Showing 6001 words to 9000 words out of 57484 words
da lawal ba? inama bantaba saninshi ba? kai inama banyi aurennan ba (Astagfirullah) na shiga istigfari ganin damuwa na neman tabamin imani
Har dare ina fama da ciwon kan ko abinci su safwanne suka girka sosai nakejin ciwon ina kwance ya shigo yarana na zaune tare da ni kusa dani ya matso "zainab ko zamuje asibitinne" harara naso ballamishi to amma idanun sunki bada hadin kai dakyar na bude idona na dubi yarana "kuje ku kwanta na samu sauki" ina kallo suka fita suna waiwayena tausayi suka bani to yanzu idan mutuwa ta dauke ni ya zasu yi? anya kuwa wannan shakuwar baza ta zamo cutarwa a garesu ba lokacinda kasa za ta rufe idanuna? saboda yanzu na fara gazawa zuciyata ta fara nauyi komai yana nema ya kawo karshe
Cikin taushin murya ya sake fadin "ki daure muje asibitin ban dauka abin ya kai haka ba" ya fada yana kama hannuna ya shiga jeramin sannu da lallabani muje asibitin wata kila yana tsoron na mutu ace shi ya kasheni
"Mu bari dasafe sai muje idan Allah yasa zan kai safen"
Ban runtsaba saboda halinda nake ciki ga zuciyata da takemin zafi abin mamaki shima bai yi bacci ba duk lokacinda zan motsa to zanji yana jeramin sannu da safe ma shiya hadawa yara abin kari yace na shirya ya aje yara sai mu wuce asibitin saida ya sauke su muka wuce yana ta min iyayi nidai shiru nayi don ko magana nayi ba dadi
Kaina na sunkuyar ganin irin kallon da anty hauwa wacca take matsayin yayata saboda 'yar gwaggona ce kuma itace likitar da ke dubani tun daga kallon da take min nasan akwai matsala
"Ka jira ta a waje" ta fada batare da ta kalli lawal ba mikewa yayi tare da fita ta maida hankali gare ni mikewa tayi daga kan kujerar da take ta dawo wadda ke fuskantata (wadda mara lafiya ke zama) hannuwa na ta riko duka biyu tana kallona " Zainab dubi idona kiyi magana dani as your sister ki gayamin gaskiya zainab me kuma ke damunki yanzu da kike neman janyowa kanki wani ciwon? ki gayamin zainab wace damuwa ce wannan zainab? jininki ya hau sosai zainab sannan halinda kika jefa kanki ko wane lokaci za ki iya kamuwa da ciwon zuciya haba zainab akan namiji? namijinma lawal da ba wani abun kirki da za'a so shi saboda shi ki tuna yaranki zainab Ummi da mu 'yan uwanki wani hali za mu shiga idan wani abu ya sameki to gaskiya na gaji zanje in sami ummi kawai a raba wannan auren bazaiyu muna kallo rayuwarki ta salwanta saboda wani banzar lawal ba wannan karon dole ayita ta kare"
Hannuwanta na jimke ina zubarda hawaye " don Allah kiyi hakuri anty hauwa na miki alkawarin cire kowace irin damuwa a raina bazanso aurena ya mutu ba anty idan lawal ya sakeni to yarana ya rayuwarsu za ta kasance? wazai rike su kinaji lokacin yanda yaya abbas yayi rantsuwar baza su zauna gidanmu ba itama maman lawal din tace duk ya sakeni bazata rika mishi su ba to ina zan barsu? don Allah karki gayawa kowa na miki alkawarin daina tunani da kowace irin damuwa"
