Showing 3001 words to 6000 words out of 57484 words

Chapter 2 - AURE DA KARATU Book Complete Rumaisa Sidi.txt

26 Jan 2025

6697

Aysha karatunsu shi kuma yana sana'arshi ta chat da kullum ko ya rasa na pure water bazai rasa na data ba


Ganin dare yayi na kashe data ta tareda tashi na dauke yarana da bacci ya dauke anan falon kayan kallon da kunna su bayada amfani nazo na kashe ganin yana falon nabar hasken falon ban kashe ba na wuce daki shirin baccina nayi ina gaba mirrow ina kichaniyar daure gashin kaina ya shigo


Tsaye yayi yana kallonta a ranshi yace "yarinyar nan fa bata tsufa wazai ganta yace ta haifi 'ya'ya har hudu a cikinta( bayanin ta hudun yana gaba) tun lokacin kuruciya zee kyakkyawace ajin farko yar kwalisa ba wanda ya taba tunanin zee zata aure shi kasancewar ta fito daga gidan manya kuma ba wanda baisan irin soyayyar da mahaifanta da 'yan uwanta ke nuna mata ba


Karasowa yayi gaban mirrow yana kallonta ta ciki "Kinyi kyau zee" gira na dage mishi ina kallonshi ta cikin mirrow " dama can ni kyakkyawace kaima kasan wannan" daga haka ta zame tareda nufar gadon ta kwanta tareda lullubo bargon har kanta ta rufe ajiyar zuciya ya sauke "hmmmm bazata canjaba kenan" dakin ya bari ya koma falo ya kwanta


Yau bacci nasha kasancewar weekend ce suma yaran daga sallah suka koma bacci sai wuraren 11 na tashi saboda kukan Amra "mai yara baya hutu" na fada ina saukowa daga kan gadon a gurguje na watsa ruwa na fito a jikin safwan na sameta tana shesshekar kuka mahaifinsu kuma na kwance kan kujera da remote a hannunshi yana canja channel


"Me aka mata" na tambayi safwan "Wayar abba ta dauka shine garin kawomin ta fadi sai....." hannu na daga mishi saboda nasan kwanan zancen "ku je ku shirya fita zamu yi da munci abinci" ai dagudu suka ruga har amra dake kuka


Kallo daya na mishi na wuce kitchen na hada mana abinci fitowa nayi jin yara na mishi addu'ar fita kamar yanda na koya musu "Amm nace abban safwan" na dakatar da shi ganin yana kokarin fita tsayawa yayi yana kallona karasowa nayi bakin kofar nace "Dama nace zamuje da yara muje muga babyn salma daga can in wuce gida" annurin fuskarshi ne ya bace da alama ba haka yayi tunani ba "Sai kun dawo" ya fada tareda ficewa daga gidan "can ta matse ma" na fada tareda juyawa nakoma inda na fito


A kofar gidansu napep ta sauke mu na sallame shi tareda shiga gidan tareda yarana gidan cike yake da 'yan uwansu lawal duk yayunshi mata su uku da sukayi aure suna gidan gaisawa nayi da wayanda ke waje yarana ma suka shiga gaida su cikin ladabi don ba alfahari ba indai a fannin tarbiyyane banida sanya ga yarana


Dakin mahaifiyarshi na wuce inda mai jegon take sallama nayi suna dakin har mama karasawa nayi gabanta na durkusa na gaidata kamar yanda na saba kullum har gobe ina ganin kimar matar "yawwa zainab ya gidan ya kuma yarannaku" sunkuyadda kaina nayi ina fadin "Duk lafiya lau muke mama ashe salma an sauka Allah ya raya akan sunna"


"Amin Amin zainab" matsawa nayi wurin mai jegon nabar su Amra wurin mama suna zuba mata zance "Sannu salma barka da arziki" "yawwa" ta amsa a dage kamar wacca akama dole jinjirar na karba na kira su safwan suma na aza musu kowa ya dauka Amra ma ta sa rigimar sai an bata "to tara hannun na dora miki ita" da sauri ta miko hannu na doramata ba tareda na sakarmata 'yar ba


