Showing 30001 words to 33000 words out of 57484 words

Chapter 11 - AURE DA KARATU Book Complete Rumaisa Sidi.txt

26 Jan 2025

6701

kiji, wannan ya zama na ƙarshe da zaki ƙara shigewa mijina ehe,ni dama tunda naji aurenki ya mutu na san ba za ki barni na samu kwanciyar hankali da mijina ba,kin kashe aurenki nima kina nema ki kassaramin nawa,to nikam mijina yafi ƙarfinki saidai na wata don................"




"Keeeeeee......." ya daka mata tsawa yana saukowa daga matattakalar benen da zata sadaka da ɗakinshi.Nuna yi yayi




"Kin san muhimmancin ta a wurina? Kin san alaƙa ta da ita da za ki zo kina faɗa mata maganganu akan wani banzar haukanki da kike kallo a matsayin kishi"




Ƙara tubure wa ta yi kamar sabon kamu "Eh ai dama tare mata faɗa za ka yi,tun da ƙaunar ta kake yi,ƙaunar da bata ma amfanin komai ba tun da ta tsallake ta ɗauki wanin ka saida ya gama gurgunta rayuwarta za ta zo tana neman tarwatsamin farin ciki,wallahi ba zan yarda ba"




Kallon mamaki nake ma ta kishina ta ke kenan ƴarta na dire mata a kan kujera sannan na tunkari ƙofa don wannan faɗan ba nawa ba ne.




Ganin yadda Zubaida ta ke da zafin kishi akan mijinta sai na shiga ja baya da shi duk da shi sam ya ƙi fahimtar hakan,a wurina Zainab ke wuni mun saba sosai da ita duk da mahaifiyar ta bata ƙaunar hakan.




Ina kitchen muna haɗa abincin dare ya shigo "Tunda na jiyo wannan ƙamshin na san kece a kitchen ɗin" Murmushi na yi "Kenan girkina har wani ƙamshi ne da shi na musamman"




Shigowa ya ƙara yi kitchen ɗin tare da haye gefen cabinet ɗin "Ai tun kina ƴar ƙaramar ki nasan ƙamshin girkinki,kamar na Ummi haka ya ke,don haka yau bazan bar kitchen ɗinnan ba sai an kammala an zubawa ɗan almajiri" Aikina na ci gaba da yi muna ƴar hira shima ya na riƙe da wayarshi ya na latsawa.




Kamar wadda aka jefo ta shigo kitchen ɗin raba idanuwanta ta shiga yi tsakanin Ni da Shi




"Me kake yi a kitchen" ta tambaya kamar itace mijin shine matar "Laifine don kin same ni a kitchen ɗin mahaifiyata?




"Ai da can baka shigowa sai yanzu da aka shigo da kai" ta ƙarasa tana bankawa bayana harara "To kenan kema shigo da ke aka yi"




Tsaki ta yi wanda a ɗan zaman da muka yi na fahimci ɗabi'ar ta ce" Ka tashi mu je an kammala haɗa abinci" hannunta ya jawo "Yau girkin Zainab za mu ci,kiji kema ki huta da ganin laifina idan ina baki labarin yadda na ke santin girkinta"




Ba tare da na waigo ba nace "Gara dai ka je ka ci wanda aka saka da kai don wannan babu rabonka a ciki"


Hannunta ta ƙwace "Allah ya kiyaye ni,kaima kuma ba za ka ci shi ba" ta faɗa tana jawo shi kamar wata mai ƙarfi,ganin haukar ta ta fara yawa yasa ya daka mata tsawa "Wai ke a komai sai kin yi hauka?




Nan ta ke idanuwanta su ka tara ƙwalla "Ai dole kace min mahaukaciya tunda ga ƴar so a gabanka,ni kuma matar cushe ce,wallahi tun mutuwar aurenta ban ƙara samun bacci mai daɗi ba saboda nasan abin da ke tunkaro ni"




Girkina na sauke sannan na bar kitchen ɗin ita ma bayana ta biyo tana ƙara sautin kukanta kamar wata ƙaramar yarinya.