"Kinji abinda ke cutar da mata har su jefa kansu a wahala daga mace ta haihu da namiji to gani yake dole ta zauna da shi kodon wa'yannan yara akwai mata da yawa da ke fuskantar irin matsalarki a gidajen aurenki amma sun boye saboda tunanin makomar yaransu karki kashe kanki akan wannan zainab wannan karon ki yaki matsalar lawal daga zuciyarki"
Na sha fama kan na shawo kan anty hauwa so tayi in kwana asibitin na lallabata nace ta bani magani kawai ta bani magunguna tare da shawarwari
Kallonshi nayi "kaina na ciwo please" daga haka yayi shiru har muka isa gida bai kara magana ba
Ayi hakuri da wannan mura🤧
AURE DA KARATU
NA
RUMAISA SIDI
Page 6
Wani tattali na ke samu daga lawal kulawa yake bani ta musamman nida yarana nidai nawa idone kawai da kuma tsoron abinda zai biyo bayan kulawar hmmm Lawal ne fa lawal bazaimin haka a banza ba dole akwai wani abun
Su kansu yaran sunga canji daga gareshi kai maganar gaskiya lawal ya iya kulawar da zata sa ka manta dukkan sharrin da ya maka Allah ya bashi baiwar tsara zance da wannan ya dinga amfani wancan lokacin yana kassarani
Washe gari Alhamdulillah na samu sauki sosai ina jin lawal yana kiciniyar shirya yara "nanny lawal" na fada ina sauka kan gadon na shiga toilet wanka nayi nima don inason in daure in shiga makaranta
Bakin gadon na sameshi zaune bayan na fito daga wanka kallona yayi yana murmushi "Lallai my zee jiki yayi kyau" nima murmushin na mishi "naji sauki sosai" mikewa yayi yana nufar mirrow ya dau key din mota " zan aje yara makaranta" sauri na kara wurin shafa man a jikina ina fadin "don Allah jirani in karasa shiri nima zan shiga makaranta"
Kamar wanda na fadi mugun abu ya waigo da sauri " ba inda za kije sai kin kara jin sauki ko gobe ba zakije ba ko makarantar ai zaki karo ciwon kai ki bari sai kin kara samun sauki" daga haka ya juya ya bar gidan shiryawa nayi nafito falon nadau abin karin da suka ragamin a raina nace " lawal anga banza" har da su kwai aka soya
Gidan naji yamin shiru ba dadi in shiga daki in fito in shiga kitchen na rasa aikin da zanyi gaskiya lawal na kokari na zaman gida ina kitchen ina goge plates dina naji sallama fitowa nayi ina amsawa da fara'a na karaso falon maman haidar ce makociyata ta amana " maman haidar ce a gidannamu" itama da fara'a take kallona "ai dole kice haka tunda ke kin gujeni yaushe rabon da ki lekamu nima shiyasa na daina shigowa sai jiya haidar ke gayamin sun hadu da safwan a masallaci ya gayamishi bakida lafiya"
Zama nayi kusa da ita " wallahi banida lafiya maman haidar amma yanzu na samu sauki" gyalenta ta kwabe ta aje kan kujera kallonta nake ganin irin ramar da tayi "bakida lafiya ne kema" na tambaya ganin wata irin rama da tayi murmushin karfin hali tayi "A'a nikam lafiyata kalau me kika gani"
