Showing 1 words to 3000 words out of 57484 words

Chapter 1 - AURE DA KARATU Book Complete Rumaisa Sidi.txt

26 Jan 2025

6686

*AURE DA KARATU*








*RUMAISA SIDI*










Page 1 (dandano)
















Kamar yanda na riga na al'adanta na gyara gidana tareda kicaniyar hadawa 'yan makaranta abin kari sauri-sauri nake komai saboda banson suyi latti har takai ga an dokesu a makaranta












Duk abinda nasan zai saka yarana farinciki har su aje hankalinsu suyi karatu inayi kama daga kan cimarsu,suturunsu( uniform) har izuwa abubuwan da zasu taimaka musu suyi karatu duk term nake canja musu uniform saboda makarantar kudi sukeyi suna ganin yanda akewa sauran yara to nima ina bakin kokarina gurin yin abinda zan iya saboda kullum ina nuna musu ba zaka taba cimma wani ba kaima wani bazai cimma ba














A kan wannan na dorasu suma akanshi suka ginu duk abinda suke so ina kokari in musu da dan abinda nake rufa ma kanmu asiri


















A halin yanzu ba abinda nakeso sama da yarana su kadai ke sakani farinciki su kadai suka ragemin idan har kaga dariyata to ina tsakiyar yarana suna min labarin makaranta da kuma burikansu da kullum suke kara yawa a kaina








Yarana uku Safwan shine babba shekararsa 12 sai Aysha dake binshi ita kuma shekararta 9 sai auta Amra 'yar rigimata kenan itama shekararta 6 kuma farincikinmu gaba daya
















Karfa kuga na cikaku da zancen yarana ku kosa dani ko kuyi tunanin ina b'ata muku lokaci ko d'aya labarin bazai tafi yanda nakeso ba sai yarana sun shigo a farkon labarina


















Zakuce a ranku to duk wayannan yaran ina mahaifinsu?????












Mahaifinsu Lawal muhammad yananan kuma muna tare da shi har yanzu saidai.......................Jin girkina na neman konewa ya ankaraddani bayan dogon zangon tunanin da naje da sauri na hada wa kowa nashi saboda nima makaranta zanshiga saboda inada lecture karfe 10






















Kukan Amra da naji yasa nayi saurin fita ganin fitowa ta yasa tayi gurina tana kara doka kafarta kasa irinna rigimammun yara




















Mommy kinga Esha ta dakkomin socks ko? hannunta na rike ina karasawa cikin falon














Ina Eshar? meyasa zaki dauka mata socks?














Wallahi mommy bandauka mata socks ba kawai na duba na dau nawa shine wai tunda na taba mata abu saita rama a tawa
















Murmushi nayi araina nace "Rigimammiya"




















Daurewa fuskata nayi sannan na nuna Aysha "Karki kara tabawa shalelena kaya bakisan batason ana sama ta datti a kaya ba karki kara"
















Kama kunne Ayshar tayi tana kunshe dariya "Am so sorry mommy bazan kara ba"


















"To kowa ya zauna kuyi breakfast tun school bus bata iso ba" shayin na hada safwan ya zubawa kanshi ya zubawa Aysha ni kuma aka barni da 'yar lelena (dama aikinta sai ni)






















Tsittt naji gidan yayi bayan wucewarsu zama nayi nima nayi break sannan na hada kofunan da mukayi amfani da su na wanke sannan na wuce dakina don in shirya kar inyi latti






















Kallo guda nayiwa gadon da yake kwance na kawadda kaina inada tabbacin ko sallar asuba baiyi ba don yanda na fita na barshi haka na dawo yanzu ma na sameshi






















Har nayi wanka na shirya yananan kwance saida na kammala komai sannan naje gefen gadon daurewa nayi na taushe abinda nakeji idan tuna abinda yamin jiya bubbuga filon na shiga yi






















"Abban safwan" na shiga kiranshi a hankali kar yace na mishi ihu amma shiru Filon naci gaba da bugawa juyawa yayi yana yamutsa fuskar da har yau na kasa tantance abinda na gani gareshi da har na dage sai shi




