"Kinason baby gashi uwarki ta rufe haihuwar" Anty mariya (yayar lawal wacca yake bi) ta fada kai tsaye tana kawadda kanta


Sarai na jita amma sai nayi kamar banjiba hirarsu suka cigaba da yi ina jinsu amma bansaka musu baki ba babbar yayarsu ce ta shigo rike da hannun Aysha Anty A'i (wacca lawal yayiwa takwara da Aysha) "Anty ina wuni" itama kamar sauran a yatsine ta karba tana zama kan kujerar dakin


"Shekaranjiya ai nazo bansameki ba nace abu ga gidan 'yan boko lawal kawai na samu nace Allah ya maka budi kaima ka fita Allah ya rabaka da tsaron gida"


Caraf Anty mariya ta karbe "Ai anty ni ina mamakin matar da take hada AURE DA KARATU kuma tace duka zatayi wallahi ina tausayawa mijin da matarshi ke KARATU don ba wata kulawa da zai samu bare kuma lawal da yake cikin jarabawa saidai fatan Allah yasa ya cinyeta"


Mikewa nayi tareda yi musu sallama na hada kan yarana mama na samu a falo don in mata sallama "zo nan zainab" umurtarsu safwan nayi da su jirani a waje matsawa nayi kusa da ita na durgusa " ya gidan naku ba wata matsala dai ko zainab"


" A'a mama ba wata matsala" numfashi ta sauke "ki kara hakuri zainab nasan kinmana kokari zama da lawal ba sana'a amma insha Allah akwai shirin da nakeyi akan hakan da anyi sunannan komai zai daidaita ki kara hakuri kinji"


Murmushi nayi "Insha Allah mama" ina ganin kimar matar sosai saboda dattijuwar arziki ce sam su lawal basuyi halinta ba "to ya karatunnaki" murmushi nayi "Karatu alhamdulillah mama wata 1 ya rage mu fara jarabawa insha Allah"
"Masha Allah to Allah yasa a kare a sa'a"
"Amin mama"


Kudi na zaro a jakata dubu 20 kamar yanda na kebesu tun gida na aje a gefen da take "gashi mama a kara ayi hidimar biki" mikewa nayi tayi saurin rike hannuna "Dau kudinnan zainab tun ban bata ranki ba duk wannan halin da kuke ciki zaki dauko wayannan kudin ki kawo"


"Wallahi ba komai mama don Allah ki karba" kudin ta dauko ta raba biyu " karbi nan na dau wannan dai mungode sosai Allah ya miki albarka"


Daga nan kofar gidanmu aka sauke mu a bakin tangamemen get din gidanmu gaida maigadinmu nayi ya amsa shima yana gaidani cikin girmamawa yana yiwa su Amra wasa


Motar da nahango a farfajiyar gidan ita ta tabbatarmin da YAYA na gidan babban yaya wanda ke taka matsayin uba a gidan tun bayan da kasa ta rufe idon mahaifinmu








Muje zuwa daiiiiiii


AURE DA KARATU
NA
RUMAISA SIDI










Page 4






Bangaren mahaifiyata na wuce kamar kullum ko ina tsaf-tsaf kamar gidan sabuwar amarya to akwai masu kula da komai


Tana hakimce akan hadaddiyar kujerar dake falon cike da kauna na karasa tareda rungumeta " nayi kewarki ummi" 'yar dariya tayi irin ta jin dadi " bansan sai yaushe zaki girmaba Abun abba ke bakisan kin girma ba wani lokacin ko yaranki basa sangartar da kike yi" gyara zamana nayi tareda shigewa jikinta "karkiga laifina ummi gurinki kawai nake samun hakan a yanzu" shafa kaina tayi "Allah ya miki albarka autata"


"To ina kika baro uwayen rigimar kuma" waigawa nayi sai yanzu na lura da bama tare idanuwana sun rufe da kaunar mahaifiyata "Suna bangaren Yaya don munga motarshi a waje"


"Eh yau bai fita ba kinsan weekend ce"


"Haka ne fa" na fada ina sauke gyalena tareda ajeshi kan kujera


"Asabe Asabe" ummi tashiga kwallawa mai aikinta kira da sauri ta fito "gani um....) maganarta ta katse tana karasowa cikin falon "Ahhh anty zee sannu da zuwa wallahi banma ji shigowarki ba ina su Amra" nima murmushin na mata "wallahi munshigo anty asabe su amra suna wurinsu Nihal"


