Showing 51001 words to 54000 words out of 57484 words

Chapter 18 - AURE DA KARATU Book Complete Rumaisa Sidi.txt

26 Jan 2025

6706

fita bayan ya tambaya idan akwai abin da nake buƙata nace babu.




Gyaran gidan na shiga yi,nan take na ƙalƙaleshi tsaf na watsa turaren da nazo dashi a cikin burner sai gashi gida ya game da ƙamshi.




Kitchen na shige duk da na gaji,amma haka na daure na girka muna sauƙaƙƙen abinci.Wanka na ɗanɗasa bayan na ƙare sannan na jiƙe jikina da turare na fesa kwalliya ta.




Dogon hijabi na ɗora akan kayan jikina sannan na ɗauki wata ƴar ƙaramar jaka na nufi ɓangaren gwaggo.




Tsaraba ce da nayo na kaimata,tare da ta Zubaida "Ki kaimata da kanki mana,ai mun gode sosai wallahi kinyi ƙoƙari"ta faɗa tana miƙo min na Zubaida




Ba zan iya musu da ita ba,wannan yasa na karɓar tare da yi mata sallama na fito.




Ɓangaren na nufa,tsayawa nayi a bakin ƙofar falon ina doka sallama,daga ciki naji an amsa min saida na shigo na samu ƴar aikinta na wurin dinning tana zuba mata abinci,ita kuma tana hakince kan kujerar tana jira a kawo mata.




Ƙara sawa nayi wurin da take zaune na ajiye mata ledar sannan nace "Maman Zainab ga wannan aci da haƙori"daga haka na juya ina ƙoƙarin barin falon




Ƙiiiii naji an janyo hijabi na da ƙarfi,ban shirya wa hakan ba shi yasa kai tsaye nayi baya cikin iyawar Ubangiji na dafe kujerar da ke kusa da Ni.




Miƙewa tayi a fusace ta watso min ledar da na kawo mata,nan take kayan miyar da na kawo mata suka zube ƙasa.




Yatsunta ta buga suka bada sauti sannan tace "Wannan ya zama na ƙarshe da zaki je gida kuyo barbaɗe-barɗenku sannan ki dunƙulo ki kawo min.Su dai da kika shanye sun shanyu Amma wallahi ni nafi ƙarfi ki"




Juyawa nayi da sauri don barin ɗakin don a yadda raina ya ɓaci komai zai iya faruwa.Amma me?Ina juyawa naji maganar ta ƙasa-ƙasa "Banza kawai Karuwa"cak na tsaya tare da juyowa da ƙarfi wanda ko ita saida ta zabura tare da yi baya kaɗan




Wurinta na matsa "Maimaita abinda kika ce"na faɗa ina juya hannuna




Cike da rashin kunya ta ƙara faɗi "To tsoron ki nake da bazan maimaita ba?Nace banza Karuwa mai ƙwacen.........."






Tasssss na ɗauke ta da mari batare da jiran ta ƙarasa ba,dafe kunci tayi tana kallona "Ni kika mara"ta faɗa tana nuna kanta




"Wannan ya zama na ƙarshe da ƙazamin bakinki zai ƙara faɗa min magana irin wannan,idan can gidanku ba a miki tarbiyya ba to ni nan zan miki.Kar kiga ina ƙyaleki,wallahi na fiki iya rashin mutunci.Amma idan kina musu ki ƙara magana ki gani" daga haka na bar falon zuciyata na tafasa sosai,na tsani wannan kalma.




Ina zaune falona ina latsa wayata don ta ɗan ragemin abinda nake ji ya shigo kamar wanda aka koro.






