Showing 9001 words to 12000 words out of 57484 words

Chapter 4 - AURE DA KARATU Book Complete Rumaisa Sidi.txt

26 Jan 2025

6702

itace shalelen yaya"( ku rera wakar da kanku)




Rausaya na shiga yi kamar kullum dariya suka shiga min saboda inda sabo sun saba indai yaya bashir yana sokoto to kullum muna tare ko wani gurin zaije to saidai mu tafi tare ko su yaya abbas bamuyi shakuwar da mukayi da shi ba bayan ummi da abbana shine mutum na uku da yasan sirrina kamar yanda zan nemi shawarar abba ko ummi haka zan kirashi in nemi shawararshi




Tambayarshi su yaya halima nayi dasu gwaggo yace duk suna lafiya sunce a gaisheni "ga tsarabarki can da suka baki sai na huta zan baki" kafata na shiga dokawa kamar wata karamar yarinya "nidai wallahi aba ni abina yanzu tun ba'a min danwaken zagaye ba" na fada ina kallon ya mubarak (wanda nake bi) tsaki yayi " nasan tsarabarki bata wuce chocolate ko sweet tunda har yanzu kallon kanki kike a wata jaririya wallahi malaman university ne maganinki" baki na murguda " eh naji dai ai nasan haushi kakeji saboda ba kaine auta ba kuma da kake cewa hakan ai dai nima kwanannan zan fara jami'ar nan kuma zan baku mamaki" wata harara ya bankomin " wallahi har na matsu na ganki a jami'a" wannan karon ya bashir ne ya taremin fada "mubarak sai mun baka mamaki zakaga shalele a jami'a hankali kwance tana karatunta wata rana saidai mu ganta a gidan tv tana karanto news kamar baturiya"
Tsallen murna na buga tareda riko hannunshi wata harara ummi ta bankomin abinda yasa nayi saurin sakin hannunshi tareda wucewa dakina don in rage kayan jikina inyi wanka




Ina zaune gaban mirrow ta shigo dakin wurina ta nufo tana hararata kunnena ta kama ta murde "banhanaki taba mutum ba idan kina magana ban hanaki ba?" kara na saki saboda yanda naji zafin rikon "ummi bazan kara ba" kunnen nawa ta saki "nasha gayamiki ba kyau amma kinki daunawa kedai wuyarta fira tayi dadi yanzu zaki cumuimuye mutum ko su mabarak na hanaki yiwa haka bare kuma bashir da zai iya aurenki "aurena kuma ummi" na fada ina zare ido dakin ta bari tana gayamin in fito mu shiga kitchen


Da dare kamar kullum bayan mun kammala cin abinci muka dawo falo har Abbana kusa dashi na zauna ina nuna mishi system din da nakeso ya siyamin " duk abinda kikeso zan siya miki Zainab indai zaki aje hankali kiyi karatu naso kiyi karatun likita sosai amma burina bai kai ya dakushe naki burinba shine kuskuren da iyaye ke tafkawa akan karatun yaransu yarinyarka tana sha'awar fanni kaza kai kuma kaza kakeso tofa ka sani idan har ka tursasata tabi naka ra'ayin to bazata taba maida hankali ba don ba shi takeso ba na barki kiyi ra'ayinki fatana ki maida hankali a karatunki banda kule-kulen samari ko tarkacen kawaye ki rike mutuncinki da kuma muruncin gidanku kece farincikinmu kema kinsan hakan to don Allah karki watsa mana kasa a ido" jikina naji yayi sanyi sosai bana cikin 'yan mata masu tara samari saboda a ganina hakan zai hanani cika burina abba yasha gayamin ko ina makaranta miji ya fito to za'a yi auren sai in hada biyu inyi AURE DA KARATU