A kufule na buge filon wannan karon sai gashi zaune tsakiyar gadon yana aikomin sakon harara " Waike wace irin matace kashemin dodon kunne za kiyi? tun safe keda yaranki kun ishi mutane da surutun tsiya yanzu kuma ke kinzo min ihu a kai"
























Hadiye bacin raina nayi sanin ba abinda zai amfana min "Dama zan wuce makaranta ne kuma gidan ba kowa ba'a san mai shigowa ba"






















"Yanzu dama saboda banzar makarantarki za ki hanamin bacci nasha gayamiki ba abinda ya shafeni da wata makaranta taki idan kin cika in kinje karki dawo kuma wallahi idan har kika wulakanta min aure ke da Allah"
























Sauri-sauri na bar dakin ina mayadda kwallar da ke neman zubomin tare da tunatarda kaina alkawarin da na daukarwa kaina na bazan kara zubarda hawayena akan Lawal ba






















Tunda na shiga makaranta na watsar da tunanin damuwata na fuskanci abunda nazo yi lecture daya ce dama 12 na fito daga makaranta inata sauri in isa gida in hadawa yarana abinci kafin su iso




















Cikin sa'a kuwa muna fitowa na samu napep na shige ina yiwa abokan karatuna sallama ina jin lokacinda Nafisa ke cemin "Sai gobe uwar son 'ya'ya" haka suke cemin wani lokaci suna ganin kamar na cika son yara ina musu uzuri wani lokaci saboda basu san abinda yasa nakejin kamar nafi kowace uwa son 'ya'ya






















Kamar yanda na tsammananta yana zaune akan bencin mai shagon da ke haya kofar gidanmu suna gardamar siyasa "ai wannan fagen ka kware" na fada a raina kudin mai napep din na bashi ina kokarin juyawa yaro ya iso wurina yana bani mukullin gidan "gashi inji abbansu safwan" karba nayi tareda wucewa na bude gidan na shige
























Hmmmmmm salon na dabanne🥰💃












Ga sabon littafin mu mai taken AURE DA KARATU comment dinku shi zai bayyana karbuwar littafin ko akasin hakan


AURE DA KARATU


NA




RUMAISA SIDI










Page 2














Gyale na na kwabe tare da wucewa daki na watsa ruwa sannan na dauko doguwar rigata mara nauyi na dora hula akai na fito














Kaitsaye kitchen na wuce na shiga hadamana abinci jallof din shinkafa na dafa da dan sauran kifin da muka ci jiya sauri-sauri nake komai kar su dawo bankare ba














Karfe 1 dayan mintuna naji tsayuwar bus dinsu bayan na kammala hada komai Amra ce a gaba tana kwallamin kira "Mommy Mommy" tashi nayi tsaye kamar yanda muka saba kullum rungumeni su kayi su duka ukun kowa na fadin "Ni ne first, ni ce first" hadesu nayi duka ukun nima na rungumesu ina jin wata kaunarsu ta musamman tana ratsani tareda tausayinsu














Dakinsu suka wuce suka cire uniform tareda aje kayansu Aysha ta canjawa Amra ni kuma na zubo mana abinci kafin su iso yasha iska suma basu ja lokaci ba suka fito










Tsakiya na aza tiren abincin muka zagayeshi saida muka zauna na tuna da ruwa safwan na duba "Yaya dakkomana ruwa a fridge" tashi yayi ya dakkoma kowa sannan ya zauna muka fara cin abinci












Amra ce tasaka rigimar ita zata fara bani abinci wannan ka'ida ce idan muna cin abinci to kowa zai bani a baki nima in basu wannan karon ma kowa saida ya bani nima na basu bayan mun kare safwan ya gyara wurin Aysha kuma ta kai kayan kitchen














Jin an fara sallah safwan ya fita masallaci ni kuma na hadasu muka je muka yi sallah kasancewar yau alhamis ba islamiyya muka dawo falo saboda zafi gashi ba wuta system dina suka dakko suna game ni kuma na dau wayata ina duba costomers dina na whatsapp wayanda ke bukatar kaya ina tura musu suna zabawa














