Showing 21001 words to 24000 words out of 57484 words

Chapter 8 - AURE DA KARATU Book Complete Rumaisa Sidi.txt

26 Jan 2025

6695

kai bazaka fahimta ba to gaskiya ni ba wata sana'a da zan bari don da ita nake ci da kaina in cida ƴaƴana kai harda uban ƴaƴanma" na ƙarasa ina murguɗa ɗan bakina


Miƙewa yayi yana nuna ni a harzuƙe "ke ki iya bakinki wallahi banida daɗi nan da kika ganni nima na iya rashin mutuncinnan" nima miƙewa nayi "to wai miye na duk wannan abun? saboda sana'a ne kodai akwai wani abu" na tambaye shi saboda abin ya fara ɓatamin rai nima


Hannuwanshi ya shiga watsawa kamar sabon kamu" sana'arki ta banza ke kika ɗauketa sana'a ni wallahi duk abinda zan siyo da kuɗina in aje shi ina jiran wani yazo ya siya ban ɗauke shi sana'a ba"


"Aiko shiyasa ka kasa kasuwancin saboda yanda ka ɗauke sana'ar da ban yanda ta ke daban" cikina yayo kamar zai dakeni yana nuna ni hannunshi har rawa ya ke dama lawal ba dai zuciya ba (ta banza tunda bazai iya ɗebewa kanshi takaici ba)


"kin fara wuce iya karki kuma zan nuna miki har yau ina sama da ke" ya gyara tsayinshi sannan ya ci gaba da magana "dole cikin biyunnan ki zaɓi ɗaya SANA'ARKI ko kuma AURENKI"


A razane nake kallonshi saboda ni ban ɗauka maganar ta kai can ba wannan lokacin ji nayi ba ni ke sarrafa zuciyata ba kamar sarrafata ake yi kai tsaye nace "Na zaɓi sana'ata" Idanunshi ya lumshe sannan ya juya baya " kije na SAKE KI saki ɗaya"


Dummmmm kaina ya buga kamar an doka guduma jina da ganina suka ɗauke na wuccin gadi wani kalar tashin hankalinda ban taɓa tunani ba ya dira a kwanyata da ƙyar na iya ɗaga hannuna na nuna kaina "ka sake ni? ni ka saka lawal"


Fuuuuuuu ya wuce ɗaki ba tare da yace komai ba kasa riƙeni ƙafafuna su ka yi na zube nan tsakar falon ina kokawa da numfashina ni nasan akwai matsala lalube na shiga yi saboda ɗif na daina gani cikin iyawar ubangiji naji wayar da nake nema farcena na ɗora abinda ya baiwa wayar damar fita security


Sashen da nasan nan nake kira na shiga number da ke sama na danna batare da nasan ko ta waye ba "hello zee" naji muryar anty halima "kizo zan mutu kizo ki tafi da ni" na fitarda maganar a wahale


Daga nan banƙara sanin abinda ya faru ba sai farkawa nayi na ganni a asibiti kwance ga ummina da kuma ya mubarak sai anty halima da ke kaina "Zainab" anty halima ta kirani ɗaga idanuwana da suka min nauyi nayi na dubeta a hankali kuma na maida su na rufe


Hannun ummi da ke cikin nawa na ƙara damƙewa jin komai yana dawomin tar a cikin kwanyata kamar lokacinne abin ya faru kuka na fashe da shi kukane nakeyi mai ƙunshe da baƙin ciki da kuma dana sanin auren lawal


Idanuwana da suka rine na ƙara buɗewa ina kallon ummi kamar wata taɓaɓɓa na fara jero zance "ya sakeni wai ummi sakina yayi anty halima ni lawal ya saka ban mishi komai ba ya mubarak ka tambayeshi kaji ban mishi komai ba to ko baisan abinda yace min ba?" na maidawa kaina tambaya


Hawaye ummi da anty halima keyi "kiyi haƙuri zainab ki daure ki kira sunan Allah innalillahi wa inna ilaihi raji'un" ta shiga ambatawa


A hankali nima na karɓa "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un ummi shikenan aurena ya mutu? na koma bazawara ko ummi? yarana ummi ina yarana" hawayenta ta share sannan ta dubeni" ki nutsu zainab kar ki bari wannan ya taɓa imaninki ki ci gaba da kiran sunan Allah"


