Showing 18001 words to 21000 words out of 57484 words
da shi naje tare da miƙa mishi " ga wannan yaya mu'azzam ne ya bani su lokacinda za a kawo ni gidannan ka siya mana koda taliya ce kafin ka samu"
Idanu ya ƙuramin sannan ya girgiza kanshi "bazan karɓi kuɗinki ba my zee saboda nauyin ciyarda ke akaina ya ke ba a kanki ba na fara tunanin ko in siyar da mota ta in siya mana kayan abinci saboda bazan juri ganinki a wani hali ba banaso kiyi nadama a aure na da kika yi"
Wata ƙaunarshi ce naji ta ƙara cikamin ruhi "duk abinda na mallaka naka ne nisful ka daina tunanin sayar da motarka insha Allah komai zai dai-daita a shirye nake da naci duk abinda ka kawo a gidannan kuma idan har kana ƙaunata kamar yanda kake faɗa to ka karɓi kuɗinnan"
Karɓa yayi ya shiga jujjuya kuɗin"ina ƙara gode ma Allah da ya bani ke a matsayin matata nagode sosai matar rufin asiri Allah ya nuna min nima na kyauta ta miki fiye da yanda kike min" wani daɗi ne ya lulleɓeni jin kyakkyar shaidar da nake samu daga mijina rakiya na yo mishi har tsakar gidan sannan na koma falo
Ina ƙoƙarin zama na ji wayata da ke chaji ta na ringing sance wayar nayi tare da duba mai kiran murmushine ya faɗaɗa a fuskata ganin number ummina na yawo akan screen ɗin da sauri na ɗaga ina karawa a kunne
"Umminaaaaaaaaaaa"naja sunan sosai ina jin kamar nayi tsuntsuwa na ganni gabanta saboda yanda nayi kewarta tun aurena banzo gida ba amsawa tayi na gaisheta a tsanake "magana nakeso na yi da ke" daga yanda naji tayi maganar nasan maganace mai muhimmanci gyaran murya tayi sannan ta ci gaba da magana "idan kina tare da mijinki ki keɓe magana za muyi kuma banaso kimin ƙarya"
"ba kowa tare da ni ummi" na faɗa cikin sanyayyar murya "yawwa jiya da dare abbanki ya siyo mana sarƙa da ni da ke nace bari in haɗe inda nake ajiyar sarƙoƙinmu amma abin mamaki koda naje ba sarƙarki a ciki bayan kuma nasan duk suna tare kuma nasan ba ta hannunki sannan idan ɓarawo ne bazai ɗauki sarƙa ɗaya ya bar saura ba shine nakeso ki gayamin gaskiya zuciyata tana gayamin kinsan wani abu akan lamarinnan"
Dakan lugude gabana keyi ni shaf na manta ma da na ɗau wata sarƙa" kar ki kuskura kimin ƙarya" ta katseni daga abinda nake shirin yi" ni naɗauka ummi" na gayamata gaskiya ganin ƙaryar ba abinda za ta tsinana min "me kika yi da ita" ta jefomin tambayar cikin taushin murya yanda bazan tsorata ba
"Lawal na baiwa yayi jari kuma yace ranta yayi da zaran ya samu zai maidomin kuɗina sai in siyi sarƙar" shiru tayi na mintota na ɗaukama ta kashe sai can tace "kin kyautawa kanki kuma nagode sosai" daga haka ta katse wayar tsorone ya shige ni don ga dukkan alamu fushi ta yi kuma nasan illar fushinta akaina kiranta na shiga yi amma ta ƙi dagawa
Kuka na shiga rerawa wata nadama na shigata number lawal na shiga nema saita muryata nayi jin ya ɗaga izini na nema inje gida ya tambaye ni lafiya na ce lafiya lau kawai naji ina kewar gidane yace in tafi amma kar in kai dare don ya yo mana siyayyar kayan abinci
Gani nayi gidan yamin nisa ko da na isa ko baba mai gadi da ke tsokanata bayan mun gaisa ban tsaya kulawa ba saida naje tsakiyar falon sannan nayi sallama "keee lafiyar ki" ya mubarak ya faɗa ganin yanda na shigo a hargitse kallo ɗaya na mishi na ƙarasa gaban ummi na zube guiwowina ƙasa hannuwana na ɗora akan cinyoyinta "don Allah ummi kiyi haƙuri kar kiyi fushi da ni" ba ta min magana ba sai ma ya mubarak da ta kalla "kaje kawai" magana zaiyi ta dakatar da shi "kaje nace"