"Masha Allah" juyawa tayi wurin ummi "gani ummi" nuna ni tayi "je ki kawowa auta abinci ki zubomata farfesunnan da kika min suma yaran ki tanadar musu abinda za su ci kafin su tuna dani"


"To ummi" ta fada tareda mikewa waigowa ummin tayi tana kallona " ko akwai abinda kike bukatar asama miki" girgiza kaina nayi inajin kwalla na neman cika min ido


Allah sarki uwa duk lokacin da zanzo gidan to zakaji tana a girkamin kaza a girkamin kaza duk abinda take ganin zaimin wahalar samu a gidan mijina to kokari take ta samaminshi nida yarana


Nan take aka cika gabana da kayan abinci kala-kala da fruit fadi take "ki bude ciki kici abinci tunda ba bakuwa kike ba" abincin na diba ina ci da kanta ta shiga kitchen ta hadomin fruit salad ta kawo gabana " kifa buda ciki kici" saida ta sani gaba naci abincin sannan ta kira asabe ta kwashe kayan


"dubi yanda duk kika rame kindauki damuwa kinsawa ranki bansan randa kika koma haka ba zainab ada bakida kawa kamata amma daga lokacinda likita ya gayamana kinada hawan jini na aje wannan tunanin nasha gayamiki duk abinda kike so ki kirani ki sanarda ni ko ki kira yayanki ba abinda zaki nema a duniyannan indai akwai shi da bazamu nemo miki ba amma kullum abin inga kina cikowa kina kiba saidai kullum in ganki zuru-zuru da ido sai dogon hanci me kike tunani zainab? shin ke bazaki kwantar da hankalinki ba kodon yaranki"


Murmushin yake nayi tareda riko hannuwanta duka biyu "ba abinda ke damuna ummi duk abinda nakeso ba abinda bakumin ba kawai dai may be yawon makaranta ne yasa kike ganin hakan" ido ta zubamin kamar mai nazari irin kallon da take mana a lokacin da idan tana zargin muna boye wani abu


"Indai ko zirga-zirgar makaranta ce ta maidaki haka to zansa yayanki ya kaimiki mota daya cikin ta gidannan"
Wannan karon kasa daurewa nayi saida na rungumeta tareda fashewa da kuka "don Allah ki yafemin ummi ku yafemin abinda kuka gudarmin kenan na kasa fahimta don Allah ku yafemin" bayana ta shiga shafawa " kingani ko? kingani ban gayamiki kar ki kara zuwa kimin kuka ba zainab kodai akwai abinda kike boyemin" kaina na shiga girgizawa tareda kara shigewa jikinta "bakomai ummi wallahi bakomai"


"To karki kara kuka kinji karkisa mudinga ji aranmu kamar ba mu cika alkawarin mahaifinki ba Abbanki har ya rasu yana maimaita a kula dake a kyautatamiki ki gayamana zainab idan akwai abinda muka kasa miki don Allah"


Ganin itama ina neman sakata damuwa yasa na ware na dinga zuba mata shagwaba ita kuma sai riritani takeyi daki ta shiga ta dakkomin abayas tace gani tayi ana talla suka burgeta tasanni da son abaya ta siyamin ai kwa nahau murna nashiga gwadawa ina tsalle kamar wata Aysha


Bangaren Yaya Isma'il na shiga (shine babba a gidanmu) matarshi Anty nasma kawai na samu gaisawa muka yi cikin girmamawa na tambayeta su Safwan


"Sun fita tareda abban nihal rigima suka sakamishi kan teddy shine ya kwashesu ke har yasir na hada nace duk a tafi"


"Ai gwanda da kika mika su can ko bakinki ya huta"


Sallama na mata na shiga bangaren yaya Abbas (shine kebin yaya babba) shikam yana nan gida gaidashi nayi cikin mutunci da kaunar juna itama matarshi na gaisawa mukayi ta kawomin dan abin motsa baki tareda wucewa dakinta ta barmu tare


