Showing 54001 words to 57000 words out of 57484 words

Chapter 19 - AURE DA KARATU Book Complete Rumaisa Sidi.txt

26 Jan 2025

6704

ta katse bata ɗaga ba,sake danna kiran tayi shima har ta katse ba amsa.




Bata yi sanya ba taci gaba da kira sai a kira na bakwai ta ɗaga cikin Muryar bacci ta fara magana "Haba Zubby,haba don Allah,ya kike nema ki ɗaga wa mutane hankali da kira a cikin wannan tsohon dare"




Dafe kai Zubaida tayi ƙwalla na cika mata idanuwa"Ina cikin tashin hankali Lailai, Zainab na asibiti tana labour"






"To shine me?baki yarda dani bane kome? Wallahi yau sai dai gawar Zainab ta bar asibitin nan ba dai ita ba"




Kuka Zubaida ta ɓarke da shi jikinta na ƙara ɗaukar rawa "Don girman Allah ki taimaka a kwance abin nan, wallahi na fasa,ba zan yi ba, wallahi banida ƙarfin ɗaukar hakkin kashe mutum"




Tsaki Laila ta buga "Wai duk saboda wannan ne ki ka bi kika ɗaga hankalinki?Mtssww,to akan ki aka fara wannan? Kuma ai bani na kira ki ba,ke kika kirani kika buƙaci a miki wannan aikin,to miye kuma na ɗaga min hankali cikin wannan tsohon daren"




Zaman dirshan tayi a wurin bayan Laila ta buga tsaki ta kashe wayar.Jikinta sai rawa yake,tayi danasani,tayi nadamar biyewa zuciya.




Ta jefa kanta a wannan rayuwar ne bayan da taji samuwar cikin Zainab, hankalin ta ya tashi ta rasa ina zata jefa kanta.




Shaiɗaniyar zuciyace ta ƙawata mata kiran Laila,don neman shawarar ta ba ɓata lokaci ta bata gurguwar shawara kamar yadda ta saba.




Ita ma kasancewar idanuwanta sun rufe yasa ta amince,ta tura ma Laila maƙudan kuɗaɗe, bayan kwana biyu tace mata anyi bincike aikin ba zai tafi yadda ake so ba,sai lokacin haihuwar Zainab ɗin yayi.




Hankalin ta ya ɗan kwanta jin Zainab zata tafi ta bar mata mijinta,da farko ita so tayi kawai a fitar da Zainab ɗin,amma sai Laila ta nuna mata ai zata iya dawowa.




Sai daga baya kuma abin yazo yana damunta,ta shiga ramewa a tsaye kullum tsoron ta yadda nauyin mutuwar mutum zai hau kanta.Bata ƙara ruɗewa ba sai da watan haihuwar ya kama,ta ma fi Zainab ɗin shiga tashin hankali.




Wannan ne yasa ta nemi Laila tare da sanar da ita a kwance wannan aikin ita dai ta fasa,ita kuma ta sanar da ita bazai yu a kwance ba.




Duk wani motsin Zainab ɗin tausayi take bata wannan ne yasa take bin ta da ido,tana jin ina ma zata iya da ta ɗauke cikin daga jikin Zainab ɗin ta mayar wa akan ta don ita ta mutu.




Zabura tayi da sauri tare da matsawa kusa ganin likitan ta fito,ajiyar zuciya suka sauke a tare jin likitan na sanar da su an haihu an samu ɗa namiji.




"To ya mai haihuwar"Zubaida ta faɗa da sauri,murmushi likitan ta yi "Ita ma tana lafiya komai normal In Sha Allah"




Koda aka fito da Babyn tubarkallah kyakkyawa,tun da ya shiga hannun Zubaida ta kama ta rungume.




Rungume Zainab Zubaida tayi bayan sun shiga ɗakin da take,hawaye na sauko mata,tana ƙara godewa Allah da wannan rufin asirin da yayi mata,dare da yawa ta kasa bacci saboda tunanin irin wannan rana.






Kowa mamaki yake yadda Zubaida ta zage ake hidimar biƙi da ita,ta saki jikinta sosai kamar ba ita ba,ji take da Babyn kamar nata.




Kaya masu kyau ta haɗawa jariri ta kawo mishi,ba wanda baiyi mamaki ba,Ya Bashir ma yaji daɗi sosai,wannan yasa ita ma ya yi mata kayan fitar suna masu kyau.




Ranar suna yaro ya ci sunan ABUBAKAR SADIQ,an sha hidimar suna,an ci an sha an kuma riƙa a hannu.




