Showing 36001 words to 39000 words out of 57484 words
Ya Abbas.Sai dai wannan karon ma ina roƙonka da ka yi haƙuri,ka janye maganar aure a tsakaninmu,saboda ni yanzu karatuna ne a gabana.Bayan wannan kuma ba na jin zan iya nisa da ƴaƴana.Shi yasa na ke roƙonka da ka janye wannan maganar a tsakaninmu"
Jin yayi shiru baice komai ba yasa na ɗago kaina na dubeshi,ganin kallon da ya ke min yasa na yi saurin mayadda kaina ƙasa.
"Yanzu na fahimta,ba auren ne bakya so ba,ni ɗin ne dai bakyaso Zainab.Kuma ba komai na gode sosai" daga haka ya ja kujerar baya tare da tashi ya bar wurin.
Na kasa tashi daga in da nake zaune har ya shiga ba jimawa ya fito ya ja motar shi ya bar gidan,duk ina kallonshi.
Kamar mai tsoron taka ƙasa haka na shiga falon,ina ƙoƙarin wucewa ɗaki na ji maganar Ummi ta ratsa dodon kunne na "Kin kyauta Zainab,kuma ki ci gaba da yin duk abin da kike so,ki bar ganin kin girma har da ƴaƴa,har yanzu ba ki wuce a miki faɗa ba.Ki shiga hankalinki da ni Zainab,wallahi wannan karon zan yi mugun saɓa miki" ta faɗa tana nuna ni da zallar ɓacin rai a cikin muryar ta.
A sanyaye na ci gaba da kasancewa a kwanakin da suka biyo baya,duk da Ya Bashir bai daina kirana ba amma ya daina min maganar Aure,Ummi kuma ta ɗaure min sosai ta daina sakemin fuska,ga shirin Exam komai ya dagulemin..
Zaune muke ni da Amna da kuma Safwan da yazo wurina kasancewar weekend ce labari ya ke bani "Mommy har da sabbin littafai Abbana ya siya min,ga na Amna can ita ma ya bayar in kawo mata,har da sabbin uniform yace zai min.Yanzu a ƙofar gidanmu ya ke saida kayan miya,kuma wallahi ana siya sosai,yace kuma Islamiyya zai kaini,yanzu daɗin mu muke ci nida Abba" ya ƙarasa da zallar farinciki.
Murmushi na mishi "To Allah ya kyauta,ya sanya alkhairi" har raina naji daɗin canjawar Lawal,ko ba komai yarona zai yi ingantacciyar rayuwa.Ko Amna da ke hannuna yana ƙoƙarin kyautatawa,wani lokacin har ni za a yiwa tsaraba idan Safwan zai zo.
Yaya Isma'il ne ya sameni da maganar Aurena "Inaso ki fitar da miji a haɗe da na Mubarak da za'ayi nan da wata 2"
Marairaice fuskata na yi "Ayyah Yaya don Allah ku min uzuri,kaga karatuna yazo ƙarshe mun kusa fara exam,na maka alƙawari da na kammala zan fitar da miji In sha Allah"
kan shi ya girgiza "Wannan ba uzurine ba Zainab,kar ki manta lokacin aurenki na farko ma kin haɗa kika yi AURE DA KARATU,to yanzu ma haka za kiyi.Kamar yadda kika sani AURE ba ya hana KARATU,kamar yadda KARATU ba ya hana AURE.Za mu yi magana da mijin na ki"
Hankalina ya tashi sosai,ga shi Ummi ta daina kulani,shiryawa na yi na nufi gidan Anty Halima.
"Ki faɗa min abin da ya dace na yi Anty" na faɗa bayan na ƙare zayyane mata abin da ke faruwa.
