Showing 12001 words to 15000 words out of 57484 words
ke har turawa zuwa indiyawa bantaba ganin tsarin halitta irin taki ba wallahi ke kyakkyawace kuma ke ta musamman ce kyawunki na dabanne musamman idanunnan naki masha Allah gaskiya dole na kara kaimi kar late comer yazo yamin abinda ya saba nidai rokona ki rikemin alkawari kar ki jefa zuciyar marayan Allah a wani hali don Allah" lumshe idanuna nayi ina murmushi tare da tuna zazzakar muryarshi
"Kanki daya kuwa zee" naji muryar anty halima da ta kwana biyu a a bayana juyowa nayi ina kallonta har yanzu da murmushi a fuskata " bakomai anty" itama murmushin tayi " ki gayawa wani ba komai amma bani ba kidaiyi a hankali karki zauce kuma wallahi ki wuce ki kwanta tun ummi bata shigo ta ganki gaban madubi a tsaye kina murmushi ba takai ga hasaso abinda na gane" isa nayi nima kan gadon na kwanta ina jan abin rufa tareda kokarin rufe jikina " wai baki yarda ba komai ba " " na yarda mana ai shiyasa naga dazu kin lake daki kina waya" ta fada batare da ta juyo ba shiru nayi da bakina gudun in ballowa kaina ruwa
Soyayyar lawal ce ta kawo rashin jituwa tsakani na da hafsat domin kullum kokarin nunamin aibun lawal take ni kuma banaso ita kuma taki fahimta wannan yasa na fara ja baya da ita
itama sai tayi fushi ta daina kulani ni kuma ban wani damuba saboda lawal ya zamemin madadinta domin ya siye babbar waya a 'yar sana'ar da ya fara da kudin da nabashi yace akwai haske sosai samuwar wayar sai muka kara dinkewa da rana muna tare a makaranta da dare muna makale a waya
Abinda na kasa tsayawa in tantance shin wace sana'a ce yakeyi da kullum muna tare kuma bai taba gayamin abinda yake siyarwa ba nima bantaba yunkurin sake tambayarshi ba saboda a ranar da na tambayeshi fushi yayi tare da cewa saboda yana kudina nake tambaya shiyasa tun farko baiso karba ba
Kwatsam yaya Abbas ya dawo daga tafiyar da sukayi washe gari ya shiga makaranta kuma a daren ranar maganar lawal ta dira kunnen iyayena da kuma yayyena
Jin muryar ya abbas yana kwallamin kira cikin hargagi yasa hankalina ya tashi duk da yanada fada amma hakan bai taba faruwa tsakaninmu ba agogo na kalla karfe 9:07 irin wannan lokacin kowannensu yana bangarenshi to me kuma ya kawo su uzuri na bawa lawal da muke waya kan zanje in dawo a tsorace na fito
Ya Abbas ne a tsaye jikinshi har tsuma yake sai abba dake zaune da ummi da kai duka ma mutanen gidan ke har anty halima isa nayi gabanshi na durkusa saboda yanda naji kafafuna sun fara rawa tun daga kan irin kallon da yakemin dakyar nasamu kwarin guiwar furta " gani yaya"
" ka zauna abbas sannan kuyi magana" abba ya umurceshi sanin halinshi ko wane lokaci zai iya rufeni da duka ajiyar zuciya ya shiga saukewa sannan ya watsomin idanunshi masu firgita mai kunnen kashi irin nawa " me kika ce mana zakije kiyi a makaranta ?" ya watsomin tambaya tareda tsareni da idanunshi saina samu kaina da rashin gane inda zancenshi ya dosa saida ya dakamin tsawa " dake nake magana nace me kika ce zakije kiyi a makaranta " cikin rawar jiki na amsa ina kara matsawa baya " Karatu"
