Showing 24001 words to 27000 words out of 57484 words

Chapter 9 - AURE DA KARATU Book Complete Rumaisa Sidi.txt

26 Jan 2025

6698

leƙen fuskar safwan "yaya kayi haƙuri bazan ƙara zagi ba"


Faɗa na ƙara yi mata sannan su ka zauna muna hirarmu kamar wasu sa'anni na muna nan zaune ya fito ya murtuƙe fuska kamar wanda bai taɓa dariya ba kuɗi ya fitar daga aljihunshi 200 "kai karɓi amsomin sugar wurin idi" ya faɗa yana kallon safwan




Dubanshi nayi "ka baiwa ko Aysha ta karɓoma zazzaɓine sosai a jikinshi wallahi" zabura yayi "zazzaɓinne zai hana mishi karɓo min sugar a waje? kai zaka tashi ko sai na ɓallaka munafuki kawai wallahi daidai na ke dakai yanzu" shiru na yi har safwan ya karɓi kuɗin ya fita miƙewa na yi na koma ɗaki ina ƙoƙarin shiga toilet maganarshi ta tsunduma kunne na




"kar ki ƙara sakamin baki idan ina magana da yarana tarbiyya nake basu don bazan sake su haka kawai yanda ake so ba"






















HMMMMMMMM✍️✍️✍️






*AURE DA KARATU*




*NA*


*RUMAISA'U SIDI*








*FARAR ANIYA WRITERS*








*Page 19*








Gajeriyar dariya na yi sannan a fili na ce"Su tarbiyya manya" na doshi toilet ɗina da shigowar shi ta dakatar da ni "Me kike nufi da su tarbiyya manya? ba nida tarbiyyar kike nufi ko me"




"Wai don girman Allah Abban Safwan me ya sa kake son mai da masassara ciwo ne? na lura kwanan nan magana kaɗan ka ke jira in yi ka hayaƙo min, wai me ke faruwa don Allah" na tambaye shi ina so ya faɗa mini laifin da na mishi da ya ke jin haushi na.Wannan zaman ya ishe ni ta ya za a ce ke da mijinki amma ba wata magana mai daɗi da za ta shiga tsakanin ku? Shikenan mu ba mu da aiki sai gasawa juna magana kamar ba Auren soyayya mu ka yi ba?




Magantuwa na ƙara yi ganin ya zuba min ido ya na kallona"Ka faɗa mi ni laifin da na maka sai in baka haƙuri,wannan abin ya ishe ni,da me kake so inji,da KARATUNA,ko da yarana,ko kuma da rigimarka?




"Au wato ma rigima na ke yi ko?tunda ga ɗan ki ko? To bari ki ji,yadda ki ke ɗauka ta ba haka na ke ba,ni ba sakaran namiji ba ne da mace za ta riƙa juyawa yadda ranta ke so ba.Ki bar ganin kina da ƴan canji a hannunki hakan bazai canja matsayina na miji a gare ki ba,waƴannan yaran kuma ba za ki canja mu su wani uban ba ni ɗinne dai idan kuma za ki canja mu su to bismillah"




Yadda ya ke fitar da maganar kaɗai ya isa ka fahimci haushina da ya ke ji,wanda ni har ga Allah ban san laifin da na mishi ba,wallahi ban sani ba ganin tsayuwar ta wa ba ta da wani amfani ya sa na shige toilet ɗina ina cewa "Allah ya kyauta"




Abin mamaki har na kammala abinda zan yi na fito yana ɗakin kuma bakinshi bai huta da masifar da ya ƙirƙirowa kan shi ba.


Ƙofa na dosa da niyar bar mishi ɗakin na ji an janyo bayan rigata da ƙarfi waigowar da zan yi na ga ya ɗaga gandamemin hannunshi alamar jikina zai yo na yi saurin kaucewa.




A fusace nima na fara magana "Kar ka kuskura,wallahi kar ka kuskura hannun ka ya sauka jikina da sunan duka,wancan ma na baya na raga maka ne saboda igiyar aurenka da ke kaina,amma wallahi tallahi yanzu duk ka kuskura ka taɓa lafiya wallahi za ka yi nadama marar iya ka"


Kallona ya ke sandare da hannun da ya ɗaga da niyyar shararamin mari jikinshi ne ya fara rawa idanunshi su ka rikiɗe "Ni kike faɗawa wannan maganar? Nufin ki idan na mare ki ramawa za ki yi?