"Yadai ZEEN ABBA ba wata matsala dai ko" murmushi nayi "ba matsalar komai yaya"


"Idan da wata matsalar kigayamin dubi yanda kika rame ko wani abun yake miki har yanzu"


"Ba abinda yakemin yaya bakomai"
"Idan har kikaga da wata matsala ki dawo gida don bazamu zuba ido ya kashe mana ke ba idan shi baya bukatarki mu muna bukatarki don haka bazamu zuba ido ya cigaba da wasa da rayuwarki ba kinji ko"


"Insha Allah yaya" tun dama can yaya mutum ne mai zuciya kuma tsayayye kan ra'ayinshi shine mutum na farko da ya fara nuna tsanar aurena da lawal tun farkon soyayyarmu baya kaunar lawal bare kuma abubuwan da suka zo suna faruwa daga baya


"Zan turo miki kudi ta account dinki ranar monday kije asibiti a duba dalilin wannan ramar"


"To yaya" na amsa cikin girmamawa


Sai la'asar nayi shirin barin gidan tareda sha tara ta arziki daga mahaifiyata da kuma 'yan uwana naji dadin fitar koba komai na kwanta jikin mahaifiyata ta kara kwantarmin da hankali


Banyi girki ba saboda munzo da abinci tun daga gida wanda ummi tasa aka girka mana na musamman saida mukayi sallar magriba sannan na zuba mana abincin


Muna tsaka da cin abincin ya shigo kallo daya yayiwa shinkafa kazar da muke ci ya kawadda kai tareda wucewa daki koda ya fito har mun kammala an kwashe kayan ina kokarin jona wayata caji ya dawo falon yana zama yaran suka dakatarda wasar da sukeyi kowannensu ya nutsu musamman amra da ta shige jikina


Kallonsu yayi " meye kuma kuka daina wasan" hannu ya mikawa amra data shige jikina "zo amra na zo inji wa ya taba ki" kafada ta make cikin shagwaba take fadin "Um um ba kaine ka dakeni ba da safe" kunnuwanshi ya kama "yi hakuri shalelen mommy zo gurin abbanki kinji"


Matsawa tayi ya dauketa ya dora akan cinyarshi wasa ya shiga yi mata tana kyalkyala dariya sakkowa yayi ya hada kan yaran duka yana musu wasa abinda na dade bangani ba sam baya cikin iyaye masu jan 'ya'yansu a jiki wani annurin farinciki nake hangowa a fuskokinsu


Iyaye kowane akwai rawar da yake takawa a zukatan yaransu basu rasa komai ba daga gareni amma kuma yau sai na hango wani bangare na farinciki a tare da su saboda kasancewar Abbansu kusa dasu kamar a mafarki na tsinci maganarshi " mama tace kunje kinkai harda gudummawa an gode sosai"


Kallo guda na mishi na kawadda kai " eh wallahi ba komai" hmmmm lawal kenan ai saidai in ba wani labarinka wallahi a wannan lokacin nasan abinda yake a zuciyar lawal na gama karantarshi tsaff kudin da mama ta rage yakeso in bashi "kaiii wallahi namiji bayada kunya"


Washe gari saiga mota ankawomin daga gida godiya nakira na musu lawal na daki naje na sameshi ina murna " abban safwan ga mota can an aikomin daga gida in rika zuwa makaranta"


"Allah ya kyauta" daga wannan bai kara magana ba jiki a sanyaye na juya na koma waje


Da motar nayi amfani na sauke su safwan a makaranta nima na wuce tawa
samuwar motar ya saukakamin sosai da ita nake kai yarana makaranta nima da ita nake zuwa


Tunda muka fito lecture muke zaune muna fira da wayanda muke tare nafisa da kuma maman ayman sai zee lawal haka muke mu hudu saboda banason tarkacen kawayennan tun dama can


Kallon Nafisa nakeyi da ta dage tana zuba kalaman soyayya a waya ko ba'a fada ba nasan Ahmad ne saurayinta ko kuma ince mijin da zata aura


kallona tayi "yadai maman amra sai kallona kike ina zuba soyayya da hubby" murmushi nayi "ai dole na kalleki irin wannan love haka amma dai da zakiji shawarata da kindan rage "


