amma yanzu za'abuga asalin wasan..tana rufe bakinta Ummu ta ƙyalƙyale da dariya cikin shaƙiyanci tace "aiko indai gindin zama ne anty Maryam tasamu kedai kemanshi ayanzu domin gindin zama duk bewuce soyayyar wanda ake yaƙin akanshiba kuma ita tarigada tasamu kekuwa bemafasan dazamankiba, taƙarasa maganar tana koma sakin dariya...gabaki ɗaya ta ƙukardasu hakan yasa bawanda yace da ita komai a cikinsu amma tabbas da ba'a gidansu suke zauneba wlh dasesun lakaɗamata shegen duka gobe bazata ƙara kawo musu renin hankaliba..
Isseta nafitowa taga anashigiwa da kayan abinci ana kaiwa kitchen wasu daga cikin sojojin gidanne keshigowa dasu yah munir nahiye dasu abaya,,,,suna haɗa ido tasakar mishi murmushi, shikuwa yace "anty Maryam Barka da fitowa, "yawwa barka yah munir tafaɗa cikin sakin fuska.."ido yaɗan waro tareda rike baki yace "Please dan Allah kidena ce mun yaya karisa babban yaya yakarairayani abanza wlh bazan iya daukar dukan sojaba, yaƙarasa faɗa yana ƴar dariya...itama dariyar tayi tana faɗar aikuwa bazan denaba tanufi part ɗin Hajiya umma...shikam kitchen ɗin yashiga bayan yakira siyana suka shiga jera kayan abincin.
Koda tashiga perlor hajima umma bakowa hakan yasa tanufi bedroom ɗinta nanma bataga kowaba juyiwa tayi zata fito tariƙa jiyo sautin magana kamar bana mutaneba kamar kuma Muryar Hajiya umma cikin mamaki taƙarabin ɗakin da kallo amma ba kowa juyawa tayi kawai zata ficewarta idonta yasauka akan wata kofa agefen widroup ɗinta, ƙarasawa bakin ƙofar tamirɗa seta jita kulle, gaya kuma tana jiyo Muryar Hajiya umma aciki.. gimbiya mardeeya dake biyeda ita tunɗazu batareda tasaniba itace tashiga ya mirɗa key ɗin ƙofar tabuɗe isseta na ƙara mirɗawa seta buɗe,,,shiga tayi tukunnah tarufe setaga hanyace me nisa tafiya tashigayi hartazo dede ƙofar wani bedroom dake cikin wurin..adede anan taji maganar Hajiya umma raɗau tana faɗar "Nima bansan misuke nufiba amma wlh bazan basu wannan damarba doline ayi komai aƙare domin aikina ya kammala,,bataji me akace mataba sedai kawai taji tace "a'a ba gimbiya laweesat bace amma tabbas akwai ko wacece tashigo gidannan, shirutayi tana sauraren maganar da'ake mata kafin takoma cewa "shikenan aida yadawo zansan abinyi za'ayita taƙare kawai domin tabbas sunason mayarminda hannun agogo baya..isseta nacikin sauraren ta setaji kamar motsi za'sfito hakan yasa tayi saurin ficewa daga wurin tafoto zuciyarta fall tunani anya Hajiya umma nada gaskiya kuwa mitake aikatawa ne datake zancen za'amaida mata baya? Wanene zekawo ayita taƙare? Ya'akayi Hajiya umma yasanda maah ɗinta? Min mike faruwa agidanan? Wacece matarda ta iskota ɗakin mejo?? Wake zuba aiyukkan sihiri acikin duka abincin mutanen gidan? Gaskiya zuciyarta takasa yadda da Hajiya umma domin itadai tunda tashigo gidannan hankalinta be kwanta da matarba sedai ba yadda zatayi da ita tunda mahaifiyar mijintace? To amma anya wai itace mahaifiyar shi ba Hajiya mama ba domin Hajiya mama tafi nuna kawaici akanshi maybe itace tahaifi najeeb kauda idone takeyiwa Hajiya umma, kai gaskiya ƙwaƙwalwarta tashiga ruɗani amma doline tasakawa Hajiya umma ido domin dai wlh baya yadda da ita ba...da wannan tunanin ta isa kitchen ɗin koda taje a gama jera komai har yah munir tafice...kayan abincin tashiga dubawa tagansu lafiya qalau murmushi tayi kawai kana tashiga neman abinda zata dafa, ɗora sanwar tuwon simo tayi cikin ƙanƙanin lokaci tatuƙa tuwon tasakashi sulala,,,tana cikin haɗa kayan miyar agusi Ummu tashigo kitchen ɗin cikin farin ciki tace "anty Maryam harkin fara ke kaɗai?? "Eh Ummu gashi kuwa inayi.. "to shikenan kawo natayaki tafaɗa tareda fara gyara mata kayan miyar...sosai Ummu tazage tataya isseta aikin sukayi towo damiyar su wadda tasha bisashen kifi da naman kaza, bayan sun gama suka haɗa fruit salad kawai tareda dafa coffee ko akwai masu buƙatar shi,,,nantake gidan yaɗauke da ƙamshi matada tsohuwar yunwa🤣seda suka gama komai suka jera a dining suna cikin gyara kitchen ɗin ne Hajiya umma tashigo tanabin kitchen ɗin da kallo kamin tamayarda idonta kansu tace...!