"Don girman Allah ummi kiyi haƙuri wallahi fushinki akaina babbar matsala ce a rayuwata nasan nayi kuskure wallahi kuma bazan ƙaraba" janye hannuwana tayi daga jikinta sannan ta miƙe tana ƙoƙarin wucewa bedroom ɗinta ƙafafunta na riƙe ina kuka ina mata magiyar ta yafemin "Yanzu har aure ya miki daɗin da za ki ɗau dukiyarki ki bawa miji? namiji? namiji kike wa wannan rawar kan? ba baki nake miki ba zainab amma ina ji maki tsoron ranar da zai nuna miki butulcin ɗa namiji in za kisan ciwon kanki ki sa ni in kuma duk abinda kika mallaka za ki miƙawa lawal ɗauka ki bashi Allah ya bar ƙauna"
Na sha kuka na sha magiya kafin ta sauko hankalina bai kwanta ba saida naga ta haƙura sannan na yi shirin komawa gida ɓangaren yaya isma'il na shiga nayiwa anty nasma sallama sannan na wuce na yaya abbas ita ma na mata sallama sannan na ja motata na lula titi
Ko da na koma gida ya dawo da siyayyar da yace yayi katin ɗin taliya ne sai mai da kuma ƴan kayan magi sai da na gama dubawa sannan na dube shi ina so inyi magana kuma ina tsoron yayi fushi daurewa dai nayi nace "Nisful da ka sa ni shinkafa ka siyo ma na"
Wani kallo ya mini sannan yayi fuuuuu ya wuce ciki kayan na kwashe na kai kitchen sannan na wuce na same shi ɗaki waigowa yayi ya dakata daga ƙoƙarin cire rigar da yake yi" bari in gayamiki bazan ɗau wannan ɗabi'ar ba idan ke san don ki sakamin doka za ki bani kuɗinki to nagode ki riƙe abin ki"
Tun daga ranar taliyar ce ta zama abincinmu kuma bantaɓa yi mishi ƙorafi ba saboda ina tsoron yayi fushi bansan ya saida motarshi ba saida aka kwana biyu ban ganta ba na tambaye shi "Nisful lafiya kwana biyu banga motarka ba? ko lalacewa ta yi"
Wani kallo ya min "saboda an bani motar daga gidanku shiyasa kike sakamin ido a kanta? to na siyar ne? ko akwai magana" kallon mamaki na ke mishi "meyasa za ka siyar da motarka nisful? wallahi banji daɗi ba"
"Dole in siyarda mota in nemi kuɗi saboda na gaji da wulaƙancin mutumennan bazan ƙara komawa wurinshi ba" inaso inyi magana to amma ina tsoron abinda maganar za ta haifar
Gyara zamana nayi sannan na sako mishi maganar da yaya abbas ya kirani ya min kan karatuna yana gayamin ƙyaleni ne abba yayi ya ga iya gudun ruwana nima kuma sai na ji ina sha'awar karatun yanzu
"Nisful maganar KARATUNA ina so in koma makaranta" baya na ja ganin yanda ya wani zabura "makaranta kuma? ni sakarai ne da zan sakeki wasu mazan na kallonki? A'a wallahi ba da ni ba karatunnan dai ana yin shi ne don tara wani abun duniya to na miki alƙawarin nema har iyakar ƙarfina don na huce miki takaici "
Haka ya ci gaba da tsara ni har na yadda naga ba amfanin wani KARATU da zanyi ya sa na kira ummi nace mata yace zan koma amma sai na haihu kamar yanda ya tsaramin
su kuma jin maganar ciki sai suka jingine maganar karatu ashe ko mun sara bisa gaɓa domin lokacin ina ɗauke da cikin safwan da ko ni bansa ni ba
Uhmmmmm
AURE DA KARATU
NA
RUMAISA'U SIDI
Page 16
Ba mu amfana da komai ba cikin kuɗin motar da ya siyar, don ɗaukar kuɗin yayi, ya baiwa abokinshi wai ya jujjuya mishi su raba riba.Lokacin da ya gayamin haka, na gayamishi sam wannan ba dubara bace, amma ya nuna min ai mai amana ne.