Na shafa'a ga mutanen arzikina har na ware ina chat da kawayena a wani group dinmu na makaranta har safwan ya dawo shima ya jone dasu Aysha suna game sam banji shigowarshi ba ganinshi kawai nayi a kaina "Wannan wane irin iskanci ne ana miki magana kamar bakyaji to yama za'ayi kiji kina hira da samarinki duk abinda kika fita kikayo bai isheki ba sai kincimin mutuncin aure a cikin gidana to wallahi baki isaba "














Kallon bangaren da yarana suke nayi suna nan zaune Safwan da Aysha sun sauke idonsu kasa amma sunbar game dinsu Amra ko kyam ta zubomana na mujiya "Safwan kuje dakinku kuyi game din" kamar mai jira suka mike












Saida naga wucewarsu sannan na maida hankalina gareshi "Haba abban safwan sau nawa zan gayama bai kamata kake fadar kowace irin magana a gaban yarannan ba ina gujema hakan ya janyo ma raini"








Kamar wanda ke jin haushina ya zaburomin "Raini na nawa kuma? bayan kingama nuna musu banida muhimmanci a garesu kina kallo nuna suke kaitsaye sun fi kaunarki a kaina kingama hore musu kunne wallahi nayi nadamar aurenki"








wani bakinciki ne ya tunzuromin nima na mike tsaye ina kallonshi cikin ido ina kara jin tsanarshi fiye da yanda nakeji "Kaine da kanka ka kada girmanka a wurin yaranka lawal kuma wallahi nafika nadama da danasanin aurenka bansan bakinciki ba saida na aure ka bansan wata cuta hawan jini ba sai a gidanka kaine..........." shiru nayi jin kowane irin lokaci kuka na iya kwacemin wayata na dauka na wuce daki shima a sanyaye ya juya yabar gidan
















Da darema tare da Aysha na shiga kitchen na dafa mana abinci daidai cikinmu don alkawari na dauka bazan kara ciyadda shi ba zan nuna mishi wannan karon nima 'yar kodimo ce bazan kara daukar iskancinshi ba
















Bayan mun kammala cin abinci kowa ya dakko littafanshi sukayi home work ina duba musu da inda basu ganeba ganin dare yayi nace suje su kwanta Amra tasa rigimar ita tare dani zata kwanta nace zuje su kyaleta "Ku tabbatar kunyi addu'a yaya"


















Banjima ba nima na fara jin baccin tashi nayi nadauki Amra da ta dade dayin bacci dakinsu na kaita kayan wutar dakin na kashe tareda tofesu da addu'a














Shirin baccin nayi nima zan kwanciya naji yana kokarin rufe gidan na gyara kwanciyata kamar nayi bacci ya dan jima da shigowa gidan sannan ya shigo daki kamar mai tunani yayi tsaye tsakar dakin yana kallona sai can ya karaso yana buga filon da nake kwance kamar mai baccin kwarai na shiga kifta ido tare da tashi zaune "Yadai" na fada tareda dage gira ina kallonshi kame-kame ya shiga yi "Am nace MY ZEE baku rage abinci bane wallahi yunwa nakeji kuma naje gida na taradda Salma ta haihu tana asibiti to abincin duk ankai can"(salma kanwarshi ce da tayi aure shekarar da ta gabata)




Abin mamaki sai banji tausayinshi kamar lokacin bayaba da wancan lokacine da dasauri zan tashi koda abincin da zan cine to ni zan hanama cikina in bashi amma wannan karon kai tsaye na dubeshi "Wallahi babu shi duk mun cinye" daga haka na juya na gyara kwanciyata ina fatan bacci ya daukeni
















Sai asuba na farka baya dakin da alama ba ciki ya kwana ba fita nayi na wuce dakin yarana na tadasu saida naga sun tashi sunyo alwala sannan na fito hangoshi nayi kan doguwar kujerar da ke falon karasawa nayi wurinshi na shiga tadashi kamar yanda ya saba kullum idan na tadashi wannan karon ma harara ya bankomin "Lafiya kuma" murmushin tura haushi na mishi sannan nace "Lokacin sallah ne yayi abban safwan nace bari in tadaka karka rasa jam'i"
