Idan banga comment ɗinku ba🧐🧐🧐 bazan ƙara update ba se bayan Sallah🧏♀️
Autar alheri ✍️
🪽🪽🪽🪽🪽🪽🪽🪽🪽🪽
MM _ NN
Book 4
Page 77 & 78
"Tace "mikukeyi a kitchen ne?? "Girki mukayi muku Hajiya umma, Ummi tabata amsa. "Girki kamar yaya? Wayasaku? "Bakowa kawai anty Maryam ce tazo zatayi Sena tayata...wani mugun kallo Hajiya umma tayiwa Ummi kamin tashigo kitchen ɗin duka tana abin kayanda tagani ciki da kallo cikin mamaki takebin komai ɗaya bayan ɗaya kamin tace"wai duk ina kayan abincin gidannan? Kuma wayakawo wannan? Cikin tsoron yanayinta ummi tace "yah munir ne yakawo wannan bansan ina yakai wanda yakwasheba. "What?? Shi munir da kanshi ne yakwashe kayan abinci yakawo wasu? Duk yoshe Alhaji yasa aka kawo wannan dahar za'abanzatar dasu? Tukunnah ma uban waye yasakashi?? Tafaɗa cikin fishi,, wanda yayi bala'in tsorata ummi...isseta kuwa da tun shigowar Hajiya umma tashigo batace komaiba seyanzu taɗago tana kallon Hajiya umma da murmushi kwance akan fuskarta tace "ayya Hajiya sorry please nicenan nasakashi domin ban yadda da kayanba shiyasa nasa yafitar dasu yakawo muna wasu kuma naje natambeki miza'adafa bansameki a part ɗinki ba shiyasa kawai narage miki aikin kafin kizo kinga har mun gama......tunda isseta tafara magana Hajiya umma kebinta da wani wulaƙantaccen kallo hartakai ƙarshe cikin kakkausar murya tace "ohh mikike nufine? Kinanufin karyamin doka zakiyi agidan daga zuwanki shekaran jiya har kin isa kisaka ayi abu agidannan batareda nasaniba? Tukunnah ma akan wanne dalili? Dawanne matsayi kike taƙama dahar zaki zartada abu agidanan. Bada saninaba? "Humm Hajiya kenan matar babban yaron gidan mana kinga kuwa inada damarda zanyi komai ayadda nakeso tunda gidan mijinane, tafaɗa tana murmushi....ido ummi tawaro ganin yadda isseta keyiwa Hajiya umma magana babu tsoro balle fargaba kuma babu girmama amma bada rashin kunya ba.
Maganar Hajiya umma ce tadoki kunnenta inda take faɗar karki sake shigowa kitchen ɗinnan kinji nagaya miki kuma kidena taƙama da auren najeeb kibari har idan yakarɓeki tukunnah tunda nasan kinada labarin ku biyu ne aurenku yake kanshi doline da wadda yazaɓa zezauna kuma baze zaɓi wadda ban amince da itaba amatsayina na mahaifiyarshi sabida hakan doline kibi umurnina agidannan kamar yadda kowa yakebi indai kinason zamada ɗana, kuficemun dagani, tafaɗa cikin bada umurni....batace mata komaiba tajuya tareda nunawa ummi wata Warmer dasuka zuba soyayyen nama tace "ummi ɗauki wannan muje...bamusu ummi taɗauka jiki narawa tafice daga kitchen ɗin.