"Kamar ya lafiyarki kalau wai kinga ramar da kikayi? sannan zaki cemin lafiyarki kalau" hawaye naga sun cika mata ido sannan ta dubeni " ina cikin damuwa zainab na rasa wanda zan gayawa naji sanyi ina cikin damuwa zainab" ta karasa tana barkewa da kuka kyaleta nayi tayi kukan ko zata sami saukin abinda takeji a raina nace " kenan bani kadai ce keda damuwa ba" saida naga tayi kukan sannan na lallasheta " kiyi hakuri bilkisu wallahi yanzu rayuwar nan sai a hankali damuwa yau akwai ta cikin zukatan kowa" hannuna ta rike " damuwata ta banbanta da ta kowa zainab banida wanda zan gayawa damuwa ta zainab banida kowa garinnan ki taimaka ki gayamin abinda zanyi" duk na rude bantaba ganinta cikin wannan yanayin ba kullum zakaganta cikin fara'a sabanin ni da kullum da sabuwar chapter da zamu buga da lawal
Mijinta yana kaunarta wanda baya boye hakan a gaban kowa ko zaman minti 2 kayi dasu zaka shaida hakan "meke damunki bilkisu meya sameki"
"Zainab ke kinsan banida kowa garinnan in ba abban haidar ba ni 'yar kano ce aurene ya kawoni sokoto ba yanda amma bai dubi wannan ba tun bayan haihuwar khairat na fuskanci Kasim ya canja ya daina dawo mana weekend sai ya kwashe wata 2 bai dawo ba kuma idan ya dawo ba alamun wata damuwa a tare da shi na yayi kewarmu ko wani abu ina shan wahala zainab saboda ya riga ya sabamin da kulawarshi nashiga damuwa sosai da wannan sauyin nashi sai a 'yan watannin nan na fahimci wani ya daina damuwa dani sai yayi wata 2-3 bai damuba idan ma ya dawo bayada lokacinmu ta wayarshi kawai yake baya bari in taba wayarshi idan ma ya dawo baya wuce kwana 3 ya koma wai ashe wata yake tareda ita acan din na fahimci hakanne ranar da yabar wayarshi ya shiga wanka zuciya ta dinga tunzurani na duba naga abinda yake boyewa a wayar nayi nadama nayi danasanin duba wayar saboda na shiga tashin hankali a wannan ranar munyi rigima sosai dashi tsorona kar abinda yakewa 'yar mutane nima wata rana ayiwa 'yata amma sai ya shawo kaina da min alkawarin ya daina na yarda ganin irin rantsuwar da yake min ashe karyace bai dainaba kwatsam shekaranjiya na fara rashin lafiya shiryawa nayi naje asibiti ana dubani akace ina fama da infection wato ciwon SANYI fadar damuwar da nashiga bata bakine zainab na tabbata shi ya kwasomana wannan abun ina shan magani zainab amma ba wani sauki har yanzu ga mahaifiyarshi da ta sawoni gaba ta hanani zaman lafiya gani take kamar na mallakeshi haka take fada kullum to nagaji da bakinshi ya gayamin bazai iya rabuwa da yarinyar ba aurenta ma zaiyi na yanke shawarar kawai ya sakeni bazan zauna da shi ya kassaramin rayuwa ba ya sakeni kawai inje in nemi magani"
Dankari wato dai matsalar nan kowa da tashi "kiyi hakuri bilkisu ki daina kuka kasim bai kyauta ba kuma dole ki shiga damuwa insha Allah zamu samo maganin sanyi ba matsala bace zan gayamiki abubuwan da zakiyi amfani dasu amma ki dakatar da maganar saki yanzu har ki samu lafiya musan mafita mikewa nayi nashiga daki na dakko papper da biro na bata "Ki rubuta abubuwan da zan gayamiki yanzu shine maganin sanyi"
Ku biyoni a page na gaba don amfana da abubuwan da ke maganin sanyi✍️✍️✍️✍️
AURE DA KARATU
NA
RUMAISA SIDI
Page 7
INFECTION
Da farko dai kisani yar uwa ciwon Sanyi ciwone da bawata ya mace face tana tattare dashi , ko tasani koma bata Sani ba
Don haka ke mace kece ke janyo bayyanarsa a jikinki ko Kuma ki kwanta dashi yar uwa Mai daraja.