Sai ga shi ya dawo ya na gayamin, kuɗi sun lalace na nuna mishi baiwa wani kuɗi da sunan ya ma sana'a ba mafita bace shi kuma ga yanda na lura sana'ar ce bazai iya ba ina mamakin yanda namiji ke ƙyamar sana'a to idan baiyi sana'a ba me zai yi?
In taƙaice miki sai da duk abinda na mallaka ya ƙare wurin cefanenmu tun ina yi har nazo na ka sa domin ko banida komai wallahi akwai ranar da muka kwanta haka nan ba mu ci komai ba saboda ni banida komai haka ma shi ga ciki na rame duk na fita hayyaci na gida ma na daina zuwa don duk abinda zai sa aga laifin lawal banason shi
Bikin anty halima da ya matso ya sa dole naje gida kusan firgicewa nayi yanda ummi da su yaya suka sakani gaba da tambayar meke damuna? bansan me zan ce musu ba kaitsaye yaya abbas ya turani mota sai asibiti gwaje-gwaje su kamin suka ce in rinƙa cin abinci mai gina jiki faɗa ya dingayi tun a mota yana gayamin ga abinda ake gudarmin
Kayan abinci ya siyamin da kuma kayan fruit ma su yawa shi ya maidani gida yana tambayata me ya hanani zuwa da motata? nace mishi kawai bazan uya tuƙi ba saida ya kawoni nazo futa ya ɗakko kuɗi masu yawa ya bani yace in sa mai wataƙila ya fahimci rashin mai ne yasa ban fita da ita ba
Lokacinda lawal ya ga kayan faɗa ya dingamin wai na je gidanmu nace ya barni da yunwa ta inda ya ke shiga ba tanan ya ke fita ba nidai bance mishi komai ba don abin ya fara kaini maƙura abin haushi kuma kayan da yake faɗa a kansu da shi aka cinye
Haka akayi bikin anty halima na shiga bikin duk a muzance yanda na lalace kamar ba ni ba cikin garinnan aka kai anty halima saboda mijinta ɗan sokoto ne kuma itama anan za ta ci gaba da aiki saboda har yaya isma'il ya samo mata aiki a inda yake aiki
Tun da na doshi watan haihuwata na fara mishi maganar ya kamata a rage siyayyar wasu abubuwan to nima ina faɗane kawai don ko cikina ban cikaba bale kuma akai ga ajiyar wasu kaya
A ranar da zan haifi safwan shi ya kaini asibiti da kayanshi aka rubuto kayan da ake buƙatar a siya abin baƙin ciki haka na kasance cikin wani hali har zuwa lokacinda ya kira gidanmu ya gayamusu ina asibiti
Faɗa yaya Abbas ya dingayi ganin asibitin da ya kawo ni ganin halinda na ke ciki yasa ya biya komi cikin ikon Allah sai ga shi na haifo santalelen ɗana
Tunda na haihu ba wani abu da ya fita daga aljihun lawal komai ƴan uwana ke yi ba abinda aka nema daga gareshi mahaifiyarshi sun zo da ƴan uwanshi
Sai daren suna aka kawo kayan barka kala huɗu ya min dukansu ƙanana sai jaririn kala goma ban wani damuba saboda duk yayyena har yaya mubarak ba wanda bai min sha tara ta arziki ba cikinsu na fantama na kuma fita kunya
Zamana gida sai gani na dawo hayyacina daga abbana har ummi wata kula suke ba ni sai gani na zama ƴar lukuta na yi wani kyau na musamman har banso inji ana maganar koma wa ta
Haka na koma gidan lawal muka ci gaba da gurgura rayuwar a haka ba wata sana'ar arziki da ya ke yi taimakon da nake samu daga yayyena da iyayena da shi muke amfani