"Me Zubaida ta miki da zakije har gidanta ki mare ta"ya katse numfashi na daga gaida shi da nake ƙoƙarin yi




"Ita da ta turo ka,bata faɗa ma abin da ya jawo hakan ba" na faɗa ina ɗauke kaina abin da ya ƙara tunzurashi




"Ba zan ɗauka ba,wannan ya zama na ƙarshe da zaki ƙara ɗora mata hannu da sunan duka,ko ni da nake mijinta ban taɓa dukanta ba.Don haka kema wannan ya zama na ƙarshe"




Zuciyata ce ta kawo wuya nima na miƙe a fusace "Wallahi muddin ta ƙara shiga gonata sai nayi fata-fata da ita,idan har kana gudun wani abu ya taɓa ta to ka maida ta ciki ƙarewar ƙauna"daga haka na ɗauki wayata don in wuce ɗauki




"Wato ina miki magana wuce wa ma zaki yi ko? Tafiyar kwana uku duk ta canja ki, ni bazan ɗauki wannan abin ba gwanda ki sani tun yanzu"




Idanuwana ne suka cika da ƙwalla na dube shi "Tafiyar da nayi ai kasan inda naje,wata ƙila can aka koyo min baƙin halin"daga haka na shige ɗaki na.




Nasha kuka sosai a wannan ranar,ko da dare yayi nayi shirin bacci tsaf na gyara kwanciyata sai gashi ya kirani in kawo mishi abincin shi.




Haɗa kayan nayi na kai,koda naje tana kwance akan kujerar ɗakin,gabanshi naje sannan na aje tiren abincin "Yawwa ƴar albarka" Zuba mishi nayi sannan na miƙe tsaye,kujerar ya nuna min "Kinga ƴar uwarki zazzaɓi ke damunta saboda kukan da ta sha.Don Allah Zainab ku dinga haƙuri da juna"




Ko gefen da take ban kalla ba nace "Ai tunda kana nan zaka kula da ita"daga haka na bar falon.




Kwana biyun nan nawa haka suka tafi ba daɗi,duk da idan muna waje ba wanda zai fahimci abinda ke faruwa a tsakanin mu.




Shima kuma shareni yayi suna zuba soyayyar su shi da sabuwar Zubaidar shi.




A tsaye na fara rashin lafiya,bana cin abinci,ga jiri,nan take na rame.Gwaggo ce ta fara ankara da halin da nake ciki "Zainab ki faɗa min damuwarki,duk gidan nan baki da kamata.Ni kamar Mahaifiya nake a wurinki.Na daɗe da fahimtar akwai abin da ke faruwa a tsakanin ku da yaron nan,ki faɗa min kinji"




Murmushi nayi mai ciwo sannan nace "Ba komai Gwaggo, kawai banjin daɗi ne kwana biyu, amma ba wata damuwa"ido ta zuba min alamun bata yarda ba




Ajiyar zuciya ta sauke sannan tace "Shi kenan,idan ma akwai abin da kike ɓoyemin Allah ya yaye miki damuwarki.Kuma gobe Kiyi ƙoƙari kije asibiti ba a zama da ciwo kinji"




Kaina na gyaɗa "In Sha Allah zanyi ƙoƙari in je"




Washe gari text na mishi nace ina so inje asibiti ko minti biyu banyi da tura saƙon ba sai gashi har cikin ɗakina.




Wurina yayo da sauri ya shiga taɓa wuyana "Ba kida lafiya Zainab?Me ke damunki?Innalillahi wa inna ilaihi raji'un"




Idanuwana na lumshe abinda ya baiwa hawaye na damar zubo wa,nayi kewar wannan kulawar tashi,ƙara ruɗewa yayi "Don girman Allah ki daina kuka Zainab"




Kaina na girgiza hawaye na min zuba "Izini fa kawai na nema ka bani,naje na dubo lafiya,bance ka baro matarka ba"




Rungume ni yayi da ƙarfi"Don Allah ki daina wannan maganar, wallahi ji nake na tsani kaina da faruwar wannan al'amari,ki yafe min Zainab"lallashina ya shiga yi da kalamai masu daɗi tare da neman yafiya a wurina




Shi yasa na shirya tsaf muka fito, ɓangaren Gwaggo muka shiga muka faɗa mata zamuje asibiti.Alamu sun nuna taji daɗin yadda ta ganmu.




