Showing 48001 words to 51000 words out of 57484 words
ɗinta ta zauna tana fuskantar ta "Meke faruwa ki gayamin"
Numfashi taja tare da ɗauke ƙwallar da ta tarammata a ido "Ina cikin matsala Anty,na rasa da wa zanyi magana in samu mafita,duk wanda na tunkara da matsalata abinda nake ganin bazai yu ba yake kawo min a matsayin mafita,shi ya sa nazo gare ki da fatan in samu warwarewar matsalata a wurinki Anty"ta ƙarasa tana ɓarkewa da kuka.
"Subhanallahi Zubaida me ya faru?Ki sanarda ni damuwar ki ni kuma na miki alƙawarin matuƙar inada dama zan samo miki mafita da yardar Allah"
Idanuwanta ta zuba mata sannan sannu a hankali ta fara jero mata halinda take ciki "Da farko dai Anty zan alaƙanta duk wata matsala da nake ciki da shigowar Zainab cikin rayuwar mijina a karo na biyu,kamar yadda kika sani Ya Bashir ya so Zainab a lokacinda take budurwa,rashin samunta yasa Anty tayiwa Abba magana akan ai gani nan,ba don Ya Bashir naso ba aka yi aurenmu.Duk da ba shi ya zaɓeni ba,amma ya zauna dani zama na amana,yana ƙoƙarin faranta min a koda yaushe,duk shirmen da zan mishi baya fushi dani.Rashin girkina bai canja da yadda ya saba yi min ba,saidai ya shaida min nayi ƙoƙari na koya ni kuma na gaya mishi bazan iyaba gaskiya.Dama kuma ni gani nake idan na roƙeshi abu baya saurin bani wannan yasa idan inason abu saidai naje na faɗawa mahaifiyarshi ta mishi magana ya bani,yasha faɗa min na daina yi mishi haka idan ina son abu na dinga faɗa mishi da kaina,ni kuma ganin kamar idan ita tayi magana yafi saurin bani yasa naƙi dainawa.Ana haka na samu cikin Zee,nasha gata a wannan lokacin daga shi har mahaifiyarshi da Abba ba wanda baya kula dani.Ƙauna suka nunawa cikin kamar me,haka ma mahaifiyata da duk wani masoyinmu.Cikin kuma ya sako min fushi da saurin faɗa wanda kai tsaye zan fara cin mutunci ko da kuwa da shi ne,kuma a gaban kowa.Sosai muka yi rigima lokacin da na haihu na samu ƴa mace,tun a asibitin ya faɗa mini yayi wa yarinya huɗu ba da suna ZAINAB a gaban kowa na hau rigima nace ni ban yarda ba,saboda sanin muhimmancin Zainab ɗin a wurinshi.Duk haukar da nayi wannan bai canja komai daga sunan da ya sakawa ƴarshi ba.Rago Anty ta siya da nufin canjawa yarinyar suna amma Daddy ya hana.Bayan haihuwar ne Anty ta samo min yara ƴammata biyu,ɗaya mai shara da girki,ɗayar kuma wadda zata riƙa kula da Zee,saboda ni ko sakamata pampers ban iya ba,mahaifinta ke saka mata,to bayan zuwan mai aikin sai komai ya koma hannunta.Kullum Ya Bashir na faɗa min na rage yawan ƙorafi,bayan kuma duk abinda nayi magana to tabbas naga an tauye min hakkine,kinga ko bazan zuba ido a tauye min hakki ba.Bayan tasawar Zee ne na sallami ɗayar mai aikin,na bar wadda zata ci gaba da kula da gidan da kuma girki,mun fara samun matsala da shine bayan ya min gargaɗin kar in ƙara tura mai aiki ta gyara mishi ɗakinshi ya fi son in gyara da kaina,ni kuma a gaskiya bazan iya ba.Na shiga tashin hankali lokacin da naji mutuwar auren Zainab,saboda nasan abinda ke tunkaro ni,ban ƙara gigicewa ba saida tazo garinnan naga yadda yabi ya ruɗe akanta,har kashedi na mata amma baiwar Allah nan ta kasa barmin mijina"ta tsagaita tana share hawayen idonta sannan ta ci gaba.