"Ni banga abin damuwa anan ba,ba wai don Ya Bashir yana ɗan uwana ba Zainab,amma wallahi da shi kika dace tun farko.Idan har shawara kike so a wurina zan baki shawara da ki baiwa Ya Bashir dama ina tabbatar miki da izinin Allah ba za kiyi nadama ba.Amma ko yanzu ki maida hankali ga Addu'a duk wanda kika ji yafi tsaya miki a rai to ki zaɓe shi"
Ajiyar zuciya na sauke "Anty ba wai Ya Bashir ne ba na so ba,ina tsoron yadda zan tsallake garinnan na bar ƴaƴana,ga kuma Karatuna da ban kammala ba"
"Haba Zainab,yanzu saboda su sai ki kasa samawa kan ki farin ciki? Ko kina tunanin yanzu kece ke tsare da su? Wallahi ko kina tare da su ke ba ki isa ki tare musu komai ba.Kuma kar ki manta Safwan yana wurin mahaifinshi kuma yanzu kema kinsan yana kula da shi,Amna kuma ta hannun Ummi,wurinda kema nan kika samu tarbiyya.To miye abin ɗaga hankali? Karatunki kuma ga yadda Ya Bashir ke sonki,ko bayan an ɗaurane zai jiraki ki kammala exam ɗinki.Kar ki bari wannan karon ma rayuwar Ummi ta ɓaci saboda ke"
Maida hankalina na yi ga addu'a da neman zaɓin Allah.Text na turawa Ya Halima kan na zaɓi Ya Bashir,ko minti 2 banyi da tura saƙon ba sai ga kiranta "Ayyirrrrrrrrrrrrrr" ta rangaɗa mun guɗa a cikin kunne,janye wayar na yi a kan kunnena
"Anty Halima ai sai ki kashe min dodon kunne"
"Barni na yi Zainab,wallahi ina cikin farin ciki sosai,yau Account ɗina zai yi nauyi idan Ya Bashir yaji wannan albishir daga bakina,don Allah kar ki faɗa mishi bari in samu wannan goron" daga haka ta kashe wayar.
Ɗakin Ummi na shiga,tana zaune a gefen gadon da waya a hannunta.Guiwowina na zube a gabanta idanuwana na cika da ƙwalla "Kiyi haƙuri Ummi da ɓata miki rai da na yi,ban yi don in ɓata miki rai ba" kaina na ƙara sunkuyarwa sannan a hankali na ce "Kuma..............."sai na kasa ƙarasawa
"Kuma me?" ta tambaya da sauri "Na amince zan Auri Ya Bashir" na ƙarasa tare da barin ɗakin da ɗan guduna.
Ɗakina na koma da sauri na zube kan gadon ina maida ajiyar zuciya,ƙarar wayata yasa na miƙa hannu tare da ɗaukota,batare da nasan mai kira ba na ɗaga "Alhamdulillah Alhamdulillah Alhamdulillah" naji muryar Ya Bashir na doka hamdala har sau uku.
"Na gode sosai Zainab,na gode da damar da kika bani,kuma na miki alƙawari da yardar Allah ba zan baki kunya ba,kuma ki shirya tarbata a ƙarshen satinnan"
"Ƙarshen satinnan kuma?Duka yaushe ka zo?
"Ganinki na ke so na ƙara yi Zainab,wallahi ji nake kamar nayi tsutsuwa na ganni a sokoto don kisan irin farin cikin da nake ciki.Wallahi yau ina cikin farin ciki"
"Hmmmmmm" kawai na ce na yi shiru,don jin abin nake wani iri.Wai yau ni ke maganar AURE da Ya Bashir,ko ya rayuwar za ta yi da ni yanzu kuma??????
Shirye-shirye kawai suke yi don nikam exam ɗina kawai na sa gaba,bansan in da Lawal ya ji zanyi AURE ba sai kirana yayi da wani sabon layin da bansan shi da shi ba
"Zainab ashe AURE za ki yi" ya faɗa bayan mun gaisa
"Eh in sha Allah a ƙarshen watannan" na bashi amsa kai tsaye
"Allah ya kyauta ya sanya alkhairi,ya baku zaman lafiya,ina miki fatan samun kyakkyawar rayuwar da ta dace da ke.Allah ya baku zaman lafiya" ya faɗa da rauni sosai a muryar shi.