Gambu ya buɗe min ina ƙoƙarin shiga muka ji Muryar ta tana magana "Ya Bashir kaifa nake jira"ta faɗa cikin shagwaɓa.




Ko da muka dawo asibitin ƙin binshi ɓangaren gwaggo na yi na wuce nawa ɓangaren.




Koda maganar samun cikina ta fita ba wanda bai yi murna ba.Kullum da kalar ƙwalamar da Gwaggo zata min,kuma ina jin daɗi sosai.




Haka ma uban gayyar,wata kulawa yake bani ta musamman,kamar wanda za a yiwa haihuwar fari.




A fili Zubaida ta nuna hassadar ta akan cikin,inda ta bi ta tada hankalin ta.Wannan yasa basa kwana biyu basu samu matsala da shi ba.




Ni dai fatana Allah ya raba ni da shi lafiya.




*LAWAL*






Tunda aka sallamo Safwan daga asibiti,Lawal ya canja mishi makaranta.Ya maida shi mai sauƙin cunkoso.




Kulawa yake baiwa yaron ta musamman,duk abinda yake so yana siya mishi.Haka ma Amna da ke gidansu Zainab duk wata yake siyayya yaje ya ganta.




Nusaiba ma ganin bazata samu riba a Safwan ba yasa ta shafa mishi lafiya.Ta fita harkar shi,duk da mugun haushin yaron ta ke ji.




Yau tun safe da Lawal ya tafi kasuwa bai dawo ba,har Safwan ya dawo makaranta ba a dafa abinci ba.




Sai bayan la'asar ya dawo ya jigata sosai ya shigo gidan,da gudu Safwan ya rungume shi "Baba Ina ka tafi, nayi ta neman ka"kanshi ya shafa yana jin wata ƙaunar yaron na shigar shi.




"Wallahi ina kasuwa Safwan,kayanne sai yanzu suka samu,idan nace na dawo ban siyo ba to ko gobe ba zan samu ba.Kaci abinci dai ko"




Girgiza kanshi yayi "Aa banci ba Abba"




Nusaiba da ke hakince ya duba "Yanzu Nusaiba shine kika kasa ranta min kuɗi ki dafa abinci ko don yaron nan"




















*RUMAISA'U SIDI*✍️✍️✍️








*AURE DA KARATU*


*NA*


*RUMAISA'U SIDI*


*FARAR ANIYA WRITERS*




*Page 38*






Wani kallo ta watsa mishi sannan ta ɗauke kanta "Ina naga kuɗin da zan ranta ma?Kuma kenan ta ɗan ka kawai kake ni kuma ko oho"ta ƙarasa tana girgiza jiki.




Wani baƙin ciki ne ya turnuƙeshi a ƙufule yace"Yanzu saboda tsabar rashin tausayi kika bar yaron nan haka?Ina kuɗin da na baki jiya?Allah sarki Zainab,wallahi ta banbanta da matan zamanin nan"






Tsaki ta buga cikin jin haushi "To amma duk wannan bai sa ta tsira a wurinka ba,kaga malam ba fa zaka zo ka saka ni gaba ka dinga min masifa ba ehe,na gaji wallahi"daga haka ta murguɗa baki tare da buga zane ta wuce ɗakinta.




Idanuwanshi ne suka rine,jikinshi ya ɗauki rawa.Hannun Safwan ya kama ya fita dashi daga gidan.




Abinci ya siyo mishi ya aje gabanshi "Kaci kaji Safwan,kayi haƙuri,na bar ka da yunwa"murmushi yaron yayi sannan ya riƙo hannun mahaifinshi ya zaunar da shi "Kar ka damu Abba, kaima ka zauna ka ci"






Shafa kanshi yayi cikin tsantsan ƙauna yace "Allah yayi ma albarka Safwan"




Sai da ya tabbatar yaron ya ƙoshi sannan shima ya samu ya siye abincin yaci,daga nan wurin mama suka wuce.




