Showing 39001 words to 42000 words out of 57484 words

Chapter 14 - AURE DA KARATU Book Complete Rumaisa Sidi.txt

26 Jan 2025

6687

AURE DA KARATU
NA


RUMAISA'U SIDI

FARAR ANIYA WRITERS



Page 29




BASHIR




A matuƙar gajiye ya isa garin Kaduna,cikin kasala ya fito daga motar tare da rufeta,sanin ya baro Mahaifiyarshi a can yasa kai tsaye ya tunkari ɓangaren Mahaifinshi da ya dawo tun jiya bayan gama ɗaurin Aure.




Cikin matuƙar girmamawa ya gaidashi,ya amsa yana tambayarshi hanya da kuma mutanen Sokoto.




Ya doshi ƙofar fita maganar Abba ta dakatar da shi "Idan ka huta kazo akwai maganar da na ke so muyi" duƙadda kanshi yayi sannan yace "To Abba" daga nan kuma ya fito tare da wucewa ɓangarenshi.




Tunda ya isa ƙofar shiga ya fahimci ba kowa a gidan,gabanshi ne ya faɗi ganin yadda falon ya koma kamar inda aka yi yaƙi.




Komai an canja mishi mazauni,hatta da kujerun falon sun tabbata anyi yaƙi a ciki,hotunansu da ke manne akan bangon falon suma duk an sauko da su,ga komai nan a harmutse.




Raɓawa yayi ya shiga tare da tunkarar ɗakinshi don ya san wannan haukar ba iya nan ta tsaya ba "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un"ya faɗa tare da dafe goshinshi ganin irin ta'asar da ta mishi a ɗaki.




Kamar dai waccan rana,yau ma duk wata sutura tashi ta fitar da ita,takardunshi ma gasu a watse a tsakiyar ɗakin.Saurin matsawa yayi ganin ledar da sababbin kayanshi na angonci suke ciki,shekaran jiya ya karɓo su ya na sauri bai tsaya jerasu a wadrobe ba ya nufi Sokoto.




Ɗaga wandon Shaddarshi mai tsada yayi yana kallon yadda Zubaida ta maida wandon three-quater kamar na ɗan yaro,rigar wani yadin ya ɗauko yana kallo ita kuma an rabata biyu an maida rigar kamar wata vest.(Kai Zubaida baki da kirki)




Ajiyar zuciya ya sauke bayan ya kalli scissors ɗin da ta yada a ƙasa bayan ta ƙare wannan aiki.Raɓawa yayi gefen gadon ya zauna tare a dafe kanshi da yake jin kamar zai cire.




Me ke damun Zubaida?Yanzu haukar tata har ta kai ta wulaƙanta sutura? Ko kuma shima wannan kishi ne?




Daƙyar ya samu yayi wanka bayan ya wanke toilet ɗin saboda yadda yake ƙazantar komai na ɗakin sakamakon wannan haukar da ke ciki.Kuma shi sam baya jin zai iya gyaran wannan gidan.




Ko da ya fito bai damu da shiga ɗakinta ba,ɓangaren ya bari bayan ya kulleshi sannan ya tunkari masallaci jin an fara kiran sallar Magrib,sai da yayi Isha sannan ya wuce ya siyo abinci.




Bayan ya dawo ɓangaren Mahaifinshi ya koma ya samu shima ya dawo.Wuri ya samu ƙasan carpet ɗin ɗakin ya zauna




"Na san ka dawo ka samu matarka bata nan ai ko?" Ya tambaya yana tsare Bashir ɗin da ido"Eh Abba" ya amsa yana ɗaga kanshi.




"Jiya bayan na dawo na samu Yayarta tazo sunyi ɓarna a gidan,raina ya ɓaci sosai kuma na musu faɗa daga ita har Amina"




Ashe bayan na shigo,janta tayi suka bar gidan,banji daɗi ba sam,abin bai min daɗi ba,abin haushin kuma sai ga Hussaina ta kirani tana faɗa min abin da sam banji daɗin shi ba.Abin da kawai zan faɗa ma shine,gobe kaje ka dawo da matarka,kuma ka ci gaba da haƙuri,ka san halin mata musamman akan kishi,sannan kuma kaji tsoron Allah ka yi adalci a tsakaninsu,kar ka dubi Zainab zaɓin ka ce ita kuma Zubaida ni na tilastama aurenta ka yi amfani da hakan ka wulaƙantata,ba zan ɗau wannan shashancin ba idan kuma har kayi wannan gangancin ka sani bazan ƙyaleka ba"




Kanshi ya ƙara sunkuyarwa "In sha Allah Abba,na gode sosai"Zaman shi ya gyara sannan yace "Abba don Allah key ɗin ɓangaren Mama na ke so ka bani,saboda ba zan iya zama a wancan ɓangaren ba,na kira masu gyara da safe za su zo su gyara"




Tsakiyar falon yayi tsaye bayan ya kunna wutar falon,ba wani datti komai tsaf-tsaf ga wani ƙamshi na musamman da ke tashi.Ɗakin da yaga Zainab ta zauna lokacin da tazo ya nufa tare da tura ƙofar ɗakin.