"Amin nima na gode sosai" na amsa ina jin wani abu marar daɗi a cikin raina.
BASHIR
Dama ya san za'a rina,dama ya tsammananci wannan daga gareta idan ta ji maganar auren,amma bai ɗauka abin zai kai haka ba.
Tun jiya take kan fashe-fashen kayan ɗakin shi,hatta suturar shi da ke cikin wardrobe duk ta zubo su ƙasa,haka suka kwana har saida ya kulleta a ɗakinta sannan ya samu ya shiga gyara abinda zai iya a ɗakin.
Baiyi yunƙurin yi mata komai ba,saboda ya san abin ba daɗi,kuma ƙaunar da ta ke mishi ce duk ta janyo hakan.Shiyasa ya ɗauke Zainab ya kaita wurin Mama don ta kwana a can.
Ɗakinta ya tunkara da mukullin ɗakin a hannunshi,tana makure ƙasan ɗakin,ta ɗora kanta akan gadon,ɗakin yayi kaca-kaca da fasasshin kwalabe.
Duƙawa yayi gabanta yana kallon yadda fuskarta ta kumbura tayi jajir kasancewarta farar fata.
Hannunta ya riƙo yana jin tausayinta na yadda ta ƙuntata rayuwarta a kan abinda bazai fasu ba sai wani ikon Allah "Kiyi haƙuri Baby,na faɗa miki ba don bana sonki zan auri Zainab ba kamar yadda kike tunani,ina ƙaunarki Zubaida,kar ki manta ke fa uwar ƴata ce ɗaya tilo da nake ƙauna.Wallahi banson wannan damuwar ta ki Zubaida"
Kanta ta ɗago tana dubanshi da ƙananan idanuwanta da suka ƙara shigewa saboda kuka "To me yasa zaka aureta? Me yasa? Na haɗaka da girman Allah ka janye maganar aurennan,wallahi duk abin da kake so zan maka,har girki zan koya in maka,wallahi duk abin da kake so na maka alƙawari zan koya in maka"
Kanshi ya girgiza " Ba saboda bakya min girki zan yi AURE ba Zubaida,ina so ki kwantarda hankalinki ki daina ƙuntata kan ki akan wannan maganar,an riga an rubuto zan AURE ki daga baya in AURI Zainab"
"Ƙarya ka ke,tun farko haka ka tsara,mugu kawai,azzalumi mara adalci" ta faɗa da hargagi tana miƙewa tsaye,shima miƙewa yayi yana kallonta tare da nuna kanshi.
"Ni ki ke kira da waƴannan munanan sunayen Zainab?
"Na faɗa,kayi duk abin da za ka yi,wallahi ba zan taɓa yafe muku ba kai da duk wanda ke da hannu a ƙulla wannan Auren na zalinci"
Juwaya yayi tare da barin ɗakin gudun yayi mata abin da bai kamata ba,saboda abin nata ya fara wuce gona da iri.
Ɓangaren mahaifiyar shi ya nufa,a falon ya sameta suna magana da Anty Halima a waya.Da gudu Zainab da ke falon ta rungumeshi tare da haye ƙafafunshi.
Sai da suka kammala ta dubeshi "Maganar kayan lehen Zainab muke yi,ya kamata ka tura mata kuɗi ta haɗa abinta,da har nace a haɗa nan shine Halima tace a tura mata zai fi"
Kanshi ya shafa "Lehe kuma Mama?