Tana fita isseta tayi wata irin juyiwa tana fuskantar Hajiya umma idonta gabaki ɗaya sunjuye ga dukkan alamu tunɗazu da suke magana da Hajiya umma ba ita bace kauda ido ne..kafeta da ido Hajiya umma tayi kogizau baba....itako cikin Issa da izza taƙaraso dabda ita yadda zasu iyya jiyo numfashin juna tace "Jamilaah, takira asalin sunan Hajiya umma...cikin mugun mamaki Hajiya umma ke kallonta amma bata nuna hakan afiliba, domin itama kallonta takeyi yadda itama take kallonta, babu ko ɗar azuciyarta. "Gyara tsayuwa Isseta tayi kana tace"Jamila inamiki kashedi akan kifita harkar Maryama babu ruwanki da duk abinda zatayi domin kuwa baki isa kidakatarda itaba kuma abincin gidannan yanzu tafara harse ta tsabtace ƙazantar dake gidannan tukkuna kozata dena yinshi kuma kisani idan baki saka mata idoba kikace zakiyi jayyaya da ita to wlh kasa ce zata tono wuƙar yankata kisani nasan komai Jamila kuma bana barin bashi domin banacin nakowa sabida hakan wlh duk wanda yaci nawa seya biya kije kitambayi mushrikin tsohon dakike taredashi kiji wacece gimbiya mardeeya idan kunne yaji jiki yatsira, tana gama faɗar hakan tanufi ƙofar zata fice anan sukayi karoda Hajiya mama zata shigo kitchen ɗin sabida Ummi tafaɗa mata abinda ke faruwa dudda cewar bataga lokacinda gimbiya mardeeya keyiwa Hajiya umma gargaɗi ba...dasauri gimbiya mardeeya taja baya tamkar isseta ce tareda cewa sannu da fitowa mama.."yawwa sannu Maryam lafiya kuwa? Tatambaya gudun kar wani abun yafaru daga baya. "Lafiya qalau mama sallah zanje nayi..to shikenan yimaza kije domin kam lokaci yayi. Tana gama faɗar hakan tajanye Isseta tawuce zuwa pert ɗin mejo......da kallo tabi Hajiya umma datayi tsaye kamar andasata kafin tasaki wani shi'umin murmushi tajuya tareda barin wurin....Hajiya umma kuwa tadaɗe tsaye a kitchen ɗin kafin tafito tanufi nata part kamar zata tashi sam, kida tashiga tadubi lokaci setaga ba lokacinda yadace tashiga wancan ɗakin bane tsaki taja kawai tajuya zuwa bathroom ɗinta..
South Africa
Yana fitowa daga wanka yashirya cikin ƙananun kaya yafito perlor sedai yaga bakowa,, wayarshi yaɗauka yakira general Faruk yafaɗa mishi inda suke,, okay kawai yace tareda yanke wayar yafita....ababbar hidikwatar sojoji dake ƙasar yasamesu inda wani commander kemusu bayanin yadda suke neman wannan ƴanta'addan suma domin su yiwa ƙasar muguwar ɓarna amma sunkasa samunsu duk inda sukaji labarin su koda zasuje sesu tarar sun gudu.....shiru dukkansu sukayi kowanne da abinda yake tunani kamar daga sama sukaji Muryar wani saurayi yace "Ni nasan inda suke domin nagansu idan kunaso kuzo zan kaiku....dasauri duk suka ɗago suna kallonshi matashin saurayine kyakkyawa wanda baze wuce shekaru 22 ba....wannan commander ɗin ne yafarayin magana cikin jin daɗi yace "that's good my buy yanzu bara ashirya runduna semu tunkaresu zuwa gobe, yafaɗa tareda zaro wayarshi yana ƙoƙarin kira. "No base anhaɗa runduna ba mukadai zamu iya kawai aje yanzu. Muryar mejo najeeb tadoki dodon kunnensu. Da mamaki wannan commander ya kalleshi kana yayi murmushi irinna manya yace "kakuwa san wakake nufin zamu tunƙara mukaɗai? Kasan haɗarin dake tattare dasu? Ɗan cije lips ɗinshi na ƙasa yayi kafin yabuɗe blue eyes ɗinshi akan commander ɗin yace "yes zamu iya kowanne irin haɗari sukedashi zamu tunkaresu