Idanunshi ya lumshe bayan ya shaƙi ƙamshin ɗakin,dagaske ƙamshin turaren Zainab ya ke ji,yana masifar son wannan ƙamshin,yana ɗaya daga cikin abin da ya ƙara janshi ga Zainab saboda tsaftar ta da kuma ƙamshinta.




Wayarshi ya jawo tare da lalubo Number ta bayan ya kwanta akan gadon,bugu biyu ta ɗaga




"Haka mace ta gari ke yiwa mijinta,bayan ya bar gari yana hanyar tafiya?" ya faɗa bayan ya amsa sallamar da ta mishi




Shiru tayi sanin batada gaskiya "Kayi haƙuri,muna exam ne kuma koda na fito ban samu na kira ba,sannan da na dawo gida ma......."






"Shikenan ya wuce,amma dai idan nayi tafiya a riƙa kulawa da ni" ya katseni daga jerin kumbun da na faro mara dalili




"Ka isa lafiya?Ina takwarata?"




"Lafiya lau na isa,takwarar ki ma tana lafiya,Ina su Amna? Ko Safwan ɗin ya koma?




"A'a gasunan duk lafiya lau suke"na faɗa ina kallonsu Safwan da ke game a system ɗina.






Fira muka ci gaba da yi daga ƙarshe yace in kaiwa Gwaggo wayar yana masallaci sun yi magana amma bayan ya fito ya kira yaji wayar kashe.




A falo na samesu na vata wayar tare da shaida mata Ya Bashir ne,sannan na bar falon ina hararar Anty Halima da ke ƙifta min ido.




LAWAL


Ba ƙaramar jarumta yayi ba wurin hana kukan da ke taso mishi bayyana.Wai yau shine a tsaye a gaban Zainab yana taya ta murnar Aure da wani,yau a gabanshi wani ke nuna ikon shi a kanta,a gabanshi ta zaɓi bin umurnin wani.




Daƙyar ya kai kanshi gidan Mama bayan mai mashin ya aje shi a bakin titi,kamar ɗan maye haka ya shiga gidan yana layi.




"Subhanallahi Lawwali lafiya"? Mama ta faɗa tana miƙewa daga gawayin da take hurawa ganin yadda ya shigo gidan kamar wanda baya hayyacin shi.




Cikin sauri ta shimfiɗa mishi tabarma tare da jawo hannunshi ta zaunar da shi,ruwa ta ɗebo masu sanyi ta bashi tace yasha.Ba yada zaɓin da yafi ya buɗe baki ya sha ruwan,shan ruwan ya ke da fatan zuciyar shi ta sanyaya daga zafin da take mishi.




Wani irin yunƙuri yayi,da sauri ya sauka daga kan tabarmar ya shiga kelaya amai kamar zai amaye hanjinshi,ba komai a cikinshi bayan ruwan da ya sha yanzu,rabon shi da cin abincin kirki tun da yaji auren Zainab,yau ma ko ruwan shayin da ya ke sha bai sha ba,Safwan kawai ya haɗawa.




"Innalillahi ba ka da lafiya?bari in ɗakko hijabi hijabi muje asibiti" ta faɗa tana zuba mishi ruwa yana kuskure bakinshi.Komawa yayi ya kwanta tare da lumshe idanuwanshi yana jin yadda bugun zuciyar shi ke canjawa.






Fitowa Mama ta yi da hijabi a hannunta"Bari in kira Yayarka ta same mu a asibiti" ta faɗa tana lalubo Number Anty A'i"




Idanuwanshi ya buɗe tare da ƙoƙarin tashi zaune "Kar ki kira ta Mama,maganin damuwata ba a asibiti yake ba Mama,Allah ne kaɗai zai yaye mini abin da ke damuna"




Zama tayi gefenshi tana kallonshi "Subhanallahi,damuwa kuma Lawwali? Ko jarin kayan miyan ne ya karye?" ta faɗa tana tsareshi da ido.