*ZUBAIDA*




Tunda taji samuwar cikin Zainab tabi ta addabi rayuwarta,ta hana kanta farin ciki,ta daina cin abinci kullum cikin fitina ta ke da Ya Bashir.




Tsaye take gabanshi shi kuma yana zaune kan kujera ya ɗora laptop akan cinyarsa yana aiki.




"Magana fa nake maka,amma ka ƙyaleni"




Kallo ɗaya ya mata ya ci gaba da aikin da yake yi "To me kike so in Miki?"




"Au wato baka ma san me zaka min ba ko? To wallahi dole ayi wacca za a yi"ta ƙarasa tana ɗaukar filon da ke gefenshi tayi jifa da shi.




Haka ta dinga jifa da duk abin da takai hannunta.Miƙewa yayi ya riƙo ta da sauri kuma a fusace "Wai kina da hankali kuwa?"




Kamar mai shafar aljanu ta juyo da ƙarfi tana watsa mishi idanuwanta da suka rine "Eh bani da hankali,ni mahaukaciya ce Bashir"ta ƙarasa tana dukan ƙirjinta.




"Wallahi bazaka taɓa samun kwanciyar hankali ba har sai ka haɗani da likitan da zai duba ni,nima na haihu kamar yadda zata haihu"




Tureta yayi ta faɗa kan kujera ya nuna ta yana faɗin "Wallahi ba likitan da zan haɗa ki dashi, lokacin da kike yin allurar ki kin shawarce ni?Har nuna miki fushina nayi akan hakan amma kika yi biris, kika ce ke bazaki iya haihuwa kamar akuya ba.To yanzu na samu wadda zata haifo min ƴaƴa miye matsalata da ke"




Zaburowa tayi da ƙarfi ta cakumo wuyan shi "Wallahi Bashir baka isa ba,kai kayi kaɗan ka tozarta ni.Mugu kawai maci amana Allah ya isar...................."






Tasssss ya ɗauke ta da wani marin da saida ta tangaɗa,nuna ta yayi hannun shi na rawa "Na gaji da matsalolin ki,haukar ki ta isheni,wallahi idan kika kaini ƙul komai zai iya faruwa"daga haka ya ɗau kayanshi ya barta nan yashe tsakar falon.






*ZAINAB*




Na tsorata sosai da yanda ya shigo ɗakunan,tashi zaune nayi ina kallon shi cikin mamaki sannan na dubi agogon ɗakina ƙarfe 12:08.




A hankali nayi magana ganin yadda jikinshi ke rawa "Lafiya dai Ya Bashir"




Kanshi ya girgiza tare da dafe kanshi "Haɗa min ruwa toilet please idan zaki iya"




A gurguje na haɗa mishi tsoro na ƙara shigata saboda ban taɓa ganin shi a irin wannan halin ba.




Ina nan zaune har ya fito,cikin kayanshi da ke ɗakin ya ƙara shirin bacci ba tare da ya dube ni ba yace"Bani key ɗin ɗayan ɗakin"




Idanuwana na zaro sannan nace "Lafiya dai,me ya sami ɓangaren ka"




Tsaki ya buga tare da dafe kanshi "Don Allah ki bani"




Washe gari ma anan ya shirya Amma yau koda ya fito ba wannan fushin na jiya,saima tsokana ta da ya shiga yi.




A kwanakin da suka biyo baya na fahimci sun sami matsala da Zubaida ne,saboda kwana biyu da yin hakan mahaifiyar ta tazo gidan mun haɗu da ita tana ƙoƙarin fitowa daga ɓangaren gwaggo ni kuma ina ƙoƙarin shiga.




Wani kallon banza ta min sannan ta buga tsaki ganin tana ƙoƙarin bangaje ni yasa na raɓe mata ta wuce.