da ƙarfin uban giji zamuyi nasara akansu nidai ashirye bakeda tunkararsu ayanzu nida brother's na yafaɗa kanshi tsaye. "What?? Sedai idan kaine zakaje amma sukan nasan bazasu tunkari wannan haɗarinba kadena yanke hukunci kabari kaji abakinsu tukunnah, cewar wannan commander ɗin. "Humm yasauke numfashi kafin yaɗago yana kallonshi ido cikin ido yace "bayankan hukunci nayiba abinda yakasance ne nafaɗa domin duk abinda naji zan iya araina nasan agun general Aliyu haidar ma hakan abin yake domin bantayin abinda shi baze iyaba sabida yadda bugun zuciyarmu ɗaya bazata saka ɗayanmu abinda ɗaya baze iyaba, hakama general Faruk yaƙullah alaƙa da wannan zuciyoyi namu tun ranarda yaƙullah alaƙa damu, ɗan shiru yayi yaname lumshe kyawawan idanuwanshi kafin yaɗago yana riƙo hannun commander ɗin yaɗora adede zuciyarshi dake bugawa dasauri dasauri...ido duk suka zuba mishi suna kallon yadda yake buɗe idon nashi ahankali yace "kaji yadda zuciyata ke bugawa da soyayyar ƴan'uwana?? Tosuma hakan tasu keyi akaina sabida hakan bazan taɓa bari suyi abinda nasan bazu iyaba koze cutar dasu so we will Reddy to going all, yana gama faɗar hakan yasaki hannunshi tareda juyawa zebar wurin...cikin sauri general Aliyu yamara mishi baya yana faɗar "Yes of course maganar mejo hakan take babuko sirki acikinta..shima general Faruk dakuma su Captain jameel bayansu sukabi,,hakama wannan saurayin....baki sake wannan commander yabisu da kallo kafin yakira wasu mutun ukku daga cikin sojojinsu cikin sauri suka marawa motar su mejo baya....sukuwa kaitsaye inda wannan yaron ke kwatanta musu suka nufa dama kowanensu dashirinshi domin duk sunada bindiga ajikinsu... general Faruk kuwa baƙaramin mamaki kalaman mejo kebashiba domin yaga sahihiyar gaskiya a idonshi kuma abinda yake gani a idonshi shiyake gani a idon general Aliyu tabbas sunayiwa junanso na haƙiƙa shiko mizeyiwa Allah inba godiyaba daya haɗa shi abota da waƴannan bayi nasa, yanacikin wannan tunanin suka ƙaraso wurin inda sukayi Perking ɗin motarsu nesa da wurin kaɗan duk suka fito kowanne ya fidda bindigarshi suna fitowa motarsu commander na isowa hakan yasa suka tunkari wurin gadan gadan babu tsoro balle fargaba sunrigada sunshiryawa tunkararsu ko sukashe ko akashesu(Allah sarki sojojin Nigeria dama nawasu ƙasashen musulmi Allah ya tsareku aduk inda kuke yakareku da kariyarsa😢) ahakan suka tunkari wurin cikin dakiyar zuciya gasu dukkansu basu wuce mutun 9 ba amma hakan suka nufi mutanenda sunfi 40 suna zuwa suka fara musu ruwan wuta tako ina babuzato babu tsammani kawai sukaji saukar harbi....cikin mugun mamakin yadda akayi jami'an tsaro sukasan inda suke suka shiga neman kayan aikinsu, amma cikin iyawar uban giji kafinma susamu nasarar barin wurin su mejo sun ƙararda fiye da rabinsu, hakan akarinƙa musayar wuta babuji babu gani kusan awa ɗaya ana ɗauki ba daɗi dakyar su mejo suka samu nasarar kama duk wanda sukeso sukama acikinsu hadda shugabansu gabaki ɗaya datemakon wannan saurayin,,,hakan suka taso ƙiyarsu agaba suka dannasu mota sojojin South Africa se jinjinawa ƙoƙarin sojojin Nigeria sukeyi domin sunyi abinda sojojin ƙasashe mabanbanta suka kasayi....ababban kurkuku suka kaisu suka rufe dazimmar gobe zasu wuce dasu Nigeria sabida ayanke musu hukunci...haka su mejo najeeb suka fito