Shekarar safwan uku na ƙara haihuwa na haifi Aysha (baiwar Allah) haihuwar aysha ko tsinke bai bamu ba daga ni har jaririyar daga ƙarshe ma samu na yayi da zancen zai ɗaga suna don bayada abin yankawa yarinya
Nayi kuka a ranar marar adadi wane irin wulaƙanci ne ka haihu ko abinda za'a yankawa ƴarka ya gagara to bale kuma wata sutura da zaka saka ga shi banida komai duk ɗan abinda na mallaka ya ƙare ga lawal da kuma gidanshi
Daga ƙarshe mahaifiyata na kira na gayamata halinda ake ciki daga gidanmu abin sunan Aysha ya fito da kayana da na jaririya ba abinda muka yi amfani da shi da ya fito daga lawal ko ƴan uwanshi
Aysha na da shekara ɗaya da wata uku Abbana ya rasu ciwon ciki na kwana guda ne ya zamo ajalinshi ina riƙe da hannunshi lokacinda yake kan gadon asibiti har ya rasu yana jaddada mana ya yafe muna sannan yana roƙon ummi da su yaya su kula da ni kar su barni nayi kukan rashin shi
Na shiga tashin hankali sosai saboda na shaƙu da abbana sosai fiye da tunaninki na daɗe ban dawo dai-dai ba saboda mutuwar ta taɓa ni
Lokacinda aka raba mana gado ummi hana tayi a damƙaminsu tace a ci gaba da juyamin su gidan da aka bani kuma a ka zuba ƴan haya
Haka na ci gaba da haƙuri da lawal yau ya bani gobe yace babu idan nayi magana kuma na yi laifi baƙin ciki ya min yawa na rasa ina zan saka kaina domin in ta ni ne abin mai sauƙine amma yaro sam baisan babu ba
Magana na mishi kan makarantar safwan tunda ya isa aiko ya tasomin da faɗa" Ana maganar abinci ina naga kuɗin kaishi makaranta in baso kike in haɗiye zuciya in mutu kan baƙin ciki ba da me zanji? na ga ai kema kinada kuɗinnan kije gida ki gaya mu su a baki wani abu ki sa ɗanki makaranta nasan dai ba za su hanaki ba ai wallahi ni kin bani mamaki in wata ce wallahi gadon nan da aka raba muku za ki samu abinda kika bani inja jari tunda kinga halinda mu ke ciki"
Da ido na bishi ina tambayar kaina "shin butulcin da ake faɗar maza na yi ne lawal ya fara nuna min"
Wani zuwa da nayi gida yaya Mu'azzam ya dawo mu ka je gaida shi ya Isma'il ke tambayata an saka safwan makaranta nace mishi A'a ya ɗauke shi suka fita
Kwana biyu sai ga uniform da komai ya kawo min yace an biya mishi komai ya fara zuwa ni ke kaishi na ɗakko shi saboda mahaifinshi yace baya da lokaci ba a wani daɗe sosai ba aka saka Aysha itama a sashen rainon yara
Ban taɓa zama da kowa na gayamishi matsala ta ba domin har lokacin banson inji ana kushe lawal a gabana ashe abin yana nan yana taɓani daga tsaye na fara rama ga cikin Amna wanda Allah ne kaɗai ya ƙaddaro za ta shigo duniya saboda kai tsaye ya nuna min shifa baya buƙatar haihuwar nan dame zaiji (kamar wani abin arziki ya ke mana)
Tun cikin bai isa haihuwa ba na fara kumburi duk na fita hayyaci na ga baƙin cikin da lawal ke ƙumsamin baya ganin tausayina ko kaɗan abincinma yanzu ya daina bani idan ina buƙatar abu saidai na kira ummi ita ma ganin kamar ina zubarwa lawal ƙima a wurinta na daina kiranta