"Lafiya Zubaida"Gwaggo da ke fitowa daga bedroom ɗinta ta tambaya.Nuna ni ta yi "Tun da wannan ta zo ya canja min Mama,komai za. a mishi sai dai yace ita za ta mishi,yanzu ma abinci na haɗa mishi wai ba zai ci nawa ba na ta zai ci"




Kallon tuhuma ta mishi "Zo ku wuce,ba za ka ci min abinci ba kuje ku ci wanda kuka girka" Kaɗa su ta yi suka tafi sannan ta same ni a ɗaki ina zaune kamar mai tunani




"Kar ki damu da Zubaida har yanzu akwai sauran ƙuruciya a cikinta,kuma ban cika son saka baki a lamarin aurensu ba tunda mahaifiyar ta bata ganin laifinta idan nayi magana kuma Alhaji zai ga dan ta na ƴar ƙanwar shi yasa na ke haka, amma shi kanshi ba daɗin zama ya ke ji da ita ba.Matar da bata san ta shiga kitchen ta girkawa miji abinci ba ai muna mata ce"






Numfashi na sauke "Allah hay kyauta,bari in zubo miki abincin" Na faɗa tare da miƙewa nabar ɗakin.




Duk kishin matar shi baisa ya fasa abin da ya ke min ba,ganin ina neman haɗa rigima ya sa na fara shirin barin garin.




"Yanzu ke Zainab har kin gaji da zama kusa da ni,ko dai wani abu aka miki"




Kai na na girgiza "A'a wallahi gwaggo ni ba abin da aka min sai alkhairi,kuma na ji daɗin zama tare da ku"




"Kar ki yarda da ita Mama,kawai dai wani bazawarinta ne yayi kewar ta shi yasa ta ke son ta koma ya ganta" ya faɗa yana tsare ni da ido




Murmushi ta yi "Dagaske Zainab surukina ne ya damu?




Fuskata na rufe da tafin hannuna "A'a wallahi,ni ba wani bazawari da nake kulawa"




"Ai ko gwanda ki kula,don ba za mu zuba miki ido a hakan ba.Miji za ki fitar musha biki don haka tun yanzu a cikin masu nemanki ki darje ki fiddo ɗaya.Ko Abbas kwanaki mun yi maganar da shi yace har da wani abokinshi ke son ki"






Ajiyar zuciya na sauke "Ku ci gaba da taya mu da addu'a Gwaggo,In sha Allah zan fitar.




Ina ɗaki ina shirya kayana domin gobe da sassafe na ke son tafiya naji ƙarar wayata,Ya Bashir ne ɗagawa na yi tare da sakata hands free na ci gaba da aikina






"Wai dagaske tafiya za ki yi Zeen Abba"




Wani abu na ji ya tsirga min jin sunan da ya kira ni da shi bayan tsawon lokaci,na tafi wata duniyar na ji maganar shi a kaina "Zainab" Ya kira ni kai tsaye "Na'am" na amsa cikin sanyin murya




"Zainab yanzu ma bari za ki yi in rasa ki?




Ya tambaya kamar zai yi kuka "Ban gane ba" na faɗa ina dakatawa daga ƙoƙarin rufe jakar da nake yi "Kin gane komai Zainab,ba abin da baki gane ba,sai dai ina son ki sani bana jin wannan karon zan haƙura ina kallo wani namiji ya ɗauke ki.Haba Zainab ki taimaka min mana,tsawon shekarun nan ina yin su ne a cikin wani kalar yanayi"






Shiru na yi ina ƙara jin ya zama dole na yi gaggawar barin garin kafin Ya Bashir ya jawo min haukar matar shi.






"Kayi haƙuri ni yanzu ba wani aure a gabana,karatuna na ke yi,bayan haka ma ni banajin zan iya auren mai mata" Na faɗa ba wai har cikin raina hakane ba sai don ya ƙyale ni amma bai ƙyale ni ba sai da yace






"Zan zama yadda kike so,wannan ba matsala bace,za ki zauna ke kaɗai kamar yadda kike so"






A tsorace nace "A'a wallahi ban ce ba,don Allah Ya Bashir ka daina wannan maganar,ka na zaune tare da matar ka cikin kwanciyar hankali me yasa za ka ɗakko wani aure yanzu"






"Ai dama ban ce miki bama zaune da lafiya da matata ba,kuma ba don bana son ta na ke neman ki ba,kowa matsayin sa daban,sai dai ki sa ni wallahi wannan karon bazan yarda ba" daga haka ya kashe wayarshi ƙittttttt






Kaina na dafe "Na shiga uku,Ya Bashir auren dole za ka yi dani????






















