Showing 27001 words to 30000 words out of 57484 words

Chapter 10 - AURE DA KARATU Book Complete Rumaisa Sidi.txt

26 Jan 2025

6692

gurgura rayuwata da ƴan yarana duk da mijina ya na bani amma dole sai na ƙara saboda ba ya bamu abin da zai wadace mu,wallahi idan na ce zan riƙe su na tauye kaina.Ni da za ka ji shawarata da ka kaisu wurin mahaifiyar su kawai don ban tunanin za ka samu mai riƙe ma su a ɓangarenka.Ka na kallon halin da Mariya ta ke ciki,Allah ya haɗa ta da maƙetacin miji ba ya bata abinci sai dai ta nema ta ci,ni dai shawarar da zan baka ka miƙa su ga Zainab"




Tafe ya ke yana tunani daga jiya zuwa yau ya tsinci kanshi a halin ƙaƙa ni ka yi ga shi sai yawo ya ke da yara kowa ya ƙi amsa a fili yace "Ke ki ka ja Zainab,da baki tunzura ni ba da yanzu kina nan tare da ƴaƴanki"




*MAMA*


Bayan wucewar Lawal hankalinta ka sa kwanciya yayi wallahi tayi baƙin cikin wannan asara da Lawal ya tabka.Wayarta ta jawo ta shiga neman layin Ummi mahaifiyar Zainab bugu uku ta ɗaga,gaisawa suka yi cikin mutunta juna




"Hajiya ashe abin da ya faru kenan,wallahi ban sani ba yanzu ya zo da yara ya ke faɗa min.Don Allah ku yi haƙuri wallahi ban ji daɗin wannan al'amari ba sam"




"Ba komai Hajiya ai dama aure rai ne da shi,zaman su ya riga ya ƙare sai dai dukansu mu yi mu su fatan alkhairi"




Haƙuri Mama ta ci gaba da bawa Ummi kamar ita ta yi sakin sai da su ka yi sallama sannan Ummi tace






"Am ni ko nace Hajiya idan ba damuwa don Allah ina neman wata alfarma a wurinki"




"Wace alfarma Hajiya"




"Don Allah ina so idan ba damuwa a bata yaran ta riƙe idan kuma ba zai yarda ba ko da ƙaramar ce ta dawo hannunta"
















*RUMAISA'U SIDI*✍️✍️✍️
08104445106






*AURE DA KARATU*


*NA*


*RUMAISA'U SIDI*


*FARAR ANIYA WRITERS*




*Page 21*




Numfashi Mama ta sauke "Kar ki damu Hajiya In sha Allah ba matsala,zan yi magana da shi" daga haka suka yi sallama.






*LAWAL*




Kukan Amna ke ƙara ruɗashi tana kiran Mommynta.Tsawa ya buga mata a karo na barkatai amma ko gezau ba ta yi ba.Kanshi ya dafe ya na jin kamar shima yayi ta ihun ina zai saka kanshi? tunda suka dawo gidan ya ke tare da su.




Ko abinci farar shinkafa kawai ya dafa musu saboda ita kaɗai ya iya itama kuma da ace babu shinkafa a kitchen ɗin da bai san yadda zai yi da yaran ba.Don bayada ko sisi dama da kuɗin Mama ya ke fantamawa to suma ƙalilan su ka rage kuma ta karɓe ba ya da wata madafa yanzu wani sashe na zuciyarshi yace "Yanzu da Zainab na nan da ita zata yi komai"




Saurin kawadda tunanin yayi don sam ba ya son ya na tunawa da wata Zainab ballantana har yaji a ranshi ta na tare mishi wani abin.




Wayarshi yaji ta na ƙara ɗagawa yayi tare da karawa a kunnenshi "Mama barka da dare" ya gaidata cikin girmamawa kamar yadda ya saba kullum




"Ina su Safwan?Ka ba su abinci? Kallonsu yayi sannan yace


"Ga su nan Mama kuma sun ci abinci"




"Yayi kyau ina so gobe ka ɗau Amna ka kaita wurin mahaifiyar ta sauran kuma ka riƙe su"




"Gaskiya Mama ni bazan iya baiwa Zainab ɗana ko ɗaya ba,zan iya riƙe abina"




"Za ka iya riƙesu amma ka bar mata ragamar su? Banson shirme umarni na ke baka ka kaiwa Zainab yarinyar nan,idan kuma ba haka ba wallahi duk abin da na maka kai kaja" Daga haka ta katse wayarta goshinshi ya shiga murzawa.Sam ba haka ya so ba don bayason Zainab ta yi tunanin ko ya kasa da yaranne,dama haka ta ke gani kullum ,ranar ma bai yi wani baccin kirki ba.