" to da kikaje karatun kikayi" nanma shiru nayi "wallahi idan na sake maimaita miki magana saina sauyamiki fatar fuskarki da mari " karatun......na...yi" na fada a rarrabe " wayarshi ya janyo tareda budewa ya dagota yana nuna min " waye wannan" kaina na daga tsuwwwwwww cikina ya shiga wani kalar kida kamar an kunna disko " na shiga uku tawa ta kare" na fada a raina taya zan cewa yaya nasanshi ai kasheni kawai zaiyi " idan kika sake kikamin karya wallahi sai na karya miki hannu zainab" ya tare numfashi na daga karyar dana kammala shiyawa a raina
Hannuwana na hade guri daya "don Allah kayi hakuri yaya wallahi bazan sake ba"
" ka mata a hankali Abbas" yaya isma'il ya fada matsowa yayi yana kallona "meye alakarki da shi? ki fada karkimin karya" Kallon ummi nayi da ta zubamin ido tana kallona kallon mamaki da kuma tsoro " wai sona yake yaya" na fada cikin sakalci " sonki yake kuma bazai zo gidanku yayi magana da ke ba saidai makaranta zainab? wannan wane irin sone kenan ba karatun kike ba ko" kaina na girgiza hawaye na min zuba " Wallahi inayi yaya"
Mikewa ummi tayi tabar falon abinda ya kara tayarmin da hankali hakama ya abbas sai yaya isma'il da ya tsaya yimin nasiha tareda nunamin kuskurena da kuma yimin jan kunne kan kar in kara in rabuda wannan mutumin saboda duk wanda bazai zo gidanku nemanka ba to ba kaunarka yake ba karin tashin hankalina abba ma baice komai ba
Kuka na dingayiwa anty halima da muka koma daki tareda rokonta ta tayani neman gafarar su ummi itama nasiha ta shiga yimin tareda nunamin kuskurena muna cikin maganar lawal ya kirani wani haushinshi naji saboda yanda ta silarshi iyayena suka shiga damuwa kin dagawa nayi da naga ya isheni da kira na kashe wayar gabadaya
RUMAISA SIDI✍️✍️✍️✍️✍️✍️
Shin an rabu kenan ko ana nan tare🤔
AURE DA KARATU
NA
RUMAISA'U SIDI
Page 11
Washe gari anty halima ta jagoran ce ni wurin ummi na ba ta hakuri haka ma abbana dukansu nasiha su ka min tare da nuna min kuskuren abinda na aikata duk na ji na tsani kaina da wannan damuwar da na jefa su har na isa makaranta ba lakka a jikina kuma har lokacin ban kunna waya ta ba ban iya tuƙa kaina ba ranar saidai driver ne ya kaini
Inda na hango hafsat can na nufa sallama na ma ta kallona ta yi sannan ta amsa "lafiya na ganku a waje na ɗauka ma an shiga lecture" na tambaye ta ganin lokacin lecture ɗin ya kama "kinsan halin malamin wataƙila ma bazai zo ba" gefenta na zauna "ai ko da bai kyauta mi ni ba wallahi ko lafiya banji a jikina amma haka na zo saboda sanin rashin mutuncinshi" sannu ta shiga min tare da tayin soyayyar farar da take ci "girgiza kaina na yi ina ya mutsa fuskata "ke kam hafsa Allah ya shiyaki da shegen kwaɗayi wallahi" lumshe idanuwa ta yi tare da buɗe ido ɗaya "bakisan daɗi bane malama fara ai ita ce kazar talaka" duk da yanda nake jin zuciyata amma hakan bai hana ni darawa ba kamar wadda ta tuna wani abu ta ɗan dubeni "na manta kinyi baƙo yace ki same shi inda ku ka saba haɗuwa" daga haka ta kulle bakinta gam tunani na shiga yi a raina naje ko kar naje daga ƙarshe na yanke shawarar zuwa domin na dakatar da shi da zuwa gurina don banason abinda zai haɗani da iyayena