Ummi ma nasihar ta shiga min kamar ance gobe zan fara zuwa jami'ar nan tana gamawa shima yaya isma'il ya dora hakama su yaya bashir kuka na saka musu ina nuna ya mubarak" yaya shima ku mishi fada wallahi baya karatu kullum saidai yasa littafi gaba yana chat da ya jiku tafe ya aje waya" harara ta ya shiga yi " wa zaki yiwa sharri? kedai in kinsan bazaki iya karatunnan ba ki fada kar ayi hasarar na man mota" kuka nasa ina daddaga kafafuna kasa lallashina yaya bashir ya shiga yi yanawa ya muby fada abba na dariya


Abin mamaki koda nazo kwanciya sai tunanin bawan Allah nan ya hanamin bacci ya iya tsara zance daga yanda yake fitarda kowace kalma cikin tattausan lafazi juyi na shiga yi da mamakin wannan sabon al'amarin da ya sameni tunanin wani namiji bai taba hanamin bacci ba saboda koda munyi magana da kai nan gurin zan barta bana sakawa raina barema abin ya dameni amma wannan mak'ale-matan ya hamin sukuni




Jin wayata tayi kara alamar shigowar sako yasa na mika hannu akan bedside drower ta na janyo wayar zaune na tashi ganin sakon da ya shigo wayata "Barka da dare Beauty na fatan kin isa gida lafiya a yau zanyi bacci da wayata akan kirjina saboda number mai daraja da wayar ke dauke da ita mu kwana lafiya kiyi bacci cikin aminci"




Sakon na shiga maimaita karantawa kamar wata hadda tabbas mutuminnan ne na dazu gurinshi kadai na taba jin kalamai irin wayannan wayar na rike ina kara kallon sakon daga nan wani bacci mai dadi ya daukeni sai asuba da naji ummi na tadani tareda yimin fadan kwanciya da waya ina kan dadduma ina azkar bayan kammala sallar asuba naji shigowar sako "MAYE" na fada a raina ganin yanzu ma number jiya ce "Barka da asuba Beauty fatan kin tashi lafiya Allah yasa haka Amin kar ki manta nima kimin addu'a sako daga MAYENKI" murmushine ya subuceminn "sai maye kam" na fada ina nade dardumata tareda komawa kan gado na gyra kwanciyata


















HMMMMM✍️✍️✍️✍️✍️


AURE DA KARATU
NA
RUMAISA SIDI






Page 9








A bun sai ya zama kamar ibada kullum zai min text da safe da rana hakama da dare amma bai taba gwada kirana ba nima bantaba yunkurin yi mishi reply ba duk da abin ya riga ya zamemin jiki kullum na saba da karanta shi kuma kullum da kalar kalaman da zai turomin


Yau haka na ke aiki ba k'wari saboda rashin ganin sakon MAYENA kamar yanda na radamishi suna na riga na saba da shi yau sai naji daban girkin kawai nakeyi amma hankalina sam ba ya wurin na damu sosai na rashin jinshi ashe haka na shaku da sakonshi


"Lafiyarki kalau kuwa zainab" naji ummi ta daka min tsawar da ta sa na dawo hayyacina "dubi abinda kike yi" ta nunamin abinda nakeyi sanwar miya zanyi ashe na cika tukunya har ga baki


Bakina na dafe ina kallonta "wallahi ban lura bane ummi" tsaki ta buga "ya za'ai ki lura? na dade da lura akwai abinda kike boyemin ki gayamin meke damunki" murmushin yake na mata "ummi dagaske ba abinda ke damuna" hanya ta nunamin "fice bani guri inyi girki na" hakuri na shiga bata sannan ta kyaleni muka dora sabuwar sanwa


Har muka doshi kwana uku ba sakon MAYENA har wani daci-daci nakeji a bakina kamar wacca tayi zazzabi a daren ranar ne na kasa hankuri zuciyata nakeji kamar zata buga wayata na dauko na shiga laluben numbershi da nayi saving da sunan da na rada mishi


Jinai kamar na samu baturiyar da ke gayamin wayarshi a kashe take na makure mata wuya tunani na shiga yi "to idan ya daga me zance mishi? ince na daina ganin text dinshi ko me? ko ince nayi kewarshi? kaii inaaaaa" wayar na aje tareda kokarin yaki da abinda zuciyata ke sakani