Tunda Asuba yaran suka hana mishi bacci saboda Zainab ta riga ta saba musu da tashin Asuba dole ba don yayi niyya ba shima ya tashi yayi sallah.




Kamar jiya yau ma ruwan da suga ya dafa Safwan da Aysha kuma suka shirya Amna.Yau ma ƙin shan ruwan su ka yi dole ya fitar da ƴar ɗari biyun da ta rage mishi a aljihu ya baiwa Safwan yace ya karɓo madara ta naira 50 wani kallo Safwan ɗin ya mishi "Abba tun yaushe aka daina saida madarar naira 50? Sai dai ɗari,ita ma wallahi ko Amna ba za ta yiwa shayi ba"




Zabura yayi "Bani kuɗina,in za ku sha haka kusha in ba zaku sha haka ba ku bari"




Haka suka yi shayin da Madarar naira ɗari abu kamar ruwan banza haka suka sha shayin ba don daɗi ba.Gidan ya kulle sannan yace su jirashi ya tunkari wurin mai shagon da yake zama "Laminu don Allah ɗari biyar za ka ranta min in kai su Safwan makaranta"




Wani kallo ya mishi "Da me za ka biya ni idan na ranta ma? Da shekarunka ko da ƙaton kanka? To bari kaji wallahi dama jiranka na ke inga kana da kunya ko ba ka da ita? to na gani don in banda rashin kunya banga dalilin da zai kawo ka wurina rancen kuɗi ba bayan ina binka kuɗi sun kai dubu biyar"




Ran Lawal ya kai ƙololuwa wurin ɓaci "Kar ka faɗa mini magana malam,kuma yadda ka samu kuɗinnan nima zan samu da yardar Allah"




"kana zaunen za ka samu? Ko kuɗin fiffike ne da su da zasu sauka kanka? To bari ka ji bazan bayar ba" Fuuuuuu Lawal ya bar wurin ya na ji kamar ya kashe kanshi ya huta don baƙin cikin wannan tozarcin da Laminu ya mishi




"Haba Laminu bai dace ka mishi haka ba,ina laifin wanda ya zo neman wani taimako a wurinka da tunanin za ka taimaka mi shi amma sai ka mishi haka,bai dace ba sam kuma banji daɗi ba" wani da yazo siyayya a shagon ya faɗa






Tsaki Laminu yayi "ƙyale shi kawai Aminu,haka ya ke kullum shi dai a ranta mishi,ko kaɗan bai san zafin neman kuɗi ba yana kwance matar shi ke nema ta ciyadda shi da ƴaƴanshi.Ba ya da aiki sai rance kuma bayada abin biya don ba wata sana'a ya ke ba duk sana'ar da ka nuna mishi zai nuna ta mishi ƙanƙanta"




Kuɗi Aminu ya fitar daga aljihunshi "Nawa ka ke binshi?




"Dubu biyar da ɗari huɗu"


Kuɗin ya bashi sannan ya fita daga shagon.A bakin titi ya samu Lawal a tsaye riƙe da hannun Amna sauran yaran na gefenshi hannu ya bashi su ka gaisa sannan ya fitar da kuɗi dubu biyu daga aljihunshi "Gashi Malam Lawal a siyawa ƴan makaranta alawa,shima mai shagon ba sai ka bashi kuɗin ba na bashi.Kuma ina roƙonka don Allah ka tashi ka nema ko don future ɗin yarannan"




Godiya ya mishi sannan ya samu adaidaita suka shiga ya sauke yaran makaranta sannan ya wuce gida wurin Mama










Kuyi haƙuri da wannan












Wallahi yau saboda farin cikin ku kawai na yi typing ɗinnan, Ina muku ƙauna lodi-lodi










*RUMAISA SIDI*
*08104445106*




*AURE DA KARATU*


*NA*


*RUMAISA'U SIDI*




*FARAR ANIYA WRITERS*




*Page 22*




*ZAINAB*




Wani sanyi na ke ji a cikin raina matsalar rashin yarana ne kawai a gabana,duk wani ƙunci da nake ji akan mutuwar aure na ya kau saboda na mayadda hankalina ga addu'a abin da na yi sakaci tun farko.