Tun daga nesa na hango shi ya na kaiwa da komowa a wurin da ya zama kamar mallakinmu a makarantar har na kusa isa wurinshi baisan na iso ba sallamar da na mishi da ƙarfi ya waigo tare da yi cikina kamar wanda zai riƙe ni ajiyar zuciya ya shiga saukewa kamar wanda yayi tsere "nagode Allah ba abinda ya same ki" wani tausayinshi ne ya shiga tsargamin a zuciya wurin zama na nuna mishi a sanyaye na ce "ka zauna muyi magana don Allah" zama yayi kamar yanda na ce nima na zauna na ɗau mintuna ina tunanin ta inda zan fara "me ya faru my zee? ko bakida lafiya?" kaina na girgiza mishi sannan na yi ƙundunbala na fara magana "kayi hakuri soyayyar mu ba za ta yuba" tsaye ya miƙe yana kallona kamar mai in-ina ya fara magana" Ba bangane me...ki ke cewa ba"
Kallonshi na yi da idanuwa na da suka cika da ƙwalla hannuwana na haɗe guri ɗaya "don Allah kayi hakuri abinda zan iya cema kenan" daga haka na miƙe tare da ƙoƙarin barin makarantar ma gaba ɗaya maganar shi ta dakatar da ni "dama an gayamin hakan za ta faru a tsakaninmu amma na ƙi yarda kinsan ba za mu ci gaba da soyayya ba meyasa ki ka sabamin da soyayyarki meyasa za ki min hakan laifin mi zuciyata ta miki da ta cancanci wannan hukuncin daga gareki? saboda kawai na so ki? ko don ina talaka?" kuka na fashe da shi tare da durƙushewa a gurin na kasa bazan iya ba lawal rayuwata ne wallahi bazan iya ba shima hawaye ya ke gabana ya duƙa ya na kallona "kiyi hakuri zainab ki gayamin abinda ke faruwa" kamar sakarya na kwashe komai na gayamishi "ki kwantar da hankalinki insha Allah wannan bazai zamo sanadin rabuwar mu ba kinji ki kwantar da hankalinki"
In taƙaice miki lawal bai bar makarantar ba saida ya tsaramin kalaman da suka saka naji bazan taɓa iya rabuwa da shi ba daga ranar kuma mu ka canja wurin haɗuwa saboda gudun ya abbas ya ganmu a makarantar ashe ba haka kawai ya abbas ya sakeni ba yana lura da kowane motsina ranar da ya damƙoni a wurin da muka haɗu da lawal ranar yamin dukan da bantaɓa tunaniba ba kukan dukan da yakemin nake ga a'a kukan rashin sanin halinda lawal ya ke ciki nake saboda tun a can ya damƙashi ga ƴan sanda ga kuma ummi da naga hawayenta na zuba nasan duk saboda ni ne
Faruwar wannan abba ya dakatar da ni daga zuwa makaranta ya kuma karɓe wayata bansan yanda aka yi ba ranar sai ga lawal a gidanmu nidai na yi mamakin daga abba har ya isma'il ba wanda ya fita har wata rama na yi saboda tashin hankalin da nake ciki kowa ya janyemin a gurin anty halima kawai na ke samun sauƙi bansan wucewar lawal ba saida abba ya aiko a kirani
Dukansu suna nan falon abba har ummi gabansu na je na duƙa tare da gaishe su kamar kullum ba wanda ya amsamin idanuwana da suka bushe kan kuka na lumshe abba ne ya fara magana "Allah ya sa ni tun tasowar ki da kuma shaƙuwar da ke tsakanin ku na kwaɗaitu na haɗaku aure ke da yayanki bashir to amma na fahimci hakan bazai sa mu ba saboda wasu sababbin halaye da kika tsiro da su a ƴan watannin nan bazan so haɗin aurenku ya zama silar taɓuwar zumuncin mu ni da 6ar uwa ta ba" Numfasawa yayi alamar abin bai mishi daɗi ba"Na kira wanda kike so munyi magana da shi ya je ya shiryo ko gobe ya tashi ya zo a ɗaura mu ku aure"