Ba wata magana mai daɗi a tsakaninmu ba hali yarana su je wurinshi zai kora su kamar ba ƴaƴanshi ba babbar asibiti ta kuɗi inda ya isma'il ke jagoranta nan ya turani ya haɗani da anty halima ganin halinda nake ciki kowane lokaci zan iya haihuwa ga wannan kumburin da na yi duk halittata ta canja
Hannu suka nema asa cikin gaggawa a min cs a cire abinda ke cikina sai da aka gama komai aka ce kuma ba za'a taɓani ba saboda jini na ya hau sosai
Duk wanda ke ƙaunata ya tausayamin a wannan lokacin saboda ina a wani hali ne na rayuwa da mutuwa kwanana biyu asibiti sannan aka min cs aka cire shalelena Amna
Tunda aka sallame mu na wuce gidanmu acan nayi jegon amna ummi ke kula da ni da kuma anty halima wannan karon ma bayan abin suna ba abinda yayi shi ko kunya ba ya ji
Daga ummi har su yaya tambayata su ka shiga yi meke damuna? me na saka ma raina da har ya janyomin hawan jini? saboda hankalinsu ya tashi sosai da jin wannan labarin ɓoye musu na yi nace cikinne kawai ya zo da hakan kula da ni suka ci gaba da yi tare da siyomin tsadaddun magunguna
Da na tashi komawa suka haɗani da maƙuddan kuɗade suka ce inyi sana'a anty halima ta banu shawarar yin sana'ar laces da atamfofi da jakunkuna cikin iyawar ubangiji abin ya karɓeni sosai itama tana min talla a gurin abokanan aikinta nima gwargwado ina samu da wayar hannuna nake amfani na ke isar da sana'ata ga sauran mutane
Hakan baisa na tsira ba sai ga lawal ya ɗanƙaramin saki kan abinda ko alama baya da haƙƙi ko ikon yi.......................
Mu tara gobe
AURE DA KARATU
NA
RUMAISA'U SIDI
Page 17
Lamarin ya faru ne ranar wata juma'a bayan saukowa masallaci dama tun kafin ya tafi muka fara rigima da shi kan sai na daina sana'ar da nake yi ta waya don baisan da wa nake mu'amala ba abin ya ƙonamin rai sosai amma sai ban kulashi ba
Sai bayan juma'ar ya dawo falo ya zauna ya na girgiza ƙafarshia alamun rigima ya ke nema naje na kawo mishi abinci zan fara zuba mishi ya dakatar da ni "wai mahaukaci kika maida ni ne da tun ɗazu ina miki magana kin ƙyale ni? shikenan ni kin maida ni namijin hotiho banida wani amfani kina fira da duk wanda kika ga dama da sunan sana'a to wallahi na gaji"
Ajiyar zuciya na sauke ina kallonshi tare da zama ƙasan carpet ɗin falon "bansan me kake so ince ba nisf................."
"Bangane baki san abinda za kice ba kenan haukar banza na ke yi kinga malama aje wani nisful gefe na gaji da ana kirana wani nisful ana yaudarata yawwa magana ɗaya ce zan gayamiki wannan banzar sana'a dole a barta don bazan yarda a wulaƙantamin aure ba"
Nima cikin ɓacin ran da ya fara tasomin nake magana "wai da kake maganar darajar aurenka shin kamani kayi da cin amanarka kome? kuma meye laifin sana'ata? naga dai kafin in amfana da sana'ar nan sau uku kaida ƴaƴanka za ku amfana sau goma to miye kuma yanzu na kawo wani sabon al'amari? meyasa kai baka ƙaunar zaman lafiya? duk yanda na kai zuciyata nesa kan lamurranka