Inaaaaaaa mutuwar aure ba abu bane mai wuyar mantawa tabone da bazai taɓa gogewa ba a zuciyar ƴa mace sai da ya abbas yazo ya lallasheni ganin ban daina ba ya koma asalin kalar shi sai gani nayi muƙus


Kwana na biyu asibiti na koma gida anty halima na tambaya "Anty wai ina su safwan tunda muka dawo nake zuba ido in gansu ban gansu ba na ɗauka suna ɓangaren su yaya sai gashi su nihal sun zo dubani kuma basu a cikinsu"


Hannuna ta riƙe "ki kwantarda hankalinki suna wurin kakarsu tazo dubaki lokacin an miki allurar bacci amma suna wurinta don yaya abbas yace ba zasu zauna gidannan ba"


Hawayene suka shiga min ɓulɓula "shikenan an rabani da yarana? shikenan suma za'a lalata musu future kamar yanda sauran yaran da iyayensu ba sa tare ke tsintar kansu? da ni kaɗai suka saba yini ɗaya idan mukayi bama tare kewata suke ya zasu yi bacci kenan? lawal ka cuceni" na ƙara rushewa da kuka


A harzuƙe ta miƙe "shikenan zainab an ƙyaleki je ki kashe kanki akan lawal nace kije tunda mu bamuda wani girma da zamu ce ki bari ki bari an gayamiki halinda lafiyarki ta ke ciki amma kinƙi kwantar da hankalinki bari in gayamiki wallahi ko yau kika faɗi kika mutu lawal bayada asara mu da ƴaƴanki kawai zamu damu ki daure ki shanye kodon yaranki da kike mutuwar ƙauna don Allah ki cire damuwa ko don MU zainab" ta ƙarasa tana haɗe hannayenta alamar roƙo hawayen idonta ta share tare da barin ɗakin


Washe gari sai ga gwaggo dije ta iso tare da yaya bashir itama ta jajanta tare da faɗan bar musu yara tace ya kamata a kawomin su ko saboda lafiya ta naji daɗi sosai ko ba komai ita ta fahimci halinda nake ciki


Yaya bashir kuwa cewa yayi sai an sa ƙara ni dariyama ya bani "to acewa alƙali don ya sake ni ake ƙararshi hmmmm Allah ya kyauta kawai?"


Da marece sai ga mama mahaifiyar lawal da kuma yaran gaba ɗaya sunzo dubani faɗar farincikin da muka shiga ni da su ɓata bakine rungume juna mukayi ni kuka su kuka saida ummi ta tsawatar haƙuri mama ta dinga bayarwa kamar ita tayi sakin "don Allah ayi haƙuri hajiya wallahi banji daɗin al'amarinnan ba sam lawal bai kyautawa rayuwarshi ba don Allah ayi haƙuri"


Da zata tafi gwaggo dije ta mata maganar a barmin amna tunda ita ce ƙarama bata musa ba kuwa ta barmin ita tare gayamin gobe idan su mariya za su zo dubani zata basu kayanta ranar rungume da amna nayi bacci ina jin kamar za'a ƙwace min ita


A haka tafiya tayi tafiya na shanye wata ɗaya da satittika a cikin kwanakin iddata za ki sha mamaki idan nace miki satina biyu a gida lawal ya fara zaryar inyi haƙuri in koma


Ko alamabanji zan iya komawa gidanshi ba na fison in koma KARATUNA kuma gaba ɗaya gidanmu ba wanda ya bada goyon bayan na koma


Ganin kwanci tashi ina neman in laƙume iddata sai hankalinshi ya tashi ya jingina da mahaifiyarshi bansan yanda ya ciyo kanta ba wata ƙila ta gaji da rainon yara sai gata a gidanmu tana roƙon su yaya su yi haƙuri gayamata su ka yi taje za su neme ni su ji ta bakina


Lokacinda suka sameni kaitsaye na ce musu nidai bazan iya komawa ba nemanta suka yi suka gayamata sai gata ta dawo gidanmu har ƙasa tana roƙon nayi haƙuri na koma gigicewa na yi ina roƙon ta tashi naji zan koma