Su anty Halima tun kwana uku da haihuwa ta iso,da su aka yi hidimar suna,taso zuwa da Safwan amma Lawal yace ba inda zai je sai anyi hurumin dariya kawai tayi a ranta tace "kishi ne"




Zaune nake ina kallon yadda Zubaida ta zage ita a dole sai ta sakawa Sadiq pampers,dariya nake mata ganin yadda take nuna ita a dole tayi ƙoƙari.




"Wallahi nayi ƙoƙarin,dubi fa,ke dai bani kayanshi kawai"kayan na miƙa mata ina ci gaba da dariya.




Tsaf ta shirya shi koda aka gama shirin har yayi bacci,miƙo min shi tayi tare da tashi tsaye "Goya min shi ki gani"ta faɗa tana juya bayanta.




Ina ƙoƙarin tashi Ya Bashir ya shigo,harararta yayi sannan yace "Wallahi yanzu Zubaida na fahimci kin fi son Sadiq da ni,tun yaushe nace ki zo ki ɗauko min takardun da kika ajiye min amma kin ƙyaleni"






Hannunta ta ɗora a bakinta"Shiiiiiiiii,don Allah kayi magana a hankali kar ya tashi"sakin baki yayi yana kallon ta sannan ya dube ni "Muje ki duba min Zee"




Turani tayi "Yawwa je ki duba mishi don Allah"




"Zubaida ta canja Honey,yanzu kamar ba ita ba"na faɗa lokacin da nake haɗa mishi takardun.




Murmushi yayi tare da gyaɗa kanshi "Na sani Zee,nima na shaida hakan,kuma naji daɗin canja War tata,ko ba komai zaman lafiya zai samu a cikin gida na.




Rayuwar da muke yi a gidan yanzu rayuwa ce ta zaman lafiya da kyautatawa juna.




Na lura yanzu Zubaida ta canja takon kishinta,gyara take yi na musamman,ta canja har girki take yi yanzu.Wannan yasa na ƙara zage damtsen gyara nima saboda na lura yanzu ne zamu yi kishin.




Sai da muka yi arba'in nayi shirin zuwa Sokoto,tsaraba na haɗa ta musamman ta ƴan uwana da kuma ƴaƴana.




Wannan karon ni kaɗai zan tafi saboda Zubaida ta riƙe takunta,ta iya baiwa miji kula.




Nima da shirin gyara na musamman na nufi Sokoto don bazan yarda na zama borar Zubaida ba.




Mun samu tarba ta musamman Ni da Sadiq,a ranar da na sauka a ranar Safwan ya zo bayan ya dawo makaranta.




Rungume Sadiq yayi kamar ya haɗiye shi, sumbatar gashin shi yayi sannan ya dube ni "Mommy Ina ta addu'a Allah yasa ki haifi mace a saka sunan Aysha"




Murmushi nayi nima "To ai sai Maman ka ta haifo ma"ɗaure fuska yayi daga nan bai ƙara magana ba.




Mun sha ziyara,sai da na gama yawon da zan yi sannan na fara zuwa wurin gyaran jiki,gyara ake min na musamman.
















Kuyi haƙuri da wannan muna fama da matsalar wuta wayata ba caji












*RUMAISA'U SIDI*✍️✍️✍️








*AURE DA KARATU*


*NA*


*RUMAISA'U SIDI*


*FARAR ANIYA WRITERS*






*Page 40 End*






*Bayan shekara 6*




A cikin shekarun nan abubuwa da yawa sun faru,na ƙara haihuwa bayan Sadiq na haifi mace Ya Bashir ya mayar min da sunan Aysha.




Aysha ƴar gatan kowa ce a gidan,kowa ji yake da ita,hatta Safwan da ba ma gari ɗaya siyayya yake ya sako a mota yace nata ne.




Kuma ni yanzu Aysha ce kawai a hannuna Sadiq yana wurin Zubaida,tun da na haife shi duk wani raino na shi ita tayi.




Da za a yaye shi ma ita tayi,tun daga lokacin kuma bata mayar min da shi ba nima kuma ban mata magana ba,saboda tausayin da take bani na yadda ta ɗauki ƙauna ta ɗora mishi.




Duk abin da ka gani a wurinta zaka ji tana faɗin "Wannan na Sadiq ɗina ne"duk da ni gaskiya bana cikin irin kishiyoyin da za su iya kyautar ɗa,ba zan iya ba gaskiya,amma nayi alƙawarin ƙyaleshi a hannunta ba zan taɓa yi mata maganar ya dawo wurina ba.




Zubaida ma ta haihu amma abin bai zo da rai ba,daga nan kuma shiru sai yanzu da take ɗauke da ƙaramin ciki.




