Showing 57001 words to 57484 words out of 57484 words
ba shi kaɗai ke zaluntar ta ba ita ma tana zaluntar shi ko don ni bana magana.To wallahi ba zan ɗauka ba,idan ma kina son ki tunatar da ni ke kika haifi Sadiq to ki kwantar da hankalinki na sani kuma ban manta ba"daga haka ta bar ɗakin.
Dariya muka sha ni da Ya Bashir bayan wucewarta,yadda Zubaida ke damuwa da sha'anin Sadiq ko kanta bata damuwa da shi haka.
Koda na fita sai da na shiga na bata haƙuri ba kunya ta amshe tare da faɗa min ya wuce.Allah ya gani ina jin daɗin ƙaunar da Zubaida ir nunawa Sadiq,saboda duk wanda yace yana son abinka kamar kai yake so,kuma inda hankali na ke kwanciya bata nuna mishi saken da zai sa ya lalace,idan yayi ba daidai ba tsaf zata zane shi ko ta mishi faɗa amma idan mu muka dake shi to yanzu za a ji bakinta.
Bayan kwana biyu Zubaida ta haihu ta haifi ƴarta mace kyakkyawa.Munsha bidirin sunan Khadijah takwarar Gwaggo.
A hankali gidan mu ya cika da ƴaƴa,Gwaggo ta tara jikoki Ya Bashir ya tara zuri'a,Zee aka samu ƙanne,idan kaji gidan tayi shiru to tabbata sun tafi makaranta.
Idan na gaji ɓangaren Zubaida nake turasu,da zarar an fara taɓa ɗan lelenta yanzu zata kaɗomun nawa ta riƙe nata.
Idan na kalli ƴaƴana sai dai na ƙara hamdala saboda na san ni'ima ce,ace duk waƴannan ƴaƴan nawa ne mallaki na ne.A wannan gaɓar ba abin da zance sai dai nace *ALHAMDULILLAH.*
Nima anan zan ce *ALHAMDULILLAH*
Ina roƙon Allah yasa wannan littafin ya amfani jama'a da dama.Ina kuma bawa makaranta wannan littafin shawara da suyi ƙoƙarin yin amfani da kyawawan abubuwan da ke ciki,su kuma yi watsi da munana.
Ina fata abinda na faɗa daidai Allah ya bani lada,ku ma masu karatu Allah ya baku.
Inda na yi kuskure kuma Allah ya gafarta min ya kuma gafarta wa masu karatu.
Allah ya gafartawa mahaifina da duk waƴanda suka riga mu gidan gaskiya.
Allah ka ƙara wa mahaifiyata lafiya da nisan kwana.
Allah ya ƙara muna zaman lafiya a jihohin mu da ƙasar mu baki ɗaya.
Allah ka kawo muna ɗauki ga waƴannan musibun,ka magance muna abin da bamu da ƙarfi ko iko akan shi.
Allah ka fi mu sanin abin da yake daidai, Allah ka gyara muna ƙasar mu.
Allah ka yafe muna kurakuran mu,ka kuma ƙara hore muna abin da zamu yi lalurorin mu.
Allah ka shirya muna zuri'ar mu,ka kare su da miyagun ƙaddarori.Ƴan mata da samari masu buƙatar aure,Allah ka aurar da su.
Matan auren da ke cikin matsala a gidajen auren su, Allah ka yaye musu.Waɗan da ke cikin wadata da farin ciki Allah ka ƙara musu.
Daga ƙarshe ina miƙa dubun godiyata ga makaranta wannan littafin da suka yi jimirin biyo ni tun daga farkon littafin har zuwa yau.Suka kuma ci gaba da bani goyon baya,ta hanyar nuna jin daɗin su da yin comment da sharing wannan littafin a mabanbantan groups,Ina godiya sosai da kuma fatan zaku biyo ni a littafina na gaba.
*NAGODE*🙏🙏🙏
*RUMAISA'U SIDI✍️✍️✍️*
*08104445106*