ABUBUWANDA KE HABAKA CIWON SANYI
1- Yawan tunanin saduwa
2-yawan amfani da Pant kala Daya ko shearing dinsa da wata
3-yawan saka Dan yasa ga al'aura yayin tsarki ko wankan haila
4-fara wanke Kashi kamin tsarki
5- Yawan tsarki da ruwan Sanyi
6-saka unders da sanyinsu
7-yawan shan yaji
8-saduwa lokacin fushi
9-fitsari a ban dakinda kowa kan shiga
10-yin amfani da hannu domin biyawa Kai bukata
KASHE - KASHEN CUTAR SANYI
1- Mai saka kai-kai ga al'aura
2-fitar wasu ruwa ga al'aura
3- Mai sanya warin al'aura
4- fitar wasu ruwa bayan kammala period
5- fitar wani gari ga al'aura
6- fitar kuraje ga al'aura
MAFITA
kisani cewa idan cutar tayimiki katutu to takan sa miji ya rinka tsanarki kila ma har yakai ga rabuwar aure (wa iyazu billah)
MAGANI
1-kisamu bawan lemun Yami , yabushe ,amma bushewar daki bata Rana ba
2- kisamu garin Dan Sudan
3-kisamu garin Jan goro
4- kisamu ruwan tumfafiya
5-kisamu zuma maras hadi
Duka kihade garin guri Daya kiyimasa Kashi biyu
Kashi Daya ki damashi da ruwan tumfafiyar kishafa ga al'aura idan zaki shiga bacci
Kashi Daya ki kwaba da zuma kina sha ( duk wadda take fama da wannan ciwon ta gwada yin amfani da wayannan don neman karin bayani
DM👇
08104445106)
Idan kikayi wannan yar uwa wallahi tallahi zakiije Dadi Kuma zaki zamo abar alfahari a wurin mijinki
"Idan kika kiyaye dukkan abubuwan da na gayamiki to insha Allah zaki rabu da infection ki kwantar da hankalinki ba dadi amma ya zamuyi"
Hawayenta ta share "wallahi maman Amna nagode sosai da na fita zan bayar asiyomin abubuwan da kika lissafa kuma zan kira Yaya Amina in gayamata wannan maganin itama tayi amfani dashi kai zainab wallahi har sha'awar rayuwarki nakeyi bakida damuwa kina zaune da babansu safwan lafiya bantaba jin ance an ganshi ya tare wata mace a waje ba hankalinki kwance wallahi Zainab tsorona Allah tsorona HIV kar ya kwaso mana mugun abu"
murmushin karfin hali na mata " ba wacca batada damuwa a gidan aurenta bilkisu duk wata macen akwai kalubalen da take fuskanta a gidanta saboda haka ki kwantadda hankalinki
Zaro ido tayi " duk yanda nake ganin zamannan naku yanzu kema kinada matsala zainab? naga baki rasa ci da sha ba sutura ma haka duk cikin zagayennan ba wanda zai nunamiki wani abu amma kice min kinada damuwa " wannan karonma murmushin na mata " bazaki ganeba bilkisu watakila damuwata tafi taki kuma duk ta gidan aurena ce bayan wa'yanda ke zagaye dani dangina ko nashi ba wanda yasan abinda ke wakana a tsakanina da Lawal ba amma ke zan baki labarina da kuma labarin zaman gidan lawal bawai zan gayamiki don inason fitar sirrina ba A'a zan gayamiki don kisan bake kadai ke fuskantar matsaloli ba"
Tashi nayi na shiga kitchen sauran cin-cin din da mukayi na zubo a plate na dauko lemo gora biyu da cups na azo a babban tire na dawo falon da su na aza a center table lemun na zuba mata a cup na mika mata " mu jik makoshi ko" karba tayi nima na zuba nawa na samu guri na zauna
Kamar yanda kika sani sunana Zainab Umar Gobirrr.............
Allah ya kaimu gobe lafiya
AURE DA KARATU
NA
RUMAISA SIDI
Page 8
Kamar yanda kika sani sunana ZAINAB UMAR GOBIR mahaifina haifaffen garin sabon birni ne wani yanki a cikin jihar sokoto kuma sanannen dan boko domin yana taka matakin proff ne su biyu iyayensu suka haifa daga shi babana UMAR sai kanwarshi khadija mahaifiyata ma 'yar asalin jihar sokoto ce auren hadi aka musu da babana saboda iyayensu aminan juna ne Itama mahaifiyata 'yar bokoce domin a gidan mijinta ta hada digreen ta na biyu