Kawadda tunaninshi nayi kokarin yi daga raina naci gaba da harkokin gabana da kuma shirye-shiryen makaranta ta da nida yaya bashir muke komai kamar wata baby zata je boarding school haka mukayo siyayyar uwayen kayan biscuit sweet dasu chocolate ya gama kwanakinda zaiyi lokacin komawarshi yayi rigima na samishi " nidai wallahi ya bashir bangaji da ganinka ba don Allah ka dawo garinnan gaba daya ni banson komawarnan taka" ido ya zubamin yana kallona " dagaske kike shalele? dagaske bakyaso na koma? indai har hakan kikeso wallahi zan nemi transfer in dawo nan" washe baki nayi ina murna " wallahi inaso" hannuwanshi ya watsa "angama shalele" murna na dingayi


Sai dare bayan munkare cin abinci ya sami abba da maganar fada ya dinga mishi wanda wani na fahimta wani ban fahimta ba "Wannan ai shashanci ne saboda tace kayi abu sai kace zakayi? ita yarinyarce zata gayama abinda za kayi to hakan za'ayi zaman ita ke bada umarni kenan ba haka nakeson ganinka a gidanka ba tsayayye nakeso na ganka shiriritarku ni ta isheni hakan nan kusa zanyi maganinku" wannan ne ya dakatarda ya bashir da dawowa sokoto




Na fara karatuna cikin aminci a USMANU DAN FODIO UNIVERSITY da motata nake zuwa duk da yaya abbas yaso ya hanani tuki yace a hadani da driver amma na tubure na ce ni zan iya karatu nakeyi amma har yanzu wannan mutumin yananan makale a cikin zuciyata har yau na kasa goge sakonninshi dake cikin wayata kusan kullum sai na maimaita karantasu kamar wata hadda


A hanyata ta komawa gida motata ta tsaya fitowa nayi gashi wurinda nake ba mutane ko ina tsit wayata na dauko na shiga kokarin kiran ummi cikin shagwaba na fara magana jin ta daga " ummi gani nan a hanya motata ta tsaya kuma ko ina tsit ba mutane"


"Gashi ba kowa a gidan ko driver sun fita da su Antynki Nasma bari in kira bakaniken yazo inda kike ya duba motar ke kuma kisamu ko napep ki dawo gida zamanki a irin wurarennan hadarine" tsoro na rikaji nima ina kallon gabas da yamma ina nema inga napep


Sai can ga bakaniken ya iso barmishi key din nayi idan ya kare ya kaimin gida na dawo dubin napep can na hangeta tafe taro na shiga yi cikin iyawar ubangiji ya tsaya "malam Arkilla za........."maganar ta makale a bakina ganin yanda shima yayi saurin dagowa yana kallona "Shine wallahi shine" na shiga nanatawa a raina dakewa nayi na karasa maganata " Arkilla zaka kaini" shima kawadda kai yayi " bismillah to" shiga nayi ya fara tuki a hankali mun danyi nisa naga ya tsaya kifa kanshi yayi akan keken sai can ya dago batare da ya kalleni ba ya fara magana " Na dauka zan iya na dauka zan saba ashe bazan iya ba na ga kamar ina takura ki tunda na hadu dake bankara bacci cikin kwanciyar hankali ba ranar da na ganki hankalina bai kwanta ba saida na koma wurin taron nabi duk hanyar da zanbi na samu number ki naci gaba da neman soyayyarki ina kaunar jin muryarki amma bana fatan hakan ya zama abinda zai bata ranki shiyasa na zabi na tura miki text da fatan watarana ki kulani kwatsam mahaifina ya rasu a wurin makokin aka dauke 'yar wayar ban san kuma inda zan kara samun number ki ba kullum fatana ina zan kara haduwa dake" juyowa yayi yana kallona " Ina sonki zainab wallahi ina sonki saidai naga kamar abinda nakeso bazai samu ba saboda ta kowane bangare kinfi karfina zainab"