Ya na maganar ne bakinshi da kuma harshenshi na harɗewa alamar ya kai maƙura ga ɓacin rai.Nima kuma haka,don har ga Allah tsayin da na gyara na gyarane da shirin da ya mare ni zan rama don ni ba jakar shi ba ce.




Zuwa da komowa ya fara yi a ɗakin,nima ina tsaye ina jiran duk abinda zai faru ya faru don ya na dukana wallahi ramawa zan yi.Dakatawa yayi tare da kallona "Na samo mafita,wannan ne kaɗai hanyar da za ki gane har yau ina gaba da ke...."shiru ya yi na ƴan sakanni sannan ya ci gaba da magana "Kije *NA SAKE KI SAKI BIYU*, ba sauran Aure tsakani na da ke,na katse igiyoyin da kike tunanin akwai sauran mutunci a tsakanin mu.Kuma kar ki kuskura ki ɗaukar min yara saboda ba da su kika zo ba,ki bar su gidan ubansu don ban faɗa miki na kasa ba"






Kamar wadda ta hau lilo haka na ga ɗakin na juyawa da ni,kunnuwana kuma kamar an jona lasifika a ciki haka na ke jin shigar kowace kalma da ke fitowa daga bakin shi daƙyar na samu na fara kiran "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un"na shiga maimaitawa jin gani na neman ɗaukewa.




Zagaye ni yayi ya bar ɗakin,bakin ƙofar na kai zaune daɓass tare da dafe capet ɗin da ke malale a ɗakin nawa na sauke kaina ƙasa.Na rasa me zan yi?Shin kuka zan yi ko ihu? Me yasa ya min haka? Tabbas ya na da dalili,ko ya na tunanin ba zan iya rayuwa ba sai da shi? Ya sha faɗa min hakan "Zee irin wannan soyayyar da ki ke min wallahi da wahala ki iya rayuwa babu ni"




To kenan haka ne? Me yasa kullum na ke bari Lawal ya na galaba a kaina? Duk abin da na sa mu ba ya wuce lawal, a kan shi na guji zaɓin iyayena.Tabbas sakamako na ke gani akan bijirewa shawarar iyayena.Na san da ace abin da na suke so na bi, da ban haɗu da wannan ƙalubalen ba.Idan kuma dama can an rubuto hakan zai faru da ni to Allah zai kawo min sauƙi ko don biyayyar da na yiwa iyayena.




Amma ko yanzu ban makara ba,zan nuna wa lawala a da ne na mishi wannan mahaukacin son,amma a yanzu tsaf zan yi rayuwa ta ba tare da shi ba.




Wani ƙwarin guiwa ne na ji ya na shiga ta miƙewa na yi na shiga haɗa tufafina da ƴan ƙananan kaya na da na ke amfani da su kullum a babban akwatina.Ɗakko hijabin sallah ta na yi da ya ke har ƙasa na zuba,agogo na kalla 8:47pm na san ba matsala zan iya tuƙi da yardar Allah.




Falon na fito ina janye da akwatin kayana,shi ma ya na nan zaune rungume da Amna,Aysha kuma na kwance akan center capet da drawing book a hannunta.Tashi zaune ta yi tana kallona"Mommy fita za ki yi" idanuwana na zuba mata tare da jin wani irin tausayinta da ya lulluɓe ni,saboda duk cikin ƴaƴana ta fisu ƙulafucin uwa,ba ta ƙaunar ko nan da can na matsa na barta.




Jin maganar da Aysha ta min ya sa Amna da mahaifinta waigowa kallon kallo muka shiga yi ni da shi,ni na fara janye idanuwana na mayar kan Amna da ta riƙe min ƙafafuwa "Mommy zan bi ki,kin san ranar da Aysha kika tafi,ki ka ce idan za ki ƙara fita za ki je da ni" hannuna na sa na janyeta sanin da na buɗa bakina kuka zai iya ƙwace min.