Kiran lawal yaya isma'il yayi nima aka kirani tun bayan rabuwarmu da shi banƙara saka shi a ido ba sai yau sai satar kallona ya ke nima kallonshi na ke ta ƙasan ido ya rame sosai yayi baƙi ( to ba dole ba an bar samun na banza)


maganar yaya isma'il ce ta dawo da ni hayyacina "Kamar yanda muka gayamaka tun a waje mun amince zainab za ta koma ɗakinta amma a bisa wasu SHARUƊƊA" kallon shi yayi yaya ya ɗaga mishi kai "yes sharuɗɗa na farko zainab za ta ci gaba da karatunta na biyu za ta ci gaba da sana'arta na uku ka kula da ita ina fatan ka gane"


Kanshi ya ɗaga kamar wani munafuki gyara zama yaya abbas yayi " sannan ina mai gargaɗinka da ka kula da abinda zai taɓa lafiyarta wallahi idan har wani abu ya sameta zan iya ɗaureka har iyakar ranka"


Da wannan na koma gidan lawal muka ci gaba da gurgura rayuwa duk da bai canja ba amma yayi sanyi sosai ga wasu abubuwan kodon yana tsoron wani abu ya same ni ace shine oho ko kuma halayyar da na dawo mishi da ita ce ke tsorata shi domin yanzu ko kaɗan bana raga mishi don naga baisan wannan ba


Bayan Amna na ƙara haihuwa abun baizo da raiba daga nan kuma nace Allah ya raya abinda muka samu


Har yau da kike gani bai canja ba nima kuma ban sauyaba abinci duk wata yayyena ke sauke min sutura banida matsalarta ina ɗinkawa kaina da yarana hakama ummi tana musu mama ma tana musu abbansu ne dai sai a hankali


Alaƙa ta da ƴan uwanshi kuwa saidai Allah ya kyauta domin bama ga maciji su a nasu jahilcin kamar ni na sakashi talauci ni kuma nayi kuɗi ban damu da su ba domin ni yanzu ko lawal ɗin baya gabana bale kuma su


Kinji labarina da kuma labarin ƙalubalen nawa auren don kima aje tunanin ke kaɗai ke cikin matsala








Ina godiya sosai da kulawarku a gare ni🙏
comments ɗinku ya na saka ni nishaɗi ku ci gaba da watsomin ruwan conment ni kuma in ci gaba da raƙashe ku da typing


Na gode ƙauna tari-tari🥰










HMMMMMMMM Saura na ji wani ya zagi lawal😹




AURE DA KARATU
NA
RUMAISA'U SIDI






Page 18




Rakiya na yiwa maman haidar ina ƙara jaddada mata ta yi haƙuri hamdala nayi bayan na dawo daga rakiyarta "wai na rabu da sha labari" na faɗa ina zama kan kujerar falon ina jin wani takaicin kaina irin yanda na matowa lawal a baya kamar wata sakarya "Allah wadan na ka ya lalace" na gayawa kaina


Ina nan kwance ya shigo kamar an jefoshi ko sallama bai yi ba nima kuma banma nuna nasan da shigowarshi ba fitowa ya ƙarayi har ya tafi ya dawo tsaye yayi akaina "mama za ta zo wai taji abinda nake saidawa nasan tsaf za ki ce baki sani ba"


Ɗago kaina nayi na ɗage girata ɗaya" to na sani ne?" kallona ya ci gaba da yi kamar mai son gano wani abu kanshi ya jinjina alamar zuciyar tana kusa" shikenan idan ta zo kice ca-ca na ke"


"to ai yanzu ka sanarda ni" na faɗa ina ɗauke ƙafafuwana na ɗauke na mayar kan kujera na kwanta sannan na bashi amsa yana gab da barin ɗakin dariya nayi a raina "ga tsoro ga ban tsoro"shine taken lawal


Ashe yasan abinda ya ke wa ƙarfe 12 sai ga mama gidan takan jima ba ta zo ba saida ƙwaƙƙwaran dalili lemu na kawo mata da sauran abincin da na girkawa ƴan makaranta bayan na gaidata