Abin mamaki sai nasamu kaina da cewa "dama mace tana fin karfin namiji" zama ya gyara "sosai ma kuwa" sai a sannan na fahimci bada kaina da nayi kallon wayata nayi " muje please ina bukatar isa gida da wuri" murmushi yamin wanda ya dakarmin zuciya "angama ranki ya dade"


Sai kofar gidan yayi parking ina kokarin fita maganarshi ta dakatarda ni "Am Zee don Allah inaso idan ba damuwa mu samu lokaci muyi magana" hmmmmm abin takaici ban musaba " Kasameni a UDUS gobe karfe 12:00"


"An gama ranki ya dade nagode sosai" kudi na zaro masu yawa bansan ko nawa bane na mika mishi girgiza kanshi yayi "Allah kiyaye ko karen gidanku na dakko bazan karbi kudinshi ba bare kuma ke" ganin zamu tsaya bata lokaci yasa na aje mishi kudin tare da shigewa gida bana son haka sam alakarmu daban sana'arshi daban kuma ni har yanzu ma ban gama tantance abinda ke tsakanina dashi ba Yinin ranar har dare ina cikin walwala ta musamman


Washe gari da zanje makaranta sai na samu kaina da tsayawa zaben kayan da zansa inje makarantar daga karshe bakar abayata data sha adon stones na dauko saiko na fito fes dani ankare nake da agogo sai 12 muka gama lectures can na hangoshi zaune cikin napep kafafunshi da jikinshi suna waje Hafsat kwasare na kalla "ina zuwa hafsat nayi bako ne" baki ta dafe "Ahhh lallai wannan wane handsome ne mai wannan babbar sa'ar bantaba jin ko ganinki tare da wani ba" dube-dube ta shiga yi tareda riko hannuna "wai ina yake? ko tsoron amiki snatching kike" nuna mata shi nayi "kinganshi can kuma nifa bance miki saurayina bane kawai nace miki bako nane" fara'ar fuskarta ta bace "Aiko shi akayi kenan har na fara murna" dariya ma ta bani takawa na shigayi na isa wurinshi da isata ya mike tsaye yana kallona da murmushi a fuskarshi "barka da isowa gimbiyar mafa" murmushi na mishi nima "barka dai mu dan isa can ko" na nuna mishi wurin zama


"Sunana Lawal muhammad kuma ni haifaffen garinnan ne maganar gaskiya tunda na ganki Allah ya dasamin kaunarki a raina sai kuma nake ganin kamar abin bazai yuba saboda ni dan talaka ne zainab a halin yanzu mahaifina ya rasu kuma ni kadaine namiji a gidanmu 'yan uwana duk matane kuma ni ke dauke da nauyinmu gashi banyi wani dogon karatu ba bare ince zan nemi aiki daga secondry na tsaya wannan keken ma ba tawa bace hayarta nakeyi shiyasa nake ganin kamar tarayyarmu bazata yuba saboda ke kam sam baki saba da wahala ba"


Wani irin tausayinshi ne ya lullubeni "saboda kana talaka kake tunanin bazaka sameni ba ko kuma saboda bazaka iya yakin neman soyayyata ba?" murmushi yayi "zan iya gimbiya indai har kin bani dama wallahi zan iya" mikewa nayi ina gyara gyalen abayar da ke kaina "Allah yaba mai rabo sa'a"


Aiko daga lokacin lawal ya dunga balbalemin zuciyata ya hanamin sukuni da zazzafan kalamanshi da suka sa nakejin zan iya komai a kanshi soyayyata da lawal ta canjamin rayuwa sosai ada duk abinda zanyi to zanyi shine da sanin Ummi amma a yanzu wani abun kafin ma ummi taji lawal yaji sannan ada can baya duk wanda zai hadu da ni to saidai mu hadu a gidanmu amma sabanin lawal da har yanzu bai taba shigowa gidanmu ba duk haduwar da za muyi saidai makaranta