Wani kallo yake bina dashi kamar ya shakeni"To ina ruwanki da sallah ta kabarinmu daya dake wai ni menamiki har haka zainab da kika bi kika addabi rayuwata ne ko so kike shima kwanan gidan in barmiki keda yaranki iye" ganin yanda yake daga murya kar ya janyo mana hankalin makwabta yasa na juya nashige daki kar in rasa jam'i wurin neman magana
















Har suka wuce makaranta yau ma yana daki ni kuma ina falo ina duba abokan business dina ina yin order kayan da mutane ke bukata nishadin da nakeji ne ya jani izuwa status din jama'a ina kallo wasu hotunansu suke posting wasu kuma sana'unsu can nakai ga status din Hannatu cousin sister dina wakokin soyayyane kala-kala tayi status tareda emojies na soyayya murmushi nayi "Su soyayya manya" na fada a raina ina tuna irin soyayyar da muka buga nida lawal kamar ba gobe idan naga masoya suna zuba soyayya saidai kawai nayi dariya tareda fatan suga mai kyau don nikam ba abinda ta tsinanamin sai tarin bakinciki














Na tuna lokacin da lawal yake duke gabana yana kuka yana fadin "Ki taimakamin my zee kar na rasaki wallahi idan na rasaki to zan iya rasa raina na miki alkawarin rayuwa mai inganci nasan gidanku gani suke bazan iya rike ki ba saboda ina talaka wallahi zee indai kika aureni ko dako ne zanyi in ciyadda ke da abinda kika saba ci a gidanku"














A wannan lokacin nima zubewa nayi a gabanshi ina kuka "Ka kwantarda hankalinka Nisful ba abinda zai rabamu ni kai nakeso da kai zan zauna banajin kona second daya zqn iya kula namijin da ba kaiba na tabbata inhar na dage kai nakeso abba zai auramin kai dawowarshi kawai nake jira"












Hawaye naji suna zubomin "Allah sarki abba Allah ya gafarta ma gashi ka auramun abinda nace inaso na guji zabinka ni kuma ga abinda nake gani Allah na tuba ka yafemin"


























Hmmmmmm muje zuwa dai🤔


AURE DA KARATU
NA
RUMAISA SIDI




Page 3


Kuka nayi marar misali saboda tuno abinda nake kokarin mantawa taurin kai duk shi ya kaini ga fadawa halinda nake ciki a yanzu bana zargin kowa da lalata rayuwata sai ni da kaina mahaifina mahaifiyata yayyena da duk wani masoyina ba wanda bai shawarce ni akan abinda suke hangomin ba amma na take saboda wata banzar soyayya tawa banci riba ba sam ba wani amfani da hakan yamun


"Wannan wace irin mummunar dabi'ace me kuma aka miki yanzu da zaki zo kina min kuka a cikin gida ko sharrin naki ne ya tashi? to wallahi wannan karon a shirye nake da duk wani dan uwanki da zai nunamin yatsa ba wanda ya isa ya wulakanta ni "


Da kallo na bishi har ya shige kitchen hawayena na goge banjin zan iya kula shi a wannan lokacin na gaji da biyemishi duk safiya muna raba hali gyara kwanciya ta nayi kan doguwar kujera tare da saka earpiece ina sauraren karatun qur'ani ina fatan samun nutsuwa da rahama a cikin zuciyata saboda abinda nakeji kowane lokaci rashin lafiyata zata iya tashi


Dawowa yayi falon yana maganar da sam banaji saboda abinda ke cikin kunnena a hankali na sance kunne daya ina watsa mishi idanuwana da yake kira da oily eyes a lokacin da muke kan soyayyarmu yasha gayamin wani sanyi yakeji a ranshi idan ina kallonshi da su


"Ina breakfast dina fita nakeso nayi" Cikin isa yake maganar kamar wanda yasiyo komai ya aje ya zo ya taradda babu


"Hmmmm" na sauke ajiyar zuciya tareda kara kallonshi " Mun cinye" na fada kaitsaye tareda kokarin mayadda earpiece dina maganarshi ta dakataddani " bangane kun cinye ba kyaleki fa nayi ko jiya daga abincin rana har na dare ba wanda naci a gidannan yanzu ma don tsabar mugunta daga ke sai 'ya'yanki zaki cinye"