A ɓangaren Ya Bashir ba abin da za a ce sai alhamdulillah,buɗi ya ƙaru,an ƙara zama Alhaji,ko da nayi mishi maganar aikina kai tsaye ya nuna min a'a duk abin da nake buƙata zai min amma ina aje maganar aiki ba yanzu va.




Ya siya mana sabbin motoci,ya bamu kuɗi muyi jari,ko da ya bincike ta abin da zata yi sai tace irin sana'a ta take so,bai yi sanya ba kuma roƙe ni da na nuna wa mata yadda ake business ɗin.




Ita ma bata saka girman kai ba,muka haɗa kanmu ina nuna mata.A ɗan zaman namu na fahimci bata da girman kai duk abin da bata gane ba zata tambaya.




Ko girki ta samu ina yi da taji ƙamshin ya mata,zata same ni "Maman Aysha ya ake wannan,me kika saka yayi haka"haka zata maƙale min har sai na nuna mata,duk da wani lokacin kishi baya bari na nuna mata komai saboda ina gudun ta kwaɓe min tazo ta fini zaƙewa.




Daga ni har ita kowa ƙoƙari yake ya ciri tuta a idanuwan mijin wanda na lura hakan yana matuƙar saka shi farin ciki.Ta dage sosai sai ta ƙwaci mijin Ni kuma na nuna mata har yanzu da sauran ta.




A nawa ɓangaren ba abin da zance sai Alhamdulillah,komai yana tafiya cikin nasara,duk da ita rayuwar nan ba za a rasa ƙalubale ba,amma ina ƙara godewa Allah da Wannan canjin da ya min.




Idan na kalli ƴaƴana sai dai na ƙara hamdala saboda na san ni'ima ce,ace duk waƴannan ƴaƴan nawa ne mallaki na ne.




Ga Safwan ɗina ya zama saurayi har mamakin girman shi na keyi,tun da ya kammala secondary School mahaifinshi ya buɗe mishi shago ya saka mishi takalma na maza da na mata.




Lokacin da ya faɗa min na yi farin ciki sosai,nima kuma na siya mishi shaddodi da atamfofi na bashi nace ya saka a ciki kuma ya kawo min riba idan an sayar.




Mahaifinshi ma yaji daɗin hakan da nayi har cewa yaron ya faɗa min yana godiya.




Cikin ikon Allah sai shago ya fara haɓaka sannu-sannu,yaron yana da nasibi sosai.Bincikar shi nayi maganar karatu yace mahaifinshi yace ya kula da kasuwanci ba ya da ƙarfin kula da karatun shi har jami'a.




Jin haka yasa nace ya bincike shi in har ya amince ni zan saka shi,yace ba matsala,nan take ina daga can nayi magana da Ya Abbas aka shiga ƙoƙarin sama mishi gurbi a makaranta.




Haka yake kula da komai,zai je makarantar shi idan ya dawo kuma ya buɗe shagon shi.






*BASHIR*




A nashi ɓangaren kullum ƙara godewa Allah yake da wannan ni'imar da ya mishi ya bashi mata kamar Zainab.Saboda zai iya cewa ta dalilin shigowarta rayuwarsu Zubaida ta canja,abin da ya ɗau tsawon shekaru yana ƙoƙarin fahimtar da ita,amma kai tsaye sai gashi ta canja.




Ya sani soyayyar Zainab ta daban ce a cikin rashi,ƙaunar ta halittace da Allah ya dasa mishi wanda ba ranar gushewarta sai ranar da numfashin shi ya rabu da gangar jikinshi.Amma kuma a yanzu ita ma Zubaida tana da wani matsayi na daban a cikin zuciyarshi wanda baya fatan rasa ta ko na daƙiƙa.Yana ƙoƙarin sosai wajen kwatanta adalci a tsakaninsu,baya fatan tashi cikin masu shanyayyen ɓarin jiki kamar yadda Manzon mu Annabin rahama ya siffanta mazan da basa kwatanta adalci a tsakanin matansu.




Buɗi yake samu ko ta ina,kuma ya san wannan baya rasa nasaba da kwanciyar hankalin da yake ciki.Ɗan gata ne a wurin iyalin shi, kowa ƙoƙarin kyautata mishi ta yake.




Ga kuma ƴaƴanshi da yake jin kamar ya haɗiye su don ƙauna,yana ƙara godewa Allah duk lokacin da ya dubi yaran,ace wai waƴannan yaran nashi ne,jininshi ne sai dai yace Alhamdulillah.