*In ga ruwan comment kawai*












*RUMAISA'U SIDI*✍️✍️✍️






*AURE DA KARATU*


*NA*
*RUMAISA'U SIDI*


*FARAR ANIYA WRITERS*




*Page 24*




Gudun haɗuwa ta da shi yasa nayi sammakon shiri,koda na fito kitchen na wuce a tsaitsaye na haɗa tea na sha,ɗakin na wuce na fito da kayana.




Cikin sauri na ke komai don ban da buƙatar haɗuwar mu.Bedroom ɗin gwaggo na shiga ina faɗa mata na shirya




"Wai dagaske tafiyar nan za ki yi Zainab?




"Tafiya Zan yi Gwaggo,banson in rasa mota"




Duk saurin da nake don kar mu haɗu ban samu riba ba a tsakar gidan muka haɗu shida ƴar lelenshi yana riƙe da hannun Zee.




Kallo ɗaya na mishi na kawadda kaina ganin irin kallon da ya ke min maganar shi ce ta tilastamin kallonshi "Yanzu saboda ba ki da kirki sai ki bar gidannan ba ki min sallama ba?




Matarshi na kalla da ta tsareni da ido sannan nace "Kaima kasan ba yadda za'a yi na bar gidannan ba ka sani ba,yanzu ma gwaggo ce tace na jira ta fito da sai dai na same ku"




"Kin yi kyau Zeeeee" naji maganar shi cikin wani kalar sauti kuma a hankali matar shi na kalla a yanayin da na ganta na tabbata bata ji ba da yanzu ta haukace gurin.




Tsaraba gwaggo ta haɗamin kamar wata GARAR AURE (Littafina na farko) Ya Bashir ne yace zai kaini tasha.


Sallama na yiwa gwaggo tare da duƙawa na sumbaci goshin Zainab sannan na buɗe gaban motarshi ina ƙoƙarin shiga naji an mangaje ni ta shige gaban motar,Murmushi na yi tare da buɗe baya na shiga.




A hasale yace "Wai kina lafiya kuwa? To yanzu ina za ki je?




Cike da rashin kunya ta bashi amsa "Inda za ku je kai da ita,nima can zan je" tsaki yayi sannan ya buɗe in da nake zaune ya ɗora Zainab a cinyata ya koma mazaunin driver.




Buɗe mishi get aka yi muka fita, ta mirrow ya ke kallona kamar ya samu TV,ido muka haɗa da shi naga ya kashe min ido yana marairaice fuska kamar wani ƙaramin yaro.




Zaman kurame suka yi a motar don nikam nida Zainab sai hira muke tana min gwaranci har muka isa tashar.




Cewa ya yi na zauna yaje ya dawo,shiru motar ta ƙara yi sai maganar ta ce ta katse shirun "Ina fatan wannan tafiyar ta zama kin tafi ne ba dawowa domin zan fi buƙatar ki zauna can duk lokacin da kika so zumunci ki kira a waya ku yi, amma don girman Allah ki zauna gidanku har lokacin da za ki samu miji kiyi aurenki.Na miki alƙawari zan taya ki da addu'a Allah ya baki miji in da zaki yi zama na har abada ko don kwanciyar hankalin mu dukan mu"




Har ta kammala bata waigo ta dube ni ba,bayanta na ke kallo ina jin yadda take fitar da maganar har ƙasan zuciyarta.Ba zan iya bar mata bashin magana ba,Lawal ya riga ya koyadda ni da an mini in rama shi ya sa wannan karon ma ban bar mata bashi ba.






"Ina so ki sa a ranki idan har Allah ya ƙaddaro aure tsakani na da Ya Bashir ke baki isa ki hana ba,sannan barazanar ki ba za ta hanani zuwa garinnan a duk lokacin da na yi ra'ayi ba.Ni mamaki ma kike bani yadda kike wani zaƙewa akan lamarin mu kamar bakisan in da aka fito ba,aro fa na baki baiwar Allah zaƙewarki za ta iya sa na waiwayo ajiya ta,zai fi miki kyau kiyi shirin tarbata don kowane lokaci za ki iya tsintar mijinki a hannuna"




Daga haka na buɗe ƙofar na fita wanda yayi daidai da isowar shi yana faɗamin komai an kammala shi yayi mini jagora har na shiga mota ya na jaddadamin ƙarshen watannan zai zo.