"Anzo gurin" na fada a raina " Banyi tunanin kana bukatar abinci a gidanka ba saboda duk maigidan da ke bukatar hakan fita yakeyi ya nemo ya kawo a dafa aci amma kai banga hakan a tare da kaiba kuma wannan abin da kake kiran ba'a baka ba wanda kace kafi karfin wulakanci a wurinsu ne suka aje kaga ko bazaka ci ba"


"Ai ba yau kika fara yimin gori ba Zainab ba yau kika fara nuna 'yan uwanki ke daukar nauyinki ba kuma ba wanda nace yayiwa 'ya'yana wata lalura abarsu su rayu kamar yanda nake rayuwa nima rashin sirrinki yasa kika gama zubarmin da mutunci a gurinsu shi aka nunamin tun farkon neman aurenki naki fahimta ana nunamin illolin auren 'ya'yan masu kudi amma kaddara ta riga fata don aurenki KADDARA CE"


Daga zaunen naji jiri na dibata "Lawal, Lawal ne ke kiran aurena auren kaddara? lawal din? wayyo Allah na" dishi-dishi nake ganinshi saboda hawayen da ya cikamin ido amma yanda ya bakanta min nima zan bakanta mishi gorin da yadade yana fadar ina mishi yau daya zan mishi yasan abinda ake nufi da gori " Aurena ya wuce ka kirashi na kaddara lawal idan har ni ban kira aurenka da auren kaddara ba kai kayi kadan ka kirani da hakan wace riba naci a aurenka bayan 'ya'yan da ke tsakaninmu? bayanshi ba komai kai kuma silar aurena ka mallaki gidannan da muke ciki da motar hawa kai har suturar sakawa lawal" matsawa nayi kusa dashi ina kallonshi ido cikin ido "Har abincin ci kasamu sanadina lawal nafi karfin ka kirani da auren kaddara" na karasa ina dukan kirjina jinake kamar in shake lawal sai ya daina numfashi na tsaneshi fiyeda tunaninku masu karatu


Shima cikin bacin rai idanunshi sunyi jajir ya shiga nuna ni hannunshi na rawa" Wallahi zainab ki iya bakinki kinsan dai igiya biyu ta rage tsakaninmu" tsaki na buga "to shine me? akwai wanda ke dannarka game da igiyoyin kayi yanda zuciyarka ke rayamaka akaina lawal"


A fusace ya juya ya fita daga dakin yana banko kofar kamar zai ballata jagwabb na fada kan kujera tareda dafe kaina da nakejin yana saramin kamar ana dokamin guduma har cikin idanuna nakejin ciwon da lalube na tashi na wuce daki na dakko magani na tsakiyar falon na zube ina haki dafe da kaina sunan Allah na shiga kira "Ya Allah ka kawomin dauki Ya Allah ka yafemin Allah na tuba na tuba ubangiji Allah kayi abinda yake mafi alkhairi a kaina Yarana Allah ka kawomun dauki ko saboda rayuwar yarana Allah Allah ka......." kuka ne ya kwacemin na kife kaina kan kafet inayi kamar wata karamar yarinya


Bansan loakci ya tafiba saida naji yarana a kaina ashe wai baccine ya daukeni a hankali na bude idanuwana da sukamin nauyi na sauke su akan Aysha da ke kallona kokarin tashi zaune nayi ina tattaro sauran karfina murmushi na musu "Kun dawo? baccine ya dauke ni ashe" hannuna Amra ta rike "mommy yau baki yi hugging dinmu ba" safwan ma matsowa yayi yana taba wuyana a razane ya zare idanunshi irin nawa (inji lawal) "Mommy bakida lafiya? jikinki zafi sosai mommy" sai hawaye " to miye na kuka kuma kamar ba namiji ba dubi kannenka suka kuka zasu yi common yarana ku kwantar da hankalinku naji sauki sosai" na fada tareda hadesu na rungume


Indomie na dafa musu ganin lokaci ya tafi dayawa daurewa naci gaba dayi saboda yarana dako tari nayi zakaji suna hada baki wurin fadin "sannu mommy"


Shareshi nayi nabawa banza ajiyarshi har dare ban kara kulashi ba shima shareni yayi dukanmu muna falo har shi nidai ina harkar business dina da wayata su kuma safwan na dubama su

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login