*ZUBAIDA*




Duk da ba wai ta daina jin kishin Zainab ba,tana ji har yanzu amma tana ƙoƙarin danne wa da kuma addu'a kamar yadda anty Maryam ta bata shawara.Kuma har yanzu a wurin wannan matar da Anty ta haɗata da ita take siyayya.




Saboda yanzu ta daina biyewa Anty Amina ko Laila,don ta lura ba inda shawarar su zata Kaita sai Wuta.Dama ita mahaifiyar ta matsalar ta ɗaya taji an taɓa ta yanzun nan zata zo ta fara cin mutunci.To da ta fahimci hakan sai ta daina faɗa mata komai,shima Ya Bashir ɗin sai ta daina kai ƙarar shi a wurin Gwaggo.




Duk abin da take buƙata zata same shi ta roƙe shi,idan yana da hali zai yi mata ita ma Zainab ya bata,idan kuma baya da hali zai faɗa mata tayi haƙuri.




Da tayi ƙorafin yana yiwa Zainab abu alhalin ai ita ta tambaya sai ya faɗa mata hakkine.Ita ma duk lokacin da taga ya bata wani abu to Zainab ɗin ta tambaya shi yasa ya haɗe ya musu.




Allah ya ɗora mata ƙaunar Sadiq,tun da aka haifi yaron take jin ƙaunar shi ta daban.A wurinta yake wuni cin abincin shi kawai ke mai dashi wurin Zainab.




Koda lokacin yayen shi ya yi ita ta yaye shi,daga nan ne kuma taƙi mayar da shi,kuma har yau Zainab bata taɓa nuna mata ko a fuska tana takura da rashin mayar mata da ɗan ta ba.




Ko wani abun aka siyo to ita ake ba na Sadiq,ita kuma Zainab a bata na Zee da Aysha.




Har ita ke fitar da kuɗi ta siyawa Sadiq Abu amma taƙi siyawa Zee,ita kuma Zainab ganin haka sai take yiwa Zee ɗin ita ma.




Ga business ɗin da take yi,wanda Ya Bashir ya basu jari kuma da taimakon Zainab ta gane kan abin.Haka ma ta aje wani girman kai duk abin da bata gane ba zata tambayi Zainab saboda ta lura mutuniyar kirki ce,bata da mugunta duk abin da ta tambaye ta zata faɗa mata matsawar dai ta sani ba abinda zata ce yanzu sai alAlhamdulillah.




*GWAGGO*




Kwanciyar hankalin ɗan ta ya fiye mata komai,duk wanda ya gan shi a yanzu ya san ya samu kwanciyar hankali.




Ita ma ta ji daɗin sauya war Zubaida ko ba komai hankalin ɗan ta ya kwanta,ya rabu da tashin hankali.




Ga ƴarta ita ma tana gidan auren ta lafiya lau,ga jikokinta zagaye da ita.Ga kuma Zainab ɗin ta ita ma hankalin ta ta kwanta ba abin da zata ce sai Alhamdulillah.




LAWAL




To shima dai a nashi ɓangaren ci gaba yake samu ta kowa ne ɓangare.Ya ƙara faɗa ɗa shagon shi,ya mayar da shi ƙaramar plaza inda yake siyarda kayan miya da su arrish,kayan ɗanɗanon miya,taliya,shinkafa,masara da dai sauransu.




Ga matar shi Nusaiba ta canja,tun bayan da ta daki Safwan ya tura ta gida tayo hutun sati biyu aka samu salama.




Duk da dama can ba wani shiri suke da yaron ba,amma dawowar ta sai ta canja sosai.Ta kama kanta dama ita ce mai shiga harkar shi.




Kuma Allah ya albarka ce shi da haihuwa ya sami ƴa mace,Safwan ne ya raɗawa yarinyar suna A'isha.Shima ya ji daɗin sunan da yaron ya saka don dama shi ya ke da burin sakawa




Haihuwar A'isha ne yasa aka fara shiri tsakanin Nusaiba da Safwan,suka koma kamar ba su ba.Yanzu an mai da ƙofar ɗakinshi ta baya, kasancewar ya fara girma.




A cikin waɗannan shekarun kuma Lawal ya rasa mahaifiyarshi, mutuwa ta fuju'a tashi kawai aka yi aka iske ta rasu.yayi kukan mutuwar mahaifiyar shi sosai,wanda har Zainab sai da ta zo musu gaisuwa.




A yanzu yana cikin rufin asiri daidai gwargwado ba abin da ya nema ya rasa.Duk wata buƙatar iyalinshi yana ƙoƙarin tsare wa har Amna da bata hannunshi yana ƙoƙarin sauke hakkin ta da ke kanshi a yanzu ba abin da zai ce sai Alhamdulillah.