"Zuciyata ce ta karye ba jarina ba Mama,Mama yau aka ɗaurawa Zainab aure,yau a gabana wani ke nuna ikonshi akan Zainab Mama,shikenan na rasa Zainab Mama,wani ya ɗauke abin da ni na kasa sanin muhimmancin shi sai da yayi nesa da ni Mama,ya zan yi? Ki faɗa min ya zanyi Mama?" ya ƙarasa yana ɓarkewa da kuka tare da kife kanshi ƙasan tabarmar.




Hannu tasa ta ɗauke hawayen da suka sakko mata na tausayin ɗan nata,ta daɗe tana gudar mishi irin wannan rana amma ya kasa fahimta,ta daɗe ta na nuna mishi muhimmancin Zainab amma yaƙi ganewa.




Ba Lawal ba ita kanta lokacin da taje labarin auren ta taya Lawal jimamin rashin Zainab,saboda bata tunanin akwai sakaran namiji irin Lawal da zai same kamar Zainab yayi sakacin da za ta suɓuce mishi.




Hannunshi ta riƙo cikin wani irin tausayi da ke tsakanin uwa da ɗanta cikin matuƙar raunin murya take faɗin "Kayi haƙuri Lawwali,dole ka yi kuka,kayi rashin mata ta gari,shi nake nuna ma tun farko amma ka kasa fahimta,ina roƙon kaima Allah ya baka mata ta gari kamar Zainab ɗin"




"Babu ta,wallahi Mama babu kamar Zainab,ba wadda za ta soni kamar Zainab,ba wadda zata tausaya min kamar ita,kuɗi,kuɗifa take bani Mama,wallahi kuɗinta ta ke bani nayi jari,har zinarenta fa ta bani Mama.Wallahi ba macen da zata iya yi min abin da ta min"




Ko da yaje kwanciya kasa bacci yayi,hatta abincin da Mama ta zubo mishi tace ya ƙara ci idan yazo, kasa ci yayi,wata irin nadama ya ke yi,na yadda rayuwar shi ta kasance a baya.Gashi baƙar zuciyar shi ta janyo mishi asara da yawa.




Na farko ya kasa tsayawa ya nema da ƙarfinshi,yana ganin duk sana'ar da zai kasa a kasuwa azo a siya ɓata lokacine wanda ya wahaladda shi sosai.




Sannan wannan yayi silar mutuwar aurenshi da Zainab,macen da ta taimaka mishi,ta kuma rufa mishi asiriasiri,a silar ta ya mallaki gidan da yake zaune a yanzu,a silar ta ya samu motar hawa,kai a silarta ya samu komai ma.




Wannan halin da ya ke ciki na rashin sana'a yasa ya rasa ƴarsa,abar sonshi,wadda bai shaƙu da su ba,sai bayan tafiyar mahaifiyar su.




Yau gashi ya rasa Zainab,yana kallo wani ya ɗauketa,ta mishi nisa.






Nagode sosai da Addu'o'in ku kuma na samu sauƙi Alhamdulillah




RUMAISA'U SIDI








AURE DA KARATU


NA


RUMAISA'U SIDI


FARAR ANIYA WRITERS




Page 30




Washe gari sai bayan ya taso aiki sannan ya tunkari gidansu kamae yadda mahaifinshi ya jaddada mishi ko yau da zai fito.




Ba ya jin zai ƙyaleta wannan karon taci bulus,dole ya nuna mata shima namijine ba wai tsoronta ya ke ba da yake ƙyaleta saboda ya lura haukarta sam batasan Allah ba.




A bakin tangamemen get ɗin gidan ya shiga doka horn,da gudu mai gadin ya fito tare da shiga kiciniyar buɗe get ɗin.




Cikin girmamawa ya duƙadda kanshi tare da gaidashi,amsawa yayi tare da ɗebo kuɗi ya damƙa a hannunshi.




Amsa mai gadin yayi yana ta murna,Allah ya gani yana matuƙar ƙaunar zuwan bawan Allah nan saboda kyautatawar da ya ke mishi,lokuta da dama a zuciyarshi yana mamakin yadda Bashir ke zaune da Zubaida saboda sam batada kirki,halayensu sun banbanta.




Sallama ya shiga dokawa a ƙofar falon amma shiru ba amsa,duk da daga inda yake yana hango yayar Zubaida wato Amina da kuma mahaifiyarsu.