"Na roƙe shi kar yayi aurennan amma saida yayi,ina raye Ya Bashir ya auro Zainab ya kawota a cikin gidanshi,wanda a wannan lokacin ni ina gida bisa shawarar Anty Amina da tazo ta tafi da ni.Zamana gida ba abinda ya ƙaramin sai tashin hankali saboda biris da Ya Bashir yayi dani tun bayan komawata gida sau ɗaya yaje nace bazan koma ba daga nan bai ƙara dawowa ba.Ni da kaina na maida kaina ɗakina Anty bayan da naji Anty ta tubure akan sai Ya Bashir ya sakeni,ni kuma har ga Allah ina ƙaunar mijina.Ko da na dawo ɗin ma ba abinda na tsinta bayan takaici,saboda a fili Ya Bashir ke nuna kulawarshi ga Zainab,duk abinda tayi zai yaba,saɓanin ni da kullum banayin daidai,har video girki nayi downloading a wayata don in mishi nima in burgeshi amma da ya ci sai ya furzar ya kirata ta kawo mishi nata.Anty yanzu komai na yiwa Ya Bashir banyi daidai ba,komai nayi bana burgeshi,na rasa ya zanyi,har wata ƙawata tace nazo ta kaini wurin wani malami da yake bada taimako naƙi amincewa saboda ina tsoron faɗawa wata halakar.Abinda yasa nazo wurinki saboda kece mutum ta farko da ta fara ƙoƙarin nusar da ni akan gidana amma naƙi saurare,a yau nazo ina roƙon ki taimakamin Anty ki faɗa min yadda zan yi yaƙin ƙwato mijina a hannun Zainab" ta ƙarasa tana saukowa daga kan gadon ta zube gaban Anty tana rera kuka.
Hannunta Antyn ta kama tare da zaunar da ita unda ta tashi,fita tayi daga ɗakin,ba jimawa ta dawo da gorar ruwa a hannunta,tsiyaya ruwan tayi a kofi sannan ta miƙawa Zubaida.Karɓa tayi tashi tana sauke ajiyar zuciya.
Komawa Antyn tayi ta zauna tana kallon yadda Zubaida ke shan ruwan,tausayi ta bata har wata rama tayi alamun tana cikin damuwa sosai ga kishi da ke cinta.
"Da farko ina so ki janye alhakin shigar ki wannan halin akan kowa,ke kika cuci kanki Zubaida,duk abinda ya same ki ke kika ja,maganar gaskiya ma Bashir yayi haƙurin zama da ke tsawon wannan lokacin.Haba Zubby sai kace ba ƴar zamani ba,ke shikenan ba abinda kika iya sai yin ɗinki ki matse jiki,bayan gyaran jikin ma baki iya ba.Ace mace da mijinta Zubaida amma ace bakya gyara?To ina mace anan,bari in faɗa miki ba wai ki shiga toilet ki bugo wanka ki saka sutura mai tsada ne kawai gyara ba a'a,ke gyara dai da zai janyo miki daraja da kuma girmamawa a idon mai gida,taya miji zai miki abinda kike so bayan ke baki mishi abin da zai ji daɗi? Ɗan turarennan ma mai ƙamshi bakya sakawa Zubaida,ba wai sai kina wari zaki saka turare ba,ke da kanki idan kika saka turare zaki jiki cikin nishaɗi,to bakya yi Zubaida,magana mai daɗi wannan bata fitowa daga bakinki a lokacinda kike magana da mijinki,namiji da kike gani tamkar jariri haka yake,duk yadda kike ganin idan ya fito yana muzurai to zaki samu ƙaramar yarinya ke juyashi a cikin gida,da zarar kin san kanki,kina gyara kanki ta ko ina,kin iya magana mai siye hankalin ɗa namiji,kina girmama iyayenshi da ƴan uwanshi,to wallahi da izinin Allah zaki same shi a tafin hannunki.Irin ku ne mazajenku ke faɗawa tarkon matan waje,saboda ku na cikin kun kasa yi musu abinda na wajen ke musu.Kinada kyau Zubaida,kinada ƙira da komai ma,to meyasa da ƙuruciyarki kike nema ki kashe kanki?Sannan da kike maganar Zainab ta ƙwace miki miji,yo ai dole ta ƙwace tunda ta samu sakarar kishiya,kinyi zaune kina kuka,kin barmata mijin,wallahi nan gaba kaɗan idan baki gyara ba har dukanki sai yayi.Saboda shi namiji zai iya yi miki uzuri a lokacin da yake tare dake ke kaɗai,amma da zarar kun zama ku biyu to bazai ƙara yi miki uzuri ba saboda zai yi tunanin dama rainashi kika yi tunda ga wata halitta irinki na mishi,daga nan ne wulaƙanci zai shiga,idan kika cika ƙorafi ya sallame ki saboda yana ganin ko kin tafi ba wata damuwa zai yi ba tunda ga wata yanada" tsagaitawa tayi sannan ta tsiyaya ruwa tasha tana kallon Zubaida da ta mayar da hankali tana saurarenta.