Daga yadda na samu Gwaggo na fahimci ba zuwan arziki matar nan tayi ba,duk da bata sanar da ni dalilin zuwan ta ba,amma ta gargaɗe ni da in tsare addu'a da neman tsarin jiki.




Kwana biyu kuma sun dawo ɗinke kamar basu ba,dama ai mata da miji sai Allah.




Rainon cikina na ci gaba da yi,ina samun kulawa sosai daga mijina har Gwaggo na.




A Wannan lokacin ne na saka rigimar sai ya nemo min aiki,dariya kawai ya dinga yi min abinda ya ƙara tunzurani na saka mishi kuka.




Tsagaitawa yayi da dariyar yana kallona"To naji aiki ko? Naji za kiyi"ya faɗa yana dafe bakinshi yana ƙoƙarin danne dariyar da ke taso mishi.




Lallaɓani ya dinga yi tare da min alƙawarin barina nayi aiki idan na haihu,wannan ne ya rufe rigimar.


A kwana a tashi har cikina ya fara tsufa,Ya Bashir da Gwaggo kullum cikin tariyar kayan haihuwa suke.Anty Halima ma ba a barta a baya ba,yadda take lissafin EDD ɗina ko ni bana lissafin shi haka.




Kullum addu'a ta Allah ya rabani da wannan cikin lafiya,domin wannan cikin ya tanbanta da sauran,tun yanzu cikin ya mata wani irin girma.






Zaune nake a kan carpet ɗin falon kasancewar yanzu bana son zaman kujera sam, na ɗora bowl da magarya a ciki akan cinyata ina sha.




Kallon wayata da ke ƙara nayi,wannan kusan shine kira na 9 da ke shigowa wayar amma ba wanda na ɗaga.




Tsaki na buga tare da jawo wayar da wani kiran ya ƙara shigowa, number Hafsa ce ɗagawa nayi tare da sakata hands free Ina ci gaba da shan magarya




"Hello kina kina"naji Muryar Hafsat




"Ina jinkiri"na faɗa ina ci gaba da abinda naie,dariyar mugunta ta saki "Takawarki lafiya uwar biyu,Amarya kuma shalelen Bashir ya hutawa"ta ƙarasa tana ƙara sakin dariya




Ƙwafa nayi "Wallahi ki guji haɗuwarmu Hafsat,na rantse sai na kafta miki tsiya,ba uwar biyu ba,uwar tara"daga haka na katse kiran ina sakin guntun murmushi a karo na farko tun wayuwar garin yau.






A kwanakin nan kowa haushi ya ke bani,hatta Ya Bashir ɗin haushin shi nake ji,lokuta da dama yasha kamani Ina harararshi sai dai yayi murmushi yace "Allah ya sauke ki lafiya Zainab"






Hutun da su Amna suka samu a makaranta yasa Anty Halima tazo min da ita.Naji daɗi sosai,ko ba komai nayi kewar ƴaƴansu.






A haka har na shiga watan haihuwa,har yazo ya ƙare shuru ba labarin haihuwa.Kamar wadda zata yi haihuwar fari haka na tusa Ya Bashir a gaba ina mishi kukan sai ya kaini asibiti an cire cikin.






Lallashina ya dinga yi tare da kwantar min da hankali,haka ma Gwaggo ta dinga bani shawarwari.






Duk lokacin da zamu haɗu da Zubaida to idanuwanta baya sauka ko ina sai akan cikina, fahimtar hakan da nayi duk lokacin da zamu haɗu naga tana min wannan kallon to zan dinga addu'a ina neman tsarin jikina.




Amma yanzu da cikin ya tsufa bala'i nake ji da kowa, idan muka haɗu naga tana min wannan kallon a fili zan buɗa murya ina addu'a.




Ko yau da muka haɗu na fito ina ɗan zagayawa,tana zaune akan wani ɗan dakali dake bayan gidan.Ban lura da ita ba saida na ƙaraso sosai,mun kwana biyu bamu haɗu ba sai naga kamar ta rame.