Ido ta zare "me zan rage maman amra? soyayyar? hmmm wallahi bazan iya ba don bakisan yanda nake kaunar hubby bane shima yake kaunata bazaki gane yanda nakeji ba hmmmm abin ba'a cewa komai" ta karasa fadi tana lumshe ido


"hmmm da zakiji shawarata da kin rage wannan haukar don wallahi ba abinda zata tsinana miki sai wahala kinganni nan ko alama bakiyi irin soyayyar da nayi ba amma ba abinda ta tsinanamin"


Matsowa zee lawal tayi " takwara bamu labari me yasa kike yawan nusarda mu akan soyayya"


















Hmmmmmm






AURE DA KARATU
NA
RUMAISA SIDI






Page 5


Murmushi nayi " nidai fatana ku hutadda zuciyarku da wannan zazzafar soyayyar da kuke dorawa kanku"
" amma ya kamata ki gayamana dalilin da yasa kike cewa hakan ko zamufi ganewa ko ya kuka ce" Nafisa ta karasa maganar tana kallonsu


Wannan karon maman ayman ce ta katse shirun da fadin " Mu bar maganar mana tunda kuka ga bata fada ba may be abinda ya shafi rayuwarta ne kuma dama ku daina tunanin samun irin wannan da kuke yi a waje a gidan aurenki"


Nidai shiru nayi ina kallon zee lawal da ke fadin " don Allah ku daina sa muna tsoron aurennan tun kan mushiga"
Wayata na duba tareda mikewa na dau jakata "Ni zan wuce gida banjin dadin jikina zan dan sha magani in gani" hada baki sukayi wurin yimin sannu maman ayman ta dubeni "kodai-kodai" saurin kallonta nayi ina kankance idona " kodai me" itama idon ta kankance kamar yanda nayi " ko ansamarwa amra kane?"


Kai na girgiza "Allah ya shiryaki"dariya suka sa gaba daya dan sukayi
takomin suka yi na shiga mota na dau hanyar gida a hanya naga mai kwa-kwa na tsaya na siya wa su Aysha da ke sonta


Hamdala nayi bayan na kashe motar na fito kofar falon na taba najita a bude abinda ya tabbatar min yana gidan sallama nayi yana kwance a kan kujera da waya a hannunshi banga alamun amsa sallama akan labbansa ba
Wuceshi nayi na wuce dakina jakata na aje tareda zare dankwalin kaina gefen gadon na samu na zauna ina sauke numfashi ina bukatar ganin likita kwanannan ciwon kannan ya matsamin mikewa nayi na wuce toilet in samu in watsa ruwa ko zanji sauki


Bandau lokaci ba a toilet din nafito jikina na tsane da towel turare kawai na goga a jikina kallon kaina nayi a madubi inaso inga ramar da mutane ke fadar nayi bazan musaba domin ko bakincikin da nake kwankwada a gidan lawal ya isa ya ramadda ni riga na samu mara nauyi na zuba na dora hulata


Har yanzu yana falon dama ina zaije kullum muna tare idan baya cikin gida to yana waje idan baya waje yana gidansu ko ni da nake mace bazan iya wannan zaman ba amma shi ko a kwalar rigarshi


Kujera na samu na zauna ina sauke numfashi " kamin izini gobe inje asibiti banjin dadi" kallo daya yamin ya cigaba da latsar wayarshi ya dau lokaci sannan yace " Kinyi marmarin tonamin asirine shiyasa zaki koma asibitin ace kinada wata cutar 'yan uwanki su sakani gaba" kallonshi nakeyi kamar wata sabuwar halitta " wai lawal meyasa abin fada bayada kadan a gurinka fisabilillah yaushe maganar nan takai ka maidata haka maganar lafiyata nake maka fa kuma ko wata cutar akace ta sameni to ko wannan karon kaine silarta lawal"


Kaina dake sarawa na dafe " wai me kakeson maidani lawal me kake nufi dani ne? na gaji wallahi nagaji" na fada hawaye na silalomin gabadaya abubuwannan sun isheni wani lokacin idan na zauna ina tunani sai na dinga jin inama ban hadu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login