"Abinda na fahimta manyan matsalolinki sune rashin gyaran jiki,rashin iya girki,rashin iya magana,da kuma rashin riƙe sirri,dukkan waƴannan abubuwane da rayuwar aure ke lalacewa matsawar aka samu ɗaya daga cikin waƴannan.Dole sai kin gyara,kin koyi girki,kinsan yadda zaki yi magana da mijinki,ba da kalar harshen da zakiyi magana da Amina za kiyi da mijinki ba,a'a muryar da kike amfani da ita idan kina tare da shi ta banbanta da wadda aka sanki da ita,kar ki kuskura muryarki tafi taki ɗagawa a lokacin da yake magana wannan haramunne,kar kiyi musu dashi,ko saɓani kuka samu kar kiyi ƙoƙarin fahimtar da shi a lokacinda yake cikin fushi,ki barshi sai ya huce tukunna sannan ki mishi bayani,kar ki ƙara kai ƙararshi wurin mahaifiyarshi ko taki mahaifiyar duka waƴannan biyun kuskurene babba.Ita dai mahaifiyarshi ƙimarki zata rage a idanuwanta,zata daina ganin girmanki za ta ga kamar kina tonawa ɗanta asirine a idon duniya.Mahaifiyarki kuma zata tsani mijinki zata ga kamar yana musguna miki,ke har ki manta ma da kunyi wani faɗa amma ita bazata manta ba zata ci gaba da kallonshi da wannan abun.Duk lokacinda ya kasance a rayuwar ma'aurata akwai third party to akwai matsala,kar ki kuskura ki bada wata kafa da third party zai shigo tsakaninku,duk wani saɓani da ya shiga tsakaninku ki rufe shi ki bari ku sasanta kanku,kar ki yarda wani ya fahimci akwai matsala a tsakaninku bale kuma har kishiya,wallahi dole ma Zainab ta rainaki"Anty ta ƙarasa tana buga tsaki tana jin kamar ta shaƙo wuyan Zubaida
"To yanzu yasan kin fito ko haka kawai kika fito"ta tambaya ganin kamar harda hauka ke cin Zubaidar.Kanta ta gyaɗa "Ya sani saida na kirashi na fito"
"Baya nan ne?"Anty ta tambaya kanta ta ƙara gyaɗawa "Eh ya rakata Sokoto,amma yace min yau yana hanya"hannu Anty ta buga a ƙirji tana salati "Yanzu mijinki na hanya ƴarnan amma kika biyo hanya kika zo? To idan ya dawo wurin wa zai sauka"ta faɗa tana riƙe haɓa.Shiru Zubaida tayi tana jin tausayin kanta
"Idan miji na hanya ba'a fita Zubby,kuma ki kwantarda hankalinki zan kaiki wurin gyaran jiki da turarukka masu ƙamshi zan kuma koya miki abinda ya samu na girki,In sha Allah sai kin ƙwato Bashir ɗinki a hannun Zainab,sai kin karkato hankalinshi ya dawo kanki,ke sai ya koma ko zama zaiyi sai ya tambayeki"ta ƙarasa tana ƴar dariya
Dariya Zubaida keyi itama tana share ƙwallar da ke mata zuba "Na gode sosai Anty,In sha Allah zan aje hankali in koya yadda ya kamata"
RUMAISA'U SIDI
*AURE DA KARATU*
*NA*
*RUMAISA'U SIDI*
*FARAR ANIYA WRITERS*
*Page 36*
Ƙara gyara zama Anty tayi tana fuskantar Zubaida "Ki kwantar da hankalinka da yardar Allah zan kaiki inda za a share miki hawayen, ki daga yanzu kin daina zubar da hawayen ki akan kishiya,kuma zaki ciri taki tuta a idon Bashir" wayarta ta ɗauko dake ajiye akan mirrow sannan ta ƙasa dubin Zubaida
"Zan haɗa ki da shahararriyar mai ingantattun magunguna da turarukannan wato MEERAH_B HERBS.A wurinta zaki samu duk abubuwan da ki ke buƙata,tsafta zata gyara ki da sahihai kuma ingantattun magungunan ta, har Amar'e take gyarawa ,ke uwar gidan ma ba'a barta a baya ba.Kin ganni nan lokacin da na haifi Marwan wurinta na siye kayan da naji daɗin su,nima wata ƙawata ce ta haɗani da ita,har yau ban daina sakawa wannan ƙawar tawa albarka ba kuma jima ban daina siyayya a wurinta ba.Kinga wannan tumbin da kika fara radawa sanadiyyar haihuwar Zauna,tsaf zai ɓata idan har kina amfani da magunguna ta.Maganin sanyi da na haihuwa duk tana yi.Don haka ki kwantar da hankalin ki"
Ajiyar zuciya Zubaida ta sauke "Na gode sosai Anty wallahi har naji daɗi" murmushi Antyn tayi "Yanzu zan kira ta zata haɗa miki kaya masu kyau" wats number ta lalubo ta dannawa Kira bugu biyu aka ɗaga
Cikin mutunta juna suka gaisa bayani ta mata akan kayan da take so a haɗa mata ta faɗa mata ba matsala.