Harararshi ta yi " To da me kake tunani?Wallahi duk abin da ake sai ka mata don bazan yarda ba,garama ka shirya da kuɗi zaka fitar tunda kace ƴata kake so"
Murmushi yayi "Shikenan zan kira Sadiyar inji yadda za mu yi"
"Haka ya kamata,kuma ka ci gaba da lallaɓa matarka,karka biye mata.Abin ba daɗi dole ka mata uzuri,Allah ya haɗa kansu ya basu zaman lafiya,kai kuma ya baka ikon yin adalci a tsakaninsu"
RUMAISA'U SIDI
AURE DA KARATU
NA
RUMAISA'U SIDI
FARAR ANIYA WRITERS
Page 28
Shirye-shirye ake ta kowane ɓangare,kowannen su ji suke kamar yanzu ne za su aurar da ƴaƴan nasu abubuwa ake shiryawa na kece raini.
A ɓangarena kuwa exam ɗina da ke tunkaroni na fi mayadda hankalina akai,wani lokacin har mantawa nake da wani maganar AURE har sai na dawo gida naga yadda su Anty Nasma ke zaƙewa a wannan karon.
"Ya Bashir ina so in roƙeka wata alfarma" na sako zancen a lokacin da muke tsaka da fira.
"Ina jinki Habibty,kiyi sauri ki faɗa min me kike so? Ko menene zan nemo miki shi da yardar Allah"
Ajiyar zuciya na sauke sannan na sanyaya muryata "Ka ga ina gab da fara exam ɗina" nayi shiru jin shima yayi shiru yana saurarena sannan na ci gaba "Ina roƙon ka barni in kammala tukunna"
Shiru yayi na ɗan lokaci har na fara tunanin yadda zamu kwashe da shi don banajin zan yadda da wannan wulaƙancin in yi faɗi tashi kan KARATUNA sannan ya zo ya ruguza.
"Shikenan,Allah ya bada sa'a"naji ya magantu bayan tsawon lokaci,naji.daɗi sosai don wannan ita ce alfarma ta ƙarshe da zai min.
Ana saura sati ɗaya ɗaurin auren Ango Ya Mubarak ya iso,bayan kwana biyu Ya Mu'azzam ya iso tare da iyalinshi shima.
Mamaki nake bayan wucewar su,na lura Safwan ya canja min sosai ko jiya da nazo kawo Amna da muka haɗu da su,gaidani kawai yayi yaja hannun Amna suka wuce,yau ma gaidani kawai yayi ya ja hannunta suka shige.
Na shiga damuwa sosai,tsorona idan ba wani abu ke damunshi ba,tunanin hakanne yasa na fasa shiga motata na tunkari cikin makarantar.
Office ɗin shugaban makarantar na nufa,gaisawa muka yi cikin mutunci kasancewar ta sanni ,roƙonta na yi kan inason magana da Safwan idan ba damuwa.
Sanin yanzu ba ma tare da mahaifinsu yasa bata ja ba ta aika aka kiramin shi,tashi tayi tabar office ɗin tana faɗamin akwai zagayen da zatayi,na fahimci ta bamu gurine don in samu in gana da Safwan.
Dubanshi nake yadda ya kame a ƙofar office ɗin ya naɗe hannaye idanuwanshi na kallon ƙasa "Meke damunka?"
Na jefa mishi tambaya daga inda nake zaune,shiru ya min kamar bai ji ni ba,raina ne ya ɓaci yadda zaka haifi yaro amma kana mishi magana yana wulaƙantaka.
Miƙewa nayi a fusace tare da isa inda yake zaune na fizgoshi da ƙarfi "Ba magana nake maka ba?" na daka mishi tsawa raina na ƙara baci.
Kuka ya fashe da shi kamar wanda na yiwa mugun duka tare da durƙushewa a wurin,kallon mamaki na bishi da shi,ni dai nasan wannan abin bai kai yasanya shi wannan kukan ba.
Komawa na yi inda na taso ina ci gaba da kallonshi har yaci kukan ya ƙoshi kamar wanda aka cewa Ni ko ubanshi Lawal ya mutu har ajiyar zuciya ya ke saukewa.