*HAFSAT*




A ɓangaren Hafsat ƙawar Zainab ma, komai na tafiya daidai mijinta yayi aure har matar ta haihu.Cikin iyawar Ubangiji ita ma ba jimawa da haihuwar matar ita ma ta samu ciki bayan wata tara ta haifo ƴan biyu mace da namiji.




Ta yi murna sosai kuma ta gode Allah da wannan ni'imar da ya mata,gashi ta ci ribar haƙurin da tayi.




Yaranta sun zama abin so ga kowa,mijinta na ƙaunar ta,bata da matsala da kishiya don ba ma gida ɗaya suke ba,ita kam ba abin da zata ce da wannan ni'imar sai Alhamdulillah.




*UMMI*




Kamar yadda muka sani burin kowa ce uwa kwanciyar hankalin ƴaƴanta,hakama farin cikin kowa ce uwa farin cikin ƴaƴanta.




Tun bayan auren Zainab da Bashir hankalin Ummi ya kwanta zuciyarta ta samu salama.Addu'ar ta kullum Allah ya ƙara basu zaman lafiya da zuri'a ta gari.




Ga ƴaƴanta maza kullum abubuwan su ƙara gaba suke saboda kyautatawar da suke mata.




Zaman Amna a tare da ita ke ɗebe mata kaɗaici, yarinyar ta girma yanzu an zama ƴan matan Jss.Amna ta riga ta zama ƴar Ummi har bata son tayi nesa da ita, kullum tana maƙale da Ummi bata ma wani kewar mahaifiyar ta.Lokaci bayan lokaci kuma tana zuwa ta gaida mahaifinta.




Ajiyar zuciya mai ƙarfi na sauke bayan na dawo daga dogon tunanin da na tafi hannuwana na ɗaga ina ƙara godewa Allah da wannan sauyin da ya min.




Juyowa nayi da sauri jin ihu Aysha abin da ya tilasta min tashi na fito "Wa ya taɓa min autah?na tambaya ina ƙoƙarin ɗagota daga faɗuwar da tayi tana turmuza jikinta a ƙasa.




"Mommy wallahi Sadiq ne ya ture ta"Zee na duba dake min bayani,raina ne ya ɓaci kusan kullum sai Sadiq ya saka Aysha kuka,rigimamme ne na ƙarshe.




A fusace na tunkari ɓangaren mahaifiyarshi ina riƙe da hannun Aysha.Yana maƙale jikin uwar tashi ita kuma tana zaune da ƙaton ciki a gaba.




Ɓoye shi tayi a bayanta alamun ta san bayada gaskiya.Nuna shi nayi cikin ƙunar rai "Wallahi idan ka ƙara dukar min ƴa sai na zane ka,na lura kai baka san ana ƙyale ka ba"




Zuro kanshi yayi tare da yin gwalo ita kuma kamar sakarya ta sa dariya,raina ne ya ƙara ɓaci abinda ya kai ga nasa hannu na fizgo shi na shiga jibgarshi.




Tureni tayi da ƙarfi sai da na kusa faɗuwa,idanuwanta suka cika da ƙwalla a fusace ta fara magana "Kin yi kaɗan ki zo har gabana ki dake shi,kuma wannan ya zama na ƙarshe da zaki ƙara dukan min yaro idan ba haka ba duk abin da na miki ke kika ja"daga haka ta kwashi ɗan ta da ƙyar ta ɗora a kafaɗa taƙui-taƙui ta wuce ɗakinta.




Ni na ma manta da anyi wata rigima kwatsam bayan dawowar Ya Bashir ya kirani yace in same shi ɓangaren shi.




Ko da naje tana tsaye sai jijjiga take kamar wadda aka kunnawa disko kallo ɗaya na mata na kawadda kaina tare da isa wurin da Ya Bashir ke zaune da murmushi a fuskata na ce "Sannu da zuwa Honey"shima murmushin yayi yana nuna min Zubaida da idanuwanshi, murmushi nayi nima bayan na dube ta.




Gyaran murya yayi sannan ya fara magana"An kawo min ƙarar ki Zainab"zaro idanuwana nayi "Ni kuma me nayi?"




Duban ta yayi "Ki zauna mana"girgiza kanta tayi sannan ta fara magana "Ba wani zama da zan yi,kawai ka jawa matarka kunne kar ta ƙara dukan min yaro,idan kuma ba haka ba wallahi Zubaidar da aka sani a baya ce zata dawo.Don ba zan ɗauki aje har cikin gidana a dukanmin yaro a gabana ba,kuma ai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login