a jigace suka nufi masaukinsu cikin matsanancin farin cikin samun nasara cikin sauƙi, tun fitowar su suke neman inda wannan saurayin daya temaka musu yashiga amma basuganshi ba ko me kamadashi basuganiba, har suka ƙarasa masaukinsu kowanne yanufi bedroom ɗinshi domin susamu suyi wanka sugasa cikinsu. Tofa abinda su mejo basusaniba wannan saurayin daya temakesu bakowa bane face gimbiya mardeeya itace tazo musu amatsayin wannan saurayin tatemakesu domin suyi saurin gama wannan aikin sukoma Nigeria ayita taƙare.👍aikinki nakyau gimbiyar mata🥳
Lagos
Isseta nashiga bedroom ɗin mejo gimbiya mardeeya takwantarda ita akan bed ɗin tukunnah taficewarta kusan minti 10 tana ahakan kamin tamiƙe ganinta kwance yabata mamaki sosai amma bata kawo komai arantaba tanufi bathroom kawai domin tayi wanka tayi sallah.....bayan tafito daga wankan tashirya kana tayi sallah tana ganawa ummi tazo kiranta aci abinci hakan yasa tabita suka fice general perlor ɗin inda suka samu kowa ya hallara a dining table harda Hajiya umma dasu Munir su juwaira kowa ya fito...kujera ummi taja mata tazauna bayan tagaidasu Hajiya umma da Hajiya mama sedai tayi mamaki sosai yadda Hajiya umma ta'amsa mata gaisuwar....itama su sajad da auta siyana suka gaidata suna santin girkinta tun basuciba sabida Ummi tabasu labarin itace tayi girkin...munir kuwa tunda yagaidata bekoma cewa komaiba domin Allah yasani yanzu yarinyar tsoro take bashi.
Ummi ce tayi saving kowa awurin hadda isseta ɗin se alokacinne kowa yakulada babu mansura Hajiya mama ce tace "Ummi ina mansura baki kirata bane? "Wlh mama nanemeta bangantaba.."eh fa inaga bata gidannan domin ɗazu dazan shigo naga fitar motarta cewar Munir..... okay kawai Hajiya mama tace amma Hajiya umma komai bataceba....hakan a kafara cin abincin inda mutanen gidan seyaba girkin isseta sukeyi suna santin amma anty hawwa da juwaira harma Hajiya umma bawanda yace komai kuma ba wanda yakulada kowa,,,sedai isseta ce gabaki ɗaya hankalinta naga hannun Hajiya umma tana kallo taga kizataga wannan zoben nata amma bata ganshiba hakan ya tabbatar mata dacewar wancan ɗin dai natane, tana zaune tana tsakurar abincin zuciyarta fall tunani har aka gama cin abincin *(inda akabawa ƴar amanarmu ragin da sukayi ita da team teemah p r v🥳 suka cinye suna wawaso dasantin girkin isseta..ohhhh su inna kwaɗairu ƴar amana aci sannu🤩🤩)* suna gama cin abincin kowa yatashi wasu suka nufi perlor wasu kuwa shiga gyaran wurin yayinda Hajiya umma tanufi bathroom ɗinta bayan taduba agogon hannunta.
tana shiga bedroom ɗin tanufi wannan lungun babu sallah balle salati tana shiga tayanjo wani ƙaton madubin tsafi tareda wasu kaya green tasaka ajikinta,,wata ƙatuwar tukkunya tajanyo kana tasaka hula, seda tagama duk abinda takeso tayi tukkunna tazauna tareda saka wannan ƙaton madubin tsakiya tashiga kiran "tsijuju tsijuju tsijuju,, hakan kawai take kira kusan minti 2 kafin wannan mushrikin tsohon yabayyana agareta yana wata irin mahaukaciyar dariya. Ido nazaro arikice ina dubansu dagashi har ita cikin mugun mamaki ganin ashe Hajiya umma ce ketarayya da wannan mushrikin tsohon domin awancan lokacin hular datasaka tahana aga kowacece lokacinda wannan tsohon yabata labarin gimbiya laweesat. "Baki tabuɗe zatayi Magana cikin sauri yadakatarda ita ta hanyar faɗar