"kiramin mijinki kice na iso na gayamishi ganinan zuwa yace idan na zo a kirashi"


"To mama" na shiga laluben number lawal da anty halima ta canjawa saving daga Nisful ta mayaddashi Abban safwan bugu biyu ya ɗaga "ga mama na jiran ka" daga haka na kashe ɗan katina


Ba jimawa sai gashi (wata ƙila kasuwar ta su ba nisa😂) gaidata yayi ya na tambayarta gida tace komai lafiya zama yayi a kujerar da ke fuskanta ta


"Na zaɓi na zo nanne muyi magana saboda tunda na baka kuɗinnan ban ƙara ganinka ba bayan kuma kace za ka zo da zainab kumin bayanin kalar sana'ar"


Hankalinta ta mayar kaina "ke zainabu gayamin wace sana'a ce ku ke yi" kallon lawal nayi da ya zubamin ido ina ganin yanda ya ke ƙiftamin ido na yi banza da shi "bansan sana'ar da ya ke yi ba mama" na bata amsa kai tsaye


"ban gane ba kai lawwali kace min tare ku ke sana'ar"ta faɗa tana tsare shi da ido nima kallonshi na ke yi sai raba ido ya ke murtuƙe fuska ya yi kamar wani zaki "da kai fa nake magana" ta daka mishi tsawa ganin ya na maisheta sakarya


"Ni fa mama bazan iya wata sana'ar takalmi ba na bincika ba wata riba ake samu ba"


"to ba ni kuɗina" ta faɗa tana miƙa mishi hannu "kai wane irin sakaran namiji ne da baisan kanshi ba? kamarka da iyali da komai ka naɗe hannu ka dawo gida ka kwanta don ma Allah ya ba ka mata ta gari mai rufin asiri ta na iyakar ƙoƙarinta akan ka duk wani nauyin yaranka ta ɗauke amma saboda zamanka sakarai ba wani alamun damuwa a tare da kai yanzu saboda kai na siyarda ɗan filina da na ke kallo a matsayin ƙadarar da na mallaka na baka kuɗin amma kake gayamin ba za ka iya sana'ar takalmi ba to ka bani kuɗina don ni ba sakarya bace irinka in rabawa ƴan uwanka su da za su iya sana'ar na baka nan da gobe ka kawomin kuɗina"miƙewa ta yi nima na miƙe ina bata haƙuri


"ke za'a ba haƙuri zainabu ke da kike tare da sakaran miji wanda baisan inda ke mishi ciwo ba"rakata na yi sannan na dawo falon yana nan zaune kamar zane wayata na ɗauka ina ƙoƙarin barin falon


"kinyi farinciki kin haɗani da mahaifiyata" waigowa nayi na kalleshi "saboda ni na cinye mata kuɗi" na mayar mishi da mai zafi don na kunna shi aiko ya kunnu don tashi yayi yana nuna ni "karki gayamin maganar banza naji ni na cinye kuɗi ai dai na mahaifiyata na ci ba na wani ba naga ai ke kinada kuɗin amma ba su da amfani tunda an makkale an hanaki ana yanda ake so da dukiyarki"


"Dukiyata tana hannun waɗanda ya dace kuma waɗanda ba su damu da abin duniya ba da ma wanda ake tunanin zai cinye ake bibiya wanda aka san dama ya saba da su sai dai fatan alkhairi da kake faɗar an mallakemin dukiya kasan dai duk cikinsu ba wanda cefanen gidanshi ya fi ƙarfinshi" daga haka na cikawa sket ɗina iska ganin yanda ya harzuƙa kar ya cafkoni ya fara kirɓa


Ina shiga na maida ƙofa na rufe da key ina sauke ajiyar zuciya don dama duk maganar da nake yi a tsorace na ke yinta ina maganar ina kallon motsin hannunshi ina tsoron saukar wannan gudumar a lallausan kumatu na




Sai da naji hayaniyar yara sannan na fito ba ya falon da alama ya daɗe da fita


Haka muka ci gaba da zaman bansan yanda ya ƙarasa da mama ba don ban ƙara kula shi ba ganin shima ya ɗau fushi da ni kamar ni na kama muka cinye kuɗin