Wata irin zabura na yi kuka na ƙwacemin "Aure kuma abba wallahi ni ba yanzu zanyi aure ba don Allah ka yi hakuri" ɓallina ya abbas yayi da ƙafarshi da ke kusa dani "za ki mana shiru ko sai na make ki ai duk hukuncin da aka miki ke kika ja" sannan ya dubi abba "Abba aura ma ta shi damuwa ce a rayuwarta na gayama nayi bincike kan yaronnan bayada wata sana'a sannan mahaifinshi ya rasu shi kaɗaine namiji a taƙaice ma har yanzu gidansu ake ciyadda shi saboda bayada hakuri duk inda yaje" hannu abba ya ɗaga mishi "haka ta ke son abinta abbas damuwa ba ta wuce na zuba musu ido suna zaɓar wurin da su ke son haɗuwa ba wata rana zanga abinda bama fata shi arziki na Allah ne indai tana son mijinta duk halinda ta tsinci kanta za ta jure"
Ayi haƙuri da wannan
AURE DA KARATU
NA
RUMAISA'U SIDI
Page 12
Tun daga faruwar wannan karatuna ya tsaya na daina zuwa makaranta ke ba makaranta kaɗai ba duk wata fita abba ya dakatar da ni daga yinta a kuma lokacinne yaya bashir ya fito da ƙudirinshi a kaina a lokacin ya diro sokoto da ƙoƙon barar neman soyayyata kai tsaye na bayyana mishi ina da wanda nake so faɗar tashin hankalin da ya shiga ɓata bakine
A wannan lokacinne kuma ummi ta magantu tun fara magana ta da lawal ɗakinta ta ja ni" kiji tsoron Allah zainab bashir bai cancanci hakan daga gare ki ba ko kina so kice tun baya bakisan ya na sonki ba?" nuna ni tayi sannan ta cigaba da magana "zainab zainab ki tsaida hankalinki wuri ɗaya kar soyayyar zamaninnan ta ruɗe ki zainab ki tsaya ki dubi wanda ya dace da ke kina ganin yanda kika ɗaga mana hankali ki dubi yayunki haba zainabu kiyiwa kanki faɗa ko don idon halima da kullum ke ƙoƙarin kare ki ya zataji kin fito fili kin nuna bakya ƙaunar ɗan uwanta ga gwaggonki da ke nuna miki ƙauna kina tunanin za ta ji daɗi kin nuna bakya ƙaunar ɗanta? shin wai ni da me wannan lawal ɗin ya fi bashir?" ban magantu ba don bansan me zance ba ƙwaƙwalwata ta toshe
Kusan kowa a gidanmu saida ya zaunadda ni ya bani shawara amma zuciyata ta ka sa laraya daga ƙaunar lawal in taƙaice miki a ƙarshen watannan lawal ya gayamin zai turo magabatanshi saboda shima hankalinshi ya tashi sosai ya na tsoron ya rasa ni a ƙarshen watan ya turo kuma aka saka biki sati huɗu sanin halin da ya ke ciki ya sa na tura mishi kuɗi masu tsoka ta account ɗinshi ya ƙara ya kama gida
Ana saura sati ɗaya biki abbana ya kira lawal bansan abinda su ka tattauna ba sai daga baya nakejin gida ya bashi da mota da kuma kayan fitar biki nima ya min faɗin murnar da na yi ɓata bakine ganin kamar abba ya fara saukowa a auren
