Showing 42001 words to 45000 words out of 57484 words
RUMAISA'U SIDI
FARAR ANIYA WRITERS
Page 31
Cikin iyawar ubangiji na kammala karatuna cikin ɗumbin nasara.Na samu taya murnar kammala karatuna tare da kyaututtuka na musawalir daga ƴan uwa da kuma abokan arzikina.
Ana gobe zan tare na haɗa ƙwarya-ƙwaryar walima a gidanmu ƴan uwana ne da kuma ƙawayena,har da su Mariya ƴan uwan Lawal sun zo yimin kara.Nasha kyau a ranar cikin wani haɗaɗɗe kuma tsadadden lashin da na saka wanda yake ɗaya daga cikin kayan da na ɗinkawa kaina da maƙudan kuɗaɗen da Ya Bashir ya bani yace na haɗa lefe na.
Washe gari muka ɗau hanyar kaduna tare da rakiyar Anty Halima,Anty Hafsat da kuma Hafsat da ta dage sai ta rakani gidan Ya Bashir,saɓanin aurena da Lawal da ta kafe bazata rakani ba.
Shiru nayi a motar ina jina kamar ba ni ba,lumshe idanuwana nayi tuna ƴaƴana da na baro,lokacin da zamu tashi naga yadda Safwan yaja hannun Amra suna kuka.Mahaifinshi ne ya kawoshi don sumin sallama a cewarshi.
Ya kuma yimin maganar dawowar Amna hannunshi tunda aure zanyi,Wataƙila ya ɗauka da ita zanje,nace mishi wurun Ummi zan barta.
Tarba ta musamman muka samu a gidan kamar wasu baƙi,ɓangaren gwaggo muka sauka aka shiga hidima da mu,na kasa sakin jikina duk irin faɗan da gwaggo kemin na in saki jikina.Na kasa wannan zuwanfa yana da banbanci da sauran zuwan da na saba.
Sai dare angon ya shigo sai watsar baki yake kana kallonshi zaka fahimci irin farin cikin da yake ciki ko kunyar mutanen falon baya yi ya kafamin ido.
Tashi nayi na bar falon jin yadda duk na takura da wannan mayen kallon nashi,ina ɗakin kwance Anty Halima ta shigo "Taso muje kar mijinki ya ƙwaƙulemin ido"ta faɗa tana jan hannuna
Fizgewa nayi ina kallonta "Haba dai yanzu sai in ratsa mutanen da ke falon inje wurinshi ni ga shugabar marasa kunya"
Hannuwanta ta watsa "To shine me? Kinga wallahi ki tashi yana bayan gida yana jiranki,idan ba haka ba zan kirashi in faɗa mishi kince ba zaki je ba.Kuma wallahi kinsan halinshi tsaf zai shigo ɗakinnan"
Mayafina na ɗora a kaina muka fito,ta ƙofar kitchen muka bi saboda ina kunyar in ratsa su gwaggo in fita,in don ta Hafsa da Anty Nasma mai sauƙice amma ina jin kunyar gwaggo sosai.
Takowa yayi har inda muke yana hararar Anty Halima "Shine kika shanya ni ina zaman jiranki ko?"
"Wallahi ba laifina ne ba,laifin Amaryarka ce gatanan"ta ƙarasa tana nuna ni
Murmushi yayi tare da gyara tsayuwarshi yana fuskantata "Wa ya gaya miki Amarya na laifi Sadiya? Musamman ma irin tawa Amaryar" ya faɗa yana ƙoƙarin lallai sai mun haɗa ido dashi
Tafi ta buga sannan kamar wadda ta tuna wani abu tayi saurin rufe bakinta da tafin hannunta.Hanya ya nuna mata "Bi nan,Kin ƙare aikinki na gode"Dariya tasa tana shigewa ta inda muka fito.
Matsowa yayi yana ƙara ƙureni da kallo kasancewar wurin akwai wadatar haske kamar da rana,jikina naji kamar ya fara ɗaukar rawa,wannan kalon ya min nauyi
"Nema kike ki kasheni da ƙaunarki Zainab,kullum kyau kike ƙarawa na musamman,kamar ba Zainab ɗin da na raina da hannuna ba,kamar ba kece uwar ƴaƴa uku ba"
Kaina na ɗago karo na farko na dubeshi jin yadda yake jero zance,a bazata naji hannunshi cikin nawa "Ina ƙaunarki Zainab,ni kaina bansan iya adadin ƙaunar da nake miki ba,don Allah karki gujeni,ki zauna da ni,na miki alƙawari nima zan kula da ke kamar yadda uwa ke kula da jaririnta,zan shagwaɓa ki Zainab,zan nuna miki irin ƙaunar da nake miki,Ina fata zaki bani dama?" ya ƙarasa da sigar tambaya
Daƙyar na iya ɗaga mishi kaina alamar "eh" idanuwana suka cika da ƙwalla wadda zan iya kiranta ta farin ciki,na tsammani daga samun irin wannan rayuwar ta farin ciki.