Kanta na shafa tare da ɗaukar akwatina na tunkari ƙofar barin ɗakin,da ƙarfi na ji an rungumeni ta baya,zafin da naji ya fara ratsamin jiki ya sa na fahimci Safwan ne.Juyowa na yi ina kallonshi hannuwana ya riƙe idanuwanshi na zubar da hawaye "Mommy don Allah kar ki tafi ki barmu,kinga Aysha kuka ta ke yi,Amna ma kuka za ta yi,duba ki gani Mommy nima kuka zan yi,don Allah kar ki tafi"




Rungume shi na yi da ƙarfi ina jin kamar in maida shi ciki saboda ƙaunar da na ke mishi.Da gaskiyar Lawal da yace duk cikin ƴaƴana na fi son Safwan bai faɗi ƙarya ba sai dai ban taɓa kuskuren nuna hakan a gare shi ba ballanta hakan ya raba min kan yara.




"Ka kula da ƙannenka,Ku ci gaba da karatu,banda shiririta Allah ya muku albarka kai da ƙannenka" sakin shi na yi na ɗauki akwatina na bar ɗakin ina jin yadda sautin kukan yarana ke shiga kunnena ina gab da isa motata na ji sautin kukan Amna ta na kirana "Mommmmmmmmyyyy" har cikin kwanyata na ji sautin,Ina tuƙi ina kiran sunan Allah,da fatan ya kaini gida lafiya.






Kamar ƴar maye haka na shiga falon na mu ina layi,Ummina da Yayyena suna zaune a falon da alama wani abu suke tattaunawa.Yaya Isma'il ne ya taro ni ganin ina neman faɗuwa ƙasa "Ke lafiyarki,Me ya same ki?




Zaunar da ni ya yi a kujera kusa da Ummi,matsawa na yi jikinta tare da rungume ta ina goga kaina a jikinta kaina ta shiga shafawa a hankali,sai lokacin na samu na saki wani marayan kukan da na daɗe ina nema ko zan samu faɗawar ƙololon da ya tokare min maƙoshi da ƙyar na samu na fizgo maganar da na ke son fitarwa "*Ya SAKE NI*,Ummi Lawal ya sake ni,yau Aurena da lawal ya ƙare,komai ya ƙare ummi"
















Uhmmmmmm😢












Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/D84KccWmLGj6Iw3z7tTAh3






*AURE DA KARATU*




*NA*
*RUMAISA'U SIDI*






*FARAR ANIYA WRITERS*




*Page 20*






"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un"Ummi da Yaya Isma'il su ka shiga maimaitawa "Allah ya sa hakan ne mafi alkhairi a rayuwarki Zainab,Allah ya baki juriya,ya kare mi ki yaranki a duk in da suke. Don Allah kar ki ɗaga hankalinki don kin rabu da Lawal ba shi ke nufin kin rabu da farin ciki ba,ki duba ga ni ga kuma ƴan uwanki masu son farin cikinki,don haka ki kwantar da hankalinki.Saki nawa ya miki?"




Ɗagowa na yi daga jikinta ina kallonta hawaye na ƙara zubo min "Saki biyu ya min Ummi"




"To ki kwantar da hankalinki ta shi muje ki samu ki kwanta kar ki jawowa kanki wani ciwon kuma"
hannuna ta riƙe ta kai ni har ɗakin baccinta sai da na ce mata bacci na ke ji sannan ta fita.Amma inaaaa,ba na jin yau duk satar ɓarawon zai sa mu nasarar sace ni,mutuwar Aure fa ake magana,duk da ba abin da Auren Lawal ya tsinana min amma kasancewa ta inuwa ɗaya da yarana ya fi min daɗi fiye da rabuwa da su.




Yanzu fa su na can hannun Lawal,ko sun yi bacci? shin ya mu su addu'a? Zaune na tashi tuna yadda na barosu su na kuka nasan in dai Amna ce sai ta raba dare ta na wannan kukan ba abin da ya dame ta,da ma can ni ce mai lallashin kayana to yanzu ga shi za mu kwana ba a tare ba,bansan a wane hali su ke ba.