Idan ƙuncin Lawal ya sako ni gaba maimakon na na tashi na gayawa Allah matsalata, sai dai na shige ɗaki na dinga kuka.Amma yanzu In sha Allah wannan ya kau,zan yaƙi matsalata da ƙarfin addu'a da yardar Allah.




Tsaf na shirya domin ina so yau in shiga makaranta a falo na sami ummi tare da yi mata sallama.




Ina tuƙi naji wayata ta yi ƙara ban ɗauka ba saboda akwai ni da tsoro in dai har ina tuƙi to bana ɗaga waya sai in wayar daga Ummi ne ko su Yaya to shine zan yi parking sannan in ɗaga.




Sai da na isa makarantar ban fita daga mota ba na duba ashe Hafsat ce ƙawata ta amana murmushi na yi tare da danna mata kira




"Uwar gida a gidan Dr"




"Kuma Amarya ba,Faɗi ki ƙara nice dai ba wata" dariya na yi "Allah ya shirya ki,na ga kiranki ina tuƙi"




"Eh wallahi kwana biyu na jiki shiru,ya su Safwan"




Numfashi na sauke "Su Safwan suna can tare da mahaifinsu"




"Ban gane ba, to ke kina ina?




"Ina makaranta Hafsat bari idan na koma gida zan kiraki mu yi magana"




Sallama na yi da ita sannan na wuce in da muke ɗaukar darasi.




Sai da na koma gida na kira Hafsat ina faɗa mata abin da ya faru


"Amma wallahi mutuminnan ya ji daɗin shi,ki kwantar da hankalinki In sha Allah hakan shine mafi alkhairi a gare ki,Ki na kammala idda za ki samo mana wani handsome.Allah na tuba ban da ma ƙaddarar aure ai ke ba sa'ar shi ba ce"






"Ni fa yanzu Hafsat na cire wani aure a raina,ki dubi ko Lawal yadda muka buga soyayya da shi,amma dubi yadda abin ya ƙare.Ni dai kawai karatuna na ke so na kammala"




Tsaki Hafsat ta buga "To saboda Lawal za ki cire hope ɗin miji na gari? Ayi sha'ani kawai Hajiyata.In sha Allah kwanannan zamu shigo sokoto da na dawo za ki ganni"




Wuraren ƙarfe 5:00 sai ga Amna ya kawo tare da kayanta.Bai shigo gidan ba Baba mai gadi ne ya shigo da ita,na yi farin ciki sosai da dawowar Amna wurina duk da dukansu na so,saboda bansan ya rayuwar su zata kasance ba.




Da dare muna tare Amna na bani labarin ruwan da suka sha a matsayin breakfast na tausaya musu sosai shi ya sa da safe da zan kaita makaranta na dafa abinci har su Aysha.




Ko da na isa makaranta su Safwan ba su je ba parking nayi ina jiran zuwan su.Sai 8:30 sannan ya shigo kamar wani almajiri ya na jaye da hannun Aysha Safwan na gefen shi.Har yaran suka shiga ina kallonsu sai bayan sun wuce nima na dawo.














Kuyi haƙuri yau biki muke yi ku karanta wannan kafin gobe








*Na gode sosai*






*RUMAISA'U SIDI✍️✍️✍️*






*AURE DA KARATU*

*NA*


*RUMAISA'U SIDI*




*FARAR ANIYA WRITERS*






*Page 23*






Tsaftataccen zawarci na keyi saboda sam Ummi ba ta bari na yi wata shiga da bata kamata ba,duk abin da nasan bai kama ce ni ba ban yin shi.




A kwana a tashi har na kammala iddata na ci gaba da sha'ani na,yarana suna zuwa duk lokacin da suka buƙaci hakan sai dai ba yanda nakeso na ke ganin su ba,daƙyar su ke komawa idan su ka zo.




A kwanakinnan duk fitar da zanyi to sai wani ya biyo ni,tun ina damuwa har na ƙyalesu na shiga sabgata don ni yanzu lamarin rijalu tsoro ya ke bani.Musamman wani maƙale matan lecturer abokin ya Abbas da ya ke damuwata.Ni dai saidai in saurare shi kawai domin ni yanzu kalaman soyayya sun daina tasiri a zuciyata.