A hankali nake ɗaga ƙafata tare da ɗorata gudun farkawar Anty Halima ko Hafsat,na kai tsakiyar ɗakin ina ƙoƙarin ɗaga ƙafar naji sun kwashe min da dariya.
Idanuwana na runtse,ba haka naso ba,wallahi sam basuda kirki,shine suka min kamar bacci suke ashe na munafunci ne.Ƙin juyowa nayi na ci gaba da tafiyata na shige toilet ina jin yadda suke min dariya.
Washe gari suka shiga shirin tafiya,shiryawa nayi cikin haɗaɗɗiyar atamfa ta na ɗora mayafina na fito a Amarya sak nayi kyau sosai ni kaina nasan wannan.
Gwaggo ce ta riƙa hannuna har sashen da yake mallakina a yanzun,ba wancan da Zubaida ke ciki ba,wani ne na daban,addu'o'i ta min kamar yadda ta min lokacin da ta kaini gidan Lawal.
Sallama suka min na rakosu har wurin motar da zasu shiga ta kaisu tasha,ji nayi kamar na ɓarke da kuka ganin motar ta bar gidan,sun tafi sun barni kamar yadda suka barni wancan karon.
Hannun Zainab na riƙe muka koma tare,na shiga duba gidan komai ya min hatta fentin ɗakina saida Ya Bashir ya zaɓi kalar da nafi so,su Yaya ma sun cancaɗeni da kaya na kece raini kamar wata ƴar gwamna,ba abinda zance sai hamdala
LAWAL
"Wai Lawal me kake so ka maida kanka? Shikenan sai ka maida kanka sakarai akan wata mace, Saboda Zainab kake nema ka kashe kanka? Kamar itace autar mata?"
Da kallo kawai yabi Anty A'i ganin yadda ta zaƙalƙale tana masifa.Mama ce ta dubeta "Zainab ta cancanci duk wani namiji da ya rasata ya shiga wannan halin,kema ƴar nan sai dai in kinƙi gaskiya,amma kema kinsan a yanzu ba macen da zata yiwa namiji abin da Zainab ta yiwa Lawwali.Nima na faɗa mishi ya kwantar da hankalinshi,yanzu dai gwargwado yana cikin rufin asiri,nayi magana da Asabe zai je yaga Nusaiba ƴarta ɗinnan da mijinta ya rasu,yarinyace don iyakarta kamar Zainab ɗin,amma zamanka haka ba zai yu ba"
Ba don yaso ba sai don matsawar Mama yaje yaga Nusaiba,ba laifi tanada kyau,ƴaƴanta biyu ɗaya na hannunta ɗayan na hannun dagin mahaifin yaran.
Ba wata ƙarya ko bidi'a aka ɗaura auren Lawal da Nusaiba cikin ɗan ƙaramin lokaci kuma Amarya ta tare.
Da farko zaman gwanin sha'awa tana nunawa Safwan ƙauna duk da yadda yaron ke ja baya da ita,amma duk dai in Lawal na kusa to kamar ta hadiye shi.
Daga baya sai ta tsiri muzguna mishi idan Lawal ya fita,to suma ƴaƴan zamaninnan yanzu sun iya yau ko ka haifi yaro ya ka ƙarasa dashi bale kuma ɗan miji.
Tsaye tayi tana girgizar jiki"zaka tashi kaje kayi wanke-wanken nan ko sai ranka ya ɓaci?" ganin ya ƙyaleta yana ci gaba da rubutunshi a littafi yasa ta fizgo littafin tare da watsi da shi tana huci "Ni zaka mayar mahaukaciya?Ina magana kana ƙyaleni,idan uwarka ce zaka mata haka?"
Idanuwanshi da suka rine kamar wani babba ya ɗago yana kallonta "Karki ƙara zagin Mommyna" ya faɗa yana huci kamar zaki
"Idan na ƙara zagin nata dukana zaka yi"ta faɗa tana riƙe ƙugu tare da zare idonta
"If you repeat again,you will regret it" ya faɗa jikinshi na ɗaukar rawa tsaki tayi tare da nufar ɗakinta tana faɗin "Kai dai ka sani,kuma idan har zagina kayi ka zagi uwarka"
Bayan Isha'i yana kwance ɗakinsu,kewar Mommynshi yake ji,ita yake son gani,yayi kewarta,yayi kewar girkinta da komai ma nata.Idanuwanshi ya lumshe abin da ya baiwa hawayenshi damar zubowa.