*FALO*




"Wallahi Ummi sai ya yi nadamar wulaƙanta Zainab,zan nuna mi shi na fi shi ɗanyen kai"Yaya Abbas ke faɗa cikin matuƙar ɓacin rai miƙewa ya yi ya tunkari ƙofa




"Abbassssss" Ummi ta kira shi da ƙarfi sanin abin da zai je yayi ba zai wa kowa daɗi ba"Dawo ka zauna"da ido Ya Isma'il ya bi shi har ya zauna




"Haba Abbas da iliminka da komai,da ma Aure rai ne da shi to su nasu ya ƙare yau addu'a kawai za ku mata Allah ya zaɓa ma ta abin da ya fi alkhairi a rayuwar ta" Ya Isma'il ya tunatar da Ya Abbas




Numfasawa Ummi ta yi sannan tace "Damuwa ta ɗaya yarannan da ke hannun shi,mutumin da ya kasa kula da kanshi ma ballantana wasu ƴaƴa.Idan har zai yu ina so a karɓo yarannan ko don kwanciyar hankalin mahaifiyar su,ni zan fitarwa da Abbas kono tun da ya yi rantsuwa amma ban lamunta da zamansu a can ba"


A kan wannan su ka tsaya,kowa ya bada goyon bayan karɓo yaran ko don lafiyar Zainab.






*LAWAL*




A kan idanuwanshi ta ja jakarta ta bar gidan,ga ihun yaran da ya cika mishi kunne,bai san me ya sa ba shima ji ya ke kamar ya ɗora hannu a ka ya yi ta ihun.Yaran ya kalla tausayi su ka ba shi ganin yadda su ka makure gefen kujera Safwan na rungume da su,tausayi su ka ba shi ta shi ya yi ya isa in da su ke,hannu ya sa ya ɓanɓaro Amna da ihun ta ya fi na kowa




Rarrashinta ya shiga yi ta na tuburewa "Wai za ku yi min shiru ne ko sai na haɗe ku na zane" ya da ka mu su tsawar da ta ƙara firgita Aysha,jikin Safwan ta ƙara shigewa ta na danne bakinta kar kukanta ya fita




Ƙwacewa Amna ta yi daga jikinshi ta nufi ƙofa miƙewa Lawal ya yi tare da cafkota,zillewa ta shiga yi "Ni wallahi wurin Mommyna zan je,ni wallahi sai na je" gajiya ya yi da rarrashinta ya da ka mata tsawar da ta ya kamata ta sa tayi shiru amma sai ta faɗi tsakiyar ɗakin ta na shure-shure "Ni wallahi sai na je wurin Mommy,Ni wurin Mommy zan je,Abban tusa kawai"




Kan shi ya dafe ya na jin kamar zai watse wannan bala'in da me ya yi kama,Zainab ta bar mi shi jaraba,Daga shi har yaran falo su ka kwana.




*ZAINAB*






Yadda na ga rana haka na ga dare,ba wai saboda mutuwar aurena na kasa bacci ba A'a saboda ƴaƴana ne da na san yadda na shaƙu da su.




Ƙwarin guiwa na baiwa kaina na fita kitchen ina taya Anty Asabe aiki saboda ya ɗebe min kewa.Muna yi muna fira jefi-jefi har Ummi ta fito,daga yanayin fuskar ta na fahimci ta ji daɗin yadda na ke ƙoƙarin danne damuwata.




Lokacin da na zo yin breakfast ɗina yarana na tuna shin sun ci abinci? To ko shi ba daƙyar ya ke samu ya ci ba ballantana ya ba su "Ya Allah ka zama gatan yarannan a duk in da su ke"




*LAWAL*


Bai ƙara raina kan shi ba sai da aka wayi gari ba ya da ko sisin da zai siyawa yara abin kari ga Amna ko yau ta tashi da rigimar ta wata dabara ce ta faɗo mishi ya tunkari kitchen sanin komai ana kawo ma ta daga gidansu.




Ruwan Zafi ya ɗora har su ka tafasa ya juye,wurin da yasan tana ajiyar kayan shayin ya tafi sai dai ga sugar amma ba madara.Kayan ya kwaso ya fito da su,ɗakin yaran ya shiga dukansu su na kwance Safwan ta duba "Kai ina Mommynku ke aje madara?