Yajin aikin da aka tafi a makarantar mu yasa na yi shirin zuwa Kaduna wurin Gwaggo na.Wurin Ummi na bar Amna saboda su basu yi hutu ba.Na so inje da ita to amma su ma suna gab da fara exam.




Driver aka haɗa ni da shi saboda Ya Abbas yace bai yarda na yi tuƙi har Kaduna ba.




Cikin zumuɗi na shiga falon ina ƙwala kiran Gwaggona "Miƙewa ta yi daga zaunen da take da wannan murmushin ƙauna da ke kasancewa a fuskarta duk lokacin da muke tare hannuwanta ta buɗe min alamar nazo gareta.




Da sauri na ƙarasa tare da shigewa jikinta ina jin wata ƙaunar ta ta musamman "Tun ɗazu nake dakon isowar ki,yayanki ma da wuri ya dawo office yana jiran isowar ki"




Sakin ta nayi ina raba idona a falon "To ina Yayan,shine kuma bai jira ni ba?


Hannuna ta ja ta kaini ga kujera "Yanzunnan ya shiga sashenshi,amma tunda ya san kina hanya yanzu zai dawo"




Kitchen ta wuce bata jima ba sai ga ta tafito tare da mai aikin ta,kaya aka shiga jerawa a gabana kamar wata sarauniya.




Shagwaɓe fuska na yi "Gwaggo hutawa zan fara yi sannan in ci abinci,wallahi bacci na ke ji"




Hararata ta yi "Zaman awa nawa kika yi? kisha ko ruwane sannan ki je kiyi wanka kizo ki ci abinci"




Lemun da ta zuba min na kurɓa tare da sanar da ita a kaiwa driver ahinci yana waje don juyawa zai yi.




Ɗakin da zan sauka ta kaini,komai an gyare tsaf.Wanka na yi tare da ɗauro alwala kaya na saka mara nauyi.Gyara kwanciyata nayi kan daddumar da nayi sallah ina jin yadda ƙassan jikina ke amsawa na gaji sosai.




Wayata na tuna da ita,tashi nayi tare da buɗa hand bag ɗita na ɗakko.Missed calls na samu na Ummi da su Yaya bansan me ya hanani jin ringing ɗin wayar ba.




Number Ummi na danna "Kin kyauta Zainab,wato daga zuwa wurin dije har kin manta da ni ko?




Zama na yi gefen gadon ina bata amsa "Haba dai Ummina,kema kin san ba yadda za'a yi in manta da ke koda na second ɗaya.Ba uwa irinki ake mantawa ba Ummin Zainab"




Ina jin sautin murmushinta ta wayar "Allah ya shirya min ke Zainab,kun sauka lafiya ina dijen?




"Lafiya lau muka sauka Ummi,gwaggo ma tana lafiya" na faɗa ina kallon Gwaggo da ta shigo ɗakin.Matsowa ta yi kusa dani suka gaisa da Ummi tana tsokanar ta na har ta fara kewata.




Jin Ummi na neman kashe waya yasa na cire kunya na tambayeta Amna




"To rasa kunya,ƴar ki na wurin su Nihal ki kwantar da hankalinki ko kewarki ma bata yi ba" Sallama muka yi tana jaddadamin na kira yayyena sun damu da rashin ji na" Sai da na kira su muka gaisa sannan na fita falon.




A falon na sami Yaya Bashir da Gwaggo da kuma Sister Zubaida matar Yaya Bashir




"Na yi fushi tunda sai yanzu za ka zo tarbata"




Hararata yayi "Haka ma zaki ce,bayan kinsa na baro office tun ban tashi dawowa ba,hala dai tata drivern yayi?




Dariya na yi sannan na dubi Matar tashi "Sannu Anty Zubaida,Na same ku lafiya,ina Takwara ta?




Abin mamaki sai naga ta ɗauke kanta duk uwayen tambayoyinnan da na mata cemin kawai ta yi "Lafiya" daga haka ta rufe bakinta gam.




Zama na yi kan kujera,miƙewa naga Ya Bashir yayi ya fara ƙoƙarin haɗamin abinci "Wai me zaka yi?