Babban kuskuren da na fara yi shine gwada siyawa lawal sutura domin shima ya rabuda wayannan kayan da yake sakawa kullum duk dan abinda nasan zai bukata ina siya in bashi batare da nayi duba da shi ya dace ya kyautatamin tunda nake dashi bantaba sanin wata kyauta ta hadani dashi ba kuma bantaba damuwa ba don ba shine gabana ba


Kwatsam mai gidan lawal ya karbe napep dinshi bansan abinda ya hadasu ba amma lawal ya gayamin bazai koma wurinshi karbar napep din ba ya shiga damuwa sosai saboda da ita ya dogara da ita yake ciyadda 'yan uwanshi da mahaifiyarshi nima na shiga damuwa da tunanin hanyar da zanbi in taimaka mishi don bazan juri ganinshi a wannan halin ba


















Soyayya ruwan.............🤔














Comment & share pls🙏


AURE DA KARATU
NA
RUMAISA SIDI






Page 10






Numfasawa nayi tareda duban maman haidar da ta kashe kunne tana saurarona "kinsan wani abu wai " kanta ta girgizamin alamun labarin ya fara tafiya da ita numfashi na kara ja


" daya daga cikin sarkar gwal dina na dauka batare da kowa ya sani ba saboda a dakin ummi suke can take a jiyar su na lallaba na dauko saboda nasan idan na tunkari Abba ko su yaya da bukatar manyan kudi za su tuhume ni ne kawai ni kuma a yanzu ban shirya bayyanarda lawal gidanmu ba nafison sai ya dawo hayyacinshi yanda ba zai samu wata matsala ba


Lokacin da na bashi sarkar fada ya dingamin tareda nuna min shi bazai karbi abina ya siyar ba nikuma kamar sakarya na shiga lallabashi harda kukana ina rokon ya karba indai har dagaske yana sona dakyar ya karba da sharadin bashi ne zaiyi kokari ya biya ni nace na yarda (hmmmm har yau ba'a biyani ba)


Kaitsaye hafsat ta nuna rashin goyon bayanta akan soyayyarmu tareda min barazanar zata samu ummi ta gayamata ba karatu nakeyi ba soyayya nakeyi aiko ba karya ta fada ba don a yanzu ba yaren da nake ganewa idan ba yaren lawal ba " haba zee da ajinki da komai ki tsaya kina kula wannan ? me na sama yaci bare ya jefowa na kasa ko haka zaku zauna abinki ya kare akanshi kullum yazo ko kunya bayaji shi bai kawo miki komai ba amma idan kika siyo abu kika bashi yana iyayi zai karbe haba zee wallahi jira kawai nake yaya abbas ya dawo daga tafiyar nan da yayi ya dawo makarantar nan in gani shin zaki cigaba da abinda kikeyi wallahi baki dace da wannan kazamin ba"


Wani irin zafi kalaman hafsat suka min domin zan jure ta zageni ta gayamin duk abinda zata gayamin amma bazan juri ta aibanta NISFUL-HAYAT a gabana ba "ya isheki malama cin fuskar ya isa haka" na fada cikin hargowa ina kara matsawa kusa da ita "Ke kin isa ki gayamin yanda zanyi rayuwata ko ke zaki gayamin wanda ya dace na kula? tun farkon tarayyata da bawan Allah nan baki taba furta alkhairi akansa ba kuma da kike kiranshi talaka a haka nakeson abina kuma a haka naji zan iya zama dashi kije kiyi rayuwarki yanda kike bukata nima nayi tawa period" na fada tare da zarar jakata nafice daga makarantar tareda jin haushin hafsat sosai duk da kawatace tun a secondary kuma duk abinda zanyi taga bai dace ba zata bani shawara na gyara amma yau sai na kasa duba abinda take kokarin nuna min




Tsaye nake a gaban madubi ina kallon kaina so nake na hango kyawun da kullum lawal ke kiran inada shi nasan ni kyakkyawace duk da kasancewata wankan darza amma ni kyakkyawace kuma inajin hakan a gurin mutane musamman ya bashir to amma yanda lawal din ke fada ya banbanta da saura hirar mu na tuna ta dazun " wallahi my zee tunda nake kallon fina-finai daga bakar fata

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login