Daren da za'a miƙa ni gidan lawal abba yamin nasihar da ta sakani kuka sosai da sosai "Alhamdulillah Alhamdulillah ina ƙara godiya ga Allah da ya nuna min wannan ranar da zan miƙa ki gidan mijinki kuma zaɓinki ina fata idan kin shiga sai mutuwa ina bqki shawara da ki kasance mai biyayya ga mijinki duk abinda ya umurce ki matsawar bai ta ka shari'a ba to ki mishi ki nuna mishi mun baki tarbiyya domin rashin misi biyayya kamar tozarta mu ne ina mai gargaɗinki da ki kasance mai haƙuri don ina so ki sa ni bazan ɗauki shashanci ba ke kika kawo min shi kina so don haka zaɓinki na baki ban miki dole na baki zaɓina ba duk da ina da ikon hakan ina miki kyakkyawar fata a rayuwar aurenki Allah ya miki albarka ya baki zuri'a ɗayyiba
Kallon maman haidar na yi da ta zubamin ido kamar ta samu tv sannan na dubi agogo zabura nayi "Wai kinga har ƙarfe ɗaya da mintuna nasan duk inda su ke suna hanya kuma ban girka mu su komai ba" ajiyar zuciya ta sauke "wallahi maman safwan na ƙagu inji irin halaccin da abban safwan zai saka miki da shi ji nake kamar mu kwana muna labarinnan don ko a littafi ban taɓa jin wadda tayiwa namiji irin halaccin da kika mishi ba" murmushi na ma ta "to sai kiyi haƙuri har wani lokaci" da sauri tace "gobe zan dawo" kallonta nayi a raina nace "matar nan taji gulma" a fili kuma na ce" gobe makaranta zan shiga saidai jibi"
Na rakota tsakar gidan muna salllama sai ga motata ta shigo alamun yaran sun dawo buɗe motar sukayi kowa na rige-rigen isowa wurina " mommy ta warke" aysha ta faɗa tana ƙara ƙanƙameni a jikinta kanta na shafa "na warke da yardar Allah indo na ya makarantar ku shiga ciki gani nan shigowa" da gudu suka shige kallona na mayar kan oga lawal da ya dunƙule hannuwanshi yana jefomin wani kallo mai haɗe da murmushinnan nashi da na raɗawa na yaudara "naji daɗin yanda na dawo na same ki my zee ni sai naga ma kamar fitar nan da nayi har wani fari kika ƙara"
Nuna mishi maman haidar nayi da ke tare da mu ganin kamar baignta ba zabura yayi kamar gaske yana sosa kanshi da key ɗin da ke hannunshi "Ahhh sannu maman haidar yau ziyara aka kawo mana anzo duba jikin madam"cikin mutunci su ka gaisa ta mini sallama tare da ƙara jaddadamin sai ta zo
Ban yi girki ba ranar saboda abincin da lawal ya zo mana da shi mai rai da lafiya har da lemu ya siya mana aiko ranar mun raƙashe domin lawal ya canja sosai daga yanda muka sanshi nikam har yanzu ban aminta da wannan sauyin ba sam da dare ma da yaran suka yi bacci shi ya ɗauke su ya kaisu ɗakinsu
To mu ma bari muje mu kwanta
AURE DA KARATU
NA
RUMAISA'U SIDI
Page 13
Sati ɗaya mukayi muna zaman mutunci da lawal hatta abinci yanzu a gidan ya ke ci duk da bashi ya siya ba a washe gari bayan yara sun wuce makaranta ni kuma ina gidan don banida lecture lawal ya sameni a ɗaki ina shirya kayana da aka kawomin daga wanki waigowa nayi na dubeshi ya tako har inda nake ya sami kujerar dake gaban mirrow na ya zauna yana fuskanta ta
"Yadai abban safwan" na faɗa ganin kamar akwai magana a bakinshi ajiyar zuciya ya sauke sannan ya kafamin idanunshi "magana nakeso mu yi dake zainab"aje aikin da nakeyi nayi na dubeshi ganin maganar mai muhimmanci ce "nasan kaso 70 na lalurorinki da na yara