Haka muka ci gaba da rayuwa idan ka ganni yanzu kamar ba ni ba,na yi ɓulɓul nayi wani kyau na musamman.




Yau ko da naje kai Amna makaranta har wuraren 8:30 ban ga shigowar su Safwan ba,sun saba latti amma ba su taɓa kai irin wannan lokacin ba.




Ganin lokaci ya tafi yasa na ja motata jikina a sanyaye,ko da naje gida kasa haƙura na yi na kira Antynsu Amna ina roƙon ta bincika min idan sun shigo.




Sai bayan 30minutes ta kira ni "Kiyi haƙuri Mommyn Amna,ko da ki ka kirani ina class amma da na fito na bincika aka ce ba su zo ba.Amma da ki kira kiji ko lafiya don gaskiya basu cika fashin zuwa ba sai dai su yi latti"




Number Mama na kamo da niyyar kiranta sai kuma na ji nauyin kiran,bayan haka kuma ba wurinta su ke kwana ba,idan ya ɗakko sudaga Makaranta can ya ke kaisu,da dare ya ɗauke su,su koma gida.




Ina ɗakina ina duba kayan da nayi order da suka iso,ina aza kowane a muhallinshi Ummi ta shigo,daga yanayin ta gabana ya faɗi ina tambayar ta lafiya?




"Ɗakko hijabinki muje asibiti,ashe tun jiya A'isha na asibiti shine sai yanzu su ka kira suke faɗa min"




Ƙirjina na dafe daga zaune "Asibiti kuma?




Ummi ce ta ɗakko min hijabin muka fita driver ya jamu sai asibitin da suka gayawa Ummi.




Da Mama muka fara cin karo,tun daga yanayinta bugun zuciyata ya canja,hankalina ya tashi daƙyar na iya ɗaga laɓɓana na gaishe ta,amsawa ta yi sannan suka gaisa da Ummi tana tambayar jikin Aysha.




"Ai A'isha jiki da sauƙi sosai,yanzu ma likitan ya fita ya kira Lawwalin wata ƙil magungunan za a ƙara rubutawa"




Cikin rawar murya na ce "Me ya same ta ne Mama?




"Wallahi jiya lafiya lau ya kaisu makaranta,bayan sun dawo ta ke cemin cikinta ke ciwo da kuma bayan ta,sai na bata magani da tunanin ko zazzaɓine ke son kamata.Zuwa la'asar abin ya rikice shine na kira mahaifinta mu ka yo asibiti,jiya daga ni har shi ba wanda ya runtsa saboda halin da ta ke ciki amma yanzu kam Alhamdulillah sauƙi ya samu"




Ɗakin da ta ke na tunkara na shiga,ɗakin yara ne kowa da kalar nasa ciwon idanuwana na shiga rabawa,can na hango Mariya a kusa da gadon da nake kyautata zaton Aysha ta ce a kwance.




Matsawa na yi tare da yi mata sallama,ban jira naji ta amsa ko ba ta amsa ba na matsa kusa ga ƴata, hawaye ne suka shiga yimin sintiri akan dandamalin kumatuna ganin yadda Aysha ta ta koma,ciwon rana ɗaya,amma kamar ba ita ba.




Hannunta da ke aje a gadon na riƙe ina jin wata ƙaunarta da kuma tausayinta suna shigata "Allah ya baki lafiya aysha" na faɗa a fili tare da barin ɗakin don nasan bazan samu amsar tambayar da nake so a wurin Mama ba.




Kai tsaye office ɗin likitan na nufa,a ƙofar office ɗin na same shi a tsaye tare da wani,sai da na matso kusa na fahimci Lawal ne.Gaisawa mu ka fara yi.




"Dr don Allah magana na ke so muyi akan rashin lafiyar ƴata,me ya same ta? Me ke damunta Dr?




"Amma ai ba shi ya kamata ki sama da maganar ba tunda ba shine ke tare da ita ba,kuma ai...................."