Karatuna na ci gaba da yi da kuma kula da tarbiyyar yarana ta ɓangaren kasuwancina Alhamdulillah ina samun ci gaba ina harkokina cikin iyawar uban giji


Jarabawar da muka fara ita ta ƙara ɗaukemin hankali daga shiga harkar lawal sosai na duƙufa ina fatan cika burina da lawal ya ɗau aniyar tarwatsawa har muka kammala cikin nasara aka tafi hutu


Yau tunda na wayi gari nake fama da faɗuwar gaba abin ba daɗi sunan Allah na shiga kira ina fatan ya bani ikon ɗaukar abinda ke tunkaro ni aiki nake yi amma sam ba ƙarfi a jikina


Ina ƙoƙarin sauke abinci naji kukan amna abincin na sauke sannan na fita ina tambayar abinda ya faru "mommy Aysha ta zaga shine na buge mata baki"


"Zagi? ina kika iya zagi? ai gwanda da ka doke mata baki" ƙara buɗe baki tayi tana min ihun kuka "za kimin shiru ko sai na ƙara miki" na daka mata tsawa wanda yayi daidai da shigowar lawal tashi ta yi da gudu taje ta riƙeshi tana shessheka


"me ta miki da za ki doketa"ya tambayeni yana tsareni da ido kamar wanda ke son turkeni "zagin Aysha tayi kuma ba ma ni na daketa ba safwan ne ni yanzu zan mata nawa"


"Saboda jakar ku ce?" ya tambaya cikin masifa kallon mamaki na bishi da shi "zagi fa aka ce maka ta yi ba wani abin kirki ba"


"To ke bakya zaginne? ko shi da ya doketa baya zagin" wurin safwan ya isa kamar wani sa'anshi ya dinga dukanshi ido na zuba mishi tare da tunanin "anya saboda dukan da safwan ya yiwa Amna ne lawal ke mishi wannan dukan sam abin bai kai haka ba amma kuma ɗanshi ne banida halin dakatar da shi" juyawa nayi na koma ga girkina ina danne abinda ke tasomin


Ɗaki na same shi bayan na bawa safwan magani saboda zazzaɓin da ya taso mishi .wataƙila harda kukan da yayi abinci na zuba musu sannan na wuce ɗaki yana rungume da ita sai wani narkewa ta ke idona na zuba mata ina nuna mata ƙofa "ki wuce ga abincinku can kafin ranki ya ɓaci" sauka tayi daga jikinshi ta bar ɗakin kallona na mayar wurinshi




"ba haka ake hukunci tsakanin yara ba abban safwan ko ba komai shi babba ne a gurinta kuma hukunci ya mata kan abinda ta yi bai kamata ka dokeshi kan wannan ba dukansu ƴaƴanka ne" miƙewa yayi kamar yanda ya saba shi kullum ba za'ayi magana da shi a zaune ba




"to sannu ƴar iya ai dama komai ban iya ba ke kika iya to bazanyi yanda kike so ba dama ba tun yau ba na fahimci duk cikinsu ba wanda kike so kamar shi ba ya laifi a gurinki to ni ba irinki ba ce son ƴaƴa bai rufemin idon da zan iya komai a kansu ba" galala na saki baki ina kallonshi wai kodai ya fara kurɓe-kurɓe? to nikam yaushe abin ya kai na ɗaga murya




"Allah ya baka haƙuri"na faɗa tare da juyawa ɗakin na bar mishi na koma falo na kwanta ina kwance sai ga yaran sun fito wurina suka yo dukansu hannu na miƙawa safwan ya tako wurina gefena na zaunadda shi tare da kwantarda kanshi akan cinyata jin har lokacin jikinshi akwai zazzaɓi kallon amna da ke matsowa wurina tana kallona na yi harara na watsa mata "kar ki kuskura ki matso wurina tunda bakya jin magana"




Kuka ta sa tana riƙe kunnenta kamar yanda suke yi idan sun min laifi "kiyi haƙuri mommy bazan ƙara zagi ba" tausayi ta bani na janyo hannunta "to ki ba yaya haƙuri kinga akanki abba ya dakeshi" matsawa tayi tana

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login