Harara na banka mata tare da shafa cikina ina karanto addu'ar tsari tare da giftawa ta gabanta "Allah ya sauke ki lafiya Zainab"naji ta faɗa cikin sanyayyar murya.




Da sauri na juyo ina duban ta cike da mamaki,kanta ta gyaɗa min tare da tashi ta matso inda nake.Ƙwallace ta cika mata ido a hankali kuma ta fara magana "Ina fatan Allah ya sauke ki lafiya Zainab,na tabbata matuƙar wani abu ya same ki to kamar ya same Ni ne,saboda ko yanzu Ya Bashir ta taki yake yi,baya bacci kullum cikin sallah yake yana roƙon Allah ya raba ki da cikin nan lafiya.Ba zan miki ƙarya ba Zainab,har yanzu bana jin ƙaunar ki a cikin raina,amma ina buƙatar zaman lafiya tare da ke.Ina roƙonki don Allah ki manta da abinda ya faru kizo muyi zaman aminci kamar yadda Ya Bashir ke so.Dama ni ce mai matsalar to wallahi na aje makamai na,zaman lafiya nake so,na gaji da wannan fitinar ba abinda ta tsinana min,sai tarin damuwa"






Murmushin farin ciki nayi tare da riƙo hannun ta "Ina sha Allah komai ya wuce Zubaida,kuma naji daɗin wannan tunanin naki,nima kuma ina roƙon ki yafe min abubuwan da suka faru a baya"




"Na yafe miki Zainab"ta faɗa tana goge hawayen idanuwanta.




Shiru muka yi dukanmu saboda rashin sabo,ni ce ma na gaji da tsayuwar na mata sallama na koma sashe na.






































*RUMAISA'U SIDI*✍️✍️✍️








*AURE DA KARATU*

*NA*


*RUMAISA'U SIDI*


*FARAR ANIYA WRITERS*






*Page 39*




Wannan ne dalilin fara gaisuwar kirki tsakani na da Zubaida,duk da ban saki jiki da ita ba saboda ban gama yarda da tuban nata ba.




Ita ma ba wani sakin jiki take sani ba,iya ka dai idan muka haɗu mu gaisa shi kenan.




A daren wata juma'a ne na farka da na ƙuda,ni kaɗai ce a ɗakin kasancewar ba kwana na bane,ba yadda bai so ya dawo wurina gudun hakan amma nace a'a,tunda ba ita tace ta amince ba.




Daƙyar na lalubo wayata na danna mishi kira,bugu biyu aka ɗaga "Hello"naji Muryar Zubaida ta ɗaga "Zubaida"na kira sunan ta daƙyar.




"Innalillahi Ya Bashir,Ya Bashir tashi Zainab bata da lafiya"naji tana faɗa cikin ruɗewa da tashin hankali.




A firgice suka shigo shi da ita,hannu na ya riƙa yana ƙoƙarin tayar dani daga tsugunnen da nake,shi ya nuna mata inda kayan da muka haɗa suke.




A tsakar gidan muka haɗu da gwaggo,shi yayi driving ɗin mu har asibiti,mun samu likitoci a asibitin suka karɓeni tare da wucewa ɗakin haihuwa da ni.




Aka bar su anan waje suna min addu'a da fatan sauka lafiya,Ya Bashir sai kai kawo yake yana jin kamar ya bini ɗakin yaga halin da nake ciki.




*ZUBAIDA*




Banbancin ta da Zainab dake naƙudar ƙalilan ne,za a iya cewa ma tafi Zainab ɗin ruɗewa.




Zufa take sharcewa kallon Gwaggo tayi sannan ta dubi Ya Bashir fakar idanuwansu tayi ta matsa kaɗan.




Number Ƙawarta Laila ta dannawa Kira jikinta na ɗaukar rawa,har

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login