"Me ke damunka?"na ƙara jefa mishi tambaya.
Idanuwanshi ya ɗago da suka rine sannan a hankali ya ɗaga laɓɓanshi yace "Mommy dagaske AURE za kiyi?"
Idanuwana na zaro "Shine kake wa wannan kukan"
Rarrafowa yayi har inda nake zaune tare da riƙe hannuwana "Mommy don Allah kar ki yi AURE,Mommy banason kiyi nisa da mu,Mommy ki dawo gidanmu,wallahi yanzu Abba ya daina faɗa,har kayan daɗi yake siyo min in ci,kema idan kika dawo zai siyo miki.Mommy duk cikin friends ɗina nine kawai Mommynshi ta bar gidansu,don Allah Mommy kiyi haƙuri ki yafewa Abba kar ki AURI wani don Allah" ya ƙarasa tare da kife kanshi akan cinyoyina.
Innalillahi wa inna ilaihi raji'un,shi nake gudu tun farko,wannan nake tsoro,yadda rayuwar ƴaƴana za ta kasance.Bayanshi na ke bubbugawa jin yadda yake sauke ajiyar zuciya
"Kayi haƙuri Safwan ba zan iya dawowa gidanku ba,amma na maka alƙawarin ziyartarka akai-akai ka daina damuwa ka ji?
Fizgewa yayi daga gareni tare da barin office ɗin kamar walƙiya,sunan Allah na shiga kira sannan na tashi jiki mace nabar office ɗin.
Tuƙi nake amma gaba ɗaya hankalina baya jikina,banason damuwar ƴaƴana ko kaɗan,shi yasa tun farko naso in tubure kan maganar AURE N nan.
Sai ga Safwan har da su zazzaɓi hankalina ya tashi sosai,tsoro ya shigeni,kar fa shima na rasa shi.
"To miye don Safwan ba ya son AUREN? Ke kika haifi Safwan ko shine ya haife ki?Wai kina da hankali kuwa Zainab? kan yaron za ki ɗaga AUREN?Wallahi zai fi miki kyau ki kawadda shirmen Safwan a gabanki,mahaifinshi yake tayawa kishi,ki ƙyaleshi kawai kiyi harkar gabanki"
Shiru nayi ina sauraren bayanin Anty Halima da ke jin kamar ta shaƙo wuyana,ƙoƙarin kawadda tunanin nayi a gefe kuma ina lallashin Safwan da kullum ƙara tubure min ya ke.
Yau ma lallashinshi na ke amma sai wani tuburewa yake kamar shine gaba da ni "Ni gaskiya Mommy ba wani AURE da zaki yi,yanzu shikenan da kinyi AURE kin daina sonmu,wataƙila ma zaki manta da mu,ni wallahi idan har za kiyi wannan AUREN to ba ruwana da ke"
Tsawa na buga mishi tare da tureshi daga lallashin da nake mishi "Je kayi duk abinda kake da niyya ina ruwana?AURE ne bazan fasa yi ba idan ma haɗiye zuciyarka za ka yi saidai ka yi,kar ka ƙara kulani ka ji ko?Na ce karka ƙara kulani,ka gani zan rayu ko bazan rayuba,ai ba kai kaɗai na haifa ba.Kaje kayi duk abinda kake so"daga haka na juya tare da barin makarantar.
Shareshi nayi na ci gaba da harkokin gabana,ana gobe za'a yi ɗaurin AURE Gwaggo ta iso tare da Ango Ya Bashir.Ba yadda baiso mu haɗu ba ranar amma naƙi fita.
Banyi mamakin rashin zuwan Matarshi ba,saboda dama nasan akwai kallo tsakanina da ita,don na lura ɗanyar haukace da ita,amma ba komai nima nayi training a hannun Dr Lawal zan bita yadda ya dace.