"Ka zo mahaifinka na kiranka"ya tsinkayi muryar matannan da ya tsana.Sai da ya shiga toilet ya wanke fuskarshi sannan ya fito.
Wurinda mahaifinshi ke zaune ya isa tare da duƙawa yana gaida shi,amsawa yayi yana kallon yadda alamu ke nuna yayi kuka "Me ke damunka?"ya tambaya da kulawa
Ɗago kanshi yayi ya dubi mahaifinshi jin ya nuna mishi kulawa kwatankwacin yadda Mommynshi ke mishi "Ba komai"
Ajiyar zuciya ya sauke sannan yace "Me ya haɗaka da Mamarka tace ka zageta hakane ko ba hakane ba?"
Zabura tayi "Au wato ƙarya ma zan mishi kenan" hannu ya ɗaga mata "Ki barni inyi magana da shi don Allah,kai Safwan me ya faru"
Leɓonshi na ƙasa ya ciza alamun abun ya mishi zafi "Mommyna ta zaga Abba,kuma ni ba zaginta nayi ba kawai na gaya mata idan ta ƙara zagar min Mommy za ta yi nadama"
"Kinji ba,to me mahaifiyarshi ta miki da zaki zageta?"Shima ranshi ya ɓaci da jin maganar "Ba zan ɗauka ba,ki tsaya matsayinki karki ƙara zagar mishi uwa,aiki kuma idan zaki iya kiyi idan bazaki iya ba ki barshi,da me kike so ya ji? da karatu ko da aikinki"
Lawal ya shiga surfawa Nusaiba bala'i kamar zai daketa,tsaki ta buga tare da shigewa ɗakinta.
Shima tsaki yayi sannan ya saka hannunshi a aljihu ya ciro ƴar ƙaramar leda "Karɓi nan je ɗakinka kaci,tsirai ne na gani nace bari in kawo ma ka saka a bakinka"
Hannu biyu yasa ya karɓa yana godiya tare da tashi ya shige ɗakinshi.Da kallo Lawal ya bishi yana jin wata iriyar ƙaunar yaron ta musamman,duk wata ƙaunar da yake yiwa Zainab a yanzu ya tattarata ya mayar kan ƴaƴanta saboda ya san wannan itace kyautatawa ta ƙarshe da zai mata.
Kuyi haƙuri da wannan
RUMAISA'U SIDI
*AURE DA KARATU*
*NA*
*RUMAISA'U SIDI*
*FARAR ANIYA WRITERS*
*page 32*
Kwanakin da suka biyo baya kwanakine na farin cikin da suka shiga sahun manyan ranakun da bazan manta da su ba.Rayuwar Aure muka shimfiɗa a gidan irin ta soyayya da kuma girmama juna.
Yana riritani da kuma shagwaɓa ni kamar wata jaririya,duk abin da nake so kai tsaye zai min,duk kuma abin da ya san zai sakani farin ciki to kullum ƙoƙari yake ya min shi.
Ban fahimci Zubaida bata gidan ba sai da na kwana 3 a gidan,wanda a ƙa'ida ranar ne zata kama girki.
Zaune nake gaban mirrow ina ƙoƙarin ɗaure gashin kaina ya iso tare da tsayawa bayana,duƙowa yayi muna kallon juna ta madubin
"Wallahi ji nake kamar kar nayi fitannan"ya faɗa yana ɓata fuska.Murmushi na mishi "To ai ba wata doguwar tafiya ba ce"
Ajiyar Zuciya ya sauke tare da komawa bakin gadon ya zauna "Yau me za a dafa muna Baby?wallahi na ƙagu naci daddaɗan girkinki" Dakatawa nayi daga abin da nake sannan nace "Honey ka manta ne yau zan aje girki?"
Shiru ya min kamar baya ɗakin fahimtar baison maganar ne yasa nayi shiru nima har na kammala shirina ya riƙo hannuna muka je muka yi breakfast ɗin da gwaggo ke aiko muna kullum sannan na koma ɗaki na ɗauko mayafina don rakoshi.
Ɓangaren Gwaggo muka nufa har yanzu hannunshi na cikin nawa,ganin har mun shiga falon baida alamar sakin hannun yasa na shiga kiciniyar ƙwacewa daƙyar na samu na fizgeshi tare da isa inda Gwaggo take zaune na durƙusa ina gaidata.