Ba tare da ya tashi ba ya bashi amsa "Madara ta ƙare ko jiya sai da ta bamu kuɗi mu ka siyo" ajiyar zuciya ya sauke tare da barin ɗakin Yaran ya ɗaga murya ya kira ya zuba musu ruwan zafin da ya zuba sugar a ciki






"Abba haka za mu sha shayin ba madara kuma ba breadi" Amra ta faɗa tana ɓata fuska "Eh haka za ku sha idan kuma ba za ku sha abinda na baku ba to ku bari"






"Ba kayanka ba ne,duk abinda ke kitchen ɗin na Mommy ne,kuma mu Mommy ba ta taɓa ba mu ruwa a matsayin breakfast ba" Safwan ne ke maganar,cikin wani sauti da ke bayyanar da tsanar mahaifinshi ƙarara.




"Kai rashin kunyar ta ka har ta kai can? Ni za ka nuna wa ka girma? To wallahi ba zan siye madarar ba,duk wanda bai sha ya bari"




Haka ya kwankwaɗi ruwan su kuma kowanen su ya kasa sha maganar makarantar su Safwan ya mi shi "Lokaci ya tafi ku bari sai gobe,yanzu ku tashi in kai ku wurin Mama don ni fita zan yi"




A tsakar gidan su ka sami Mama ta na jawo ruwa a rijiyar da ke gidan,jawo gugar ta yi tare da zube ruwan da ta ɗebo a bokiti ta na kallon su cike da mamaki,saboda duk zuwan da su ke yi ba su taɓa sammako irin yau ba.




"Wa'alaika salam,yau su mai gida ne tun da sassafe" durƙusawa ya yi a gabanta ya na gaida ta amsawa ta yi tare da wucewa ɗakinta Lawal da kuma yaran su na bayanta.




"Lafiya na gan ka da yara tun da sassafe kuma na ga jakar kaya a hannunka?




Kallon yaran ya yi "Ku je waje kafin in fito" sai da su ka fita sannan ya mayadda kallonshi ga Mama "Za su zauna ne na ɗan lokaci kafin in samo mafita"




"Ban gane za su zauna ba ina mahaifiyar su? ta tambaya tare da fatan Allah ya sa ba gajiya Zainab ta yi da zaman ta yi yaji ba




"Mun rabu da Zainab ne jiya Mama"




Hannunta ta buga ga ƙirji "Kun rabu da Zainab? kana kuwa da hankali Lawwali?Zainabun ka saka? Matar da ta rufa ma asiri Allah ya rufa ma,ka na buƙatar ci gaba a rayuwar ka kai kam,innalillahi wa inna ilaihi raji'un"






"Ita ce ta kai ni bango Mama,kullum nema ta ke ta mayadda ni sakaran namiji kuma................."




"Dallah yi min shiru,to miye kai in ba sakaran namiji ba,hotiho wanda ba ya da aiki sai bacci,wallahi idan akwai abin da ya fi sakarai to kai ne.Kuma wallahi ba baki na maka ba sai ka yi nadamar wannan sakin da ka yiwa Zainab.Kuma wallahi ka yi gaggawar ɗaukar yaranka ku bar min gidana don bazan riƙa su ba sai ka san inda za ka kai su" daga haka ta tashi tare da shigewa ƙuryar ɗakinta ta mai da ƙofa ta rufe.




A sanyaye ya kaɗa yaran su ka fita,tsaye ya yi bakin titi ya na tunanin yadda zai yi da yaran,Allah ya gani shi ya san bazai iya kula da su ba don ko abincin da zai ba su baya da shi ko na cikinshi wuya ya ke mishi ballantana na yara har uku.




Gidan Anty A'i (yayarshi) ya nufa da su,tunda ta ganshi ta ɗaure fuska don ta ɗauka ya zo roƙonta ne kamar yadda ya saba.Sai da su ka gaisa ta sa aka zubowa yaran masa da miyar da ta ke siyarwa sannan taje ta samu Lawal da ke jiranta a falo.




"A gaskiya Lawal idan na ce ma zan riƙe su Safwan na yi ma ƙarya,ka na kallo nima yadda na ke

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login