"Dan Allah Malam ba da kai nake magana ba,shi na tambaya kuma shi nake neman amsa a wurinshi,ina son in san abin da yasami ƴata,zai fi ma kyau kayi addu'a kar wani abu ya sami ƴata,domin wallahi banajin wannan karon zan zuba ido ka gurgunta rayuwar yara,kamar yadda ka so gurgunta tawa"






Na faɗa ina nuna shi hawaye na wanke min fuska tare da wata kalar tsanar Lawal da na ke ji.














*RUMAISA'U SIDI*✍️✍️✍️










AURE DA KARATU


NA
RUMAISA'U SIDI


FARAR ANIYA WRITERS


Page 25




"Doctor,don girman Allah ka faɗa min halin da ƴata ta ke ciki"
Na faɗa ina maida hankali na ga likitan.Office ɗin shi muka shiga na zauna ina jiran bayani daga gare shi.




"A gaskiya yarinyar ki ta shiga wannan halin ne sanadiyyar cutar Thyphod da ta kama mata ƴan hanji,sakamakon cin abinci da kuma ruwa marasa tsafta.Wannan ya sa dole ta na buƙatar theater da gaggawa,shine ki ka samu ina faɗawa mahaifinta"




Ashe a zaune ma ana jin jiri,ji nayi kamar ba ni. da sauran lakka,daƙyar na iya ɗaga laɓɓana nace "Doctor ka taimaka min ba na so in rasa ƴata,ko nawa ne zan biya a mata aiki"




A sukwane na dawo inda su Ummi suke zaune na zube a tabarmar da suka shimfiɗa a gefen ɗakin da aka kwantar da Aysha.




Hannuna Ummi ta riƙo "Ya dai Zainab,me suka ce na damunta? Na shiga na ga tana bacci"




Idanuwana da suka tara ƙwalla na ɗaga na dubeta "Ummi aiki za a yiwa Aysha,Thyphod ce ta mata mugun kamu, a cikin satinnan za a mata aiki"




"Innalillahi..........."Ummi ta shiga maimaitawa abinda ya ƙara karyar min da zuciya hawaye suka shiga ambaliya akan dandamalin fuskata.




"In sha Allah za ta samu lafiya ki kwantar da hankalin ki Zainab,Lawwali na kan ƙoƙarin haɗa kuɗin aikin"




Ji nayi kamar in ɗora hannu akai in fasa ihu "Idan har za a mata aikin ko yau,to zan bada kuɗin lafiyar ƴata na ke so" A ranar na shiga shirin yiwa Aysha aiki,kuma a gobe zasu mata.




Sai bayan magrib Aysha ta farka,lokacin da ta farka ina gefen gadon riƙe da hannunta da aka cire wa drip,ina kallon yadda hannun ya fara kumbura.Motsin da naji ta fara yasa na dubi kyakkyawar fuskarta, a hankali ta fara buɗe idanuwanta tana kuma motsa hannunta da ke cikin nawa.




A hankali kuma ta waigo fuskarta tana kallona a hankali ta furta "Mommy" ganin motsawar laɓɓanta yasa na fahimci abin da ta ke faɗi.




"Na'am Indo na,ya jikin na ki?




Hannuna ta cira tare da ɗorawa a cikinta "Mommy cikina,cikina na ciwo sosai Mommy"




Miƙewa na yi "Bari in kiran likita sai ya duba ki"hannuna da na ji ta riƙe yasa na dubeta,a hankali tace "Mommy don Allah kar ki tafi ki bar ni,zan bi ki" ƙwalla ce ta cika min ido,duƙawa na yi na sumbaci goshinta sannan na fita don kiran likita.




Wurin da su Ummi ke zaune na nufa don bawa likitocin damar yin aikinsu,ina isa Lawal ma na isowa tare da Safwan da aka baro gidan Anty A'i.Rungumeni yayi ya na hawaye.




Gefe muka koma ni da Safwan ya na bani labari "Mommy kin ga Aysha ko? Tun bayan tafiyar ki ba a daɗe ba kullum sai ta yi ciwon ciki, na faɗawa Abba ya daina siya mana abincin gidan su Lami basu da tsafta an faɗa mana a makaranta zai iya samu ciwon ciki,sai yace ƙarya ce don kar mu ci

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login