"Wai kai baƙone da sai an amsama sallama zaka shigo" Mahaifiyar zubaida da suke kira Anty ta faɗa cikin tsawa




Shigowa falon yayi tare da duƙawa gabanta "Barka da yau Mama,na same ku lafiya"
"Lafiya"ta faɗa tare da ɗauke kanta




Shiru falon ya ɗauka kamar ba kowa sai shine ya gaji da zaman ya magantu "Mama na zo tafiya da Zubaida ne"




Wani kallon wulaƙanci ta bishi da shi "Saboda Zubaidar ƴar roba ce ko? Ko an gaya ma na gaji da ita ne? To ban gaji ba,har yanzu ina ƙaunar ƴata kamar yadda uwarka Dije ke ƙaunarka.Wallahi Bashir Zubaida tafi ƙarfin wulaƙanci a wurinka,duk rashin mutuncin da kuke shiryawa kaida Uwarka ba wanda bansani ba,to wallahi ba zan ɗauka ba ehe,dole ka zaɓa ko Zubaida ko ƴar Dije don ƴata bazata yi kishi da zuri'ar Dije ba wallahi"




Daga haka ta miƙe tare da nufar ɗakinta,dakatawa tayi tare da dafa ƙarfen matattakalar "Na baka yau zuwa jibi,kaje kayi tunanu kuma ka zaɓa tsakanin ƴar uwarka ko ƴar uwar Dije"daga haka ta haye sama.




Miƙewa yayi tare da ƙoƙarin barin ɗakin,ranshi ya ɓaci matuƙa,ba yau ta fara zagin mahaifiyarshi a gabanshi ba duk lokacin da zasu haɗu sai tayi haka.Ya rasa me Mama ta tare mata da kullum bata faɗar alkhairi a kanta.




Yana ƙoƙarin buɗe motarshi ya shiga motar gidan ta shigo tare da yin parking,da mamaki yake kallonta tana janye da hannun Zainab,itama kallonshi ta ke kamar taga baƙuwar halitta.




Fasa buɗe motar yayi ya tsaya yana kallonta "Yanzu haukar taki har ta kai matakin da zaki fita bada izini na ba?" ya faɗa cikin matuƙar ɓacin rai tare da shafa kan Zainab da ta zo da sauri ta rungume shi.




Ɗaure fuskarta tayi "To ai yaji nayi don haka ba ƙarƙashin ikon ka nake ba"ta faɗa cike da sakalci.




Duƙawa yayi tare da ɗaukar Zainab "Zan je da ƴata,duk lokacin da kika yi ra'ayi kya iya biyo mu daga baya"




Ƙoƙarin sauko da Zainab take daga jikinshi "Ni ba inda zanje,in har kana son in koma sai dai ka saki waccan bawarar don bazan iya zama da ita ba"




Motar ya buɗe ya saka Zainab sannan ya dubi Zubaida "Ki zauna kina hauka,bazawarar da kike faɗi tazo ta kula miki da miji harma da ƴarki tunda kin maida kanki sakarya"daga haka ya shige motar yaja ya bar gidan.




ZAINAB




Saida gwaggo ta ƙara kwana biyu sannan ta wuce.A cikin gidan aka kawo.Amaryar Ya Mubarak tanada kirki sosai kamar su Anty Nasma.




Anty Halima ko kusan kullum sai tazo gidan da sunan wai shirye-shiryen tarewata,nidai sai dai kawai nayi dariya don nasan yawonta ne kawai ke cizonta.




Ita ta haɗani da wata mai gyaran jiki da kuma kayan ƙamshi wadda zan riƙa zuwa wurinta ana min,ba dan naso ba nake zuwa cikin kwana biyu sai gani na fara wani irin kyau na musamman ga ƙamshi duk inda na zauna sai na bar wannan ƙamshin.




Yau ma daga makaranta can na wuce kasancewar yau muka yi exam ɗin ƙarshe,sai bayan da aka ƙare gyaran jikin na maida niƙab ɗin da na tsiri sakawa tunda aka fara gyarannan.




Wayata na ɗauko na lalubo number Ya Bashir na doka mishi kira,kashewa yayi sannan ya kira kamar yadda yake min kullum.




Saita muryata nayi cikin wata ƴar shagwaɓa da na fahimci na koya a yanzu "Ya barka da aiki"




Daga cikin wayar ina jin yadda ya sauke ajiyar zuciya sannan yace "Barka dai Amaryata,ya ex da kuma shirye-shirye zuwa gidana"






Murmushi nayi ina jin kamar ana yawo da ni a sama "Komai lafiya lau,ya aikin"?na tambaya da tsantsar kulawa fahimtar hakan yana ɗaya daga cikin abin da ya ke so.




"Aiki ga yanan muna yi Dear,sai dai kewarki da nake" ya faɗa kamar wanda zai yi kuka.