Mu biyar iyayenmu suka haifa kuma ni kadaice mace a cikinsu yaya isma'il shine babba kuma kwararren likita ne yanada mata daya anty nasma da kuma 'ya'ya biyu sai yaya Abbas shine mai zafin zuciya a gidanmu yanada fada sosai shi kuma lecturer ne a usmanu dan fodiyo university shima yanada mata anty yasmin da yara uku sai yaya mu'azzam shi ma yanada mata daya da yaro daya kuma yana aiki da gidan man NNPC sai yaya Mubarak shi kuma soja ne yana ibadan sai kuma ni shalelen abba da ummi
Kasancewata nikadai mace yasa na taso cikin gata da kulawa ta iyaye da kuma yayye gata na musamman nake samu a gidanmu ba abinda na nema na rasa kai hatta gwaggona da take aure a kaduna to duk lokacinda za tazo ita da yaranta yaya bashir da kuma anty halima to suma burinsu su sakani farinciki zan iya cemiki nice farincikin gidanmu gaba daya bansan yanda zan misalta miki kaunar da nake samu daga gidanmu ba wallahi bansani ba
Tun lokacin kuruciya nakeda burin yin karatun masscom inaso sosai sanin burina iyayena da 'yan uwana suke kara bani kwarin guiwa duk da ba haka suka so ba burin abbana nayi karatun likita hakama 'yan uwana lokacinda yaya abbas yaji karatun jarida nakeso nayi fada ya dingamin na bazan yishi ba na tsorata sosai kuma naji karatun yana neman fitarmun arai saboda ana nema a dakushemin burina saboda a lokacin nake rubuta jarabawar fita daga secondry saida babanmu ya taka mishi birki da gayamishi a barni nayi ra'ayina tunda shi nake kauna
Banida kawa sama da mahaifiyata da ita nake shawara hakama yayyena komai tare mukeyi idan fita nayi saurayi ya biyoni ita zan fara gayawa ke zan iya cemiki a wurin mahaifiyata na koyi komai ta sakani a jikinta sosai ta yanda kaitsaye zata gane gaskiyata ko akasin haka
RAYUWATA ta fara canzawa ne bayan haduwata da lawal dan wanka kuma dan kwalisa saurayi irinsu lawal ne akewa lakabi da (bakyau gareku ba shiga rai) mun hadu dashi ne bayan kammala secondry dina a bikin yayar kawata hafsa wankan lawal ne ya jani na kulashi a lokacinda ya fara min magana cikin yanga na tsaya na saurareshi bayan tsayuwarmu kuma labari ya sauya
" banga laifinki ba don kinki kulani a karon farko domin kin cancanci hakan kyakkyawa saidai ina rokon don girman Allah ki aramin koda minti 3 ne cikin lokacinki" cikin wata sabuwar yangar da naji tana tasomin na fara magana "ina jinka minti 2 na baka saboda inaso in koma gida da wuri" tsayuwarshi ya gyara "nagode sosai Beauty tun lokacinda kika shigo idona ya sauka akanki ganin shigowarki na kara godewa Allah da ya sanya ina cikin wayanda aka gayyata a bikinnan" kallonshi nayi "saboda me?"
"Saboda na hadu da beauty wanda bansa ran haka ba" kallon wayata nayi duk da yanda zuciyata ke ingizani da son sauraren yanda yake fitarda sautin kalamai kamar wani mawaki "zan wuce lokacinka ya cika" daga haka na fara tafiya har na isa wurin motata shi ya budemin na shiga " kiyi tuki a hankali beauty Allah ya tsaremin ke ya kaiki lafiya a gaida mommy ace sabon danta na gaishe ta" motata na rufe na shiga kokarin kunnata ba don wulakanci ba sai don yanda naji zuciyata na karbar sabon sako daga wannan mai zazzakan kalaman Ina tuki ina tunani to shi haka ake soyayyar? kofa number ta bai nema ba duk da bana raba number ta amma ina jin da ya tambaya shi zan bashi
A bakin tangamemin get din gidanmu na shiga doka horn da sauri aka shiga wangalemin shi sauke glass nayi ina wa dattijon mai gadin namu murmush " barka da dawowa shalele kuma farincikin gidan gaba daya"
"barka da aiki baba" shima da murmushin a fuskanshi yake fadin"Allah ya huce gajiya" amsawa nayi da "Amin tare da wucewa da motata na kaita ma'ajiyar motocin gidan kashe motar nayi tareda fitowa farinciki naji ya cikamin zuciya ganin motar yaya bashir a gidan sauri-sauri na karasa falon tareda kwalla mishi kira shima kamar kullum da murmushi a fuskarshi ya mike yana mini waka kuma yana tafi lokaci daya "ga shalelen abba ga shalelen ummi kai ga shalelen gwaggo kuma