"Ki saka number ta idan kika tashi ki dinga kiranta"
Wayar Zubaida ta ɗauka tana saka number da Anty ke karanto mata "08142800199.Wannan ita ce number MEERAH-B HERBS ki riƙa siyayya a wurinta za kiji daɗi"
Kaya Anty ta duba mata masu kyau ta haɗa mata "Kiyi amfani da wannan kafin naki su iso,don Allah Zubaida ki maida hankali,ki cire wannan sakarcin,kisan ciwon kanki.Idan muka bi daki daki kema zaki ciri tuta a idon Bashir"
Sauri-sauri ta dawo gidan,tana fatan wannan ya zamo silar warware war damuwarta.
Kitchen ta shiga bayan tayi download ɗin video yadda ake kallon.Step step ta dinga bin abin har ta samu ta kammala daƙar.
Toilet ta wuce ta feso wanka da wani sabulu da Anty ta haɗo mata a cikin kayan,turaren ta murza a jikinta tana jin wata mutuwa na shigar ta.Ƙamshin na daban ne,kayan ma na daban ne.
Kallon kanta tayi a madubi bayan ta gama kafa ɗaurin ɗan kwalin atamfar ta.Ita kanta ta san tayi kyau.
Turaren ta ƙara ɗaukowa ta fesa tana jujjuyawa gaban madubin.Wayarta ta ɗauka tare da fita falon, talabijin ta kunna sannan ta koma kan kujera ta ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya tana danna wayarta.
Bataji tsayuwar motar shi ba sai sallamar shi taji a bakin ƙofar,da sauri ta juya tare da tashi a hankali tana ƙawata fuskarsa da kyakkyawan murmushi.
Sanarwar yayi a wurin yana kallon ta,saboda irin kyaun da ta yi a cikin atamfar.Kallonta ya ke Yadda take takowa a hankali kamar mai tausayin ƙasa.
Ya shagala da kallon ta yaji tana mishi magana cikin wata sanyayyar Muryar da bai santa da ita ba"Sannu da zuwa Hubby"ta faɗa tana wani karairaya tare da zare jakar da ke hannunshi.
"Bismillah muje ko"ta faɗa tana yin gaba ganin yadda ya zuba mata ido.Ɗakinshi suka nufa kallon ɗakin yake shima duk da ba wani gyara na musamman aka mishi ba amma sai ƙamshi ya ke.
Toilet ta shige ba jimawa ta fito tare da samar da shi ga ruwan wanka can.Saitin zuciyarta ta dafe bayan ya shige,bata taɓa aza zata iya abinda Anty ta koyar da ita ba,amma ga dukkan alamu akwai nasara daga yadda taga ya fara canja wa yana bin ta da mayen kallo.
Koda ta zuba mishi abincin ma kallon mamaki yake mata yadda take mishi fira mai daɗi kuma cikin natsuwa.
Ba laifi tayi ƙoƙari wurin dafa abincin.Kallonta yayi bayan ta dawo daga kai kayan kitchen "Abincin yayi daɗi Babu,kin yi ƙoƙari sosai,haka ma wannan ƙamshin ya tafi dani sosai,wannan ma ya min kyau"ya faɗa tana shafa dogon gashinta da ta taje ta shafe da mayukka.
Murmushi tayi tare da riƙo hannunshi ɗaya"Na gode da yabawar ka,idan har zaka ci gaba da min hakan ni kuma zan ƙara ƙaimi don in ga na farantama.Don Allah Ya Bashir kar ka daina so na,na maka alƙawari zan canja,duk abinda baka so zan daina,Ni dai fatana ka soni fiye da yadda kake son Zainab"ta ƙarasa ƙwalla na taruwa a idanuwanta.