Ƴar ƙaramar dariya nayi sannan nace "Ya don Allah ina son in shiga wurin Hafsat idan ba damuwa" na sako buƙatar da ta sa nayi kiran tun farko.




"Allah ya tsare hanya,amma ki tabbata kin saka niƙab da safar da na gaya miki kinji ko?"




"Zan saka Yaya,Na gode sosai"




"Na faɗa miki banson wannan Yayan ko? ko haka kika ji Zubaida na kirana?"




Ɗaure fuskata nayi "To ni miye damuwata da ita bale abin da take kiranka?" na faɗa ina jin wani ƙololo ya tokare min maƙoshi tare da kashe wayar jin dariya ma ya ke min




Sallama na yiwa matar tare da fitowa daga gidan,napep na tara na shiga sai gidan Hafsat uwar rigima




Rungumeni tayi cikin matuƙar farin ciki "Wallahi na ɗauka wasa kike da kika ce zaki shigo"harararta nayi ina cire niƙab ɗin fuskata tare da hijabin.




Sakin baki tayi tana kallona har na zauna a ɗaya daga cikin kujerun falon "Malama ya da wannan kallon?" na faɗa ina ɗage girata ɗaya ganin yadda ta zuba min idanuwa






"Wai kinga yadda kika koma Zee? Irin wannan kyaun ga wannan mayen ƙamshin,wallahi har na fara tausayin Zubaida,Allah sarki Zubaida baiwar Allah" ta ƙarasa tare da tafa hannuwanta.






Harararta na ƙarayi "Allah ya shirya ki wallahi,miye abin tausayi a Zubaida?Ita ma fa kyakkyawace ko kin manta?"




Bakinta ta taɓe "Na dai yarda farar fata ce amma daina batun kyau hajiya,kuma wallahi ko da wannan sheƙin kaɗai zaki ƙwace mijin,gaskiya Zee bakida kirki irin wannan ƙamshin ai kin gama yi musu farraqu"




Kitchen ta shiga tare da zubo min abinci da kuma kayan sanyi,zama tayi kan kujerar da ke kallon tawa,hannunta tasa ta tallabe kumatu tana kallona kamar ta samu TV.




Shareta nayi kamar ban gani ba,har yanzu Hafsat bata canja ba,tana nan da wannan sheɗanar da kuma tsiwa.




"Zee" ta kira sunana,ɗago kaina nayi na dube ta "Ya aka yi"




Marairaice fuska ta yi "Don Allah ki bar wannan ƙamshin hakan kar ki shiga haƙƙin Zubaida" filon kujerar da ke gefena na wurga mata.Dariya ta rinƙayi sannan ta gyara kwanciyarta kan kujerar.




Saida na kammala muka kwashi kayan kamar wasu yara muka kai kitchen,sai da muka dawo taja hannuna muka wuce bedroom ɗinta,turaruruka ta shiga kwasomin da kuma kayan gyaran jiki wai ni ta siyawa.




"Na gode sosai Aminiyata,kema Allah ya kawo haske a rayuwarki" na faɗa ina ƙara damƙe hannuwanta da ke cikin nawa.




Itama ƙwallarce ta cika mata ido "Amin Amin Aminiyata na gode sosai"




"Ki kwantar da hankalinki in sha Allah kema matsalarki ta kusa zuwa ƙarshe"




Hawayen da suka sauko mata ta ɗauke "Jiya nake ji ashe mahaifiyarshi na nan tana nema mishi auren ƴar wata aminiyarta har ma yaje ya ganta amma ni bai faɗa min ba" ta faɗa tana ƙara ɓarkewa da kuka.




Rungumeta nayi "Kiyi haƙuri Hafsat kowa da inda aka jarabceshi ke taki jarabawar kenan,ki kwantar da hankalinki In sha Allah kema kin kusa ganin jininki ki rabu da su duk wadda zasu aura mishi su auro ɗin,ai kowa da halinta za ta zauna bana shakka akan ki Hafsat kar ki ɗaga hankalinki don Allah"




Lallashinta na shiga yi da kalamai masu daɗi ina jin wani tausayinta na kamani.Dama daga anyi aure shekara ɗaya,biyu ba a haihuba sai ƙananun zance su fara tashi.Bale kuma Hafsat da aurensu keda shekara 5 amma ko ɓari bata taɓa yi ba.




Har dangin mijin suka fara magana,duk da bata fuskanci wata matsala daga mijinta ba amma ƴan uwanshi sune matsalarta.














RUMAISA'U SIDI














AURE DA KARATU


NA


Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login