Hannuna ta riƙo tare da zaunadda kusa da ita tana tambayata yadda na tashi "Allah ga bawanka,ba wanda ke tambayar yadda na tashi" Ya Bashir ya faɗa yana taɓe baki kamar yaro zai yi kuka
Hararar shi tayi "To dama wa zai tambayeka kai,kinci abinci?" ta ƙarasa tana maida akalar tambayarta wurina "Eh munci gwaggo,mun gode sosai Allah ya ƙara girma,ina Zainab"na faɗa ina raba idanuwa ganin ban ganta a falon ba
"Tana can ciki bacci take magani tasha jiya da zazzaɓi ta kwana" shiga muka yi tare a ɗakin,tana kwance sai baccinta take amma zazzaɓin ya sauka.
Ƙofa ya tunkara yana yiwa gwaggo sallama,tsaye nayi a tsakiyar falon ina jin kunyar bin bayanshi,lura da hakan da gwaggo ta yi tace "Je ki raka mijinki mana" a hankali na ja ƙafafuwana na bi bayanshi.
A bakin motar na same shi a tsaye,hararar wasa ya min "Ai na ɗauka ba za ki zo kimin sallama ba"shagwaɓe fuskata na yi kamar wata yarinya sannan nace "Kai ma kasan da kunya wallahi"
Taɓe bakinshi yayi "Kunyar me to" gambun motar na buɗe mishi ya shiga sannan na duƙa ta tagar motar ina kallonshi kamar yadda ya ke kallona.
Cikin wata murya da ni kaina bansanin ina da ita sai ina gabanshi nace "Ka kula min da kanka don Allah,ban lamunce ko ƙuda ya taɓa min kai ba har ka je ka dawo,kuma ban yarda ka dubi kowace mace ba"
Ajiyar zuciya ya sauke sannan yace "Na miki alƙawarin kula da kaina kamar yadda kike so,mata kuma ki daina kawo su a tunaninki daga kanki na daina banbancewa tsakanin mace da namiji"
Murmushi nayi har raina naji daɗi saboda a halin yanzu a yadda nake jin ƙaunar Ya Bashir ko Zubaida idan na tuna da ita ji nake ina ma ni kaɗai ya aura.
Wata irin rayuwar soyayya muke yi wadda ban taɓa tunanin za a sameta a irin ƙasashen mu na Hausawa ba,ba muda matsalar komai har na manta da shafin wata Zubaida rayuwar mu muke gwanin sha'awa.
Satin mu 3 sai ga Zubaida ta dawo,ina zaune ina lissafin kayana ta waya ta shigo falon ta matse jiki da wata fitted gown da ɓingilen mayafi a hannunta.
Kallo ɗaya na mata na ci gaba da abin da nake,tsaki ta buga sannan ta nuna ni "Na gargaɗe ki da shiga sha'anina da mijina baki ji ba saida kika shigo,to wallahi ina so ki sani sai kinyi nadama a lokacin da batada amfani,sai na nuna miki ba irin Zubaida ake shigar ma hanci ba,banza kawai mai ƙwacen miji"
Har tabar falon ban ɗago kai ba bale kuma na dubeta,wayata kawai nake latsawa ina ƙoƙarin kawadda ɓacin ran da ke tasomin.Maganar gaskiya banji daɗin dawowar Zubaida yanzu ba sam ban kawo yau zata dawo ba,ni sam na ma manta da shiginta.
Tsaki na buga tare da shigewa bedroom ɗina na kwanta,sallah kawai ke tadani.Ina jin lokacin da ya shigo falon yana kiran sunana.Runtse idanuwana nayi kamar mai bacci jin ya shigo ɗakin "Wai bacci kike Baby?" ya faɗa yana janye zanen da na rufa kaina.
A hankali na buɗe idanuwana na dube shi,ruɗewa yayi ya shiga taɓa wuyana "Lafiya dai Baby,ko bakida lafiya?"
Kaina na girgiza tare da sauka gadon na shige toilet na barshi nan zaune,koda na fito baya ɗakin komawa nayi na kwanta ina jin ko ɓangaren gwaggo ba zan iya shiga ba don banason ta tambaye ni meke damuna.
Ina nan kwance naji ƙarar sabuwar wayar da ya canja min,shine ke kiran ɗagawa nayi tare da ɗorata saman kunnena tambayata jikina yayi na amsa mishi da sauƙi "Za ki iya zuwa ɓangarena ko mu zo nan mu same ki?"