Hannunta ya ƙara damƙewa yana jin wani kalar tausayinta na ratsa shi,hannunshi yasa yana ɗauke ƙwallar da ta zubo mata "Bana son kina saka damuwa a ranki,ko kiyi tunanin bana sojoji,wallahi ina sonki Zubaida matsawar zaki ɗore a yadda na dawo na same ki yau,to zakiga zallar ƙauna"
Wani daɗi ne ya ratsa ta,yaushe rabon da ta sami irin waƴannan kalaman daga mijinta.Tun zuwan Zainab komai ya canja,tana fatan wannan ya zama silar warwarewar matsalolinta.
Wata kalar duniya take jinta a kwana ukun nan da tayi da mijinta ba Zainab tsakani.
Zaune take tsakiyar gadon tana kallon yadda yake taje sumar shi "Gaskiya Ya Bashir kana ji da suman nan taka kamar wani gaye"ta ƙarasa tana sakin dariya
Juyowa yayi ya dubeta tare da mata hararar wasa "Na san dai wata harda suman nan tawa ta jata ta ƙara soma,har take kuka idan bata aure ni ba zata mutu"ya ƙarasa yana mata gwalo.
Ɓata fuska tayi tare da doddoka ƙafarta akan gadon"Ai kaima haka kace"
Rakoshi tayi har bakin ƙofar,har ya saka ƙofarshi da niyyar fita sai kuma ya dakata tare da juyowa"Am nace Zubaida kar kiyi girki dani, kin san yau Zainab zata dawo"
Shiru tayi tana binshi da ido,tana jin kamar ta saki ihu.Daƙyar ta iya jawo ƙafafuwan ta ta dawo falon,zubewa tayi kan kujerar falon tare da sa hannu biyu ta dafe kanta "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un"ta samu ta faɗa daƙyar.Ba ta so Zainab ta dawo yanzu ba,taso ace ta samu koda sati ɗaya da mijinta amma wannan makirar bazata bari ba.
Number Anty ta dannawa Kira,gaidata tayi bayan ta ɗaga "Ya dai Zubaida,komai lafiya dai ko"
"Lafiya lau Anty,ina murna farin ciki na ya dawo gare ni amma matar nan bazata bari ba Anty,yanzu yake faɗa min wai yau matar nan zata dawo"
"To shine me?"Antyn ta tare numfashin ta "Ko baki san da ita ba?Dama ai kin san zata dawo,to miye abin damuwa?Ina magungunan da kika siya?"
"Suna nan Anty ina amfani da su,kuma suna da kyau sosai"
"Yawwa to ki ci gaba da harkokin gabanki kawai,matsawar zaki gyara to wallahi kin fi ƙarfin wata Zainab.Ke dai kawai ki ci gaba da gyara kuma ki dinga addu'a shine kawai"
Bayan la'asar taji shigowar Zainab ɗin,tana zaune kan kujerar ta ko ɗaga kanta bata yi ba.Jin Muryar Bashir yasa ta miƙe tare da fita tsakar gidan tana kallon shi yadda ya tattalo jakar kayan Zainab ɗin.
"Sannu Maman takwara mun same ku lafiya"Zainab ɗin ta faɗa tana duban Zubaida.Ƙyaleta tayi kamar bata ji ba tayi tsaye tare da riƙe ƙugu tana kallon Bashir
"Bakiji tana gaida ki ba"Bashir ɗin ya faɗa ganin kamar bata ji ba.
Tsaki ta buga sannan ta zubda yawu "Na jita,sannu ta min ko? To ni asibiti ce da zata min sannu?Ko kuma wata nakasa ta gani a jikina?"ta juya wurin Zainab ɗin tana nuna ta "Na gaya miki ki fita harkar,ba ruwana da ke,kiyi rayuwarki inyi tawa.Mijine dai kin aura ko? Kije ke da Allah,kuma wallahi duk wani hakki nawa da aka ci ban yafe ba"daga haka ta juya tare da komawa sashe ta.
*RUMAISA'U SIDI*✍️✍️✍️
*AURE DA KARATU*
*NA*
*RUMAISA'U SIDI*
*FARAR ANIYA WRITERS*
*Page 37*
Guntun murmushi na saki bayan ɓullewarta,Allah ya gani na tsorata da irin kyaun da naga jikinta yayi,ga wani fitinannen ƙamshi da ke fita a jikinta.
Amma daga lokacin da ta buɗe bakinta sai hankalina ya ɗan dawo.Shi ya jamin jakata har cikin gida,sannan ya