Na tambaye shi ganin abinda ya ke shirin yi " Abin da annabi ya umarce mu da muyi,mu karrama baƙin mu.Shi ya sa zan zuba miki"




Matar shi na kalla da ta kafa mana ido,plate ɗin na karɓe daga hannunshi "Ka bar shi zan zuba da kaina,ai ni na wuce ka kira ni baƙuwa Yallaɓai"




Har na kammala cin abincin ina jin idanun matar shi na yawo a jikina,duk hirar da muke yi ko ɗaya bata saka bakinta ba,ban jima ba na musu sallama kan zanje in kwanta.




"Ina gayyatar ki karin kumallo a gidana da safe"






Waigowa na yi na dube shi "To sannu masu gida,gayyata bata karɓuba" na faɗa ina ƙoƙarin shigewa ɗaki,ban daɗe da shiga ba,bacci ya ɗauke ni.




*WASHE GARI*




Tunda na yi sallah na koma bacci saboda gajiyar da nake jin har lokacin bata fita jikina ba.Na daɗe ban yi irin tafiyar nan ba,auren Lawal ya hana mini zuwa ko ina iya kata kula da shi da ɗiyanshi.




Sai ƙarfe 9 na tashi shima ba don na gaji ba,wanka na yi na zuba doguwar rigar abaya ta ban damu da shafa komai a fuskata ba saboda tun dama ni ban cika yin kwalliya ba.




Ban samu Gwaggo a ɗakin ba shi yasa na wuce bedroom ɗinta a can na same ta gaida ta nayi ta amsa tana tambayar yadda na kwana




"Tun ɗazu yayanki ke yawo nace baki tashi ba,kuma ba za a tada ki ba.Muje ki gaida Abbanku jiya ko da ya shigo kin yi bacci,sannan ki wuce ɓangarenshi tun bai dawo min neman ki ba"




Sai da muka je na gaida Abba dattijon arziki,cikin nuna ƙauna muka gaisa da shi yana tambaya ta su Safwan.




Na fito ɓangaren Abba na hangeshi tafe,murmushi na yi tare da tsayawa wurin da nake "Kin wahalda ni da yawa Zainu,tun ɗazu kin hana mu cin abinci ni da madam"




Girata ɗaya na ɗage "Na hana ku cin abincin ne? Kuma ai bance muku nayi accepting wannan IV na cin abinci ba"




Hararar wasa ya min "Wallahi ba ki isa ba,ko kina ci kina amai sai kin ci shi,baki isa ki hana matata cin abinci ba sannan kice ba za ki ci ba"




Jerawa muka yi har ɓangaren nashi yana tambaya ta makaranta ina bashi labarin yadda abin ke tafiya.




A ƙofar kitchen muka samu madam ɗin Ya Bashir da alama magana ta ke da mai aikinta,kallo ɗaya ta min ta kawadda kanta.




Ina kwana na mata tare da isa ga Zainab da ke wasa a tsakar falon,ƴar Yaya Bashir wadda ya min takwara shekarar ta 2 yanzu,bayan haihuwar Amna yayi aure,shima saida suka shekara sannan aka samu cikinta.Dariya ta shiga ɓingilamin tana min gwaranci kallon Yaya Bashir da ya zuba min ido na yi.






A bazata na ji maganar shi "Wallahi yau na ƙara ganin kamanninki da sweet heart da kullum Mama ke faɗa,kamar ke kika haifeta"




"To da wa ya haifeta? Ni na haife ki ko Zainab" kamar ta san abin da nace ta shiga ɓingilamin dariya tanawa ubanta gwaranci.




Dinning ɗin da aka shirya muka nufa ina ɗauke da Zainab abin mamaki matar gidan ma kamewa tayi a kujera tana ƙwalla kiran mai aiki ta zo tayi serving ɗinmu.




Miƙewa nayi ina cewa ta barshi ni zanyi,ita na fara zubawa sannan na zuba mishi na zuba wa kaina.Zama na yi ina ci ina baiwa Zainab da ta maƙale min kamar ta saba da ni.




Saida na kammala na tashi na koma falo tare da Zainab ina nan ya wuce sama yana cemin in jirashi ya fito.




Ganin mutum kawai na yi a kaina tana girgiza jiki kamar wadda aka kunnawa disko "Bari

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login