Washe gari dubban mutane suka shaida ɗaurin AURE NA da Ya Bashir akan sadaki mafi daraja daga nan kuma aka wuce gidan Amaryar Ya Mubarak.
Shigewa nayi ana hidimar bikin Ya Mubarak,ina ɗakin Ummi ina gauda baƙinta da ta naje na gaisar aka ce ana sallama da ni.
Mayafin Lace ɗin da ke jikina na ɗora a kaina tare da tunkarar waje,daga inda ake aje motoci na hangeshi,wurin ne kawai yake da damar jama'a amma ko ina mutane ne wasu daga ɓangaren Ummi wasu kuma dangine na ƙauye.
A tsaye yake cikin kamilalliyar shigar Yadi ya kafa hula a kanshi,murmushin ƙarfin hali ya aro ya watsawa fuskarshi bayan isata wurin.
Sallama na mishi ya amsa muka gaisa cikin girmama juna "Zainab an ɗaura AURE,Allah ya kyauta ya sanya alkhairi"
"Amin ya Allah" na amsa ina jin nauyin kallon idanuwanshi yadda naji muryarshi ta sanyaya sosai.
"Bamu samu gaisawa da Angon ba,ya na ta hidima da baƙi,ina mishi Allah ya kyauta,ina kuma yi mishi barka da samun wannan kyautar ta ubangiji"
Murmushi na yi tare da juyawa jin takun tafiya a bayana,Ya Bashir ne cikin wata dakakkiyar shadda,sai maiƙo take fara ƙal,ga hular da ya kafa kai daga ganin hular kasan ba ƙananan kuɗine suka ɗauko ta ba.
Hannu Lawal ya bashi,sai da ya ɗan ja sakanni sannan ya bashi sukayi musabaha.Kallona yayi "Ki shiga ciki ko"
Jiki a sanyaye na koma cikin gidan,ɗakina na wuce kai tsaye a can na sami Safwan zaune tare da Amna sai Labari take bashi shi kuma yana shareta.
Kallo ɗaya na mishi na kawadda kaina,ɗakin nake ƙoƙarin bari ya riƙo hannuna da ƙarfi "Mommy don Allah kiyi haƙuri,ba zan ƙara ba"
Hannunshi na cire daga nawa "Shikenan naji" na faɗa ina ɗago wayata dake ƙara,karawa nayi a kunnena bayan na ɗaga.
"Ki same ni bayan gida"daga haka ya kashe wayar ƙittt.
Ta ƙofar kitchen na bi kasancwwar wajen akwai mutane sosai,tun daga nesa na hangeshi a tsaye ya soke hannayenshi a aljihun wandonshi ya cire babbar riga saɓanin ɗazu da yake sanye da ita.
Sallama na mishi bayan na isa inda yake,amsamin yayi sannan ya tambayeni baƙi nace Alhamdulillah.
"Layinki na ke so ki bani"ya faɗa yana miƙo min hannunshi
"Layina kuma?Da shi fa nake aiki,komai nawa da shi nake yi"
Ajiyar zuciya ya ƙara saukewa ya shiga zarya a wurin "Ba zan iya ba,ko da can da ban mallake ki ba,baki san irin ƙunar da nake ji idan na ganki da wani ba,bale yanzu da kike tawa ni kaɗai,Zuciyata ba zata ɗauka ba"
"Lawal ne fa Yaya kuma..............."
"Akwai banbanci tsakanin Lawal da sauran maza?Ba wani banbanci Zainab"
Duƙewa wurin nayi na ɓarke da kukan da ni kaina bansan dalilin yinshi ba.
Shima duƙawar yayi "Kuka kuma Zainab? Ni wallahi ban yi don in ɓata ranki ba,amma kiyi haƙuri don Allah ki daina wannan kukan banason kukanki kinji"
Lallashina ya shiga yi kamar wata jaririya abin da na kasa samu a inda na fito,ni kuma sai ƙara narkewa nake ina shagwaɓewa.
RUMAISA'U SIDI