"A'a zan iya" na dakatar da shi,mayafi kawai. na ɗora akan doguwar rigar jikina,ɓangaren nashi yana nan tsakiyar namu ɓangaren.
Tura ƙofar falon nayi tare da sallama,suna zaune a falon sai wani shigewa jikinshi ta ke,kallo ɗaya na musu na kawadda kaina tare da samun kujera na zauna.
"Baby ya jikin da sauƙi dai ko" ya tambaya yana miƙomin wata leda da ke kusa da shi "Karɓi magani ne na karɓo miki ki samu kisha mu gani zuwa gobe da safe muje asibiti"karɓa nayi tare da yin godiya.
Tsaki Zubaida ta buga tare da miƙewa cikin iyayi tace "Darling in zuba maka abincin? Yau dai nima zaka ci girkina" hannu ya ɗaga mata "Ki bari mu kammala maganar da tasa na tara ku anan"
Nasiha ya muna tare da jan hankali in da daga ƙarshe ya kawo zancen rabon kwana inda ya tambayi meye ra'ayinmu,ni dai shiru nayi sai itace tayi magana "Yanzu dai Darling kaga sai an fara biyana kwanaki na da aka ci"
"Wane kwanaki kuma?" ya faɗa yana tsareta da ido kamar yadda nima nayi.Cikin rashin kunya tace "Kwanakina da ka ƙarawa wannan azzalumar mana ai bance na yafe ba"
Tsaki ya buga tare da kauda kanshi "Na rasa yaushe za kiyi hankali Zubaida,muna maganar kwanakin da zasu biyo bayane ba zancen ranka kwana ko wani waye,banson tashin hankali na riga na faɗa miki"
Bakinta ta murguɗa tare da kauda kanta,guntun murmushi nayi a raina ina ƙara raina sakarcin Zubaida tambayata yayi me na yanke nace duk abin da aka yanke banida matsala.Daga ƙarshe ita tace a barshi kwana biyu,sallama na mishi tare da barin ɗakin.
Kuka na ɓarke dashi bayan na zube kan gadona,birgima na shiga yi a kan gadon,ina jin gadon ya mun faɗi ji nake kamar zuciyata zata buga.Sunan Allah na shiga kira ina ƙoƙarin yaƙi da shaiɗaniyar zuciyata dake haskomin abin da bai kamata ba.
Ina nan kwance naji ƙarar wayata,ɗaga wa bayi batare da nasan mai kiran ba,a hankali naji muryarshi "Baby idan akwai abinci wurinki ki zubo min ki kawo min ɓangarena"
Har naji kamar nace babu amma sai naga rashin dacewar hakan shiyasa na amsa mishi da "To" tashi nayi na shirya mishi abincin da na dafa na kasa ci.
Ɓangaren nashi na nufa dashi tare da yin tsaye a wajen na kira shi "Ka buɗe ka karɓa" na faɗa bayan ya ɗaga kiran "Ki shigo a buɗe ta ke" ya amsamin shima
Ba don naso shigar ba na buɗe tare da shiga falon,yana zaune da remote a hannunshi sai kuma abincin da aka zuba wanda da alama ba'a ci cibi biyu a ciki ba gabanshi na dire kayan "Yawwa Baby Allah ya miki albarka"
Amsawa nayi da "Amin" ina ƙoƙarin tashi "Ki zuba min mana" ya dakatar da ni.
Zuba mishi nayi tare da janye wanda ke saman center table ɗin nakai gefe "Ki kaishi kitchen kawai"ya umarceni kaiwa nayi tare da wanke hannuna na fito wanda yayi daidai da fitowarta daga bedroom cikin shirin bacci.
Ƙugunta ta riƙe tana kallonshi "Kam balastinnnnnn wato nawa abincin ne ba zaka ci ba kenan"
*RUMAISA'U SIDI*✍️✍️✍️
*AURE DA KARATU*
*NA*
*RUMAISA'U SIDI*
*FARAR ANIYA WRITERS*
*page 33*
Takowa tayi har gabanshi tana kallon abincin da na zuba mishi,maida kallonta tayi a kaina ƙwalla na taruwa a idanuwanta "Yanzu saboda tsabar wulaƙanci ranar girkina zaki kawo mishi abinci"
Ji na nayi wani iri saboda nima sai yanzu nake jin ban kyauta ba domin kuwa idan nice ba zan ji daɗi ba duƙawa nayi da niyar tattara abincin "Kar ki taɓa komai,za ki iya tafiya"
A sanyaye na bar ɗakin,koda na